4
by @nanadiso10
RUDIN ZUCIYA
NA NANA DISO
PAGE 4
Nazo naja maka kunne ne, Rayuwata ba rayuwarka ba billahilazi kak'ara samun Babana akan maganar bana zuwa makaranta sai nace masa Fyade kak'eso kayimin shine kake ta k'okarin bibiyata. Gumi ne lokaci daya yarufe Ustaz Auwal, mafarki yak'eyi k'okuma k'unnen sa ne baiji masa daidai ba? Innalilahi wainna illahirrajiun shine kalmar da yadinga ambata, Surayya? Surayya danAllah kicemin mafarki nakeyi, innalilahi wainna illahirrajiun yaa hayyu yaa qayyum." Kaga Ustaz dan mai tuwo da miya wannan shine warning din da zanyi maka Na karshe akan rayuwata kuma maganar wai aure tsakani na dakai daga yau babu kamaje ka janye don nafi karfin d'an mai tuwo da miya matsiyaci jinin tsiya" sannan ta fita daga office din tana mai jan tsaki. Gaba daya fuskarsa ya canza ta koma kalar abun tsoro duk tayi ja, Anya ba aljanu suka shiga Surayya ba? Kai subhnallahi wallahi ba Surayya bace ba wannan tabbas ba'ita bace ba, A'a to ko aljanun ne? To tayaya haka zai faru innalilahi wainna illahirrajiun wani irin bakar ranace wannan wacce iriyar Rudin Zuciya tashiga hasbunallahu shine kalmar dayake ta ambata, yarinyar da bata taba tsayawa a tsaye yarinyar da'ita ce ameera acikin makarantar nan yarinyar da yana tunanin babu dalibin da yakaita k'okari da fahimta tabbas dole yaje gurin malam bayan yatashi daliban sa.
***************
Tunda suka sauka a kasar London gaba daya bakin Ahmad yakasa rufuwa, tararsu akazo akayi sannan aka nufi wata unguwa dasu gidaje ne masu kyau amma basuda girma wani bature ya bude musu yace nan ne inda zasu zauna ba acikin makaranta ba, Sannan ya nuna wasu maza biyu mubarak da muktar yace musu wannan shine Ahmad. Kallon Ahmad sukayi suna masu k'are masa kallo yaro kyakyawa gashi dogo Amma kuma ba fari bani ba, Amma kana kallonsa kasan wahala ce tasashi yayi duhu,kana kallonsa kasan bazaifi sa'ansu ba, amma shi yanada irin manyan gabban nan na girma, ga idanu da hanci MashaaAllah ga wushirya da takara fito da kyawunsa, kana ganin kasan jinin shuwa ne ko fulani don Ga tsantsar kyau nan yafito. Saurin basu hannu Ahmad yayi yana fadin " barkanku". Sunji dadin kulasu da yayi sosai din sunyi tunanin irin masu girman kan nan ne haka suka shiga gidan dakuna biyu ne sai kitchen acikin palour sai bandaki biyu da filin gida bayan wannan babu wani daki acikin Gidan Amma gidan MashaaAllah suna shiga suka tarar da wani da shima bazaifi sa'ansu ba zaune kan kujera yana zugar shisha, lokaci daya ran Ahmad yafara jagulewa sai kuma yaji karatun ya fita ak'ansa har zaiyi magana sai kuma ya tuna da maganar yayansa Umar da yake fada masa " Zakaga abubuwan mamaki da tsoro sosai mutane ma banbanta, tarbiya kala kala haka kuma addini mai yanayi yanayi, wani gashi musulmai amma duk wasu kaba'ir yanayi, idan kana k'allon irin mutanen bazaka samu nasara ba Amma idan kana kallon mutanen kirki to tabbas zaka samu manyan nasarori, ba kowa ake gyarawa kuskurensa lok'aci daya ba dayawa basusan ba daidai sukeyi ba dayawa kuma babu yadda zasuyi da jarabawar su, Ahmad ka hango mutanen kirki arayuwarka ka hango wanda suka bar tahiri mai sai ka fuskanci nasara a rayuwark'a. mukhtar da mubarak ne sukace kai abokin mu kace har kazauka da zafinka? Dan matashin ne ya dago kansa yace " Ai ku nake jira maza" " Nifa da man jira nakeyi insamu tallafin nan in zabga tsiyata fitina sai wacce naga dama cewar mubarak " muktar ne yace" kai mutane na ai ni daman jira nakeyi in bar su old man inzo nan inje gidan giya in shana da mata in tsula tsiya wallahi babanmu harda kuka wai danAllah kasani farin ciki hahaha " Ali ne ya ajiye shishar hannunsa yace " Su old man ansha kuka yadda yakamata kam, Ni kunsan mamata tasamar min da kyar fa harda cewa wai inyi aiki innazo bayan karatu nace mata zanyi mana yanzu dai ku karasa ciki ku huta mutafi club, kallon Ahmad yayi yace " Abokina ya kayi shiru bakace k'omai ba?" Da ido kawai Ahmad da jikinsa yayi Sanyi yabisu sannan yashiga dak'in kayansa yashiga jirawa sannan yashiga bandaki yayi wanka yayi sallah abun duniya gaba daya ya'isheshi yanzu ma yakejin kewar gida Allah sarki iyaye yanzu duk k'okarin da sukayi masu Ace sakayyar da zasuyi musu kenan? Allah yashirya shine abunda yafada sannan ya kwanta, ko alamun sallah baiga suna kokarin yiba sai ma kida da suka ware acik'in gidan.
************
Tunda yafara zuwa makaranta sai yazaman bashida lokaci sosai dan daga makarantar yakan huce gurin aikin mak'ani kancinsa baya dawowa sai dare yau ma yayi sallama hannunsa dauke da nama da kayan miya. " Sannu da zuwa Umaru" karaso wa yayi cikin dak'in yace " Sannu da gida mama ya yau banga alamun alala ba? " Shiru mama tayi sai daga baya tace " Jiki da jini Umaru in dan hutawa ne" Tunda yaji lafazin yasan mama tabawa na baba kudin data Tara domin yak'ara jan jarinsa. Hannu yasa ya dakko kud'in cikin aljihunsa ya mik'awa mama yace " Dubu goma ne kyakara jan jarin daman kaya zan siya inkara Amma yanzu bukatarki tafi tawa." " Allah yayi muku albarka .... bata karasa ba akace " Ina kike tsinanniya? An asurcemun d'a yanzu har jik'ana yatafi amma babu....
MORE COMMET MORE TYPING.