RUDIN ZUCIYA

6

by @nanadiso10

RUDIN ZUCIYA


NA NANA DISO





WANNAN PAGE DIN NAKI NE KE DAYA HAJIYA AISHA INA GODIYA DA COMMENT DINKI DA KUMA ADDU'A.



Saurin Rungume Ahmad tayi tana Mai k'ara nifo da fuskarta kusa da fuskarshi lumshi idanu takeyi tana faman cije lips dinta, lokaci daya taji ya kwanta mata, irin wannan mazan takeso. Ihun da maza da matan dakin suka shiga yi suna fadin " Yauwa pretty jawomana hank'alin sa " wani nauyi kanta yak'arayi hakan yasata saurin wura masa iska a fuskarsa tana wani jan numfashi, bata idda karasawa ba taji an wanketa da mari yana k'okarin kara marinta tayi saurin ja da baya tana dafe fuskarta, da hannu Ahmad ya nuna ta yace " Ni zakizowa da halin dabbobi? Mahaukaciya mara kamin kai bakyajin tausayin iyayenki da suka turoki? Bakisan ni ba bakisan koni wanene ba shine zakizo kina rungumeni! Wannan shine na farko na karshe wallahi mukhtar kukakara kawo mata gidannan ina tabbatar muku sai nayi sanadin barinku wannan gari, marasa tsoron Allah da basa tausayin k'an su, ku da kuke mata kune kuke bada kanku sai anyi maganar miji nagari kune masu cewa amin alhali ko tsoron Allah bakudashi bama kwajin kunyar Allah gurin sabon nashi to wazakuji tsoro? Duk Rudin Zuciya yashigeku, Allah yaganar dani daku." Sosai jikin kowa yayi sanyi dan su a tunanin su Ahmad dan gidan wani shahararren mai kudin ne,Ali ne yaja shishar kusa dashi sannan yace kutashi mufita, kuma kaima wallahi wallahi indai ina numfashi sai kayi joining cikin wannan group din namu shine lafazin Ali kafin subar gidan. Tunda Ahmad yashiga bandaki yakasa koda cire kaya gaba daya tsigar jikinsa ce ke tashi wani zazzabi yana k'okarin rufeshi, Tabbas yana tsoron Allah yana kuma gudun Rudin zuciya da tuni yashiga wannan group din abokanan nasa, wanka yayi sannan yafito, cikin yadi mai laushi yashirya yatafi gurin masu gyaran da zai dinga tayawa.


Pretty ce kusa da Ali tana faman k'uka sosai tace " Ali do something wallahi inason Ahmad, danAllah kayi wani abun." " Pretty stop crying kinji indai ni sunana haidar to tabbas nayi miki alkawarin kasancewa da Ahmad ina tabbatar miki Ahmad har ciki sai yayi miki." Wani smiling tashiga yi tana goge hawayen fuskarta " Are you serious Ali?" " More than serious baby." Rungumeshi tayi tana fadin" 1 night for only you."


Bakaramin wahala Ahmad yasha ba acikin makaranta saboda yanayin turancin su wai ahaka shi yayi ma makarantar private shine ma yake zuwar masa da sauki, daga lokaci sai yazamana yanajin wahalar karatun ga kuma aikin makanikanci da yake zuwa gashi kwata kwata gurin basuda yarda duk k'okarin ogan sa sai ya gwasale da ya fahimci musulmi ne basaso sai yaja baya sosai da shigemusu yazamana da yagama aikinsa yake tafiya, bak'aramin fada sukeyi dasu Ali ba akan kayan mayi, hakama pretty yazamana kusan kullum tana cik'in gidan,watarana yana fitowa daga bandaki ta fado dak'in ranar ba karamin mari tasha a gurinsa ba, sosai zazzabi ya rufe Ahmad wanda sai da akaje asubuti haka rayuwa tacigaba da tafiya dai yau dadi gobe akasin hak'a.


***********


Yanzu malam haka gidanka ya lallace Amma baka sanar min ba? Ko da yake kausar tacemin kana tsoron surayyan dan bakayi mata fada ma, amma mu uku Allah yasa kaka fulani ta haifa ai ko bakaje birni kasanarwa da yaya ba ai kazo ni kasanarmini tunda cikin kauyen nan nake, To yanzu innar kausar ina Surayyan take, itadai inna nata ido gana daya bata iya cewa komai haka shima malam din, kawu ne ya jijjiga k'ansa cike da mamaki wato duk shirmwn kausar da yake gani yarinyar tanada hank'ali kenan, kausar dake gefen malam ce tace " kawu tafi wata 7 bata gidannan " gyara zama kawu yayi yana mai kara sauraron kausar din yace " wata hudu kikace fa?" " Wallahi kawu da takan dan lekomu koda atsaitsaye ne Amma yanzu ko zuwan ma batayi," " Innalilahi wainna illahirrajiun inbanda abunda naji ana fada a kauyen nan bazan taba yarda surayya zata zama haka ba gaba daya bana tunanin surayya tayi shekara ashirin acikin duniyar nan, yanzu ke kausar kinsan inda tatafi? Ko kuma kinji labarin inda akace ana ganinta?" " Eh kawun ya mudin mai unguwa yacemin wai yana ganinta acik'in kasuwa tana yin rawar gala kuma ya tabbatar min ma yau in inason ganinta naje karfe 5 na yamma yau ita zatayi " wani sabon hawaye ne ya wanke fuskar kawu wai surayya? Innalilahi wainna illahirrajiun, tabbas shiriya ba ahannun kowa take ba bazai manta wasu shekaru baya ba lokacin da inna tashiga tafita sai da ta kalawa diyarsa asiya sharri akan taka masu suna zina da almajirinsa alhali bahaka bani ba, haka tadinga yawo sako da lungu tana la'antar asiya da almajirinsa, har tana ikrarin ban bata tarbiya baniba yau gashi mafi nutsuwa acikin zuriar su tafada cikin Rudin zuciya da kaddarar rayuwa jarabawa mai tabo da bazata taba goguwa ba. Muryan kausar ce ta katseshi daga dogon nazarin da yak'eyi " Kawu nakira yan hizba yau zasuje su kamo mana ita." " Allah yayi miki albarka kausar bari natsaya har su k'araso sai muje tare". " DanAllah kawu kasa baki malam ya aura mata ustaz auwal wallahi shine ma yakira 'yan hizban" malam tunda ya sunk'uyar da kansa baya iya cewa k'omai yanzu ne ma yakejin zafin abun a hank'ali yace " ibrahim wallahi tsoron Surayya nakeji Aduk lok'acin da nake kokarin yimata fada wani sa'in har...sai kuma yafashe da kuka sosai." Kawu ne yayi shiru na wani lok'acin wannan ya tabbatar masa da Surayya ta rufe bak'in iyayen nata ne Amma yasan me zaiyi inshaaAllah. Haka kuwa ya zauna har karfe biyar Ustaz auwal yazo shida yan hizbah da motarsu shi k'ansa yarasa kalar kaunar da yak'eyiwa surayya dan har yanzu bai yarda cewar ba aljanu ne suke damunta ba, haka kuwa suna shiga cikin kasuwa bangaren karuwai tsakiyar filin gala sai ga surayya da wata arniyar riga tana tsaye kenan zata fara sai yan hizbah suka saka kai ai kafin kace k'omai kowa yasa gudu itama har tasaka gudu taku biyu kawu ya kamota yana kifa mata mari, har suka karaso gida bai dai na duk'anta ba malam fitama yayi dan tsoron surayyan yakeji, duk irin duk'a da marin da kawu ibrahim yakeyi baisa surayya tayi shiru ba sai am k'allon inna datayi tace " Haba inna yaya ina tsakiyar filin gala zaki ce a dakko ni? Yanzu duk girgije girgijen da zanyi ya huce ni? Kai gaskiya tsohuwa kina takuramin gwarama ki hutu na huta da wannan saka idon, muna cikin duniyar free world, sosai inna tasa kuka tace " yanzu saboda Allah shaye shaye kikeyi surayya innalilahi surayya? " " dole na caza kaina dole na hau network in zuka in yar inyi yadda nakeso ko zakisha?" Kausar ce tasaka kuka tace "danAllah yaya kibari kidaina danAllah yaya wallahi bahaka kike ba yayata mai tsoron Allah mai addini mai son gaskiya mai bin dok'okin Allah." Kawu shima yakasa cigaba da dukanta dan duk yadda yayi tunanin abun yafi k'arfinsa. Dan haka yacewa inna suyi tayi mata Addu'a shima da safe zai kawo mata rubutu, haka kuwa akayi malam cikin dare ya hau jibgar surayya babu yadda su inna basuyi ba ak'an yabari amma ina zuciya tajashi sai da ya wadi agurin sannan ya k'yaleta. Da safe kuwa babu wanda ta kula sai datayi wanda kausar ta kawo mata abun kari sannan tafito ta samu kawu da malam da inna tace " DanAllah danAnnabi kuyafemin bazan kuma ba tabbas nasan nashiga Rudin Zuciya amma yanzu ban kumawa." Inna harda dan kukanta akan cewa asiri akayiwa yarta taja surayya tana bata baki haka suka hadu akayi mata fada. Sai da ta kintatayi karfe 4 daidai tacewa bintu ta k'araso ta shirya haka ta ajiye musu takarda tayi gaba. Kausar itace tafara ganin takardar ta fito da sauri ta kaiwa malam tana kuka budewa yayi sannan yafara karantawa " Tabbas nasan ku iyaye na gari ne Amma kuma ni ban kasance diya ta gari ba, kuyi hakuri natafi tafiya ta har abada zanje bariki zanyi bariki zan samu kud'i idan natara zan waiwayo gareku diyarku na bukatar addu'ar ku." Kuka malam da inna suke kausar ma takasa fadin komai. Tun daga wannan ranar ko labarinta basu karaji ba.


******


Tunda Ahmad yafara turo kudi gaba daya sai Umar yadaina gane kan mahaifiyarsa duk tafara canza tabbas ko naira daya umar ke da ita sai yayi musu hidima da ita, yau ma haka yasiyo buhun shinkafa da mai yana kawowa mama tace " Yanzu umaru babu Maggi babu taliya? Sai shinkafa ai kayimana mix ko? Bakaga dan uwanka dubu dari dari biyu yake turowa dashi ba ai kaima kayi k'okari gurin samun lada ko" Gabansa ne ya wadi gaba daya yaji babu dadi wannan kudin aikinsa ne nakusan sati 3 ya tara domin asiya abinci Amma hakan baiyiwa mahaifiyarsu ba cikin sanyin Hali irin nasa yace " Kiyi hak'uri mama inshaaAllah inasamun kudi zansiyo taliyar." "To ba laifi shine lafazin mahaifiyar nasu, amma da sai ta tayi masa addu'a. "


_____________________


Kwanaki na tafiya haka satika suna komawa watanne shekaru suna ja yau kusan shekara uku kenan da fara k'aratun Ahmad cikin taimakon Allah yacanza gaba daya yayi kyau ga wata kasumba da yatara, yayi fresh, Yau ma kamar kullum yanata aikin project acikin system wayarsa ce tayi ringing hakan yasa shi saurin dagawa yana murmushi handsfree yasa duk da su Ali dasuke cik'in palour din hakan baisashi jin dar ba. Cikin fara'a da muryar Murna yace " Allah yaja ran mamata dafatan kina lafiya kina sumul keda Alhaji baba" " Dan albarka munanan kalou wallahi ya karatun? Anadai mai da hankali ko? " " Mamata karatu babu dadi yazo karshe inshaaAllah" " To Nidai nama rasa bakin yimaka godiya Ahmadu ubangiji yayi maka albarka jiyama ka turo da kud'i Allah yarabaka da duniya lafiya kaji Allah yatsaremin ku kai da dan'uwanka." " Mama in kinamin godiya banajin dadi wallahi tsakani na daku dole ne ba Alfarma ba nidai kiyita yimin addu'a nida yayana" Addu'a ai dole nayi maka Ahmadu yanzu dai bari na barka Allah yataimaka Ameen yace mata sannan yakashe wayar. Zuciyar Ali ke faman tafasa a komai Ahmad yafisu, tundaga kyan hali kokari gashi nan ma bangaren iyayensa, don shi mukhtar ma jiya da babansa yakirasa kin dagawa yayi.


*************


Surry what are you saying ne? Why can't you stop this? Dubu dari 3 Nabaki yanzu Amma you're saying sunyi kadan why surry I really need you please." Tsaki tayi tana gyara glass din fuskarta tana tauna chew gum tace " Badoo Am not repeating myself again in zaka bani 1m to that's okay if not I think am going?" Zaro idanu yayi yana k'allonta shi bai taba tunanin yarinyar ta waye haka ba shiyasa ma yace mata 300k Amma ashe idonta abude yake. K'okarin mikewa tayi tana gyara wayar hannunta " Duk uban kudin dakaci gurin gomna shine zaka raina min hank'ali?" Lok'acin daya yayi dariya yana tuna aikin bokansa dayasa akan indai yakawo pant din macce tabbas zai samu kwangilar da yake nema, " Surryta zama baki 2million ." Jiyowa tayi with suprise tace really??" Kashe mata ido yayi yace " very sure baby come on...."