RUDIN ZUCIYA

7

by @nanadiso10

RUDIN ZUCIYA


  NA NANA DISO



PAGE 7


Jiyowa tayi with suprise tace "really?"  "Very sure baby come on, my surry change my mood please."


 Kallonsa tayi daga Sama har kasa sai tayi fari da idonta, " you don't make the transfer and kana cewa inyi canjin mood dinka?"  wayarsa ya lalubo daga kwancen da yak'e sannan ya shiga cikin app na transfer, cikin mintin da bazai haura uku ba taji alert yashiga.  Murmushi tayi sannan tasa ihu tana fad'in My badoo sai kayi gomna da yardar Allah." wangale baki yayi yace " Allah ya yarda surry baby". Tana kok'arin bude Baki takarayin wata maganar yayi maza gurin jan hannun ta suka fada duniyar masha'arsu. Bayan wasu awannin tana kwance zuciyar ta cike da farin ciki dan wannan kudin tayi dashi zataje ta karasa ginin da takeyi, kafafuwan ta ta sakko dasu daga gadon tana mai bin jikinta da kallo ita kanta tasan MashaaAllah agurin halitta ga farar fatar ta da harda na kanti take karawa, ga shegun magungunan matan da kullum take aikin siya, Kallon dak'in tayi next target dinta babban mutun ne acikin kasar tasu sunan sa alhaji ismail bandir kowa yasansa indai dukiya ce, kuma tasan batakai ayi mata hanya gurinsa ba, murmushi tayi ta dauki wayar badoo dake kan gadon cikin hankali da nutsuwa tashiga lalubar numbar alhaji bandir, wata ajiyar zuciya tasaki alok'acin da taga numbar saurin haddacewa tayi sannan ta ajiye, kayanta tagani amma ta nemi pant dinta ta rasa, hakan yasata acik'in shock sosai, badai da gaske akeyi ak'an abunda badoo yakeyi ba? Amma zatayi maganinsa yanzunnan ma kuwa. Bude bandakin yayi sannan yafito fuskarsa dauke da murmushi kallonsa tayi tace " my badoo ashe kaima kana kungiyar mu?" Lokaci daya yaji jik'insa yayi sanyi cikin kare kansa yace " wacce kungiya kenan?" " Ba sai kaji kowacce bace ba amma ina bukatar wandonka dan nima dashi akace zan samu kudi, kuma kasan menene duk sharadan mai wandon kacika" cat walk tafara sannan tashige cikin bandak'i. Wani sabon gumi ne ya zubo masa bude cik'in zakar kudinsa yayi ya dakko pant dinta ya ajiye akan gadon yacigaba da shiryawa. Surry na fitowa daga bandaki Tayi murmushi ganin ya ajiye mata, cikin ranta tace shegen karya ai da ka dauke da baka karaba, ko kulasa batayi ta shirya ta dauki Jakarta kallonsa tayi tace " Love you badoo " " Haba surry yazaki tafi yanzu nazata nan zamu kwana?" Murmushi tayi sannan takara gaba tana fad'in am not that cheap sannan tafita.


 Motar ta tashiga sannan ta kara gaba wayarta ce tayi kara tana dubawa taga Bintu dauka tayi tana " Manyanmu ya harka?" " Wallahi surry bakida mutunci wato yanzu ke harka ta bude bakya tunawa da uwar dakinki ma? Nace ki taimaka ki hadani da ko k'aramin alhaji ne please." " Ke Bintu bakya gyara kinzama sai kace wata ragaje ragaje hajiyata ki gyara skin ki gyara gashi ki zama yar gayu sai na dama dak'e amma wani alhaji zai soki haka?" " DanAllah to aramin ko 100k ce banda kudi Allah." " send account details inada aiki yanzu see you later." Kashe wayar tayi tana murmushi.


 Tafiya tayi ba yar karama ba kafin tashigo dan kauyen nasu daidai wani shago ta tsaya malam tagani gefen shagon gaba daya tausayin iyayen nata sai yadawo mata sabo har yanzu goron yake siyarwa sai da ta tsaya tasha kuka tana fadin " Wannan itace kaddarata da ko a mafarki bantaba tunanin zatasomin ba, innata kuyafemin ke da malam kuka yakara subuce mata a hank'ali ta bude motar tashiga karamin shagon kauyen nasu dattijo ne ciki haka suka gaisa ta k'alleshi tace " baba danAllah zan iya sanin mai sai da goron nan? " " Diyata me zakiyi masa kinsan fa muna lok'acin yan garkuwa yanzu." " Ka kwantar da hank'alin ka baba da alkhairi nazo." " Shiru yayi na dan lok'aci sannan yace " to to madallah " " To baba inason buhun shinkafa da taliya da mai da masara da wake sannan inason Kayan shaye komai a hadamin bibbiyu sannan kayimin lissafi. Haka dattijon nan yashiga hada mata sannan yace " dubu dari biyu da hamsin suka kama" " Jakarta ta bude ta fito da kud'i tashiga lissafi kafin ta mikawa dattijon jiki na rawa yace " hajiya a mota za'a sakamiki? " " Baba inaso a bawa wannan dattijon na waje kashi daya sannan ga dubu dari biyu akara masa akai, sannan kaso dayannan karabawa mabukata ." Tuni dattijon yasa kuka yana mata godiya ita kuma tayi waje inda yatafi gurin malam yana jansa yana masa bayani tana shiga mota taga malam yayi hanyar motar yana godiya " Allah yasaka miki da alkhairi diyar nan yayimiki albarka nagode yasa kuka, sosai itama surayyan tashiga k'uka tanason iyayenta amma kaddarar ta ta babbanta ta dasu cikin muryar kuka tashiga fad'in malam inasonku nima kuyi min addu'a sannan taja motarta tayi wajen gari, wani shagon kayan mata tashiga tasiya manyan lace guda 4 sannan tasiya atampha guda 10 material takalmi da jaka haka tasiyawa inna da kausar sai da takashe musu kusan dubu dari biyu da hamsin sannan tace abata kananan lace da atampha guda 30 dan tasan matan layin su bazasu huce haka ba duk da tadade batazo ba haka tasa aka sassaka kowanne leda da atampha da kuma lace laidar su inna kuma daban, Suna gama hada mata ta shiga mota ta koma cik'in kauyen bakin layin bata tarar da kowa ba sai wasu matasa nan tabasu kowanne 5k sannan tace su rabawa matan unguwar sannan ta samu wani yaro daman tasan almajirin malam ne tace wannan kai ka kai gidansu kausar ta koma mota taja.


  Gaba daya gurin kowa addu'a yakeyiwa yarinyar batare da sunsan surry bace ba, haka malam ya dauke goronsa ya nufi gida inda yatarar da matasan nan na rabon atampha sallamar da zaiyi yaga inna ta fiffito da kaya. Kausar dake kusa da ita tace " inna to ko kawun birni ne ya aiko miki dashi?" Malam ne ya washe baki yace ai ba ku kadai ba duk matar unguwar nan wata hajiya tazo ta raba musu, nan ya nuna musu kudinsa da kayan abincin, ai inna addu'a tashiga zubawa hajiyar nan kausar kuwa daki tashiga ta rufe tasa k'uka dan tabbas jikinta yabata Surayya ce, sosai taci k'ukanta.


***********************


  Ali dasu pretty tare da mukhtar suke zaune, mukhtar ne yagyara zamansa yace " Ali lafiya ka taramu kuma ka kasa magana?" " Wacce shawara kuka yanke akan Ahmad?" Cewar pretty. mukhtar ne yace " Mu kashe shi!!! " pretty ce tace are you mad " I love him so much dan haka ban taba yarda hakan yafaru ba." Ali ne yasa dariya yace " Ina bakin ciki da hassadar irin nutsuwar Ahmad tunda yazo kasar nan kullum faba yakeyi, abun takaici ku kalli yadda iyayensa suke masa addu'a it Hurt me banson ganin haka we have to do something." Mukhtar ne yace " what are we going to do? " Abu daya ne kadai zaiyi aiki akansa jiya nayi tunani shine musa ayi masa asiri kuma malamin yacemin dole sai dai ayi masa wanda zai iyaci a nama and kusan baya cin abun hannun mu shine matsalar." Mukhtar ne yace " shege to asiri akan me zamuyi masa?" " Da farko naso akan karatu mu lallata rayuwarsa daga baya malam yacemin bai yihuwa haka sai nacewa malam to baza'a iya yimasa wanda zai tsani iyayensa ba yadinga yi musu rashin biyayya ba? Malamin yace min sosaima amma maganin dole sai dai yaci a nama." Pretty ce tayi dariya tace "that's my work zanyi." Ali ne ya kalleta yace "how?" " zan shiga jik'insa nace na tuba shikuma a time zaiji tausayi na tunda ni macece sauran aikin ba sai nasanar muku ba" ihu suka saka sukace " Sai dake pretty".