RUDIN ZUCIYA

8

by @nanadiso10

RUDIN ZUCIYA


  NA NANA DISO



PAGE 8


Sai dake pretty". Murmushi tayi tace " don't know yadda nakeson Ahmad duk abunda zai kauda hank'alin sa da nutsuwarsa that's what I really need." Ali ne ya gyara zamansa yace " And you got it, yau maganin zaizo hannu na zuwa gobe zan baki but ...." " Don't say anything kabarmin aikina da kaina." Tunda Ahmad yatashi a barci bai k'oma ba yau jiyake kamar bashi ba, wayarsa ya dauk'a missed called biyu yagani na Umar, hakan yasashi hanzarin bin kiran, " Am sorry yaya ina bacci ne." Ba matsala Ahmad ya karatu? Kana dai maida hank'ali sosai ko? Naga kayi transfer na kudi shine nace na menene?" Daga yanayin maganar Umar yasan yana cikin damuwa duk da baya k'allon fuskarsa, gyara kwanciyarsa yayi yace " Yayana what wrong with you?" Umar da yaji maganar ba zato yace " Babu k'omai kawai mura nakeyi, nan cikin zuciyarsa zafin abunda mama takeyi masa ne, don yau ma sai data cimasa mutunci akan bai siyo bread ba alhali babu kudi a hannunsa ne harda ce masa " haka dai zaka k'are da yawan koyarwar islamiyya bazaka mai da hank'ali kaima kana samun kudi ba"" yaya kayimin magana bayan ni kanada wani abok'in hirar ne kokuma abok'in shawara, kaga nima zan shiga damuwa idan baka sanar dani ba yayana" Sosai yaji magangunun Ahmad amma yabada tabbacin bazai iya sanar masa da komai ba yanzu. " Babu komai Ahmad banajin dadi ne idan da inada damuwa ai zan sanar maka" " To yaya Allah yakara lpya kudin dana tura idan ka canza bazaifi dubu dari uku ba, sai ayi gyaran gidan dashi." Da mamaki Umar yace " wani ya gayamaka gidan na bukatar gyara ne?" Dariya sosai Ahmad yayi yace " kai yaya baka daina ustazancin nan dai, to mama ta kirani tace gidan na zuba" " To zan bawa baba kud'in anjima idan na canza." " Nagode yaya mu yini lpya." A gaggauce yatashi ya shiga bandaki wanka yayi yafito yana tsane jik'insa fuskarsa dauke da murmushi, kyakyawar yarinyar nan tajiya kawai yake tunani with her first look tun jiya yake murmushi, kananan kaya yasaka sannan ya dauke wayarsa ya fita, cikin mintuna yak'arasa cikin makarantarsu bangaren bussiness relation ya nufa, yana daf da zai shiga aji ya hangota tana nufarsa " excuse me please shine harafinta tana nufosa"K'allon ta yatsaya yi nawasu mintu nan sannan yaja jik'insa guri daya ya tsaya cike da mamaki da karfin halinta da yake gani har ta nufi kusa dashi. Cikin yaren turanci tace " Kullum in nayi maka magana baka kulani me isa? Kai bakada 'yammata ne? I love you you're so cute." Karfin halin yar budurwar yagani yana dariya sosai har sai da hak'urin sa suka bayyana, ita dai gata nan gata nan ba hausa ba bakuma turawa ba. Cik'in muryar shagwaba tace " am talking to you my handsome, can't you speak?" Da mamaki yakara k'allon ta yace mata " yanzu lok'acin aji ne zamuyi magana after idan baki shiga lok'acin aiki ba". Mamaki ne yakamata da taga har yashige ajin, tabbas wannan ne saurayin da takeso shine abokin rayuwarta ta fada tana mai juyawa gurin kawayenta.


 Sai after magrib yakoma gida bai tarar da kowa ba sai pretty tanata kuka kana ganinta dole ta baka tausayi bai ce mata uffan ba yashiga dak'in su wanka yayi sannan yafito domin yayi girki nan ma yaganta tanata k'uka lokaci daya tabasa tausayi tabbas akwai abunda ke damunta wannan k'ukan ba na haka kurum baniba, cikin shashek'ar kuka tace " danAllah kayafemin Ahmad wallahi na tuba na gane hanyar da nabi ba itace mai billewa ba, kataimaka min ka daukeni tamkar kanwarka mahaifina idan yaga abunda nakeyi zai iya mutuwa lokaci guda da k'yar yasamu kud'in kawoni karatu, danAllah kayimin taimako ka dorani hanya tagari kada kabari Rudin zuciya yacigaba da tasiri agareni." Tunda ta ambaci iyaye gaba daya jikinsa yayi Sanyi Tabbas yadda yaganta kadai ya nuna masa tana bukatar taimakonsa, " shiga muje zan tambayeki " biyosa tayi nan yashiga yimata nasiha kamar gaske sai kuka takeyi tana masa godiya, bandaki yatashi yashiga inda tayi saurin bude kwalbar ta barbada maganin cikin kazar daya siyo tayi saurin juyawa, tana ganin yafito tace bari taje gida danma ya tabbatar ta shiryu, baice mata uffan ba ya karasa abincin ya zauna ya fara ci, saboda yunwar dayakeji ko bismillah yau mantawa yayi.


**********

Ustaz Ummaru shine furucin mama asanda ya karaso kusa da baba, baba ne ya kalleta yace " menene haka kikeyiwa d'ana?" Umar ne yace " baba wasane fa k'awai." Allah dai yayi maka albarka Umaru yanzu wannan kudin menene daka bani masu yawa haka?" Mama ce takara fadin " ina yaga wannan uban kudin zuciya duk ta mutu ai inaji bai taba rikesu ba nasan danAlbarkan nan ne ya turosu." " Tabbas Asma'u kina cikin Rudin zuciya" shine lafazin baba na karshe yana barmata gurin. Kajimin baban nan nasu zan tsine masa ne? Ina dalili ga yaron dake kyautatamin zan dinga yiwa wani addu'a a'a iya farantawar da iya addu'ar sa Ahmadu na kuwa dole ne inyi masa addu'a kullum cikin faranta mana yakeyi dan aljannah." Hawaye ne ya zubowa umar bai ma saniba bawan Allah hakan yasa yatashi yabar gurin.


*********


Yau ce ranar karshe indai Alhaji bandir bai daukaba to tabbas bata sake kiransa mutum sai shigen izza da isa mtseww shine karshen lafazinta, Daga can gefe wayar tata ke ringing hakan yasata saurin dauk'a tana murmushi daga can akace " wacece?" Cikin isa tace " Surry baby". Daga cikin wayar aka kara fad'in why do you call me? Surry ce ta harari wayar tace " I want to meet you uncle bandir." Guntun tsaki taji anja sannan yace " don't call my number again" " InshaaAllahu I will not call you again, thank you" kallon wayar tata tayi da mamaki tasu dai sunaji da kansu wallahi mtsew can kuma tak'arajin wayar tata tana ringing dauka tayi ta kara a kunnenta, " ina homebon hotel we can meet, when you arrived text me don't called me." Ya katse qayar, wane ihu tasa tana badin yarinya mai sa'a kenan yar gidan malam da inna, yayar kausar tasa dariya wanka tayi cik'in mintuna d bazasu gaza goma ba sannan ta fito tasa wasu short skip and half vest, mashaaAllah shine last word din data fada, after dress tasa akai taja mukullin motarta da glass dinta tasa afuskarta sannan ta fita ta hau motarta cikin nutsuwa take tuk'in ta zuciyarta fall zata hadu da mutumin da take ganin tayi arzuki, tayi alkawarin jiyar dashi dadi fiye da duk wata wacce zatayi masa d'an tazara tsakanin inda take da hotel din.


  Alhaji bandir dake kwance yaji gaba daya duniyar ta juya masa, baya cikin masu bin mata dan matansa biyu ma, sannan yana mugun taka tsantsan gurin kiyaye ubangijinsa, duk yadda zuciyarsa taso ta rudesa yana mutukar kiyayewa, yasan masifar zina yana ganin yadda rayuwar abokansa wasu take lallacewa yana ganin yadda ake blackmailing din wasu, lok'aci daya kuma yaji babu dadi me isa ma ya amsa mata? Yana fatan ace wannan yarinyar ce da suka taba haduwa a airport yana bukatar ceto rayuwar ta, text ne yashigo cikin wayarsa, dubawa yayi yaga itace wasu nambobi yakira sai gashi anshigo da'ita, kwas kwas shine sound din dayaja hank'alin sa har ya dago yana k'allon ta, samun guri tayi ta zauna tace " ina gaisuwa uncle." Murmushi yayi wai uncle wannan ai na girmi iyayenki ma baki ba aransa yafada, " ya sunanki? Me yakawoki gurina? Me kikeso? ". Dariya tayi kadan tace " all this question for only me? Any way sunana Surayya, inason in zama girl dinka." " Shekararki nawa malama surayya?" " am 22 yanzu " " To young yafada da dan karfi, na tabbatar satar numbata kikayi." " me isa zan saci numbarka ? Sai dai in banso samu ba" " that's a big lie don ni banayin abunda kikazo yi...