BINTUN BATUUL

Introduction

by @takwalam



Somewhere around the Globe!


1980s and there about!


Tamkar me tafiya akan iska Haka ta fito daga dakin baccin nasu, kamar kiftawar idanu har ta isa wani daki dake can gefe, tana zuwa ta murda door knob din, Wanda a take dakin ya bude, babu haske kasancewar tsakiyar dare ne, tana shiga ba tare da ta kunna wutar dakin ba ta karasa gaban gadon inda yaro yake kwance lullube da duvet, ta karasa har kafafun ta na hardewa gaban gadon, ko data yaye duvet din se ta samu Babu kowa a gadon illa pillows da aka jera, yayi kamar yaron ne a kwance, tayi saurin ja da baya tamkar wadda taga wani abu me tsoratar wa, sede hakan ne dai yaron baya Kan gadon da tayi coaxing din shi not long ago, tayi saurin bude wata kofar Dake dakin, tunanin ta ko toilet ya shiga, Amma wayam Babu kowa, ta fito daga dakin cikin wani yanayi me firgitar wa, sede ko Ina idan ta duba Babu trace ko daya na yaron balle na uban yaro, ta tsugunna a tsakiyar parlon wani kuka Yana kubce mata, ta Fara yin shi Babu kakkautawa, tana Yi tana shesheka kamar zuciyar ta zata fito, wani irin tsoro take ji Yana shigar ta... Kada fa ace sun dauke Mata Babyn ta? Se Kuma ta tuna ai kuka ma ba maslaha bane ba, ya kamata tayi making report ASAP Dan duk inda Imam yake to tabbas baiyi nisa ba, ta Mike zuwa inda wayar gidan ta landline take, ta dialing number cops, cikin mintuna se ga shi an Fara Mata magana cikin harshen larabci, itama cikin harshen larabcin tayi filing complaint din bacewar yaron nata, Suka tambaye ta address nan ma ta fada musu, Suka tabbatar Mata zuwan su ba da jimawa ba!


Ko da ta sauke wayar se ta Kuma sakin kuka, abin da Imam ya kulla kenan shiyasa yazo out of nowhere? Dama zuwa yayi ya tafi da yaron shi da ya manta shekara da shekaru? Ta Kara fashewa da kuka lokacin da ta daga idanun ta ta sauke Kan katon hoton shi Dake manne jikin bangon parlon, yaro ne kyakyawa, yayi kiba irin ta yaran da suke samun kulawa, ya daga hannun shi guda Yana sakin dariya, bakin  babu hakori ko daya amma dukda Haka idan ka kalla hoton zaka samu Kan ka da yin dariya ko Kuma murmushi! Har anan a durkushe cops suka same ta, bayan ta zauna sun Dan Yi bincike cikin gidan suka tabbatar da Babu shi fa yaron se Suka dawo Dan daukar statement din ta!


Da farko dai ita din Yar Qatar ce, sunan ta Zainab, iyayen ta sun kasance musulmai Kuma larabawa kamar yadda muka San asalin Qatars! Ita din ma wanke hannu ka taba ce, kyakyawa Fara balarabiya, mahaifiyar ta ta rasu tun tana yarinya Kuma ta kasance ya daya tilo a wajen su, mahaifim ta shima ya rasu bayan ma ta Gama O level din ta. Ma'aikaci ne  a wani babban company cikin kasar, ranar da rasuwar tashi ta kasance,  Zainab ta fada Masa tana son cin abincin dare tare da shi, Yana ta kokarin kammalla aiki dan cika Mata alkawari Amma aiki se ya Sha Kan shi, ya kasa fitowa sallar maghrib, se a office yayi, ita Kuma tun da yace ta zaba masu top restaurant, ta riga da ta isa wajen har ta bada order kafin mahaifin nata ya karaso, a banagaren shi ya kammalla komai ya Mike tare da daukar wasu takaddu Dan zuwa ya samu tilon diyar tashi, Amma yana zuwa kofar da zai bude ya fita se kawai ya yanke jikin shi ya fadi, daga wannan faduwar bai sake shurawa ba Rai yayi halin shi!


Shiru shiru har karfe Tara da wani abu Zainab na jiran mahaifin ta amma bai dawo ba, a lokacin ta tabbatar Babu lafiya, Dan Haka ta Mike ta fice zuwa wani nearby phone booth, ta Kira number office din shi sede Babu Wanda ya dauka, hakan ya sake tayar mata da hankali, kawai se ta kashe wayar ta nufi office din shi a mota, tana zuwa an fito da shi daga main building din company din akan stretcher, ga ma'aikatan da Basu tafi ba dukka suna alhinin abin da ya faru da Mr. Fahad!




                              ***




"Bintu! Bintu!!"


Na Dan mikar da hannu na tare da kwankwasa kofar bayin Wai dan na fada musu Ina toilet, Amma hakan da nayi se ji nayi


" Ke Bintu wai dama tuntuni kina toilet? Kina ji Ina ta babatu akan ki, to Mamaa ke Kiran ki se ki fito"


Ban ce komai ba, na cigaba da abin da nake, ni nasan ko Ina nake zaayi min uzuri tunda a toilet nake, seda na kammalla na fito na tarar dakin Babu kowa sannan na fita zuwa dakin Mamaa, tana zaune saman gado ta baza atamfofi Wanda take siyarwa, inaga tana sorting din su according to kudin su. Nayi sallama a hankali na shiga, ba tare da ta dago ba tace


" Bintu Ina kike tuntuni nake neman ki?"


Nace


" Mamaa Ina toilet!"


Ta dago ta kalle ni na Dan lokaci kafin tace


" Suleiman na parlor, ki gyara shigar ki kije ki Kai musu ruwa!"


Nayi shiru Ina kallon Mamaa, Ina Kuma son tabbatar da abin da take fada, ya zanyi Wai nayi hakan? Ya zaayi Rana tsaka ace wai na Fara soyayya da Suleiman? Ya ma zaayi Haka?


" Baki ji abin da nace ba ne ba?"


Ta fada muryar ta na Dan dagawa, ban ce komai ba na juya a hankali na koma dakin da na fito daga ciki! Na tsaya gaban mirror Ina kallon Kai na, wani boubou style material ne a jiki na, color din shi me duhu ne Wanda ya sake saka fata ta tayi duhu, fuska ta duk kuraje ne saman ta wanda tun da na Kai puberty nake fama dasu, ni ko kadan bani cikin sahun Mata masu kyau, shiyasa nake da low self-esteem, bana son shiga cikin mutane ko kadan, bani da confidence, a kusan komai na rayuwa ni ce karshe.


Ba tare da nayi adjusting shigar tawa ba, na dakko katon hijab na kima akan boubou din, Wanda ya sake fito da kibar da nake da ita, ban ko damu ba na nufi kofa Dan fita, se mukai kicibis da Batuul Dake kokarin shigowa, nasan an turo ta taga me nake har yanzun ban fito ba, ta kalle ni tana bude Baki in exclamation


" Bintu! Ba dai a Haka Zaki je wajen shi ba? Kin ganki kuwa?"


Na kalle ta Ina Kara Shan kunu, Amma cikin zuciya ta da jiki na tamkar an sassare min gwiwa Haka naji,


" Ki koma ki danyi touching fuskar ki, ki canja Kaya. Amma wannan ai se yaga kamar..."


Kafin ta karasa na bude Baki na nace


" Se yaga kamar me? Kamar giwa? Ko kamar bull?"


Se tayi shiru ta kasa fadin komai, ganin har idanu na sun Fara cikowa da kwalla, na gyada Kai in annoyance na bi gefen ta na wuce, wani irin radadi nake ji cikin zuciya ta, Wanda ba lallai wani ya fahimci yadda nake ji ba, ko da naje kitchen se da na danyi kuka kafin na samu zuciya ta ta huce!


"Wai Kai Suleiman zaman me muke har yanzun anan?"


Wannan shi ne abin da na Fara jiyowa lokacin da na nufi parlon, na ja na tsaya Ina kokarin daidai ta yanayi na kafin na shiga


"Nima dai abin da na gani kenan, since ba zasu baka Batuul ba, to me kake jira"


Dan kada su Fadi wani abun yasa nayi saurin summoning courage na shiga, da sallama a Baki na, dukkan su Suka dago idanu Suka zuba min Wanda yasa naji kamar na koma da baya, Amma Babu yadda zanyi na riga da na shiga. Na aje tray din hannu na sannan cikin rashin kuzari da kasa da murya na gaishe su, Suka amsa Amma ko kadan na kasa daga idanu na na kalle su, saboda gani nake dukkan su suna iya hango munin fuskata! Shiru na wajen mintina hudu kafin na Mike na dubi Suleiman a Karo na farko tun shigowa ta wajen, Sanye yake da men lace coffee da zare milk, Kan shi da hula wadda ta Kara fito da shigar ta shi, na Dan Yi ajiyar zuciya nace


" Allah ya kiyaye hanya!"


Ba tare da na jira sun amsa ba na Kama hanya ta Dan komawa daki, sede Ina barin wajen naji daya daga ciki yace


" Sule! Wai wannan golf din zaka aura?"


Yadda yake dariya, yadda dariyar take shiga kunnuwa na tana sauka a zuciya ta tare da piercing zuciyar, ba Wai nayi niyyar tsayawa bane ba, kawai dai kafafu na ne Suka tsaya Dan Kan su,


"Ba kada kirki Fahad, Wai golf?!"


Shima dariyar shakiyancin yake irin ta abokin shi, wannan karon se naji zuciya ta tamkar yayyaga ta ake in pieces, kafin a Kara fadin abin da zanyi shekaru Yana hunting zuciya ta, Naga gwara naja kafafu na kawai na tafi. Aikuwa Ina zuwa daki na fada gado Ina sakin kuka....



Taku har kullum


Ayshatuuu


Shin kina da labarin wannan karon ma tafiyar ta top-notch ce? Season 3 ake magana na shatuuu, me dambu da Kuma Aziza! Me kike jira 'yar uwa? N1500 kacal Zaki mallaki NAZNEEN, BINTUN BATUUL  da Kuma GEN. NASIR ZAKI!