Page 7
*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_
©️ *OUM MUMTAZ.*
_No: 7_
_Free Page_
*Lawisa $ Lawal*
Wayar Lawal yana hannun ta a lokacin da ya shiga wanka, tana tura wasu waƙoƙi zuwa wayarta, ƙiran farko da ya shigo ta fahimci wacce ta ƙira sabida sunan 'Ummu Amir' da ya fito, amman sai ta basar ba tare da ta ɗauka ba, dik da yanda taji ƙirjinta ya buga da tsananin kishin Umaima sabida a kalaman Lawal sosai ta fahimci irin son da yake mata dik da yana ƙoƙarin boyewa, sai a ƙira na uku kamin ta ɗauka ba tare da tayi magana ba. Sallama akayi ta amsa da, "Wa'Alaikumussalam." A daƙile. "Baiwar Allah dan Allah mai wayan nake nema." Taji Umaima ta faɗa cikin sanyin murya, wanda hakan ya sa ta tsuke fuska sabida gani tayi idan ba rainin wayo ba Umaimar ba ta san sunan ta bane, ko kuwa ba ta san matsayin mata take a wajen Lawal ɗin ba da za ta wani ce wai baiwar Allah mai wayan nake nema? Hakan yasa ta bata amsa da faɗin, "Ya shiga wanka idan ya fito wa za'a ce masa ta ƙira?" Tayi maganar a salon rainin wayo, sai kuma taji an kashe wayar ba tare da an bata amsa ba, wanda hakan yasa ta taɓe baki tare da ci gaba da tura waƙoƙin ta.
Lawal fitowar sa daga wanka ya kalli Lawisa da take kwance kan gado tana turi yace,"Naji kamar kin min magana ina banɗaki?"
Cike da kissa Lawisa ta ajiye wayoyin tana miƙewa daga kishingiɗen da take tace, "Ba da kai nake ba, wata waƙa nake nema shine nake dan rairawa." Ta fada a sanda take taya sa goge ruwan da yake jikinsa sakamakon wankan da ya fito.
"Ok, bari na shirya a gaggauce naje na dubo Amir da Mamansa mun kwana biyu ba mu haɗu ba kar dare yayi." Faɗar Lawal a lokacin da yake saka kayan sa, dik da yanda yake jin gabansa na faɗuwa da sunan Umaima kawai da ya tuno, sabida shi karan kansa yasan cewa bai mata adalci ba,kuma yaci amanar soyayya tinda har zai iya yin aure ba tare da masaniyar matar sa ta gida ba, a lokacin da ita kuma take can gidansu wajen rasuwar mahaifinta, kuma dik cikin gari guda.
"Amman Sweetie sai dai mu tafi tare, nikam bazan iya zama a gidannan ni kaɗai ba tsoro nake ji." Inji Lawisa cike da shagwabar da yasa Lawal amincewa ba tare da ya shirya ba.
Tare suka fito bakin kwalta zuciyar Lawisa kamar yayi bindiga don baƙin ciki da takaici na wannan fitar, a ranta kuwa Allah-Allah take taje taga wannan Umaimar da me har ta fita wanda dik wani abinda Lawal yake sunanta ba ya taɓa ficewa daga bakin sa?
Wayar hannun Lawal ne ya fara ƙara,yaron da yake masa tsaron shago ne ya ƙirasa, yazo ɗauka sai akayi rejecting da yasa shi fahimtar flashing yaron yayi masa, wanda hakan yasa shi shiga call logs domin ya ƙirasa, kawai idanunsa suka sauƙa kan lambar Umaima da yake nunin ta ƙirasa mintuna ashirin da suka wuce. Kallon Lawisa da hankalin ta yake kan wayarta yayi yace, "Umaima ta kirani har kinyi receiving amman shine baki fada min ba miyasa?" Yayi mata tambayar yana tsare ta da ido ta hasken farin wata da ya haska tare da taimakon wutar solar da ya raba tsakiyar kwalta, a ransa yana addu'ar Allah yasa Lawisa ba ta kwaɓa masa danyen aiki ba.
A ɗan daburce Lawisa da kwata-kwata ta manta ba ta goge kiran da Umaiman tayi ba tace, "Ayya dai Sweetie, wallahi shaf mantawa nayi ban faɗa maka ba." Tayi maganar tana langwabar da kai cikin fuskar tausayi, wanda hakan yasa Lawal maida masifar da ya so sauƙe mata, amman dik da haka ya dinke fuska sosai, yace, "Mai kika ce mata da kika ɗauka?"
A hankali Lawisa da ta sha jinin jikinta ganin irin kallon da yake mata tace, "Sallama nayi mata don mu gaisa amman sai ta fara zagi na uban wa yace na ɗauki wayar mijinta, shine kawai sai na kashe wayar ba tare da nace mata komai ba, gudun kar nayi mata rashin kunya matsayinta na matarka ta farko kuma uwa a wajen ɗanka." Tayi maganar tana ƙif-ƙifta ido, tare da tunanin za taga Lawal ya dau zafi ko kuma yace su koma gida yama fasa zuwa dubo Umaimar tinda ta zage ta, amman sai taga akasin hakan, domin kuwa gani tayi fuskarsa ta washe daga ɗaurewar da yayi da farko, tare da furta," Alhamdulillah tinda baki ce komai ba,bari na kirata." Wanda hakan yasa wani mololon baƙin ciki tsaye mata a makoshi jin abinda ya faɗa, ba tare da ya nuna jin haushinsa akan zagin da tace Umaiman tayi mata ba me hakan yake nufi?
Shi kuma Lawal sai da yayi ma Umaima ƙira huɗu har ya fara shiga damuwa, sai a ƙira na biyar ta ɗauka, wanda hakan yasa shi sakin ajiyar zuciya, ya ma manta a inda suke da kuma waye yake tare yace, "Don Allah Umaima kiyi hakuri ki yafe min, nasan cewa ni mai babban laifi ne a wurinki, ban kuma kyauta miki ba, wanka na shiga shine Ummita ta ɗauki wayar yanzu nan zan hau mashin nazo ki fito kofar gidan zakiji dalilin da yasa ban samu damar zuwa naganki ba tin ranar sadakan ukun Baba."(Ummita kanwar Lawal ce da take makarantar kwana, wanda Lawal ya zabi da ya ambace ta a matsayin wacce ta ɗauki wayar tasa, sabida bai ya son fada ma Umaima dik wani abinda ya faru har sai ta dawo dakinta su zauna suyi magana ta fahimtar juna,ya zabi da yayi mata karya sabida shi bai san cewa ita Umaima already ta koma tinda rana ba.)
Baiji ta masa magana ba, har ma yayi tunanin ƙiran ya katse, sai kuma yaji abinda Umaimar ta fada masa tare da katse wayarta, wanda hakan yasa shi shafa sumar kansa cike da damuwa, sannan ya kallo Lawisa da ya ma manta da tsayuwarta a wajen tana kallonsa kaman mai son fahimtar wani abin, cike da tsananin kunyar da ta sauƙo masa na ganin irin kallon da take masa sakamakon karyar da ya yanko a gabanta yace, "Mu koma gida sai da safe zanje na ganta kinga dare yayi sosai." Ya kare maganar yana juyawa haɗi da gangarawa, Lawisa da ta cika da mamakin dalilin da yasa Lawal yima Umaima ƙarya bazai ce ita ta ɗauki wayar ba ta bi bayansa cikin sanyin jiki, a ranta kuwa gulmar ganin yanda dik ya fita a hayyacinsa alamun rashin gaskiya ƙarara ya bayyana tare dashi take yi.
*Umaima*
Tsawon mintunan da ba ta san adadinsu ba, ta ɗauka cikin fargaba da zurfin tunani, na inda Lawal ya tafi har ya shiga wata mace ta ɗauki wayarsa ta tabbatar mata da cewa wai ya shiga wanka, ita dai tasan Lawal mijinta ba manaimin mata bane, kuma ta tabbatar babu ɗaya daga cikin gidajen yan uwansa da zaice ya tafi har ya shiga wanka tinda dikansu mata ne, ita yanzu fargabarta ɗaya Allah yasa a dan tafiya gida kwana takwas da tayi mijinta bai canza hali ba wajen naiman mata, wanda zata iya dafa kur'ani baya ɗaya daga cikin mazaje masu bin matan layi.
Ƙiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata guntuwar tunanin da ta lula, ganin lambar Lawal yasa ta gagara ɗauka har kiran ya katse, sai a kira na biyar kafin ta samu kwarin gwiwar dagawa ba tare da tayi magana ba, sai da ta gama saurarar abubuwan da ya faɗa tas, har za ta katse ƙiran sabida haka nan jikinta ya bata ƙarya Lawal ɗin yayi mata, domin kuwa ita tasan wacce sukayi magana da ita a takaice muryarta ko kusa, ko ta nesa bai yi kama da muryar Ummita ba, bugu da kari kuma ina ita Ummitar ta tafi tinda gashi da ta dawo gidan bata ji wani yayi mata zancen dawowarta ba? "Ka bari gobe kazo da safe, na riga da na kwanta ko kazo bazan iya fitowa ba." Ta faɗa masa tare da katse wayar ba tare da ta ce masa ta dawo ba, sabida tana son ganin lokacin da zai dawo gidan daga dik inda ya tafi.
Ƙarfe sha ɗaya, sha biyu, ɗaya, biyu, uku amman Lawal shiru bai dawo gida ba, wanda hakan kuwa sosai ya sanya Umaima cikin matsananciyar damuwa, domin kuwa babu matar auren da mijinta zai kai tsawon wannan lokacin bai dawo gida ba, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba tace hankalin ta a kwance yake muddin tasan kanta. Bacci ɓarawo ne yayi nasarar ɗauke ta bayan tayi sallar asuba.
Can cikin barcin ta take jiyo muryar Amir da yake ta faman zabga uban kuka kaman ana yankar naman jikinsa, wanda hakan yasa ta bude idanunta, sai kuma ta rintse sabida hasken ranar da ya ratso cikin parlon ya ɗauke mata ido, a hankali ta sake buɗe idanunta ta sauƙe akan Lawal da yake ta faman jijjiga Amir din yana lallashinsa amman yaro yace bai san wannan karatun ba, da dan kuzarin dole da ta lalumo ta tashi zaune haɗi da duba agogon wayarta da ya nuna mata karfe sha daya har da rabi na safe, wanda hakan yasa ta idasa wartsakewa babu shiri ta ture mamakinta na ganin Lawal a dai-dai lokacin.
"Sannu da zuwa, ina kwana." Ta furta a lokacin da take karbar Amir daga hannunsa.
"Lafiya kalau yaya kike, ya kuma karin hakurinmu? Ashe jiya kika dawo daga gida shine baki ƙira kin fadamin ba? Kawai yau ina tafiya muka hadu da Amina, Allah yaso ko shiga gidan banyi ba ta tabbatar min da dik kun waste jiya, gaskiya baki kyauta min ba." Lawal ya kare maganar cike da ƙarfin hali, sabida ganin irin kallon da Umaima take binsa dashi kamar mai son fahimtar wani abin.
"Haƙuri mun gode Allah, batun kuma ƙira ai na kira ka jiya da dare wata ta ɗauka, ta tabbatar min da ka shiga wanka." Umaima tayi maganar, a kaikace kuma tana ƙare ma Lawal kallo sabida ganin yanda ya wani yi fresh dashi, fuskarsa na fidda annurin da rabon da taga haka a fuskarsa tin watan farko na aurensu.
Lawal bai samu zarafin mai da ma Umaima amsa ba suka ji sallamar Innayo, wacce ta kasance Yaya a wajen mahaifinsu Lawal marigayi Sa'idu Maraya. A gaggauce Umaima da take bai wa Amir nono ta ciresa haɗi da ajiye shi akan cinyar Lawal, ta kunce gidan sauro haɗi da kudundune shimfiɗar ta janye zuwa ɗaki tare da janyo ɗakin, inda ma Allah ya taimake ta a share kuma a kimtse gidan yake sakamakon aikin gyarar gidan da jiya tayi,kawai dama shimfiɗar ce, sai kuma dan kurar TV, fridge sai kuma mashigar parlon.
Cike da girmamawa take gaisawa da Innayo wacce take zaune a kan kujera, ita kuma Umaima na zaune gun ƙafafunta, sai kuma Lawal da yake zaune akan wani kujerar hannunsa rike da ɗan sa da yake ta faman haɗiyar zuciya sakamakon kukan da ya jima yanayi.
"Ya muka ji da ƙarin hakuri yar nan? Allah ubangiji ya jiƙan mahaifinki, yasa aljannatul firdausi ce makomarsa, da dik wayanda suka rigamu gidan gaskiya, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani." Innayo tayi maganar cike da alhini.
"Amin ya rabbi Innayo, Allah ya ƙara girma, ya ƙara miki lafiya da kuma tsawon rai mai amfani." Umaima ta faɗa a sanda idanunta ke ƙoƙarin cikowa da ƙwalla tana jin kaman tayi kuka, amman sai ta shanye kayan ta, sabida tasan cewa kukanta babu abinda zai amfani mahaifinta dashi. Sai kuma ta dago kanta a hanzarce sabida jin abinda Innayo ke fadi cike da matsananciyar bugun zuciya.
"Daman zuwa nayi na maki sallama, yau ni zan koma garina, na kuma yi maki nasiha a matsayi na, na uwa a wajen Lawal, nasan ke yarinya ce mai natsuwa da kuma hankali, zanyi amfani da wannan damar na miki nasiha na kuma baki haƙuri akan abinda wannan shashashan mijin naki ya aikata miki ba tare da kin sani ba, wanda nasan dik wata mace da mijinta ya mata abinda ya miki ko da kuwa kwatan-kwacinsa ne zai yi wuya ta iya yafe masa cikin ruwan sanyi, to amman ke kuma Umaima ina da tabbaci akan ki bakya ɗaya daga cikin irin wayannan matan da basu karbar ƙaddararsu da hannu bibiyu a dik yanda tazo musu. Kar dai na cika ki da surutu a takaice nake son sanar dake yau kwana biyar kenan da aka daura ma mijinki aure, wanda yazo ya sameni babu jimawan nan wai ashe dik shirye-shiyen auren da akayi a baya bai faɗa miki ba, wanda mu kuma matsayinmu na iyayensa da yan uwansa dik a namu tunanin kina da masaniya akai, hakan yasa babu wanda ya taba tinkarar ki da zancen, ganin cewa ke ma da za'a yima kishiyar baki tuntuɓe mu da zancen ba, dan haka nake rokonki ta girma da arziki don Allah don annabi kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, ina son ki bai wa masu zuba ido wajen ganin yaya zakiyi tinda an miki kishiya kunya ta hanyar nuna musu da akoi da babu kishiyar zaune kike lafiya lau da mijinki babu abinda ya sauya kinji ko diyar albarka?" Innayo ta kare maganar tana dafa kafaɗar Umaima da take wajen ƙafarta cike da lallashi, zuciyar ta cike da tausayinta, sabida tasan cewa cin amana dai Lawal ya riga da yayi ma Umaima a zaman aurensu, wanda da farko ma ba tayi niyar zuwa lallashin Umaiman ba kaman yanda Lawal yaje ya roƙeta dazunnan, amman kuma sabida tsoron kar ƙin zuwan ta a matsayinta na babba kuma uwa abubuwa suzo su lallace ba a yanda aka so ba tazo ta.
"Babu komai Innayo, ban kuma ji dadi da kike bani hakuri ba a matsayinki na mahaifiya a wajena, ni nasan cewa Rayuwa, mutuwa, aure, rabuwar aure, 'ya'ya, arziki da komai da yake cikin duniyar nan LOKACI NE, dan haka ni wacece da zance zan ja da ikon Allah akan abinda ya kasance rubutaccen al'amari ne daga ubangiji Allah subhanahu wata ala? Wallahi har cikin zuciya ta Innayo na karɓi auren Abban Amir da hannu bibiyu, tinda haka Allah ya kaddara, da sani na ko kuma babu, nasan hakan bazai sa a fasa wannan auren ba, dan haka nake mai tabbatar miki da cewa insha Allahu bazan taba baki kunya!" Umaima ta kare maganar cikin natsuwar ta, dik da yanda zuciyarta take matikar karye akan wannan al'amarin, wai Lawal da take fuskantar abubuwa mabambanta akan aurensa da tayi ya rasa da mai zai saka mata sai wannan cin amanar.
Sosai Innayo tasa Lawal wanda yake zaune kaman ruwa ya cinye sa sabida da tsananin kunyar Umaima da faɗa, wacce taji zuciyarta ta cika da tsananin tausayinta da kuma ƙaunar ta, ta kuma saka shi ya bata hakuri, sannan ta tabbatar masa da ya rike matar sa da hannu bibiyu, idan kuma ya sake rudin duniya yasa ya rabu da ita to tabbas zai yi matikar wahala ya samu wacce zata yi masa hallacin da Umaima tayi masa.
*Tambaya zuwa ga makaranta!*
_Idan kika kasance a matsayin Umaima wani irin action zaki dauka? Akan Lawal?_
*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*
1- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*
2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*
3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*
4- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*
5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*
_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_
_LITTAFI BIYU:- ₦800_
_LITTAFI UKU:- ₦900_
_LITTAFI HUDU:- ₦1000_
_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_
_VIP 2k._
Za ku biya kuɗi ta wannan account...
*6314170140*
*FIDELITY BANK*
*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*
sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*
katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*
*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*
_LITTAFI ƊAYA:- 350f_
_LITTAFI BIYU:- 600f_
_LITTAFI UKU:- 650f_
_LITTAFI HUƊU:- 750f_
_LITTAFI BIYAR:- 850f_
```ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-```
*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*
*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*
*_•TICTOK 1500_*
*_•INSTGRAM 1500_*
*_•FACEBOOK 1500_*
*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*
```ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)```
*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*
MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*