FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Full house wife# Ngizim tribe from Potiskum LGA Yobe State # Living at BADE LGA Yobe state Nigeria # Also a student af computer science @ Yobe state University (YSU)# A writer of Hausa Novels.. #
Sample · Ɗandano
_*Ɗanɗano daga littafin LOKACI NE ƙarƙashin tawaga ta Fitattu Biyar*_Idan tace ba taji wani irin mugun fargaba da kuma bugawar zuciya ba a sanda Lawal ya furta mata kalmar saki a gare ta ba tayi ƙarya,domin kuwa ba ta taɓa tsammanin haka mata da dama suke tsintar kan su cikin irin wannan yanayin ba dik lokacin da kalmar saki ya gitta tsakanin su da abokan zamansu. Ƙiris ya rage wata mota da ta shawo kwanar da ta fito ba ta bangaje ta ba sabida nisa da tayi sosai cikin tunanin rayuwar daga lokacin da auren ta ya rage saura kwanaki uku ba,bin bayar motar tayi da kallo tana jin yanda hankalin ta sam bai kwanta mata da irin gudun da motar take ba.Acaɓa ta tara ta faɗa masa sunan unguwar su,a ƙofar gidan su yayi parking,ta sauƙo tare da akwatin ta,sannan ta sallame sa tasa kai zuwa cikin gidan su dik da irin yanda gabanta yake faɗuwa.Cak ta tsaya kaman wanda aka dasa ta a wajen tana bin ɗanta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.