LOKACI NE

Page 10

by @oummumtaz123

*LOKACI NE...!*

_Fitattu Biyar_


©️ *OUM MUMTAZ.*



*Promo promo promo! Ga waƴanda suke bibiyar littafin LOKACI NE! Za su iya biyan ₦350 daga yau zuwa ranar Friday da ƙarfe sha biyu na dare promo ya ƙare,zai koma ₦500 kamar yanda yake asalin price ɗin sa insha Allah.*


  _No: 10_

_Free Page_


"To kai Lawal yanzu sabida da Allah ina kai ina dukan Sani? Sanin nawa yake baki ɗayansa da har zaka masa irin wannan dukan,wanda nake da tabbacin idan da yazo da karar kwana mai zaka ce ma duniya?"

Yaya Masa'uda ta fada cike da fushi sosai tana kallon Lawal da yake zaune kan kujera ta three seater shi da Umaima, ita kuma tana zaune kan one seater.

"Amman Yaya ke baki ji kalar cin zalin da shi Sani yake ma Amir bane na tsawon lokaci? Sai ni yau kawai ɗaya da na nuna fushina na dauki mataki zaki ɗauki ƙarya da gaskiya ki hau kai ki zauna sabida Allah?" Lawal ya faɗa shima cike da fushi.

"Ai nasan tin da baka dauki matakin ba sai yau sabida taku ta hado ka da ubansa, sannan kuma Ƴar goal din naka ta nuna maka cewa bata yarda ba sabida ita isashshiya, ana ƙoƙarin kashe wuta idan ta kama, amman ita ƙoƙarin ta shine ta saka masa makamashi yaci gaba da tashi sabida ita makira ce da bata ƙaunar zaman lafiya tsakaninka da y'an uwanka." Tayi maganar tana watsa ma Umaima harara sabida dama can ba wai shiri suke ba.

"Ni kuma miye nawa a nan Yaya? Kowa da yake cikin gidannan ya kwana da sanin halin Sani na cin zalin na kasa dashi, wanda kuma abin nasa yafi yin ƙamari akan Amir tin bai kai haka ba, nasha yima Ummansa magana kan ta tsawatar masa, amman kuma kullum abin ƙara gaba yake ba baya ba, yanzu idan da ace shi ake ma abinda yake ma yaranmu nasan cewa wallahi an ringa tashin hankali da Babansa sabida bazai taɓa yarda ba, amman shine don yau ya kaini bango nayi magana shine zaki ce wai nice mai kunna wuta? Haba Yaya! Kema fa uwa ce, ki duba wannan lamarin mana." Umaima tayi maganar ba tare da ɗaga murya ba, dik da a saurarar farko idan kayi ma muryarta zaka fahimci tsantsar fushin da yake tattare da ita. 

"I, lallai ta tabbata abinda ake faɗa ba kunya bane ya ishe ki Jummala ko wa kike da suna? Wato sabida tsabagen wuyanki ya isa yanka shine ina faɗa kina mai da min sabida baki ɗauke ni da daraja ba?" Inji Yaya Masa'uda cike da mamakin maida mata da magana da Umaima tayi, sabida tsawon zamansu tinda suke hakan bai taɓa faruwa ba, dik abinda za su mata sai dai ta kauda kai albarkacin tana auren na ƙasa da su, wanda hakan ya tabbatar mata da cewa lallai an kaita bango ne, amman da yake girman kai na ɗawainiya da ita ba za ta taɓa karɓar gaskiyar a yanda tazo ba sabida wai kar Umaima ta samu ƙofar raina ta, wanda hakan yasa ta kalli Lawal da ya dafe kansa da hannu bibiyu yana saurarsu ba tare da ya tanka musu ba tace, "Kai kuma da yake shashasha ne solobiyo da har ka buɗe ma ƙadangarun bariki damar raina maka dangi kana jin rashin kunyar da matarka take ƙoƙarin yi min shine ba zaka taka mata birki ba sabida kaine tattabara sarkin soyayya ko?" 

"To sabida Allah me kike son nace ma Umaima Yaya? Tinda nasan ko ke ake musguna ma ƴaƴan ki baza ki iya haƙurin da ita Umaiman tayi ba? Kuma shine don yau ɗaya tayi magana sai ku dinga ganin bakin ta sabida bakwa son gaskiya." Inji Lawal yana kallon Yayar tasu da itama muguwar masifaffiya ce, kusan halinta ɗaya da na Yaya Yusuf, wanda shi nasa ya haɗe masa har da talauci amman ita kuwa ba ƙaramar Hajiya bace, domin kuwa mijinta mai kuɗi ne sosai, gashi kuma ita kanta babbar dillaliya ce da take dillancin ƴan mata da samari zuwa ƙasashen ƙetare domin yin aikatau, wanda kuma idan dai ta sama ma mutum hanyar da zai tafi ƙasar waje akwai percentage ɗin da take samu mai tsoka, wanda a cikin irin haka ne ma da Lawal ya sako zancen a cire masa kasonsa a gidan ta basa million ɗaya da dubu ɗari biyar bayan anyi lissafi,kasancewar anyi ma gidan nasu kudi. 

"I,lallai wuyanka ya isa yanka Lawal, wato ka goyi bayan matarka sama da ni yayarka da muke uwa ɗaya uba ɗaya? To wallahi tallahi tinda naga ba farillan mutunci bane da kai yau ɗinnan ka kwashe kayanka da wannan yakunanniyar matar taka ku bar mana gida, idan kuma kace ba haka ba kuwa sai dai a yanzunnan ka maido min da kuɗi na."

"To shine me? Ga nan kudin naki sai inga ta tsiya tinda dai kinsan ba wai yanke talauci kika bani b....."

Bai karasa faɗar abinda zai ce Umaima tayi wani tsalle da diro gabansa dik da irin ciwon da kanta yake mata ta toshe masa baki tana kallon Yaya Masa'uda tace,"Wallahi tallahi mun yarda a yau dinnan za mu bar muku gidan nan." Tayi maganar a wahale, sannan ta kalli Lawal da yake binta da ido babu damar magana cikin sigar rarrashi da roko tace, "Indai don ta nice kar ka damu Abban Amir,zanyi parking na kayana a yanzun nan, kaje ka nemo mana mota mu koma can gidan ni ko 1 bedroom ka bani, yaso Lawisa ta dauki biyu ta hada da parlo bani da matsala indai hakan zai sa na bar wannan gidan sabida wallahi bazan iya ci gaba da zama a gidannan ba, hakuri na ya kusa ƙarewa, kar muzo muyi abinda za muyi dana sani daga baya dan Allah!" Ta ƙare maganar tana mai fashewa da kuka sosai, wanda hakan yasa Lawal rungume ta a jikinsa dik da yanda yake jin wani irin tsanar ta na taso masa daga can kasan zuciyarsa da bai san musabbabin tsanar ba."Ki shiga ki hada mana komai ki killace sa Umaima, karki ɓata lokaci yanzu zanje na taho mana da mota a kwashe kayan." Lawal ya fada yana bubbuga bayan ta da yasa Yaya Masa'uda buga wani uban salati irin tayi mugun ganin nan na ganin Lawal rungume da Umaima matarsa a gabanta,wanda hakan ya sa ta fice ba tare da ta gama amayar abinda yake cikinta ba.

Fita Lawal yayi, wanda hakan ya bama Umaima damar shiga ɗaki tana faman zubar da hawaye ta sauƙo da akwatinan ta na aure ta kwashe musu kayan sawansu tas da kayan shafe-shafen ta, ta fiddo su ƙaramin tsakar gidansu, sannan ta ɗauko wasu manya-manyan buhuhuna da suke shimfide ƙarƙashin gadonta tin aurenta wanda a ciki aka zubo mata kayan kitchen ɗinta ta kwashe dik wani abinda yake kitchen din kasancewar dama ba wasu masu yawa bane cikin kankanin lokaci ta kammala. Cikin abinda bai wuce awa daya ba ta hada komai da komai, wanda ta zauna kusa da Amir da tin dazun yayi baccin dole bayan ya gama kukansa tana kallonsa, zuciyarta a raunane, tare da rokon Allah kan ya raya mata shi, sannan kuma yasa ya zamto shine sanyin idaniyar ta a nan duniyar zuwa bayan ranta. 

Lawal ne ya shigo, wanda Umaima tasha jinin jikinta sosai ganin yanayinsa, a ranta fadi take Allah yasa ba wani mugun abin bane kuma ya faru sabida tasan may be yaje can gidansa ya samu Lawisa da maganar komawarta. 


*LAWAL*


Zai iya cewa a yanayin zamantakewar sa da Lawisa ya fahimci abubuwa da dama da suka bambanta ta tsakaninta da Umaima, ya fahimci cewa Umaima ba ƙaramar kyauta bace gare sa daga Allah, domin kuwa dai yaga abubuwa mabambanta daga Lawisa, wanda a baya a nasa ƙarancin fahimtar yayi tunanin yanda Umaima ta kasance mai tsananin biyayya da guje ma dik wani abinda tasan zai baƙanta masa haka ko wacce mace take, har ma a wasu lokutan sai yaga cewa Umaima tana zafafa masa akan abubuwa da sai aurensa da Lawisa ta goge masa haddar sa tsaf, ya fahimci cewa a cikin kaso dari na cikin mata zai wuya a samu kaso goma masu hali irin na Umaima, ko miye ya kawo mata ko da ace bai mata ba haka za ta saka hannu bibiyu ta karɓa godiya tare da fatan alkhairi ya biyo baya. Wanda a ɓangaren Lawisa kuwa dik wani abinda ya kawo mata muddin bai mata ba, nan take za ta buga tsalle ta dire ta kushe abin babu kara. Umaima tana masa ladabi, biyayya, kawaici, iya sarrafa abinci, tsafta, bugu da ƙari ruko da addini dikda bata da zurfi sosai a ilimin addinin, ga ta da gudun zuciya, sannan kuma ba ta taɓa rokarsa akan abinda tasan bai zama dole akansa ba, wanda babu abinda zai iya cewa sai godiya ga Allah madaukakin sarki da ya azurta sa da mata ta gari irin Umaima. 

Lawisa kuwa a kaf cikin halayan da Umaima ta mallaka babu abu guda da zai iya bugun ƙirji yace ta kama ko da ƙafafun ta ne, sai zallar kishi na fitar hankali, wanda da farko bai fahimci irin kishin da take da Umaima irin na jahiliyya ba sai daga baya, wanda kuma shi dai tinda yake bai taɓa jin Umaima ko da wasa tayi masa wani ƙorafi ba akan zuwansa gurin Lawisa, da har yake tunanin ko dai sonsa da kaunar sa ne Umaima ta daina? Amman ita fa minti goma idan ya ƙara akan lokacin da ya saba komawa gida ta ringa sababi da mita kenan kan ai hakan rashin adalci ne ƙarara yake gwada mata, yana nuna ma matarsa cewa bata da wani mahimmanci a wajen sa yasa yake son kuntata mata, ko don yaga cewa ba ta haihu dashi har zuwa lokacin bane yake neman ya juya mata baya sabida Umaima ta basa abinda ta gagara basa? Da farko yana ɗaukan abin nata na hankali, sai daga baya kuma yazo ya fahimci abin nata ba na Kari bari bane, hakan yasa shi fara tsayar mata da hakan ya janyo musu kullum cikin faɗa suke kaman filin sansani, har ma yazo ya fara nadamar auren Lawisa da tin farko bai san me ya rude sa akanta ba, tinda dai a fagen kyau da tsarin halitta na dik wani abinda ake bukata a a wajen cikakkiyar mace ko ƙafar Umaimarsa bata kama ba, sai gashi kuma bayan auren ma yazo ya zamana soyayyar da yake mata ya fara bin iska sannu a hankali sabida halayenta marasa tsari da suka fara bayyana kansu a lokacin da ita karan kanta ba ta farga ba, ga shegen roko kamar masifa wanda shi dik a zaman aurensa da Umaima bai san hakan ba, da yake daman can shi a nasa halin babu baima mace kudi cikin tsarinsa har sai idan ta kama dole sabida tsarinsa wanda Lawisa kuwa ta karya masa wannan record ɗin. 

A bangaren zamantakewarsa da y'an uwansa kuwa ƙadaran-ƙadahan, domin kuwa family's nasa wasu irin mutane ne masu shegen ƙananun maganganu da munafurci, ga kyashi da son ganin ɗaya daga cikin su ya wulaƙanta, su kuma yi amfani da wannan damar wajen ɗauke masa wuta baki daya su ja gefe suna gulmarsa kaman ba ciki guda suka fito ba. Sannan gasu dikkansu fitinannu ne na bugawa a jarida, idan kuma kana son jin daɗin zama da su to ya zama dole kaima ka aro halayansu na fitina ka yafa ma kanka sai a zauna lafiya, amman kuwa idan ka kasance mutum mai hakuri da kauda kai sosai za kasha wahalarsu kaman yanda Umaima ta sha a hannunsu, Lawisa kuwa da yake daman itama fitinanniya ce sai suke shakkar shiga shirginta sabida dik wanda yayi mata ba ta taba raga masa. 

Ƙure hakurin matarsa Umaima da yaga sun fara ne yasa shi bukatar a cire masa kudinsa a gidan, sabida yasan kudin zai ishe sa ya saya mata gidan ta mai kyau, idan ya so kuma sai yayi amfani da asalin kudinsa wajen gyara mata, tashin farko kuwa Yaya Masa'uda ta cire masa kuɗin sa bayan sun nemo dillalai suka yi ma gidan kuɗi, wanda kuma sai da ya karɓi kudinsa satin da ya gabata Yaya Yusuf ya sako shi gaba kan lallai-lallai ya ara masa kuɗin ya so daga baya wai zai biya sa cike da gadara, shi kuwa Lawal yayi tsalle ya dire yace bai isa ba, idan dai har da gaske bukatar kudin yake mai zai hana shima yasa a cire masa kuɗin sa? Hakan shine yayi sanadin da har suka samu sabani a yau, ya kuma kaisu ga fadar da basu taɓa yi ba tsawon zamansu, Lawal yana tsaka da dokin fushin abinda ya faru, sai ga Amir ya shigo musu da kuka akan marin da Sani yayi masa, hakan yasa Lawal naɗa masa dukan kawo wuƙa sai da ƙyar aka karɓe sa, ubansa kuwa da dama bayan gama fadan nasu ya fice daga gidan cike da matsanancin fushi, shigowarsa kenan ya tarda ɗan sa mafi soyuwa a wajen sa kwance kan tabarma uwarsa tana shafa masa man zafi fuskarta a matikar hade, ai kuwa yana jin abinda Zainab matarsa ta gama kitsa masa karya da gaskiya ya harzuka ya tada ballin yau mai raba sa da Lawal sai Allah, sannan kuma sai ya bar musu gida tinda bashi da ko taku guda a cikin gidan. Masa'uda ya kira a waya, ita kuma da tazo taga dukan da Lawal yayi ma Sani sai ta hau sababin cewa wannan ai niyar kashe dan yaso yayi, Zainab da yake a matikar fusace take ta kuwa sake kwararo ma Yaya Masa'uda karya kan cewa, ai Umaima ce ta zugo Lawal ya kusan kashe mata ɗa, da yake dama idan dai mutum yayi magana da budaddiyar sauti cikin gidan ana ji. 

Yana fita daga gidan bayan ya umarci Umaima da ta haɗa musu kayansu, acaba ya tara zuwa can gidansa da ya ajiye Lawisa, yana jin yanda yake kokawa da zuciyarsa wajen ganin ya danne tsanar Umaima da yake taso masa daga can kasan zuciyarsa a gefe guda, a kulle ya tadda gidan, wanda hakan yasa shi mamakin inda ta tafi ba tare da ta naimi izininsa ba, dik da cewa yasan ba wannan ne karo na farko a fitar ta ba tare da neman izini daga wajen sa ba. Da yake daman yana da makulli cirowa yayi daga aljihunsa ya buɗe gidan. 

Ƙaramin tsakar gida ne mai ɗauke da part guda ɗaya, wanda a farko idan ka shiga parlo ne, daga cikinsa kuma akwai ɗaki guda ɗaya daga bangaren hannun hagu, hannun dama kuma akwai 2 bedrooms da basu kai girman ɗakin da yake ta gafen hagun ba, daya daga cikin dakuna biyun dauke yake da toilet guda daya, kaman yanda ɗakin da yake ta ɗayan ɓangaren ma yake ɗauke da shi, parlon akwai kujerun Lawisa a ciki, sai kuma dakin da yake a bangaren hannun hagu set ɗin gadonta ne a ciki, wayan nan biyun da suke manne da juna kuwa babu komai a ciki tinda daman kayan Lawisa ba wani na azo a gani bane, hakan yasa Lawal yanke hukuncin baima Umaima 2 bedrooms ɗin tayi maleji kafin ya samar mata da nata mahallin, ya so suyi amfani da kitchen ɗin dik wacce take da girki, wasu kayayyakin sa ya tattara sannan ya fito ya kulle gidan, akwai wani abokinsa da yake tuƙa babbar mota yana diɓan yashi, ya ƙira sa a waya Allah yasa a lokacin bai da deban ƙasa, ya hau machine ya dawo unguwar tasu ya tarda abokin nasa a kofar gida da wasu yaransa guda biyu har sun iso, tare suka shiga bisa ga Umarnin Lawal din bayan ya shiga ya faɗa ma Umaima ta saka hijab.



*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*


1- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*

2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*

3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*

4- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*

5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_

_LITTAFI BIYU:- ₦800_

_LITTAFI UKU:- ₦900_

_LITTAFI HUDU:- ₦1000_

_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_

_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...

*6314170140*

*FIDELITY BANK*

*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*


*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_

_LITTAFI BIYU:- 600f_

_LITTAFI UKU:- 650f_

_LITTAFI HUƊU:- 750f_

_LITTAFI BIYAR:- 850f_


'''ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-'''


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*

*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*

*_•TICTOK 1500_*

*_•INSTGRAM 1500_*

*_•FACEBOOK 1500_*

*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


'''ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)'''


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*


MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*