LOKACI NE

Page 12

by @oummumtaz123

*LOKACI NE...!*

_Fitattu Biyar_


©️ *OUM MUMTAZ.*


*Promo promo promo! Ga waƴanda suke bibiyar littafin LOKACI NE! Za su iya biyan ₦350 daga yau zuwa ranar Friday da ƙarfe sha biyu na dare promo ya ƙare,zai koma ₦500 kamar yanda yake asalin price ɗin sa insha Allah.*


_No: 12_



"Abban Amir dan Allah idan akwai wani abin da na maka, wanda ban sani ba, ka yi hakuri ka yafe min, bazan iya jure wannan yanayin naka ba ka tausaya min." Umaima ta fada cike da sanyin murya, tana zube kan gwiwowinta gaban Lawal da yanzu shigowar sa gidan. 

Lawal da yaji numfashin sa na ƙoƙarin ɗaukewa sabida tsananin warin da yake shaƙa da ga wajen ta yayi hanzarin ficewa daga parlon wani irin amai ta taho masa gadan-gadan, a bakin barandar parlon ya tsuguna ya dinga kela amai sabida tashin zuciya. Umaima da take nan a yanda ya bar ta, hawaye na zubo mata wani na koran wani ta taso da hanzarinta jin aman da yake, kaman zai zubo da kayan cikinsa. Lawal da yake neman fita hayyacinsa kuma jin wannan warin yana sake doso inda yake yasa wani aman sake taho masa da tsananin ƙarfi, isowar ta wurin kuwa ji yayi lumfashin sa ya dauke na wucin gadi, ya tattaro dikkan wani ƙarfin da ya rage masa ya hankaɗa ta daga ƙoƙarin dafa sa da take, wanda hakan yayi sanadiyar faɗuwarta ƙasa war-was, sabida taji yanda abin yazo mata a un-espected,wanda hakan yayi sanadiyar da goshinta ya bugu da jikin windo. 

Kuka mai tsananin ƙarfi Umaima ta fashe da shi mai cike da tashin hankali, domin kuwa dai ita a iya tsawon zamanta da Lawal ba za tace ga wani taƙamai-mai laifin da ta aikata masa ba da har ta cancanci fuskantar wulaƙanci da kuma ƙasƙanci daga wajensa. Ga kuma azabar da take ji a goshinta da yasa ta rintse idanunta. 

Lawal kuwa tin hankaɗa ta da yayi da gudun gaske ya fice daga gidan, ya samu kan wani dutse da yake kofar gidan karkashin wani bishiya ya zauna, yana mai da lumfashin wahala. 


Umaima


Sai da taji kan ta da zuciyarta sun lafa mata daga radadin da suke mata kafin ta mike da niyyar shiga dakinta, sai kuma ta dakata sabida ganin inda Lawal yayi amai, wanda hakan yasa ta zagaya wa bayan ɗakin ta inda suke ajiye abin zuba shara ta ɗauki faka, har za ta juya haka nan taji kawai bari ta daibi ƙasar da za ta je ta rufe aman da shi, ta sunkuya kusa da bolar wajen da taga alamun ƙasar gurin zai yi daɗin ɗeba, cika fakar tayi da kasan wajen taje ta zuba amman bai rufe mata yanda take so ba, hakan yasa ta sake komawa taje ta sunkuya da yake ba ta jin ƙarfin jikinta kawai sai ta zauna a wajen, tana cika hannun ta dika biyu tana juye wa a fakar, hannun ta ne ya sauka akan wani dunkulallen tsumma da aka yi ma kyakkyawan dauri,har za ta wurga abin shara sai kuma tayi sak, da mamaki Umaima take kallon kyallen sabida sak irin na dan kwalin ta da sati daya da ya wuce taga an yankar mata, wanda take mamakin wanda zai aikata mata haka, sanin da tayi cewa a tsawon zaman ta hakan bai taɓa faruwa da ita ba, zuciyarta ce ta umarce ta da ta kunce. 

Gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin laya ce cikin ƙyallen ɗan kwalin, wanda hakan yasa ta miƙe a kidime ta fara warware wa, tana gamawa kuwa wani farar takadda ta fadi ƙasa, jikinta yana karkarwa ta sunkuya ta ɗauko, ba ta damu da tsananin warin jabar da yayi ma hancin ta maraba da zuwa ba, wani mitsitsin gawan jaba ya faɗo daga cikin takaddar a lokacin da ta gaba buɗe linkakkiyar takardar, sunan ta ne ya bayyana ɓaro-ɓaro da harshen larabci 'KHADIJA USMAN BAƘO', sai kuma daga kasan sunan ta aka rubuta 'LAWAL SA'IDU MARAYA' dik da harshen larabci, sai kuma wani chakuɗaɗɗen yaren da ba ta fahimta ba, inda ta tsinto 'LAWISA' rubuce da manyan harrufa na ABCD daga can ƙasa. 

Zufa taji ya jika mata rigarta sharkaf, sabida tashin hankali sai faman zare ido take, domin kuwa indai a yanda tayi hasashe da kuma tunanin ta ya bata dai-dai to tabbas warin da Lawal yayi iƙirarin tana yi akwai saka hannun Lawisa dumu-dumu, wanda idan ba ta manta ba jiya da safe sai ta tayi mata wata da magana wanda a lokacin Umaima ba ta bai ma maganar mahimmanci ba sai a yanzun da take ganin wannan abu mai kama da almara, tana tunanin mai nene Lawisa ta ɗauki duniyar da har akan ɗa namiji za ta iya yin shirka sannan kuma ta hada ta da warin jaba don kawai sun hada miji? Wanda inda ace zafin kishi ne ma ita ya kamata ta nuna sabida a irin yanayi na wulakanci, kaskanci da cin amanar da Lawal yayi mata a lokacin da zai auro ta? Ta ɗauke kai ta nuna komai ba komai ba dik don sabida a zauna lafiya amman shine ita Lawisa ta rasa da mai za ta saka mata sabida son zuciya sai warin jaɓa? 

Umaima tana kuka da majina yana zuba a hancinta, ta ɗauko ashana tazo ta cinna ma shirgin layar wuta, bayan tayi dogon addu'oin neman tsari daga mutum da aljan,aman da ba ta kwashe ba kenan tayi shigewarta daki tana kukan da ta jima ba tayi irinsa ba, inda ma Allah ya taimake ta Amir yau bai ma kwana a wajen ta ba, can gidan Maimuna jiya Amina tazo ta dauke sa suka tafi. 

Ba ta san tsawon lokacin da ta ɗauka tana saƙe-saƙe ba, taji muryar Lawal yana kwaɗa mata kira da yasa gabanta ya yanke ya faɗi, dik da wani sashe da yake zuciyarta na tabbatar mata da cewa wata ƙila kukanta ne yazo ƙarshe sanadiyar ƙona wannan layar da tayi, da gaggawa ta mike tsaye tana kallon Lawal da ya shigo dakinta, wanda ko da gigin wasa tin last week da ta gama jeran kayan ta bai sake shigowa ba. 


Lawal 


Ya ɗauki tsawon lokaci zaune akan dutsen kafin ya dawo hayyancinsa, wata yarinya mai sai da pure water ya tsayar ganin za ta wuce, ya sayi guda biyu, kurkure bakinsa yayi sannan ya shanye guda ɗayan. 

Yana nan zaune kaman wanda aka zare ma allura cikin ƙirjisa haka yaji tsanar Umaima babu ko digo, tsanar Lawisa na maye masa gurbin linkin ba linkin tsanar da yayi ma Umaima,ya tuno yau tsawon sati kenan yake ma Umaima wulakanci akan warin jaɓar da take, tausayin ta ne ya mamaye zuciyarsa yana jin tsananin kunyar ta na lullube sa, lalle ya aikata ma Umaima abubuwa da dama wayan da ba ta cancanci haka daga wajensa ba, duba da irin soyayya ta gaskiya da ta nuna masa wanda babu algus, da sauri ya tashi ya shiga cikin gidan yana kwaɗa mata kira,har sai da ya danganta da ɗakin nata. 


*UMAIMA & LAWAL*


Akan gwiwowinsa Lawal ya zube yana kallon Umaima da ta zuba masa ido tana kallon sa hawaye na sauko mata daga cikin idonta. 

"Umaima don Allah, don darajar Annabi Muhammad Rasulillahi(SAW) kiyi hakuri ki yafe min abinda na miki tin farkon haɗuwa ta da ke har zuwa yanzu da abubuwa da dama suka faru wanda ni karan kai na bansan miyasa nake jin tsanar ki da kuma tsananin jin warin jaɓa daga wajen ki ba, nasan a zaman aure da kika yi da ni ban ƙare ki da komai ba sai tsananin bakin ciki da damuwa, don Allah ki yafe min... " Lawal ya ƙare maganar yana fashewa da wani irin kuka da tin rasuwar mahaifinsa da mahaifiyarsa bai sake irin sa ba sai a yau,na tsananin jin tsanar kansa sabida yasan ya cutar Umaima mai tarin yawa cikin zamantakewarsu. 

Umaima da take tsaye a bakin gadonta idon ta na zubar da hawaye na tausayin kanta da kuma shi Lawal ɗin da ta riga ta fahimci cewa abubuwan da dik yayi mata ba cikin hayyacinsa yake ba, haɗuwa yayi da muguwa kuma makirar mace tace, "Kar ka damu Abban Amir wallahi daman ni ban rike ka a zuciya ba, ubangiji Allah ya kare na gaba yasa kuma mufi ƙarfin zuciyarmu." Tayi maganar cikin sanyin murya wanda har zuwa lokacin hawaye bai bar zubowa daga cikin idanunta ba. 

Da sauri Lawal ya taso yazo ya rungume Umaima cikin tsananin son ta da kuma kaunar ta da a kullum ba ta gajiyawa wajen nuna masa tsananin so da kauna, da kuma fahimtar sa ko da ace ita ya cutar, wanda daman shi kam zai iya dafa alkur'ani a dik iya tsawon zaman sa tare da ita bai taba kama ta da laifin ha'intar sa ba, wanda yake jin a kaf cikin mazan duniya a wannan lokacin babu wani namijin da ya kaisa dace da samun mace ta gari kaman Umaima, dik dai ance tsakanin harshe da hakori ma ana samun saɓani, wanda idan wani matsala ya faru a iya tsakanin su suke solving na dik wani matsalar su, Umaima ba ta taɓa kaisa gaba wajen iyayensu ko yan uwa ba da sunan sulhu.


Bayan shuɗewar awa ɗaya da rabi.

Umaima da Lawal zaune bakin gadon ta, sunyi wanka sun canza kaya, Lawal sai faman tarairayar Umaiman yake dik don sabida ya wanke mata zuciyarta akan ɓata mata da yayi, ko da ace ba za su fita gaba ɗaya a yanzun ba. 

Umaima da babu abinda take a cikin zuciyarta sai faman gode ma Allah akan kawo mata mafita cikin sauki ba tare da tsumi ko dabararta ba kafin abin yayi nisa, sai faman biye sa take tana nuna masa komai ba komai ba, inda suna cikin wannan moment din mai matikar dadi a wajensu Lawisa ta fado dakin kamar wacce aka koro ta fuskarta afujajan. 


*LAWISA* 


Yau da safe ta tafi gidansu wajen mahaifiyarta domin kai mata rahoto akan irin yanda aikin da boka na kan tudu yayi matikar tasiri, wanda suka fita tare da Lawal akan zai yi tafiya, bazai dawo ba sai bayan kwana biyu. 

Suna nan tare da mahaifiyarta suna hira cike da nishadi suna shewa, kawai sai ji tayi gabanta yayi matsanancin bugu, wanda hakan yazo mata da tsananin ciwon kai da yasa ta dafe kanta. 

"Ke Lawisa kashi ki ka yi ne a zaune nake jin wani irin wari yana tasowa daga inda ki ke?" Ƴar Madina ta faɗa tana toshe hancin ta, tare da mikewa daga kusa da Lawisar sabida warin yana sake girmama. 

A dan tsorace Lawisa tace, "Mama nice nake wari kuma?" 

"Kwarai ma kuwa, gashi wani warin mushen jaɓa da nake ji daga inda kike zaune, wai kina nufin babu abinda kike ji?" Yar Madina ta faɗa tana idasa ficewa daga dakin, hannunta kan hancin ta a toshe. 

"Mama kaina ciwo yake min zai tsage gida biyu, kizo ki taimaka min." Lawisa ta faɗa a wahale sabida jin wani irin ciwo da kanta yake mata kaman ya tsage gida biyu. 

"Ai kuwa dai bazan iya shigowa wannan warin ya min illa ba don ubanki." Ƴar Madina ta faɗa tana daga murya, wanda hakan ya janyo hankalin matan gidan, da kuma yaran gidan baki ɗaya. 

Kuka Lawisa ta fashe da shi cike da tashin hankali ta taso a daddafe ta fito ƙofar ɗakin, wanda hakan yasa Ƴar Madina zurawa da gudu zuwa wajen da kishiyoyin ta suke tana fadin, "Amman dai Allah ya kwashe maki albarka Lawisa, ina fada miki irin warin da kike mai ta da min zuciya, shine don iskanci na fito daga dakin za ki sake biyo ni waje salon ki ƙarasa ni?" 

"Mama na shiga uku na, kar dai abin wajen na kan tudu aka sami yar iskan can ta tone? Kinsan fa yace dik ranar da muka yi saken da wani ya tone shikkenan ƙai-ƙayi ne zai koma kan masheƙiya, kuma abinda zai faru da ni sai ya linka nata, tinda ita iya shi kaɗai ne zai na jin wari daga wajen ta, amman idan ya dawo kaina dik wanda ya rabi inda nake ko da kuskure warin zai dama." Lawisa tayi maganar cikin tsananin kuka, mai haɗe da tashin hankali, wanda tayi wannan maganar ma ba tare da ta kula da cewa gidan nasu kowa da kowa kallon ta yake ana toshe hanci ba.

Ƴar Madina kuwa, jin abinda Lawisa ta faɗa ne, wanda ita ko da wasa bata taɓa kawo hakan a ranta ba, ta daura hannu aka, ta yanka wani irin ihu,cikin tsananin tashin hankali da manta inda take tace, "Shikkenan nan mun mutu mun lalace idan cewa kishiyarki ta tone wannan layar, kiyi maza-maza kije ki tabbatar, sannan kuma kiyi dik yanda za kiyi sabida kar aje mijinku ya koma, kinsan idan har muka yi saken da ya sadu da ita shikkenan mun bani daga ni har ke, sabida ba ke kaɗai abin zai shafa ba, har da ni kaina tinda tare muke zuwa wajen na kan tudu."

Kamin ma ta rufe baki, Lawisa da babu ko takalmi a ƙafarta, ta falfala da gudu, sauran mata da kuma masu wayon da suka fahimci inda maganar ya dosa suka saka salati, suna kallon Ƴar Madina da ta zame musu sabuwar halitta, wanda suka dauka abin nata a iya cikin gida ya tsaya, ashe bai tsaya din ba, har sai da tayi sanadiyar da mugun alkaba'in ta ya shiga cikin rayuwar auren Ƴar ta? 

Dik ɗan acabar da ta tarar, yake guduwa sabida warin da yake masu welcome, bugu da kari kuma yanda suke kallon ta kamar wata mahaukaciya ko takalmi babu a ƙafarta, ga kuma uban kukan da take har tana shidewa majina da hawaye ya dame mata fuska kaca-kaca. Da kafanta ta iso gidan dik da uban nisan da yake tsakanin gidansu da nan inda take auren. 

Gabanta ya faɗi sosai ganin takalman da Lawal ya fita da su a ƙofar parlo, wanda hakan yasa ta ida shigewa cikin parlon, cak ta tsaya tana kallon dakin Umaima da take jiyo muryar Lawal a kwance, wanda za ta iya rantsewa da Allah a iya tsawon zaman da tayi da shi na shekara biyu da watanni bai taɓa faɗa mata maganganu masu dadi da suka ko kama kafan wanda yake fada ma Umaima ba, wanda hakan yasa ta tura ƙofar dakin a haukace tana hakin wahala. 


UMAIMA, LAWAL & LAWISA. 


Lawal ya tashi kaman wanda yaga wani mugun halitta yana toshe hanci sabida uban warin da yayi ma hancin sa sannu da zuwa, Umaima da take zaune itama ta toshe hancin ta tane zare ido, wanda zuciyarta ya fara tashi sosai ba kaɗan ba. 

Cike da karaji Lawisa ta ci gaba da tinkaro inda suke, su kuma suna ja da baya tace, "Lawal dan kutumar ubanka ka faɗa min ka sadu da wannan dangin ibilis da fir'aunan ko kuwa?" 

Umaima da ta dake a tsaye ta sauke hannun ta akan hancinta, dik da irin warin da yake kaima kayan cikin ta farmaki cikin tsananin fusatar da tinda take ba ta taɓa shiga ba tace, "Kece dai dangin ibilis da fir'auna don ubanki Lawiza kike ko waye? Dubun ki ya cika akan zalincin da kika min ba tare da nayi maki komai ba sai don kawai mun haɗa miji, wanda kuma ke karan kanki kinsan cewa idan ma kutse ne, kece kika yi ma rayuwar aure na kutse da ya kamata ace na ɗauki mataki akan ki amman ban ɗauka ba sabida haka nan auren ki yana cikin littafin Lawal, shine sabida jahilci da dabbanci za kiyi shige da ficen da yayi sanadin da mijina zai juya min baya, sannan kuma ya dinga jin wari a dik sa'adda ya doso inda nake, to Allah ya toni asirin ki, kuma insha Allah sai Allah ya saka min akan zalincin da kika min bazan taɓa yafe miki ba, muguwa azzaluma mai bakar aniya, wacce ba ta samu tarbiyar kwarai daga gida ba sai na bin malaman tsibbu."


*FITATTU BIYAR 2023 paid books:-*


1- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*

2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*

3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*

4- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*

5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_

_LITTAFI BIYU:- ₦800_

_LITTAFI UKU:- ₦900_

_LITTAFI HUDU:- ₦1000_

_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_

_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...

*6314170140*

*FIDELITY BANK*

*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*


*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_

_LITTAFI BIYU:- 600f_

_LITTAFI UKU:- 650f_

_LITTAFI HUƊU:- 750f_

_LITTAFI BIYAR:- 850f_


'''ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-'''


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*

*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*

*_•TICTOK 1500_*

*_•INSTGRAM 1500_*

*_•FACEBOOK 1500_*

*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


'''ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)'''


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*


MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*