ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 03

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


     

        *🅿️03*


Suna tafe a cikin motan Fahad ya kalli Asma'u yana faɗin "Wai ni rabin ranmu ya maganar abokina ne Ja'afar? Har yanzu banji wata magana mai ƙarfi ba...?

Kallonshi tayi kafin ta ɗan murmusa tace "Kai zan tambaya abokinka ne, ni ai banda labarinsa yanzu." 

Ta faɗa kai tsaye tana maida hankalinta ta gefen window tana bin motocin dake wucewa da kallo, furzar da numfashi yayi kafin yace "Kinsan Allah Ma'u? Na daɗe rabona da waya da Ja'afar. sai jiya rabin ranki tasa na laluboshi, ina fara mai maganarki naji ya fara min zille zille bai bari munyi maganar ba ya yanke kiran."

Ajiyar zuciya ta sauke tayi shiru tana kallon gabanta kafin tace cikin sanyin muryanta "Nima nafi sati biyu rabona da jinsa awaya. tun ranar da yazo na gaya masa saƙon Abba, da yace ya fito inda gaske yake, wlhi tun daga ranar bai kara kirana ba har yau. sai ni ne da naji shirun yayi yawa na kirasa sai kuma akayi rashin sa'a matarsa ta ɗauka. Kaji irin zagin rashin mutuncin data min? Tun daga ranar na goge nombarsa acikin wayata, na ganeshi shima yana cikin layin sauran ne, da sunji maganar su fito ayi maganar aure sai su gudu." ta ƙarashe faɗa muryanta na sarƙewa kamar zatayi kuka..

Ran Fahad ya sosu ya kalleta cikin tsantsar tsausayawa yace "Ita matar tashi..? Kuma bai kiraki daga baya ba..?" Gyaɗa mai kai tayi kafin tace "Tun daga wannan ranar bai ƙara kirana ba, ni kuma sai na rabu dashi, inaga nidai kawai bani da rabon aure ne a duniya Fahad." tana faɗa wasu ƙwallah masu zafi suna zubo mata...

Yana karya kwanar gidansu yace "Assha! Haba Asma'u ya zaki ce haka, ashe kin ma fidda rai da rahamar ubangiji kenan? Ki kwantar da hankalinki keep on praying Asma'u muma masoyanki muna tayaki insha Allahu mijinki na tafe wanda kowa sai ya yi mamaki da ikon Rabbi.." maganarsa ta sanyaya mata rai, duk da koda yaushe shida matarshi kalamansu kenan agareta, kuma bakomai bane yasa suke faɗar hakan ba, sai don kawai suga ta kwantar da hankalinta. tayi ta saka farin ciki da walwala a zuciyarta kamar kowa, shiyasa duk duniya bayan mahaifiyarta bata da kamar Aisha da mijinta.

Bata samu zarafin sake magana ba, ya faka motarsa a ƙofar gidansu daidai lokacin da ake ta fitowa daga masallaci gashi a ƙofar gidansu hasken ƙwai ya gauraye wajen babu wuta amma an tada inji, gabanta ne ya faɗi ganin Abba shida su Walid sun fito daga masallacin dake gefen gidansu tana sallama da Fahad suka haɗa ido, gabanta ya faɗi ras! Da sauri ta ɓalle murfin motar ta fito tana ɗagama Fahad hannu, baima lura dasu Abba ba shiyasa bai fito sun gaisa ba yaja motarsa yayi kwana ya fice daga layin.

Jikinta asanyaye tazo zata shiga gida taji muryan Abbanta yana kiranta.."Asma'u.." Muryarsa a kausashe, da rawan jiki ta juyo tana faɗin "Na'am Abba...ina yini..?" Bai amsa mata ba illah binta da wani irin kallo da yayi kafin yace "Mu shiga gidan tukunnah.." ya faɗa yana yin gaba, shi ya fara shiga cikin gidan, hannunshi riƙe da na Walid, dayan kuma yana riƙe dana Khalipa. bayanshi tabi jikinta ba inda baya rawa don Asma'u akwaita da tsoro sosai.

Suna shiga harabar gidan ya waigo yana kallonta cikin muryar dattako yace "Meke tsakaninki da Fahad ne Asma'u..?" Cikin wani yanayi ta ɗago tana kallon Abban nata cikin mamaki tace "Wane Fahad ɗin kuma Abba..?" Fuska ya ɗaure tamau kafin yace "Wane Fahad kika sani ke? Fahad dai mijin kawarki Aishan gidan Mallam Wada nake nufi."

jin haka yasa jikinta ya ƙara yin sanyi kanta na duƙe tace "Laaaa Abba wlhi babu komai, na biya ta gidan ne da muka tashi aiki na duba Amir baya jin daɗi. shine ya matsa sai ya kawo ni gida, tunda yammah tayi"

Ta faɗa tana sadda kanta ƙasa, ya daɗe yana kallonta kafin yace "Yayi kyau, amma ki kiyaye" daga haka bai ƙara cewa komai ba ya sakai ya shige cikin gida.

Da kallon mamaki Asma'u ta bishi kafin ta riƙe kai tana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu kenan har Abba sai da aka kaima wannan gulmar da aketa yawo da ita agari? kuma wlhi tasan daga gidansu maganar ta fita waje har ta kai gidansu Aisha.

wai ita Asma'u wacce suka taso tun suna yara ita da Aisha tare sukayi yarinta suka girma makarantan islamiya tare boko ma tare su wuni tare wata rana ma tare suke kwana, amma ace wai awayi gari itace zata so mijinta ta aureshi, wanda duk duniya bayan iyayenta suna cikin jerin mutane masu matuƙar muhimmanci arayuwarta, tayi tirr ga duk munafukin da yake ƙulla wannan abin har ya zama ana zarginta, har abada ko da yau Aisha zata faɗi ta mutu ta bar duniya sai dai ta mutu ba miji. amma bazata taɓa auren Fahad ba, cike da wannan takaichin ta shiga cikin gidansu, su Baba Lami kaɗai ta gani atsakar gida suka gaisa suna mata barka da dawowa.

ɗakin Umma cike da hayaniya, nan taji muryarsu Anty Ruƙayyah da Anty Bilki suna ta hiransu da dararraku bata leƙa ɗakin ba kawai ta wuce ɗakin Anty Amarya ta leƙa suka gaisa. kafin ta wuce zuwa ɗakinta makulli tasa ta buɗe ƙofar ɗakin kafin ta tura ta shiga, ranta duk a cunkushe saboda ɓacin rai, takalmin ƙafarta kaɗai ta cire da safa sai hijabin jikinta da jakar hannunta. 

ƙofar toilet ɗinta ta tura ta shiga domin ɗauro alwala don lokacin sallar Magrib har ya fita ana shiryen shiryen kiran sallar Issha'i ne.


***


Bauchi.


Zaune yake a gaban Hajiya inda ita kuma take zaune kan kujera. dogon matashin saurayi ne fari yana sanye da shadda mai ruwan toka ɗinkin tazarce kansa ɗauke da hular zanna bukar, daga yanayin fuskarsa zaka san yana cikin tsantsar damuwa, cikin wani yanayi yake faɗin "Wai Hajiya kina nufin Baffa ko awaya bai kiraki ya gaisheki ba..?"

Cikin damuwa Hajiya tace "Bai kirani ba Yusuf, wai anya ma kuwa Baffa yana lafiya.? Kodai bai da lafiya ne yana chan kwance rai ga hannun Allah.?" Kai ya girgiza yace "Lafiyarsa ƙalau Hajiya ko last week munyi waya dashi na sanar dashi baki jin daɗi. Kuma ya nuna min zai kiraki har na mai faɗan ya kamata yazo ya ganku keda Mallam ya roƙi gafararku, ni kafin mu rabu ya tabbatar min da yanason yazo abubuwa ne suka sha kanshi.."

Tagumi Hajiya ta zabga cike da damuwa tace "Oh ni Hajara, Ya Allah ina roƙonka ka dawo min da ɗana Baffa gareni." Ta faɗa tana sharan ƙwallah kamar wata yarinya. Yusuf ya kalli hajiya cikin ɓacin rai yace "Don girman Allah hajiya ki daina zubarma da Baffa hawaye, kefa uwace a garesa wannan kukan naki wlh in baki yafemai ba Allah zai kamasa" batayi magana ba illah share hawayen data keyi cikin yanayin damuwa.

Wayarsa ya zaro acikin aljihun wandonsa yana cewa "Bari na kirasa, ni zan gaya mai gaskiya in yaji ruwansa, in bai ji ba ma ya rage nasa. don baida kamar ku kar ya ga kamar don Mallam ya kawo ido ya sanyamai shikenan ya sallama shi ba, wlhi matukar bai zo ya roƙi gafaranku ba ya mutu cikin wannan halin wuta zai shiga" 

ya faɗa yana manna wayar a kunnensa cikin ɓacin rai, amma haka wayar ta gaji da nemam ɗauki ta yanke ba'a ɗaga ba, bai haƙura ba ya ƙara kira a karo na biyu, nan ma ba'a ɗaga ba sai ana ukun ne aka ɗaga kiran.


****


Zaune suke su huɗu asaman wani makeken dinning suna breakfast lokacin around 11 ne na safe. da yake yau ɗin takama weekend ne, Wasila na kusa da gogan nata ta chaɓa uban ado ana wani kwarkwasa, sai Jamila da Hafsa dake gefensu suma cikin tasu kwalliyar amma su dressing ɗinsu babu kyan gani kamar wasu ya'yan arna.

Karo na biyu kenan wayarsa na ɗaukan ruri sai ya daga yaga mai kiran sai ya share, ganin haka yasa Wasila jikinta bai bata ba, cike da kissa da makirci tace "My Dee wai wake kiran ka ne kake ƙin ɗagawa..?"

Bai ba maganarta muhimmanci ba. sai da ya kai lomar chips ɗin daya ɗebo bakinshi kana yace "Yusuf ne." ya fad'a cikin halin ko in kula, gaban Wasila ya faɗi amma sai ta basar cikin nuna wani yanayi tace "Wane Yusuf ɗin..?" Bai kalleta ba yace "Wanda dai kika sani, Yusuf ɗina mana."

Wani abu taji mai girma ya tokare mata a maƙoshi jin ya ambaci Yusuf di'na, kunu tasha tana wani faman zare idanu, kiran ya sake shigowa akaro na uku, M.A ya ɗaga kiran dai-dai lokacin da yake share bakinshi da tissue yace "Kai ɗan wutar ciki ne wlhi, ka kikkira kaji shiru baka ma mutum uzuri ko yana cikin wani laluri?"

ya faɗa kai tsaye daga chan ɓangaren Yusuf ya saki ajiyar zuciya jin Baffa ya ɗaga kiran, ganin yadda Hajiya ta saka mai ido ne yasa ya saka mata wayar a speaker tana jin muryan Baffan.

Cikin ƙuluwa Yusuf yace "Dallah Mallam gafara chan, wai ka manta abunda na kiraka last week na gaya maka ne..?" Ɗan shiru yayi kafin yace "Kamar name kenan, sorry na manta kasan yanayin aikin namu? muna yawan shiga busy ne sosai" Kai Yusuf ya girgiza kafin yace "Na rashin lafiyar Hajiya Abdallah, Hajiya da Mallam suna buƙatarka ka duba ka gani ka kusa shekara guda baka zo gida ba hatta da a waya ka daina nemansu. ka manta sune iyayenka waɗanda baka da kamarsu? Hajiya kullum jininta cikin hawa yake saboda rashin ka Baffa, koda yaushe a cikin zubda maka hawaye take, kana tunanin in ka mutu cikin wannan halin Allah zai yafe maka..?" ya faɗa cikin sanyi da lallami ta sigar nasiha,

Gaba ɗaya kalaman Yusuf sun kashema M.A jiki, yayi shiru bayan ya saka hannu ya Dafe kanshi, Wasila dake gefenshi dayake ya ɗan saki karar wayar tana jin duk abunda Yusuf ɗin yake faɗi, tuni taji zuciyarta ta rine ta koma baƙinƙirin saboda tsantsar baƙin ciki da takaichi, waye yake neman ɓata mata aiki..? ai bata gama mamaki ba taji M.A yana faɗin "Am so sorry Yusuf, wlhi inaso nazo naga su Hajiya da sauran yan'uwana. Ammah duk sanda nayi niyyar tahowa sai naji kwata-kwata garin ya fitar min aka ko waya na daga da niyyar kiransu, sai wani abu yazo ya hanani kabama Hajiyata haƙuri, kace mata ta cigaba da min addu'a insha Allahu na kusa zuwa gareta da ikon Allah.."

Ya faɗa idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur, cike da rauni bai jira cewar Yusuf ɗin ba, kawai ya katse kiran yana jin wani irin abu ya tokare mai ƙirji, kwata-kwata baya ƙaunar yaji an ambaci garin Bauchi yanzun nan zaiji duk zuciyarsa ta ɓaci yaji baya ƙaunar zuwa garin, iyayensa kuwa gasu aranshi amma an ciremai duk wani tsausayinsu balle har ya tuna dasu yaji ƙansu yaje ya dubosu, gashi abun na damunsa amma ya rasa wazai faɗama damuwarsa ya tallafa masa yaji sanyi.

Wasila da ƙirjinta ke tsananta bugawa jin kalaman Abdallah ta matso kusa dashi cike da makirci tana faɗin "What wrong my Dee naga ka shiga cikin wannan hali.?" Bata ƙarasa ba ya tashi daga wajen ba tare daya kalleta ba, cikin wani irin yanayi ya haura sama kamar wanda bai da lafiya, da kallon mamaki ta bishi, ita da sauran ƙannenta.

Tana jin ƙarar buga ƙofarsa. miƙewa tayi ta riƙe kugunta da hannuwanta tana zagaye gurin take faɗin "Ni za'a batama aiki ? Toh wlhi baku isa ba, nayi alƙawarin mallakar Abdallah ni kaɗai har abada. saboda haka bazan taɓa bari ya dawo gareku ba," ta faɗa cike da tsantsar tashin hankali tana wani huci fuskarta a ɗinke babu wani annuri.

Jamila ce tace "Anty Wasila sai fa kin mike tsaye, zuwan da mukayi wajen boka last nida Momcy dama ya faɗa mana komai na shirin lalacewa Saboda Mamanshi da Babanshi basu zauna haka ba. hatta da yan'uwanshi mata suma tsaye suke a kanshi da addu'o'i kuma wannan Yusuf ɗin ma shima har sakawa yake ana mai saukan Alqur'ani, duk don alalata miki aiki.."

 Wata uwar ashar ta danno ta lailalaya kafin tace "Ni zasu tozarta? Ni WASILA Wlhi basu isa ba! Ban fito ba sai da na shirya, ai wannan shegen tsohon nashi tun lokacin aurenmu sai da Dukaji ya sanar dani baya wasa, hakama uwar tashim dukkansu ƙyalesu nayi sai na rabasu da abunda suka fiso, shi kuma wannan ƙaramin alhakin Yusuf so nake na mai zuwa ɗaya na gama dashi, wlhi matuƙar boka da Mallam na cikin duniyar nan sai nayi FARRAƘU a tsakanin Abdallah da iyayenshi da ƴan'uwanshi na ƙara mallakarshi ni ɗaya tal a hannuna.."

Ta faɗa tana ƙara jadadda kalamanta, Hafsat ce ta miƙe tana mata jinjina tace "Muj riga mun sanki Sister. in kikace zakiyi tofa sai kinyi ne, ya kamata keda Momcy ku sake wani sabon shiri, tun kafin su karkatar da hankalinsa wata rana kiji labarin ya tafi Bauchi baki sani ba" 

Cikin murmushin nasara tace "Ina! In su a tsaye suke toh wlhi ni Wasila a tafe na kwana, mu zuba dani dasu shege ka fasa, bani aron wayarki na kira Momcy tawa na barta a ɗaki.."

Da hanzari Jamila ta miƙa mata wayarta ita kuma ta latso nombar Momcy ta latsa wajen kira, ringing uku tayi naji wata ƙatuwar mace ta ɗauka da wata ƙatuwar murya take faɗin "Hello my Dota."

Wasila na tafiya zuwa cikin ɗakin su Jamila lokaci d'aya tana faɗin "Momcy komai fa ya fara lalacewa. ki shirya zamu koma wajen boka na kan dutse, dan shegun tsofaffin nan sunƙi barina Momcy komai nayi sai sun lalata min."ta faɗa cikin karyewar murya.

Cikin wata irin murya wacce aka kira da Momcy tace "Don't worry my Dota. Ai ni nayi miki alƙawarin har abada Abdallah naki ne ke kaɗai, in har bazasu gaji da lalatamana aiki ba muma bazamu taɓa gajiya da lalata musu dukkan al'amuransu ba. kishiryo gobe mu tafi, a wannan karon zan nuna musu ni cikakkiyar banufiya ce gaba da baya...!"


*****


Hajiya data gama jin komai, sulalewa ƙasa tayi tana kiran sunan Allah. shima Yusuf ɗin shiru yayi ya sa hannu ya dafe kanshi kawai, Hajiya ta daɗe a haka kafin tace "Ba komai Yusuf, insha Allahu zamu cigaba da gayama Allah, shine zai mana maganin duk wani abunda bamu sani ba. Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.

Da Ameen Yusuf ya amsa kafin ya ɗora da faɗin "Tabbas hakane Hajiya. wlhi Baffa baya cikin hayyacinsa, wannan shegiyar matar tasa ce ta bake komai itace ta juyar mai da kai. wlh tunda Baffa ya auri wannan watsatstsiyar yarinyar ya chanza gaba d'aya, amma ba komai zamu cigaba da gayama Allah, kuma insha Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe.." ya faɗa yana miƙewa tsaye, kuɗi ya ijiye ma Hajiya agefenta yana faɗin


"Zan koma Hajiya, dama nazo dubaki ne. Allah ƙara lafiya Zainab na gaisheki kila sati mai zuwa direba ya kawosu ita da yara, ta matsa sai tazo ta ganki"

Hajiya na murmushi tace "Yusuf baka gajiya da ɗawainiya? Toh an gode Allah ya saka da alheri ya jiƙan magabata, ina amsawa daka ƙyaleta kawai tunda naji sauƙi sai dai ko in zata zo saboda sauran yan'uwanta don naji suna jajenta.."

'Yar dariya yayi kafin yace "Ba komai Hajiya, zata zo insha Allahu bari na leƙa nama Maman Fati sallama, sai na koma wajen Mallam daga chan zan wuce."kai ta gyaɗa ta mai fatan Allah ya kaishi lafiya.

 A kitchen ya tadda Maman Fati yayi mata sallama itama bayan ya bata kuɗi alhalin kuma yazo musu da kayan abinci shaƙe da booth, kai Yusuf dai baya gajiya shiyasa wani lokacin su Hajiya ke kallonsa kamar Baffa, saboda yadda yake ɗawainiya dasu.

Falon Mallam ya koma suka ƙara tattauna maganar Baffa, shi dai Mallam baiyi magana ba, don in yaji ana asiri ya kama Baffa, sai dai kawai yayi dariya yace su daina cewa haka. Asiri gaskiya ne domin a tabbattar mana da hakan ya kama Fiyayyen Halitta Annabi muhammadu Salallahu alaihi wasallam. kawai su dage da addu'a koma miye Allah zai warwareshi cikin sauƙi a haka suka rabu da Mallam bayan shima nan ya cikashi da kuɗi.

Yusuf kenan baya gajiya ko kaɗan, addu'an gamawa da duniya lafiya yayi ta kwararamai, kafin su rabu cikin tsantsar farin ciki da fatan Allah ya kaishi lafiya..








*Janafty*