ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 04

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


        *🅿️04*



TUSHE MAFARI


PROFFESSOR MAHMUD ABDALLAH AZARE Shine Cikakken Sunan Mahaifin M.A,wanda ya kasance Haifaffan garin Azare ne, Local goverment ce Dake Jahar Bauchin YAKUBU.

Proffessor Mahmud Abdallah Azare,Yana da tarin ilimin Addini dana Boko wanda yayi gwagwarmayan a Jami'o'i da dama har Zuwa yanzu da yake Matsayin proff.a Abubakar Tafawa balewa Federal University Bauchi. A bangaren Islamic Studie,kuma yana Zaune a agarin Bauchi. yana Da matan Aure Biyu HAJIYA Hajara ce Babba sai Matarshi ta Biyu HABIBA Yana da ya'ya Guda Shida,Namiji biyu Mata Hudu,hajiya Hajara keda Biyar Mata Hud:u Namiji Daya,sai Habiba data keda Biyu Mace daya Namiji daya.

 Babban D'ansa Shine ABDALLAH Wanda Shine D'ansa na Fari. Wanda Hajiya Hajara ta Haifa masa bayan Shi sai tayi Safina,sai Nafisa,sai Zainab,sai Farida wacce Allah ya karbi Rayuwarta awajen Haihuwarta na Fari,ta rasu Duka daga ita har Abunda ta Haifa. Sai Habiba data ke da Biyu Fati,da mahmud,Wad'anda sune Kanana,Dalilin dayasa kowa ke Kiranta Maman Fati kenan.

Gidan Proff. Muhmud Abdallah Gidane Babban gida ne,ginin zamani mai Cike da Wadata da Rufin Asiri. Suna zaune ne a Unguwar FEDERAL LOWCOST dake cikin garin Bauchi Gidane daya kunshi Tarbiya da girmama Manya. Ya:yansa suna da kyakyawan alaqa da girmama juna, bai Auro Maman Fati ba sai daga baya,ammh kuma sai zaman lafiya yakara wanzuwa agidanshi bayan Zuwanta Suka had'a kansu da Hajiya suka zama tamkar yaya da kanwa. Ya'yansu ko suna Tafiyarsu dasu yadda ya dace. Tana Kokarin kyautata musu suma suna Bata girmanta amtsayinta na matar mahaifinsu Duk da ba aurenta na Farko ba kenan Tayi aure A dutse har ta Haifi yarta mace kafin Su Rabu da mijin Allah yasa kuma Tsakaninta da Proff. Abdallah akwai zama atsakani sai yazo ya aureta har ta Haifi ya'ya Biyu dashi.

Adallah D'ane Mafi Soyuwa awajen Iyayensa sakamakon yaci Sunan kakansa ne,wanda ya Haifi mahaifinsa wato Abdallah,Shiyasa suke Kiransa BAFFA Tun yana karaminsa Sunan Baffa ya bisa sakamakon Haka iyayensa suke kiransa. sai kannensa kowa ya Dauka Yaya Baffa yaya baffa,shikenan Sunansa Abdallah ya bace abakin kowa.

Hajiya Hajara Tana matukar Son Abdallah acikin Ranta,sai dai Tana mai kawaichin D'an fari bata cika Shiga Sha'aninsa ba. sai dai Mallam wanda baya mai Wannan alkunya jawosa yake ajikinsa Kamar wani kaninsa,Tun yana karaminsa yake da hazaka da wata baiwa mai Tarin yawa. shiyasa Mahaifinshi ya dauki Dukkan Buri ya Daura akanshi,sakamakon Shine Namiji kwara D'aya da Allah ya basa,sai daga baya aka samu Muhmud.

International school yayi dake nan Bauchi anan yayi primary dinsa har Zuwa secondary Sch dinshi Bangaren Addini kuwa bayan islamiyan da suke Zuwa mallam bai barsu haka ba musamman ma Shi da yake ganin Namji ne,A internatinal Sch suka Hadu da Yusuf Tunda ga Primary ajinsu daya har Zuwa gama mkrantansu. wanda Shi Yusuf ya kasance Maraye ne,Allah yayi ma mahaifinshi Rasuwa mahaifiyar sa ne Kadai ce Wacce yake Kira Anne.

Dalilin Abokantanka Yusuf da Abdallah da kuma Shakuwarsu yasa Duka iyayen suka san juna. domin in Baka ga d'aya to yana tare agidan da'ya,Saboda Shakuwarsu ko makwannci basu iya rabawa suna tare yau su kwana gidansu Yusuf gobe kuma gidansu Abdallah Abunsu gwaninin ban sha'awa gasu yarane masu Tarbiya da Sanin ya kamata...

Sai dai Tun Tasowarsu suna da Bambamcin Ra'ayi Wanda Shi Abdallah bai Da Yawan Fara'a da Sakin Fuska. Sabanin Shi Yusuf ne Mutum ne mai Raha da barkwanci koda kannen Abdallah ne haka zaka ganshi yana ta Hira dasu ana Dariya sabanin Abdallah da bako da yaushe yake Saka musu baki ba ko sakoshi akayi sai dai ya murmusa ba kasafai ya cika mgana ba,Wani lokacin Mallam na mai kirari da Miskili kafi mahaukaci ban Haushi.

Ahaka suka samu nasarar samun Gurbin karatu ajami'ar Ahmadu bello dake zaria da Kokarin Proff.Muhmud Azare ammh kowanne da course din zai karanta,Shi Abdallah zai karanta Quantity Survey ne,ayayinda Shi Yusuf zai karanta Engenering ne.

Ko A mkaranta Duk da ba Department D'insu Daya koda yaushe suna tare,Domin Hostel dinsu daya,kuma koda yaushe suna tare a suna karatu Domin basu da wasa ko kad'an koda yaushe Cikin Maida kai Suke ga karatu Domin Cikar Burin Mahaifansu.

Basu Rabu ba sai da Suka kammallah Digree dinsu na Farko. shi Yusuf BUK ya tafi ya Dora Masters dinshi ayayinda Shi Abdallah ya Zauna anan Abu din yana Cigaba da master dinshi,Tun Abdallah na matashin sa Zatinsa da kyansa suka Fara bayyana koda Suke mkranta ko Friendship bai yarda ya kulla da wata mace ba. gwara ma Yusuf yakan dan kulasu ammh Shi Abdallah sam basa gabansa,Yan matan Jami'a da dama sun Sha Zuwa su kawo Tayin Soyayyarsu ammh baya karba daga karshe sai dai ya bar Yusuf da yar Murya yana basu Hakuri.

Bawai Baya son Mace bane,No Tun yana yaronsa yake da Burin irin macen dayake Muradin Aure,yana son Auren Doguwar mace. Fara kuma ta kasance tana da ilimin addini dana Zamani wacce zata mutumta iyayensa ta kuma kasance Wacce ke Tsoron Duniya,to yagama Auna yan matan wannan Zamanin Duk ya Fahimci Basu da kamun kai ballatana Mutumci ,ga Rashin aji. shi kuma ya Tsani mace mara Fasali da Rashin aji,Shiyasa har yagama Had'a masters dinshi ba'a ce ga Budurwansa ba.

Cikin ikon Allah yana Gama Had'a masters dinshi aka kawo ma proff. Mahmud Tayi aikin Costom yana Tuntunbar Abdallah shi kuma ya Amince kafin Wani lokaci ya Shiga aikin Costom Wanda ko Shekara Uku baiyi ba yadinga samun Cigaba sosai a baya a lagos aka ijiyesa ammh da aka bashi matsayin DCG sai aka maidashi Porthercourt.

 Duk da Proff.Mahmud Azare yayi karatun Boko soaai ammh bai sai ya bar ya'yansa mata saka saka, ba,da kin kammallah Secondry sch Dinki bai bari ki dora karatun Cigaba agidanshi da Zarar kin samu miji zai Miki Aure.

ya Aurar da Safina da Nafisa,Duk anan garin Bauchin sukayi Auren,yanzu Farida ce tayi SSCE Dinta sai Zainab dake aji biyu amatakin karshen,Ita ma Faridan tana da mai Sonta,Zainab kuma yar gida za'ayi domin Allah ya Had'a Soyayyah mai karfi Tsakaninta da Yusuf wanda Tun tana karamarta ya Furtamata. Anne ita kuma tazo tama Mallam mgana ya Amince.

Ba'ayi Auren Nasu ba Sai Da ya samu aiki A NNPC dake Kaduna tare dana Farida aka Had'a. wacce ita kuma tayi aure a kano,lokacin da akayi biki da agidansu Tafara zama Wajen Anne,sai bayan Wata hudu kana Suka tattara suka Koma Kaduna NDC,achan ya Siya gida domin ragema kansa Zirga Zirga,ganin Yusuf yayi aure sai Mallam ya matsama Abdallah kan ya Fito da Mata yayi aure,ammh Abdallah yace amai Hakuri Har yau bai ga Wacce yakeso ba.

A baya Abdallah Mutum ne Nagari mai kokarin kyautatama iyayensa,ga kawaichi da Kuma Dattako. sai dai Tun yana yaro Mallam kemai Fad'an yana Sakaci da addu'a. Abdallah bai damu da ibada Sosai ba,Banda kamsin salawatun baya Wani ibada, ko yan Nafilfilin nan bai da kokarin yi Balle akai ga Azkar din Safe dana Maraici da Anyi mgana yace Baida lokaci ne. Hajiya da Mallam suna iya bakin kokarinsu suna kuma Tsaye kanshi da addu'o'i Tunda shi ga Abunda ya zama.

 A baya Duk Wata yake Zuwa Bauchi yayi Kudi ya sai gida da Mota. Koda wani Lokaci cikin kyautatama iyayensa yake da yan'uwansa. Rana tsaka komai ya Chanza daga Rayuwar Abdallah sakamakon Shigowar Wasila cikin Rayuwarsa.


WASILA ARMAYA'U BIDA Shine Cikakken Sunanta.

Banufiya ce ta Uwa ta Uba,Haifaffiyar Niger State,Agarin Bida Dake Minna. Wasila Su uku ne awajen Iyayensu,Sunan Mahaifiyarsu Hajiya Kudirat,sai Mahaifinsu Alhaji Armaya'u.

Rayuwarsu wata rayuwace babu kwaba balle gyara,Tun Suna kanana Sun Taso Sunga Mahaifiyarsu Tagama da Mahaifinsu domin Daga ita sai ya'yanta da yan'uwata yake gani da gashi,Hajiya Kudirat ta gama mallakeshi dashi da Dukiyarsa sai Abunda tace yakeyi. Shiyasa Tun Suna kananana Suka Taso da wannan Tarbiya,gashi Hajiya Kudirat tana Sonsu bata son Abunda zai bata musu Rai Shiyasa ta barsu Suke Abunda Suka ga dama.

Shiyasa Dangin Ubansu Suka kawo Ido suka sanya musu,domin babu mai gaya musu,Suji Wasila ita ce Babba dai Jamila sai Hafsart Wanda tabasu Tsawon Shekara Shida,wasila ba mace bane mai kyau ammh akwaita da Son Mu'amala da abu mai kyau Tun tana karamarta Tana San Mamanta na Shigen Shigen Malamai,Kuma Yadda take Gudanar da Mulkinta yake Bata Sha'awa itama tana Fatan in tayi Aure ta mallake Mijinta yazama yana Tafin Hannunta.

Wasila Tun Tana karamarta idonta Abud'e yake,Tun Suna Secondry schl Taasan Dadin Namiji ya Taba mace,Tunkafin Wasila ta gama Secondry Sch dinta tagama lalacewa da Harka da maza. sai kuma Ta tafi Federal Universty Dutse achan gabadaya Rayuwarta ya kara Gurbacewa,Tazama Yar iskan karfi da yaji,kuma Mamanta ta sani ammh bata taba Cemata Abunda take aikatawa ba Daidai bane.

Saboda yadda Rayuwar Bariki tayima Wasila kamun kuku taji bata ma bukatar Aure,domin ita haryanzu bata ga Wanda yayi Mata ba. Kuma bata iskanci don Kudi No mahaifinta yana da Kudi Daidai gwargwardo Domin dan Siyasaa ne. 

kawai Tana yi ne Saboda Jin dadinta. Shiyasa suma kannenta Suka bi bayanta Suma ba irin lalacewar da basayi da Sunan Wayewa suyi Shigarsu yadda Suke so,Su kuma yi Abunda Suka ga Dama Mahaifinsu bashi da Abun Cewa Balle yan,'uwanshi Wanda Dama Hajiya Kudirat tayi musu Farraqu atsakaninsu Sai dai kallo daga Nesa 

Had'uwar Wasila Da Abdallah ta samo Asali ne Bikin Wata course Mate Din Wasila,Sunanta Zubaida yar nan Garin Dutse ce. Zatayi Aure kuma Suna good Time da Wasilan,Duk da ita Zubaida Din ba yar Duniya bace irin Wasila,sai kuma akayi sa'a Wani ma'aikacin Costom ne zata aura kuma Wajen aikinsu Daya da Abdallah anan Porthecourt.

To Dukkansu sunzo mai Daurin Aure,Itama Wasila tazo Ta ganshi ne Acikin Jerin abokan ango Sanda Suka Shigo gidan su Zubaida gaida iyayenta. Anan ta kyalla ido ta ganshi da Farko Wasila bata dauka Wani Serious bane,kawai ta Dauka burgeta yayi,sai kuma me Tunda ta koma mkranta takasa zaune da Tsaye akan Abdallah Wanda ko Sunanshi bata sani ba,Barci take Shi take gani Komai take Shi take gani karatun ma Tadaina ganewa,Cikin wannan Hali ta kira Kawarta Zubaida Wacce Aka kaita porthercourt,Tana tambayanta Abdallah ammh sakamakon bata Fadi Suna ba yasa daga Zubaidan har Mijinta suka kasa ganewa,ammh tana yin Misalinshi Nura Mijin Zubaida ya Gane Abdallah ne,domin Shi dabam ne awajen aikinsu,Nombar Wayarshi ya bata ammh bayan ya Sanar da ita Mata basa gaban Abdallah ammh Wasila bata damu.

Tafara kokarin kiranshi ta Waya ammh har Wajen Sati baya daukan Wayarta. Ranar daya amsa kuma Gaisawa kad'ai Sukayi ya Tambayeta Wacece ita,ta tsayamai Wani Dogon Turanci ya katse kiran bayan ya Bata Hakuri,Wannan Abun yama Wasila Ciwo Wasa,Wasa Ciwon son Abdallah ya kama Wasila mai Tsanani ganin irin Wulakancin dayake Mata ne gashi yaki Sauraranta tasa Zubaida Ta Turo mata Full adreess Din wajen aikinsu Abdallah na porthercourt sai dai kawai Abdallah ya ganta kwatsam.

Akaron Farkon ganinta yaji ya Tsaneta,kuma koda ma tana cikin Jerin irin macen dayake Son Aura bazai taba auran Mace mara aji ba Balle ma kwata kwata bata dace da Ra'ayinshi ba Fata Fata yayi mata bayan yamata koran kare. yasa Security suka Fita da ita,Wannan Abun shi yadasa ma Wasila Alqawarin ko ta Halin kaka sai ta Auri Abdallah ko ta Halin kaka ne. Daganan Bidda ta koma Taje ma Hajiya Kudirat tana kuka tana Sanar da ita Abunda Ke Faruwa,Ran Hajiya Kudirat ya baci Ta Dinga Huci ita kad'ai Tana Fad'an Duk Duniya bata ga Wanda ya isa Ya Tozarta mata iyalai ta bari ba ko Zatayi yawo Tsirara sai ta mallakama Wasila Abdallah atafin Hannunta.

Washegari suka Shirya ita da Wasila suka Nufi acikin Wani kauye a cikin garin Bidda. wajen Wani boka wanda ke Zaune awani Tsauni. Sunansa Boka D'andugaji, Aikinshi kamar yankan Wuka da zarar yayi miki aiki To Shikenan kawai. Tun Kafin su isa Aljanunsa sun karantamai komai,Suna Zuwa ya shiga karanta musu ya kuma Tabbatarmusu da su koma nan da Sati d'aya Abdallah Zai zo da kafarsshi nan yake Fad'a musu aikin zai ba da Wahala saboda akwai Wasu Taurari Guda Uku da Suke Dabaibaye dashi, Masu matukar Hasken,Taurarin Guda biyu Kariyar Addu'an Mahaifinshi ne dana Mahaifiyarshi ke Tare dashi. sai D'ayan Taurarin da Allah bai bashi ikon ganin ko menene ba. ammh ga Duk alamun Taurarin yafi Haske ajikinshi kuma yayi mai Dabaibayi ne.Wani Al'amari ne Kuma ga dukkan alamun Zane ne acikin kadarraransa.

bai Fad'a musu Haka ba, saboda karsu ga gazawarshi,sai dai ya Tabbatar musu da zasu ci galaba akan Abdallah Domin baya Kokarin ibada yana da Sakaci da addu'a ta hakane zasu samu Nasaran yin aiki akanshi. Cike da Farin ciki suka baro Boka bayan Sun Cikashi da kudi.

Aikin Boka yaci Abdallah Domin Ba'a Rufe Sati d'aya ba. yaji Duk Duniya bashi da Wacce yakeson ganin Wacce ta wuce Wasila yayi ta Nemanta har yagaji ammh bai Sameta ba,Wayarta kuma yayi ta bugawa bata Dauka ba,sai da ta bashi Wahala kana ta kirashi da kanta. Ranar kuwa ko Minti daya Abdallah bai kara a Porthercourt ba ya Iso Bidda da kwatacen da Wasila tamai.

sai ga Abdallah Durkushe afalon Su Wasila yana ma Wasila kukan magiyan tasoshi ta Aureshi ita kuma tace bazata aureshi ba Tunda ya Wulakantata afarko. Hadda Hajiya kudirat ta Shigon Falon tana mai Tsawa kan yatashi ya Fita bazata tab'a bama Wanda ya Wulakanta mata yarta aure ba. ammh aikin Asiri ko gizau Abdallah baiyi ba, saima kara Sadda kai da yayi yana ta Rokon Wasila datayimai Rai ta ceci Rayuwarsa,Tace zata aureshi in tana so yaji Dadin Rayuwarshi.

A wannan Ranar dai Wasila bata amsama Abdallah ba. sai da yayi kwana biyu agarin Bidda yana Rokonta kana ta amsamai Ranar kuwa kamar ansaka shi ajannah, saboda Murna ganin sun Sameshi ahannu Shikenan kuma kakarsu ta yanke saka. Abdallah bai isa ya tsallake mganar Wasila ko Wuta tace ya taka zai taka,Uwa uba kuma bayason ganin bacin Ranta,yanzunan zai Fita daga cikin Natsuwarsa.bGabadaya Rayuwarsa ta Susuce ko wajen aiki bai cika zama ba,Duk sati yana kan Hanyar Bidda. kamar wani Zazzautattace,Yasha kwana agidan Su Wasila bayan ta Ribace Shi Sun Fara aikata masha'a Tun awaje. Ai Wasila bata kara jin Tana son mallakar Abdallah ba Sai Ranar daya kusanceta bayan Ta Nuna bacin Ranta,shi kuma baya son ganin bacin Ran Wasila nan ya Biye mata ya Fara aikata Zina afarkon Tarihin Rayuwarshi. Tunda suka Fara Shikenan suka ji dadi koda yaushe Cikin kusantar Juna suke,Duk da Shi Abdallah yana biyemata ne Domin Bai da yarda zai yi. Ga wani karin Abunda ke Damunshi Shine ba'a son ransa yake Biyema wasila suna aikata sabon Allah ba. sai dai bai da yarda zai yi ne bai isa yayi ma wasila gaddama ba shi ba jin dad'in abunda suke aikatawa yake yi ba wasila kuma Gatanan ne dai kawai baisan awani babi zai sakata ba,Kuma bai Taba Nuna mata ba, saboda Wasila ce Sanyin idanuwanshi.

Basu Rufe Wata Biyar da Had'uwa ba Rayuwar Wasila ta chanza Domin Abdallah na kashe mata kudi daga Naira daya har Zuwa Miliyoyi,Tuni Wasila ta watsar da karatu ta koma cin Duniyarta da Tsinke. Shi kuma Abdallah gabadaya gida da wajen aikinshi aka ga ya chanza,

koda wani lokaci yana wajen Wasila kamar Wani Mijin tace,Bauchi ko Tunda Wasila ta asirceshi bai kara marmarin Zuwa ba,yadaina kiransu akai akai sai dai in sune suka kira sai ya samu wata karya ya lailaya yace Baida lokaci ne ammh yana Tafe.

Wasila ce Tafara bijiro mai da mganar Aure,shi kuma sai bai Tunkari Mallam kai Tsaye ba sai yafara Tunkarar Yusuf da mganar,Yusuf bai kawo komai ba Yaje ma Mallam da mganar. shima baiyi gaddama ba ya kira Abdallah yana Tambayanshi Sunan Mahaifin Wasila,nan kuwa ya sanar dashi Dayake Mallam yana da Mutane ako'ina ga kuma Tsofaffin dalibansa nan da nan Yasa akayi mai Binciken Gidansu Wasila sai dai lbrin da'aka Dawomai dashi bamai Dad'i bane,Tun daganan Mallam yaji Ransa ya baci da Abdallah ya kirasa awaya yana Fad'amai mai ya kaishi Neman Aure a Gidansu Wasila gidan da ba Tarbiya,to ahir dinshi maza yazo nan Bauchi ya Nemi yar Mutumci,Duk Abunda Mallam ya Fad'a sai da Abdallah ya sanar ma Wasila ita kuma ta sanar ma Hajiya.

Ita kuma Washe gari nayi ta Tafi Wajen Boka ta sanar dashi komai,Dariya ya kece mata dashi yace ta tashi tatafi za'ayi wannan Auren nan da Wata daya kuma yana bata albishir din Wasila zata mallaki Abadallah kamar Dan tsako atafin hannunta.

Ai kuwa haka akayi Domin Abdallah yakara Haukacewa in ba Wasila ba zai iya Mutuwa.

afujajan yaje Bauchi yana Sanar da Mallam har abada bazai iya Rabuwa da Wasila ba, har yakai yana tanka in tanka da Mallam,har sai da Hajiya ta Tsinkeshi da mari. Bai kuma sa yayi nadama ba,gabadaya kanshi ya juye haka ya Fita fuu yabar garin yana kara jadadda musu ko Sunki ko Sun so sai ya Auri Wasila Domin itace Rayuwarsa. Wannan al'amarin daya Faru ya daga Hankalin kowa agidan ya Hargitse hajiya kwana tayi kuka,Shima Mallam Abun ya tsayamai arai ammh bai taba kawoma kanshi Asiri akama Baffa ba, yafi barinshi a Duniya ce da kuma Rashin kunya irin ta D'an yau.

Babban lbarin dayafi Tayarma Iyayen Abdallah da Hankali Shine Zuwan da Yusuf yayi har Gidan Baffa a Porthercourt,Yaje yayi mummunar gani. domin Wasila ta koma gidan Abdallah ta tare,suna zaman Fasikanci Wa'izubillah da yusuf yaga haka yanemi ya ma Abdallah mgana,wlh bai Saurareshi ba Daga karshe Wasila tace ya koreshi nan da nan ko ya sa Masu gadi suka yi waje dashi. wannan al'amari ya razana Yusuf har yakai Bauchi yana kuka. haka ya Fad'i gaban Su Hajiya yana Fada musu Abunda ya Gudana,wannan lbrin Shine Sanadin da Hajiya ta yanke jiki ta Fadi,Lokacin ne Kuma ta kamu Da hawan Jini.

Iyayen Abdallah basu taba tsintar kansu cikin bakincikin ba sai lbrin da Yusuf yazo dashi na zaman Zina da Abdallah ke gudanarwa da Wasila. yasa Mallam ya wanke kafanshi har Bidda wajen Mahaifin Wasila ya kuma bukaci yanaso a daurama Abdallah da Wasila aure. ammh sai ta dawo gida tayi Tsarkin istibura'i Domin inganta aurensu da Farko yaso yayi gaddama ammh yana gayama Hajiya Kudirat ta Daga tsalle tace maza ya amince nan da nan ko ya amince ya kira yan'uwansa Duka duka ko Mutun goma basu kai ba aka gudanar da Neman Aure inda Mallam yace sai Wasila tayi tsarki kana zai Amince Abdallah ya Aureta saboda yanzu Aurensu ya Haramta. 

A haka suka amince bayan Hajiya Kudirat ta kira Wasila ta sanar da ita Abunda ke Faruwa kuma tabata Umarnin ta tattaro kayanta ta dawo gida.

Har Mallam ya koma Bauchi Zuciyarsa Tana cike da bakinciki da kunci Halin Da Abdallah ke ciki tare da Tirr da irin gidan daya dauko Mata. kuma koda wasa bai sanar da kowa Abunda ke Faruwa ba saboda bayason Hankalinsu ya kara tashi Fiye da na da,domin haka su Anty Safina suka tasa hajiya suna ta mata kuka yusuf ne da Maman Fati keda kokarin basu baki tare da Shawartansu Su rika saka Abdallah acikin addu'o'in su.

 Duk Abunda ya Faru Wasila take Sanar da Abdallah daganan kuma ya Cigaba da Shiryen Shiryen Biki Batare daya kara bi ta kan iyayen nashi ba. Wasila ko kusan sati suna tare,sun daina raban Juna Saboda tsarkaka Aurensu ammh Shafe Shafe kam basu Daina ba adaddafe Wata uku ya cika. Sai alokacin Mallam ya sanar dasu Hajiya Abunda Ke Faruwa,Ranar Hajiya ta kwana kuka da takaichin Halin da Baffa ke ciki Ranar Daurin Aure kuwa Mallam bai gayyaci kowa ba Dagashi sai Yusuf suka tafi Bidda. Agida kuwa yan'uwanshi da Suka zo babu wanda suka Fad'amawa balle Suyi gayyah ko Taron biki. ko zainab dake Kaduna Yusuf bai barta tazo ba,saboda kada su karama Hajiya damuwa Ranar ban da kuka babu Abunda Suka Dingayi Ranar ma Hajiya a asibiti ta kwana Saboda yadda jikinta ya Rikice Sosai..

 A wajen Daurin Auren Suka gamu da Abdallah dashi da tawagarsa Murna ta kama Abdallah bakinshi baya Rufuwa yau Burinshi ya Cika ya tabbata Wasila matarshi ce. Saboda bakinciki ma Su Mallam basu Tsaya ba Suka juyo,shiko Abdallah sai da suka kwana biyu A bidda ana Shagali kafin Su baro Bidda Shida Wasila ajirgi suka yada zango A parthercourt.

Suka cigaba daga inda Suka tsaya Kafin bikin ma Sai da suka kara komawa gidan Boka suka kara bashi kudi yakara Karkatar da Zuciyar Abdallah garesu ya kuma Tusamai Tsanar iyayensa aranshi.

Shiyasa har ya Auri Wasila da Wata goma bai zo Bauchi ba,kuma baya kiran Wayar kowa ko an kirasa ba'a samunshi.

Domin ko Sunan Bauchi yaji an ambata yanzu Ranshi zai Baci yaji Zuciyarsa na tafarfasa.








*Janafty*