Dr. Asmeenat Xeeyan
by @halimahz
Dr Asma'u Zayyanu, ƙwararriyar likita kuma marubuciya, mace mai aiki tuƙuru da tausayin marasa lafiya.
___________________________________
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.
TAMBAYA: Da fari zamu so jin cikakken sunanki da kuma tarihin rayuwarki?
AMSA: Assalamualaikum barka da safiya! A tak'aice Sunana Asma'u Zayyanu sai dai mutanen social Media sun fi Sanina da ASMEENAT XEEYAN, ni haifaffiyar garin sokoto ce Kuma Alhmdulillah duka b'angarora guda biyu na ilmi da muke da Islamiya da bokon du ka anyi sai godiyar ubangiji domin kaso mafi yawa na Alkairan wannan karatun ana damawa damu "Alhmdulillah".
TAMBAYA: Masha'Allah ta ya kika tsinci kanki a harkar rubuce rubuce?
AMSA: Yadda na tsinci kaina A harkar Rubutu zan iya cewa Rubutaccen Al'amari ne, saboda tun asalina ba gwanar karatu littafan Hausa bace ba Kuma gwanar shigowa social media ba, wata rana 2017 ina zaune Aminiyata ta sani cikin group d'in littafai bisa tsautayi Ko da nazo ana cece kuce akan Wani littafin batsa da wata marubuciya ta wallafa wannan littafin kamar shine littafin batsa da yafara bayyana yayi suna A social media 2017. So irin yadda Ake zagi da Maida martani sai yasa naji ina son karantar wannan littafin na kira aminiyar tawa nace ta bani zan karanta tace min to sai ta turomin..na fara bin littafin Kuma na karanta sai nayi nazarin ni a tawa gudummuwa da zan bayar ta hanyar canja d'abiu da tsoratarwa ai Ina da labarai masu tarin yawa....sai kuwa na fara Rubutu na sanyawa Labarin HUKUNCI, Ina turawa sai na had'u da wata marubuciya tace min itama writer ce amma sabuwa na ce Nima sabuwa ce sai tace mai zai hana mu had'e kanmu mu yi Ƙungiya akwai wad'anda ta sani itama haka kuwa aka yi daganan sai abubuwa su kayi taci gaba.
TAMBAYA: Kin rubuta littafai sun kai guda nawa?
AMSA: Littafan da na rubuta sun kai Goma; HUKUNCI, BAKIN GANGA, KUYANGAR ƘUNCI, BAƘIN DARE, BANKAD'A, RAYUWAR BANUJA, MAZA ALLURAR GUBA, DUNIYAR SHAHARA.
TAMBAYA: Me ya dakatar da ke da rubutun littafi?
AMSA: Abunda ya dakatar Da ni yanayin aiki...inda na ke ada yanzu an samu cigaba nauyin ayukka sun ƙaro Amma har kullum in lokaci ya bani Dama b'ul za'a ganni Ina rubutu.
TAMBAYA: Bisa ganin wasu mutanen a cewarsu karatun littafin sam baida wata fa'ida. me za ki iya cewa game da wannan batu?
AMSA: Fahimtarsu ce A haka, Amma Magana ta gaskiya karatun littafin na da matuk'ar amfani domin akwai ilmi me fad'i a cikinsa sak dai akwai abun nadama me tafe da takaici duba da yadda wasu marubuta suka yi ruwa suka yi tsaki wurin rubutun batsa da sunan isar da saƙo.
TAMBAYA: Akwai wata ƙungiya ta marubuta da kike ciki? Idan akwai ya tafiyar ƙungiyar ga membobinta? Suna samun ƙaruwa ko kuwa kawai dai ana zaune ne kara zube?
AMSA: Ƙwarai ina cikin Ƙunqiya mai suna GAMJI WRITER'S ASSOCIATION...tafiyar ƙuniyar ba'a cewa komai sai San barka, domin ƙungiya ce d'aya tilo da Bata ajiyeka komi k'warewarka A rubutu komai masoyanka sai ta tabbatar da nagartarka, ƙungiya ce Da ke yaƙi da batsa da tir da alƙalamin batsa, sannan ƙungiya ce da Bata zama da Wanda bai mallaki Ilimin zamantakewa ba don haka manbobinta kowa na zaune da kowa lafiya kamar ma yan u'wan juna mu ke.Duk bayanan k'ungiyarmu na da Wani Reshe mai take GAMJI HEALTH PROGRAM, wannan reshen Yana wayar da kan mata ne akan abunda ya shafi lafiyarsu, haka mabobin da ke cikin group d'in kanyi Tambayar duk abunda ya shige musu duhu abasu amsa A kimiyance, saboda haka ga wanda yaci karo da wannan fira tawa idan yana sha'awar shiga GAMJI HEALTH PROGRAM sai ya tuntuɓemu.
TAMBAYA: Ya yanayin mu'amalarki da marubuta?
AMSA: Yanayin mu'amala da marubuta kam bana mu'amala da kowa sai mutanen GAMJI domin ni ba gwanar yadda da mutane ba ce, bana son k'aramar Magana bana son anyi ance, shiyasa na zab'i warewa gefe.
TAMBAYA: Daga fara rubutunki zuwa yanzu kin fuskanci wani ƙalubale ne?
AMSA: Ƙalubale ba za'a rasa ba....Wani lokaci kana son ka huta Amma saboda tunanin mabiyana na jirana sai nayi...Wani lokaci kana k'ok'arin ISAR da saƙo makaranci yace kai wannan labarin yayi tausayi da yawa bai kamata wance ko wane su had'u da wannan masifar ba, wasu su ce ni dai na haƙura gaskiya in har kaza zai ci gaba da faruwa, da sauran dai k'alubale da Ake cin karo da su.
TAMBAYA: A matsayinki na ƙwararriyar likita, zamu so kiyi mana bayani dangane da magungunan mata da aka raja'a yanzu akansa, wanda har ƴan mata ma ba'a barsu a baya ba.
AMSA: Magungunan matan Aure da y'an mata ke amfani da su yanxu sun Rabu gida biyu akwai kayan mata da mu ka sani hallau akwai supplement.
Kafun na ce komi bara In fara shimfid'ata da wannan...domin har yanxu matanmu hausawa bamu waye da saninin meye "Supplement" ba, wannan rashin sani shi ya jefa mata da yawa a wannan harkar domin su masu kasuwacin amfanin supplement su ke bayani suna mantawa da illollin da ke biyowa baya ga duk matar da ta k'ullah k'wance da supplement, kafun naje ga illolin mu tsaya Muji menene Supplement?. Supplement Yana nufin duk Wani Abu da Ake k'ara shi a cikin Wani Abu don a cike gurbin da aka rasa ko Kuma ya k'ara masa yawa....su wannan Supplement suna Nan daban daban akwai na k'arin k'iba, nonuwa, fari, gashi, k'umba, farin idanu, farin fata DS...sai dai tambayar da zan jefawa mata idan har kina cin abunci me kyau da Gina jiki me yasa dole sai kin k'ara da supplement, shi fa wannan supplement anyi su ne domin wasu marasa lafiya da ke buk'atar haka bisa tilas duba da manya manyan k'alu bale da ke tattare da wad'annan magungunan....zan d'au d'aya daga cikin supplement d'in da muka fi amfani da shi Kuma mu ke yayinsa wato Dexamethasone ko zumar k'iba domin bincike ya Nuna zumar k'iba ana h'adata ne da k'wayar Dexamethasone domin ayi k'iba....mace ta fito cikin tsaranta ta nunawa duniya Nima mijina ya kai don haka dole a sakani a layin manyan mata. To anji kin sha Dexamethasone ko zumar k'iba kinyi k'iba barka da arziƙi kinji! sai dai Magana ta gaskiya ki jira k'alu balen da zai biyo bayanki domin da kud'inki ne kike siyowa kanki bala'i da zai jefa Rayuwarki cikin nadama me tafe da danasani Nan gaba. Domin shi wannan Dexamethasone na cikin group d'in maguguna da mu ke kira "Corticosteroids" misalin wasu magunguna da suka had'a da:-Budesonide, Hydrocortisone, Prednisone, Betamethasone, Dexamethasone. Duka wannan magungunan artificial form ne na Wani hormone da Ake kira "cortisol". Shi wannan hormone na "cortisol" Ubangijin mu ya azirta mu da shi ne domin ya rik'a taimaka mana wurin magance gajiya da metabolism d'in cikin jikinmu, sosai ya ke taimakamana wurin k'arfafa immune system d'inmu (Garkuwar jikinmu). Shi Dexamethasone d'innan ana bayar da shi ne kad'ai ga masu lalurar da su ka had'a da, cutukan da su ka shafi Garkuwar jiki kamar old age kenan, masu Cancer, masu tarin huka DS cututuka masu Had'ari. Bayan wannan "corticosteroids" na cikin nau'ukan magungunan da mu ke kira Dangerous Drugs, su wannan magungunan suna da bala'in Had'ari ga d'an Adam, shiyasa A dokance ba'a siyar da wannan maganin sai da umurnin likita, in tak'aice miki Mai gabatarwa duk marar lafiyar Da ke Shan wannan maganin to tabbas likita na saka mishi Ido fiye da yadda ba kya zato saboda had'arin da ke zagaye da maganin. Abunda ya d'aga min hankali wai mata na shan "steroids" kamar Dexamethasone da zumar kib'a ne wai Dan su yi k'iba, kib'a fa? In kina Shan zumar kib'a ko Dexamethasone wlh ki kiyayi kanki domin Ni dai iya sanina babu Likitan da za kije ya baki wannan magani kawai don kiyi k'iba ,domin idan ya baki to tabbas yaci amanarki cin amanar da Allah k'ad'ai zai Miki sakkaya. K'arfi ko dabara basa iya maye Miki gurbin cutar da yayi Miki. Nasan idan kina karanta wannan so kike ki sani Zuma da gaske tana sa ƙiba Kuma tana da illah? Zuma nasa k'iba? Eh! tabbas tan Saka k'ibaji ba Sha kifashe su ka rad'a mata suna ba,? Sunan ya samo asaline daga maganin da Ake had'ata da shi wato Dexamethasone. hanyoyin da wannan supplement Su ke k'ara Miki k'iba, na farko:- Suna k'ok'arin k'ara Miki cin abinci kirik'a cin abinci ba yadda kika sababa (Increase Appetite). Na biyu suna rik'e Ruwan jikin d'an Adam sai su kumbura mutum (increase water retention). Na uku (Redistribute Fat.) Idan kika sha to tabbas bisa rashin sa'a za kiyi kama da k'ibar Nan ta uwayen Cartoon, ma'ana wuya ya kumbura, fuska tayi Round ba'a ganin gemu sosai, gashi ya fito saman bakinki, hannuwa basa k'iba sosai, ciki yayi k'ato, koma in tak'aice muku za kuyi kama ne da masu cutar Cushing syndrome, wannan magani zai zo ya rik'a saka ki saurin gajiya, zai kawo Miki ciwon ƙafafu, suna Saka hawan jini, ciwon Suger, Cancer, steroids sbd suna kashe immune system to kullum za ki rik'a samun infection domin ba ki da Garkuwar jikin da zata kare shigata haka curutoci daban² za su riƙa shigarki, yo ko hawan jini da ciwon Suger kad'ai su ke sakawa ai yakamata ki yiwa kanki hisabi kice Allah ya tsinewa zumar k'iba. Kuma duk wannan curotocin ba sune abun kallon ba ga masu Shan zumar kib'a...abun kallon shine Wanda muke tsoro ga Dexamethasone wato "Adrenal insufficiency" idan mutum na shan steroids ba'a tsayawa haka kawai bawai irin PCM ne Ko Amoxicillin ba da kike tsayawa lokacin da kikeso, steroids are tapered down not stopped abruptly (ba'a tsayawa haka kawaii) na ce muku likita na sanya masu Sha Ido ko? To kad'an kaɗan Ake rage Dose har a daina Sha, ana yin haka ne sbd abunda muke cewa Non reactive fever. Mu koma baya dama nace maku muna da Wani hormone da Allah ya bamu me suna "cortisol " na Kuma ce muku steroids artificial ne na cortisol d'in, to k'wak'walwarmu akwai Wani halitta da in mun gaji sai yayi signal ma Adrenal gland su sake wannan cortisol d'in ya rage mana gajiya. to ke me Shan Dexamethasone Kinga kina samun naki cortisol d'in ne ta Drug d'inki ko zumarki, daga nan sigina d'inki ta Brain zata mutu, to Kinga da kuskure ya d'ibeki kika Daina Sha Kai tsaye me kike tsammani? Sigina cortisol d'in ki ta mutu kin zo kin daina Sha Kai tsaye wlh labarin mutuwarki kawai za'a ji....sbd ba likita ya baki bare ta Nuna Miki yadda sigina d'in zata dawo...
Da wannan zanja kunnen mata masu Siya..domin su masu siyarwar kud'i su ke nema sun yi nisa basa Jin kira Wlh...ke dai da kike Siya domin kawai k'iba ki daina domin ba yanzu ba gaba Ake Miki kallo Kinga kenan k'ibar ba tayi amfani ba tunda har zata iya zama makamin da ke iya raba ki da lafiyarki .
TAMBAYA: Masha'Allah, jazakillahu khairan da wannan bayani na ki...A cikin littafan da kika rubuta, wanne za ki zaɓa ki recomending wa mutane su karanta don su fa'idantu da darasin da ke ciki?
AMSA: MAZA ALLURAR GUBA domin ina da yak'ini ko wacce mace na da buk'atar Darussan da yaqunsa.
TAMBAYA: cikin gajerun kalmomi ya halayyarki ta ke?
AMSA: Ba na son Rainin Wayo, ina son kad'aici, ba na son hayaniya sannan Ina son yara Sosai...
TAMBAYA: Akwai wacca kike kallo matsayin madubi ko uwar ɗaki a cikin ƴan uwanki marubuta?
AMSA: Ba ni da uwar d'aki sai dai Aminai.
TAMBAYA: Ya mu'amalarki da masoya littafanki?
AMSA: Sai San Barka domin da littafi da babu suna tare Dani d'ari bisa d'ari tare da Alkairai da su ke min gari ya gari haka kullum In dai zan gaisa da su sukan yimin Addu'a da fatan Alkairi...don haka Ba abunda na ke iya saraffawa A harshena bayan Kalmar Alhmdulillah domin wannan yaddar ta Ubangijin Muhammad ce babu wayo na babu dabarata a ciki.
TAMBAYA: Me ke ɓata miki rai?
AMSA: Y'an uwana marar lafiya.
TAMBAYA: Abincin da kika fi so?
AMSA: Shinkafa da Miya.
TAMBAYA: Me za ki iya cewa daga ƙarshe?
AMSA: Daga ƙarshe zan ce da marubuta da masu sana'ar zumar k'iba wadda ke da had'in Dexamethasone su ji tsoron Allah domin dukansu abubuwa ne masu tafiya da zamani idan zamaninka ya wuce kana raye Zaka ji mutanen duniya sun manta da kai...Kuma duk batsar da kika yi da mutanen da kika bada gudummuwa suka lalace labarin ko shekara miliyan akayi za ki zo gaban Allah kiyi bayanin abunda kika rubuta, masu zumar k'iba Kuma in zamanin ya wuce wad'anda kika cuta Allah zai saka musu, wasu za suce su suka Siya karki manta lokacin da kike siyarwa Baki gaya musu illarta ba zuxuta alkairanta kawaii kikeyi.
TAMBAYA: Wanne fata za ki yiwa wannan shiri namu na tattaunawa da marubuta?
AMSA: Ina maku fatan Alkairi mai tafe da mad'aukakin cigaba...Allah ya k'ara k'arfafa muku guiwa.
Amin Ya Hayyu Ya Ƙayyum. Na gode matuƙa da lokacinki.
___________________________
Alhamdulillah! Ƙarshen Tattaunawar tamu kenan tare da Dr Asma'u Zayyan wadda aka fi sani da Asmeenat Zeeyan. fatan kun ji daɗin tattaunawar tamu. kuna iya ajiye saƙon ra'ayoyinku a comment section ko kuma ta DM *** dangane da tattaunawar da muka yi da ita marubuciyar, tambaya a game da ita, tsokaci akan shirin, ƙarin haske dangane da abin da ya shige muku duhu. ku ci gaba da kasancewa tare da ni Halimahz a shafin ArewaBooks domin katari da muhimman abubuwa, ku yi following domin ta hakanne shirye shiryen da zan ke gabatarwa zai riskarku akan lokaci.
FATAN ALKHAIRI...