A SANADIN SOYAYYAR SHAN MINTI

010 Soyayyar shan minti

by @jameelarhsadiq6388

*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*


Na

*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*


***


010


Kallon number din na tsaya yi, dan bansan number din ba amman sai na dauka na kauga a kunne nayi shiru bance komai ba, ji nayi ance "My life fatan kinje gida lafiya.?"Tsaki nayi sannan nayi rejecting din wayar, kallona Aunty Asiya tayi sannan tace “Khady lafiya naga kin chanza lokaci guda? Kuma an kiraki waya kiyi tsaki ka kashe, ko wani abu ya haɗaku da Aminu ne."? Girgiza mata kai nayi sannan nace "Aa lafiya lau Aunty, kawai dai wayar bata amfani ne shiyasa kikaga na kashe." sai a lokacin Dejja ta dauko ta kalleni sannan kuma ta maida hankalinta wajen karatum novel din da takeyi a waya, matsowa Aunty Asiya tayi ta dafa ni sannan tace "gaya man waye ya kiraki waya a yanzun kika kashe bayan kin hadashi da tsaki? Shin kodai a akawai matsala baku gaya man ba? Dejja ajiye wayar nan ku gaya man abunda ke faruwa dan na lura Khady bata cikin natsuwarta sosai fa."


Murmushi Dejja tayi sannan tace "Aunty Asiya ba dole kiga bata cikin natsuwarta ba, Aunty Auta tasama kanta damuwa tunda wannan wawan Nurandeen ya dawo cikin rayuwa ta." dafe kirji Aunty Asiya tayi sannam tace. "Kamar ya Nurandeen ya dawo cikin rayuwa ta Dejja."!? Tayi question din cikin tsoro, dariya Dejja tayi sosai sannan tace "Aunty Asiya Nurandeen ya dawo wai yana son Aunty Auta kuma aurenta zaiyi, wai amman inji karyar shi ni na tabbata duniya bai maison Aunty Auta da aure sai mutun biyu, kuma cikinsu ni yanzun Dejja na kasa gane waye gwani dan ko wane yana iyakar bakin kokarinshi wajen nuna mata irin soyayar da yake yi mata" Harararta Aunty tayi sannan tace "Daughter ban gane mutum biyu ba? Kina nufin akwai wanda yake neman yayi ma Aminu shiga sauri."? Ɗaga mata kai Dejja tayi sannan tace "tabbs Aunty Dr Umar yana nan ya matsa shima yana son Aunty Auta, kuma mun gaya mashi abunda ya faru da ita yace yaji kuma yana so a haka, kuma sosai yake nuna mata soyayya kamar ba gobe ni wallahi har tausayi yake bani watarana Aunty idan kikaji yanda yake sonta sai dai matsala ɗaya."



Iska Aunty Asiya ta furzar a bakin ta sannan tace. "Maiye matsalar Daughter."? Gyara zama Dejja tayi sannan tace. "Yana da mata fa Aunty kuma abun taƙaicin ko shekara uku baiyi da yin aure ba, sai dai har yanzun matarshi bata haihu ba ina tunanin bata haihuwa ko kuma lokacin haihuwar ne bai kai da yi ba."


Numfashi Aunty Asiya tayi sannan tace "dole Khady ki shiga damuwa, kuma dole kiji tausayin Dr Umar sai dai ni a gani na baki dace da ko wane miji ba inba Aminu ba, dan Aminu yafi sonki da gaske tsakani ga Allah kuma badan wata suhura ta jikinki ba yake sonki kawai Allah ya ɗaura mashi sonki kin san maiyasa nace haka."?


Matsowa nayi kusa da Aunty Asiya sanann nace "A'a." murmushi tayi sannan tace "saboda ya soki lokacin da kike tare da budurcinki, ke kuma a lokacin kika nuna mashi tsana mai girma gami da karfi a fili kike cemai kin tsaneshi amman hakan baisa ya hakura dake ba, a lokacin saboda shi da rai yake sonki ba da zuciya ba, sannan kuma sonki a jinin jikinshi yake baya iya rayuwa idan ba tare dake ba, saboda da soyayarki yake rayuwa da sonki yake yawo a jinin jikinshi, akazo kika rasa abunda zaisa yace ya fasa sonki dan yanaso yanda yake saurayi shima ya fasa budurwa, dan ko wani saurayi gurinshi kenan a duniya fasa sabuwar budurwa gal a cikin leda, amman shi bai damu da wannan ba ke kawai ɗin dai yake so ba budurcinki ba Khady, wallahi Khady Aminu shine masoyinki na gaskiya karki yarda dadin bakin Dr Umar ya kwasheki kizo kiyi da nasani daga baya."


Numfasawa tayi sannan tasha ruwa ta cigaba cewa." shima Dr Umar din mutumin kirki ne, kuma masoyinki ne na gaskiya, amman baikai Aminu sonki ba Khady, naji Dejja tace yana da mata kinga ko shi ya ɗanɗana zaƙin budurci kuma yana ƙasa zuciyarshi ba zai taɓa mantawa da ranar da ya fara kusantar matarshi ta farko ba, sannan kuma tsarin da take tafiyar da gidanta haka zakibi idan kinje sannan kuma watan watarana dole sai yayi maki gori a yanda ya samaiki, ke bari kiji yana da mata fa kuma dole tayi kishi dake balle ma taji abunda ya faru dake itama sai tayi maki gori ko kuma ta zugashi cikin dubara irin tamu ta mata har tayi nasara watarana a gabanta yayi maki gorin rashin kawo mashi budurci da bakiyi ba, shiyasa ake son a rike mutunci saboda da haka Khady, kiyi tunani sannan kuma ki cigaba da addu'a." Shiru nayi kawai na kasa magana ina tunanin maganar Aunty Asiya, tabbas gaskiya ta faɗaman kuma take maganar Nurandeen ta faɗo man inda yake cewa babu wanda ya dace ya aureni sai shi, shinee kawai wanda zan aure mu rufama kanmu asiri tunda shine sillar rabani da budurcina da yayi, hawaye kawai na share na kwanta bance masu komai ba suma basu matsa da nace masu komai ba, sake kirana akayi ina dubawa naga number din Nurandeen ce dauka nayi, cewa yayi. "Haba Mylife mai yasa kike man haka? Ina sonki ina kaunarki amman ke baki gani, tabbas nasan ni mai laifine a gareki amman ki sani idan da laifi glove to harda na battery, saboda kece kika nunaman hanyar duk abunda nayi maki Khadija, karki manta ranar da na fara ganinki naji ina sonki kuma inason ki zamo mata a gareni kuma uwa ga ƴa'ƴana, tsakani ga Allah nayi murnar ganinki sosai amman ina zuwa da dare wajen ki kika zoman da wata irin shiga Khadija sannan kuma kinsa wani irin turare wanda ba zan iya control din kaina ba akanki ba Khadija, asilima kamshin turaren kawai naji na shiga cikin wani yanayi a lokacin idan banyi maki abunda nayi maki ba a ranar ina tunanin bani iya kwana duniya Khadija lokacin da na taɓaki abun mamaki bakiyiman shamaki ba sannan kuma baki nunaman ɓacin raiki ba, uwa uba kuma take kika biye ma bukata ta akanki Khadija, kenan duk abunda ya faru a tsakaninmu harda laifinki da kuma laifina wallahi ba halina bane kuma ban taɓa sex da wata yarinya ba duniya sai ke, ko Aziza da tazo man da bukatarta a kaina da na fara biye mata Khadija bayan rabuwata dake sosai muke soyayya da ita, amman ban taɓa kusantarta ba dan ban yarda da ita ba, ina tunanin bata rasa cuta dan na lura yar'hannu ce, kuma take na gane komai kikayi itace sila, itace tasaki a harkar duba da yanda Dejja ta nuna damuwarta akan ki, kuma ta gaya man yanda kuke da Dejja."


Yanda naji muryarshi nasan kuka yake shirin yi man da Nurandeen kuka baya yi mashi wahala, zaiyi magana na katseshi nace "dan Allah Nurandeen kayi hakuri ka rabu dani sannan ka barni naji da abunda ke gabana, dan ni yanzun na manta da baya ina gyara gaba ne, san... "No Khadija sai kin barni na ida gaya maki iyakar gaskiya ta, da ki yarda da karki yarda dole na gaya maki sannan na nemi yafiyarki akan abunda nayi maki Khadija, amman ki sani wallahi ni ba mazinaci bane kece kikasa na fara zina a rayuwata kuma akanki ban sake zina ba Khadija, haka na cigaba da soyayar shan minti da Aziza, amman ban yarda nayi sex da ita ba gudun matsala, ba yanda Aziza batayi ba akan na kusanceta amman naƙiya, ita kuma ta nace akan kudirinta akaina, wallahi Khadija watarana bayan mun gama waya da ita tace man gidana zata kwana tana wani hotel wajen saurayinta zai biya mata bukatarta dan tasan ko tazo wajena ba abunda zaiyi mata dan ta lura bani sonta kece kawai nike so shiyasa na baki kaina, amman ita na kasa dariya kawai nayi mata sannan nace sai tazo bayan na gama wayar da ita na cigaba da hidimata dan wallahi ko lokacin na kira wayarki sai naji ta a kashe duk ina cikin damuwar rashinki dan ni ba wanda nike so sai ke Khadija, dare yayi Aziza bata dawo ba dan har ɗaya tayi nikuma ina ganin haka na kwanciya ta nace ma gate man idan tazo ace mata karta tasheni." Kuka Nurandeen ya fashe dashi sannan yace. "Wallahi Khadija da safe aka kirani waya wai nazo hotel din da Aziza ta kwana da wayarta aka kirani akace nazo, da nace bani zuwa akace dole nazo ko, haka na shirya naje wannan hotel din Khadija nayi baƙin gani *INALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJUN* Khadija ina zuwa hotel din nace gani ance nazo akace na shiga wani room ina shiga na tadda gawar Aziza akan wani mutume suna cikin *ZINA* Allah ya aiko da mala'ikan mutuwa ya zare rain Aziza ita da wannan mutumin suna cikin aikata masha'arsu, wallahi Khadija a ranar naji na tsani kaina na tsani rayuwar da nayi dake, bansan lokacin da na fashe da kuka ba, nace ni maiye haɗina da ita da har za'a kirani? Kallona akafara yi ana mamakin maganar da nayi ina kuka, wani ne ya dafaman kafaɗa yace man Alhaji hakuri kawai zakayi amman ko matarka ta cuceka kuma ta cuci kanta da kanta gashi ta biye ma son zuciya ta mutu ta hanya bamai kyau ba, mu yanzun zamu kaisu Aminu kano mu samu a raba gawar sai mu baka taka suma mu basu nasu dan ba musulmi bane shi."

"Kallon mutumin nayi sannan nace a'a wallahi ni ba matata bace kawai dai muna soyayya kuma bansan tana wannan halin ba da ko soyayyar ma bani da ita."


"Nan take kallo ya dawo kaina mutumin yace kana nufin ba matarka bace wannan? Ɗaga mashi kai kawai nayi ina kuka Khadija kuma a lokacin ba wanda nike tunawa sai ke dan tabbas nasan nacuceki nida Aziza gashi ita Aziza ta tazo karshe tayi mutuwar asara Allah ma ya soni ba a gidana ta mutu ba, da bansan mai zance ma mutane ba sunaman kallon mutumin kirki, sannan bansan mai zance ma Dad dina ba da Mom, ji nayi mutumin yace yanzun kai bakasan gidansu ba? ɗaga masu kai nayi sannan nace wallahi bansan koda gidansu ba, asalima ban taɓajin tayi waya da yan gidansu ba, amman ta taɓa ceman majoji take anan kano daga nan bansan komai ba wallahi akan taba, shiru wajen kowa yayi yana mamakin abunda na fadi wayarta aka dauka aka nunaman yanda tayi saving din number ta tasa man *MIJINA* da abunda tayi saving kenan banyi mamaki ba dan nasan Aziza tace man tana sona kuma idan na yarda aurena zatayi nine na nuna mata rashin yarda da hakan da nasa tabar maganar ashe abun yana rainata." "Jinayi mutumin yace man muje majoji mu nuna pictures dinta may be ayi dace, da wanda ya santa haka muka tafi cikin motata su kuma sauran suka dauki gawarsu aka wuce hospital da ita.


*INALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJUN, nasan page din yau ya sosa ma wasunku zuciya wasunku kuma ba abunda sukaji duba da abunda Aziza tasa Auta akai ko🤔😭*


*bari kuji abunda nikeson ku sani shine, ba laifin Aziza bane kawai harda ita Khadija fa, dan ita taba Aziza fuska harta tasa bisa hanya, da ita Dejja bata bada fuska ba Aziza ta tasata?*


_sannan kuma ya kamata ku duba kuma kuyi tunanin maganar da Nurandeen yayi ma Dejja, tabbas harda laifin Khadija sosai, saboda idan zaku tuna randa zata fara zuwa wajen Nurandeen sai dai Aziza taba Auta turare mai karfi ta shafa, shin abun lura da abun shine shin shi Nurandeen ba mutum bane? Kuma babu jini a jikinshi ne? Dole yaji felling ya taso mashi idan har shi yana da lafiya._


*Note:-zuwa gareku yan'matan ya kamata ku daina shafa turare mai karfi kuna fita ko kuna zuwa wajen samarinku yin hakan yana bada tasiri wajen zina da dai abubuwa nagode*


Numfasawa Nurandeen yayi sannan yaci gaba da cewa. "Haka muka tafi unguwar su Aziza dan samun wanda Allah zai sa yace ya santa dan, dan kuwa addu'a tun ina wanda na sani har sai da yakai da ina yin addu'a kawai amman bansan abunda nike cewa ba tsabar shiga tashin hankali da nayi a ranar, cikin ikon Allah muka isa unguwar majoji nan muka raba ƙafa kowa da hoto a hannunshi muka fara nuna ma mutane ko sun san wannan baiwar Allahr, amman ansa ɗaya a'a bansan sanda kuka ya ida ƙwaceman ba saboda shiga ruɗu da nayi nidai bani ansa gawar Aziza saboda gidanmu ba'a santa , idan n kaita mai zance masu game da ita? Ita ba accident tayi ba balle na kaita gidanmu nace ba'a san danginta ba su taimakaman ayi mata sutura akaita gidanta na gaskiya, amman a hotel ta mutu suna zina, kinga dole mutuwarta tayi suna a faɗin nigeria Khadija, nidai bansan ina nike takawa ba kawai jefa ƙafa nike, sannna duk wanda na gani sai na nuna mashi picture dinta koda kuwa ƙaramin yaro ne wanda baisan kowa ba a unguwar, cikin ikon Allah naga wani matashin saurayi kamar ni koda ya girmeni ba zai wuce ya girmeni da shekara ɗaya ba, amman bada shekara biyu ba, zaune yake bakin wani shago a unguwar ga dukan alamu shagon nashi ne ma, ida zuwa nayi wajen shi na nuna mashi picture din nace ko ya santa, kallona ya tsaya yi sannan yace man ina na samu wannan picture din? Ce mashi nayi gidansu yarinyar ake nema a unguwar nan, dan Allah idan ya sani ya taimaka ya gayaman dan ana son gani iyayenta ne, girgiza kai mutumin yayi sannan yace ai na santa karka damu bari na kulle shagon na kai ka har gidansu, ai bansan sanda na rungume shi ba,na kuma fashewa da sabon kuka, kallona yake yana mamaki sannan yace kukan mai kakeyi ne bawan Allah, girgiza mashi kai nayi sannan nace nidai dan Allah abokina ka kulle shagon ka kaini gidansu kaji komai maiye idan muje, muna cikin magana muka hadu da mutumin da mukazo dashi , kallona yayi sannan yace fatan kai ka dace ka samu wanda ya santa ko? Bansan sanda Murmushi ya kauceman ba, na ɗaga mashi kai ina nuna mashi mai shagon nan, shima zuwa yayi yace mu tafi."


"Nan muka tafi mu dukanmu ba wanda yake magana, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyarshi Khadija, wani babban gida muka iso, dan gida yana da kyau ba laifi tsayawa mukayi bakin gate wannan mutumin ya shiga ciki bai jimaba sai gashi yace mu shigo, tare muka shigo dan harda police muke ni ban ma lura da wasu police ba sai lokacin da zamu shiga cikin gidansu, muna shiga aka kaimu part din baƙi nan muka zauna munyi jiran kusa ten minutes sai ga wannan mai shago ya shigo mana da ruwa da lemu yace kuyi hakuri mun barku zaune, ga Baban nan zuwa yanzun ya dawo baya gida, amman na kira shi waya yama shigo ya shiga part din shi dan ya rage kayan jikinshi, da sauri na ɗago kaina aiko muka haɗa ido biyu da wannan mutumin nan naga yana yar'kama Aziza, sauke kaina nayi kasa ban sake ɗagowa ba, can sai ga Babanta ya shigo da sallama a bakinshi, ansawa mukayi sannan muka bashi hannu aka gaisa, bayan an gama angaisawa aka fiddo picture din Aziza aka nuna mashi aka wannan yarinyar ƴarka ce."? "Allah sarki ɗaga kai yayi kawai amman baiyi mana magana ba, kuma na lura tunda aka nuna mashi picture din Aziza fuskarshi ta chanza ta tashi daga walwala ta koma rashin walwala, tunda muka lura da yanda yanayin shi ya koma sai muka kasa yi mashi bayanin abunda ya kawo mu, daurewa wannan mutumin yayi sannan yace Alhaji hannunka ba zai ruɓeba ka yanke ka yada, duk abunda Aziza tayi maka ya wuce dan Allah ka yafe mata, dan yanzun ba abunda Aziza take bukata a wajen ku idan ba wannna yafiya ba, sannan kuma addu'a idan har kuka yi mata haka to kun gama mata komai kuma kunyi mata abunda ita ta kasa yi maku, dan Allah Alhaji karkace ba zaka yafema ƴarka ba ƴarka ce ta cikinka komai tayi maka ayi hakuri kar a tuna baya a yafe mata."

"Tunda ya fara maganar Baban Aziza yake kallonshi har ya gama, sannan shima yace Bawam Allah ai Aziza da bakintaa tace ni ba ubanta bane, sannan kuma tace man na manta da na taɓa haihuwar wata mai suna Aziza kuka ya fashe dashi ya cigaba da cewa yarinyar nan ta zaɓi wata gurba marar kyau nida yan'uwa ba yanda bamuyi da ita ba akan tabar wannan ƙazamar rayuwa amman tayi kunnan uwar shegu damu, kaga wannna har aure sai da na daura mashi da ita, ranar da aka daura masu aure a ranar ta gudu daga nan bamu sake ganinta ba, koda kuwa labarinta ban sake ji ba sai yau ku da kuka zo mana da labarinta, daman ai haka bariki take angama yayinta shine aka dawoman da ita ko? To wallahi bani ansarta taje ta cigaba da rayuwar da ta ga itace ta dace da ita." "Dafashi wani police yayi sannan yace hakuri zakayi Alhaji dan yanzun haka Aziza bata bisa doron duniya, Allah S. T.W ya anshi rain Aziza dan kuwa yana hannunshi sai dai mai Aziza ta mutu ta hanyar da mai kyau ba dan kuwa a hotel ta mutu suna aikata *Zina* da wani wanda ba ma addininsu ɗaya ba, a haka rai yayi halinsa da akazo gyara room aka tadda gawarsu sai muka kira wannan bawan Allah ya nunani sanna ya cigaba da cewa munsa matarshi ce dan tayi saving din sunanshi da *Mijina* koda yazo yaga gawarta ya tsorata sosai kuma har yanzun bai daina kuka ba, yace mana baisan tana wannan harkar ba shi dai yana soyayya da ita suna shirin auren juna, sai yace mana ta taɓa ce mashi ita yar majoji ce, amman bai taba zuwa gidansu ba shine muka shigo majoji dan nemo gidansu yanzun haka gawarta ta hanya dan anraba gawar anba ancan nasu kuma mun bada address za'a kawo maku taku."


"Tashi tsaye Babansu yayi sannan yace inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Aziza tabbas kinyi mutuwar asara sai dai muna rokan Allah ya yafe maki nidai ko na yafe maki ƴata na yafe maki har abada inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Asiya Allah ya baiyanaman ke cikin aminci tabbas alhaƙin Asiya shine yake biyayarmu a gidan nan, alhakin marainiyar Allah shine yake biyayarmu Allah na tuba, tabbas na kasance uba marar kyautatama iyalansa, kallonshi muka fara yi sannam akace wacece Asiya? Ce mana yayi Asiya ɗiyarshi ce ta cikinshi mahaifiyarta ta rasu ta barta cikin matanshi suka matsa mata bata da gata sai su Aziza da suke da uwa a cikin gida ba soyayyar da bai nuna ma su Aziza ba da iyayensu amman banda Asiya da tazama baiwa a gidansu Aziza dan duk wani aikin bauta Asiya ce take yinshi lokacin da suna zaune a kunya chemist ɓarayi suka shigo gidansu nan sukayi ma Asiya fyaɗe yace mana yayi kuka a lokacin daga baya matanshi suka zugashi akan Asiya ta samu hanya tana bin maza tunda taga ɓarayi sunyi mata hanya, da bani yarda sai daga baya na fara yarda sai kuma ga ciki ya baiyana a jikin Asiya ni kuma ido ya rufe sai nace wajen iskanci ta samaishi dan daga yi mata fyaɗe rana ɗaya ciki ba zai shiga ba, da bakina da kaina na kori Asiya a gidana haka ta tafi tana kuka, ni kuma a lokacin ko a jikina dan gani nike ba zan yarda ba a haifa man shege a gidana ba, haka ta tafi muka cigaba da rayuwar mu cikin gidanmu muka manta da Asiya, bamu damu da wani hali take ciki ba sai ga Aziza ta bullo da halin bin maza na girgiza sosai tana level one a university ba faɗan da banyi mata ba, karshe na aure mata aure da Kamalu gashi nan ɗan ƙanenane amman sai ta gudu, bayan ta gudu kuma ƙanwarta ita kuma take neman mata😭, yanzun haka sana'arta kenan bin mata take dan itama ta tashi ta barman gidan tana zaman kanta, in kaiku karshe yanzun haka baki ɗaya yarana bana maijin magana daga mai shaye shaye sai mai yi ma ciki, yaran Amarya tane kawai masu ji su biyu ne suma ba wani girma sukayi ba sosai balle nasan ya nasu girma zai zo masu, inalillahi wa'inna'alaihirajiun 😭, wallahi Khadija sosai labarin Baban Aziza ya samu kuka muna cikin kukan akazo da gawar Aziza nan kuka ya zama sabo, haka aka gaya ma matan gida kamar anbusa isul haka unguwar ta kaure da rasuwarta haka muka hadu muka sallaci gawar Aziza muka rakata gidanta na gaskiya, bayan mutuwar da kwana uku nabar zuwa gidan su Aziza, kinji yanda karshen Aziza yazo Khadija dan Allah Khadija ki yafema Aziza na rokeki ki yafe mata dan al'farma Annabi Muhammad S. A. W."


Shiru nayi kawai ina hawaye dan har ga Allah naji mutuwar Aziza sosai, duk da ta bada gudumuwa wajen lalacewar rayuwata amman nasan harda laifina ba laifinta bane dan nice na bata fuska har ta sani a hanya, nayi mamaki da naji Aziza ƙanwar Aunty Asiya ce ji yayi shirun yayi yawa naji yace. "Khadija ya naji kinyi shiru say something please Khadija." Nima ajiyar zuciya nayi sannan nace "tabbas naji mutuwar Aziza sosai Noor, na yafe mata balle ma batayi man komai ba, tunda komai ya faru dani bata sani nayi dole ba, asalima iyakacinta dai kawai ta bani shawara nice nan mai laifi da na biyema son zuciyata na aikata aikin da nasani, kuma da nasani ance ƙeyace kuma kuskure na riga na aikata sai dai mu roki Allah ya yafemana baki ɗayan mu, ita kuma Allah ya kyauta makwancinta Amin."


Ajiyar zuciya naji yayi sannan yace "Alhmdullh Allah abun godiya tabbas Khadija keɗin ta daban ce kina da kyawkywan hali, wallahi halinki mai kyau ne wallahi Khadija ina sonki ba zan iya rayuwa babu ke ba dan Allah Khadija ki yafeman mu auri juna mu rufama junanmu asiri Khadija, ki tuna son da kika nunaman a baya ki maidoshi wallahi zan kula dake sannan kuma zan baki kulawa ta mussaman wanda ba zakiyi tunani ba Khadija, kin... "Ya isa haka enough please Noor, har da sauran soyayya a tsakanin mu daman? Har kana da bakin da zaka dawoman da soyayyarka a cikin zuciya ta? Kayi hakuri Noor tabbas ka faɗi gaskiya da na soka so wanda na sani har na mutu ba wanda zan ƙara yi ma irinshi sai dai yanzun kayi hakuri ba zan iya aurenka ba, ina maka fatan Allah ya baka wanda ta fini." ina gama faɗa mashi haka ban barshi yayi magana ba na kashe wayar baki ɗaya na kalli su Aunty Asiya da suka zuban ido tunda na fara wayar cewa nayi. "Daman bakuyi bacci ba."? Ɗaga man kai kawai Dejja tayi sannan tace. "Taya zamuyi bacci, bayan munji kinata salati harda kuka, mai kuma shi Nurandeen ɗin ya gaya maki."? Murmushi na ƙalilo mai ciwo sannan nace. "Aunty Asiya ina tambayeki mana."? Nayi mata maganar ina murmushi na samu na kauda damuwar da ke raina dan bansan na tada mata hankali duk da inajin ɗaci da ciwo na mutuwar Aziza, itama murmushin tayi sannan tace "tambayarni ina jinki Khady." kallonta nayi sannan nace. "Daman da kukaje kano kai da su Mama bakuje kuka gaida su Baba ba da matanshi." Chanza fuska ta ɗan yi alamun tambayar bata yi mata dadi ba, kallon juna mu kayi da Dejja tayi man alamun mai yasa nayi mata tambayar sai na nuna mata ba komai, maida kalona nayi gareta nace. "Yi hakuri Auntyna bansan tambayar zata ɓata maki rai ba da banyi maki ita ba." kamo hannuna tayi tana murmushi sannan tace. "Ko ɗaya Khady, kawai dai nayi mamakin tambayar ne, ai ni bani zuwa gidanmu har abada, Baba da bakinsa yace na bar mashi gida, kinga kenan da hannunshi ya yankan man ticket din shiga duniya, Kinga kenan banga amfanin komawa wajen shi ba tunda ni yar'iska ce ina neman maza har sunyi man ciki, Khady ba amfanin komawa karda na koyama yaranshi bin maza."


Girgiza mata kai nayi sannan nace. "Dan Allah kiyi hakuri ki sasanta da Baba, nasan yayi nadamar abunda yayi maki Aunty kin manta kece kika maidoni gida? Maiyasa ke ba zaki sasanta da Baba ba ki maida komai ba komai ba please Auntyna." murmushi tayi sannan tace. "Zan koma gida saboda ke Khady, amman ba yanzun zan koma ba sai nayi aure may be har haihuwa sai nayi sannan zan koma masu da mutuncina, su san na cigaba ba baya ba."murmushi nayi sannan nace. "To fatan ankusa auren ko."? Dariya tayi sannan tace. "Ai naso gaya maku tunda kuka dawo sai naga kina cikin damuwa shiyasa ban gaya maku ba." Dariya Dejja tayi sannan tace. "Wallahi Aunty ni nasan zakiyi aure kuma nasan Baba zaki aure." kallon Dejja nayi cikin surprise nace. "Ke wai wane Baban? Ba dai Yaya Jamilu ba."? Cewa tayi."ehmana shi, kiji Aunty Auta daman ina da wani Baban bayan shi."? Girgiza mata kai nayi ina dariya dan naji dadin yanda Yaya zai auri Auntyna, kallanmu tayi taga yanda muke ta farinciki tace. "Ku yanzun bakuji haushi ba? Bama kamar ke Dejja da za'ayi ma Mamanki abokiyar zama."? Girgiza kai Dejja tayi sannan tace. "Wallahi ba abunda mukeji harda Momy dan Momy ta gayaman yanda akayi har ƙin yarda da kikayi sai da aka sha wuya ai mun zama ɗaya Aunty kuma da zuciya ɗaya muke zaune dake, da yaje ya auro wata wanda bamu sani ba fa? Ai kinga gwara ke mudai fatanmu Allah ya bamu zaman lafiya." "Amin ya Allah."nace dan kuwa Aunty kasa magana tayi, kallon su na sake yi sannan nace. "Dejja kinsan kuwa Aziza ta mutu."? Kallona tayi sannan tace. "Taya zan sani Aunty Auta? Allah ya jikanta da rahama muma Allah yasa mu cika da imani."

Banji dadin yanda Dejja ta nuna rashin damuwarta ba, akan mutuwar Aziza sai dai kawai nayi murmushi nace. "Amin, ni zan kwanta sai da safenku."

Haka na kwanta ina tuna da nawa da Aziza kuma ina mata addu'ar dace wajen maiduka.


*Some weeks letter*


Washe gari da safe muka shirya mukaje gidan Aunty Fatima mun daɗe sosai, nidai ina cikin damuwa sosai akan masoyana guda uku, dan har ga Allah duka nike sonsu duk wanda na aura ina so, to taya zan fidda indan akace na fidda wanda ya dace da ya zama abokin rayuwata? Idan na tuna abun yakan sani cikin damuwa dan Yau da safe Mama tace mu fara shirin fidda miji dan aure za'ayi mana mun ida karatun a gidan mazajenmu, kuma Yaya Jamilu ya yarda da shawarar Mama yace ana gama bikinshi da Aunty muma za'ayi namu, hakan ya saman damuwa sosai.


Kallona Yaya Fatima tayi sannan tace. "Wai Auta mai ke damunki naga baki cikin wata walwala sai kace an gaya maki sakon mutuwa."? Murmushi nayi na kwantar da kaina bisa ƙafaɗarta sannan nace. "Bakomai kawai ina tunanin wa zan fidda cikin masu sona guda uku shine kawai damuwar Yaya." ɗago da kaina tayi tana kallona sannna tace. "Ikon Allah bangane masoya guda uku ba? Daman kina da wanda ya dace ki aura inba Aminu ba.?" Banyi mamakin tambayar Yaya Fatima ba, dan nasan su duka Aminu suke so na aura bayan kuma bashi ya dace ya zama miji a gareni ba, tabbas Aminu masoyina ne kuma masoyi na gaskiya sai dai ina tsoran ranar da zaiyi man gora akan rashin bashi kyautar budurci, amman idan na auri Nurandden shikenan ba batun gori danshi ya fara sani na, murmushi kawai nayi sannan nace. "Ehmana Yaya Fatima akwai Dr Umar da kuma Nurandeen, kuma duka suna zuwa gida."Murtuƙe fuska tayi sannan tace. "Daman ke har yanzun baki san ciwon kanki ba Auta? daman baki kishin ƙanki ban sani ba? Taya za'ayi ace kina kula wanda ya lalata maki rayuwa har yanzun? Kina sashi a jerin masoyanki Khadija? Wai Khadija yaushe zakiyi hankali kinsan inda yake maki ciwo? Wai... "Amman Yaya Fatima fissabillah ya kamata ki duba wani shine ya ɓataman rayuwa shine ya dace na aura dana auri wani yazo daga baya yanaman gori ko."? Na ida maganar ina shirin yi mata kuka, dan nasa araina bani auren Dr da Aminu dan basu suka dace da su aureni ba, Nurandden shine ya dace ya aureni ya zama miji a gareni, kallona kawai tayi sannan tace. "Tashi ki barman gida dan ubanki tun kafin ranki ya ɓaci kuma ki sani ba wanda zamu aura maki idan ba Aminu ba, ki rubuta ki ajiye shasha wanda bata san maiye rayuwa ba." tashi nayi ina gunguni, itama Dejja tashi tayi ranta ɓace dan duk taji abunda mukace da Yaya Fatima haka tasa driver ya maidomu gida bamuyi rabuwar arziƙi ba.


Itama Dejja bata ce man komai ba, koda muka koma gida da yake mutane sun fara zuwa ana hidimar bikin Aunty da Yaya dan sauran kwana biyu daurin aure, wanka mukayi muka huta Dejja ta dauko mana abinci mukaci, kallona tayi sannan tace. "Yanzun Aunty Auta da gaske Noor zaki ba dama ba Uncle Aminu ba."!? Cikin tsoro da tarin damuwa a fuskarta tayi man magana, itam Aunty Asiya da saura ta ida isowa wajenmu ta sama room din key tazo ta zauna ta zubaman ido tana jiran ansar da zan ba Dejja, su duka na kalla naga suna cikin damuwa girgiza kai nayi dan nasan nafisu damuwa dan kawai ni ta zama jinin jikina ne shiyasa, cewa nayi. "Insha Allah Dejja, Noor zan aura da yarda Allah." tashi tayi zauna tana girgiza kai tace. "No! No!! No!!! Impossible wallahi Aunty Auta, anya kuwa kina cikin hankalinki kodai Noor asiri yayi maki yasa kika fita cikin tunaninki Khadija Bello."!? Cikin masifa Dejja tayi man tambayar, nima tashi nayi nace mata. "Tabbas ina cikin hankalina kuma nasan abunda nike ba asiri Noor yayi man Khadija Jamilu Bello."Tashi Aunty Asiya tayi taga faɗa yana shirin kaurewa tsakanina da Dejja, kallona tayi sannan tace. "Bamai yi maki dole Khady, amman kuwa kina da hankali a yau ɗinan? Shin Khady a barshi kina cikin hankalinki to mai yasa zaki auri wanda ya wulakanta maki rayuwa yaci maki mutinci gaban Dejja kodai kin manta abubuwan da yayi maki? Idan kin manta zauna mu sai mu tuna maki Khady."


Murmushi nayi sannan nace. "Tabbas ban manta abunda Noor yayi man ba, dan kuwa har na mutu ba zan manta da abunda yayi man ba, sai dai ku sani zan aureshi saboda na cika wani burin nawa a kanshi, kuma wallahi sai na aureshi ni kaɗa nasan abunda yasa zan aureshi kuma ba zan gaya maku ba, sannan karku matsaman na roƙeku Allah yaba Aminu wanda tafini, amman ku sani babu rabon aure tsakanina dashi." Su duka shiru sukayi ba wanda tayi man magana, nocking din ɗakinmu akayi na tashi na buɗe abun har mamaki ya bani ganin su Yaya Fatima su dukansu sukazo kuma nasan aikin Yaya Fatima ne dan ta iya haɗa meeting din cikin yan lokaci shigowa sukayi suka kulle kofa Yaya Amina ce ta fara magana tace. "Sannu uwar masu hankali, wallahi Auta yau na ida yarda da baki da hankali mai zakiyi da wanda ya wulakanta maki rayuwa yaci maki mutinci ya rabaki da martabarki."? Kuka kawai na fashe dashi sannan nace. "Haba dan Allah ya dace kuyi man uzuri ku barni na auri Noor shi Aminu yayi hakuri haka Allah ya kaddara." Yaya Aisha ce tace. "Kika dai kaddara ma kanki Auta, ya kamata ki duba Auta wallahi Aminu shine masoyinki na gaskiya ba Nurandeen ba Auta kinji yar'autar Mama." murmushi nayi sannan nace tabbas nasan Aminu shine masoyin na gaskiya amman a haka zan hakura dashi na auri Noor dan kawai na ida wani buri na a kanshi." "Wai wani buri ne har haka Auta.?" Kallon Yaya Fatima nayi sannan nace. "Zaku ganshi idan na cikashi, yan'uwa kuyi hakuri nasan yau na ɓata maku amman haka Allah Ya kaddara karki damu." cewa sukayi a tare. "Allah ya zaɓa maki alkhari Auta mu zamu tafi."

"Amin." nace na kwanta su kuma suka kama gabansu a daren na shedama Nurandeen yazo gobe inason ganinshi haka a daren na shedama Aminu shima ya shigo gobe inason gani magana dashi, sannan na kashe waya na kwanta bacci..Washe gari da safe na shirya ma zuwan nasu cikin ikon Allah Aminu ya fara zuwa bai jima da zuwa ba sai ga Noor shima yazo, tare na anshesu na kaiku ɗakin baƙi bayan sun gama shan ruwa na shigo Kallonsu nayi sannan nace. "Fatan duk kunzo lafiya."? Murmushi sukayi a tare sannan sukace. "Lafiya lau, ya mutun gida."? Samun waje nayi na zauna sannan nace masu. "Lafiya lau, nasan kuyi mamakin kiranku da nayi ko."? Shidai Aminu baice komai ba kallona kawai yake sai Noor da yace. "Eh gaskiya Mylife nayi mamaki sosai nashiga damuwa karfin hali ne kawai nikeyi a yanzun haka." Murmushi nayi mashi naaida kallona a wajen Aminu da naga yayi mutuwar zaune tunda yaji Noor ya ceman Mylife take naji tausayinshi ya kamani amman mai bani da zaɓi dolene na daure nabi zaɓin da zuciya tayi man, sannan kuma nabi zaɓin Allah dan nasan kaddararce ta haɗani da Noor sannan kuma jina da Aminu haɗa suke wajen ɗaya da sona aka hallaceshi duniya, sai dai mai dole na auri Noor dan cima wani guri nawa a kanshi, amman Noor gangar jikina zai aura amman zuciyata tana wajen masoyin gaskiya Aminu, numfashi na sauke sannan nace. "Hakane Noor, daman nasan zakuji ba dadi da kuma fargaba samakon kiran gaugawa da nayi maku, daman ba wani abu yasa na kiraku sai dai a cikinku zanyi ma wani albishir sannan kuma zan ba wani hakuri saboda daman duniya dole a samu maiyin nasara sannan kuma dole a samu wanda zai faɗi."


Kallon Aminu nayi naga ya dukar da kanshi ƙasa, jikina ne yayi sanyi amman sai na daure nace mashi. "Aminu tabbas kai masoyinane na gaskiya wanda zan fito duniya na nuna shi ina cewa babu karya babu tamama masoyina yafi na kowa, tabbas Aminu duk macen da ta samaika a matsayin miji tayi dace, dacenma na har abada domin kuwa kai mutumin ne mai son kaga farincikin wanda kake so sannan kuma kake gudun ɓacin rain wanda kake so, zaka iya yin komai dan kawai farin cikin masoyinka sannan kuma zaka hakura da duk abunda kake mudun wanda kake so baya so, Aminu kayi hakuri haka Allah ya kaddara zuciya ba kai ta zaɓa ma a karo na biyu zuciyata da soyayyar Nurandeen ta aminta ba kai ba, Aminu haka Allah yaso nikai ba zamuyi taraiya ta aure ba sai dai muyi soyayya kawai kuma ina godiya da soyayyar da ka nuna man." Tashi tsaye yayi ya dafe kai sannan yace. "Inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah nagode maka da kake jarabani Allah ka bani ikon cinye wannan kaddara da ka sake dauroman, tabbas hakane Khadija banda saa a soyayya kuma ba zan sake soyayya kuma ba zan sake katanta yinta ba, daman ban taɓaba sai a kanki kuma ban shigo soyayyarki ba a sa'a Khadija ina sonki ina kaunarki ina maki so wanda bansan adadinshi ki tayani addu'a Allah ya rageman sonki Khadija Allah ya baki zaman lafiya da wanda kika zaɓa na barki lafiya saduwar alkhari." yana gama faɗin haka ya fita yabar room din ya barni daga ni sai Noor wanda dadi ya hanashi koda motsi dan yaji shi na zaɓa a matsayin miji bai damu da yanayin da Aminu ya fita ya barni ba, take naji nadama ta kamani dan nasan banyi ma Aminu adalci ba, bai cancanci haka daga gareni ba amman ya zanyi dole tasa na rabu da masoyin gaskiya dan cima wani guri nawa, ji nayi Noor na cewa. "Mylife daman nasan baki zaɓar kowa sai ni dan ni kaɗa ya dace dake ba wani Aminu ba, daman nasan har yanzun kina sona kamar yanda nima nike sonki Alhmdulillahi hankalina ya kwanta kuma ya dawo jikina tunda Khadija zaki dawo gareni wallahi nayi maki alkwarin ba zakiyi kuka ba sannan kuma ba zakiyi da nasanin aurena ba, zan nuna maki so wanda koda Aminu kika aura ba zai nuna maki shi ba, ilove you with all my heart.” Kallonshi nayi naga bai damu da damuwar na shiga ba a yanzun amman banga laifinshi ba dan yanzun baida damuwa tunda shine zaɓina Murmushi nayi sannan nace. "Hakane MyNoor ina sonka ina kaunarka ba zan iya rayuwa ba tare dakai ba, gari ga ka ɗanɗanaman dadinka ka koyaman sonka a zuciyata, zuciyata ba zata laminci zama da waninka ba, nidai fatana ka riƙeman amana kamar yanda na baka." Murmushi yayi sannan yace. "Na rike maki amana haka nima ni rike tawa amanar Mylife sonki ba zai taɓa barina na kalli wata mace ba har naji sonta balle har nayi tunanin haɗaki da wata Mylife kece ni kuma kece rayuwata wallahi inasonki sosai ni bansan irin son da nike maki ba abar sona, yaushe zan turo su Dad."? Murmushi nayi sannan nace. "Tun yanzun kuma." dariya yayi sannan yace. "Ai bani sanya akanki Khadija, kwara da zafi zafi kan buga karfe nidai tinda ni kika zaɓa ki bani dama na turo iyayena ayi maganar ko anyi aurenmu dan wallahi a matse nike sosai Mylife." ɗukar da kaina ƙasa nayi sannan nace. "Naji ka bari a gama bikin Yaya sannan muji abunda yace ko."? Ɗaga kai yayi sannan yace. "Hakane kuma kinga gobe nayi niyar zuwa daurin aurenshi, amman normal gobe zan dawo sai na gaisa da su Yaya Fatima ko."?

"Eh." kawai nace mashi sannan ya tashi na rakashi har bakin mota sai da naga tafiyarshi sannan nayi cikin gida duk jikina a mace balle da naga motar Aminu a parking space din gidanmu nasan bai tafi ba yana cikin gida, kasa shiga nayi dan ina tsoran abunda zan tadda a gida, amman sai na daure nayi ta maza na shiga zaune na taddasu a parlourn kowa yayi shiru sai kace wanda aka gaya ma sakon mutuwa, shi kuma Aminu ya dukar da kanshi kasa ga dukan alamun kuka yake suke bashi hakuri, sallama nayi ba wanda ya amsa man sai ma kallon banza da suke jifata dashi, bansan ɓacin rai yan'uwana balle kuma Mama amman sun kasa fahimta ta ko ɗaya, samun waje nayi na zauna nisa dasu a cikin parlour ina kallonsu dan banda bakin magana, Yaya Jamilu ne ya taso ya kamo hanuna ya haɗa waje ɗaya sannan ya kwasaman wani irin wawan mari, tunda nike a duniya Yaya bai taɓa buguna ba sai yau dan kawai naƙi Aminu, sake faskaman wani yayi bansan lokacin da na kwala wata irin ƙara ba dan naji marin ji nayi dama ace nabar duniya baki ɗaya, Aminu ne ya taso da sauri ya fisgeni daga rikon da Yaya Jamilu yayi man ya maidani bayanshi sannan ya fara cewa.


"Dan Allah Yaya Jamilu kayi hakuri ku kyaleta, idan har dan ni ka mareta har haka to bakayi man adalci ba dan ƙaraman ɗaci kayi a zuciyata dan baki jin yanda nikejin kukanta ba wallahi ji nike kamar ana ɗigaman dalma a zuciyata, na yarda da kaddara muyi mata fatan zaman lafiya da Nurandeen mana Allah ya kaddara ni ba mijin Khadija bane karda muyi jayaiya da ikon Allah mana Yaya." kallonshi Yaya yayi sannan yace. "Aminu ko ka matsa kaban guri wallahi ko kaima rainka ya ɓaci yanzun." yanda yayi ma Aminu maganar yasa na ƙara kwala wata uwar ƙara, dan banga alamun wasa a wajen Yaya ba danshi Yaya bai iya fushi ba, idan yayi abun ba dadi, rike Aminu nayi ina cewa. "Dan Allah karki barni wajenshi wallahi kasheni zaiyi Aminu ka rufaman asiri kamar yanda Allah ya rufa maka." cikin kuka nayi maganar Yaya Aisha ce tazo ta fisgeni daga bayanshi ta dawo dani a tsakiyar parlourn sake kamoni Yaya Jamilu yayi sannan yace. "Wallahi Khadija ba zan aura maki Nurandeen ba, koda kuwa zaki mutu saboda sonshi sai dai ki mutu, dan ubanki ki rasa wanda zaki sake aura sai wanda ya ɓata maki rayuwa yaci maki mutinci, kodan kinga ana kyaleki kina abunda kika dagama a gidan nan eyeh."? Girgiza mashi kai nayi ina hawaye dan na tsora sosai dashi yau dan ban taɓa ganinshi a irin wannam yanayin ba, murɗeman kunne yayi har sai da na ƙara kwala ihu sannan yace. "Yaushe kika zama mahaukaciya marar hankali? Yaushe zakiyi hankali Auta."? Cikin kuka nace. "Yaya dan Allah kabarni na auri Noor, kuyi man hakuri nasan banyi ma Aminu adalci na amman haka Allah ya kaddara nima bansan yanda zanyi ba dan Allah Yaya." bugeman baki Yaya Fatima tayi sannan tace. "Aiko sai dai ki mutu Auta, amman ki sani ba zamu aura maki wannam ya wulakantaki ba, kenan ance gobe yaje yayi ma wata saboda yasan idan yazo yace a bashi ya aura za'a bashi ko? To ki sani mu ba haka muke ba, mutuncinki muke nemanki kuma wallahi kiyi maza ki fidda wannan shashan yaron a zuciyarki dan ki sani wallahi bake ba auranshi." Shidai Aminu komawa gefe yayi yana kallon ikon Allah, dan kuwa Dejja ba abunda take man sai kallon banza dan duka haushi nike basu, sun kasa fahimta baki ɗaya nidai kuka nike dan na lura ba wanda yake bayana sai Aminu kuma sun hanashi ya basu hakuri balle ya fahimtarsu cewa babu kaddarar aure a tsakaninmu dan shi ya fahimceni duƙewa nayi ƙasa na kama kuka maicin rai, dan sosai nike ba kaina tausayi tunda na lura dasu bamai tausayina mun kusa 1hour ana abu guda wannan yace kaza wannan yace kaza dan ba wanda yake goyan bayan na auri Noor, sai a lokacin Mama tayi magana tace. "Wallahi Khadija kina ban mamaki, kaf yarana ba wanda take ban matsala sai ke tund na haifi Jamilu har nayi mashi aure na rabu dashi bai taɓa yi man laifi ba, ba an'rasa laifi ba ko dan ko harshe da hakori ana samun saɓani, amman dai laifi wanda raina zai ɓaci har nayi mashi kuka wallahi bai taɓata kuma bai taɓa tsalake umirnina ba koda kuwa baiyi mashi dadi ba zaice to Mama yanda kika ce haka za'ayi koda kuwa baiyi mashi dadi ba, gashi har zaiyi mashi aure na biyu zai auri Auntynki Asiya, haka Fatima har na aurar da ita itama bata taɓa yi man laifi ba haka Amina ma zuwa Aisha cikin ɓakin ciki muka rabu da juna sukaje gidajen aurensu dan aure ya zama dole sannan basu taɓa yi man gardama ba dan kuwa Aisha bata san Abduljalal zata aura ba sai da aka samata rana dashi sannan aka gaya mata abokin Jamilu zata aura batayi gardama ba tace bata so duk da alokacin tana da wanda take burin aure amman sai tayi godiya ta anshi zaɓinmu, amman banda ke Khadija dawa kikayi shawara da har kika kira su Aminu kika gaya masu abunda kika gadama? Gaban wannan sakaran yaron Nurandeen zakice baki son Aminu, Wallahi Wallahi Khadija duk duniya babu wanda na tsana a rayuwata kamar Nurandeen danshine yayi maki ciki, a sanadinshi kuma SANADIN SOYAYYAR MINTI dinki kika rasa mahaifarki dan ance ba dole mahaifarki ta sake riƙe ciki ba, amman shi Aminu yaji yace ya yarda zai aureki ko nayi rantsuwa bani kaffara wallahi idan kika gaya ma Nurandeen bai zama dole ki sake haihuwa ba sai yace ya fasa aurenki Khadija, to bari kiji wallahi Aminu zaki aura kuma mudun kika nace da wannan bakar zuciyar taki wanda ba'a gaya mata kikace sai Nurandeen to ki sani bani bake shasha wanda batasan ina ke mata ciwo ba, ni Hafsat wallahi tunda nike ban taɓa ganin shasha ba kamar ki Khadija, wallahi badan a gida na haifeki ba kuma ina kama da yan'uwanki da nace ke ba jinina bace masanyarki akayi man a abisiti sakara marar tunani." Kuka na sake fashewa dashi tashi nayi da gudu na rungume Mama nace. "Na shiga uku ni Khadija na lalace yau naga kaddara Mama dan Allah karkiyi man baki karki tsineman saboda Nurandeen, wallahi na hakura dashi na fasa aurenshi zan auri Aminu Mama ku yafeman ku dukanku bansan abun zai kai ga haka ba da ban zaɓashi ba wallahi." ina cikin kuka naji wayata tana ringing Dejja ta miƙoman tace. "Ga wayarki Noor ne."ƙin ansa nayi dan a halin da nike ciki ban iya daukar waya, kallona Yaya Amina tayi sannan tace. "Maza ki dauka kice mashi kin fasa auranshi karda ya sake yace zai turo iyayenshi Auta." sake miƙoman wayar Dejja tayi sannan na dauka nasa wayar a speaker cikin kuka naji ance. "Sallama Alaikum dan Allah ina magana da Khadija katsina."? Take gabana ya faɗi dan muryar mace naji kuma naji kamar tana kuka, kasa magana nayi sai ma kallon su Yaya Jamilu da nike da ido Dejja ce tace. " Wa'alaikumus Salam eh itace." sake fashewa da kukan matar tayi sannan tace. "Allah sarki Khadija sai dai muyi hakuri dake damu dan yanzun nan Allah yayi ma Nurandeen rasuwa sakamakon accident da yayi bayan ya dawo da katsina ya gaya mana kince ya turo to fitar da yayi aka dawo mana da gawarshi Allah yayi ma Nurandeen rasuwa inalillahi wa'inna'alaihirajiun." matar tace ta kashe wayar tana kuka, kasa motsin komai nayi sai ma kallonsu da na kama yi kama hannun Yaya Jamilu nayi sannan nace. "Yaya da gaske ne abunda kunena suka ji man wai Noor ya rasu ya mutu ya bar duniya baki ɗaya."!? Kama hanuna yayi ya rungume ni a jikinshi yana lailashi,dan kasa cewa komai yayi fidda jikina nayi daga rikon da yayi sannan naje wajen Dejja nace. "Dejja sunyi shiru sun kyaleni ba wanda yace man komai wai da gaske ne abunda kunnena yaji man? Nasan kece kawai zaki gaya man gaskiya dan nasan bai mutu ba karyane wallahi Dejja karyane bai mutu ba ɗazun nan ya tafi kano yace man gobe zai dawo daurin auren Yaya Jamilu sanna har ya gaisa dasu Mama anyi maganar aurenmu, Dejja dan Allah kice man karyane bai mutu ba wallahi sai na cika burin da na dauka kanshi Dejja."


Kuka Dejja ta fashe dashi sannan tace. "Inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Aunty Auta da gaskene ya mutu Allah yayi ma Noor rasuwa,Noor ya rigamu gidan gaskiya a halin yanzun addu'armu kawai yake bukata ba wannan kukan ba dan Allah." wata irin uwar ƙara na kwala sannan nace. "Tabbas na yarda ya mutu tunda kin gaya man da bakinki Dejja, amman naso ace da hannuna na kashe Nurandeen, naso ace nice nayi silar barin shi duniya, naso ace nice na ɗauki wuƙa da hanuna na ceka mashi a ciwo ya mutu idan yaso nima daga baya a kashe ni nasan na cika burina na dauka akan Nurandeen, amma... Tas! Tas! Tas! Yaya Jamilu ya wanka man mari har sau uku, dafe kumatuna nayi sannan na sake fashewa da kuka ina cewa. "Mainayi har haka Yaya zaka yiman irin wannam marin? Damai zanyi da rashin cika burina ko kuwa da marin da kayi man Yaya Noor ya cuceni ya zalunceni yayi amfani da soyayyar da nike mashi ya rabani da mutuncina duk wannan bai isheshi ba sai da ya sake dawowa a rayuwata dan ya ida dani daman ba dan komai na hakura da na auri Aminu ba sai dan na cima burina na kashe Nurandeen, ammm... "Ya isa haka Khadija." Yaya Jamilu ya katseman maganata sannan yace. "Wai ke wata irin zuciya ce garekine Auta? Wanda bata yafiya zuciya wand batajin shawara daman dan ki kashe shi kikace zaki aureshi? Daman ashe ba soyayar gaskiya kike yi mashi ba Khadija."? Cikin kuka nace. "Yaya soyayyar gaskiya nayi ma Nurandeen amman a da banda yanzun, Yaya dan Allah kuceman bai mutu ba dan Allah." Kamani Aunty Asiya tayi sannan tace. "Ya kamata ki dawo cikin natsuwarki Khadija, Nurandeen bai cancanci haka daga gareki ba Khadija, Nurandeen masoyinkine na gaskiya ya soki a lokaci biyu shima kinga addu'a ya dace kiyi mashi ba wannan kalaman ba Khadija, ki tuna soyayyarku mana yaci arzikinta kiyi mashi addu'a karki manta ya mutu da soyayyar ki a ranshi dan har gidansu, yaje yagaya azo ayi maganar aurenku Khadija munama Allah laifi muzo mu tuba ya yafemana balle mutun Khadija, tabbas bawan Allahn nan yayi maki laifi amman ki sani harda naki laifin komai ya faru a tsakanin ku sannan kuma harda kaddara dan Allah ya kaddara sai hakan ta faru kedashi, sannan kuma ya tuba kema kika tuba yazo ku auri juna inaga ai shima ya zama masoyin gaskiya ko Khady? Amman mudun kikayima Nurandeen haka bakiyi mashi adalci ba, dan haka maza kije ki wanke fuskarki kukan ya isa haka kuzo muje kano ayi jana'idarshi damu har kwana muyi zuwa gobe mundawo." Share hawaye na nayi sannan nace. "Hakane Aunty, tabbas kina tunatar dani abunda na manta, Allah sarki Allah ya jikanta Noor Allah ya haskaka kabarinka Nurandeen, daman Aziza tazo ta mutu kaima kazo ka mutu sauran ni kenan, Allah na tuba Allah ka yafemana tabbas mun aika laif." duka parlourn sukace Amin sannan muka shirya muka dauki hanyar kano dan zuwa jana'idarshi, ko a mota kuka nike dan sai yanzun nikejin mutuwar Noor sannan kuma nikejin soyayyarshi a zuciyata, sai dai mai rai yayi halinshi ya tafi ya barni.


Bamu san gidan su Nurandeen ba, location mukabi ta waya sannan muka isa, ban sake yarda da Nurandeen ya rasu ba sai da muka shigo unguwarsu mukaga mutane a unguwar zau zaune take na fara salati ina kuka haka mukayi parking muka fito cikin motocinmu mu mata mukayi cikin gida mukabar su Aminu da Yaya a kofar gida, bamu san kowa ba amman muna shiga wata budurwa age mate dinta tazo ta kama hannuna tana kuka tana cewa. "Allah sarki Yaya Noor haka Allah ya kaddara ba rabon muga abunda zaka haifa a duniya sannun da zuwa Aunty Khadija." ɗaga mata kai kawai nayi dan ni kuka kawai nike ko magana na kasa haka take riƙe da hannuna har ta kai ni wajen Hajiyarsu, ina shiga kuka ya zama sabo dan kowa ni yake kallo yana kuka ko yana fadin yanda Noor yake gaya masu yanda yake sona idan yaje gidansu zuminci har wanda basu san da labarina ba a ranar aka kama nuna masu ni ana cewa maganar ta karshe kenan da Hajiyarshi yace idan Dad dinshi ya dawo ta gaya mashi ance ya turo iyaye gidanmu, wai ashe aikanshi tayi taje kasuwa yayi masu provision din gida a hanya suka haɗa da mota Allah yayi mashi rasuwa, a ranar munyi kuka kamar ba gobe sai kunsan mangariba sannan muka dawo gida, ɗaga bikin Yaya Jamilu akayi saboda da mutuwar aka barshi next week , haka muka kama zuwa kano duk rana a gidan su Noor har akayi sakarakar uku sannan muka daina zuwa, duk sai nayi sanyi banjin dadin komai, dan komai na duniya yayi man fadi ashe yaudarar kaina nike da nike cewa zan kashe Nurandeen? Bansan har yanzun ina sonshi ba sai da bar duniya, ina zaune Aminu ya kirani waya yace ina fito yana parlour, tashi nayi nayi wanka sannan na shirya nasa hijab naje wajenshi zaune na tadda shi samun wajen nayi na zauna na gaidashi ansawa yayi sannan yace. "Dan Allah Khadija kiyi hakuri ki fidda wannan damuwar a rainki wallahi banjin dadi ina ganinki haka, a yanzun Nurandeen addu'a yake bukata tabbas anyi rashi amman hakuri za'ayi a cigaba da addu'a please." Murmushi nayi sannan nace. "Insha Allah zanyi kokari, kaima dan Allah kayi hakuri akan abunda nayi maka da yarda ba zan sake yin abunda zai ɓata maka rai ba." tashi yayi yace. "Har abada Khadija baki taɓa yi man laifi ba, kije ki shirya kizo ki rakani wani waje yanzun ina bakin mota zan jiraki."

"To."nace mashi sannan naje nayi sake kayana na shafa poder da janbaki nace naje na gaya ma Mama sannan na tafi dan ko Dejja ban gayyata ba bata gidan ma suna kumshi ita da Aunty da yake sauran kwana biyu bikinsu, haka na fito muka tafi yayi yawo dani sosai tun abun bai burgeni har ya burgeni ina dariya sosai sai dai ya tabbatar da ban cikin damuwa sannan ya kaini wurin salon aka gyaraman kaina akayi kunshi sannan muka dawo gida shima ya wuce gida. Koda na shigo gida gaida yan'biki nayi sannan na shige room dinmu tadda su Dejja nayi sun dawo zaunawa nayi na nuna masu abunda Aminu ya saya mana da kuma kunshi na nima, bamu kwanta ba sai da muka gama duk abunda zamuyi bukata a biki sannan muka kwanta washe gari mukaje muka haɗa gown din da zamu sanya ga biki sannan muka dawo munyi shirin biki yanda ya dace dan Aunty cewa tayi ba bidi'ar zamuyi mata a biki mu bari sai namu yazo sannan muyi amman ba anata ba, anyi mata lefe akwati biyar haka ma Mamar Dejja ita kuma akwati uku Yaya ya sake yi mata, komai nasu yana birgeni dan sun hada kansu tun yanzun suna shawara akan yanda bikin zai kasance dan ina iya cewa Maman Dejja ita babbar kawar a bikin.


Washe gari aka daura auren Yaya Jamilu da Aunty Asiya akan sadaki naira dubu hamsin, haka muka sha bikinmu aka kai Amarya dakin mijinta, sai dare muka barosu muka dawo muda Dejja muna masu fatan zaman lafiya, bayan bikin da sati ɗaya Yaya yasa Dejja tasa Registra ya turo iyayenshi aiko ya turo akayi maganar komai nima yasa Aminu ya turo iyayenshi duk akayi maganar sannan akasa baikon bikinmu wata biyu..Tunda akasa bikinmu Aminu yake ƙara kokari yana nunaman so, nima hankali na fara cire soyayar Noor a zuciyata ina saka soyayyar Aminu, cikin wata ɗaya sai gani inajin soyayyar Aminu har cikin raina dan har jinike bani iya rayuwa ba tare dashi ba, dan sosai muke nunama junanmu soyayya a bangare guda kuma muna ta shirin bikinmu dan Aunty Asiya itace uwarbiki dan da ita muke yi komai, komai zamuyi sai mun tambayeta shawara da yanda ya dace ayishi, Haka muka cigaba da yin shirin bikinmu, dan ba wata ƙawa da muka gaiyata daman bamu da ita balle har mu gaiyaceta ƙawarmu ɗayace Aunty Asiya muma bamuyi wata bidi'a ba tunda tace karda muyi haka ko akayi wa'azi kawai mukace ayi sai kuma walima.


Yau aka kawo lefen Dejja da yake bikin sauran sati ɗaya, anyi ma lefe masha Allah dan akwati bakwai kayi mata abun dai yayi kyau, bayan ankawo nata da kwana biyu aka kawo nawa nima akwati shabiyu akayi man munyi murna sosai, an kawo lefena da kwana ɗaya akayi wa'azi sannan kuma washe gari akayi walima, next tomorrow kuma cikin ikon Allah da kuma yarda shi aka daura auren *AMINU IBIRAHIM* da Amaryashi *KHADIJA BELLO* akan sadaki naira dubu hamsin sai kuma aka daura auren *MUHAMMAD SAGIR* da Amaryashi *KHADIJA JAMILU BELLO* duk akan sadaki naira dubu hamsin haka aka daura aurenmu cikin aminci da mutunta juna, bayan daurin auren angwaye sukazo akayi hotona, anan ne naga Dr Umar yazo yayi man fatan alkhari sannan mukayi picture dashi da Aminu da yake shine baban abokin mijin Dejja, bayan an gama shagali aka tafi damu Yaya yayi mana wa'azi aka kaimu wajen Mama itama tayi ma sannan Maman Dejja duk sukayi mana sannna aka wuce da ko wace gidan mijinta muyi kuka sosai inaji Inagani aka rabani da Dejja ita aka tafi da ita kano ni kuma aka tafi dani gidan nawa mijin anan katsina..Bayan an kaini angama ganin gida kowa yayi mana addu'a aka barni ni ɗaya dan banda ƙawa balle ta tsaya sai anrako ango sai ta tafi, kwanciya nayi na cigaba da kukana inaji aka rakoshi ban daina kukana ba koda ya shigo naje kin fita nayi sai dai yaje sukayi maganarsu sannan ya rakasu ya kulle gida, ya shigo ya tadani yace. "Myluv ayi hakuri ki bar kukan nan hakan nan pls."ɗaga mashi kai nayi ina share hawaye, cireman hijab din yayi sannan yace. "Maza kije kiyi wanka nima bari naje nayo sai muzo muyi sallah ko."? Again banyi magana ba shiga toilet kawai nayi inaji shima ya fita, wanka nayi na fito na shirya nasa hijab, sannan shima ya shigo mukayi sallah yayi mana addu'a, ya dauko kaza ya zuba mana yace muci haka mukaci bayan mun gama ya maida kayan kitchen, wanko bakina nayi sannan na dawo na kwanta, bayan ya dawo ya hau bisa gadon ya fara yiman cakulkuli yana cewa. "Shine sai ki kwanta ko ki jirani nazo muyi hira."? Dariya na fashe da ita haka ya kama yi man cakulkuli yana magana, a haka ya fara chanza mana salon wasa, dan kafin na ankare har yayi nasarar rabani da kayan jikina, kuka na fara yi mashi, nan ya fara girgiza man kai yana cigaba da aika man wasu zafafan kissing wanda kesa ka manta da idan kake haka ya kama juyani yanda yake so yaya shafata har ya fara neman hanyar shiga.


Tunda na auri Aminu muke soyayyar mu abun gwanin ban sha'awa dan duk abunda nike so shi yake man, shiyasa nima bani son ɓacin raishi, dan soyayya muke ba kama hannun yaro..Itama ba bangaren Dejja hankalinta kwance a gidan mijinta dan kusan kullun sai munyi waya, muna jin lafiyar juna, bayan munyi aure da wata guda na hada kayana na koma makaranta dan cigaba da karatuna, idan na samu time nazo weekend shima idan ya samu time yazo man weekend haka muketa rayuwarmu cikin aminci da jindadi.


*After some years*


Abubuwa da dama sun faru harda gama karatunmu da kuma haihuwarmu dan na riga Dejja haihuwa sai da na haihuwa da wata biyu sannan itama na haihu ni namiji na haifa yaro yaci sunan NURANDEEN muna kiranshi da Noor, ita kuma Dejja ta haifi JAMILA muna kiranta da Meelat, itama Aunty Asiya ta haifi mace ansa mata gudu biyu ta farko sunanta HAFSAT sai ta biyun sunan AZIZA aka samata dan taje sun sasanta da yan'gidansu yanzun zuminci sukeyi sosai abun gwanin burgewa..Bayan wasu shekarun na sake haihuwar IBIRAHIM, haka muka cigaba da rayuwa da yaranmu dan bani aikin gwananti saboda mijina baya yarda..Sis Jameey abunda yasa kikaga nayi maki magana akan ki rabuta labarin rayuwata saboda wasu yan'matan su gyara idan kuma suna da niyar yi su daina, maganar gaskiya nasha wuya kafin mijina na yarda na bada wannan labarin sai da na nuna mashi mahimmancin abun sannan ya yarda sai kuma akayi sa'a na karanta wani novel dinki mai suna A SANADIN LINk na tsorata sosai na karanta anan na samu numberki har muke chating, a hankali na fahimci hankalinki baki da wulakanta jama'a ke macece mai saukin kai har mamaki nike watarana nace anya ke marubuciyatace saboda saukin kanki yayiwa baki da shariya harda wannan dalilin yasa na zaɓaki da ki rubuta, har yanzun ina garin parthcourt da zama nida yarana dan can akamaida mijina da aiki, kuma tunda nike dashi bai taɓa yi man gorin rashin kawo mashi budurcina da banyi ba gashi har muna da yara biyu ina dauke da cikin ta uku insha Allah.


*Masoyan Jameey yar'mutan kankia ku gyara zama sannan kuma ku karkaɗa kunnunwanku dan kusan dai alqalamin Jameey baya rubuta shirme😌to ku shirya sabon zafaffan littafinta yana nan tafe,salon tafiyar daban take da sauran dan kun karanta DA'IMAN ABADAN kunji yanda yake ina tabbatar maku da sai....ya fi shi sau 1000 dan soyayyar, chakwakiyar, munafirci,zamba cikin aminci,rashin tausayi da imani,ban dariya harda ban haushi dai-dai sauransu duk sun hadu a cikin new book mai suna....🫣 Ba zan fadi sunan ba dan rowarshi nike soon zai fara sauka dai 😊*


*Alhamdullahi Allah ngd maka da ka bani ikon kammala labarin nan abun da yake dai-dai Allah ya bamu ladar Ni da ku a tare inda mukayi kuskure Allah ya femana baki ɗaya..har kullum ina sanar da ku idan na gama littafi a ɗauki darashin da ke ciki a watsar da shirmen da ke ciki dan Allah*


*Dan nayi labarin soyayyar shan minti dan na nutarsar damu ilar yin hakan Allah kuma yasa yan'uwana yanmata sun hankalta da ilar abun ngne*


*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*


*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*