Chapter 1
MAKAUNIYAR SHARI'A
_( Sai a Lahira)_
*IKILIMA ADAM* _( Kyauta daga Allah)_
_Marubuciyar da ta_ _nishandatar daku a_ _littafan ka kamar haka_:
*Kaikajawa kanka*
*Kanwata*
*RAI DAYA ( Jan Zaki)*
*RUDANI*_( mai tafiya daukan rai)_
_Da sauran su_ .
_Yanzu gani dauke da sabon littafina mai suna_ *_MAKAUNIYAR SHARI'A_*
_Wannan Littafin na kudi ne , da zaran na gama free page , bazaki sake samun sa ba , saide na sata_
Kibiya *dari biyar* kacal domin samun shiga group na musamman .
Domin Karin bayani a tuntube ni ta wannan lambar *** ko + 22953726162 .
Siyen nagari maida kudi gida.
_Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imomin_ _ka a gareni , yanda nafara Lafiya kabani ikon gamawa Lafiya , Alkhairan dake cikin sa _ka bani ladan sa , _sharrin dake ciki ka _yafemin_ .
_Allah ka dauka_ _Alkalamin marubuta a _duk in da suke_
_Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta_.
*Besty ( Sarat Alkasum)*
*Maman Amatullah*
*Ummu shkura*
*Fadila Sani Bakori*
*Maman Sharifa*
*Mamashu*
*ABBA Yakubu*
*Dan Salma*
*Da Autan Jarumai*.
_Wayanda ban samu damar Kiran sunan su ba , duk ina Mika sakon gaisuwata a gare ku_.
_Yayyena abun Alfaharina_
*Hadiza*
*Hussaina*
*Hassana*
*Maryam*
Gaisuwa ta mussaman gareki
*Anty Zulai* , mutan kano , surukar Auta na.
_Jarumai writ association_ _marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma_
SHAFI NA ƊAYA
Ahankali take bin kusurwa na jejin tana tafiya cikin wahalilliyar azabar ciwon baya da ya sa take taku kamar wacce aka daurawa kaya a bayan ta , ba tare da ta ankare ba , tsohuwar kofin dake hannun ya fadi kasa wargas, nan dan nan idanunta , suka cika da ruwan hawaye , cikin rawar murya ta ce , " Washh bayana ta ya zan durkushe daukar wannan kofin ". ta kai karshen zancen cikin rawar murya , lokaci daya idanun ta ya kada jajir kamar gauta , kwallan da take dannewa ne ya samu daman zirarowa yanabin kyakkyawar fuskarta , kallon hagun ta ta yi ta hango wasu yan Yara matasa da bazasu wuce shekaru sha-uku , sha-biyar ba , kallon su take yanda suke tafiya suna jifanta da kallo me nuni da tsantsan tsana da takaicin ganinta , Lura da hakan ya sa zuciyarta harbawa da karfin tsiya kamar ze bar gangar jikinta , kallon banzar da suke bin ta dashi , banda mutum daya daga cikinsu da ya nuna kalan tausayi a gareta , yasa ta yi kasa da kanta , ganin sun harare ta suna kokarin wuce ta ya sa cikin Karfin hali , murya raunace cike da fargaba tace,
" Dan Allah ku dauko min kofin nan ban iya durkushewa bayana ke masifar yi min ciwo ". Ta idasa zancen tana tunanin me ze biyo ba , domin tsayuwar da suka yi tasan akwai badakala.
Wani kallon Banza suke bin ta da shi , hade da kallon jikinsu , kana suka kai dubansu akan suturar dake jikin ta ayage kana iya hango saman na shanunta da suka fara tasawa daga kirjinta , daya daga cikinsu mai dan hankali ya yi karfin halin Fadin" Subuhannallah sannu !! ko"!. kokarin Dauko mata kofin yake , yaji yan uwansa , suna fadin " haba ya zaka dauko kofi ka bata, so kake ta shafa maka bakin fenti , wannan Yarinyar ina tabbacin mayu ne , yo inba maita ba , tun tana yar shekara biyu zuwa uku suke makale karkashin bishiya itada tsohonta da rashin gaskiya yasa kwata_kwata yaki bari asan fuskarsa kullum sanye yake da rawani kamar Sarkin Aska , fuska kuma arufe kamar buzaye , su ma buzayen basa rufe fuskarsu , ya maida kansa kamar mata masu yawo da nikaf, tsabar rashin gaskiya duk inda yarinyar nan tazo to babu nasara awajen ". ya yi magana yana kara nuna mata tsanarsa a fili , lumshe idanunta ta yi domin kalamansa ba karamin huda na gashin jikinta ya yi ba , ji take kamar yagama ci mata fuskar , batasan meya kalmar mayyah yake nufi dan wasu maganganu Papynta ke koya mata bata taɓa rabar cikin mutane ba .
Shi ko be kula da batun dan uwansa ba , hakan nan yaji yana bukatar taimakonta kamar yanda ya saba zuwa kai musu taimakon abinci da sauransu ba tare da yan uwansa sun sa ni ba , dauko ma ta kofin ya yi yana goge kasar da ya taba kofin da rigarsa , kana ya mika mata cike da girmamawa .
Duk da mawuyacin halin da take ciki hakan be hanata murmusawa ba , cikin langwabar dakai ta ke ma sa godiya , kauda kanta ta yi da kallon takaici da sauran suke bin ta dashi , hanzarta barin wajen tayi gudun kar su ma ta mugun abu , dan matuka sun ji haushin dan uwansu da ya taimaka ma ta , tafiya take , tana jin tashin hayaniyarsu da yan uwansa akan sai sun fadawa iyayensu , ya taimaka mata , tana tafiya tanajin tausayinsa.
Kallon ta suke dukan su , yan uwansa , cikin takaici suka ce , "wannan Yarinyar mai tsufar Al'janu ka taimakawa , yarinyar sai shegen kyau kamar ita tayi kanta , ga shegen bakin jini kamar mujiya , ni fa banda kyaun halittar ta da zubin kirarta da wallahi inna ganta a hanya canza hanya zan yi."
Cikin damuwa wanda ya taimaka ma ta ya ce , "be kamata ka yi wannan furucin ba saboda ita ma ba yin kan ta bane ta ke cikin tsinannen talauci ba , kuma maganar sai kun fada a gida dan Allah kubar shi ." Nan dai sukayi ta surutai akanta shikuma sai hakuri ya ke basu karsu ballo masa ruwa yasan yanda iyayensa suka tsani yarinyar nan .
Ita kuwa tafiya ta ke tana bin rairayi na titin jirgin kasa , tana tafiya tana ciza yatsarta har ta isa bakin titi , kasantuwa duk ranar Juma'a ne ranar da ake rabon nonon shanu , a hankali take taku kamar kazar da kwai ya fashe mata aciki , har ta karaso wajen amsar sadakan , fararen idanunta masu haske kamar kyandir ta ke kallon jerarrun kofuna da suke a kasa , kasa durkushewa tayi bare ta ajiye nata kofin ajerin na sauran yaran.
Tana kallo wani Alhaji , cikin farar shaddarsa sanye da babban riga , ya siyan nonon shanun wajen jerin matasan yara fulanawa masu sanye cikin kayansu na asali , be bata lokaci ba , ya zo ya daidaita sahun kofofuna dake jere a kasa , cikin nutsuwa ya ke zubawa jerin kofufunan da suke akasa nonon yana gama zubawa ya dago daga durkushen da yayi caraf idanunsu suka tsarke cikin na juna shi da Yarinyar , ahanzarce ya dauke ganinsa akanta , jin mummunar faduwar gaba , dan ba karamin kidimewa ya yi ba , ganin ya gama zuba sadakan Nonon , wanda ya jawo yaran fara kokawan wajen daukan kofinansu . Yarinyar kuwa kwalla masu zafi ne suka cika kwarmin idanunta , cikin kukan zuci ta ce," kenan yau bazan samu sadakan ba , kuma sun ki koda kallo na bare nasa ran samun Nonon" . Fara neman wajen zama take yi domin ba tasan yanda zata koma muhallinta babu Nono a hannunta ba , duk matasan yaran da aka yiwa rabon nonon kowannen su , daukar rabonsa yake yana ficewa tare da kwabe baki suna kallon ta. Na karshen ne da ze fice yayi karfin halin Fadin " kin tsaya girman kai anyi rabo babu ke ." Tsunkuyar da kai ta yi dan a zatonta be cancanci amsa ba , wata zuciyar ta ce" , karki damu da abinda yake fade duk da besan zuciyarki da niyarki ba" . Da wannan tunanin ne tayi banza da shi ya yi ta maganganun sa tayi biris kamar batasan yana yi ba , yana gajiyawa ya kama hanya ya fice yana surutai . Ita kuwa cikin kunan zuciya take bin bayan sa da zararan idanunta masu haske da kallo . Cike da mamaki take kallon matasan yan matan fulanin masu siyar da nono awajen ko wacce ta daukan kwarya ta , suna kallonta suna kwabe baki hade da jinjina taurin kai irin nata.
Kusan mintuna talatin ta dauka tana a wannan yanayin , bata ankara ba sai ji ta yi muryar wata Mata daga sama , cikin karfin hali Matar tace, " yan Mata me kike yi anan wajen ? ina Gidan ku? ina iyayen ki? kike zaune nan wurin ke kadai da duk alamun ma bakida isassen lafiya ".tayi magana cikin tausayawa.
Afirgice take kallonta jin maganganun ta daga sama ba zato ba tsammani , kallon ta take da idanunta , masu cike da damshin ruwan hawaye, numfashi me karfi ta fesar kana cikin rawan muryan , da kadawar harshe ta ce, " yanzu nan zan koma Gida tun da sadakan nonon ma dana zo karba ban samu ba , ga kishi mai tsanani yana damuna ko zaki taimaka min da Ruwa ". takai ayar zancen idanunta nakan matar dake sanye cikin doguwar riga bleu sky mai zanen tsuntsaye , gajera ce me yar kiba da kauri , kana fuskarta tana da zanen Kanawa me uku-uku , baka ce mai dan fadin fuska.
Matar kuwa tsaf ta kura mata idanu cikin kankace Murya tace ," ya sunan ki Yar nan".? Kallon take babu kiftawar idanu , ganin kamar batada shirin bata amsa yasa tayi kwafa tare da sake narkan da murya cikin salon jan hankali . Maganar da take shirin yi ne ta katse jin yarinyar na magana.
" Sunana *Farida* , amma Papy na , nakira na da " *Amatullah*." Tana kai aya , ta fara yunkurin tashi domin ta tsani tambaya.
" Dan tsaya mana , ga me tsaida ruwa cen dan Allah tsaya ki amsa sannan naga kina hucin zazzabi akwai magani a jakata , shin zaki karba ?."
Gyada mata kai tayi ba tare da ta kalle ta ba , matar hanzarta karbo ruwan ta yi tare da bata tasha , ga mamakin ta sai gani tayi ta shanye ledar pure water biyu nan take , kana ta fara mai da numfashi , ballo ma ta maganin tayi ta mika mata hade da kara karbo ruwan , nan ma sai gani tayi ta karba hannun ta na rawa ta hadiye ta shanye shi .
Murya cike da kuka Amatullah tace, " yanda kika farantamin kema Allah ya faranta miki , kinsan darajan dan adam ke ce ta biyu a nahiyar nan da kike iya bani abu babu shamaki ko tsoro ". tana kai aya , bata jira cewar Matar ba takama hanya cike da dan tsaurin ta , tana tafiya tana waige -waige sam bata son Matar taga hanyar da tabi bare tasa ran biyota , koda tayi nisa ganin ta bacewa Matar ne yasa ta canza hanya izuwa ainihin hanyarta.
Ita kuwa da kallo ta bita har ta bacewa ganinta . Ta dade daga tsayuwar da take tana nazarin fuskar yarinyar da kamanninta , domin yanda take magana akwai hikima aciki ." Barin wani tunanin ta yi ,tare da kai dubanta akan me siyar da ruwan da ke jiran ta biya shi kudinsa , cikin hanzarinta tattare da kuzarin ta ,ta karasa gaban sa , Fesar da numfashi me zafi tayi kana furta .
" Wannan Yarinyar dana karbarwa Ruwa a hannunka , dan Allah daga ina take fitowa ?." tana kai ayar zancen , wayarta yafara ruri, hankalin ta da nutsuwarta , ta tattara gun amsa kiran daya shigo wayar ta , sosai ta maida hankalinta akan wayar da take , batare da ta ankare ba mai saida pure water gaba ya yi abun sa yana banbamin fada akan bata ma sa lokaci da tayi ga shi ze je islamiyya , itakuwa tana gama Wayar , Murmushi kwance a kan Fuskarta ta waigo da shirin yi masa magana , ragowar kalamanta ne suka samun damar makalewa nan da nan annurin ta ya dauke , ganin wayam babu shi babu dalilin sa kamar saukar aradu , zazzare idanunta , ta soma hade da kara ware su dan tabbatar ba gizo idanunta suke ma ta ba , ganin dagaske babu shi a wajen ta fara nazarin ta ina yabi bayan be karbi kudin sa ba , idanunta , ta mai da akan kasar wajen , sahun kasar take kallo duk da yashi ne amma ga mamakin ta , bata ga sawayen sa ba , hankalin ta kara tashi ya yi cikin tsoro da fargaba ta fara tafiya cikin sauri-sauri , kokarinta , shine taga tabar wajen , gabanta wani rass rass yake badawa da masifar karfi.
_______
Garin Abuja Asokoro
A hankali ya ke taku yana tafiya cikin isa da kasaita yayin da mabiya bayansa suka kewaye shi kamar sun taho da Sarki ko shugaban kasa .
Baki daya all Gidan dukar da kansu su kayi , suna kwasar gaisuwa , fuskarsa babu yabo babu fallasa yake amsa musu , kana ya gyara tsayuwarsa yana mai binsu da kallo daya bayan daya.
Sautin muryansa ne ya sa ni kara matsowa domin tun da nake bantaba jin murya mai daɗin amo da dadin saurare irin nasa ba , kallo daya na masa naga hadadden gaye tsaye sanye cikin riga da wando bleu sky mai suite , bakin takalmin kafarsa mai shening ba karamin daukar hankalin mai kallonsa ya ke ba , fari ne sol zubin larabawa , kwantaccen sumar kansa da ya yi yanayi daya da sajen fuskarsa wanda suka kara miki kyau da cikar haibarsa , hancinsa kamar biro yayi daidai da karamin bakinsa mai jajayen labbai. Gefensa daya kuwa Aminisa ne Mansur wanda suka taso tun suna yan yara dasu , ra'ayinsu daya basu taba canza ra'ayi ko tunaninsu ba , saide afannin mata shi Ridwan ya tsani Mata , hatta Mahaifiyarsa sam baya sake mata , kannensa mata da dan sauki-sauki dan wataran su kan ga Annurinsa, dariyarsa ce zasu iya rantsewa basu taba gani ba , banda Mahaifiyarsu kila ita ma tun yana Yaro ne . Mahaifiyarsa Hajiya Saratu Abubakar , da kannensa kannensa hudu mata uku namiji daya.
" Ina ga mun iso Gida kowannen ku yana iya komawa muhallin sa." Cewar kyakyawar matashin .
Hannun ya mikawa na kusa dashi da dukan alamu shine Abokinsa Mansur , na kut-kut , musabaha suka yi yayin da abokin nasa yake fadin" Ridwan na samu labarin a Jahar Kano a Garin Daguzau babu Wutar nepa kimanin yau wata biyar kenan". Ya idasa zancen nasa yana kara fito da wata farar jaka transparent mai dauke da file bil adadi marasa iyaka , wata yar farar takarda ya mika masa hade da kara kusanto inda Ridwan yake.
Shi kuwa kamar andauke dauke Wutar Lantarkin jikinsa haka nan yaji jikinsa yafara tsuma , a zahiri kana kallon sa zakayi tunanin fuskarsa babu fushi ko damuwa amma kasar zuciyar sa kamar ana dandatshi da dutsen Wuta , wani irin zufa da ya fara keto masa a dukan sassan jikinsa . Hannayensa na rawa ya karbi File din daga hannun Mansur abokinsa , kana ya fara ware zararan idanunsa masu ɗauke da eyelashes da medical glass , yana kallon file din cikin tafasar zuciya ba tare da ya iya furta wata kalma me tsawo ba ya ce, " Mansur Muje daga ciki." daga haka be kara furta komai ba . Yayin da yayi gaba Mansur ya take masa baya , mabiyan sa kuwa , tsayawa suka yi suna kus-kus suna fadin wai ace *Minister of power* shima yana fuskantar kalubale ga aikin sa, kuma Gidansa sam ba'a yanke Wuta da...... Sauran kalamansa ne suka makale yayin da yaga duhu ya mamaye da ilahirin Gidan ko ina. dafe da kirji suka ce , " subuhananallah yanke wuta agidan *Minister of power na Nigeria* , sossai suka tsaya suna mamakin lamarin , nan dai suka bar hiran tare da fara neman tochla domin haskawa kasantuwa ko ina na gidan ya dau duhun gaske. Wasu daga cikinsu tochla wayoyin su haska domin gudun afkawa inda cancanta ba .
C'en cikin Gida
Cikin gigita Mamy ke tafka salati hade da fara lalubar inda wayarta ya ke , razana tayi jin kamar an shako wuyar ta daga baya , callara ihuu tayi wanda yasa , ta fara kokarin faduwa a harzance , Ridwan da ya karaso falon rike da hasken Tochla din Wayar sa ya haskata akanta , kafun takai ga yin kasa tuni ya sa hannayensa masu taushi ya tallafe ta . Itakuwa zazzare idanu ta ke tana fadin" Ridwan shake ni akayi fa!." Cikin zararre idanu me nuni da zallan tsoro da fargaba take bin haske tochla din Wayar sa , da ya dan haske daidai fuskarta kana yana kashe ma ta idanu da mugun hasken , hakan ya sa ta sa tafukan hannayenta , ta tarufe fuskarta , ahanzarce ya'yan ta dake falon suka zagayeta kowannen su , cikin damuwa suna ta fadin" anya Mamy ba tsoro kikaji ba? , babu wanda ya shigo falon nan sai , Ya Ridwan."
Ganin sun ki aminta da zantukanta ya sa ita kanta ta fara tabbatar wa kanta eh Lallai ze iya zama tsorone ya firgita ba .samun wuri tayi ta zauna da taimakon Ridwan, Wayarta suka lalubo ma ta tare da mika mata , sannu suka jero mata lokaci daya .
Ridwan da sam be mance bacin ransa da yake ciki ba cikin hanzarin sa ya mike tare da kama hanyar da zata sadashi da dakinsa kamar daga sama yaji muryan Mamy tana fadin,
" banganeba me kake nufi ba? Ko kuma wani wurin ne akace maka basu da wuta shine zaka yanke mana wutar gidan mu , haba Ridwan kai wani irin Yaro ne da sam baka kula fushin iyayen ka , meyasa baka son farantamin rai akan komi na rayuwa , harda wutar nepa? ".
Cak ya tsaya beyi gaba ba beyi baya ba , sossai gabansa ke bugawa gab gab da karfi , cikin rauninsa ya dan juyo tare da dawowa falon taku befi uku ba ya karaso gab da ita hade da kama hannayenta , Mamy cikin zallan mamaki take kallon yanda ya rike mata hannu dan zata iya rantsewa rabonta da ta ga hakan tun yana karaminsa, cikin sanyin murya wanda da ita kadai yake wa magana a hakan , cikin tausasa Lafazi yace,
" Mamy kiyi hakuri bari a kunna sola kawai , ba zan iya kunna Wutar nepa ba sai har na tabbatar da na gyara matsalar wasu yankin ". ya dire ayar zancen sa cikin sanyin murya, sam ba ya son jin wasu kalami daga bakinta , hakan ya sa ya mike kaman ana tsira masa allura fit ,
Yana kokarin barin falon ne hasken sola ya mamaye Gidan gabakidaya , nan take ko ina ya dau setti fanka da esi da Tv duk suka kawo , Tv yacigaba da aiki kamar yanda yake kafun yanke Wutar , isowar Mansur ne ya tabbatar masa da shi ne ya kunna solar dan sai yanzu ya karaso hadadden falo na Alfrma mai cike da kayan jin dadi na rayuwa , Mansur yana mai bin Ridwan da kallon mamaki , kana ya maida kallon sa akan Mamy dake zaune cikin dan bacin rai alamu dai anyi mata laifi.
"Biyoni". Shine kalmar daya furta ba tare da ya kai dubansa akan Mansur ba.
Shi kuwa Mansur Girgiza kai ya yi tare da karasowa gaban Mamy , durkushewa yayi ya gaisheta cike da ladabi.
fuskarta babu yabo ba fallasa ta amsa masa kana ta tura dan yatsar ta daya abaki alamun tarin mamaki game da dauke wutan da Ridwan yake musu agida ko wani time , bayan tasan ko da wasa a Yan nepa basa yanke musu Wuta.
Mansur kuwa gaisawa da kannen Ridwan yayi , inda suka amsa masa cike da da Fara'ar su .
Hankalinsa yana kan dakin Ridwan hakan yasa beyi wata_wata ba , kai tsaye yayi hanyar dakin sa cikin sassarfa da zakuwa , a hankali yake murda handle kofar , murya a sanyaye ya doka sallama jin babu amsa ya tabbatar masa kila yana cikin banɗaki ne , ga zallan mamakinsa , yana shiga , hango sa yayi cen bakin karshen Gado yana rusa kuka kamar karamin yaro harda sheshekarsa , nan da nan ya hanzarta karasawa dakin, cikin barin jiki hade zallan damuwa tattare dashi.
" Ridwan me ya saka kuka? Shin Ridwan kanada damuwar da ban cancanci in sani bane ?, ko kuma bani da matsayin da zan san Personnel dinka bane? ." Yakai ayar zancen yana mai kokarin dago kansa daga durkushewar da yayi.
Cike da nutsuwa Ridwan yakai duban sa a garesa kana ya dan langwabar da kai , cikin zakin muryan sa mai sanyi da dadin sauraro yace,
" Babu tashin hankalin dake daga min hankali irin in ga kauyuka basuda wutar nepa , ina gudun bakin mutane akaina , ina tsoron tsinuwar Allah shin ya ka ke tunanin in iyayenka ne a kauyen ko yan uwanka , shin baka gane Alkibla ta ne? , Mamy sam bata gane inda na dosa , kuma bana fatan ta gane ko da anan gaba ne domin....". Saurin katse shi Mansur yayi cikin karkada kai , ya maida masa da amsa tareda fadin.
" A'a Ridwan banason kace komi dan Allah kayi shiru basai karasa ba ".ya kai ayar zancen yana mai kamo hannun sa a cikin nasa . suna face din juna , kallon kallo sukewa juna inda kowannen su da abinda. yake sakawa yana kwancewa a cikin zuciyarsa.
Kashe Gari
Garin Gabasawa Daguzau loct ( Kano state)
Tunda sanyi safiya Amatullah ta tashi da dan karfin ta sakamakon jin sauki sossai tattare da ita , ahankali cikin kuzari tafara kokarin dan gyara wajen da suka kwana, sai a sannan nakai dubana inda na hango katuwar tsohuwar bargo shinfide a kasa , a gefenta kuwa yan roba ce mai dan murfi guda sai kofofina da cokali , kana a gaban ta tsohuwar buta ce wacce duk cikin sa yayi gansa kuka .
Muryan ta ne yadawo da dubana akan ta , jin tana fadin " Papy dan tashi ka dan zauna in gyara maka shinfida nasan tun jiya rabon da muci wani abu , nonon ma da muke ajiyewa shima bamu samu ba a jiya ". Ta idasa zancen cikin halin damuwa.
Dattijon da yayi zurfi a tunani , firgit kalamanta suka dawo da shi hayyacinsa , cikin muryan sa da basa fita sosai yace , " Amatullah karki damu ai akwai sauran Dabino a tattare damu , ki tuna ayar da Allah yake fadi duk tsanani yana tare da sauki , shakka babu in dai muna raye wataran sauki na nan tafe ". Yakai ayar zance yana mai kokarin tashi .
Itakuwa gyada masa kai tayi ba tare da ta sake furta komi ba , cike da nutsuwa ta dan gyara wajen , ganyayyakin dake zubo musu saida ta tattara su waje daya , sai a lokacin na kula cikin ciyayi suke kwana ga katuwar bishiyar mangwaro da yayi musu rumfa.
Zabga uban tagumi ta yi bayan kammala gyaran wajen , a hankali ta ke jin hawaye masu zafi suna bin kuncinta ganin har rana tayi haske basu karya ba , agogon roban dake hannun ta , ta kalla ganin karfe goma ya sa ta yin mika hade da tashi , kana a sanyaye ta dauko dabino taci me dan yawa wanda be zarce goma ba hade da bi da ruwan yar, cikin dan kuzarin ta, take kokarin fita dan nemo abunda zasu karya da shi .
" Papy zanje ko Allah ze sa na samu na safiyar nan ." tayi magana hade zura kodaddiyar takalmin ta a kafarta .
Da Allah yatsare ya bita dan shi kansa yasan yana jin yunwa.
ABUJA CITY
Bangaren Ridwan da Mansur sammako sukayi tun karfe bakwai na safiya domin Zuwa kauyen *Daguzau* sun kusa isowa Garin ne Wayar Ridwan ya fara ring , a hankali yakai duban sa akan Screen din Wayar sa ,ganin mai Gadin gidansa ke kiran sa, yasan magana ce mai muhimmanci, a hanzarce ya kara Wayar a kunnensa bayan ya daga , yana kokarin yin magana yaga motarsa tafara juyi dashi tana kokarin kade Wata Yarinya dake tafiya ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba .banda innalillah babu abinda suke maimaita sakamakon ganin har motar su ta.............
*Makauniyar Shari'a* yanzu a aka fara kudai ku biyoni domin ganin yanda abubuwan zasu kasance
***
Taku har kullum ( kyauta daga Allah)