Free page 1
๐ฆ๐พ *BADRIYA* ๐พ๐ฆ
A lady with concealed gender (MX)
~Storie and written by~
*~Unknown Author๐ ๐ป๐~*
*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya๐๐คฒ๐ป*
*~PAID BOOK 300~*
~Little note!!!~
*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za'a kiyaye nagode๐๐ป*
*ุจุณู ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู *
Kamar yadda mukai da kai tin a farko Alhaj buba kudin daka fada bai kai na dau ya guda na baka ba,saboda abu na farko banma sanka ba bansan mazaunin kaba in akai duba da ribar da kace shima bai kai dalilin da zaisa na dau yarinya na baka ba dan mutun ake magana ba kaya ba dan haka ka dai kara wani abu sai na duba nagani.
Kayi hakuri malan sule amma ni iya abunda zan'iya badawa kenan miliyan hudu da dubu dari tara kai kanka kasan tafiyata mai nisace sannan in na tashi komawa bani kadai zan koma ba dan dole na cire kudin cinta shanta da kudin motar ta har allah ya kaimu inda zan mika ta
kasan ma dan anriga da ansan yarinyar da aka turoni dauka ne da wallhi yata ta kaina zan bada kodan na amshe wadannan makudan kudaden da kuma sauran kudade masu zuwa dan iya masu aikin gidan ma kadai a wata na farko da fara aekinsu indai kayi yadda ya dace to tabbas duwani makusancin ka wahala ta dauko karewa masa,bare kai yadda aka zabo sunan yarka tin acan kasar ai kasan abunda yafi aikatau zatai,
dan haka du yadda kaga ya dace kayi nidai daga haka bazan kara komai ba dan ribar gaba taka ce bata kowa.
ya kare maganar cike da gajiya ganin kusan awa na hudu kenan suna abu daya shifa har mamakin malan sule yake dan tin kan suzo nan saida sukai bincike akansa alamu na nuna baya daya daga cikin mutane masu san zuciya ko son abun duniya shiyasa sukai zatan zasu sha wahala wajan fahimtar dashi da kudi hakan yasa suka kaiyade yawan kudin amma yadda malan sule ke nuna zalama akan kudin kamar ba malan sulen da aka basu labari ba.
Dan muskutawa wanda aka kira da malan sule yay yana sosa gemunsa hadi da yin mici mici da ido yana kara lissafa ribarsa a abunda yake shirin aikatawa mai kama da san zuciya. Saida ya gama yan tinane tinanensa kan ya dago yakara kure alhaji buba da ido kamar maisan sanin asalin gaskiyar batun ta idonsa.
kau da kai malan sule yay sannan ya dora da fadin nagane toh amma indai hakane dole ni ina da yan wasu sharidai wanda karbar kudinku bazai hanani gindaya muku suba in kun amince zance ya kare in kuma baku amince ba saidai nace ku kara gaba
Shuru dakin ya dauka alhaji buba baiyi magana ba yana ta tinanin shawarar yanke wa
Yayin da malan sule shima azuciyar shi yake cewa tinda naji kace wadan da suka aiko ka sun riga da sun santa nasan cewa tafiya da ita ta zama dole toh dan haka bazaku tafi da ita haka kawai ba koba komai dai wai hausawa suka ce amfanin zunubi rom__gyaran muryar alhaji buba shiya kaste masa zancen zucinsa.
Nisawa alhaji buba yay kan yace
ina sauraran ka malan sule minene sharudan naka bayan naji zanje nai magana da wanda ya turoni sai muji ko zamu iya cika su.
Hakan yayi sharadi na farko bamai wahala Bane aguna bansan agun kuba sharadin ko shine kan tafiya da yarinyar nan dole sai da igiyar wani akanta dan bazan ci amanar siyar da ita ba kuma naci amanar mutuncin taba sannan ta haka ne kawai mahaifiyar ta zata kuma yarda da tafiyar ta cikin sauki
abu na biyu shine komai na auran za'ayi shine ba tare da wani boyeboye ba musanman dai daurin auran inaso ayishi agaban mu bawai sai anje can ba kaga ba wanda zai yada jitajitan da ba ita bace sanna koda zuwa gaba wani abu mara kyau ya biyo baya kamar ta dawo ita daya da yara ba mai sheganta min jika ko kuma batawa yata suna wanda bana fatan hakan ma,
sharadi na karshe shine ina san sanin inda zaka tafi da yar mu,gunda zata zauna, da kuma mazaunin ka kasan koba komai itadin jininace wataran inna samu dama zan iya kawo mata ziyara ko ni ko yan uwanta,
wadan nan sune sharudan๐
ni kuma nace wanan shine karshen page 1 lol๐๐
**_________*Tata huf huf ya to ya kukaji?! nace ya kukaji*
*Hi๐๐ปโโ๏ธall my peoples how was the first episode* ๐ *hope u guys like and also love it*
*what is ur expectations about it huh* ๐ *i need a good good comments it's just first page your read more for tomorrow goes besed on ur today's comments so ina jiran ruwan comment Ku dauka Mu hadu gobe domin jin yadda zata kayak*
_*shin alhaji haba zai yadda da sharudun malan sule*_
and don't forget this book isn't for free is 300naira only
*The unknown author๐ ๐*