Mutum Mugu Ne

16

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     16


Alhaji Kadi na fitowa da Waheeda daga d'akin tsafin shi ya jata a k'asa har falo sannan ya fara kiran Jameel. Jameel ya fito da gudu ganin Alhaji Kadi tsaye ga Waheeda kwance a k'asa kamar ba rai yasa shi tambayar "Oga Lafiya?"

"Dan ubanka ya akayi ka barta ta fito daga d'akin da take, yanzu tariga taga komai"

"Oga yanzu ya za'ayi kenan?"

Alhaji Kadi ya daka masa tsawa " kayi maza ka kawar da ita ka jefar da gawarta a jeji" 

Duk da ba yau Jameel ya fara kisa ba amma gaskiya jikinsa yayi sanyi saboda duk cikin 'yan matan da yayi harka dasu Waheeda ta dabance baya gajiya da ita, ba wai yana sonta bane amma gaskiya a yanzu tausayinta ne ya shige shi yana ganin ba zai iya kasheta da kanshi ba.

Alhaji Kadi ya koma d'akin tsafin sa dan tabbatar da shigar Waheeda d'akin bai sa gunkinsa yin fishi ba. Tunda ya gina gidan babu wanda yasan da d'akin nan, Layla ce da ta ke k'arama tsautsayi yasa ta shigo, saboda haka nema yasa ya jirkitar da tunaninta ta manta da duk abinda ta gani har yau kums baza ta taɓa iya tuna abinda ta gani a d'akin ba.

Yau gashi Waheeda ta sake gani, dole ya k'ara matakan tsaro na d'akin saboda idan mutum na uku ya sake shigan d'akin ba shiba to fah komai zai iya lalacewa, yana daga cikin kashedin da aka masa kafin ya fara wannan tsafi.

Wayar Waheedar ya d'auko wanda har lokacin kiran bai katseba. "Hello...Hello Waheeda kiyi magana mana" shine abinda ake fad'a cikin muryar kuka sannan ya k'atse kiran ya fito.

Tsaye ya ga Jameel ya sa Waheeda a gaba yana kallonta da alamar tausayi a tattare da shi.

"Mi kake jira da baka aiwatar da abinda nace ba" Alhaji Kadi ya daka masa tsawa.

Jikinsa na rawa ya tallafo da Waheeda da idonta ya fara bud'ewa ta farfad'o daga suman da tayi.

Haka Alhaji Kadi yana tsaye a wajen yana gani Jameel yasa hannu ya shak'e wuyar Waheeda har sai da ta dena numfashi.

" Now je ka nemi wani waje ka jefar da gawarta ko ka bisine, just dispose her body immediately without leaving a trace" Alhaji Kadi ya fad'i cikin tsawa.

Jiki na rawa Jameel ya d'auki gawar Waheeda a kafad'arsa ya d'au wayarta da Alhaji Kadi ya jefar ya fita da ita idonshi fal da hawaye. Ya sani tun da shi ba mutumin kirki bane amma had'uwarsa da Alhaji Kadi yasa ya zama marar tausayi marar Imani, gashi ko me Alhaji Kadi ya sashi baya iya yi masa musu haka zai aiwatar......




.....BAUCHI


Tunda Nazira ta ji abinda waheeda ke faɗa hankalinta ya tashi musamman da ta dena jin maganarta, sanda Alhaji Kadi ya katse kiran suman tsaye ta yi, jikinta ya gama bata cewa wani mummunan abu ya faru da waheeda. Da k'yar ta k'arasa d'akin da aka kwantar da Abba. Cikin sheshsheqar kuka tacewa Baba Malam da bai jima da isowa daga Azare ba " Baba zan je kaduna yanzu"

Cikin tashin hankali Baba ya kalleta "Nazira lafiyarki kuwa, cikin daren nan kice za ki yi tafiya"

Batason tada hankalin Abba da bai jima da farfad'owa ba gashi likita yace kar su d'aga masa hankali.

"Waheeda" Abba yace karo na farko da yayi magana tunda suka kawoshi asibiti.

"Ina Waheeda tah?" Ya tambaya

Cike da bak'in cikin halin da suke ciki tace "Abba tana zuwa yanzu, nayi waya da ita tace gobe da sassafe zata zo"

Baba ya lura da akwai abinda take 'boyewa dan haka, bayan Abba ya koma da bacci ya kirata suka fita waje. Tambayarta abinda ke faruwa yayi dan shi bai san komai ba ta kirashine tace masa Abbansu ba lafiya suna asibiti, kawai ya biyo mota sai Bauchi.

Nazira a tak'aice ta sanar dashi abinda ke faruwa ta k'ara da bashi labarin abinda ta ji Waheeda na fad'i.

Tabbas Malam ba dan k'arfin hali ba da kuma Innalillahi da yake ta maimaitawa da shima hawan jinin ce zata kamashi a lokacin.

Yafi minti goma yana addu'o'i dan ya rasa ma mi zai ce. Wannan abu da mi yai kama, wai mutum ne da wannan hali na mugunta da rashin imani. Badan yasan illar tsinewa 'ya'ya ba da ya tsinewa Laure, wannan ma ai halin tsinannun tayi.

"Baba ka bari kawai na wuce Kaduna yanzu dan na san halin da 'yar uwata take ciki"

Baba yai ajiyar zuciya idonsa fal da hawayen bak'in ciki yace " Nazira kiyi hak'uri dare ne yanzu gobe idan Allah ya kaimu da sassafe sai ki tafi ke da Baffanku Ahmad"

Badan taso ba haka ta hak'ura.

Ganin zuciyarta yak'i nutsuwa yasa ta binciko numbar wani tsohon saurayinta police d'an Kaduna da suka ta'ba harka da shi ta kirashi ta sanar dashi halin da ake ciki. Ya tabbatar mata zai yi bincike akai.

Yadda taga rana haka taga dare barci kam yak'i zuwa mata. Ta kira numbar Waheeda yafi sau hamsin amma a kashe take.

Bayan ta idar da sallan asuba tana zaune kan sallaya tana jiran Baba su dawo daga masallaci ta wuce gida ta d'au kud'i ta tafi park. Aka fara kiran wayan Abba, ganin number ne babu suna yasa bata d'auka ba ta sharekiran ta san ba zai wuce masu mai ya jiki bane.

Shigowar Malam ya kat'se mata tunani tace mishi zata wuce gida ta shirya yanzu.

Kafin Baba yace wani abu aka sake kiran wayar Abba wannan karan Baffa Ahmad ya d'auka.

"Ba shi bane amma ni k'aninsane..... Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oon.....toh, Shikenan muna zuwa"

Zuru zuru Baba da Nazira sukayi suna sauraron wayar da yakeyi. Yana k'atse wayar yai shiru.

Baba ya tambayeshi lafiya yace masa lafiya kawai ance wani abokin Yaya ne yai hatsari.

Nazira dai jikinta yai sanyi.

Baffa Ahmad yace ta tallafawa Abbansu ya shiga bayi yai alwala tunda ya tashi zasu je suga likita shi da Baba.

Sai da suka fita daga d'akin sannan ya sanar da Baba 'yan sanda ne suka kira daga Kaduna an tsinci gawar Waheeda jiya da dare. Kuma an buk'aci suje su tabbatar da ita d'ince sannan su k'ar'bo gawar.

Baba kam wannan karan kasa hak'uri yai saida ya fashe da kuka. Da k'yar Baffa Ahmad ya rarrasheshi ya samu ya dena kukan. 

Baffa Ahmad da wasu abokanan Abba suka wuce Kaduna. Baba ya tsaya da Nazira a asibiti, zuwa k'arfe goma na safe Arif, Anty Amina da mijinta suka zo daga Kano.

Duk yadda Nazira tayi dan ta bi su Baffanta Ahmad amma Baba ya k'i amincewa haka ta hak'ura.

Abba ma sai tambayar Waheeda yakeyi amma ba wani labari.

Baba yaja mijin Anty Amina gefe ya masa bayanin abinda ke faruwa.

Nazira taje gida ta chanja kaya ita da Arif aka kirata, tsohon saurayinta data sa ya mata bincikine ya kira yake shaida mata an tsinci gawar Waheeda a gefen hanya gawar tana mortuary, sai dai an sanar dashi iyayenta na zuwa dan kar'ban gawar....ai bai gama bayaniba ta yanke jiki ta fad'i.........




........LAGOS.........


Tana zaune a d'aki tana karanta littafi mai suna Jane Eyre ya shigo d'akin.

Zama yayi kusa da ita ya ce "my angel inaso muyi magana mai mahinmanci dake"

Ta d'ago ta kalleshi da mamaki " Nickolas miya faru?" Ta tambaya

Ya d'auke littafin daga kan lap d'inta yace " Irene ki gayamin gaskiya, mi kika sani gameda case d'in dasu Mommy B suke yi?"

Tashi tayi tsaye da alamun damuwa a tattare da ita tace "please Nick kabar wannan magana, bata shafeka ba. Kada kayi shishshigi cikin case d'in nan you'll get hurt"

Nick ya tashi shima ya kamo hannunta d'aya ya rik'e " ina da tabbacin kin san wani abu gameda mutuwar mijin mommy B, ki kwantar da hankalinki ki sanar dani komai, I swear to you Irene that I'll protect you no matter what".

"I can't Nick, I just can't tell you. Saboda hakan zai jawo rasa rayuka masu mahinmanci a gareni" ta k'arasa maganar tana goge hawaye.

Nick ya rungumeta jikinshi ya rad'a mata a kunne " Irene na san kina tsoron abinda zai biyo baya amma ki sani idan har kin san wani abu gameda case d'in nan kika yi shiru and the innocent suffers. Za ki ƙarisa rayuwarki cikin dana sani" 

Da haka ya fita daga d'akin ya barta tsaye tana tunanin ya zata yi.


                            ***

Naziha na chatting a wayarta taji ana k'wank'wasa k'ofar d'akinta, da sauri ta tashi ta je ta bud'e.

Uncle Sajid ne tsaye bakin k'ofar hannunsa rik'e da shirt d'insa. "Ziha taimakamin na kasa saka rigar da kaina"

Ta sani cewa ba da wani manufa ya fad'i hakan ba, tsakaninsa da Allah yai mata maganar, saboda wajen da aka harbeshi. Amma sai taji wani iri.

Shiru tayi tana kallon kyakyawar fiskanshi zuciyarta na ayyano mata wasu abubuwa.

"Hello..... Ziha" Sajid ya fad'i bayan ya snapping fingers ɗinsa a dai dai fiskarta

Tayi firgigit tace "oh, ok, Uncle ba matsala"

Fitowa sukayi falon ya mik'a mata shirt d'in yace ta taimaka masa ya cire singlet din da yasa

A hankali ta fara d'agawa har ta kai sama, daya d'an d'aga hannunsa mai ciwo taji ya d'anyi "esh" alamar yaji zafi. Nan ta fara masa sannu. Haka dai ta cire mishi singlet d'in.

Ta fara 'balle button na shirt d'in sannan ta fara k'ok'arin saka masa, k'anshin turaren jikinsa dana shirt d'in ya fara drawing nata gareshi. Allah kad'ai yasan irin k'arfin halin datayi ta gama sa masa ba tareda ta rungumeshi ba, dan k'anshin da ya keyi kamar ta shige jikinshi take ji.

Tana saka masa button d'in rigar hannunta na shaking, yadda gashi ya kwanta a k'irjinsa kamar ta sa hannu ta shafa take ji.

Naziha, snap out of this dream, he belongs to someone else. Daga anyi kwana biyu ya d'an warware shikenan zai koma rayuwarsa na da, baki da matsayinma da zaki tsaya kusa da shi balle kiyi tunanin ta'ba shi. Dr Sajid yafi k'arfin ki Naziha wani 'bangare na zuciyarta ya fad'i


"Thank you" ya fad'i bayan ta gama saka masa rigar

Ba k'aramin kyau kayan suka masa ba, da shike bak'in kayane sai ya k'ara fito da farinshi da ainihin kyaunshi.

Tana gani ya koma d'akinsa ta bi bayansa da kallo tana murmushi.

Yana shiga d'aki Madam B ya kira da d'aya wayarsa

" Kina tunanin hakan da kukamin zai sa na ji tsoro ne, toh ki sani na riga na filing report a kanki idan wani abu ya sameni ko iyalen gidan danake zaune dasu ko iyalen Barrister Idris" yai wata k'aramar dariya yace "kin san sauran..... another thing ba abinda zaku samu a wayata daya wuce hotona dana iyalina"

yana gama fad'in haka ya kat'se wayar.

Madam B tayi cilli da wayar hannunta tareda cire gashin wig dake kanta tana sosa asalin gashinta wanda ya tsaya iya k'eyarta "it's not yet over Sajid, sai dai na mutu amma asirina ba zai ta'ba tonuwa ina raye ba".

Wata wayar ta fiddo a jakanta ta fara kiran Joseph.....

Da rana Naziha ta kawo masa sallaya da Qur'ani ganin yana kwance yana waya yasa ta ajiye ta fita daga d'akin...

Bayan ya idar da sallah ya fito falo bai ganta ba can yaji motsi a kitchen dan haka ya tabbatar tana wajen. Zama yayi ya kunna TV ya kai tashar aljazeera news suna maimaita wani shirinsu mai suna witness

Kusan minti biyar sai gashi ta fito da yake taji k'aran TV batayi mamakin ganinsa a falo ba.

"Uncle mi zakaci?" ta tambayeshi bayan ta k'araso wajenshi

"No bana jin yunwa" ya amsa mata

"Ok" tace sannan ta koma kitchen d'in abincin data girka masa da safe shi ta d'umama taci tun d'azun.

Ta had'a masa cornflakes a kofi da yaji madara sosai ta yanka ayaba aciki ta kawo masa.

"Ziha da wahala haka" ya k'ar'ba yasa sokali ya fara sha.

Sai daya kusan shanyewa yace "yawwa baki gayamin dalilin da yasa kika dawo gidan nan da zama ba"

Ajiyar zuciya tayi sannan ta fara bashi labari.....

Bayan jikina ya warware, yayana AbdulBar ya koma makaranta. Alaja Kudirat itama ta koma Jos taso ta tafi dani amma Yaya AbdulBasid yace yanaso na zauna dashi tunda nafi sabawa da Kano.

Farko farkon zamana dasu komai na tafiya dai dai tsakaninmu daga baya Anty Zainab ta chanja mini gaba d'aya.

Ni nake komai na gidan tun daga gyaran gida, girki harta wankinta dana Yayana duk ni nakeyi. Ban damuba saboda koba komai na lokaci kad'an ne kafin na tafi makaranta.

Lokacin da ta chanja salo ne abin ya fara damuna, sai ina wanka ta shigo band'akin kai tsaye sai ta wayance da batasan ina ciki ba. Da ta min haka sau biyu saina koma idan na shiga band'aki sai na saka key. Bayan an kwana biyu ta k'ara 'bullo da wani sabon abu, idan ina aiki a kitchen ta shigo ba abinda takeyi saita rungumeni ta fara tatta'bamin jiki. Tun ina shiru ranar data k'ulani nace idan ta sake min haka zan had'ata da yayana.

Kwana biyu da haka Yaya AbdulBasid ya tafi Ilorin, ya rage dagani sai ita a gidan. Da dare ina cikin barci naji ana shafamin jiki nayi firgigit na tashi na kunna wutar d'akin, Anty Zainab ne akan gadona da wata rigar barci da bai kamata ace tasashi ba alokacin tunda Mijinta baya nan.

"Anty lafiya?" Na tambayeta cikin tsoro

"Haba Naziha na baki hint da ido da jiki duk baki gane ba, na d'auka kin waye ai tunda boarding school kika yi" tace dani

A firgice nace mata ban gane mi take nufi ba, ta fara k'ok'arin matsoni tana cewa " Naziha tunda na fara ganinki naji na kamu da sonki, ke macece mai k'ira irin wadda kowa ke so, wallahi kinga duk aikin da nake saki ina gwada kine amma wallahi kullum da sha'awarki nake kwana dashi nake tashi, ki taimaka min ko sau d'aya ne naji taste d'inki"

I was really dumbfounded alokacin, tunanina ya tsaya cak na kasa gaskata kalaman dana keji, nasan muna school ana yin tad'i akan 'yan lesbian amma ban ta'ba gaskata hakan ba, ni anawa tunanin abune mai wuya a samu mace wayayyiya tayi hakan but to my uttermost dismay sai gashi matan aurema basu tsira ba akwai masu irin wannan mummunan d'abi'a.

Kokawa muka yi sosai da Anty Zainab dake shirin min kota k'arfi da k'yar na k'wace kaina na gudu a d'akin, kitchen na shiga na saka key ta ciki anan na kwana ranan.

Washe gari ko kunya bata ji ba ta fara rarrashina wai na amince dana ga fah da gaske takeyi na tsaya na zazzageta na mata tatas nace idan ta sake min maganar zan kira Yaya na gaya mishi.

Ranar duk aikin dana keyi atsorace nakeyi har na tafi Islamiyya, danaje na fara ciwon ciki dan haka na nemi excuse na dawo gida.

Dana shiga falo na farajin ana ...ana... sai kuma tayi shiru

Sajid ya ce "ana me ?"

Kunyarsa takeji, taji bazata iya gaya masa ba.

"Look Ziha, abinda ya faru ya riga ya faru so dan haka ki gayamin koma minene, I won't judge you"

Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da labarin

Ina taji daga ciki ana moaning, har da ihu, inajin muryar Anty Zainab tana ihu "wayyo Allah, wayyo na shiga uku, wayyo...." Abinda ya fara zuwamin shine ko wanine ya shigo mata sata ya ke dukanta.

Sajid bai san sadda ya sake murmushi ba da jin tunanin da tayi alokacin. Gaba d'aya sai taji kunyarsa ya sake cikata.

" ci gaba"

Ta d'an had'a rai tace " Uncle ba dariya kake min ba"

"Sorry dear tunanin da kika yi ne ya bani dariya"

'Did he just call me 'dear'?' Ta tambayi kanta

Muryarsa ya kat'seta " inajinki Ziha mi ya faru kuma?"

Ta cigaba

Na yi hanyar d'akinta da gudu ina bud'e k'ofa ya bud'u, abinda na gani har yau ina tu'ajjibin abun, idan da labari aka bani wallahi ba zan ta'ba gaskatawa ba amma da idona na gani.

Shiru tayi batace komaiba, Sajid cikin sigan zolaya yace " kin kama 'barawo mai dukan Antynki ko?"

Da sauri ta d'ago ido tana kallonshi, she can't believe he says that, ta san he's just joking, amma kuma abin ya mata dad'i at least ya nuna cewa he's enjoying her company har yana zolayarta.

Ta biye mishi itama " yes Uncle na kama 'barawo amma macece ba namiji ba" ta cigaba They were both naked and enjoying themselves on the bed.

Tsorone ya kamani alokacin, ganin abinda ban ta'ba ganiba abinda ban ta'ba tunanin zan gani ba, sai gashi a gidan da nake na gani wai hakanma matar yayana.

Innalillahi na fad'i wanda yaja hankalinsu suka bar abinda sukeyi suna kallona dan basuma san na shigo ba. Anty Zainab maimakon ta tsorata saima taja tsaki tace min "miye zaki shigomin d'aki ba sallama" abin ya bani mamaki, ganin bata damu na kamata tana aikata masha'a ba yasa na fita daga d'akin na shiga nawa kawai na fara kuka. Ranar ko fitowa banyi daga d'aki ba har washe gari. Duk tunanin da nayi akan yadda zan 'bullowa al'amarin amma na kasa domin ba lalle Yaya AbdulBasid ya yarda ba idan na gaya mishi musamman yadda yakeji da ita. Shawara na yanke da zaran ya dawo kawai zan koma gidan k'anwar Papa wato Alaja Kudirat da zama dan bazan iya zama da ita ba kuma idan Yaya AbdulBar ya dawo zan gaya mishi dan shikan nasan zai yarda dani koda bani da evidence.

Da tunanin haka na tashi, dana fito da safe bata falo dan haka nayi sauri na shiga kitchen na had'a custard na d'auko sauran cake danayi wa Yaya AbdulBasid kafin ya tafi na dawo d'aki naci. Ban kuma fita ba sai dana ji alamar ta fita daga gidan na fito na yi ayyukana na girka abincin rana.

Har nayi la'asar bata dawo ba Dan haka na shirya na tafi Islamiyya na bar mata key d'in gidan a wajen da muke ajiyewa dan ban saniba kota fita da nata key d'in.

Ina dawowa daga Islamiyya na shiga gida, nan na farajin hayaniya, muryar yayana yasa nasan ya dawo. Abin mamaki daga d'akina nakejin maganan. Nayi sauri na k'arasa na shiga da sallama. Amma mi, Yaya AbdulBasid ya yo kaina yana zagina tareda kai min mari cikin tashin hankali nace " boda mi, kini mo sè?"

Wani marin ya sake min sannan yace "Naziha ki rasa halin da zaki d'auko a boarding school sai lesbianism, Funmi cin mutuncin da zaki yiwa Papa kenan ki hana shi kwanciyar k'abari"

Cike da mamaki nace mai ban gane ba,

Zuwa yayi ya k'ar'ba wayata a hannun Anty Zainab ya bud'e gallery ya nunamin wasu videos da bansan dasu a ciki ba, video ne na 'yan lesbian. Ganin Haka na Fara kuka Ina rantse rantsen cewa ban san dasu a wayata ba.

Cikin bacin rai yace " idan bakisan da zaman wannan ba wannan fah Dan ubanki a cikin akwatinki na samu" ya nuna min wasu dildo guda biyu akan gadona. Na zaro ido cikin tashin hankali ina kuka ina muzanta abinda yace min. Amma ba alamun ya ma yi shakkar zargin dayake min. Na fara gaya mishi ai matarshi ce 'yar lesbian ba ni ba, jin maganganun da nake yi ya nufoni ya fara dukana. Tun ina kuka har na dena saboda wahala. Da kanshi ya barni ya fita daga d'akin yanata zage zage. Anty Zainab ta k'araso wajena tana dariya tace " da kin amincemin da haka bata faru dake ba"

Da k'yar na tashi daga inda nake naja jiki na shiga bathroom dan gyara jikina . Ina fitowa naji muryar yayana yana waya daga yadda yake magana na gane da Alaja Kudirat yake magana yana gaya mata abinda ya faru, yana gama wayar ya kira Alaji AbdulWasi'u wanda yake shine a matsayin kakanmu yanzu shima ya fara masa bayani.

Na sake wani sabon kukan shikenan tawa ta k'are wato kowa a family yasan sharrin da aka mini.

K'arshen maganar da sukayi da Baba (Alaji AbdulWasi'u) shine gobe dashi da ni duk mu shiga mota mu tafo Ilorin. Yaya AbdulBasid yace masa ba zai samu zuwa gobe ba saboda dole sai ya sake d'aukan excuse a wajen aiki idan an kwana biyu zamu zo.

Ranar kam nayi kuka na godewa Allah dan ban yi barciba, k'arshe na tashi nayi sallah ina neman taimakon Allah.

Da safe babu wanda ya lekoni nima ban fito daga d'akin ba, sai da naji fitar yayana daga gidan na fito na lek'a d'akinsu naji alamar Anty Zainab na wanka na fito na bud'e k'ofa na fita, dama tun asuba na had'a kan 'yan takadduna na makaranta da wasu abubuwana ma su mahinmanci na sa a jaka. 

Shagonsu wani d'an anguwarmu Haroon da muka yi secondary tare kafin a maidani boarding na tafi na samu shi kad'aine a shagon babansa baya nan, na rok'eshi ya rantamin kud'i dubu sha biyar bayan kwana biyu zan turo masa. Saboda lokacin da muke school friend d'ina ne sosai yasa shi amincewa ba tareda wani tambaya ba. Yace min bashida cash amma zai kira k'aninsa yaje gida ya d'auka ATM ya ciromin.

Ina zaune a shagon har k'aninsa ya kawomin kud'in. Ban zame ko ina ba sai park.

Banida wajen da zanje yanzu da yafi wajen Daddy dan haka na nufi Lagos.

Da nazo na yiwa Daddy bayanin komai abin mamaki ya yarda da maganata ya kuma d'au alkawarin kula dani. shi ya bani kud'i na turawa Haroon ta account ɗinsa.

A Lagos na fara sabon rayuwa, farko farkon gudowana inajin haushin kaina miyasa na gudu yanzu kenan zasu yarda da sharrin da Anty Zainab ta min, daga baya na wartsake.

Alaji AbdulWasi'u da Yaya AbdulBar kad'ai suka kira Daddy suka tambayeshi ko nazo wajenshi yace musu a'a amma Yaya AbdulBasid bai nemeni ba.

Idonta cike da hawaye tace "Uncle kaji dalilin dawowa nan da zama"

Ya tausaya mata amma kuma ya ga wautarta maimakon ta tsaya ta kare kanta sai ta gudu.

"Kina nufin har yanzu sauran 'yan uwanki basusan kina nan ba?" Ya tambayeta

"Gaskiya daddy bai gaya wa kowa ba"

Yinin ranar haka suka wuni tare a gidan bayan sunyi sallar la'asar Naziha ta fito da board ɗin chess suka fara yin game d'in.....

Da dare kaman yadda suka saba dawowa haka Daddy da Tim suka dawo, ta riga ta yiwa uncle Sajid tuwon semovita da dry okro soup kuma ya ci sosai.

Uncle Sajid da Daddy sun jima a falo suna tattaunawa tsakaninsu kafin daga bisani kowa ya koma makwancinsa, Timothy haka yasa Naziha a gama wai ta bashi labarin zaman da suka yi kafin su dawo, ta gulmata masa wasu, wasu kuma ta barwa ranta.

............washe gari jikin Sajid ya sake warwarewa dan haka bayan sun yi breakfast Ishola ya zo ya tafi dashi. Naziha ta tsorata da tafiyar ko dai shikenan ba zai dawo ba, sai data ga akwai kayanshi a guest room sannan hankalinta ya kwanta.

Yau su Mama da Ronke zasu dawo.

Tunda taje aiki yau tunanin Sajid ne ya cikata, kominsa burgeta yakeyi musamman idan ta tuna moments ɗinsu na jiya.

Wani order ta kai room 44. Wani mutumine bak'i d'an lukuti ya bud'e k'ofan d'akin yace ta shiga ta ajiye masa, ba tareda ta kawo komai ba tunda aikintane data saba ta shiga d'akin. Tana shiga ya rufe d'akin da key, dama ya ta'ba zuwa hotel d'in ya ganta kuma tun lokacin yake cike da sha'awarta.

Ta juyo zata fita tayi karo dashi harda ce masa sorry zata wuce ya rik'e hannunta " baby I'll give you anything you want, just let me taste you this evening"

Tayi saurin wafce hannunta tace " Sir I'm not what you think" tayi niyyar ra'ba gefenshi ta wuce ya yafitota ta yace "baby 50k ...no 100k" k'ok'arin tureshi takeyi amma ta kasa ganin zatayi gardama ya fara nuna mata k'arfi tuni ya turata kan gado ta fad'i tana ihu tana rok'onshi.........



......ABUJA........



Tunda tayi waya da Sajid hankalinta ya d'an kwanta amma still tana kewarshi.

Sady ta tambayeta ko lafiya Sajid d'in yake nan ta kwashe abinda Sajid ya fad'a mata ta sanar da ita.

Sady cikin dariya tace " niko babe sai nake ga kamar za a k'wace miki Sajid a Lagos"

"Kan ubancan, wallahi har kinsa dole zanje Lagos, Azra na gama exams zamu tafi tare, Aamir da Nurain zan kaisu gidan Daddy" Zaytunah ta fad'i tana huci

Sady ta kuma cewa "kai Zaytunah kishi haka, yanzu ace ki je Lagos sai ki ga Sajid da wata ya za ki yi?"

"Mutuwa zan yi Sady, ni Dan Allah ki denamin irin wannan maganan. Sajid nawa ne ni kad'ai, abinda bai yi ba lokacin da yake matashi ba zai yi ba yanzu da ya doshi 50yrs. Nida Sajid mutu ka raba ne. Kima daina kawomin zancen da zai tada min hankali ina zaune lafiya"........