ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 07

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


        *🅿️07*

    

Bikin Aisha da Fahad ya rage Saura Wata Hud'u aka sanyama Fa'iza Rana wata bakwai Wanda lokacin yayi Daidai da tagama Candy Dinta.

wannan karon Ban hana kaina kuka ba, Domin inaji ina gani agidanmu sai karewa ake ana barina. 

Dama mu uku ne muke kwana ad'aki daya ni da Fa'iza da Rabi'a. Su Maryam d'akin Mama Suke kwana don daga ita har ya'yanta basu Cika shiga Shirgin yan gidanmu ba yadda kasan Suma ba ya'yan gidan ba ne.

Ba laifi Fahad yana da Rufin ASirin Domin ma'akaicine A Hukumar Nepa. shiyasa akayi komai Cikin Wadata a ka yi sa. Lokacin da bikin ya kariso Duk sai Aisha ta zabge ta rame kamar ba ita ba,haka itama Asma'u Suna jimanin Rabuwa da juna Saboda sanin yadda Suka Shaku. ammh babu yarda zasuyi Tunda haka Allah ya kaddara.

Tun ana Saura Sati d'aya biki Na nesa dana kusa suka Fara Cika gida. Mamana Tazo Ana gobe biki tazo da Tsohon cikinta Haihuwa ko yau ko Gobe, Murna wajen Asma'u ba'a mgana ganin yadda Mamana tayi kyau Sosai dagani ta samu kwanciyar Hankali ita kuma ganin yarta ta Sai Tsausayin ta yakamata sosai. na ganin yadda zatasha kewa in Aisha Tatafi ta barta.

Ranar biki komai Tare Suka sanya Aisha da Asma'u Domin hatta ita Sai Da Fahad yama kaya kamar wacce zai aura saboda sanyayama Aisha Zuciya, Tun da Suka ga yammah tayi suka Fara kuka kar Aisha taji lbri koda motocin Daukan amarya Suka zo Aisha bata yarda hannunta ya Rabu Dana Asma'u ba har aka kaita Dan madaidaicin gidanta dake GRA.

Kuka da Tashin hankali bai Faru ba sai da Asma'u zata bi yan kawo amarya Aisha ta kamkameta tana kuka,duk yadda Asma'u taso Daurewa Abun ya gagara itama kukan Ta Fashe dashi. Ganin Sunki rabuwa da juna yasa aka bar Asma'un anan Sai da angwaye suka zo suka Siya baki kana Suka Wuce da Asma'u Suka Sauketa agida.

shi kanshi Sai da Asma'un ta ma Aishan Dubaran Zata Shiga Bayi ne ta Fito sai dai ta waiga taga batanan, Ranar Fahad yaga kuka,kuma yakara Jadadda kaunar dake Tsakanin kawayen Biyu.

Auren Aisha shi yakarama Asma'u zaman kad'aici da kuma zaman gidansu Tunda yanzu bata zuwa mkranta. kullun Cikin yad'a mata Habaici Umma keyi ita da Hajiya Iya ba wajen wanda take samun mgana mai Dadi sai Wajen Anty Amarya, sai Baba lami da hassatu sabbin masu aikinsu. dayake Suna da kirki Sosai,mama ko dama ban da gaisuwa babu Abunda ke Shiga Tsakaninsu daga ita har ya'yanta.

Tun bayan Abunda ya faru ni Asma'u Nayi alqawarin bazan kara kula kowani Namiji ba,ammh kuma ya zan yi domin Zaman gidanmu na neman ya Fita kaina. Kwatsam sai ga Ishaq ya Shigo cikin Rayuwata wanda kai Tsaye wajen Abbana yafara Zuwa Neman izini Shi Abban da kanshi ya kirani yana Fad'amin. ban yi gardama na karbi ishaq tare da addu'ar Allah ya sanya Shine mijina,Shima yana da Abun hannunshi Domin ma'aikacin banki ne,haka nake Duka jinin samarina masu dashi ne. Aisha dataji lbri kamar ta Zuba Ruwa kasa tasha saboda Murna har gida na Kai musu Ishaq suka gaisa da Fahad.


Tun ban saki jiki da ishaq ba Har nazo na Saki ganin mun kwarari Wata biyar Tare. har akayi bikin Fa'iza wanda ko ankonin bikin Shi ya dinkamin naci biki dashi.

Ana gama bikin Fa'iza nasa Araina Insha Allahu nice alayi wannan karon, ashe Tsugunne bata kare ba, mganata da Ishaq tayi karfi wanda waliyansa Sun Had'u da Waliyaina,Wannan karon har an kai ga saka Ranar Aure na da ishaq wata goma masu Zuwa Baikon da ya sakani cikin Farinciiki har sai nayi Azumi bakwai Na nuna godiyata ga Allah.

Masoyana aduk inda Suke sun Nuna jin dadinsu tare da Fatan Alheri kar Aisha taji lbri hakama Ammi mamana ko sai da tayi Sadaka, duk da lokacin tana jego ne Domin ta Haihu Abunda ta Haifa baizo da Rai ba.

Bikina da Ishaq ya Rage Saura Wata biyar Aka sanya Ranar Auren Rabi'a Wanda Abbana yace zai had'a Rana daya ne, ita a jigawa zatayi Auren ban Wani damu ba nidai ina ta Shiryen Shiryen biki na tare da murnan zan Wuce gorin Hajiya iya da Umma. Bikin na Saura wajen kwana 30 Na samu lbrin Haihuwar Mamata wanda ko nace sai naje,dakyar Abba ya barni Ranar ko Bauchi tayi baki. domin ishaq da kanshi ya kaini har gidan kakannina kuma ya Shiga Suka gaisa,daganan muka Wuce gidan Mamata, shima har Ciki ya Shiga ya gaida Mamata ya mata barka ta samu mace,ya gaida Hajiya abokiyar zamanta Nan ya barni bayan mun Rabu akan Zai zo ya Daukeni

Murna ta cikani ganin nayi k'anwa ina nan har akayi Suna Kanwata taci Sunan FATIMA Suna cemata Fati.

gaskiyan gidan da mamata tayi Aure yayi ne,gidane mai Cike da tarbiya da Son Mutane haka Abokiyar Zamanta hajiya da ya'yanta ke Dawainiya dani kamar jininsu basu Nuna bambamci Tsakaninmu. hakama Shikanshi Proff.din Tun ban saki jiki ba har na saki jiki,su Anty Nafi da Anty Safina kowa na son Asma'u taje gidanshi ne,vTuni Farinciki ya sa na manta da zaman gidanmu na Share kafata,sai da Abba ya kira awaya yace Nadawo, sannan na Fara Shirin Dawowa.

Wani Abunda na lura dashi Tun Zuwa na Bauchi da sati d'aya Ishaq ya rage kirana ta waya wani lokacin ma sai na kirasa sai yace aiki ne yamai yawa ban kawo komai ba.

sai Da Abba yace na dawo na kirasa na Fad'amai kuma yace gobe zai zo ya Daukeni ammh sai me,har nagama Shirina ina jiransa baizo ba kuma nayi ta kiranshi awaya bai dauka ba. har Washe garin Ranar bai daga kirana ba Hankalinna ya Tashi na Shiga damuwa. Na kuma Nuna ina son komawa Dutse ammh sai Mamanta ta hana ni, wacce Suke Kira Maman Fati.

A She Tun Ranar da Ishaq yace na jirasa,ya aika waliyansa suka karb'an mai kayan Aurensa tare da Sakon ya Fasa aurena. Ita ma Maman Fati Ammi ce ta kirata awaya tana Fad'amata Abunda ke Faruwa tare da Shawartarta kada ta bari na dawo na Tsaya wajenta ta nemamin Taimakon don Tabbas al'amarin ba na lafiya bane, Ba Mamana kad'ai ba Duk masoyina Sai da Ya Shiga Tashin Hankali Da Abunda ya Faru 

 Ganin na Tubure sai na Taho yasa Maman Fati ta saka Mallam ya kirani Falonsa ya Fad'amin bayan ya gamamin Nasiha karb'an kaddara hannun bibbiyu,Nayi kuka kamar Raina zai Fita wanda Shima sai da na kwanta ciwo harda su karin Ruwa agida,Tundaga lokacin Naji kila bani da Rabon Aure ne ni kaina ban Kara mganar komawa ba har akayi Bikin Rabi'a ina Bauchi Mamana da Hajiya da Su Anty Safina harda Shi Mallam din kanshi Suna kokarin Jana ajiki Domin Ciremin Duk damuwar dake damuna.

Bayan Bikin Rabi'a Sai ga Aisha da Fahad sun sauka A bauchi Ranar Wuni mukayi kuka kamar Wasu yara, Aisha tana ta Fad'amin Wlh Umma ce takemin Asiri domin Tasha Fad'an cewa nafi ya'yanta Farinjinin Samari kuma gasu masu Hali bazata taba bari nayi Aure har naji dadi ba,ban Dauki mganarta ba illah na Bar Abun akan kila ni kuma Tawa kaddaran kenan Zaman gidanmu mai Cike da Kunci. Hajiya Iya ce ta matsama Abbana kan ya kira awaya maza na dawo,ba yadda na iya haka na Had'a kayana ina kuka Maman Fati na kuka,ammh bayan Mallam ya kirani yabani Wasu addu'o'i ya kuma yace Na zama mai Yawan Ibada,insha Allahu Allah na sane dani.

Komawata Dutse sai da nayi Nadama Haka hajiya iya ta tasani gaba da mganganun Son Ranta itako Umma wani kallo take bina dashi Cike da jin dadi Ranta fes Duka ya'yanta ta Aurar dasu A gidanmu bansa adadin kukan danayi ba, ko gidansu Aisha bana Son Shiga saboda bani so Ammi ta Fahimci Halin danike Ciki.

Aisha ce tabani Shawaran mezai Hana na koma makranta Tunda takarduna Sunyi kyau na yaba da Shawararta kuma kai Tsaye na samu Abbanmu mukayi mgana kuma ya amince nan na Sanar dashi School of Nursing nakeso yace zai saka A nemarmin. 

Nayi ta jiran Abbana ammh naji Shuru Koda na sakemai mgana sai ya nuna gwara na Hakura da karatun jin haka sai banji dadi ba na Kira Maman Fati na sanar da ita,ita kuma batare da Sanina ba tama Mallam mgana waya kawai yayi sai ga Sakon Maman Fati ta kira tace Na Shirya Duka takarduna Wani Mutumi zai zo ya karba.

haka ko akayi yazo har kofar gidanmu ya karbi takarduna,ko Wata ba'ayi ba Maman Fati ta kirani awaya ta Sanar dani na samu kurbin karatu a *SCHOOL OF NURSING BIRNIN KUDU..* Murna ta kusa ta kasheni saboda Farinciki. lokacin danaje na sanarma Abbana Umma na Falonsa baiyi mgana ba ammh ita sai da tanka wai dama dalilin danaki Auren kenan zan tafi chan nayi ta yawon Iskanci da Sunan karatu 

 Hakama Hajiya iya Ta inda take Shiga banan take Fita wai harda ikararin Mamata tayi asara wlh ba inda zani wannan karon nayi musu bore don ko ta kansu ban bi ba,Tunda Abbana ya amince kuma har 20k ya bani da zanyi Siyayyaar tafiya Tunda Bording zanyi,Kafin sati biyu ta cika na gama Had'a Dukkan kayana,mijin Maman Fati da kanshi yazo har kofar gidanmu Wato Proff.Abdallah Mahmud Azare,ya tafi dani har cikin makranta aka karisa sauran cike cike kunga yadda ake karramani malamai jin yace musu ni yarsa ce,ko kafin ya Tafi har an kaini Hostel, nan ya tafi ya barni bayan ya cikani da kudin harda sakon Maman Fati da Hajiya.


Shigata Sch of Nursing Birnin kudu Ta taimaka wajen Chanza Rayuwata daga kunci Zuwa Farinciki.

Na maida hankalina wajen karatuna,ban yarda na karayin Wata kawa ba Aishata kadai ta Isheni saboda kada wata ta Shiga jikina watarana taji lbrina har tayi min gori, Gashi ina jin dadin karatuna,Shekarata ta farko a mkrantan ammh har Sunana ya Fita saboda hazaka ta uwa uba kuma ina amsan Suna ya' ce ga Prof Abdallah Muhmud Azare,Duk da Asma'u Ladan Sharif nake amfani.

 A rayuwata bana kaunarma ace zamu samu Hutu saboda zan koma Zaman gidanmu mai Cike da kunci kowata daliba tana murna Zuwa hutu gida ammh ban da ni. 

ga kuma karatu ba Halin nace Zani Bauchi,Sai da na koma gida hakanan na zauna dakin da Fa'iza da Rabi'a Suka Tafi suka barni,Aisha ta yi bari sau biyu bata da lafiya Infection ke damunta Suna Zuwa asibiti Neman mgani Fa'iza kuwa har haihu Mace, Ina Shekara ta Biyu naji Lbrin Auren Kursum da Fati,ko daya ban damu har akayi bikin nasu banzo gida ba.

ina Tunanin tafi tafi gashi har gida ya watse Dagani Sai Maryam,kuma ita karamace acikinmu.

Haka aka Dinga Dauki D'aid'ai agidanmu Aka wayi gari har Maryam din tayi Aure ammh ita kano aka kaita Wani dan'uwan Mahaifiyarta Ta Aura. lokacin da akayi bikinta Ina mkranta muna jarabawar Karshe ce ta gamawa ko da ace bamu jarabawa ba Abunda zai kawoni don Babu Abunda Zan Tsinta sai Bakinciki.

mganar Samari kullum na Fita sai nayi Saurayi ammh kuma ni na yankema kaina Hukunci bani kara kula wani Namiji Tunda alamu ya nuna kila bani da Rabon Aure Aduniya.

Mun gama Jarabawarmu Ta Fita kenan Bayan mun je Asibti munyi pratical kenan. wanda a babban Asibtin Dutse nayi nawa,lokacin ne kuma Aisha ta Haihu Namiji,yaro yaci Sunan Mahaifin Fahad.

Aminu suna kiranshi Amir, Rayuwa haka ta cigaba da gangarawa har na Dawo gida ina jiran Fitowar sakamako koda Sakamako ya Fito ta hannun prof.Abdallah Azare yazo saboda yadda komai yayi kyau batare da sani na ba har ya neman min aiki a asibtin Jaharmu Wato General Hospital Dutse,wanda Jin haka yasa na Shiga Farinciki ko banza zan Rage zaman gidanmu mai Cike da kunci.

Inda Ace kudi na Siyan Miji toh da Aisha da Mamana Sun Siyamin gangariya ma kuwa. domin Sun fi nuna damuwa ga Abunda ke Faruwa dani, niko na cire Abun Raina na maida al'amura ga Allah bana barci Sosai adare kullum cikin kai kukana nake ga Rabbil izziti kan yamin Zabin Alheri bana Wasa da azkar saboda kariya ce gareni.

Kuncin gidanmu ya Riga yazama acikin jikina,Ko Hajiya iya na Mganarta akaina bana tanka mata. balle kuma Umma wacce na Riga na gane Har Abada bata Sona,Anty Amarya ce kadai ta kwarai Acikinsu Balle Mama da ba shiga harkan kowa take ba daga ita sai ya'yanta.

 Abbana Yana jin zafin Abunda a ke min ammh kuma bashi da ikon Nuna wa,saboda kamar yana Shakkar Umma ne,ga kuma Hajiya iya Wacce bata kama Tsufanta kullum cikin Tsegumi take kamar wata yarinya.

ba yadda basu kulla min Wajen Abbana akan ko waye yasamu ya Had'amu Aure dashi wai Tunda naki fito da miji, wai ko Samarin dake tafiya na baya ni nake Koransu da bakin Halina. Ammh meyasa su Sauran yan'uwa nq sukayi Aure..? ni na tsaya zabi da kuma jiran Mai kudi,duk Abbana bai bi ta kansu ba,domin Shi mutum ne daya san Hakkin Dan Adam. ammh Tabbas zamana babu Aure ahaka yana damunshi sai dai bai taba Furtama kowa ba, Domin kowa yasani Burin kowani Uba ya ga Duka ya'yansa Sun mallaki gidajen Aurensu.

Aikina Shine Rufin Asirina da albashina nake ma kaina Hidima,in aka ga na Fita,toh gidan Ammi na Shiga ko kuma Naje gidan Aisha,. sai ko Fa'iza wacce har yau bata yadani ba, Duka ya'yan gidanmu ba wacce bata haihu ba,daga mai Haihuwa daya sai me biyu, su Anty Rukayyah dai Sune masu garke,duk da suma bana Hulda dasu,wani lokacin sai mun hadu dasu Sunzo gida mu gaisa wani lokacin saboda gulma har cemin suke wai bana Zuwa gidansu Alhali ba wacce tataba Nemana.

Mamana ma takara Haihuwa inda samu Namji yaci Sunan Mahmud, Shi kan ban samu zuwa ba Saboda Wajen aikina.

 Duk sadda naje gidan Aisha ita da Fahad da Amir sun dinga murna kenan Su rasa ina zasu sakani,in kuma zan dawo Fahad ya dauko ni amotarshi ya kawoni. wannan Dalilin ne yasa Gulma ta Fito kuma Daga gidanmu ne,wai cewa ina Son Mijin Aisha Fahad wanda mgana ta Zagaye gari har gidansu Aisha, Ammi dataji sai tayi dariya tace Da haka zai Faru da tafi kowa murna Yadda Asma'u da Aisha zasu zauna karkashin kulawar namiji daya jin haka yasa ba'a kara Kawo mata gulman ba.

naji mganar Abun ya bani mamaki,Aisha ma dataji sai ta dinga Tusama Fahad ra'ayin Aurena. shi kuma yana Kaucewa daga karshe har Fada ta Faru tsakaninsu,Shi Fahad din ne ya kirani ya Fad'amin Banje gidan ba ta waya na kirata ina mata Dariya bata da hankali nan na Dinga lallashinta Dakyar ta hakura ta bar mganar shine labari har kunnan Abbana,kuma wannan ba aikin kowa bane sai na Umma itace Bata kaunar Taga ina Farinciki arayuwarta.

Duk Da kuncin gidanmu yazamarmin jiki,ammh Wani lokacin Abun na kaini bango. na koma daki nayi ta kuka kamar Raina Zai Fita, shiyasa bana kaunar ace yau bani da Zuwa Asibiti duk saina Wuni cikin kunci ko ban Fito ba Daga waje zakaji Umma da Hajiya iya Suna yada min habaici wai naji kunya muna kwana daki daya da kannena har Sun Yin Aure sun barmin dakin niko naga wajen zama harda gyara daki Tunda Banda niyyar Aure.

saboda Sunga na Siya karamar katifa da karamin Wardrope,niko ban bi ta kansu ba, Acikin Raina ina Fatan ko banyi Aure ba Insha Allah bayan na mutu ina Fatan Rabauta ranar gobe kiyama.


Lokacin dana Fara aiki,Umma da hajiya sukayi Borin Hauka saboda Sunga ina Zuwa aikin kwana,har cema Abbana Sukayi ba Asibiti nake Zuwa ba Yawon iskanci nake zuwa,Duk da haka bai bi ta kansu ba sai ranar kwatsam Walid ya tashi cikin Dare yana ta amai,nan suka daukosa Zuwa Asibtinmu,Lokacin muna babban Falo nida Sister bahijja mu muka karbeshi muka bashi Taimakon gaggawa kafin likita yazo.

Abbana yana ta kallona nasan ko bai Fad'a ba Aransa yaji dadi,Inaga Tunda lokacin ya Toshe kafar kawo Wata mgana Domin da yawon iskanci nake zuwa da bai ganni ba.

Fahad ya had'ani da abokansa Dadama bana bashi hadin kai,sai da naga Aisha ta damu,kana na yarda na Fara kula wani Ja'afar sama sama,shima tafiyarmu bata yi nisa ba Ranar na kirashi Matarshi ta Dauka tamin Zagin kare dangi.

Tundaga Ranar na goge Nombarshi na kama kaina bai kirani ba nima ban kara kira ba,shima yabi Sawun Sauran kenan,ban damu ba Domin daman ban sakashi araina ba.

Na riga na Fidda rai da Aure kwata kwata arayuwa na maida kaina ga bautar ubangiji ina Fatan mutuwa ta Riskeni ina cikin Bautar Ubangiji.

 

********


Portharcourt


Wasila ta Fito daga Dakinsu jamila A fusace Fuskarta sam Babu Fara'a ko kad'an.

Ko barayin su Jamila bata kalla ba Wad'anda Suka baro Saman Dinning Suka Dawo kan Lumtsum lumtsumar kujerun Falon Sukayi Dai dai.

Bata musu mgana ba illah jefama Jamila wayar datayi ita kuma ta Cafe,Cikin Fushi da Takaichi ta Haura sama kamar zata kife .

Tana Shiga Bedroom din Ta Iske Abdallah yayi kwance Rigingine ya kurama Rufin dakin Ido Hannayensa Suna Harde akirjinsa da alamu ya Shiga kogon Tunanim

Wasila ta Dad'e Tsaye akanshi tana Nazarinshi Gabadaya Ranta ya gama baci,Hayowa gadon tayi hannu ta sanya ta Cire hannuwanshi dake saman kirjinsa ta Maida kanta awajen.

Ajiyar Zuciya ya sauke yana Bin Wasila da kallo asanyaye kamar Wanda bashi da lafiya.

Cike da makirci Take Shafa Kirjin nashi tana Fadin"Dee wai meke Damunka ne,Tun bayan da kayi waya da Yusuf mood dinka ya chanza Meya Fada'maka ne Wanda ya Tadamaka Hankali haka Dee..? Bai mata mgana ba,kuma bai taba ta ba Ganin yayi mata Shuru yasaa ta Dago kanta tana kallonshi Ganin idonshi biyu yasa Abun ya Fara bata Tsoro Cikin Wani yanayi Tace,"Dee..."Lum yayi da ido kafin ya Diresu akanta yana kallonta.

Hannunshi ta Riko tana Fadin"Wai meke Faruwa ne.? kasani cikin Duhu ko wani Abun ya samu Hajiyar ne?

Ta Fad'a Cike da Wani Salo. Bai mata mgana ba illah Hannunta daya Raba danashi kafin yace"Babu komai Noory plz Ina bukatar Kadaici"

Yafad'a yana juya mata baya.

Zaro ido Wasila tayi Zuciyarta na Rawa,Kan bala'i Yaushe Abdallah ya Fara mata haka ita da ko Tari tayi Abdallah sai yaji Dalili,in tayi mai mgana jikinsa na Rawa yake amsamata.

Bata jira komai ba ta Diro daga kan gadon ta Fad'a Tiolet da Sauri bayan ta Kalli agogon bangon dake bangon Bedroom din nasu 12 ta kusa,Agurguje tayi Wanka ta Fito.

koda ta Fito yana inda ta barshi ammh wannan karon ya Runtse Duka idanuwansa kamar mai barci bata bi ta kansa ba Ta Shafe jikinta da Lotion dinta Wardrope dinta Na nufa ta Fito da Wani less dinta Dinkin Doguwar Riga ne,Attachement din dake kanta ta gyara ta Daure da Band kafin ta Yafa wani karamin gyale bisa kanta ma'ajiyar Takalmanta ta Nufa ta jawo Wani baki mai Tudu ta sanya.

daganan bangaren Jakunkunanta ta Nufi ta Dauko wata karama baka,Wata Drower naga Ta bude sai ga Kudi da yawa basu da iyaka,bata tsaya kirgawa ba ta sanya hannu ta Diba iya Dibanta ta Maida ta Rufe.

ganin har yanzu yana yarda ta barshi yasa ta karisa gaban Dressing Mirrior din ta Dauki key din motarta Tana Fadin"Dee zani Bidda Sai gobe zan Dawo in na gama Abun nakeyi in kuma Ban gama ba sai jibi."

Dakyar ya bude Idanuwansa da Suka chanza Launi,yana kallonta Bai iya mata Wani dogon mgana ba don lokacin kanshi ke Saramai Cikin Siririyar murya yace"Wazai kaiki baki ganin Rana tayi..?

Far tayi da ido kafin tace"kada ka damu Samuel zai kaini. Ba da kai na zanyi Driving ba."

Kai ya gyad'a maka kafin yace"Safe landeed Noory.."

Mirmishi ta saki kafin ta Duka ta Sumbaci Kuncinsa,ta Fice da hanzari.

Da kallo ya bita har ta Fice Daga dakin,maida idanuwansa yayi ya kulle yana jin gabad'ya yanayinsa Babu dad'i kamar Wanda akama Dukan Tsiya.





Janafty*