ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 08
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️08*
Nan inda ta barsu nan ta iskesu
ganinta cikin Shirin Fita yasa Duk Suka tashi Zaune.
Jamila ce tace"Anty Fita zakiyi.? Kai ta gyad'a musu kafin tace"Eh Bidda zani kuma sai jibi zan dawo, Saboda haka ku kula da kan ku kun ji ko?
Gabadayansu suka gyad'a mata kai kafin Su mike Suyi hugging d'inta lokaci d'aya Suna Fad'in"Allah ya kiyaye hanya ki gaida mana Momcy."
Suka Fada atare. kumatunsu ta Shafa kafin tace"Alright. in kuna bukatar kudi kawai ku Tambayi Dee, kunji ko"
kan su suka kara d'aga mata alamun Sunji.
Wucewa tayi da Sauri Suka bi bayanta har Farfajiyan gidan inda morarta Kirar prado take Samauel ta Shiga kwalama kira sai gashi ya Fito da Gudu yana Fadin"Yes Madam."
Key d'in hannunta ta Wurgamai kafin ta Bude bayan motan ta Shiga batare da yayi mgana ba ya Shiga mazaunin Direba Ya Tada motar.
bayan ya Zuba hon,megadi ya wangale musu kofar Makeken gidan Suka Sulala waje, Su Jamila na Daga musu hannu har Suka Karisa Ficewa daga gidan.
Falon Suka dawo suka sake Da'i da'i a saman kujera kowacce nata Faman Danne dannen A faska faskan wayoyin su. Motsin Saukowan Abdallah Sukaji duk suka waiga yana sanye da Riga da wando Blak and White.
Fuskarsa ta bayyana alamun kamar yana cikin damuwa, wayarsa ke hannunsa sai key din motarsa,Bai ko kalli barayin da Su Jamila Suke ba. ya Fice yana Taku cikin Sanyi da Rashin kuzari.
Da kallo Jamila da Hafsat suka bisa kafin su koma Su kalli juna,suna tabe baki ,dama ko da chan bai Cika Shiga Shirginsu ba koda yaushe Fuskarsa adaure in dai ba yana tare da Anty Wasila bane. ba wacce Ta damu sai ma kara Lafewa da Sukayi bisa kujerun Falon,yayinda Jamila ta shiga kwalama Josepen kira, jiki na rawa ya Fito daga kichen jikinsa daure da Rigar Girki,Yamutsa Fuska Jamila tayi tana bashi odar ya kawo musu lemo ita da Hafsart.
jikinsa na rawa ya amsa kafin ya Fice daga Falon da hanzari,Hafsat ta rakashi da Wani Dogon Tsaki tana Fadin"Arnen banza dan Wahala"
yana Fita haraban gidan Emeka ya taso da hanzari yana gaisheshi hannu kawai ya Dagamai.
bai mai mgana ba ya Nufi motarsa matrix,Emeka yayi hanzarin bud'emai bayan mota,ammh sai ya Daga mai hannu kafin yace"No i will drive my Self'
Yafad'a kafin ya bude bangaren Direba ya Fada,cikin kwarewa yayi ma motar key. kafin ya saki Hon baya Emeka yaja lokacin da Abdallah yayi kwana da Motar ya Fice da Sauri kamar Zai tashi sama. yanayin yadda Emeka ya ga Ogan nashi yasan wani abu na faruwa.
Elelewo yanufa,Bakin Get din gidan ya Saki Hon, Polina dake kwance kan Daya daga cikin kujerun da Suka ma Falonta kwanya Kewar Abdallah Duk ya cikata yau Wajen kwana biyu kenan bataji shi ba.
kuma tana ta kiran wayarsa baya dagawa sai dai ya yi mata Text dacewa zai Kirata ammh har yau Shuru, Tafara damuwa kuma gashi yau Sunday balle tace zata sameshi A office kamar amafarki taji Hon din mota,cikin Fitan hayyaci ta tashi ta Fito da gudu wanda daga ita sai Wata kamarar yaloliyar Riga wacce Bata boye komai na Surar jikinta ba.
bata bude get din ba,sai da ta leka ta karamar kofar taga Abdallah ne kana Tafara jan get din gidan cikin Farinciki da Zumudi.
Yana kallonta ta cikin madubin motan ya sakarmata mirmishin nasa mai Saka mata dadama Farinciki,cikin Hanzari ya Sulala da motar cikin dan karamin Haraban gidan nata.
Tun kafin ya gama Daidaita parking Polina ta Rugo da Gudu ta Bud'emai Kofar mota ta sa hannu ta jawoshi waje Ta fad'a jikinsa Cike da Farinciki ta kamkamesa. ajiyar Zuciya ya saki lokaci daya yana kara Riketa cikin Wani yanayi take Furta"I Realy Miss u my Sugar."
Take Fad'a tana kara Tusa kanta acikin Kirjinsa cikin Wani yanayi Shima kara Riketa yayi yana Shafa Bayanta Zuwa Tudun Hips dinta yake Fadin"Me too my Babe."
Yake Fad'a cikin Wani yanayi yadda taji muryansa ne,yasa tayi Saurin dagowa tana kallonshi Cikin Wani yanayi take Fadin"My Sugar,waht Wrong With u? look so Cool Today?Tafad'a tana Shafa Sajensa da hannunta tana kuma gangarowa zuwa Kasan Wuyanshi
Lumshe ido yayi kafin ya Rike hannunta bai mata mgna ba. illah Janta dayayi Suka Fara tafiya Zuwa cikin gida,yana kankame da ita Tun acikin Falon yafara Sumbatar polina cikin Wani yanayi ganin yadda yake aikamata Sakoninsa nasa cikin Zafi zafi Shiyasa ta gane Wani Abu na damunsa batayi Wasa ba itama ta tallafeshi.
Tana bashi dukkan Halin kai,nan suka fara watsewar da suka saba tun a tsakar falon kafin su rankaya zuwa cikin bedroom.
******
Karfe 5:30pm Motar Wasila ta Shiga haraban gidansu,Cikin Isa da takama Wasila ta Fito Ta nufi cikin gidansu Tun daga Falon Farko take kwalama Hajiya kudirat kira. yan aikinsu kuwa Suna ganinta sai Duka mata Suke Suna mata barka da Zuwa,Ammh ko kallo ba wanda ya Isheta, tana kokarin Tusa kanta abedroom din Momcy dinta ne Ta Fito Suka cikaro da Juna,Cike da Mamaki Hajiya Kudirat ke kallon Wasila kafin tace"Wasila Kece tafe yanzu..?
Bata mata mgana Ba illah Fad'awa datayi jikin Momcy ta Fashe da kuka tana Fadin"Momcy Zan Rasa Abdallah,Momcy Abdallah yanzu bayason Kallona,yadaina jin mganata. Komai yana so ya Lalace Momcy."
Tafad'a ta na kara Sautin kukanta Rikota Momcy tayi Suka Fad:a cikin Bedroom dinta gefen makeken gadonta ta Zaunar da ita tana Fadin"Wai meya Faru ne naganki da gaggawa haka,ba mun gama mgana sai gobe zaki Taho ba..?
Wasila ta Yamutsa Fuska tana Share Hanci tace"Haba Momcy taya zan iya zama har nakai gobe. Zuciyata bazata jura rasa Abdallah ba Momcy wlh Shegun Tsofaffun nan Suna neman yin Nasara akanmu."
Tafad'a cike da bakinciki kafad'anta Momcy ta dafa tana Fad'in"Kalleni nan Wasila. Matukar ina raye wlh Abdallah zai cigaba da tabbata naki Har Abada ki kwantar da hankali in Sun sa wata basu san Wata ba, Gobe da Sassafe zamu ma Boka dandugaju Sammako. Kisa ranki a inuwa Abdallah haryanzu yana Tafin hannunki ne.."
Wasila ta Riko hannun Momcy tana Fadin"Toh nidai muje yanzu Momcy plz" Kusa da ita ta zauna kafin tace" Baki da Hankali ne Yanzu fa yammah tayi so kike kafin mukai Dare yayi mana ahanya,kuma kin manta boka Dandugaji baya ganin mutane da Zarar 4 tayi? kibari gobe mana,kina fa da Taurin kai Wani lokacin Wasila"
Tafad'a cike da Kufuluwa,Gyada kai Wasila tayi kafin ta Sadda kanta bisa kafad'an Momcy tana sauke tawagen ajiyar Zuciya.
Ita kuma momcy ta Riko Gefen Cikinta Tana Bubbugawa alamun lallashi.
Momcy da kanta ta Fita tama megadi mgana kan ya Shigar da Sumuel Dakinsa, bayan tasa an kawo mai Abinci. wasila ko Dakyar ta iya Shan Fressh Milk,Ta kwanta ko Babanta sai dai yaji lbrin Zuwanta abakin Momcy bai tsaya tambayan me ya kawota ba,saboda indai Wasila ce bata wata sai Tazo Bidda.
Tun around 9 wasila keta kiran Nombar Abdallah tana Ringing baya dauka,Shiko Har lokacin yana gidan polina Suna Sheke ayarsu wayarma tana Falo baisan Wasila na kira ba.
itako Duk inda hankalinta yake yakai Dubu ya tashi. Tafara safa da marwa tana Jijjigan jiki,Zuciyarta na hango mata Abdallah ya Tafi Bauchi ne bayan Tafiyarta. Wayar Jamila ta kira tana Tambayanta Abdallah,nan take Sanar da ita ta Fita ba Dadewa ya fita shima kuma haryanzu bai Shigo ba.
Nan fa Wasila ta Tsure ta fara kuka tana Duren Duren Ashar tana Zagin Hajiya da Mallam tana kuma ikirarin har Abada Abdallah nata ne ita kad'ai cikin Wannan Halin Momcy ta tarar da ita cikin bacin Rai Ta Rikota tana Fadin"Are u mad..? kina Abu kamar Wata yarinya Waya Fada miki Abdallah zai barki ehe...? Wlh in baki daina Wannan Wutar cikin naki ba Zaki lalata Duka aikinki da kanki kin Manta Sharad'in Boka Dandugaji? ya jadadda mana banda gaggawa ya Fad'a ba Sau d'aya basau Biyu ba. ammh kwata kwata Shigen Zuciyarki na neman Warware komai"Tafad'a cike Da bacin Rai..
Kuka Wasila ta Fashe dashi tana Fadin"Momcy Sun Rabani da Abdallah,wlh Sun Rabani Da Dee. ina ta kiran wayarshi bai dauka ba na kira su Jamila sunce ina Fita ya Fita, ina zaije Momcy yau fa babu aiki Kilama Bauchin ya Tafi"
Tafad'a tana Dora hannu akai Momcy bata samu Zarafin mgana ba wayar Wasila dake hannunta Ta dau kara a zabure ta Duba mai kiran ganin Sunan my Dee ya Fito baro baro yasa ta Daka tsalle tana Fadin"Momcy Dee na kirana."
Tsaki Momcy taja kafin Ta fice Daga dakin Cike da Haushin Wasila.
Ita ko Wasila kuka ta sakama Abdallah yuyuyu. Tana Fadin ta kirashi yafi Sau nawa bai daga kiranta ba, Shiko lokacin ma ya baro gidan polina around 11pm na dare nan ya Shararamata karyan cewa waya ya samu Daga office kan wasu kaya da'aka Rike so tunda yaje yazama Busy bai samu kanshi ba sai yanzu,ma yake hanyar komawa gida. sai alokacin Hankalin Wasila ya kwanta Dataji ba Bauchi yaje ba don ayadda take ganin Shegiyar Uwar Abdallah din komai Baffa yanzu Tunda ta samu Baffa Bazata barshi Ya dawo gareta ba,Shiyasa zatayi Duk iya bakin kokarinta na ganin tayi musu katangar karfe dashi Domin Abdallah Shine rayuwarta bazata taba bari Wata mace ta kusanci Abdallah bayan Ita ba.
********
Da Sassafe Su Wasila Suka Fita. Da kanta ta kw Driving din motar yayinda Momcy ke gefenta. kauyen Bazumagi Dake garin Bidda Suka Dosa Chan cikin Daji Bukar Boka Dandugaje take.
Lokacin da Suka je wuraren goma ne Don ma Sunyi Gudu ahanya Wajen akwai Nisa Sosai,sai da Suka jira Wata mata Ta Fito don layi akemai Domin kowa yasan aikinshi kamar yankan wuka yake.
Suna Shiga Suka Zauna kan Wani Buzu dake gabanshi Takalminsu Rike a hannunwansu Domin ba'a Shigo mishi Bukar da Takalmi.
ko kallonsu baiyi ba illah kansa dake Duke ya kurama Wata Kwarya dake gabanshi ido,yana kuma mgana kasa kasa.
kallo d'aya nayi ma Bokan sai da na Tsorata Domin Halittarsa ba Abun Sha'awa bane. Wani Wada na gani Kamar an kifeshi da kwarya kanshi kato yana Rinjayar gangar jikinsa,ga Katon ciki ga baki bashi da kaya ajikinsa sai wani ganye da ya Rufe gabanshi dashi. Akidarshi da kin Shigo baza ki yi mgana ba sai ya baki dama,cikin wata katuwar Murya yace"Meke Tafe Daku.?
Momcy ta gyara Zama ta fara Fad'in"Boka kan mganar yaron nan Da kake Mana aiki akanshi.."
Katseta yayi da hannu yana Fadin" Kitafi Kai Tsaye Duk munsan da wannan Jawabin naki"
Yafad'a yana Zuba mata jajayen idanuwansa kamar gawarshi Wuta. Wasila ta kalli Momcy tana Tabata Tsawa ya daka mata yana Fadi'n"Ke. Kya kanki ba'a mana Munafunci anan. Duk Abunda kika aikata Aljanu Suna Lura dake Saboda haka Ki shiga Hankali ki barta tayi mgana da kanta.."
Wasila ta Tsorata ammh haka ta dake, Momcy ne ta Rusuna tana Fadin"Amata afuwa Ran Boka ya Dad'e dama Yaron ne yanzu yake son Zuwa garin iyayen nashi. toh Shine mukeso Don Allah Boka..."
Wata Tsawar ya kara daka musu Wacce ta sakasu Tsorata cikin Wata Firgitattaciyar murya yace"Kul kika kara kiramana Don Allah anan. Don Ubanki kinsan Da Allahn kika zo Wajen mu, Maza ki Tafi kai Tsaye ga bayaninki in kuma kika kara yanzu aljani Tsidugu Zai Raba kanki da gangar jikinki.."Yafad'a lokaci d'aya yana Kecewa da Wata Mahaukaciyar Dariya.
Wasila da Momcy Suka Kamkame juna Suna rawan Jiki. Momcy cikin Rawan Murya take Fadin"Amin Afuwa Boka Subutar Harshe ne"
Hannu ya Dagamata kafin yace"Mgana ta Farko gargad'i ne daman. Ina jinki yanzu me kuke so asake yi mishi.."Jin haka yasa Wasila tace"Muna so ahanashi Zuwa garin gabad'aya bayan an Ciremin Sha'awar DuK Abunda ya Danganci Garin.."
Shuru yayi ya kura ma Waje Daya Ido kafin ya gyad'a kai yana Fadin"Wannan karon baza mu taba iya Hanashi Zuwa garin Mahaifansa tabbas sai yaje.."Yafad'a lokaci d'aya ya na wani Zare ido.
Wasila da Momcy Suka Zaro ido bakin Wasila na Rawa tace"Sai yaje kace Boka..? Tafada da Sigar Tambaya ammh da alamar Ficewar Hankali.
kai ya gyad'a mata kafin ya sakarmata idanuwansa yana Fadin"Eh haka nace Tabbas wannan karon Sai Abdallah ya Danganta da Mahaifansa. Dole yaje"
Jin haka yasa Wasila ta Dora hannu akai tana Fadin"Na Shiga uku Boka Don Allah ka hanashi Zuwa. Wlh Zuwarshi Bauchi babban Matsala ce wajena da Rayuwata"
Wata Dariya ya kece dashi kafin yace"Baki Shiga uku ba Tunda kika Kawonana kukanki. Na sanar daku Tun abaya Iyayen yaron Suna tsaye akanshi ba Dare ba Rana, Ko alokacin Aurenku dana Turama mahaifin yaron Aljanu sai dawomin yayi Duk jikinsa Rauni bai samu Nasaran Rab'anshi ba Saboda Mutum ne mai Riko da Ibada da kuma yawaita karatun alQur'ani ko Shima yaron mun samu Nasara akanshi ne Saboda yana da Sakaci da ibada kuma baya Addu'a."Gyada kai Sukayi bai ba su Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin.
"Aljanun dana Turama Abdallah wanda yake Nesantashi da Garin Bauchi da kuma Abunda ya Shafi ahalinsa yanzu haka yafara jigata. Domin addu'o'in da iyayensa Suke masa yana Zuwa garesa. Dama na Fad'a muku Afarkon Zuwanku zamu yi aiki akan Abdallah ammh kuma Zai dinga warwarewa Lokaci bayan Lokaci Saboda yana da Wasu Taurari Guda uku wanda Suke da Matukar Tasiri akanshi, Saboda haka Abdallah Zai Tafi Ga Mahaifansa Dole sai yaje."Yafad'a cike da Tsaawa.
Wasila da Ta fara hawaye tace"Boka ka min Rai kahana Abdallah Zuwa Bauchi wlh in yaje rabani dashi zasuyi."
Wata Shegiyar Dariya ya saka lokaci d'aya ya na Fad'in"Ai indai kin yarda da aikinmu Dole zai Dawo gareki bazai taba iya Rayuwa babu ke ba. Mune fa muka Sanya yake zaune Dake haryanzu ammh Abdallah baitaba Sonki ba. Mace irinki ma ba tab'a Burgeki ba. Mune muke Dauke da Duka Gundin zamanki Atare da Abdallah, KumaTunda kikaji nace Sai yaje Toh Zuwanshi Shine Mafita"
Wasila da jikinta kaf ya jike da Zufa,ta kalli Momcy tana Neman saka mata kuka ganin haka yasa Momcy tace"Boka kadai Taimaka mana. Yanzu ba wata hanya da za hanashi Zuwa..?Cike da Jin Haushi ya Daki Kwaryar dake gabanshi sai da Ta Fashe cikin karaji da Tsawa yace"Nace bazai Yuyu ba ko..? Indai kuka matsa Toh komai naku zai lalace. In nace lalacewa ina Nufin Abdallah zai sakeki kuma ya koreki daga gidanshi bayan kuma ya Wulakantaki ya Tozartaki a idon Duniya Daga karshe Ki Haukace Saboda Abunda kikayi ya koma kanki." Ya karishe fad'a lokaci d'aya yana Sakarmusu jajayen idanuwansu.
Zaro ido sukayi atare Kafin su Samu Zarafin mgana ya Daga musu hannu yana Fadin"ku tashi ku Tafi. Kada ku Dawo sai bayan ya Dawo daga Bauchi lokacin ne zamu sake sabon aiki. Ku tashi ku Fita Lokacinku ya kare."
Yafad'a yana Nuna musu Hanya,da hanzari Suka Mike Momcy ce kema Boka godiya kafin Wasila ta damko Kudi acikin jakarta Ta Zubesu anan Suka Fita Jikinsu na Rawa da jin Abunda Boka Dandugaji yace.
Akwai Tafiya tsakanin inda Sukayi parking da inda Bukar boka yake Saboda Halin da Suke ciki ba wanda yama Dan'uwansa mgana.
Wasila ko Tafe Take,kamar wacce Akace tarasa Uwa da uba, koda ganin yadda Fuskarta ya bayyana tashin Hankali kara kara Har Suka isa wajen Motarsu Wasila ta Wurgama momcy key din ta na Fadin"Ban iya janmu Momcy kaina Saramin yake.."
Momcy ba tayi mgana ta chabe Key din ta Shiga bangaren Direba ta Tada motar Suka Fara Fita daga Dajin sai da Suka Fita kwalta, kana Momcy ta kalli Wasila wacce ta jingina kanta ajikin Cussion din Kujeran motan Hannunta na Dafe da kanta. Cikin wani yanayi Momcy tace"Plz Wasila cool down. kada ki Tada hankali kindai ji Abunda Boka yace ko? Toh gaggawa ga banamu bane.."
Ido Wasila ta Bude wad'anda Suka Kada sukayi jajir tace"Ya zanyi momcy.?Bazan iya juran Rasa Abdallah ba inajin Tsoron Shegun iyayen nashi. kada su Rabani dashi har Abada.."
Momcy tace"Basu isa ba Wasila. Da zarar ya dawo Ki zo mu koma wajen Boka mu ji Abunda zai ce mana. kinji yace zai sake Sabon aiki akanshi.."Runtse ido Wasila tayi Tana Furzan Da Numfashi take Fadi'n"Zuciyata Zafi take. Ni Bauchin ne da naji an ambata sai yanayi na ya Chanza, Allah na gani bana Kaunar naga Abdallah yarabi wani bayan ni da Abunda na yarda dashi.."Tsaki Momcy taja tana Fadin"Owk Kenan kin Shirya Abdallah ya koreki kenan ko? Ko kuma kin Shirya tababbata cikin Hauka na har abada Bisamillah.."Jin haka yasa Wasila tayi Saurin Cewa"A'a Momcy Na bari Wlh."Kai ta gyada tana Fad'in"Better...'kafin ta Maida hankalinta Bisa kwalta Daidai lokacin Datake Duba agogon Fatan dake Hannunta Taga karfe 3:24pm na yammah.
****
Dutse
Yau ta kama Alhamis ne.
Aikin dare gareta ,karfe 6 na yamah tayi Shirin Tafiya,kuma ayau din take so ta ma Abba mgana kan mganar Tafiyarta Bauchi gobe takoson Tafiya Tun da Har Ranar Sunday bata da Duty,Sai da ta Shirya zata Tafi Asibitin ta Shiga Falon Abba yau din tayi Sa'a Umma batanan taje biki kuma bata Dawo da Wuri ba.
Har kasa ta Duka tana Gaida Abba kafin ya amsa cikin Sakin Fuska,Kanta na kasa take Fadin"Dama Abba ina so naje Bauchi gobe ne.nShine nace bari na Sanar dakai.."
Shuru yayi yana kallonta kafin yace"Bauchi..? An yi Wani Abu ne..?Kai ta girgiza kafin tace"Hajiya ce batajin dadi zan Je na Duba.."Kai ya gyad'a kafin yace"Aikin ki fa? Kindai san ku ma'aikatan lafiya Koda yaushe Cikin Taimako kuke"
Kanta na kasa tace"Nasani Abba. Ai Ranar Lahadi zan dawo monday ina da aiki.."Jinjina kai yayi yana Fadin"Toh Shikenan Allah ya kaimu ya kuma kaiki lafiya.."Da Ameen ta amsa cike da jin dad'i Kafin tamai sallama ta Fito Cike da Murna,Tayi waje Ranta Fari tas Da murnan Gobe sai Bauchin yakubu.
Wajen Ammi ta biya ta Fad:amata kafin ta Wuce wajen aiki.
har Ammi na Fad'in ba domin gobe zatayi sammako Zuwa jigawa ba wajen kanwarta da ta Haihuwa da Sun Tafi tare.
Ko a Asibiti Kowa yaga Asma'u yasan tana cikin Farinciki Saboda yadda Abun yakasa boyuwa bisa kyayawan Fuskarta.
*Janafty*