11
by @nanadiso10
RUDIN ZUCIYA
NA NANA DISO
Wattpad:NEIRNAHDISO
PAGE 11
_________________________
Lantana ce ta shiga tak'awa tana rawa tana fadin " Sai mijina mai fuskar muminai cikin ransa k'uma fuskarsa arna." Murmushi sosai kawu ibrahim yayi yace " ai lantana bazakisan ina sonki ba har sai na mallaki gonar nan nasiyar da'ita na siyamiki sarkar gold." " kai mai maigidana Allah ya idda nufi, Nikuma zan tabbatar da kausar tafi Surayya bariki nidanake da malam tsalle ai karka damu aikin nan mu biyu zamuyi shi.Kausar dake k'okarin shigowa gaba daya taji kalamansu cik'in bak'in ciki tatoshe bak'inta da kuka ke kokarin kufce mata saurin ja datayi da baya ta koma hanyar waje, cik'in gudu gudu sauri sauri ta nufi gidansu inda ta tarar da malam har yanzu jikin sai a hank'ali karasawa kusa dashi tayi ta zauna tana mai tsananin bakin ciki da kawun nata, a hank'ali malam yadago yace " 'yar albarka menene naga kina kuka nace miki kidaina damuwa da ciwon nan nawa lok'aci ne in Allah ya rubuta zan warke to tabbas zan warke idan Allah bai kawo warakar ba babu yadda zamuyi kinji." " Malam " shine kalmar data fada tana k'uka karfin kukan nata ma yahana karasa lafazin bak'inta. " Kausar menene haka kinfara girma zaki shigo mana gida kina koke koke sai kace wata yarinya." "Innata" nan ma kausar ta fada bata karasa ba tacigaba da kuka. " Duk abunda zan fadi nasan ba lallai ku yarda dani ba kamar yadda kulum kuke kallan kuruciya ke dawainiya dani, amma ina neman Alfarma agareku danAllah duk abunda yaya tayi ku yafemata, kuma inaso akoda yaushe ku kasance masu yi mata addu'a. Malam dake kwance ne yace " ni bantaba tsinewa Surayya ba kuma bazan taba ba jarabawa ce babu wanda yafi k'arfinta Allah yashiryata aduk inda take." Inna ma da idonta yaciko da hawaye tace " kausar kintaba ganin uwa tak'i danta? Nima bantaba yiwa surayya baki ba kuma bazan taba ba, ina rokamata shiriya a gurin Allah yakuma sakata cikin mutane nagari sannan tayi shiru dan kuka ke kok'arin kufce mata.
Bakaramin dogon tunani kausar tashiga ba ' duk yadda mukeson kawu ibrahim duk irin nunawa malam soyayyar da yakeyi amma ace shine babban makiyin mu? Tabbas yanzu data fara girma ta yarda da kalmar da ake cewa 'mugu bashida kama' tabbas kawun su ya zalunci su tsawan wani lok'aci, yanzu yanada hannu gurin ganin yayata tazama abar k'yama? Yaa Allah kadubi ahalina kabasu kulawa, yaa Allah ka iddamin nufina naganin nazata lauya,
***********
P.a ne ke tsayi kusa da alhaji bandir yana jira yakarasa wayar ya dauki kusan mintuna 30 kafin ya ajiye wayar hannunsa yana kallon p a dinsa dan tabbas yasan akwai magana a bak'insa, " ranka yadade barka da wannan lok'acin maganar gaskiya wannan yarinyar bata dace da zuri'arka ba kwatakwata, a tsawan lokacin da na zauna dakai kafin kai na zauna da wasu nayi musu aiki amma maganar gaskiya kana cikin mutane masu tsoron Allah da bin dokokin Allah, bantaba ganin kayi hulda da matan banza ba, amma wannan yarinya dakasa aka bincika maka ba yarinyar k'warai bace ba, kamar yadda nayi binciki yau shekararta 4 da guduwa daga gaban iyayenta sannan ban san adadin mazan databi ba kamar yadda wata aminiyarta wai ita bintu ta gayamin, sannan tacemin tun tana yarinya take bariki yadda tagayamin ma iyayenta sun tsine mata ne, sannan tagayamin tana bin mata, ranka yadade idan kaga gidan datake ginawa nan unguwar dallah sai ka girgiza wallahi ta iya takun bariki kuma duk kudinka bata maimaita zaman hotel dak'ai, sannan nasamu yaron da suke bussiness tare inda ya sanar dani cewa tana kawo kayan jarirai daga waje da dogayen riguna amma batada shago suna rabawa 'yan kasuwa ne, ranka yadade agaskiya banason tarayyar ka da'ita ga matanan birjik agare masu tarbiya Amma wannan yarinyar bata da tarbiya." Murmushi Alhaji bandir yayi duk da yaji badadin rashin shaidar arzuki da ba'ayi mata ba, " Naji duk bayanan ka p a amma abunda banganiba baka nemi ganin Iyayenta bani ?" " Ranka yadade ita wannan kawar tata bintu na nuna mata ubangidana ne ke sonta shiyasa tagayamin komai amma tacemin iyayenta sun gudu daga kauyen saboda bakin cikinta da kuma abun kunyar data jawo musu." " Yaa Allah, tabbas kowa zai iya shiga Rudin zuciya amma Surayya is too young p.a Surayya tayi yarinya da wannan abubuwan ina kallonta kamar diyata mansurah yau idan diyata ce p.a kana tunanin zan barta tacigaba da wannan kazamar rayuwar? Kokuma kana tunanin zanji dadin bayanan ka? Kokuma kai idan taka diyarce zakaso tazama haka? Wallahi jarabawar Allah babu wanda bazata shafa ba, a zuwan datayi gurina nasa andubamin account dinta 2million ne kadai ciki kaga kenan tana tsananin bukatar kudi yanzu saboda gininta da kasuwarta, tundaga ranar ancemin kudi bai kara shiga account dinta ba, kaga kenan bata samu harka ba! Amma abun mamakin shine ta saci numbana agurin badoo kamar yadda na fahimta dan shine last mutumin danayi waya d'ashi aranar kaga kenan suna harka da badoo dan nasanshi ko million nawa indai yanadashi to tabbas zai sakar mata, to amma p.a duk yadda surayya taso kudi guna dataji zancen aure taji kuma bazanyi abunda takeso ba hakura tayi tatafi, wannan zai tabbatar maka yarinyar nan akwai dalilinta na shiga bariki, sannan akwai rashin jindadin abunda tak'eyi don daga ranar da mukayi waya da'ita sai yau dinnan Alhaji tukur yakirata wanda inason zama dashi yanzu yanzun nan p.a nasan zai taimakawa yarinyar nan duk dashima tsoron Allah dinsa da sauki amma nasan me zanyi." Jikin p.a ne gaba daya yayi sanyi tabbas yana alfahari da ubangidansa mai kyakyawar zuciya mai kuma zaton alheri ga bayin Allah, " Ranka yadade ai yana waje ma kasan yanason kwangilar kayan nan dazasu sauk'a bari nayi masa iso." " Madallah" lafazin alhaji bandir na karshe.
***********
Ke bintu wannan masifar ta mecece? " Ke kursum kinga mutumin dayazo dazu kuwa wai yana binciken yar iskar yarinyar nan Surayya, nifa da zaki taimaka min ma mukashe shegiya da bahaka ba," " To me kikace masa ince dai baki ce masa ta kwarai bace ba?" " Lallai ma kursum kina tunanin zan kara barin surayya ta tseremin kinsan malaman danakesawa suyimata aiki akan rashin nasara a barikinta amma kinaganin shegun motocin datake ja, ai da nadinga gayamasa karya sai da yace inaa wannan ba kalarsu bace ba, " " Yauwa akawata kinsan fa tun muna school na tsaneta yadda takeda hazaka da kok'ari shiyasa koda mutumin nan yabamu aikinta banji tausayinta sai yanzu da takeso ta zame mana ciwon ido, ai kawata wallahi ingayamiki mu zubawa shegiya guba mu huce gurin, dariya kursum tasaka suka cafke suna cigaba da bidalarsu.
****************
Shirye shiryen graduation dinsu sukeyi pretty duk yadd takai gurin Ahmad yakulata ina sai tsananin yafi na da dan yanzu ko tsayuwa inuwa daya basayi, ko su baba sun kirashi bayabi yau ma yana zaune acik'in class wayarsa tayi ringing dauka yayi yana mai sallama dakyar, baba ne yace " lafiya kalou kuwa sai kira nakeyi bak'a dauka?" " Baba kuna damuna ne akan maganar kudi bazaiyihu ina nan ina shan wahala ina turawa garada kudina suna cinyemin ba, shi Umar din menene amfaninsa da bazai fita ya nemo muku kuci ba? Sai ni zanna turo muku, danAllah ku rage son abun aduniya baba." Sosai baba ya cika da mamaki yace " Ashe da gaske ne abunda uwarka ta fada to kasani hakkinka ne ci damu ayanzu kamar yanda dan uwanka yayi jahadi abaya yayi sannan kamanta alfarma kasamu aka kawoka nan garin ne?" " To ai baba sai kayita yi banason dogon magana" sannan ya katse kiran. K'arasowa gurin tayi tana kwarkwasa duk da kasam cewar ta mara jiki kwatakwata tun daga nisa take dago masa hannu har ta nufi kusa da inda yake ta zauna, har lok'acin bai dago ba saukar hannunta yaji a kafadarsa tana fad'in " My handsome" da wata rikirkitacciyar murya da tasashi dagowa ya zuba mata idanunsa, cikin bazata tace " you're so cute handsome I love you, lok'aci daya tsigar jikinsa tashiga mik'ewa yau kasa dauke idonsa yayi daga kanta, small lips dinta yak'urawa ido he wish he can....