12
by @nanadiso10
RUDIN ZUCIYA
NA NANA DISO
Wattpad:NEIRNAHDISO
PAGE 12
______
Small lips dinta yak'urawa ido he wish he can kiss wannan lips din dak'eta daukar Idanunsa a rayuwarsa yanason macce mai tsafta da gayu wacce take kula da kanta gurin gyara, look at this fresh lips kana ganinsu kasan sunashan gyara, likewise wasu matan da zakaga duk lebensu ya bushi wasu har ma ya tsage wasu har dan jini yake fitarwa,that's why baya damuwa da wata soyayya dan indai macce danshi zata gyara jik'inta tabbas ba mai tsafta bace ba. " My handsome naji kayi shiru, anyway am Ayrah husain am just 22 years old muna zaune a London me and my dad and we are from Nigeria aiki yakawo dad dina nan, what about you?" Ahmad da hank'alin sa duk yatafi k'an Ayrah hatta maganar datakeyi sai yabaka sha'awa saboda tanayi ne cik'in kamun kai da yanga, and that's abunda ke jan hank'alin sa, kawai yaji shima he want to tell her about him, kauda kansa yayi a karo nabiyu yace " Am Ahmad from Nigeria " muryarta ya tsinkayo tace "woow kace kasarmu daya?" Murmushi yayi yana bin bak'in ta da k'allo tsigar jik'insa ce tafara mimmikewa hakan yasashi saurin kauda kansa a karo na biyu, indai yacigaba da zama a kusa da Ayrah to tabbas zazzabinsa zai tashi, hakan yasashi mikewa yafara hada takaddunsa, itama tashi tayi ta mik'o mai hannu tace " can I be your friend?" Jiyowa yayi yace " friend? How can you be my friend bayan I don't know you."Murmushi Ayrsh tayi takara matsowa daf dashi tanajin numfashin da yaja, " please my cute !" Wani narkakken kallo yayi mata sannan yace " lok'acin is over so bye bye." " saurin biyoshi tayi tace then help me with your number pls my handsome, kamar bazai karbi wayar yarubuta mata ba sai kuma ya karba sai da yagama rubuta mata ya mik'a mata yayi saurin fita. Wani shu'umin murmushi Ayrah tafito daga class din inda kawayenta suke ta nufa daya daga cikin aminan nata ne tace yaya yakulaki?" " Ba dolensa ba, kinga yadda yake k'allona ai ina tabbatar miki ya mutar mun wallahi, lok'aci daya zan siye zuciyarsa." " Yanzu Ayrah shima target zaki hada mana?" " No kawata wannan mijin aure ne in aureshi in cikaba da abunda nakeyi." " But fa wannan bahaushe ne ayrah ba kamar arnan da kika saba aura baniba?" " Sunansa Ahmad daga yadda yakemin kallo nasan lok'aci daya zai mutu akai na sannan zan mallakeshi hatta iyayensa sai ya gagareshi kulawa in cinye dukiyar sannan ya sallameni, ai ba sonsa nak'eyi ba danAllah kyansa kawai da kudinsa zanci." Ihu suka saka kawayen nata.
Ahmad kuwa tunda yakarasa gida wanka kwai yayi sannan ya dakko system dinsa yacigaba da karasa aikinsa,Ali da mukhtar ne sakashigo cik'in gidn nasu suna shiga babban palour sukga Ahmad sai faman aiki yakeyi da system Ali ne yace " Abok'ina zamuyi missing dinka, karatu yazo karshe komawa zakayi gida ko." " Ahmad ne yace I don't think so, inaso nayi har master tukunna.." Bai karasa ba wayar Ali ta hau ringing dagawa yayi ya kara a kunnen can sukaji yace " Wai me isa kafiya damune tsoho? Banida kudi nacemaka ! Sannan ya kashe wayar nan ya dubi mukhtar yace wai ni kadai ne ake damu a gida da abada kudi?" Ahmad yace " munada yawa ai basu san zafin neman da muke ba amma kullum cik'in yimana lissafin kudi suke" Nan suka kwashe da dariya bashiri kuma hira ta barke tsakanin su .
*********
Yau da wurwuri inna ta shirya zataje taron bik'in 'yar makociyar su da akeyi, malam dake fama da jiki yabata dariya biyar yace sai tabasu Allah yasanya alkhairi, tana isa gidan bikin sai tazama abun nunawa sai gulmarta akeyi daga karshe ma uwar bikin tace " kaga uwar karuwa surayya dai bariki tayi dadi ko waiwayonku batayi." Sosai kalmar tayiwa inna zafi acik'in ranta amma batace k'omai ba tace Allah ya shirya mana zuri'a." Wasu daga gefe suka kwashe da dariya suna nunata da hannu, ai gaskiya iyayen yarinyar ma sunyi hak'uri da har zuciyarsu bata buga ba bayan guduwar diyar tasu." " To banda abunku ba gara data gudu ba ta zauna a nan ta dinga lallata mana yara tana koya musu." Inna dataga cin mutuncin yanaso yafi k'arfin ta sai ta Mike tafita daga cik'in mutanen amma har cikin soro ci mata mutunci akeyi.
Shigowar kausar kenan daga makaranta ta nufi dak'in mahaifin nata zama tayi kusa dashi tana fad'in " malam sannu da jiki" 'yar albarka har kun tashi?" To malam ai yau guda biyu kadai mukayi gobene zamuyi uku" " To Allah yataimaka kafin ku gama ma zan biyamiki neco din itama." "Kasan malam karatu zanyi inshaaAllah so nake nazama lauya" " Kausar ina laifin aure? Kinsan dai banida karfin dawainiyar jami'a" dariya tayi sosai tace malam kamanta duk shekara ana daukar k'aratun dalibai a makarantar mu" " Kausar ai gomnati ce makarantarki ba lallai su baki ba duk irin k'okarin ki kinga surayya tanada k'okari sosai amma basu taba bata ba," " To malam ka manta ita yaya private kasata nifa gomnati nakeyi kuma inshaaAllah zan samu ko bansamu ba zanyi k'okari in dawo da sana'ar awarata." " Allah yadafamiki kausar ya kulamin dake da mutuncin ki" Ameen malam bari nazubo abinci, zonan kausar a hankali ta dawo ta zauna, " Banaso kina yawo babu hijjbi aduk inda kika shiga kada shigar banza tadinga rudarki kinji, ki kiyayye mutuncinki abun duniya indai ba tahanyar halal ba kada kibari ya burgeki, kinji yar albarka kinga ke kinada manyan gabbai babu wanda zaice baki shiga ashirin ba, ki kula da mutuncin kanki duk wanda zai nemiki d haram dan yabaki haram ba masoyi bani ba kinji yar albarka? Dan ina tunanin kuskuren danayi kenan da ace nayiwa yaruwarki wannan bayanin d haka bat faru ba, Amma hakan ma ina mata fatan shiriya. " InshaaAllahu malam zan kula tatashi the ta zubo abinci zata zauna tafara ci kenan kawu ibrahim yashigo hakan yasata matsawa kusa da malam ta zauna, har ya zauna kausar bata dago ta kalleshi ba bashi kadai ba har malam abun yabasu mamaki sosai, " Kausar ko abincin yayi dadi ne.." cikin danne zuciyarta tace " Au kawu kai ne sannu da zuwa ina can tunanin halin dan adam banji shigowar ka ba" sai da kawu ya zauna sannan yace " Diyata kidaina kasa damuwar surayya aranki ki maida hank'ali kiyi karatunki kinji " " Damuwa dole nayi kawu dan nasan tarbiyar da yaya surayya tasamu gurin iyayena idan ba babbar kaddara da sa hannun wani ba da mamaki rayuwarta tazama haka, nasan duk inda take wallahi hank'alin ba akwance yake ba nasan duk inda take bata son abunda takeyi." Malam ma dai shiru yayi yana sauraran kausar din amma kawu dayake babban munafuki ne sai cewa yayi " Aa kausar kada ki dorawa kowa laifi sai yayarki ita ta zabi rayuwar nan babu ruwa..." " To kawu koma dai menene Ai Allah baya bacci ko? Komai nisan dare ai gari zai waye." Sosai kawu yashiga tunani anya yarinyar nan kausar ba aljana bace ba ? Daga can kuma takaraji yace " Da malam nayi shawara ne ak'an kausar ko zata koma can gurina da zama saboda can kaga da sumayya ko?" " haba kawu kai dakake masoyin malam ai baka dauke masa niba bayan ni daya yake gani yaji dadi a'a babu inda zanje wallahi iyayena nada rai ina kusa dasu dan haka kadaina maganar nan ma inje inyi me agidanka bayan lantana duk duniya ni ta tsana." Murmushi yayi sannan yace " MashaaAllah daman nagwada tunaninki ne ashe dai da alamun kinfara hank'ali." Shiru tayi batace komai ba har inna tashigo tana kuka wanda hakan yasa hank'alin su gaba daya yakoma kanta, kausar ce ta karasa kusa da'ita tace innata kidaina kuka fa abunda mutane sukeci miki Allah baya bacci ai darajar fiyayyen halitta wanda yashafa mana wannan bak'in tabon shima sai an shafawa zuri'arsa." Kawu da yayi shiru yana sauraro lafazin kausar."
***********
Umar dake zaune kusa da baba amsa kiran da yayi masa, wayarsa ce tayi ringing hakan yasashi dagawa yace " Afwan Ahmad bana kusa ne" " Wai babu mai zuwa graduation dinane? " " Ahmad gaskiya babu dan kasan bamuda kud'in zuwa nan garin" haba Umaru duk uban kudin danake turomuku uban menene kukayi dashi???