17
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
17
Yau Zaytunah tana tashi daga office gidansu ta wuce saboda mommy da ta buk'aci ta zo. Tana zuwa ta samu Anty Hafsa matar k'anin Babansu tareda mommy.
Bayan sun gaisa mommy ke ce mata dama masu kai kayan lefene ake so a had'a da ita idan Sajid ya barta.
Zaytunah ta d'an yatsina fuska " haba mommy Dan Allah, Ni gaskiya a nemi masu zuwa bani da lokaci"
Mommy ta rik'e baki " lallai Zaytunah, yanzu ko kara baza kiyi ba, Kai tsaye kice baza ki je ba"
Anty Hafsa tace " lah mommy ki barta, ai tayi min k'ok'ari ma, ita ta taimakamin wajen had'a kayan, ga walimar da zan shirya ma, ita ce me had'a komai"
"Ki dena biyewa Zaytunah, yanzu tsabar rashin kunya lefen Uncle d'in nata shine baza ta je ba"
Zaytunah ta zaro ido dan ita Anty Hafsa ce mata tayi k'aninta ne zai yi aure ta taimaka mata wajen had'a lefe da walimar da zata had'a masa a gidanta.
" Mommy I don't get you, wani irin lefen Uncle Adam?, Na ga Anty Hafsa tana da 'yanwanta mata, su taimaka mata mana miye nawa aciki"
Tsaki mommy taja tace " ki ji min shirme, cikin 'yan uwan Hafsa da ke wa ya fi kusa da wannan aure?"
Zaytunah tayi shiru tana yiwa Anty Hafsa kallon tuhuma.
Mommy cikin fad'a tace " maza ki kira Sajid ki sanar da shi jibi za a kai lefen Uncle d'inki"
"Mommy ba dai Uncle Adam ne zai yi aure ba ko?"
"Shirmemmiya kawai, duk zancen da ake yi tun kwanaki kinaso kice baki sani ba kenan?"
" OMG!" Zaytunah ta tashi a firgice tana kallon Anty Hafsa
" Please tell me it's a lie"
Anty Hafsa ta sunkuyar da kai tace "nasan na gaya miki gaskiya ba za ki taimaka min ba"
Cikin kid'ima Zaytunah ta zaro ido tace "aure! Uncle Adam zai k'ara aure! @ 52yrs, uban mi yake nema yanzu a jikin mace. Kai gaskiya asiri aka masa, the girl is a bloody gold digger"
Ba Anty Hafsa ba hatta mommy kallon mamaki suke mata kamar taji wani bak'on al'amari.
Cike da takaici mommy tace " kina da hankali kuwa, ko kuwa zaman turai ne ya saki wannan banzar tunani"
" Mommy seriously, miye Uncle zai yi da mace yanzu after 22yrs of marriage, Anty Hafsa is still in her prime @44yrs fah and they've being blessed with 5kids mi yake nema kuma?, Ai daga jin wannan lamari kinsan aikin asirine"
Mommy da takaici ya cikata tace " to bari kiji yarinyar da zai aura budurwace 'yar 26yrs, this year ta gama service ɗinta, kuma Hafsa da kike gani ita ta had'a auren, da kudinta ma ta had'a masa lefe"
Zaytunah ta fara salati da sallallami dan ita kan wannan abu ya d'aure mata kai.
"Wallahi da nasan kayan lefen nan a kishiya za ki yiwa da ban taimaka miki ba, kar dai kice min honeymoon suite dana sa aka booking a Amsterdam da Paris na Uncle Adam ne da amaryar da zai aura?"
"Kanki akeji" mommy tace da ita.
Zaytunah k'wak'walwarta ya d'au zafi da jin wannan zance, ganin sun yi banza da ita suna tattaunawa tsakaninsu yasa ta d'au jakarta sai gidan Sady.
Ta zayyane mata wai k'anin Babansu zai yi aure kuma budurwa zai aura.
Sady ta kur'bi juice tace " Ni ai na d'auka kin sani ai, saisa ban miki maganarba, tunda kunfi kusa amma ni banyi mamaki ba"
Zaytunah ta harareta "kinaso kice min it's a normal thing kenan?"
"Sosai ma, indai a Nigeria ne za ki ga fiye da haka ma, ke dai kawai dan Sajid tashin turai ne, amma da anan ya tashi k'ila da yanzu kina da kishiyoyi biyu ko uku"
" A'uzubillahi, Sady ki dena wannan maganar zuciyata zata buga"
Sady tayi murmushin jin dad'i tace "yanzuma a hakan bai makara ba, ba dai ya dawo Nigeria da zama ba, ki shirya zuwan kishiya kawai"
Zaytunah ta k'walla k'ara " never, wallahi never, My Sajid daban yake ba shi da lokacin wata mace sai nawa, duk wadda tayi k'ok'arin tunkaran sa ma mutuwa take kirawa kanta"
Sady ta kwashe da dariya " kina ban mamaki Zaytunah, wai nufinki Sajid yafi k'arfin k'ara aure ko mene?"
Jikin Zaytunah har rawa yakeyi " he is mine, and will always be mine, ki dena tsoratar dani Dan Allah, wallahi har naji na tsani dawowarmu Nigeria"
Sady tace " yi hak'uri babe, amma be very careful, kinada miji irin Sajid, kyau, kud'i, ilimi, wayewa, above all he's man enough for every woman ai kawai ki shirya, wallahi ko budurwa 'yar 15yrs zata iya aurenshi, ai yanzu a man is never old matuk'ar yanada kud'i"
Hawaye ya gangarowa Zaytunah kanta har wani sarawa yake yi. Ba ko sallama ta bar gidan Sady.
Sady ta kwashe da dariya " Zaytunah kenan, wallahi sai na rabaki da Sajid kota halin k'ak'ane na mallakeshi".......
Zaytunah na isa gida zazza'bi ya rufeta, kota kan yaran bata bi ba, taje ta kwanta ko zata sami nitsuwa.
*Wacece Sady?*
Sadiya Yakubu shine sunanta, mahaifiyarta Suwaiba 'yar Kafanchan ce sai dai kasuwanci ya kawo iyayenta Suleja, tun tana yarinya Allah yayita da kwad'ayi wannan hali shi ya bita har ta girma, akwai wani Alhaji Isa da yake zuwa wajen mahaifiyarsa duk karshen wata, kasancewar suna mak'otaka da gidan yasa duk sanda yazo suma suna samun alkhairi daga wajensa. a Abuja yake aiki yana da mata da yara hud'u. Suwaiba ta k'wallafa rai a wannan bawan Allah sai dai babu hali dan ya mata nisa.
Mahaifinta ya aurar da ita wa wani dan abokinshi msi suna Yakubu, duk da bata sonshi amma haka ta hak'ura dan ba yadda ta iya, sai dai ba Suleja suke zaune da mijinta ba. Yakubu yana koyarwa a wata makarantar primary a Zaria. Suwaiba ko kad'an bata da godiyar Allah duk yadda yakubu zai kyautata mata bata gani, musamman data fara had'uwa da k'awayen da mazajensu suke da hali. Cikin haka ta haifi Sadiya amma har lokacin zamansu sai a hankali.
Ana haka ta had'u da wata Hajiya Altine, tazo gidan mak'ociyar Suwaiba kitso suka had'u, nan ana tad'i ta ga tasu tazo d'aya ta bata address d'in gidanta dan zumunci.
Ranar da Suwaiba taje gidan Haj. Altine taga ikon Allah, yadda taga mijinta na yiwa Hajiyar biyayya kamar wani wawa shine ma ya kawo wa Suwaiba ruwan da zata sha.
A hankali fa k'awance ta shiga tsakaninsu daga nan Suwaiba ta gane asiri Hajiyar ta yiwa mijin yake binta sumsum haka. Nan fa Suwaiba ta nemi taimakon Hajiya kan kudirinta data jima tana buri.
Aiki boka ya mata sosai bayan tasa Yakubu ya saketa, tana gama idda Alhaji Isa ya fito nemanta, iyayenta sunyi mamakin hakan amma haka dai aka yi auren ba mai iya yin jayayya.
Gidan Alhaji Isa Suwaiba taci karenta ba babbaka, ya koma yana walak'anta matarsa da yaransa. 'Ya mace ta haifawa Alhaji Isa wadda ta ci sunan Fatima, Fatima nada shekara uku Suwaiba ta kashe aurenta da Alhaji Isa bayan ta wawuri dukiyarsa mai yawa, ta auri wani Alhaji a Lagos ana ce masa Alhaji Maidala.
A tak'aice Suwaiba ta koma irin matan nan da basu da imani da Allah, komai nasu boka ne, kai kace ko tari zasuyi sai sun tambayi boka tsabar yadda sukayi imani dashi.
Da wayon Sadiya tasan mahaifiyarta aurenta goma sha biyu, Kuma duk masu kud'i take aure, Sadiya ce kad'ai ta taso gaban mahaifiyarta dan Fatima na wajen mahaifinta, tunda ta rabu dashi da k'yar ya farfad'o daga karayar arzik'i data sashi, matarsa da yaransa babu wanda yake kyamatar Fatima saboda Maryam matar shi salihar macece data yarda da k'addara ta d'auka rabon Fatima yasa Alhaji Isa ya auri Suwaiba dan haka tsakani da Allah ta raini Fatima.
Tasowa gidan kud'i da kuma rashin kulawa daga mahaifiyarta, yasa Sadiya sangarcewa, bata k'ara lalacewa ba ma sai data tafi k'asar waje karatu. Tunda Sadiya ta rasa budurcinta wajen wani d'an ajinsu bature yasa ta gane ko ita d'in wacece.
Sadiya irin harijan matan nan ne da basa gajiya, Maimakon tayi karatu kawai ta koma sha'aninta acan.
Suwaiba ce ta had'ata aure da 'Dahiru d'an wani Minister. Da shike da asiri aka yi komai 'Dahiru ya koma solo'biyo a hannun Sady. Ganin fa Dahiru ba sa'ar karawanta bane ta fara neme nemen maza (wa'iyazu illah) . Daga k'arshe tace wa Suwaiba ta gaji da Dahiru baya iya biya mata buk'atarta aka raba auren.
Suwaiba aurenta na goma sha uku ta auri wani Alhaji mutumin Edo amma a Abuja yake zama, shima d'in saida tasa ya saki matarsa sannan ya aureta, abinda bata saniba shine k'anwar kakar matarsa mayya ce, bayan matar ta koma gida, mayu suka sata a gaba, nan ta fara ciwo, ga wasu cikin asirin datayi a baya sun karye abu yazo ya kacame mata, Suwaiba ta fara kumbura tana wari ga wasu tsutsotsi na fita a gabanta duk asibitin da aka kaita sai suk'i kar'banta. K'arshe duk ma'aikatan gidan da take saboda tuni Alhajin data aura ya saketa suka gudu suka barta, cikin wannan hali Sady ta dawo ta sami mahaifiyarta, ba k'aramin tsorata tayi da ganinta haka ba, ta riga tasan mahaifiyarta na bin bokaye. Itama d'in da k'yar ta kwana da ita washe gari ta tafi Suleja sanar da kakanninta wanda suma tun lokacin da Suwaiba ta fita daga gidan Alhaji Isa suka fita sha'aninta, da k'yar wani k'anin Suwaiba ya biyo Sady suka zo Abuja saboda kowa yak'i zuwa, suna zuwa suka tarar ta mutu gaba d'aya gawanta ba kyan gani, tsutsotsi suna cin jikinta ta ko ina, ganin gawar mahaifiyarta yasa Sady sumewa sai da tayi kwana uku bata gane kanta ba. Tun daga wannan lokaci Sady ke tsoron bin bokaye dama harka da masu yinta. Ita dai ka barta da kissa da makirci amma sam tana tsoron shige shigen bin bokaye ko malamai.
Sady da kud'in mahaifiyarta data samu ta fara business dan kam karatu tak'iyi ko degree bata had'a ba ta watsar. Ita d'inma sau uku tana sake aure amma bata zama, duk inda tayi aure saita renawa mijin duk k'ok'arinsa sai taga ya gaza mata. Aurenta na k'arshene ma ta auri wani saurayi shima d'in kwad'ayi yasa ya aureta, KB ne kad'ai mijin data d'an d'aukeshi dama dama, dan dashi kad'ai ta zauna har shekara biyu, sai dai KB biye mata ya dingayi har ya samu ya wawuce mata kud'ad'e dayawa da wasu kadarorinta ya gudu. Dama ci rani ya kawo KB Abuja batasan asalinsa ba dan koda sukayi aurenma batasan kowa nashi ba. Hakan ya mata ciwo sosai ta hak'ura da aure take shek'a ayarta, idan ta kawo namiji taji dad'insa zasu kwana biyu kafin ta neme wani idan kuwa bai mataba daga d'aya ba ƙ'ari.
Fatima da tarbiyar Matar Babanta Hajiya Maryam ta zama mace ta gari, karatun likitanci tayi ta auri wani lecturer a BUK suna zamansu lafiya da yaransu uku. Saita shekara bata saka yayarta Sadiya a ido ba, duk da idan sun had'unma tsakaninta da ita nasiha amma sam bata ji.
Sady ba ruwanta da kowa hatta mahaifinta wanda yayi aure harda yara biyar yanzu bata damu dashi ba rabon data ganshima tun wani lokaci da akayi auren k'anwarta a Kafanchan taje bikin kusan shekara uku da suka wuce kenan......
Sady ta had'u da Zaytunah a wani shago a Dubai ita taje kasuwancinta, Zaytunah kuma sunje had'a kayan lefen wani k'aninta Habib da zai yi aure, kasancewa hotel d'aya suka kama yasa koda suka bar shagon tare suka tafi, bayan kowa ya gama abinda yazo yi da zasu tafi suka exchanging contact inda Zaytunah ta gayyaci Sady bikin tunda itama tace a Abuja take.
A lokacin biki suka sake had'uwa nan suka sake sabawa, ganin Zaytunah irin matan nan ne da abu d'aya zaka tambayesu amma sai sun gaya maka goma yasa ta sake manne mata dan tanason irin mata haka.
Sanda Zaytunah zata koma USA ta bata address ɗinta tace duk sanda zatazo ta nemeta, haka suka rabu. D'an sati d'aya da suka yi tare Sady taji labarin Sajid yafi sau irge, domin abu kad'an My Sajid ko my one, ana kawo labarin miji yanzu Zaytunah zata fara yabon mijinta tana fad'in how perfect yake.
Sady taga hoton Sajid kuma ta yadda shi d'in kyakykyawan gaske ne kuma ya amsa sunan namiji sai dai ita ba damuwarta bane saboda duk muninka indai zaka biya mata buk'atarta yadda takeso to fah zaku dad'e tare.
Sady nada code nata " even the ugliest man can be the best man in bed" saisa bata damu da kyau ba.
Abinda yasa Sady ta fara bibiyar Sajid shine watarana kamar yadda ta alk'warta duk sanda ta shigo America zata nemi Zaytunah hakan akayi. Bayan ta gama abinda ya kawota ta wuce New York lokacin Sajid ya tafi LA wani aiki. A gidan Zaytunah ta kwana, lokacin Zaytunah nada tsohon cikin Azra.
Suna cikin tad'i Zaytunah ke tambayarta maganar aure, take ce mata ai ita har yanzun batayi sa'ar miji ba,
" Ban ganeba, kinada kud'inki balle kud'i ya had'aku fad'a mi zai had'aku, ko kinada kishiya ne?"
" Ko d'aya Zaytunah, the thing is...." Sai tayi shiru
" Haba babe ki gayamin mana yanzu tsakaninmu har akwai wani sirri?"
Sady ta kalli Zaytunah data cika bakinta da strawberry tanaci tace " Zaytunah nayi aure sau hud'u amma banyi daceba, dukkansu sun gaza mini, basa iya biyamin buk'atata yadda ya kamata"
Zaytunah ta yatsina fuska toh bazakiyi manage ba su dinga miki wasa harki gamsu koda ba'ayi sex ba"
Sady ta rik'e kai " bazaki gane ba babe, daga mai 3inches sai mai 4 the last one nema nashi yakai 7inches fah, kwata kwata basa wuce 5-10mins dani, me k'ok'arin nema 15 mins"
Zaytunah ta kwashe da dariya " 3inches fah kekace Sady"
"Iyi"
"Barin gaya miki wani sirri, My Sajid has 12inches, kuma zai iya kaiwa 45mins even 1 hr depending yadda kika kunnoshi"
Sady ta zaro ido baki na rawa tace " 12inches fah kikace, Dan Allah da gaske?"
Zaytunah da bata d'auki maganar da takeyi a bakin komai ba (wa iyazubillahi da fad'in sirrin miji) tace " wallahi na gaya miki 12inches long fah, and it's thick and........kai! shiyasa idan ina cewa my Sajid is perfect kuke ga kamar k'arya nakeyi, wallahi ta ko ina mijina ya had'u k'arshene. In dai ta ɓangaren sex ne Wallahi sai kin gaji dan girmansa ma wani lokacin har ciwo yake ji min"
Wannan furuci na Zaytunah shiya sa Sady k'wallafa rai akan Sajid musamman data sameshi sau d'aya taga zahirin abinda Zaytunah ke fad'i (koya hakan ta faru?) har yau tana farautar Sajid sai dai bata kuma samu ba.
Wannan kenan.
...........BAUCHI...........
Yau kwana takwas kenan da rasuwar Waheeda ko ince aka kawo musu gawar Waheeda, halin da iyalen Dr Sulaiman suka shiga a wannan kwanaki ba a magana, Laure ko sau d'aya bata lek'o ba, tunda ta bar asibiti ranar da aka kawo Abba ba su sake sakata a ido ba. Shamsiyya ranar da akayi ukun Waheeda tazo ta yini sannan ta tafi, Mal Adamu ya tambayeta inda Laure take, ta ce bata sani ba ta dai kar'bi aron kud'i a wajenta.
.......Idan kaga Nazira a wannan lokaci sai ka d'auka tayi watanni tana jinya ne. Idonta taf da hawaye take rok'on kakan nata, akan ya bari ta shigar da k'aran Alhaji Kadi amma yak'i.
"Baba wallahi, Alhaji Kadi shi ya kashe Waheeda, dole a shigar da k'ara, shiya kasheta, ya kashe 'yar data haifa"
A hankali ya fara mata bayani " Nazira, adaidai wannan lokaci ba abinda yafi dacewa dake face kula da mahaifinku, abinda ya faru yafi kowa shiga cikin tashin hankali, da wanne zai ji, Cin amanar Laure ko rasuwar Waheeda. Tun da akayi jana'izar Waheeda kin sake jin Abbanku yayi magana?
Ikon Allah ne kawai da kuma nisan kwana amma da tuni sai dai wani bashi ba, idan har inada iko da ke Nazira to ki bar zancen shigar da k'ara, ki rungumi k'addara ki tuba wa Allah sannan ki kula da mahaifinku, abinda ya faru da waheeda k'addarantane babu halin tsallakewa. Shigar da k'ara tamkar kina ja da hukuncin Ubangiji ne, sannan ki tonawa mahaifinki asiri sannan a k'arshe babu biyan buk'ata. A duniyar nan shari'a kanada hujjoji ma akan juya su balle baka da hujja, musamman shari'a da Maikud'i. Kiyi hak'uri Allah Ubangiji ya yafe mana gaba d'aya".
Kwana goma sha biyu, da rasuwan gidan gaba d'aya an watse, Baba ma yau ya tafi . Nazira,Arif da Tijjani autan Baba kenan kad'ai ya rage. Ba laifi yanzu Abba yana d'an magana kad'an kad'an.
Yau gyara gidan tayi gaba d'aya tareda su Arif d'in ta shiryawa Abba favorite food ɗinsa, sai da take gyara ne ta lek'a d'akin Laure nan taga wayam an kwashe duk wani kaya mai amfani aciki, batayi mamaki ba, dan tasan kila lokacin da suke asibiti Lauren tazo ta kwashe kayan.
Ba laifi yaci abincin kad'an ba kamar da ba. Sai data tattara komai ta tsugunna har k'asa ta fara bashi hak'uri, kuka ne ya ku'buce musu gaba d'aya, musamman Abbansu wanda tamkar yanzu yake ganin gawar Aisha da kuma Waheeda, wai ace duka sanadin Laure. Yasan tun tasowarsa agidan Malam Adamu, babu jituwa tsakanin Aisha da Laure amma bai yi tunanin har hakan zai kaiga kisan ba, Bata tsaya anan ba ta 'bata masa tarbiyan yaransa. Gaskiya mutum da kake gani mugu ne sai dai Allah yasa mu fi k'arfin zuciyarmu kawai.
Da k'yar ya samu ya tsaida kukan nashi ya rungumi 'yarsa yana sa mata albarka yana k'ara yi mata addu'ar shiriya....
***
.....Laure tunda tabar asibiti ta je gida ta tattare kayan ta masu kyau, ta kai ajiya, wajen bokanta na baya ta fara nema aka ce mata ya jima da barin wajen, nanfa ta fara neman wani bokan wanda zai mata aikin da takeso, ta riga tasan yadda asirinta ya tonu Sulaiman bazai ta'ba zama da ita ba, amma tayi imani da k'arfin asiri dole ya manta da komai ya zauna da ita. Wani hatsabibin boka da aka mata kwatance acan kudu ta wajajen Enugu, nan ta nufa, sai dai kafin su kai 'yan fashi suka tare su a hanyar Makurdi kud'inta da kud'in data k'ar'ba a wajen Shamsiyya kusan dubu d'ari da hamsin 'yan fashi suka wawure mata, motarsu ta tashi bayan 'yan fashin sun tafi tayi hatsari da wata babbar mota, tana cikin wad'anda suka jigata sosai, aka kaisu wani asibiti a jahar Benue.
Kasancewa ba a samu wayartaba, yasa ba wanda aka nema ana jira ta wartsake dan ko magana batayi ta fad'i garin da take da kuma 'yan uwanta.
....... LAGOS.........
Tunda suke meeting Zaytunah ke faman kiranshi, da farko ya tsorata ya kirata ko lafiya kawai ta fashe mai da kuka ganin irin sakalcin data sabane yace zai kirata da dare bayan ya gama aikin daya keyi.
A gajiye ya dawo gidan, dama ba wai ya gama warkewa bane, gashi yaje wajaje dayawa asibiti, prison, police station office d'in barrister Idris.
K'arfe tara da rabi ya k'wank'wasa k'ofar gidan, ya riga ya gayawa Daddyn Timothy kan bazai dawo da wuri ba. Wata yarinya ce baza ta fi 11 ko 12yrs ba ta bud'e k'ofar da alama itace Ronke da Ziha ke ce masa sunyi tafiya da mamanta. Har k'asa Ronke ta tsugunna ta gaidashi sannan ta kar'bi jakarshi ta wuce dashi guest room, zama yayi suka gaisa da Daddy da kuma Mama dake gefen Daddyn, abin mamaki Timothy ya gani ya wani rungume Ziha alamar dai kaman bata da lafiya dan yadda ta langwa'be kamar marar lafiyan ne. Tim ya gaisheshi amma Ziha batayi magana ba ko d'agowa bata yi ba.
Tambayar Daddy yayi ko lafiya ya amsa masa da ba komai, ganin dai basuda niyyar magana yasashi wucewa cikin d'aki amma zuciyarsa na wasuwasin miyake faruwa.
Da k'yar ya samu ya cire kayanshi saboda da safe ma Timothy ne ya taimaka masa wajen sawa amma yanzu yasan ba hali, band'aki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fito ya saka kayan bacci.
Laptop ɗinsa ya d'auko ya zauna kan gado yana danne danne.
Yana aiki amma yana jiyo maganganunsu daga falo duk da ba jin yaren yake yiba amma yana tunanin akwai abinda ya samu Ziha yau.
Wayar Zaytunah ya katseshi, yana d'aukan kiran as usual complain ne, miyasa bai kirataba tun tuni tanata jiran kiranshi.
" Zaity kin san dai komin dare zan kiraki ko, I'm still working"
Zaytunah cikin murya k'asa k'asa ta fara masa kirari.
"Mijina na kaina, my one and only Sajid, Uban 'ya'yana, masoyina, abin k'aunata, mamallakin zuciyata angon Zaytunah ita kad'ai"
Murmushi yayi dan yasan halin kayansa daga ta fara irin wannan kirarin to tana neman wani abu a wajensa ne. " Ya aka yi matar Sajid" ya amsa mata
Wani sanyi ya ratsata dan bak'aramin dad'in sunan taji ba, ya jima bai kirata da hakaba, gashi yau da take cikin tashin hankali ya kirata da sunan da takeso.
Gulmar abinda Uncle Adam yake shirinyi ta fad'a masa sai dai da mamakinta taga bai damuba hasalima yace ai ra'ayinsa ne kuma ai har yanzu yanada k'arfin da zai zauna da budurwar mace. Jikinta yai sanyi tsoro ya cikata, karfa Sajid ma zuwansu Nigeria ya sauya masa tunani, tun da gashi uncle Adam ma da take ganinshi shiru shiru, dan duk cikin familyn Daddynta babu mai sanyi irinshi amma wai har zai sake aure @52yrs.
" My Sajid nasan baka da ra'ayin mata biyu amma inaso kamin alkawarin ni d'ayace har abada"
Tana gama maganar Naziha ta shigo d'akin d'auke da tray da kayan tea kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa, hijab tasa navy blue mai hannu ya rufe mata gwiwa kad'an, sai kuma yana ganin wandon pyjamas ɗinta, idonta ya kumbura sosai alamar ta sha kuka. Ganin zata fice daga d'akin yasa shi kiran sunanta "Ziha" ta juyo ta kalleshi ya mata nuni da hannu alamar tazo ta zauna, ba musu ta dawo ta zauna k'asa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
Kamar d'aukewan wutan NEPA numfashin Zaytunah ya tsaya lokacin da taji yace " Ziha"
Da k'yar ta tattaro nitsuwarta tace " my Sajid Ziha kuma? Wacece Ziha? Kana tareda mace k'arfe goma na dare har da minti biyar...."
Saurin kat'seta yayi dan yasan yanzun zata fara masa kuka, gashi tsayawa yi mata bayani yanzu 'bata lokaci ne, yasan kayansa " Zaity, wani code ne aka turomin yanzu shine zan rubuta"
Naziha tayi saurin d'ago ido ta kalleshi koda batasan mi ake cewa ba amma yanayin maganar Uncle Sajid ya nuna k'arya yayi"
Suna had'a ido tayi saurin sunkuyar da kai, shi kuwa yaji ba dad'i dan yana tunanin ta gane abinda yace.
Zaytunah dai hankalinta bai kwantaba amma ta dake tace " my one kamin alk'awarin Dan Allah"
" Alk'awarin mene?"
" Daga ni d'aya ba K'ari"
"Haba Zaity must I promise you that? Kin riga kinsan halina kin san ba ra'ayina bane auren mata biyu" ya k'arasa maganar a hankali wanda ko Ziha bata ji mai yace ba.
Cikin shagwa'ba Zaytunah tace " na sani amma ni dai kamin alk'awarin saboda hankalina ya kwanta"
Yasan idan bai mataba ba barinshi zatayiba gashi ya tsaida Ziha yana son tambayanta miya sameta, kawai yace " I promise"
Zaytunah kan gadon da take ta buga wani tsalle tana ihun murna, sai yanzu hankalinta ya kwanta tasan Sajid d'inta mutum ne mai rik'e alkawari. Yanzu tanada 100% assurance cewa Sajid natane ita d'aya babu kishiya.
Ganin zata cikashi da ihu yace zai kirata da safe yana aikine....
Kallon Naziha data takure guri guda yayi yace ta taso ta zo ta zauna kan gado. Da farko tak'i sai daya sake maimaitawa tazo ta zauna amma idonta na kallon k'asa.
"Miya sameki kikayi kuka?"