ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 09
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️09*
Sai around 8am na safe ta baro asibitin. dayake sai da Suka tsaya Sukayi Round din safe, Cike da Farinciki ma'u sukayi sallama da Sister Bahijjah Banki ta fara biyawa ta cire kudi daganan kasuwa ta Wuce Ta siyanma Su Fati tsaraba ,ko Bauchin bata kira ba so take ta basu Suprise,Tana Adaidaita zata koma gida ta kira Aisha awaya tana Fad'amata Yanzu zata tafi Bauchi.
Bata Fuska Aisha tayi tana fad'in Asma'u bata kyauta mata ba,Da bata fadamata Tunda Wuri ba. data Shirya Sun Tafi tare Cike da Dariya Asma'u ke Fad'in kibarma wa mijin naki da kuma my Son..? cike da Shagwaba Aisha tace Su zauna Su kad'ai mana Rabin Raina,Jin haka yasa Asma'u yin dariya sanin wacece Aisha.
kafin suyi sallama sai da Aisha tayi ta jaddama Asma'u ta isar da gaisuwanta wajen Mama da su Hajiya.
Koda ta Shiga gidansu bata iske kowa atsakar gidan ba,Dakin su Baba lami ta leka suka gaisa.
Nan take sanar da ita yanzu zata tafi Bauchi baki Baba lami ta washe tana Fadin"Ehe yau ma'u sai kwananan dakin Mama ko.."Asma"u na dariya tace"Sosai ma Baba lami. bari naje na Shirya kada nayi dare ahanya ba,da dad'ewa zanyi ba Ranar Sunday zan dawo.."
Gyada kai Baba lami tayi tana Fadin"Gaskiya kamm hanzarta kada Rana tayi.."Kofar dakinta ta isa bayan tasa makulli ta bude.
ta Shiga da sallama tana kwabe hijabin gidan dake jikinta,Tiolet dinta ta Fad'a bata ma tsaya neman Ruwan zafi ba ta tara Ruwa afomfon dake Bayin ta Cikashi da Ruwa kafin ta Tube tayi wanka agurguje ta Fito Fuskarta kadai in ka kallah zaka san Asma'u na cikin Farinciki.
Good 1hr Yabata ta kamallah Duka Shirye Shiryenta,Ta Zuba kayanta akaramar akwatinta Kala Uku. Sai kayan barcinta da Dan Abunda zata bukata ita kuma ta Shirya Cikin wata Doguwar Rigar Atamfa wanda Ammi ta dinka musu sanda Aisha ta Haihuwa mai kalan orange da Brown
Mayafinta ta sanya brown babba Fuskarta ba wani makeup dama ita ba ma'abociyar kwalliya bace.
Jakar hannu ta Dauka baka ta kuma sanya Wani Flat Shoe dinta baki,Sai da ta Kauda komai ta kashe Wutar dakin kana ta Jawo karamar Trolley dinta da hannun hagu.hannun damarta kuwa tana dauke da karamar Jakarta da kuma wayarta ta Fito Fuskarta na bayyanar da Annuri.
Umma ce da Mama ke Tsarkan gidan,Umma ce ke kofar dakin Hajiya iya atsaye da alama suna mgana da ita ne ita kuma Mama ta coge akofar dakinta Tana kallon Umma kamar dai wata mgana ce ta had'asu.
cike da mamaki Suke bin Ma'u da kallo ganin ta Ijiye akwatin tana kulle Kofar dakinta da makulli. A Galala suke kallonta musamman ma Umma,don ita mama Sau da'ya ta kalleta ta kauda kai,ita ko Umma kallon Kurillah tabi Asma'un dashi ganinta yau Cikin walwalwarta.
Basu samu zarafin mgana ba Asma'u tagama kulle dakinta ta waigo tana Riko akwatinta gefe daya tana gyara zaman mayafin kanta. Hakoranta duka Suna waje take Fadin"Umma,Mama zan tafi Bauchi."
Mama ce tace!"Ayyah Allah ya kiyaye hanya.."Fuskarta bata Nuna me Zuciyarta ke Ciki ba.
Umma ko ido ta kwalalo tana fadn"Bauchi kuma..? Asma'u bata bi ta kanta ba tace"Eh. Anty amarya batanan ne.."?Bata samu amsa ba Hajiya iya Ta Fito daga dakinta tana Fadin"Waye nake jin ana zai Tafi Bauchi kuma...?Umma tace"Wai Asma'u gatanan ta Fito ma."
Kallonta Hajiya iya tayi Shekeke kafin tace"Bauchi kuma.. ? Toh da izinin wa zaki Tafi.?
Abba da Shigowarshi kenan yace"Da izinina Iya. Jiya take Sanar dani tana So taje akwai wanda ba lafiya ne,ba dadewa zatayi ba Ranar Lahadi zata dawo"
Yafad'a yana kallon Hajiya iya wacce ta wani mele baki tana Fadin"Sai ta dawo Tunda kai ka Daure mata gindin gantali Agari. Mutum bazai ma kanshi Fada ba, Sa'o'inshi da kannenshi Sun gama kammaluwa agidan Aure,Allah dai ya Sauwake Wlh""Tafad'a lokaci d'aya tana shigewarta d'akinta.
Mirmishin yake Asma'u ta saki aranta tana jin bazata bari Hajiya iya Ta bata mata Mood di:nta na Farinciki ba. Kallo Abba tayi tana Fadin"Abba zan Wuce bana son nayi dare ahanya.."Gyada kai yana Fadin"Gaskiya ne Ma'u Duk inda zakaje katafi ido na ganin ido. karb'i kiyi na mota,kinji dai yadda mukayi dake kidawo Ranar lahadi na barki ne Saboda kin Dade bakije ba.."
Girgiza kai tayi tana Fadin"Toh Abba,
ammh kabar kudinka ina da kud'in Mota."
Kallonta yayi yana Fadin"Karb'i mana," Jin haka yasa ta sa hannu bibbiyu ta karb'a tana mai godiya. Wucewa yayi yana Fadin"Allah ya kaiki lafiya ki gaida Habiban.."da Toh ta amsa kafin ta Dauki akwatinta ta kama hanyar Waje,saboda Su Baba lami basu nan Sun Tafi kasuwa hassatu ce kad'ai. kuma kamar Mama ta aiketa,Umma dake Binta da kallo haka kurum takejin gabanta na Faduwa ta rasa Dalili yanzu Asma'u kwarjini take mata Sosai.
Bata tafi ba sai da Ta Shiga wajen Ammi ta Mata sallama,ita kuma ta bada Sakon Fulawa da garin Danwake Akaima Mama. har kofar gida ta rako Asma'u ta mata Allah ya kiyaye,Tana Zuwa bakin Titi ta samu Adaidaita ta Shiga sai Tasha.
tana zuwa ta samu Motar Bauchi kai tsaye saura Mutun Hudu ta cika,Ansa Akwatinta abayan Mota kenan Aisha ta kirata awaya tana Tambayanta tana ina,tace tana Tasha yanzu zata Wuce,Tace ta dan Jira ga Fahad nan Zuwa zai kawo mata Sako zata kaima Su Mama. Mirmishi tayi Aranta tana yaba Kyan Hali irin na Uwa da yarta.
Minti Ashirin sai ga Fahad yazo Tashan Dambum Nama ne Dayawa anyi Raping dinshi Cikin wata Leda kafin ta sanyashi Cikin wani karamin Botiki kuma Bai barta haka ba Sai da ya bata 4k yace ta kara ma mota tasan ko tace bazata karba ba bata baki ne shiyasa ta karb'a tana mai Godiya. Suna wajen aka samun Cikon Mutum ukun Sai da Motarsu tatashi kana Fahad ya Shiga motarshi ya Juyo Zuwa gida.
Suna Fita daga garin Dutse Asma'u ta kalli agogon Fatan dake hannunta taga 11:06Am daidai mai da kanta tayi kan Littafin Azkar din dake hannunta tana karantawa cikin Ranta tana Fatan Allah ya kaisu lafiya.
Ammh yau da ta tuna sai kwanan Bauchi sai taji Farinciki yaki Barinta Allah na gani Duk sanda ta Shiga mota Zata Bauchi tana Tsintar kanta Cikin Farinciki ammh kuma wannan karon Sai Murnanta yafi na ko yaushe kodon Ta dade bata je ba ne oho
****
Wasila kuwa Tunda suka dawo daga Gidan boka take kwance Ad'aki Zuciyarta kamar zata buga Saboda bakinciki Data Tuna Cewa Boka yace sai Abdallah yaje Bauchi Zataji kamar Tayi Bindiga ita kad'ai.
Arayuwarta bata kaunar taga wani ya Rab'i Abdallah Saboda Son data kema Abdallah Wlh Zata iya kashe Rai Saboda Shi. Tun momcy na bata baki hartazo ta Fita batunta,Har Washegari Wasila Sukuku take Abunda ma ya sanyayamata Rai Suna waya da Abadallah ammh bai Nuna mata alamun Zaije Bauchi ba, Su kuma Su Jamila Sun Fad'amata Tun Safe yake Fita baya dawowa sai Tsakar dare Wani lokacin.
Ita kuma data Tambayeshi sai yace mata Wlh busy yake zama a office Saboda kwananan Akwai cases dayawa ne.
Toh Wasila dama tafi yarda Da Abdallah shiyasa ta watsar da Batunsu Jamila, ta yarda Dana Abdallah Shiko Tun safe in ya Fita zai biya wajen Polina su Sheke ayarsu a office din ma ba Sosai yake zama yana gidanta chan yake Raba dare. Dalilin dayasa yake Dawowa ma Saboda Su Jamila ne,ya Lura yaran Munafukai ne tsab zasuyi kaima Wasila lbri. in ko Wasila taji lbri baya kwana agida Sai ya Raina kanshi.
Itako Polina sai tayi ta Rib'antan shi da salo kala kala Sabida karya tafi dayace zai Tafi sai tafaramai kuka tana Makaleshi dakyar yake samun Damar tahowa itako Polina Duk burinta bai wuce ta Raba Abdallah da matarsa Wasila ba,Domin Ta lura yana Sonta Sosai komai kaji yace My Wasi ko Noory. ko ita baya Sonta haka Shine ta tattara Duka burinta na sai ta Rabasu Domin itama Abdallah ita kad'ai takeson Mallakanshi Saboda Shi ta daina bariki.
Saboda maye mata gurbin iyaye da yan'uwa..shi amatsayin Zaratan maza goma ne a wajenta. Ta yardan ma kanta Abdallah 1 in million ne.
*****
BAUCHI
Misalin karfe 4 na yammah Suka iso tashar Bauchi Tunda Asma'u ta Shaki iskar bauchi walwalarta ya karu daga Tasha.
Mai adaidaita Ta dauka daganan sai gidan kakanininta dayake Irin Family house ne,kowa ya tashi sai dai yaja barayinsa yayi gini.vDuk da iyayensu sun Rasu ammh kawu wanda ya Rike Mamanta yana nan da Ranshi, sai dai Suka ganta kwatsam ta Shigo haka Suka zagayeta matan kannen mama,da yaransu suna mata barka da Zuwa.
kowa sai mamakin ganinta yake da yarda ta zama,Sallah kawai tayi adakin Jummai matar kawu,ko abinci ta kasa ci ta kosa isa gidan Mamanta tsaraban yaran gidan ta Diban musu, ta mike tace zata karisa Federal Lowcost.
Jummai tayi tayi ta tsaya ta jira kawun ya dawo tace Sai dai ta dawo gobe,vDole ta kyaleta ta tafi.
Wani mai Adaidaitan ta samu ya Dauketa Direct sai Federal lowcost bai Direta ko'ina ba sai abakin katon gidan Proff. wanda ya kawatau da wani Tamgamemen get mai kyau dana Tsari.
Cike da Farinciki ta biya mai ADaidaitan Kudinshi ta Dumfari get din gidan tana Rike da akwatinta. Get din ta buga kafin mai gadi ya leko yana Tambayan wacece tace Asma'u ce bai ganeta ba don duk ta chanza tsaya a yayi yana kallonta Mirmishi tamai tana Fadin Asma'u ta Dutse ne.
ware ido yayi yana dariya kafin ya Bude mata kofar ta Shigo yana mata barka da Zuwa dayake Tun wanchan Zuwa Sun saba dashi sosai.
Tashigo Haraban gidan kenan taci karo da Fati da Mahmud sun Fito Da Kayan islamiyansu ajikinsu Mamman
ma Direba yashiga mota Zai kaisu.
Fati ce ta fara ganinta ta Zaro ido ta yarda jakarta ta Rugo da gudu tana Fadin"Anty Asma'u Oyoyo Oyoyo"
Take Fad'a tana Kamkameta har jakar hannunta na Fad'i Rikota Asma'u tayi tana dariya Shima mahmud Gudun ya kwaso yazo ya Rumgumeta suna ihun murna ga Anty Asma'u tazo.
Tana dariya Farinciki yaki Barin Fuskarta, Akwatinta Fati taja Shi kuma mahmud ya karbi jakar hannunta Sukayi Cikin gida da Gudu,Tabisu da kallo tana Dariya Mamman ne yake gaisheta ta waiga Tana amswa Shima harda Zolayanta wai lalle Bauchi nada manyan baki,Dariya kawai tamai ta Nufi koridon da zai sadata da Cikin Babban Falon gidan.
Anty Safina da Anty Nafi ce ke Zaune a babban Falo Suna hira sai ga Fati da Mahmud Sun Shigo Suna ihu murnan ga Anty Asma'u nan.
Anty Nafu ce tace"Wata Asma'u kuma..? Fati yar Shekara Tara tace"Anty ma'un jigawa."
Anty Safina zatayi mgana kenan sai ga Maman Fati ta Fito daga kichen tana Fadin"Wai hayaniyar me nake ji ne"? Da gudu Mahmud yatafi wajenta yana Nuna mata jakar Asma'u yana Fadin"Mama Anty Asma"u ce tazo."Kallonsa tayi Cike da mamaki tana Fadin"Wata Asma'un? karya ne.."
Asma'u data Sawo kanta Falon lokaci d'aya ta na Fad'in"Ba karya bane Mama.."
Tafada tana Dariya Zaro ido Anty Nafi da Anty Safina sukayi suka kuma had'a baki wajen Fadin"Asm'u. Ikon Allah wlh Ma'u ce maman Fati.."Suka fada Suna dariya.
Dukkansu suka taso Suka Rumgumeta suna Murnan Zuwanta.
Janta Sukayi kan Kujera cike da Murna Maman Fati ko baki yaki Rufuwa cikin Murna tace"Ma'u yanzu kike tafe baki yi ko waya kin sanar kina hanya ba.."
Mirmishi tayi kafin tace"Mamaki nakeson Baku Mama.."Anty Nafi tace"Aiko kin bamu mugun mamaki ma Ma'u wai yaushe Rabonki da gidannan? kinsan jiya muke zencenki nda Hajiya"Asm'i tace"Allah sarki Hajiya Ita nazo Dubawa wlh Tunda mukayi waya da mama take sanar dani jiki yaki dadi, na kudurtaa insha Allahu karshen Sati zan zo In Dubata ya jikin Nata?
Basu samj zarafin mgana ba Hajiya ta Fito daga Falonta tana Fadin"Nafi hayaniyar suwa nakeji haka ne? Su fati basu Wuce mktanta bane..? Tafad'a tana Tsaye akofar Shashenta kallo daya zakamata ka fahimci Ciwo na Cinta Saboda yadda Duk Ta rame.
ido ta Zaro tana bin Asma'u da kallo batayi mgana ba Anty Safina tace"Wlh Hajiya hayaniyar Murna Zuwan Asma' u muke gatanan yanzu take tafe"
Hajiya ta kariso tana Fadin"Ikon Allah Ma'u. Taho taho diyar albarka jiya nake zencenki ashe kina Tafe.."Da hanzari Ma'u ta mike Ta fad'a Jikin hajiya Suka Rumgume juna.
Asma'u ta dago tana kallon Hajiya tana Fadin"Sannu hajiya ya jikin ki? meke damunki yanzu."?
Hajiya ta Dafa kafad'ann Asma:u tace"Naji sauki Ma'u. kawai Ciwon kai ne ke Damuna yanzu."
Kwabe Fuska Asma'u tayi alamar Damuwa tana Fadin"Hajiya jinin ke ne ke kara sama shiyasa kike Fama da Ciwon kai, Da zarar kin Rage Shiga damuwa da Tunanin mai Zurfi jininki zai daidaita yakoma Normal har Ciwon kan yatafi kina Shan mgani kuwa..? Mirmishin dayafi kuka Ciwo Hajiya Tayi kafin tace"Hakane Ma'u ina Sha Allah dai ya nuna mana iyakar Abun ammh dai sai kinyi Wata zaki koma ko..?
Dariya Asma'u tayi kafin tace"Naso haka hajiya. ammh Saboda aikina Ranar Lahadi zan Tafi.."
Bata Fuska hajiya tayi kan tace"Kai wai meyasa Mallam bai Neman ma Ma'u aiki anan garin bane.."
Gabadaya Falon Suka saka mata dariya,itama dariyan tayi tama kamo Hannu Ma'u suka karisa ga kujera suka Zauna tana Fad'in"Fati da mahmud maza ku Shigarma da Ma'u kayanta Shashena Duk inda akaje ko Jikoki Ma'u tayi masaukinta na d'akina.."Nan ma Dariya Suka sakamata Su Anty Safina na jin Dadin yadda Zuwan Asma'u ya saka hajiya ta saki jiki.
Fati ko da Mahmud da Hanzari Suka ja kayan Asma:u zuwa Shashen Hajiya har Suna Fad'a. Su hajiya suka bisu da Dariya nan Mama ta kawo mata abinci tana ci Suna hira nan take Tambayan Mallam Hajiya tace ya Shiga mkranta,Sai da tagama cin abinci ta natsa kana ta Shiga Shashen Hajiya ta Bude jakarta ta Fito da Sakon Ammi dana Aisha tabama su Hajiya Suka karba Suna godiya nan aka Bude Dambun Naman ana ci ana Hira,babban Abun Farinciki Shine Zuwan Asma'u yazo da Farinciki dadama Tunda ga Hajiya ta warware ta Shiga cikinsu anata Hirar Duniya ko Su Fati basu samu Zuwa islamiyan ba Tunda Suka ga Ma'u.
Gabda mangariba sai ga Mallam yadawo. yayi mamaki jiyo hirarrakinsu Tunda ga haraban gidan, sanin dayayi Tunda Hajiya ta Farama sama kanta damuwa gidan yazama wani iri.
Cikin mamaki ya sawo kanshi Falon yana sallama sai dai Tambayanshi ta Tsaya da ganin Asma'u Shima yayi mamakin ganinta. nan Suka gaisa yana mata barka da Zuwa haryana ma Hajiya Tsiyan Taga Yarta ta warware ko?
shima Daga ganin Walwalwar Hajiya yafi komai Yimai Dadi koda bai Furta ba,vShashensa ya Wuce Mama ta bi bayanshi ta bar Su hajiya anan Falon.
Kosu Anty Nafisa Dare nayi kowacce Mijinta yazo ya Daukesu suka koma gidajensu. Ran su kal na ganin Hajiya ta Fara Dawowa cikin walwalarta, Ranar Maman Fati keda Miji,shiyasa da Wuri Asma'u Suka Shige Daki ita da Hajiya,da Farko dayan bedroom din ta Shiga dayske kowacce tana da babban Falo da Bedroom guda biyu kowanne kuma da Bayi.
Kichen kadai Suke da guda d'aya wanda ke Babban Falon gidan Gabadaya.
Hajiya ta Hanata tace tadawo Dakinta Su Dinga kwana.
Haka ko akayi,Ranar kusan 12 suka kai Suna hira da Hajiya da Asma'u kafin barci ya kama Hajiya, Wajen 2pm na dare ta Farka nan ta Iske Asma'u na sallah ita ma bata koma ba ta mike ta Shiga Tiolet da Dauro alwala tazo ta Jera da Asma'u ta tada sallah.
sai wajen 4 na asuba kana Suka idar kowa ya Daga hannu sama yana Rokon Allah Bukatunsa.
Hajiya ko kallonAsma'u take tana yabawa da Natsuwar yarinyar tare da Hankalinta. da kanta ta gyrama Hajiya wajen kwanciya tace tataso in ta idar da addu'ar Ta koma ta Kwanta Saboda lalurarta.
koda ta kwanta da kanta Ma'u Lullubeta da Bargo,kafin ta koma ta Zauna kan Darduma bayan Ta bude karatun alQur'anin dake Cikin wayarta Tafara karantawa Cikin Siririyar muryanta mai Cike da gardi da Dadi.
Kuramata ido Hajiya tayi Sha'awarta na kamata tare da Sha'awar Ina ma ace yau Asma'u yarta ce ta Cikinta datafi kowa murna gaskiya Duk Namijin daya samu Mace kamarta yagama Morewa.
Haka kuma Duk Surukar data sameta amtsayin Suruka ta Godema Allah, Har aranta tana ji Da'ace tana da wani D'a bayan Baffa da sai ta nema mai Asma'u ko kuma Da'ace tana da wani kani ko wa,wlh bazata taba bari Ma'u ta Subuce musu ba.
Tun tana Sauraran Karatun Nata Har Barci ya Fara Daukanta batasan Sadda ta idar da karatun ba ita dai lokacin da Aka fara Sallar asuba awasu masallatai ne Ta Farka ta iske Asma'un tana Sallah.
Jikinta asake ta Sauko daga kan gadon Ta fad'a Tiolet tana kallon Asma'u Aranta tana Fad'in"Anya Wannan yarinyar na barci kuwa.."?
Take Fad'a acikin Ranta kafin ta yi tsarki ta Dauro alwala ta Fito tana jin jikinta yamata Dadi.
ciwon kan ma ya Lafa Tunda ta Samu ishashen barci.
*Janafty*