ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 10
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️10*
Koda Suka idar da Sallar Asuban ma Ma'u kara Matsama Hajiya tayi saida ta koma barci. Ita kuma sai da ta gama Azkar Dinta kafin ta Tashi bayan ta Sanya karamin Hijabinta Datazo dashi acikin kayanta,
Ta Fita Zuwa babban Falon babu kowa sai dai taji motsi a kitchen haka yasa ta gane Mamanta ne Ke aiki,da hanzari ta karisa kichen din tana Mai Maman Fati Sallama, wacce ke ta Faman Soya kwai hade da Dankalin Turawa.
Waigowa tayi tana amsawa lokaci D'aya Ta washe baki tana fad'in"A'a Ma'u. Harkun tashi,ya hajiya ta kwana da jikin..? Asma'u na karisawa gareta take Fad'in"Ina kwana Mama? Hajiya taji Sauki Don na matsa mata tayi barcI Sosai yanzu hakama na Sata ta koma ne.."Cike da Farinciki Maman Fati tace"Masha Allah naji Dad'i Sosai Ma'u"
Asma'u Ta kad'a kai tana Fad'in"Toh ai dama Mama koda Hajiya na Shan mganin Hawan Jini, matukar bata samu Hutu da kuma Kaucema hayaniya ba Toh bazata rabu da Wannan Azababbar Ciwon kan da ta ke fama da shi ba."Jinjina kai Maman Fati ta Cigaba Da yayi alamun gamsuwa kafin tace"Hakane Kam. Allah yayi Miki albarka kema Allah ya jikanki ya baki mai miki Asma'u.."Ta amsa da Ameen Cikin Farinciki kafin tace"Me zan Tayaki Dashi Mama..?
Maman Fati tace"Na kammallah komai Saura kad'an na Karisa. Ammh Sai dai ki Shigarmin wajensu Mahmud yanzu haka Suna chan Wajen Tsiyansu na Fama. Shida Fati basu Shirya ba.."Kad'a kai Asma'u tayi tana Fadi:n"Toh mama,"
Tafad'a tana Kokarin Ficewa Daga kitchen din Mama fati ta saka baki ta kirata.
"Asma'u"
Ta fad'a da kakkausan Murya alamun ba wasa kafin ta juyo tana maida hankalinta kan Asma'u Data waigo tana Fadin"Na'am Mama"
Ajiyar Zuciya Maman Fati ta Sauke tana dafa hannunta ajikin Cabenet din dake kitchen din lokaci d'aya ta na fad'in "Ya zaman gidan mahaifinki yanzu ta chanza zani koko har yanzu yana nan ayadda na Sanshi..."? Tafad'a tana Tsurama Asma'u ido.
Saurin Sadda kanta kasa Ma'u tayi kafin tace"Bai wani Chanza ba Mama Kawai kinsan yau da gobe sai Allah, nida ba wuni ma nake agidan ba ina zasu ganni"Tafad'a tana kokarin boye Damuwarta.
Girgiza kai Maman Fati tayi kafin tace"Haka dai kika ce Asma'u ammh ni na Haifeki nafi kowa sanin Zurfin Cikinki. Abunda nake So dake ki kara hakuri akan wanda ki ke da shi,Insha Allahu Jinkirinki ya kusa Zama alheri.."
Kan Asma'u na kasa ta amsa da Allah yasa acikin Ranta.
Maman Fati na kallonta sai ma ta kad'a kai Ta juya tana kokarin Juya Dankalin Dake Cikin Mai take Fadin"Shikenan Dama. Jeki Dubamun Su Fatin in Sun Shirya.."Bata yi musu ba ta juya jikinta asanyaye ta Fita Daga kichen din. Maman Fati ta bi bayanta da kallo Cike da Tsausayi kafin Ta Kada kai Tana Fadin"Allah gamu gareka..."
Koda Asma'u ta Shiga Falon Maman Fati babu kowa,cikin bedroom taji hayaniyar Su Fati koda ta Shiga ta Iskesu Sun sarke da Rigima kan Wandon mkrantansu Na hadda dayake iri d'aya ne,Karisawa tayi garesu Tana Musu Yar dariya. suna ganinta gabadayansu Suka tafi gareta Suka Fad'a mata Suka Rumgumeta suna gaisheta da kwana,amsawa tayi tana Shafa kawunansu,Cike da Farinciki da Annuri.
Ita ta Raba Rigimar bayan ta Fidda ma kowa wandonshi kuma ta Taimaka musu Suka Shirya. Kafin 7:30am Sun Fito Falo,lokacin kuma Maman Fati Tagama Hada musu Breafsat. ta kuma Zuba musu Cikin Luch box dinsu,Karyawan ma Sama sama Sukayi Ruwan Tea kad'ai Suka Sha, Fati ne ma taci buredi ammh Shi Mahmud irin Mallam ne bayacin Buredi dayake ma takwaranshi ne. kuma Mallam din da kanshi ya hana Kowa ya sakaya Sunan Yace kowa ya Kirashi da Mahmud dinsa.
Sai da Suka Biya Shashen Proff.Suka gaisheshi da kwana zasu Shiga wajen Hajiya Asma'u ta hana tace ta kwanta Dole Suka Hakura, haraba gidan Suka Fita da gudu kowanne da jakarsa,hanuun kowanne Rike da basket d'in shi.
Tunda Haddan mai Had'e da Islamiya ce sai yammah Zasu Dawo. Koda Suka Fita har Mamman yazo,Shiga mota kadai Sukayi yajasu Suka Fice Daga gidan Zuwa mkrantar Nasu.
Suna Fita Asma'u ta koma Shashen Hajiya,Tunda Maman Fati ta Shigarma da Mallam Abun karinshi Shashenshi ta bar mu su na su ita da Hajiya a kicthen tace ta Dauka tatafi Dashi Chan Shashen Hajiyar.
Tana komawa Ta Shiga gyaran Falon Hajiya dayake ma ba wani datti yayi ba Cikin lokaci ta gyara ko'ina, hatta Dayan bedroom din sai da ta Shiga ta gyarashi ta wanke Tiolet.
Dakin Hajiya ta koma ta isketa Haryanzu Tana barci, Toilet din d'akin ta Shiga wanka ta wankeshi tas kafin ta Fito tana kauda wasu kayan Hajiya dake Bisa gado.
Duk ta Ninke mata ta Bude Wardrope dinta ta Saka mata,bganin har Lokacin Hajiya bata tashi bane yasa ta Shiga wanka,bayan ta Fito ta Tsane jikinta ta Jawo jakarta ta Fito da Manta Olive ta hau mulkama jikinta.
sai da ta gama tsab,Kana ta Fito da wani Less d'inta Doguwar Riga mai Kalan Maruon, da Zanen ja,Dinkin A shape ne ya Dace da Surar jikinta.
Dankwalinta ta Daura irin Daurin Zamani na Zahra Buhari, Bata yi ma Fuskarta kwalliya ba,illah Liptick data Shafama bakinta.
Tana gaban Madubi tana kallonta Kanta Cike da Sha'awa yadda Fuskarta ke nuna Annurin datake Ciki Kwarmin Wuyanta ta taba.
Tana wani Mele baki,vYar dariya Tayi kafin ta Juyo Ta maida Sauran kayanta Cikin akwatinta Ta maidashi a ma'ajiyarsa.
Fita tayi Daga dakin Cikin Natsuwa, Babban Falo ta koma na Ta iske Wata yar Dattijuwa na Share Falon, bayan ta gama Gyarashi, tana ganin Asma'u ta Shiga Gaisheta Cikin Girmamawa. Ma'u ta amsa Tana kara gaisheta Duk da bata santa ba,Tana jin mai aikin ne Wacce ke tayasu Share Share ammh bata kwana da zarar tagama ne kila take Tafiya gida ,Don ko Jiya data Iso bata ganta ba.
Dakin Maman Fati ta koma,sai Ta iske batanan ,Tana Shashen Malam kenan,Fitowa tayi ta Fada kitchen ta Iske Abun karinsu,Cikin Wani katon Faranti mai Fad'i,Dauka tayi Ta fito ta Nufi Shashen Hajiya Cikin Tafiyarta Na natsuwa,da Kallo Yalwa ta Bita tana Tunanin ina kuma aka Samu Budurwa mai Kirki haka ganin bata da amsa yasa ta koma ta Cigaba da Abunda ke gabanta.
Afalon hajiya Asma'u ta ijiye Farantin kayan karyanwansu,bayan ta Ja Center Table din Tsakiyar Falon Ta Dora akai, Bedroom ta Shiga tana Fatan Allah yasa hajiya ta Farka,tana Shiga ko ta ganta Zaune Mirmishi Asma'u ta Saki tana Fad'in"Sannu Hajiya,ina kwana.."
Hajiya na Hamma tace"Lafiya lau Ma'u sannu da kokari Nagode fa,Allah ya saka miki alheri.."Bata amsa ba ta Kama hanyar Tiolet tana Fad'in"Hajiya bari na Had'a miki Ruwanka mai D'an Dumi ki Shiga ki Watsa kizo ki karya Kisha magani Zaki karajin Dadin jikinki.."Tafad'a tana Tura Kofar Tiolet. D'in.
Da kallon Sha'awa Hajiya Ta bita dashi kafin tace"Toh ,Ma'u Yanzu kuwa don Wlh Tun jiya Zuwa yau naketa jin Dadin jikina. Babu Abunda Zence dake sai godiya."Ma'u tana jinta ta cikin bayi ammh bata ce Komai ba sai dai kawai ta Murmusa.
Tana gama Had'ama Hajiya Ruwan wanka ta Fito,da hajiya ma Zata tashi ita ta Taimakamata ta rakata har bakin Tiolet din kafin ta barta ta Shiga koda Hajiya ta Fito ,har Asma'u ta Fito mata kayan data zata saka harda man da Zata Shafa, Hajiya bakinta ma ya kasa mgana Gyada kai kawai take Cike da Murna ta kuma kara Sakama Asma'u albarka acikin Zuciyarta Falo Asma'u ta koma bayan ta Sanar da Hajiya in ta Shirya ta Fito Su karya da Toh ta amsa tana Fadin"Allah yayi albarka Asma'ul Husna.."
Kan D'aya Daga Cikin kujerun Falon ta yada Zango,wayarta dake hannunta wacce ta Dauko da Cikin dakin Ta kunna sai ga haske ya bayyan,dan Kishingid'a tayi kafin ta latso Nombar Rabin Ranta,Ringin Uku tayi Aisha ta Daga tana Fadin "Nayi Fushi Rabin Raina. Shikenan kuma daga Zuwa Bauchi an samu Mama da Hajiya an Manta dani ko..? ta karishe Cike da Tabara.
Yar dariya Asma'u ta saka kafin tace"Kedai bari Rabin Raina,Allah Bauchi Tafi Dutse dadi."Wata Dariya Aisha ta saka kafin tace"Da gaske,? Kodai...Ko...Kodai....."
Katseta Asma'u tayi tana Fad'in"Kodai. Me...? tafad'a tana Hade rai kamar ta na gabanta.
Shekewa Dadariya taji Aisha ta yi, sannan tana jin muryan Fahad,shima yana Tayata Dariyan. girgixa kai Asma'u tayi kafin tace"Allah ya Shiryeku daga ke Har Mai goya miki baya"
Tafad'a tana Gyara Zama, Ameen Aisha tace kafin ta Shiga Tambayan Su hajiya Asma'u na Fadin Duk Suna lafiya basu gama mgana da Aisha ba ta yanke Kiran tana Fad'in Rabin Raina ina Zuwa.
daidai lokacin Hajiya Ta Fito Daga Bedroom d'in ta, cikin shirinta tayi Tsab da ita.
Da Hanzari Asma'u Ta mike ta taro Hajiya akasa ta Zaunar da ita bayan Ta kara mata Filullunkan Kujera guda biyu, tana ta kuma Jeramata sannu Farantin Abun karyawan Ta dauko Ta ijiye agaban Hajiya Tana Fadin"Hajiya me zan Had'a miki ne,?gadai Soyayyen Arish,da kwai sai Ruwan Tea,sai Soyayyen Buredi.."
Gyada kai Hajiya tayi kafin tace tace" Bani Soyayyen Buredi,sai ki Had'amin Ruwan Shayi" Cikin Natsuwa Asma'u Ta had'a mata komai Ta Tura mata gabanta tana Fadin"Gashi Hajiya,Ki cinye sai kisha mgani. Ko zaki koma barcin ne bayan kin gama..?Tafad'a tana yar Dariya.
Mirmishi Hajiya tayi Mata Kafin tace"Kina Shagwabani Asma'u. na Zama yar gata"
Asma'u na Mirmishi tace"Toh Hajiya in bamu ji dake ba, wazai ji dake..? Kuma wannan barcin Dakikeyi, Shine kad'ai Zai kara Taimaka miki wajen Saukar Da jininki.."Jinjina kai Hajiya tayi kafin tace"Naga alama.."Tafad'a lokaci d'aya tana jan Filet din Soyayyen Buredin gabanta ta Gutsura ta Tura abaki Lokaci Daya Tana Kurban Shayi.
Gefe Asma'u Ta koma bayan ta Zuba Shayi awani karamin Kofi tana kurba, Kallonta Hajiya tayi tana Fadin"Ma'u bazaki ci Ko dankwalin ba naga Shayin kad'ai kika Zuba.."Yamutsa Fuska Asma'u tayi kafin tace"Wlh ya Isheni Hajiya. bani Son Cika Cikina da Safe ne yanzu Duk Jikina Zai Mutu sai Zuwa anjuma kila naci.."Hajiya bata ce komai ba Sai da Ta hadiye Abunda ke Bakinta kafin tace"Toh Shikenan. dama ku ma'aikatan lafiya Koda yaushe Cike ku ke da ka'ida haka Dr,Nura yake Kullum Cikin Tsari.."Yar dariya Asma'u Tayi batayi mgana ba.
Sun Dad'e da Hajiya anan Falo, har bayan Sungama karyawa ta Maida Kayan da Suka bata kichen ta Iske yalwa na wanke wanke,sannu da aiki ta mata kafin ta koma wajen Hajiya. mganinta ta tambaya ta sanar Da ita Inda yake,ta Dauko ta Zo tana Dubawa kafin ta babbala ta bata tasha tasha kenan Sai wayar Hajiya ta Dauki Tsuwa.
Daga cikin daki Asma'u ta Shiga dakin ta Dauko mata. yusuf ne ke kiranta ta d'aga Suka gaisa bayan ya Tambayeta jikinta tace da Sauki,Zainab ya bamawa Ta gaishe da Hajiya nan Hajiya ke Fad'amata taji Sauki Sosai Asma'u tazo tana Kara Kula da ita.
Zainab Taji Dadi nan take tace abama Asma'u Waya Su gaisa.
Cike da Fara'a Suka gaisa da Asma'u kafin Suyi sallama. Asma'u ta mikama Hajiya wayarta tana Fadin"Hajiya ki koma ki kwanta Zuwa anjuma kya Tashi.."
Hajiya batayi gaddama ba ta yunkura ta Mike Asma'u na mata sannu.
har dakin Ta Rakata bayan ta kwanta ta Lullebe kafafunta da blanket.
kallonta Hajiye Keyi tana kara Yabawa da Kirki da Natsuwar Asma'u, Falo Ta koma hannunta rike da waya,ta Kwanta Bisa kujera tana Danne Danne Bisa wayarta.
****
Yau Tunda ya Tashi yakejin kanshi yana Saramai.
bai damu ba haka kuma ya Shirya ya Fice Zuwa Office Cikin Wannan Halin,Yana wajen aikin wayar Wasila ta samai Inda take Sanar Dashi yau Zata Dawo. Abunda ya kara bata Tsoro Shine Bai Nuna wani Dokinta ba kamar abaya,wanda wani lokacin ma,sai dai kawai Ta ganshi a bidda yazo daukanta ammh sabanin yau sama sama ya amsamata kafin ya yanke Kiran.
Kuka ta Fashema momcy dashi sai da tayi ta lallashinta Kafin ta Hakuri, jikinta ba Laka Suka kamo Hanyar Portharcourt,Ita da Samuel bayan Momcy ta jaddadamata Ta Danne komai,Kawai da Zarar Abdallah ya Tafi Bauchi Tayi mata waya.
*****
Misalin 09:08am Na rana yana Zaune acikin Office di'nsa,duk yau yakasa Tabuka komai,Kujerarsa ke Faman juyi dashi Shiko Hannayensa kan Kuncinsa kamar Wanda akace Wani Nasa ya Mutu.
Sanye yake da American Suit,Masu Ruwan Toka,Farar Rigarce kadai ajikinsa ya Cire Coat din ya sagaleta jikin kujeran dayake kai, Wuyansa kuma yana Matse da Tie dinsa mai Ruwan Toka,kallon Farko zakamai ka Fahimci Fuskarsa na so ta bayyana Damuwarshi, Idanuwansa har Sun Chanza launi.
Yana Cikin Wannan Halin ne, wayars dake kan Tiburen gabanshi Ta Dauki ruru,Sai da ta kusa yankewa kana ya Dago da kansa ya Dauki wayan,ganin Sunan *POL* 2 yana yawo akan Screen din wayarshi Bai d'agaba illah Maida kanshi da yayi ya kwantar yana kara juya kujeran,Har wayar Tagaji da Neman Dauki ta Kashe kanta..
Ko Minti biyar ba'ayi ba. Naga ya Zabura yana Dafe kansa kamar Wanda aka Dakeshi akanshi, Mikewa yayi da Hanzari jikinsa na rawa Sosai,wayarsa ya Dauka yana Duba lokaci 09:30am,Kwakwalwar kanshi Banda Kiran Sunan garin Bauchi Babu Abunda Take,Yana jin kowani bangare na Zuciyarsa da Ganganar jikinsa tana Kara Izashi.
bai tsaya Neman wata Shawara ba ya Zari Coat dinsa,Wayarsa ya Dauka kafin ya Fice Daga Office din da Sassarfa, Yana Fitowa masijansa ya Matso hannu kad'ai ya Dagamai kafin yace"Ka Rufe Office din,Zanyi Tafiya ne.."Daga haka ya Fito haraban Wajen,Emeka dake cikin Mota Zaune Kawai sai ji yayi M.A Ya bude bayan Mota ya Shigo,cikin Hanzari ya gyara Zamanshi,ganin yadda Ogan nasa yake Arikice yasa bai Wani tsaya Tambayanshi ba ya Tada Motar Suka Fice daga Haraban wajen
Sai da Emeka ya Daidaita Motar a saman kwalta,kafin ya waigo,zaiyi mgana kenan M.A ya katseshi Cikin Numfarfarshi yana Fadin"Airport.." Ya fad'a lokaci d'aya yana Dafe Kanshi da yaji ya na saramasa tare da da gudun zuciyarsa.
Da Hanzari Emeka ya Tada Motar Suka Fice Daga Haraban Wajen,Cikin Lokaci Suka isa portharcoaurt International Airport. Cikin ikon Allah kuma M.A Na Fita ya Shiga Cikin Airport,nan ya samu Jirgin da Zai Tashi Zuwa Bauchi nan da Minti arba'i Mota ya Dawo ya Umarci da Emeka ya Fita yayi Mishi Buking din Jirgi da zai Tashi Zuwa Bauchi,Cikin lokaci kalilan Komai ya kammallah,Emeka bai Tafi ba sai da yaga Tashin Jirgin su M.A kafin ya Tada Motar ya Nufi hanyar komawa gida yana Cike da Mamaki yau yallabai Zashi Bauchi wanda kusan Shekaru biyar yana Tuka oga, Ammh zuwanshi Bauchi kiragage ne,Koda ga ganin yanayin M.A din akwai babban Abunda ke Damunsa.
******
Around 2pm jirginsu ya sauka Abubukar Tafawa Balewa international Airport,Bauchi. Daganan bai Tsaya ba ya Nemi Taxi yayi Tashanta har Zuwa Federal Lowcost.
Sai akofar gidan Makeken Get di'n gidan Mallam aka saukeshi, Fitowa yayi Cikin Wani yanayi yana bin gidan Nasu da kallo,kafin ya Fiddo Walet dinshi ya Biya Mai Taxi din kudinsa..
Jikinsa Duk asanyaye ya Nufi bakin Get d'in yana Kwankwansaawa,Megadi daya Taso ya hau Tambayan Waye..? Bai amsa mai ba Domin kunya yakeji ma yace Shine jin anyi Shuru yasa Megadi ya Bude karamar Kofar yana Lego da kansa daidai lokacin da M.A yadawo da kansa wajen,Zaro ido Megadi yayi yana Rawan Jiki da Baki yace"Ya..Yallabai...Barka da Zuwa..."
Yafad'a Cike da Farinciki ya Bude masa kofar,Yake kawai yamai bayan ya Shigo gidan,hannun ya mikamai Sukayi musabaha, Shiko megadi kallonsa yake yana Fadin"Ikon Allah,wai da gaske Yallabai kaine..?
Yafada Cike Da mamaki.
D'an Murmusawa Abdallah yayi ya juya ya Fara Tafiya Zuwa Cikin gida hannunsa Rike da Coat dinsa da wayarsa Ko'ina na gidan yake bi da Kallo Cikin Wani yanayi ya iya Shekarun daya kwashe bai Zo gida ba,Babu Abunda ya Chanza sai ma Wasu gyaran da baisan dasu ba, Shiko Megadi har ya Kule yana kallonsa Don har Kulle idonsa yayi ya sake Budewa wai ya Tabbatar gaske ne ko Mafarki.
Cikin Takunsa na Isa,da jarumta ya Saka kanshi Afalon. sai dai kuma babu kowa,sai Talabijin dayake tayi Shi kadai Atashar Sunna Tv inda Suka sanya karatun alQur'ani Cikin Suratul Maryam Cikin kira&ar Sheik sudes .Ganin haka yasa ya Tsaya yayi Shuru yana bin ko'ina da Kallo,wata kewa na Tasomai Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Dumfari Hanyar da Sai da Shi da Sashen Hajiyarsa Domin ayanzu idanuwansa Sunfi kewar ganinta Fiye da kowa.
Asma&u na kan sallah Tana Addu'a bayan ta Idar da sallah,barci ne ya kwasheta kan kujeran nan bata sani ba .
har wajen 2 na rana ganin Shuru ya Sanya Maman Fati ta Shigo,ganinta tana Barci ne yasa tatasheta tace Tatashi tayi sallah Taci abinci, Tashi tayi Tana Mika lokacin data Duba lokaci acikin agogon wayarta tayi Mamakin barcin data Sha,wanda Tadad'e batayi Irinshi ba.
A kasalance ta Shiga bedroom din Hajiya nan ta tarar Da ita tana barci bata Tashi ba,AC dakin ta Rage mata kadan Duk taga iskar tayi yawa Tiolet ta Fada ta Dauro alwala tana Fitowa sai ta Dauki sallaya da Hijabinta ta Fito Falo ta Shimfid'a ta Tada sallarta Saboda bataso Tatashi Hajiya tafiso ta Tashi da Kanta.
Ta shafa Addu'ar kenan ta mike Kafarta Ya sawo kanshi Falon. inda Wani Siririn kamshi ya Biyo ta Kofar Hancinta na Turarenshi na mai dad'in kamshi.
Lumshe ido tayi batare data bama Ina kamshin Ke Fitowa Muhimmanci ba, Shiko yana Shigowa da karamar Sallama jin ba'a amsa ba,sai yayi Tunanin Kila Hajiya na Ciki ne. kuma Shi harga Allah bai Lura da Asma'u dake Zaune Tsakar Falon ba, kawai Sai ya Fara taku Zuwa d'akin Hajiya Asma'u na Zaune sai ganin Mutum Tayi Tinkis Tinkis ya Wuce ta gabanta
Gabanta ya Fadi Ras! ga Asma'u da Tsoro ammh haka Tamike tana Dafe da kirji take Fadin"Kai waye...? mallam lafiya zaka Shigoma mutane gida haka kurum kuma ka Wuto dakin Mutune ba Neman Izini..?Tafad'a lokaci d'aya tanabin Bayansa da Kallo Cike da Tsoro.
Cak ya tsaya kafin ya Waiwaiyo kad'an Suka Had'a 4 eyes da Asma'u yadda ya Zubamata ido ne yasa gabanta ya kara Fadi. Shiko ganin Farko dayayi mata Shima sai da gabansa ya amsa basarwa yayi kawai Bai mata mgana ba Illah kallon Sama da kasa da yayi mata,Ya wani tabe baki kawai ya Juya Ya Shiga Dakin Hajiya.
Asma'u Tayi Wuri Wuri Cike da Tsoro saboda yadda ta Firgita ne yasa bata ga Tsantsanar kamar Baffa da proff ba. cike da Tsoro ta kwashi Gudu Zuwa Shashen Maman Fati,bata Falo tana bedroom dinta tana Ninke kaya kafin Su Fati Su dawo Daga mkranta shi kuma Mallam ya Shiga mkranta Sunada Taro.
ji kiran da Asma'u ke Mata ne Tundaga Falo yasa gabanta ya Fadi,ta yarda kayan dake Hannunta ta Fito da Sauri sai gashi Sun Ci karo da juna.
Cikin Mamaki Maman Fati ke Fadin"Lafiya Asma'u meya Faru..? Ma'u na haki ta Rike hannun Maman Fati Tana Fadin"Mama..Mama..Taho ki gani wani ne. Ya Shigo Har Falon Hajiya mama, kuma ya Shiga bedroom dinta ina ta tambayan waye yayi banza dani.."Cike Da Mamaki Maman Fati Tace"Wani kuma..?Kai Asma'u ta Daga har tafara kwallah Saboda Tsoro.
Maman Fati bata Saurareta ba ta Kwashi Sauri Zuwa Shashen Hajiya Itama Asma'u ta Rufamata baya ammh Zuciyarta kamar ta Fito Saboda Tsoro Ita Duk Atunaninta Barawo ne.
*Janafty*