NAZNEEN.....

Page 6

by @maidambu41

*NAAZNEEN❤‍🔥 <6>*

EXQUISITELY BEAUTIFUL 


#Mai_Dambu


'Top-Notch

Season 3

بسم الله الرحمن الرحيم

Ba karamin mamaki ta sha ba, lokacin da ya ajiye ta a winti, ya juya yayi tafiyarshi. Tow kuma me take so ya mata? Wani bangare na zuciyarta ya tambaye ta, shiru tayi tana nazarin abin kafin ta tari abin hawa ta nufi gida, tunda ta isa ta kasa rintsawa, idan ana neman love at first sight shine ya faru tsakaninta da Saifullahi-Khalid. Al'amarin da ya gigita Gimbi ai ba karami ba ne, don haka koda gari ya waye bata leka ko waje ba, asalima wani irin zazzaɓi ne ya rufeta. Washe gari Linah da Siyamah suka zo mata, ganinta suku-suku yasa suka matsa mata da tambaya. 

"Baby lafiya?"

"Ku bari kawai, tun ranar da naga gayen nan na rasa meke min dad'i, domin kuwa kamar na zauce nake ji a raina."

 Sakin baki sukayi suna kallonta, kafin su ce mata. "Ina honorable ɗinki?" "Bana son bura uba, ni ba shi nake nufi ba. Ina gayen da ya bude taro da addu'a a wurin bikin nan?" 

"Eyeeeee!" Suka fada bayan sun ware idanu akanta, "Kinsan me kike faɗa kuwa? Saifullahi-Khalid?" Hadiye yawu Siyamah tayi tana faɗin. "Hala hauka kika fara? Gayen da bai kula mata shi ne kike tunanin zai so ki?"

"Haba Siyamah, Gimbiya kawarmu ne wannan karon ta ga abu tana so me zai saka ba zamu taya ta nemanshi ba, Gimbi matukar kina sonshi zan taya ki." Kamar tayi kuka haka take kallon Linah ta ce mata. "Wallahi ban tab'a jin haka ba, sai wannan karon."

"Na sani, amma ku sani Linah akwai hatsari. Saifullahi-Khalid ba gama garin mutane ba ne. Yana da addini sosai, sannan yasan abin da yake wallahi ba zai tab'a yarda yaso Gimbi ba."

   "Zai so mana, yanzu abin da zamu yi dole daga yau mu fara niman sanin waye shi. Kafin mu cimma shi." Dake Linah tana da mugun shige-shige, babu abinda yake razanata. Haka suka shiga fafutukar sanin waye Saifullahi-Khalid. Sosai suka binciko waye shi, sannan suka shiga tufka da warwara. Kafin kuma suka shiga bin Malamai. Duk inda suka je babu wanda yake iya nimo musu koda kurwanshi balle kuma a san waye shi. 


  Karshe dai sai da suka tafi har kaltungo, suka dira wurin Ba Allah, yana ganinta ya kwashe da dariya,kafin ta bashi labarin kome ya bata labarin abin da bata sani ba , sannan ya ce mata. "Aikinki kala uku ne,na farkon kayanshi na sawa, rigar shi da wandonshi sai takalmi da hula, na biyu zaki bashi abu yaci domin ta haka ne za a same shi. Na uku za a mishi kiranye, domin ana gab da hada shi aure da yar Kawunshi gata nan!" Kallon hoton tayi yarinyar ta hadu ta gaji da haduwa.

Tana kwance a kasa ta ce mishi. "Ba Allah, taya zan samo kayanshi?"

   Murmushin mugunta yayi kafin ya farawa kanshi kirari. "Sai ni na deluwa baban Korau, uban dan tsugudidi baban ifiritai, Mijin aljana angon shaidaniya. Na ci dubu sai ceto. Ni ne nan ba Allah!"

     

  Kwanciya tayi sannan ya ce mata, "zan duba miki cikin gidanshi domin yana rayuwa ne daga shi sai masu mishi hidima, zan tura yan aikina domin su duba mana waye me son zuciya a cikin mutanenshi."

    Suna zaune kuwa aka nuno gidan Saifullahi-Khalid a madubin gabansu, babu wanda aka nuna yana da son zuciya sai da aka kusan daina nuno gidan, sai ga me mishi girki, yana leke leke, sannan ya ficce da wasu kaya a hannunshi. Murmushin mugunta Ba Allah yayi sannan ya ce musu. "An gama, yanzu na baki nan da kwana ashirin ki tafi har can, ki nimo kayanshi sannan ki bawa mutumin wannan abin ya saka mishi a cikin abincin shi. Wannan kuma ki tabbatar ya binne a cikin gidan, wannan kuma ki nimo inda kika san ana girki ba dare ba rana, ki saka. Wannan kuma ki nikashi ki zuba a cikin mazubi, kina sakawa a idanunki. Amma sai ranar da zai zo. Wannan kuma ki zuba aman shafawarki, kina shafa shi. Wannan duk ranar da zaku haɗu, ki turara jikinki da shi."

   Gyada kai take, don ma Allah ya taimaka duk abin da ake bata, Linah tana rubuta mata, suna gamawa ya ce musu. "Da me zamu biya sadaka?"

"Bakin karfe da jan kare, bakar akuya da jar akuya, da yar kasa gajeruwa. A kai duk inda aka san ruwa yana taruwa. Da carton din giya, jar dawa da farar dawa. Jariri wanda aka haifa yau sabo fil!"


 "Jariri?" Suka tambaye shi, a razane jikinsu yana rawa. Murmushi yayi ya ce musu. "Jimawa kaɗan zaku haɗu da shi, don haka a hada min da shi, aikinki yana bukatar jinin Dan Adam. "

  Wani irin tsoro ne ya kama ta ce mishi. "Ina tsoron kada a kama ni?" "Hhhhhhh! Babu mahalukin da ya isa kama ki, sai na ga baya shi, maza b'ace min da gani!"

   Daga haka suka mike zasu fita ya ce mata. "Nan da sati Uku, ki tabbatar aikin ya kammala ki sha mamaki."

    Haka suka fito daga dutsen jikinsu a mace, suna jin kamar ba cikakken mutane ba, a cikin sati daya da ya wuce Gimbi ta shirga karya, bayan ta nimo address din gidan Saifullahi-Khalid, har da inda yake aiki.

  Kukunshi me suna Wasim, dan kabilar igla ne, sai dai mutum ne mai shegen son kai da son zuciya, bai da kirki sannan shi kanshi Saifullahi-Khalid yasan cewa yana mishi barna, amma hakuri da taushin zuciya yasa yake tare da Wasim, amma da ya bi na zuciyar Nassef tsaf da ya kore shi,

    Wannan yasa shi kuma Wasim yake ganin kamar ai Saifullahi-Khalid bai san kome da yake yi ba, kasancewar ba unguwar yake ba, zuwa yake da sassafe da wannan damar Gimbi taci gallabar bashi kudi me yawan gaske ya kawo mata kayan me gidanshi, sannan ta bashi wanda zai na saka miishi a cikin abincinshi.


   Wannan lamarin ba karamin dadi ya mata ba, domin kuwa yadda taso haka ta yi. A cikin kwanaki goma sha takwas. Suka dawo Bauchi da kawayenta, ranar da suka cika kwana biyu da dawowa, aka tsinci jariri a makarantarsu, dama abun da suke fata kenan, Siyamah ta shiga makarantar taji ana an samu Jaririn, kafin ace wani abu ta tafi ta sace jaririn a asibitin makarantar, sannan ta kawowa Gimbi.


  A can makarantar aka nime Jariri sama da kasa, ganin dama suma gidan Marayu za a kai shi, yasa babu wanda ya wani damu. A bangaren Gimbi da Siyamah da Linah, kuwa duk abinda aka bukata sai da suka saya. Sannan suka ajiye bakin ruwan dumduma.. sannan suka wuce kaltungo , suka kai kayan kome, kallon jaririn Ba Allah yayi ya tashi ya amshe shi sannan ya saka Gimbi ta durkusa, aka fara buga tsafi me sunan tsafi, da kayan Saifullahi-Khalid.


   Da wannan jaririn haka yayi ta aikin, musamman aka yanka Yaron babu tsoron Allah ko imani, haka suka yanke shi, aka binne shi da kayan Saifullahi-Khalid, sannan aka dawo jinin jaririn Ba Allah ya mata wanka da shi, ya kuma dauko wasu irin tattabaru guda biyu aure ya yankesu, aka ɗauki hular Saifullahi-Khalid aka saka su a cikinshi, sannan aka dauko budurwar kare da saurayin kare, aka yanke su jininsu aka zuba aka cikin hular, aka haka rami aka binnesu. Kafin ya kalleta. 


  "Ban tab'a aiki me haske irin naki ba, don haka tashi maza ki je, nasara tana gaba kada ki sake ya zo ki bashi fuska kai tsaye, ki bashi wahala da zai gane ke ba kanwar lasa ba ce."

  Gyada kai tayi tana faɗin, "Godiya nake ba Allah" daga haka suka bar kokon dutsen, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin. "An gama kome"

"Ya zaki yi da honorable?!" Tsaki tayi tana faɗin, "ke kyale dan wahala, ba abin da zan iya mishi." Suka kwashe da dariya, sai dare suka iso Bauchi, suka.ajiye ta a gud'un sannan kowa ya kama gabanshi.

***

Azare.

 Unguwar Zaweeya.

Unguwa ce me dinbin tarihi a garin Azare, unguwar manyan hafizan Alqur'an, uwa uba kuma manyan malaman mazahabar darika, 

      Unguwar da ta kasance kamar quarts kasancewar kafin boko ya shiga cikin su, manyansu da Yaransu anan suke zama kuma anan suke auratayyarsu. Gidan Sheikh Saifullahi Goni, marigayi domin ya rasu shekaru takwas. Ya bar mata uku, Hajiya Mariyah wacce suke kiranta Hajja Mari. Sai Hajja Maliyyah, suna kiranta Mama Hajja, sai Hajja Kubrah wa. Gidan Sheikh Saifullahi Goni yana da yara goma sha huɗu ne, kofar Hajja Marih tana da Yara biyar.

 Alhaji Mansur Saifullahi katagum

Hajiya Adamah Saifullahi katagum, sannan Gwana ta shekarar talatin da suka wuce domin ta shiga musabbaka ta karamar hukumar katagum, sannan tayi na jahar Bauchi, sannan tayi na kasa baki ɗaya. Hakan yasa aka mata lakabi da Gwana tana da yara biyar, dukka mata kuma abin burgewa mahaddatar Alqur'ani ne.

Alhaji Abideen Saifullahi katagum, shugaban kamfanin wutar lantarki na shiryar arewa maso gabas, yana garin Jos da zama. Shi wannan asalin dan boko ne Yaranshi uku ,

Hajiya Na'imatullah Saifullahi katagum, itama gwana ce, Yaranta hudu maza.

 Alhaji Yahuza Saifullahi katagum, shima nan alaramma ne,.mai jan baki a duk watan azumi, ga Sheikh Abubakar Goni. Shine karaminsu, yana da Yara kusan goma sha. Domin matan shi uku ne rurus, kuma haihuwa suke kamar me?

  Hajiya Maliyyah, Yaranta biyu ne rak kuma duk mata, suna nan cikin zaweeya da yaransu,

Hajiya Ummulkhairi, yaranta takwas itama gwana ce, shida maza manyan kenan biyu mata.

 Hajiya Sadiya itama gwana ce, har tana koyarwa a high Islamic dake nan azare.


Dakin Hajiya Kubrah, Mama Hajja. Mace me kirki da barkwace da son kowa nata ne, mace me ilimin addini, duk abinda zata fada sai ta saka Allah kafin ta kawo Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, macen da duk inda ta shiga sai ka fahimci ana yiwa Muslunci da muslamai hidima, mataimakiyar shugaban Fomwan, uwa uba sakatariyar Da'awa ta yankin arewacin Nigeriya kungiyar nasarul Islam.

    Mama Hajja akwai ilimin addinin kamar me, tana da Yara bakwai. Hudu maza uku mata.

Dr Khabir Saifullahi katagum yana garin Bauchi da iyalinsa suna aiki a asibitin Ni'ima, Matar shi daya da Yara uku.


Alhaji Awwal Saifullahi katagum shi kan Custum ne yana garin katsina a iyakar bodar Nijeriya da nijar. Matar shi bata jima da rasuwa ba, don bata samu haihuwa ba, sai daga baya, kuma tana haihuwa ta rasu, ta bar mishi Y'a mace


Rukayya Saifullahi katagum Nurse ce, ita kan Allah bai bata haihuwa ba, har yau. Sai dai sun san lokaci ne.


Mubarak Saifullahi katagum, gwani ne yana garin Lebanon da matar shi inda yake aiki yarshi daya.


Zakiya bata jima da aure ba, don tana da tsohon ciki ma. Itama gwana ce amma tana karatu a nan Bauchi, a Atbu.


Fatihatulkhair wacce aka yi bikinsu tare da Zakiyah don kusan babu tazarar shekara a tsakanin juna. 


Jalaludeen dan auta baki daya a cikin gidan, domin ya rasu Jalaludeen bai wuce shekaru goma a duniya ba. A wannan shekarar da aka yi musabbaka Jalaludeen shi ya lashe gasar a garin Qatar. 

 Gidan Sheikh Saifullahi katagum idan aka ce babu tarbiyya tow an ci amanar Malam, domin baki daya yan gidan Malam ya daura su akan tafarkin Allah, kuma ya koya musu soyayyar Manzon Allah. Kuma suna kan daura yan bayansu akan soyayyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, Duk cikin gidan ba zaka tab'a banbance Yaran Mama Hajja da Yaran Hajja Maliyyah ba, domin kowannensu ya rungume Yaran gidan, Hajja Mari tana matukar kunyar Yaran Ambassador Mansur Saifullahi katagum, daga kan Mariya Shamsiyah da Saifullahi-Khalid, tana matukar kunyarsu, ita kuma Mama hajja saita Rungume su, ita kuma Hajja Kubrah ta rungume Yaran Mama Hajja, ita kuma Hajja Marih ta rike na Hajja Marih ta rungume Yaran hajja Kubrah, saboda tsananin zumunci da hade kai, kome iyayen suke so ba tare da gulma ko tsegumi ba, zasu tattauna abinsu.


   Iyayen sun rike junansu, Babu batun kishi ko tashin hankali, ba kyashi ko hassadar Yarana suke kaza, matan gidan sun fi mazan Yawa. Mazan gidan Allah ya albarkaci rayuwarsu ba kadan ba.

-----------

Sukuku Mama Hajja ta tashi, hannunta rike da casbi. Tunda tayi sallah waalaha. Ta kishingida. D'aga labulen dakin Hajja Mari tayi cikin zolaya ta ce mata.

"Mata a gidan Malam Alhaji, me ake roka mishi ne?"

 Tashi tayi a kishingida ta sake murmushi ta ce mata. "Hajja Marih kenan, Bana jin dadi ne, amma in sha Allah gobe juma'a zan saka a daka min fura, yau zan tura kira min Yalwaji......