TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

Episode 16-17-18

by @queenofsurprise1

đź’žTRIPLET'Sđź’ž



***



*THE BEGINNING*




đź’ž*STAR LADY*đź’ž





EPISODE 16-17-18



________________________________


Hajiya na ganin sun nufosu da wayan nan zabga zabgan bulalun, habawa ai sai ta fasa ihu tana kokarin guduwa ta haye sama suka damkota suka jawota zuwa tsakiyar Palon suka fara zabga mata bulalun sai ihu take, sauran dodannin kuma suka damko Abba suka kwantar da shi kusa da Hajiya suka hau zabga musu bulalun,


dai dai lokacin Akil ya shigo palon yana sauraron kira'ar sudais a wayar sa ya kure volume, shi ma yinwan dare ta tashe sa, jin kira'ar yasa dodannin ɓacewa ɓat, kamar kuma yadda suka ɓace haka suka ɓace da tunanin su Abba.


Ganin su Abba kwance a tsakiyar palon ne yasa Akil karisowa wajen da sauri yana faɗin "Abba Ammie lafiya kuka kwanta a palo yau kuma?" Shiru sukayi basu amsa masa ba, mamaki ne ya kara kama shi yasa hannu yana taɓa su, yana kiran sunan su.


Hajiya ce ta fara tashi a nitse kafin Abba ma ya tashi, "Abba me yasa kuka kwanta a Palo?" Akil ya jefo musu tambaya, kallon juna sukayi kafin su ɗaga ido suna kallon Palon, da mamaki har suna haɗa baki wajen cewa "Me ya kawo mu palo kuma?" Miƙewa Akil yayi tare da rage volume na kira'ar da yake ji ya nufi table yana faɗin "Kila barci kuka yi a wajen kuna hira" ya kai karshen maganar tare da zama saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin, ya fara bubbuɗe takeaway ɗin dake saman table ɗin, dan ya duba wani abunci ya dace yaci.


Jiki ba kwari su Hajiya suka miƙe suka nufi bedroom nasu ransu cike da mamaki yaushe suka zo palo kuma, da kyar suke jan kafar su, har suka wuce Bedroom na su.


Shi kuwa Akil abincin sa ya fara ci yana yatsine fuska


After some minutes.


Wayar sa ta fara kara, dogon tsaki yaja kafin ya É—auki wayar ya kawo ta sai tin face nashi Abla shine sunan da ya bayyana a kan screen É—in sake jan dogon tsaki yayi kafin ya É—auki kiran ya sata a hand-free ya É—aura saman table É—in.


Daga ɗayan ɓangaren cikin sanyin murya a kayi sallama, rai a ɓace Akil yace "Wai Abla baki ganin time ne da zaki kirani yanzu?" Murya kamar zata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Akil wallahi tun karfe 10 nake kiran yaya Imran yaki ɗaukan waya ta" "To naji me kike so yanzu kuma?" "Kuɗi nake so yaya Akil" guntun tsaki yaja kafin yace "Za'a turo" ya kai karshen maganar tare da katse kiran yana faɗin "Da daren nan zaki kira mutun kice masa wani kuɗi gari ba zai waye bane ku baku da aiki sai takurawa mutun, ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗau wayar sa ya fice daga palon ya koma part na su.


_____________________________


*WASHINGTON DC*


Motar Micheal na gaba motar James na bin sa a baya, har suka kai babban titin da zata sada su da unguwar su, wayar James ta fara kara, a hankali yayi parking na motar sa a gefen titi dan hakan yana daga cikin dokan Romeo ya hana su ɗaukan waya suna tuƙi.


Sai da ya kashe motar san nan ya É—auki wayar tare da picking call É—in ya manna wayar a kunnen sa, Jim kaÉ—an ya cire wayar daga kunnen sa, sauri sauri ya tayar da motar tare da juya kan motar da wata mahaukaciyar gudu ya figi motar ya bar layin ya sauka daga titin ya canza hanya, yayin da shi kuma Michael ya É—auki shinfiÉ—aÉ—iyar titin gida.


Kai tsaye unguwar *Adams alley* ya wuce, ka ta faren unguwa ne mai cike da dogayen gine gine, na alfarma masu kayatarwa, kai tsaye wajen wani katon guest house ya nufa, tun bai kariso ba suka wangale masa gate É—in gidan kamar daman sun san da zuwan sa, da gudun gaske ya kutsa hancin motar cikin gidan kamar mara gaskiya, yana shiga masu gadin suka mai da gate É—in suka rufe, kai tsaye parking space ya wuce.


Yana kashe motar ya fito ya shige cikin gidan da yar gudun sa.


Still wan nan ogan nasu ne a wajen shi da wasu mutane, da alama wani abun mai muhimmanci suke tattaunawa, wucewa James yayi yaje ya zauna kusa da ogan nasu.


Cikin harshen turanci ogan nasu ya fara magana "Lokacin yayi da zamuyi Oder makamai a China dan kayan aikin mu sun yi kasa, san nan karku manta Jams kai zaka ja ragamar sayo makaman kamar dai yadda muka saba, ina son mu kai hari mumbai mu tura wa gomnatin su gargaÉ—i ta hanyar boom,

sai magana ta gaba, manyan mutane daga sama sun aiko mana da hoton wani matashin soja mai ji da karfin iko, a yanzu shi yake juya gomnati, suka ce mu kawar da shi dan babban barazane a gare su kasan cewar sa a raye, dan yana aiki da gaskiya kuma shi ci-gaba mutane yake so, mu kuma kun san bama son hakan, mun fi so muga talakawa cikin ukubar rayuwa, James na naÉ—a ka a kan wan nan aikin, kai zaka kashe sojan, dan nasan kai kaÉ—ai zaka iya, zan tura maka hoton sa a WhatsApp sai kayi kokarin cika aikin, idan ka gama aikin kashe sojan ne sai ka jagoranci sayo makamai É—in daga nan sai mu fara shirye shiryen meeting a kan cocaine da zamu shigo da su this year, sai muga container nawa ya kamata mu kawo kuma kasashe nawa ya kamata mu sayarwa"


jinjina kai James yayi tare da miƙe wa tsaye yana faɗin "I'm leaving now, saboda ina da meeting da brother na a gida, kuma bana son su fahimci abun da nake suna jirana ne" gyaɗa kai ogan nasu yayi kafin yace "Okey see you next time" sauri sauri James ya fice daga wajen, dan kar Michael yaje gida yayi ta jiran har ya fara tunanin wani abu, motar sa yaje ya shiga ya ja da gudun gaske ya bar wajen.


Yana cikin tafiya wayar sa ta ɗan yi yar kara alamar shigowar sako, sauke hannun sa ɗaya yayi daga kan staring ya ɗauki wayar yayin da ɗayan hannun nasa ke tuƙa motar,


Ganin sakon ogan sune yasa cike da zumuɗi ya buɗe sakon dan yaga menene zai kashe, a sukwane ya taka wata irinyar mahaukaciyar birki wadda tasa sai da ya buga kan sa da jikin staring motar, waro light ash eyes ɗin sa waje yayi yana kallon wayar, a fili cikin tsawa yace "GAR zan kashe kai ina never" lokaci guda yaji kan sa na sara masa kamar zata fashe, jikin sa har tsuma yake saboda ɓacin rai shiru yayi yana tunanin mafita, dan magana ta gaskiya ko wani ya gani zai cutar da GAR sai in da karfin sa ya kare, yau shi za'a cewa ya kashe GAR da kan sa, ina hakan ba zata yiwuba, gashi duk wanda ya shiga wan nan aikin nasu tofa bai isa yace zai fita ba, yana cewa zai fita to fa kashe shi suke har lahira, shi bama fitar bace a gaban sa ya za'ayi ya ceci GAR ya za'ayi ya sauyawa ogan su ra'ayin a kan su rabu da GAR, dan ya san yanayin aikin su, duk wanda a kasa hoton sa a layin wayan da za'a kashe tofa ba makawa sai sun kashe sa, sosai James ya shiga damuwa da fargaban ya za'ayi ya samu mafita.


Yana tsaka da tunani sai zufa yake yi yayi tsuru tsuru da shi lokaci guda, wayar sa dake hannun sa ta fara kara ala'mar shigowar kira yar firgigit yayi tare da É—ago wayar dan yaga wanene, blood Shine sunan da ya bayyana a kan screen É—in wayar, jikin sa har kerma yake wajen yin picking call É—in tare da manna wayar a kunnen sa, ya tattaro dukkan nitsuwar sa waje É—aya, cikin girmamawa yace "Hello" shiru a ka É—an yi na yan sakanni kafin wata zazzakar murya mai batikar daÉ—i da sanyi yace "I'm on my way" zaro ido waje James yayi muryan sa har sarkewa take wajen furta "Wow, remain how many hours?" Shiru a ka sake yi kamar ba za'ayi reply ba, sai zaro ido waje James yake, can wan nan sexy voice É—in yace "Few minutes" "What? James ya faÉ—a da karfi, katse kiran a kayi ba tare da an sake magana ba, a sukwane James ya ja motar kamar wani zararre ya bar wajen ya nufi gida.


Yana shiga gida ya wuce parking space, yana kashe motar ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu ya nufi cikin gida, gaba ɗaya jubga jingan sojojin nan sai da suƙa tsorata ganin yadda James ke rikice sun san ba lafiya ba


Tun daga kofar babban Palon kasa James ke kwalawa daddy ƙira, a ruɗe daddy da Uncle Herry suka sauko daga sama, suna tambayar lafiya James ke kwala musu wan nan uban kira haka, dai dai lokacin Michael da John da Jay suka sauko suma


a ruÉ—e James yace "Romeo is back" daddy da Uncle har suna haÉ—a baki wajen cewa "What?" Shi kuwa John ihu ya fasa ya nufi hanyar fita a guje "where are you going John?" Daddy ya tambayi John dake kokarin nufar kofar fita, tsaki Jay yaja kafin yace "School zai je mana ina da tabbacin shaidar exam da Hangout zai je ya nemo" shiru Michael yayi yana tunanin yadda zai yi a ransa,


wuce su James yayi ya haye sama ya nufi bedroom na shi, kallon Uncle Herry daddy yayi kafin yace


"Let's go in, ko?" Girgiza kai uncle yayi yana faÉ—in "No let me check first, what and what I did last week might be i did something wrong, i don't know, I want to correct my mistake before lion reach here" wucewa daddy yayi dan shi ma yaje ya duba ko ya aikata wani abun da ba dai dai ba, shi kuma uncle ya nufi waje


kallon tsab Jay yayiwa Micheal kafin yace "To kai me ya tsayar da kai? Ko dai kai ma zaka je ka duba ko kayi wani abun ne?" wucewa Micheal yayi ba tare da yayi magana ba, wucewa shima Jay yayi ya koma bedroom na shi.


_______________________________


*KADUNA*


A toilet din baba mai gadi Imran ya kwana, a nan wajen barcin ya ɗauke sa, saboda donanin nan na ɓacewa dukkan su barcin ya ɗauke su, suma su Abba Akil ne ya tashe su ba dan shi ba da a haka za su kwana, shi kuwa Imran sai da baba mai gadi yazo shiga bayi da asuba san nan ya samu a ka tashe sa,


yana fitowa ya rinƙa tikar amai kamar zai mutu ga jikin sa duk ciwo yake masa, sai dai shima ya manta komai yayi kokarin ko zai iya tuna abun da ya kawo shi toilet ɗin mai gadi amma abun yaci tura dan ya kasa tuna komai, shiru sukayi suna ta mamaki, ita dai Hajiya duk da ta kasa tuna komai hakan bai hana tasa su Imran su mata saukan Al Qur'ani mai girma ba dan tana ji a jikin a koi matsala,


haka ko a kayi Hajiya da Abba suka shirya suka tafi yiwa yan uwan Alhaji Mustapha jajen ɓatan Alhaji Mustapha da Hajiya Zainab, su kuma su Imran suka zauna shi da Akil da Akila suka fara karatun Al Qur'ani mai girma dan su sanu saukin matsalar su.


Bari mu leƙa KANO mu dawo kila kafin nan sun gama karatun.


_______________________________


*KANO*


Daddy na zaune saman sofa shi da Jelly ɗin sa sai buga game suke a Palo, Jelly sai winning na sa take tana ta dariya, shi daman bai san ma me yake taɓa wa ba, saboda damuwa da suka masa yawa


Yayi nisa cikin tunanin da yake wayar sa ta fara kara alamar shigowar kira, da sauri Jelly ta miƙe ta ɗauko masa wayar ta dawo ta miƙa masa, gabyin Engineer Muhammad ne yasa yayi saurin ɗaukar kiran tare da kara wayar a kunnen sa, da kyar ya iya furta "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Engr yace "Waalaikumussalam barka da safiya sir" "barka Engr ya aikin? Ya office ɗin?" Yayi maganar da murya irin na marasa lafiya, cikin zumuɗi Engr yace "Sir gomnati tayi rejected na later da muka tura a kan rejected na contract ɗin nan da muka yi, to suma sun yi rejected sun ki ansa san nan sun haɗo mana da nasu later"


zubur daddy ya miƙe tsaye tare da zaro ido waje yana faɗin "Me suka ce a later?" "Sir ban buɗe later ba ai" tsabar sauri har daddyn Jelly na haɗe words wajen cewa "Ɗauko later ka buɗe ka karanta muji" da sauri Engr ya ɗauko later ya buɗe ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana fatan ka na lafiya, ya kake ya yata Jalila? Ina fatan komai normal Allah yasa haka, ban san dalilin ka na yin rejected na contract nan ba amma koma ne bazakayi rejected ba korafin ka ba zai ansuba dan na sha wahala sosai kafin na samun maka contract nan dan haka dole kayi aikin nan, ka kula kayi aiki da amana kamar tadda na sanka, ban da ha inci na barka lafiya sako daga Hussain" "What? Sako daga wane" daddyn Jelly ya faɗa a razane "Sako daga Hussain" Engr ya mai mai ta masa, "Husaini daman kana raye ina kake? me yasa ka guje mu please ka dawo gare mu muna son ganin ka kaman ta da abubuwan da suka faru a baya dan Allah" "Sorry sir" Engr ya faɗa cikin girmamawa, a sukwane daddy yace "daga ina sakon ya fito?" "Kamar fa daga Dubai ne sir dan ga tambarin kasar a jikin later" cikin sauri daddy yace "a jiye min later da kyau gani nan zuwa yanzu" ya kai karshen maganar tare da katse kiran sauri sauri yace "Jelly ɗauki system ɗin ki shiga bedroom bari naje office ina dawowa yanzu kinji?" Gyaɗa masa kai kawai tayi san nan ta miƙe ta haye saman kujera ta kara tsayi ta manna masa kiss a kumatu, shima ya manna mata a goshi san nan ta sauƙo ta ɗauki system ɗin ta wuce bedroom, shi kuma ya fice daga palon daga shi sai jallabiya amma haka ya fice saboda sauri ba zai iya tsayuwa ya shirya ba, haka ya shiga mota ya bar gidan ya nufi office.


_________________________________


*WASHINGTON DC*


*03:00 pm*


Agogon Washington ta buga, wasu dankara dankaran motoncin 6 ne masu numfashi wadda suka amsa sunan su motoci, a jere motocin nan su danno hancin zuwa cikin gidan su Michael, sai da suka wuce gate 1 gate 2 tayi scanning na su tsab san nan suka wuce suka nufi parking space na gidan,


koda suka je bakin gate É—in parking space É—in, sai da suka tsaya a nan ma wan nan na'uran ta gama kiran numbers É—in motoncin san nan gate na parking space É—in ya buÉ—e suka shiga


suna kashe motocin wasu jibga jibgan sojoji suka fito da yar gudun su, suka kewaye É—aya daga cikin moton cin wadda ke a tsakiya, sojoji ne masu jiki a jika jibga jibga da su, sun samu horo mai kyau fuskokin nan nasu masu firgitar da zuciyar maza babu alamar wasa ko kaÉ—an a tattare da su, jeruwa sukayi a bakin wata dankareriyar mota kirar *Bugatti La voiture noira* wani jebgegen soja ne ya fito daga nashi motar, jibgege da shi mai kiran basawa shima fuskar nan tasa babu alamar wasa, sai sara masa wayan nan sojojin suke, bai kula suba ya wuce ya nufi wan nan motar *Bugatti La voiture noira* ya sanye hannun sa dake cikin hand gloves baka ya buÉ—e kofar motar tare da komawa bayan kofar motar ya tsaya ya É—aga hannun sa É—aya sama ya É—aura saman goshin sa alamar respect, cikin nitsuwa mamallakin motar ya zuro kafafun sa dake sanye cikin bakaken Booth waje, kafin daga bisani ya fito a hankali


yana fitowa sojojin nan suka buga kafa a tare har sai da kasa ya amsa da dum san nan suka ɗaga hannun suka sara wa matashin da ya fito daga cikin motar, sanye matashin nan yake cikin wandon jeans blue da t-shirt ya ɗaura kyakkywan jacket mai ɗan girma zuwa gwiwar hakan yasa t-shirt nasa na cikin bai samu damar bayyana ba, ya ɗaura wani abu mai kama da rawani mai kauri a wuyar sa, san nan ya sanya black face mask a face nasa tare da black glass a idon sa, hannun sa na cikin hand gloves baki, a ta kaice dai baka iya ganin komai na shi sai dark black curly hair sa mai tsawo sosai, ya tara curly hair ɗin ya kulle a bayan wuyar sa ya nannaɗe jelar da kyau ta yadda ba zata masa yawo a bayan sa ba, duk da yana cikin jacket mai girma hakan ba zai hana ka gane cikakken jarumin Namiji bane, yana da tsawo sosai, dan yafi duk sojijin dake wajen tsawo san nan yana da ɗan giɓa kaɗan yana da murɗaɗen jiki sosai, wadda da gani kasan cikekken jarumin sojane.


Zura hannun sa yayi cikin manya manyan aljihun dake jikin jacket ɗin cikin takun ƙasaita irin na jaruman maza ya nufi hanyar fita daga parking space ɗin, a sukwane wayan nan jibga jibgan sojojin suka take masa baya, wow abun gwanin ban sha'awa, taku yake suna take masa baya, duk in da ya saka kafa ɗaya sai suma sun saka, duk wani sojan da suka zo wucewa kusa da shi sai ya sara musu cikin rawan jiki,


su Michael suna tsaye a bakin kofar shiga palo suna jiran sa, suna ganin sa tun daga É—an nesa, nan take suka kara nitsuwa shi kam John jikin sa har kerma yake saboda tsoro, duk cikin su Jay da James ne masu É—an kwari sune tsoron su bai tsanan ta sosai ba.


Har wajen da su Michael ke tsaye sojojin nan suka rako matashin nan san nan suka tsaitsaya a wajen yayin sa shi kuma matashin ya nufi cikin palo kamar bai ga su Michael ba, murya na rawa har suna haɗe baki wajen cewa "Welcome lion" kai kawai ya ɗaga musu ba tare da yayi magana ba ya wuce cikin palon, da sauri suka bi bayan sa, su kuma sojojin suka tsaya a wajen kamar wasu saƙaguna.


Koda suka shigo palon lion baya nan ya wuce bedroom na shi dan a gajiye yake, kallon juna sukayi kafin daddy da Uncle Herry su wuce bedroom nasu


"What is wrong with you John?" James ya tambaya dan yaga yadda jikin John ke rawa kamar mazari, tsaki Jay yaja kafin yace "An fara Exam a school kuma basu yi ba mana shi yasa ya fara kuka tun yanzu tun lion bai damke saba" shi dai Michael ko a jikin sa dan yasan ya riga da yasa uncle na su ya rubuta masa Exam É—in, shi kuma John ba É—aya kanin biyu


wucewa James yayi ya nufi bedroom nashi yana faÉ—in "Johnn you are in big trouble I pity you" tsaki Michael yaja kafin shi ma ya wuce bedroom na shi, kallon sama da kasa Jay yayiwa John kafin ya wuce shina ya nufi bedroom na shi yana faÉ—in "ina fatan lion in ya damke ka ya maka hukunci da sai ka gwammaci mutuwa tun da kunce ku bakuji" durkushewa kasa a wajen John yayi ya dafe kan sa yayi shiru kamar bashi a wajen, ya shiga damuwa sosai mafita.


After some hours


08:00 pm


zaune suke saman katafaren table É—in cin abincin su dake cikin Katafaren palon su, gaba É—ayan su suna wajen kama daga Uncle Herry, daddy Michael, James, John, Jay, sai jibga jibgan Bodyguard masu basu tsaro tsaye a kan su suna aikin su wato basu tsaro da kula da abubuwan da zasu ci da kuma in suna bukatar wani abun sai su kawo musu, kamar irin su tissue paper idan zasu goge hannu ko baki, sai idan suna bukatar shan ruwa ko wine sai su zuba musu, wan nan shi ne aikin wayan nan jibga jibgan Bodyguard É—in masu lafiya da jini a jika, masu fuska kamar wasu zakuna.


"Where is Romeo?" Cewar daddy shiru palon yayi ba wanda ya amsa sai John ne yace "he is inside his room" kallon Michael daddy yayi kafin yace "Michael go and call him, yazo muci abinci mana" "I can't go anywhere dad because I'm tied" ba ƙaramin tsorata duk wani halitta mai rai dake cikin palon suka yi ba jin daddy ya ambaci a kira Romeo, nan take wayan nan jibga jibgan bodyguard ɗin suka kara nutsuwa tsit kamar basu a wajen


daddy na kokarin yiwa Michael magana Jay ya miƙe yana faɗin "let me call him dad" jinjina kai daddy yayi ba tare da ya sake magana ba yana mamakin halin yaran sa kwata kwata basa girmama shi ko kaɗan abun da suka ga dama kawai suke, ɗan gara James ma shine mai ɗan tausayi da saukin kai a cikin su, Michael kam sai dai Allah ya shirya, lion kuma ba'a magana dan nashi yafi na kowa shi karshe ne


wucewa Jay yayi ya haura sama ya nufi wata katafaren kofa launin golden color mai bala'i kyau wadda kamar da gold aka yi ta.


A hankali cikin tsoro Jay ya tura kofar ya shiga, wani katafaren palo ne gari guda, girman palon nan ya kai 1 plot da É—ori, tampatsa tampatsan kujeru ne masu mumfashi set uku a cikin palon launin sky blue, fari, da kuma milk, ko wani set na gefe guda,

ga wani haɗaɗiyar sofa table mai bala'i kyau a tsakiyar kowani sofa set, manya manyan fridge uku ne a palon masu shaƙe da kayan drinks da sauran abubuwa, daga gefe kuma ga wani makeken Tv plasma zaune saman Tv stand, shi kan shi Tv stand ɗin abun kallo ne, dan ya tsaru iya tsaruwa, gaba ɗaya palon gauraye yake da haske kwayayen wuta dake manne a saman POP palon, ba abun da ke tashi a palon sai sanyin Ac da wani fitinannen kamshi mai bala'i daɗi da ratsa zuciya, gaba ɗaya curtains na palon farare ne kal kamar hannun bai taɓa taɓa su ba, saboda haske ma kamar yanzu a ka fitar da su daga cikin ledar su, san nan su kan su curtains ɗin abun kallo ne, dan sun tsaru kai da gani kasan ba wajen wasa kazo ba, kowani sofa set a koi Chinese carpets mai bala'i laushi kamar audiga a tsakiyar su, kowani sofa set Chinese carpet kalan sofar a ka sanya masa, tiles na kasan palon da kuma na jikin bango dukka farare ne kal a ka sanya, tsayawa zayyana muku haɗuwar palon nan lokaci guda ba zai yiwu ba sai dai a rinƙa sako abubuwan a hankali, dan wan nan palon ya wuce tunanin mai tunani, wan na palon shi a ke wa laƙabi da aljannar duniya,


a hankali Jay ke taka kasar palon kamar mai tsoron wani abu haka ya tura wani katafaren kofa ya shiga yana faɗin "excuse" Wow Aljanar duniya part 2 bedroom ne mai girman plot 1, ga wani makeken gado mai girman gaske, tsawon saman kayin kadon nan ya kai 2.1m (miter) kusan girman gini, dan ma dai ginin suna da tsawon 3m ne shi yasa, shi kan sa kayin gadon abun kallo ne, an kawata shi da kwalliya golden color kamar gold ga wasu hasken fitullu masu bada wuta launin sky blue a jikin kayin gadon, kayin gadon round ne (arp) while jikin gadon kuma 4 kwana, daga farkon kayin gadon har karshen sa duk kyawawan fitillun ne masu kyan gaske ke bada wuta sky blue, wan nan katafaren gadon shin fiɗe yake da lausasan bedside da kuma bargo masu laushi kamar audiga, daga bed sheet ɗin har bargon farare ne kal kamar hasken audiga, gaba ɗaya kyawawan bedside drawer, nan wasu kyawawan lamp ne ɗaure a saman su, mirror dake cikin ɗakin nan ma kawai ya isa mutun yayi kauyanci a wajen, kwalliyar saman mirror iri ɗaya ne da kwalliyar kayin gadon wato kamar kwalliyar gadon manya manyan sarakuna ta duniya, haka aka kawata wan nan bed ɗin da artists na shi, saman mirror shaƙe yake da lotions da perfumes kala kala masu kamshi da tsada, ga combs for combing hair and hair cream kala kala shake a wajen kai da gani kasan tsabtar mamalakin bedroom nan ya wuci tunanin mai tunani, mutun ne mai son gyara dan ko ta ina kayan gyara jiki ne saman mirror. Gefe da gefen mirror wasu haɗaɗun show glass ne a wajen ma su ɗan tsawo, ɗaya cike yake da air freshener da perfume na ɗaki kala kala masu daɗin kamshi, ɗayan kuma shake yake da takar su irin su Christian Bible, da dai sauran takardun su, floor tiles na ɗakin farine kal, kamar kafa bai taɓa taka tiles ɗin ba saboda hasken sa, da gani kasan mamallakin ɗakin nan yana son white color sosai dan kusan komai nasa na ɗakin fari ne, kusa da katafaren gadon nan wani hamshakin Chinese carpets ne mai bala'i lausi ga gashi a jikin sa kamar gashin mage wadda kana takawa kafar ka na nitsawa cikin gashin saboda laushi, tsadaddun curtains na ɗakin launin white color ne suma masu bala'i kyau da tsada, a koi ƙofofi guda uku a cikin bedroom ɗin, dukkan su kuma ƙofofin glass ne, ɗaya na toilet ɗaya kuma na balcony, while ɗayan kuma na dressing room ne, bedroom nan ya kawatu iya kawatu wa,

ga wani sky blue haske da fitillun jikin furniture É—in ke badawa hakan ba karamin kara kawata É—akin yayi ba, kwayayen fitillun dake manne a POP bedroom É—in ma dukka hasken wuta launin sky blue suke badawa, hakan ba karamin karawa É—akin kyau da É—aukan hankali yayi ba, ko ina a gyare tsab kamar sabon waje, sai daddaÉ—ar kamshi da sanyin Ac mai ratsa zuciya ke tashi a cikin bedroom É—in gwanin dadi da É—aukan hankali.


Kallon saman katafaren gadon Jay yayi, lion na kwance ya rufe jikin sa har izuwa wuyar sa da lallausan bargon sa mai kama da audiga saboda laushi, while long dark black curly hair sa ya barbazu ya rufe masa kyakkyawan face nashi, baka iya ganin komai na jikin sa, sai wan nan dark black curly hair É—in nasa da ta rufe masa face, da alama barci yake, ya lafe luf a lallausan gadon, yabi lafiyar gadon, ganin haka yasa Jay ja da baya a hankali, kamar mara gaskiya ya fice daga bedroom É—in ya koma Palon kasa wajen su daddy.


Yana komawa ya zauna saman kujerar table É—in yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo É—in ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su.



Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai


đź’žStar Ladyđź’ž


đź’ž TRIPLET'Sđź’ž 17



*đź’žTRIPLET'Sđź’ž*



***



*THE BEGINNING*




đź’ž*STAR LADY*đź’ž





EPISODE 17



*KANO*


_______Daddyn jelly na zuwa office jikin sa har rawa yake wajen amsan later ya fara dubawa ko zai samu address É—in Hussain a jiki, sai dai kash bai samu ba, ba karamin haushin hakan ya ji ba, jiki ba kwari ya juya ya koma gida cike da dana sanin abubuwan da suka faru a baya, sun yasar da É—an uwan su gashi shi kuma bai yasar da su ba yana bibiyar al amuran su yana taimaka masu, gaskiya basu kyau taba, da wan nan tunani ya koma gida.


Zaune tsakiyar gado ya isko jelly tayi É—ai É—ai abun ta ta sanya system a tsakanin kafafun ta sai buga game nata take bata san me duniya ke ciki ba.


Zama yayi gefen gadon yana faÉ—in "My Jelly har yanzu baki gaji da buga game É—in bane?" A sukwane ta É—ago kai da alama bata san da shigowar sa ba, ture system É—in tayi gefe guda ta rarrafo ta faÉ—a jikin sa tana dariya, shafa kan ta yayi cike da so da kaunar ta, yana kokarin yin magana wayar sa ta fara kara


Cikin sa ya ciro wayar daga aljihu sa, dum dum gaban sa ya bada dukan uku uku ganin sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, Baban Muneer cike da damuwa ya ɗauki kiran tare da kwantar da Jelly saman gadon ya miƙe ya nufi waje


Murya na rawa yace "Hello" dogon tsaki baban Muneer yaja kafin yace "Naji duk abun da ya faru wai gomnati sun yi rejected na later da ka tura ko? To ai ba damuwa in sun san wata basu san wata ba, ka buɗe kunnen ka da kyau ka saurare abun da zan faɗa maka, ina son duk wani abun da zaku saya na aiki, ka raba kuɗin biyu ka bani rabi, ma'ana idan zaku saya abun 10k sai ku sayi local na 5k sai ka turomin ragowar 5k ɗin a Account na, na san duk wani abun da zaku saya a wajen aikin nan kuɗin original gwamnati suka baku, to kai kuma da fake ko in ce local zaka musu amfani da shi, sai ka rinƙa turomin sauran kuɗin, kai engineer ne nima engineer ne nasan komai so baka isa ka cuceni ba kana jina ko?" da kyar daddy ya iya buɗe baki yace "Dan Allah Baban Muneer kayi hakuri wan nan abun da kake son nayi zalunci da ha inci ne kuma zan zubar da nutunci na da kuma darajar company ni nane, kowa yasan ni mutumin kirki ne dan girman Allah karka sa na zama maha inci karka zubar min da mutunci" ya kai karshen maganar hawaye na bin kuncin sa, bushewa da dariyar shakiyanci baban Muneer yayi


sai da yayi dariyar mai isar sa san nan ya tsagaita, cike da iya shege ya fara magana "Yanzu maik har wani mutunci ne da kai? Ko ka manta abun da ka aika tane? Kai fa mazina ci ne number É—aya ko shima ka manta ne? To in ka manta na tuna maka, wlh ko kayi abun da nace maka ko kuma ka tsinci video ka a media" yana kai karshen maganar ya katse kiran, dafe kai daddy yayi yana mai dana sanin zuwan sa duniya, wan nan masifa da me tayi kama, yanzu da hankalin sa da ilimin sa na addini zai cuci mutane, sun yarda da shi su bashi aiki a kan ya sayi kaya masu quality amma dan zalunci baban Muneer zai sanya shi cin amana zai sanya shi sayan fake kaya, why baban Muneer, sosai daddy ya shiga damuwa da tashin hankali mai tsanani, a wajen zaune saman sofa barcin wahala ya É—auke sa, dan kwana biyu kenan baya samun barci tunani da damuwa sun hana sa rintsawa, ita ma Jelly barcin ne ya yi awon gaba da ita rungume da system a hannu tana latsawa.




________________________________


*ABUJA*


Kwance Rimsha take saman sofa 3 seater a palon su na kasa, ta kurawa wayar ta wan nan dara daran sleeping eyes É—in nata tayi shiru tana kallon hoton GAR sanye da face mask a face nashi, shi kullun cikin face mask yake ba wanda zai ce ga kalar face na shi na asali, ko a gida bai cika cire face mask na shin ba, duk wanda zai baka hoton sa to cikin face mask za ka ga face nashi


Kamar wadda a ka muntsina ta miƙe da sauri ta haye sama, jim kaɗan ta dawo hannun ta riƙe da cardboard paper da kayan design irin su color da pencil da dai sauran su


Saman sofa table ta É—aura ta karawa wayar ta hasken sa ta kurawa hoton GAR ido, tana kallo tana zanawa, ta dage yau sai ta cire face mask É—in nan nasa da design nata dan taga asalin face na shi


A wan nan halin gwaggo ta fito ta same ta, zama tayi gefen ta tana faɗin "Rimsha anya ba zamu dakatar da ke daga kallon wan nan Christan ba kuwa? Ɗago dara daran kyawawan sleeping eyes nata tayi ta kalli gwaggo da kyau kafin tace "Gwaggo me ya muku kuma?" Girgiza kai gwaggo tayi tana faɗin "A'a Rimsha abun ne naga ya fara yawa kar abun yazo ya zame miki matsala kin san kwakwalwan yaro da riƙe abu" shiru Rimsha tayi ta ci-gaba da zana GAR ɗin ta, kamar daga sama sukaji murya daddy yana faɗin "Nima nayi wan nan tunani, kaunar da Siha ke wa wan nan mutumin yayi yawa kar yazamo mata wani matsalar dan haka dole a dai na kunna shi a gidan nan daga yau na dakatar" a razane Rimsha ta ɗago dara daran sleeping eyes nata ta kalli daddy, yayin da shi ma ita yake kallo, a hankali tayi kasa da kan ta kamar zata yi kuka, ta ci-gaba da zanen ta


wucewa daddy yayi ya nufi waje yana faɗin "Aunty Aisha zan je meeting na yan takara shugaban kasa na zaɓe mai zuwa" da fara'a gwaggo tace "Allah ta bada Sa'a" Amin ya amsa da shi san nan ya fice


Rimsha na tsaka da zanen ta bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata a idon ta ba, sai dai kawai taga hawayen a kan cardboard paper É—in suna zuba, cikin sauri ta sanya hannu a firskar ta dan taji da gasken kuka take, jin da gaske hawaye ne yasa tayi saurin gogewa ta ci-gaba da design nata, nan take taji kan ta na sara mata kamar zai fashe, idan ta tuna daddy yace kar a sake kallon GAR sai taji kan ta ya kara sara mata da karfi kamar zai fashe, a haka ta jure ta ci-gaba da zanen yayin da ita kuma Gwaggo ta kafe Tv da idon ta, tana kallon Arewa 24,


Sosai Rimsha ta kawata kyan GAR a ranta kuma haka ta fito da shi fili ta zana a cardboard paper ta, wow gashi daman ta kware a fannin zanen, abun ba'a cewa komai, zanen yayi kyau over ta tsara kyan sa iya son ranta har da sanya masa pink lips, da pink color na zane ta zana shi ya fita kamar ki kirashi ya amsa, nan take murmushi ya kubce mata ta kura masa ido cikin ranta tana kawata kayan sa yafi haka


Babu ko sallama Jehan ta shigo palon ta fito daga wajen motsa jiki, sanye take cikin wando skin tight baki da riga irin na yan kwallo shi ma baki, sai zufa take haÉ—awa da alama ta motsa jiki sosai, ko kallon in da su gwaggo suke ba tayi ba ta wuce zata haura sama, cikin sauri gwaggo tace


"Jehan ke dai ba zaki dai na wan nan abin ba ko? Wai ma da kika dage kike wan nan shirmen waye ya faɗa miki a gidan nan a koi wan da zai kyaleki kiyi aikin ɗan sandan?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Wai ke gwaggo ina ruwan ki da ni? To sai ki hanani yin abun da nake so ɗin mu gani, aikin ɗan sanda nake so ko kuma aikin jarida, kai ni nafi son aikin ɗan sandan ma kuma zanga wanda zai hana ni, Kinga gwaggo wlh ki fita sabgata idan ba haka ba ina fara aiki kece mutun na farko da zan fara sanyawa a cell in ce kina dillancin kwayoyin maye kuma ba wanda ya isa ya fitar da ke dan har kwayar sai na nemo na sanya miki cikin jaka dan a ji daɗin kama ki" waro ido waje gwaggo tayi tana faɗin "Sabon topic yau kuma, tohh a ina kuma kika koyo wan nan sabon topic ɗin kuma yau? A ba shakka dole ne kiyi aikin ɗan sanda, tun yanzu kin iya shirya sharri kiri kiri a'a Allah ya bada Sa'a Allah baki hakuri ni Aishatu jeki yi wanka da yamma ma ki kara motsa jiki abun ki daga nan sai koyan harɓi, daga nan sai kaki dan duk wani muna furci na yan sanda kam kin iya shi ba sai kin koya ba kai tsaye kawai zaki shiga aiki" sai murmushin dole Rimsha ke musu dan gwaggo da Jehan basu rabuwa kuma basu haɗuwa


Tsaki Jehan taja ta nufi sama tana faɗin "Ai na zaci zaki yi wata magana ne da kin ga yadda ake tsiya kuwa" shiru gwaggo tayi dan tasan halin Jehan ba sauki yanzu sai ta sa hawan jinin ta ya tashi, miƙewa Rimsha tayi tana faɗin "Gwaggo let me go and sleep I'm feeling headache" zaro ido waje Gwaggo tayi tare da jawo ta jikin ta tana faɗin "Sorry Allah ya baki lafiya" ta kai karshen maganar tare da manna mata kiss a goshi, kakalo murmushi Rimsha tayi kafin ta miƙe daga jikin gwaggo ta haura sama ta nufi bedroom nasu


Ko da ta shiga bedroom ɗin nasu Jehan na toilet tana wanka, hayewa saman gadon ta tayi ta kwanta ta shige lallausan bargon ta ta rufe jikin ta dukka har kan ta, san nan ta rungumi zanen GAR da tayi ta fara ruwan hawaye kasa kasa tana faɗin "Me yasa daddy zaka hana ni kallon sa?" Sosai take hawaye wani na bin wani, nan take zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ga bala'i ciwon kai mai tsanani, a haka barcin wahala ya ɗauke ta,


koda Jehan ta fito daga toilet, bata ma lura sa Rimsha É—in ba, ta wuce taje ta shirya cikin jallabiya irin na shan iska nan Black colar, ta saki gashi har baya san nan ya haye saman gadon ta, tajawo wayar ta ta shiga latsawa tana murmushi tana addu'ar Allah ya cika mata burin ta na zama yar sanda.


_______________________________


*KADUNA*


03:00 pm


Gaba É—aya su Abbi suna zaune a Palo Irfan ya gama shirye shiryen tafiya Uk on Monday zai wuce, sai murna yake while su Aafia na taya sa, sai hira suke cike da kaunar juna, kowan nan su fuskar sa É—auke da murmushi.


Da sallama mai gadi ya shigo palon, Abbi da Irfan har suna haÉ—a baki wajen amsa masa sallamar tasa "Lafiya mai gadi" cewar Irfan, cikin girmamawa mai gadi yace "Wani bako ne yazo yace na kira masa matar sa, shine na tambaye sa waye yace bai sani ba idan naje kawai nace a na kiran matar Akil tasan kan ta" tashin sense kallon su Aafia Abbi yayi kafin yace "Yau she ku kayi aure ban sani ba? Dan ku kaÉ—ai ne mata a gidan nan" Jinjina kai Irfan yayi kafin yace da mai gadi "Je kace ya shigo" da sauri mai gadi ya wuce ya koma bakin gate, shi kuma Akil ya dawo da kallon sa kan Abbi cikin nitsuwa ta fara yiwa Abbi bayanin abun da ke faruwa ta sigar da zai fahimter, shiru Abbi ya É—an yi kafin ya É—ago yana kokarin yin magana mai gadi ya dawo bakin sa É—auke da sallama.


"Ina yake?" Irfan ya tambayi mai gadi, Mai gadi yace "Oga yace wai in ce muku idan shiga gidan yake son yi ai ba sai an masa iso ba, ba sai an bashi izini ba yasan hanyar shigowar dan haka bai da niya kawai in ce matar sa tazo yanzun nan ya bata 2mins" shiru Irfan ya ɗan yi na yan seconni kafin yace "Shike nan jeka abun ka, ke kuma Umaisha ta shi kije" Abbi zai yi magana Irfan yayi saurin cewa "Dan Allah Abbi kayi hakuri na yau kawai zan ga gudun ruwan sane" shiru Abbi yayi bai yi magana ba, miƙewa Umaisha tayi jiki a mace cike da jin kunya ta haye sama.


Jim kaɗan ta fito sanye da yar karamar gyale a jikin ta tazo ta wuce su Abbi kunya kamar ta shige cikin kasa haka ta nufi waje, ba karya da Abbi yaji Akil na son Umaisha yaji daɗi sosai ko ba komai zasu kara dankon zumunci, amma sai dai yana tausayawa Umaisha ɗin dan yasan zama surukar hajiya Umaiya ba karamin abu bane sai wanda ya shirya dan masifaffiyar mace ce lamba ɗaya, sai dai duk masifar ta sai ka taɓo ta san nan kuma idan tana son ka zaka ji daɗi dan tana da kyau ta over ga wadda tayi niya, kuma tana da kirki ga wadda take so.


Baki É—auke da sallama Umaisha ta isa wajen sa, yana tsaye jikin motar sa ya bawa gidan nasu baya ya Kifa kan sa a jikin motar kamar mai tunanin wani abu, yau sanye yake cikin dakakkiyar shadda milk color mai bala'i tsada É—inkin ta zauna a jikin sa sosai, half jomfa a ka masa yasha hula kamar ustaz,


jin sallamar ta yasa ya juyo cikin nitsuwa, kallo ɗaya ya mata ya ɗaure fuska sosai kamar bai san Menene dariya ba, a kule yace cikin tsawa "Ki koma kije ki sanya hijabi!! Kuma idan kika kuskura na sake ganin ki ba hijabi sai ranki ya ɓaci!!" Ya karisa maganar kamar zai wanka mata mari saboda haushi, murya na rawa tace "Kayi hakuri yaya Akil bani da hijabi ne shi yasa, duk wanda yaya Irfan ya saya mana na kyautar da yaya Irfan ya koma Zaria lokacin" a fusace ya ɗaga hannu har zai mareta sai kuma ya fasa cikin fushi yace "Shiga mota muje" cike da tsoro tace "Ina zamuje?" Shiru ya mata kamar bai ji me tace ba, ganin haka yasa tace "To bari na faɗa wa su Abbi sai nazo mu tafi...bata kai karshen maganar ba taji saukan mari a kumatun ta, rai a matukar ɓace yace "A matsayin kanwa na mareki ba mata ba, ke har kin isa nace muje kice min ina zamuje, san nan kuma daga yau idan nace kiyi abu kika ce min bari ki tambayo wani Allah sai ran ki ta ɓaci, dan ba wanda zaki tambaya ida zakiyi abu sai nine, nine mijin ki ke mallaki nane, ni kaɗai nake da iko da ke, ba wanda ya isa ya nuna min abun da zan yi a kan ki, dan ke ɗin mata tace!!" Ya kai karshen maganar tare da ciro handkerchief daga aljihun sa ya miƙa mata a kan ta goge hawaye, a hankali ta sanya hannu tana hawaye zata ansa handkerchief ɗin, ganin tana abu a hankali zata ɓata masa lokaci ne yasa, ya sanya hannun sa da kan sa ya goge mata hawayen yana faɗin "A matsayin kan wa nake miki hakan" bayan ya goge mata hawayen da kan sa ya buɗe mata motar ta shiga gidan gaba san nan shima ya zagaya ta ɗayan gefen ya shiga ya tada motar suka bar wajen.


Kai tsaye *ABC supermarket* suka nufa, yana tuki yana zuba mata kashe di da dokokin irin kayan da zata rinƙa sawa, gaba ɗaya yayin cancel ɗin gyale a cikin kayan ta, haka riga da wando yace kar ta sake sawa sai tazo gidan sa, san nan attachment da eyelashes duk ya hana yayi cancel, hijabi har kasa ya yarje mata tarinƙan sawa idan zata je school, dokoki kala kala iri iri ya kafa mata, tare da kashe din idan ta karya masa doka ɗaya zatayi bayani sai ranta ya ɓaci, ita kuwa cikin ranta cewa take "zan dai na duk abun da ka hana amma wlh ban da sa gyale, sai na sa in dai gyale ne sai dai ka kashe ni" shiru yayi bai sake magana ba har suka isa super market ɗin


cike da bada umarni yace "Ki zauna a nan karki yarda ki leka waje" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga Motar ya nufi cikin super market É—in, sai tsaki take ja, a kule tace "Sai an sa gyale mugu kawai"


Haka tayi ta surutan ta ita kaɗai, har ya dawo hannun sa rike da ledoji manya manya guda biyu, ba tare da ya mata magana ba ya ajiye a gidan bayan motar san nan ya shiga gidan gaba, ya tada motar kai tsaye suka wuce *kasuwar barci* a nan yaje da kan sa ya zaɓa mata manya manyan hijabai wadda yana da tabbacin zasu kai mata har kasa, dan a wan nan karon ma a mota ya barta ya hana ta fita, hijabi 12 ya saya mata manya manya har kasa san nan ya sayawa Aafia ma 12 ya wuce ya dawo mota, yana zama wayar sa ta fara kara, guntun tsaki yaja tare da ɗauko wayar ya duba, a nutse yayi picking call ɗin yana faɗin "Sorry Abla na manta ne amma bari na sa miki yanzu, sai yaushe zaki zo ne?" Daga ɗayan ɓangaren Abla tace "Yaya Akil wai ina yaya Imran ne? Sai kiran sa nake amma baya ɗagawa" kallon face ɗin Umaisha yayi ta cikin mirror motar kafin yace "Abla ni bana gida na fita da Auntyn ku amma idan na dawo zan duba miki me yasa baya ɗaukan kiran, amma dai koma me kin dai san ba da gan gan yaki ɗauka bako?" Da sauri Abla tace "Yaya Akil Auntyn mu kuma? Jinjina kai yayi yana faɗin "Eh Auntyn ku" cikin zumuɗi tace "Dan Allah yaya Akil ka bata waya mu gaisa" "Me zaki faɗa mata?" Shagwaɓa murya tayi kafin tace "Kai yaya Akil gaisawa kawai zamuyi" girgiza kai yayi yana faɗin "A'a ai na sanki ne da iya yi" "Kai yaya ba wani iyayi Allah" sanya wayar yayi a hand-free san nan ya miƙa wa Umaisha, jikin ta har kerma yake wajen ansar wayar tana faɗin "Assalamu alaikum" da murna Abla tace "Waalaikumussalam Auntyn mu ina wuni?" Kallon sa ta kasan ido Umaisha tayi kafin tace "Lafiya lou Aunty Abla yasu mama?" kunna motar sa yayi ya ɗauki hanya yana sauraron hirar tasu


Sai murmushi Umaisha ke yi, Abla tace "Auntyn mu waye baban ki? Yar gidan sarki ne ke ko yar governor? Dan nasan yaya Akil ba zai zaɓo mana yar gidan kananan mutane ba" nan take face ɗin Umaisha ta sauya ta dai na murmushi jiki a mace tace "Ni ba...bata karisa ba ya ansa wayar cikin faɗa yace "Abla abun da zaki tambaye ta kenan? Wan nan tambayar ni zaki yiwa ai ba ita ba" murya na rawa Abla tace "Kayi hakuri yaya Akil" tsawa ya daka mata "Abla kullun ina faɗa miki ki ɗauki duniya da sauki ki dai na jin zancen Ammie a kunnan ki baki ji ko? Kullun sai na faɗa miki ki dai na cewa kina kyamar talakawa amma baki ji ko kaɗan ko? Ya miki kyau to ba yar kowa bace yar talakawa ce, kuma a haka nace nake so ko akoi wadda ya isa ya hanani auren zaɓin rai na ne?" Murya har sarkewa yake tace "Kayi hakuri yaya Akil tuba nake" dogon tsaki yaja tare da katse kiran, shiru Umaisha tayi tana tunani "Ashe daman yaya Akil yana da hankali, ashe kawai zafin rai gare sa ba wai rashin hankali ba Allah sarki, Allah ya sassauta masa zafin kan nan da zuciyar nan tasa"


shiru sukayi dukkan su, ba wanda ya sake magana har suka isa kofar gida, ya kashe motar sa ya fito ya É—auka mata ledojin dan yasan ba zata iya É—auka ba


suna shiga harabar gida a nan suka isko Abbi da Irfan da Aafia, suna tsaye cirko cirko saboda da sukaji Umaisha shiru bata dawo ba shi sukazo su leka ko tana wajen ganin bata nan shine suka tsaya suna tattaunawa ta ina Irfan zai je neman ta


ganin su yasa Umaisha ta tafi da sauri ta faɗa jikin yaya Irfan tana ɓoye fuska dan ita a koi ta da kunya sosai, har gaban su Abbi yazo ya ajiye mata ledojin cikin girmamawa yace "Sannu ku ina wuni uncle" da fara'a Abbi yace "Lafiya lou Alhadulillah ina kuka je ne na fito ban same ku ba?" Juyawa Akil yayi ya bawa Irfan hannu yana faɗin "Yanzu dan na fita da matata sai na faɗa wa wani in da na kai ta, wan nan sirrin mune ai" tashin sense kallon Irfan Abbi yayi kafin yace "Ni kam Irfan ko dai ka aurar da Umaisha ban sani bane?" Wuce Akil yayi abun sa ya nufi gate yana faɗin "My wife sai mun yi waya" kallon sa Irfan yayi har sai da ya fice san nan yace "Umaisha ku kwashe kayan kuje ciki" cikin sauri suka kwashe kayan da sauri suka wuce ciki Aafia tana ta kallon Umaisha tana jiran suje ɗaki ta tambaye ta ina Akil ya kai ta


Gyara tsayuwa Irfan yayi cikin nitsuwa ta fara magana "Abbi kayi hakuri haka halin Akil yake muna masa fatan yayi hankali ta dalilin Umaisha mun yi magana da Imran a kan hakan san nan kuma Abbi idan ka lura yaro ne fa 22 years yake da shi" cikin fushi Abbi yace "A'a wlh bai isa ba wan nan iskanci ba zan ɗauka ba, bai isa yazo ya min wan nan iskanci a gida ba ya ɗauki yata lokacin da yake so ya fita da ita san nan ya dawo da ita lokacin da yake so in masa magana yace min shi da matar sa to a yau she ta zama matar sa? Wlh idan yamin tsiya sai na haramta masa auren Umaisha in ga wanda ya isa ya sa na bashi ita, ya koma ya tambayi yaya cikin kannen sa waye mai zafi ma faɗa ci zai faɗa masa, daga yau ka sanar ma sa idan ba zai shigo cikin Palo yayi hira da Umaisha ba to ya bari bana bukata daman bance masa tana neman mijiba kwata kwata ma nawa tace 15 years fa gare ta zai fara koya mata wasu ɗabiun ya sauke min ya daga tarbiyar dana ɗorata to bai isa ba yaya ma yayi kaɗan a kan wan nan zance bare shi, kuma nayi cancelled fita da Umaisha suje wani wajen, idan wani abun yake son nuna mata ko ya saya mata to sai dai yaje shi kaɗai ya dawo ya kawo mata nan!!!" Shiru Irfan yayi dan yasan halin Abbi yana da saukin kai da fara'a amma idan a ka taɓosa yana da zafi sosai, yana da faɗa kuma wan nan karon a kan gaskiya yake faɗar sa dole su nunawa Akil Umaisha na da daraja dole su saya mata kima


Wucewa Abbi yayi ya shige cikin palo ransa a matukar ɓace, jiki ba kwari Irfan yabi bayan sa, ko da ya shiga palon Abbi ya wuce bedroom na shi, shi ma sai ya wuce bedroom na shi jiki a mace.


A ɓangaren su Aafia kuwa, suna shiga bedroom na su da murna Aafia ta fara watsa kayan tana fitarwa, ganin manya manyan hijabai ne yasa taja dogon tsaki ta ture ledojin, ta jawo wan da ya sawo daga super market tana faɗin "Lallai Umaisha kina da babban aiki a gaban ki wan nan hijabai dukka lallai kina ruwa" da sauri Umaisha tace "A'a Aunty Afi muna dai ruwa, dan hijabai ɗin ba nawa ni kaɗai bane, nawa 12 naki 12 ne ai" zaro ido waje Aafia tayi kafin tace "Sannu Uban na wlh bai isa yace zai sani sanya hijabi ba, ina ruwan sa ma dani tab aiko gyalen ma sai na ga daman sawa in ga uban da ya isa ya sani sawa, shegen idon sa kamar na duji" dariya Umaisha tayi tana faɗin "Ni fa da yace naje na sanya hijabi har karya na masa nace bani da su, na ɗauka zai kyaleni yace na ci-gaba da sa gyalen, amma sai na ga akasin haka ya tasani a gaba mukaje kasuwa ya kwaso min wan nan abubuwan dukka dan iskanci" ta kai karshen maganar tare da kwanciya saman gadon, tsaki Aafia taja tana fitar da abubuwan cikin ledojin super market ɗin, chocolate ne kala kala dasu hollandia milk su biscuits sweet da sauran kayan kwalama, nan Aafia ta ware wanda zata ci lokacin ta tattara sauran ta zuba su cikin bedside drawer, ta tasa wadda ta ware a gefe kuma tana ci suna yar hiran duniya.


__________________________________

*WASHINGTON DC*



Jay


Yana komawa ya zauna saman kujerar table É—in yana sauke ajiyar zuciya ba tare da yayi magana ba, tun da daddy yaga haka sai bai tambaye sa ina Romeo É—in ba, yayi shiru suka ci-gaba da cin abincin su.


Kallon Micheal James yayi cikin kulawa yace "My bro bana son ka rinƙa yin irin abubuwan nan da kake yana da kyau kayiwa sauran mata adalci, mum daban suma sauran mata daban, ba dukka suka taru suka zama ɗaya ba, ba wai ina faɗa maka haka bane dan ka kula mata ko wani abu no nima bani da lokacin kula mace kwata kwata a rayuwa ta, ba kuma ina faɗa maka hakan bane ko dan ka yarda da mace ko kuma mum batayi laifi ba, no mum tayi babban laifi, wadda ta cancanci mu tsaneta kuma dole mu kasa yarda da mata saboda abun da mun tayi ta cutar da zuciyar mu ta sa mana tabon da ba zai goge ba, amma yana da kyau ka cire tsanar su a ranka, dan wani lokaci suna da amfani, kuma ina son kayi hakuri ka shirya muje New York mu gaida mum gobe, please na san bata da burin da ya wuce ta gan mu, ba wai dan wani abu zamu je gaishe ta ba sai dan sada zumunci, ba wai dan muna son ta ko zamu yafe mata ba a'a kawai yana da kyau ne muje ɗin, shekara 18 kenan rabon mu da mugan ta fa tun da tazo sau ɗaya daddy ya koreta bata sake zuwa ba why mu ba zamu je ba?" Miƙewa Michael yayi tare da buga table ɗin cikin fushi yace "I told you to stop talking about that human for me!! I said I don't like, wai a na dole ne? Nace bana son jin zancen wata mata ni bani da uwa daddy shi ne kawai duniya ta, karka sake cewa muje wajen wata mummy idan kuma ka sake wlh barin muku gidan zanyi!!!" a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya




Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai


đź’žStar Ladyđź’ž


đź’ž TRIPLET'Sđź’ž 18





***



*THE BEGINNING*




đź’ž*STAR LADY*đź’ž





EPISODE 18



*Washington DC*



a fusace Shima daddy ya miƙe rai a matukar ɓace ya fara magana "be careful James, idan ka sake mana maganar wata shashashar mata a nan sai ranka ya ɓaci, bamu son ta kuma babu in da zaku je, idan ma ka sake maganar ta to sai dai ka nemi wani uban ba ni ba" ya kai karshen maganar tare da rungume Micheal yana rarrashin sa yana ɗan bubbuga masa baya, girgizar kai James yayi kafin ya miƙe tsaye cikin fushi ya bar palon, yana jin haushin abun da mum ta musu da kuma irin tsanar da Romeo, daddy, Michael, Tga, uncle herry, suka mata.


A gefen su Michael kuwa komawa daddy yayi ya zauna shi ma Michael ya koma ya zauna,


"Micheal where is your exam card?" cewar Jay yayi maganar yana tsare Michael da ido, a kule Michael yace "Wai Jay meye ruwan ka da ni ne? A koi wani business ne tsakanin mu?" Dariya Jay yayi yana faÉ—in "Michael baka da gaskiya" a fusace Michael ya buga table É—in ya fara sunfa uwar masifa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba sai dannan sa su daddy suke,

cikin wasa John yace "Kai Micheal is it not our brother? kake masa tsawa haka" cikin fushi Micheal ya danko wuyar rigar John yana kokarin yin magana sukaji takun tafi daga bayan su, wadda ko basu juya ba sun san mai wan nan takun, a sukwane Michael ya saki wuyar rigar John É—in tare da tattara nitsuwar sa waje guda, gaba É—aya palon yayi tsit, duk wani halitta mai rai a palon sai da ta nitsu tsit kamar ba kowa.


A hankali yake sako kafar sa yana taka staircase ɗin kamar bai san taka kasa matashi ne mai jini a jiki farine tas farin Bature dogo ne sosai mai faffaɗar kirjin kamar wani zaki yana da murɗadɗen jiki wadda kallo ɗaya zaka masa kasan yasamu training mai kyau ya koshi da training, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fashe saboda horon da ya ke bawa kan sa, sanye yake da wando guntu 3 cutar hakan ne ya bawa kyawawan kafofin sa bayyana ga wasu gashi dark black mai tsantsi da laushi kwance a kyawawan fararen kafofin nasa har izuwa idon sahu na kafar sa hakan ba karamin kyau ya kara masa ba, yana sanye da riga mai ƙaramin hannu hakan ya bawa tuma tuman ɗamtsen hannun sa damar bayya kamar zasu fashe saboda horo, ga wasu kyawawan gashi dark black sai sheki suke kwance a hannun na sa har izuwa idon sahu na hannun sa, kasan cewar a komai face mask a face nashi baka ganin face na shin sai dai dara daran light blue eyes na shi masu bala'i kyau da ɗaukan hankali gwanin burgewa, yana da dogayen gashin ido kamar ya sa eyelashes, gashin geran sa kuwa a cike suke kamar zasu haɗe saboda cika gasu a kwance luf kamar an zana masa sai sheki da kyalli suke, sai faman lumshe dara daran light blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan dark black curly hair sa da ya sha gyaran nan kuwa ya ɗaure a bayan sa, kaɗan ya zubo masa ta gaban goshin sa, hakan ba karamin kyau ya kara wa face nasa ba, ya kara kawata kyan sa sosai ya fito da face ɗin gwanin ban sha'awa da burgewa, soft skin nasa nan kamar ka taɓa jini ta fito saboda kwanciya da laushin da yayi yaji hutu kamar bai taɓa fita waje ba, kyawawan fararen kafofin sa na sanye cikin wani haɗaɗiyar bedroom slippers mai bala'i kyau da laushi jikin takalman duk gashi kamar gashin jikin mage, san nan yana da dogayen yatsun kafa da na hannu farare tas mai ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga yatsun nashi a koi lallausan bakin gashi mai tsantsi kwance a kan su haka zalika yatsun hannun sa dogaye ne sosai suna da ɗan kauri kaɗan masu ɗauke da kumba (farce) farare tas kamar audiga, yana da kwantatciyar lallausan bakin saje a gefen kumatun sa har izuwa gemun, sai dai bai bar gemu ba,

a hankali yake takowa kan sa na duƙe kan wayar sa kirar *falcon Supernova IPhone 6 pink diamond* wadda a kalla kuɗin ta ya kai ($48.5 million) a hankali yake latsa wayar kamar baya son taɓa screen ɗin wayar, hannun sa na ɗaure da dangareriyar gold watch irin na hannun su Michael sak. Duk in da ya sanya kafar sa, sai wani kyakkyawan ƙaton karen sa dake gefen sa mai suna Brady ya sa na shi kafar.

Brady irin manya manyan karen nan ne masu gashi ajiki sosai wadda yake har kasa duk in da Romeo yayi taku É—aya sai Brady ma yayi taku É—aya, tun bai karisa shigowa palon ba wan nan daddaÉ—ar fitinanniyar kamshin perfume na shin ta kauraye ko wani lungu da sako na cikin palon, sai shakan kamshin bodyguard nasu ke yi suna lumshe ido, dan kamshin perfume na shi number É—aya ne a duniya wajen daÉ—i


```````ROMEO```````

Cikakken namijine mai Jini ajika, lafiyayye kuma kakkarfan jarumi., kaifi É—aya ne ba mai iya tan kwara shi idan ya faÉ—i abu tofa ya faÉ—a ne kome za'ayi baya sauya magana miskiline na karshe baya shiga harkan kowa baya son magana, idan ma yana waje tofa kome zai faru shiru ake ba wadda ya isa yayi magana har sai ya tashi a wajen dan bai san hayani ya, idan baka san shi ba sai kace kurma ne, bai son kallon mace a Area da yake saboda Mahaifiyar sa ya tsani kalmar mace a rayuwar sa kamar yadda ya tsani jin sunan mahaifiyar sa, Allah ya masa farinjinin da mata da maza ke haukan son shi, daga kasashe daban daban yayan manya manyan masu kuÉ—i na duniya na son shi, ta ko ina mata son shi suke suna burin ko sau É—aya ne suga face na shi, sai dai kuma babu macen da ta isa tayo area da yake, saboda ba shi da sauki basu ga alamar face É—in wasa a tattare da shi ba, baya dariya kullun face nashi a É—aure take tamau kamar hadari kamar wadda a ka aikowa da sakon mutuwa, ganin face na shi kawai yana sa hantar manyan maza ta kaÉ—a bare ku ma mata, ganin face na shi kawai tana jirjiza daula, yaci sunan sa da daddy ke kiran sa wato lion, lion É—in ne da gaske,


...Taku yake cikin nitsuwa da kwanciyar hankali Brady na gefen sa suna saukowa tare. Nan take su Johnson suka kara shiga hankalin su, suka nitsu ba su Johnson kawai ba har su daddy uncle Herry duk sun nitsu numfashi ma a hankali suke fitar wa dan gudun kar wani sauti da zai sa Romeo É—ago kan sa daga kan wayar sa ya fita. Saukowa yayi yazo ya wuce su bai ko kalli in da suke ba kamar bai san da zaman mutane awajen ba ya fice ya nufi waje, Brady na biye da shi a gefen sa.


Yana fita suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya a tare, miƙewa Johnson yayi ya ɗan leƙa kofar palon dan yaga Romeo yayi nisa ne ko bai yi ba, ganin babu alamar sa awajen ne yasa ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali ya dawo ya zauna, kasa kasa ya dubi Michael cikin harshen turanci yace "We're finally saved Michael it seems like kana da rabon yin tsere da doki kwanan nan" harara Micheal ya watsa masa kafin ya miƙe ya bar palon yana huci kamar wani zaki shi a dole an ɓata masa rai,


miƙewa daddy yayi ya nufi waje yabi bayan Romeo, a ransa yana faɗin "na sanya maka sunan Romeo da murnana, a tunani na zaka girma kamar Romeo sai kuma nayi rashin Sa'a ka girma kamar lion kwata kwata baka san wani abu wai shi felling ba ba ruwan ka da wani abu wai shi kaunar yan uwa da iyaye kai dai umarni kawai ka iya badawa gaskiya sunan Romeo bai dace da kai ba da tun kana yaro na fahimci haka da na jima da canza maka suna, amma yanzu time ya kura wayyo ni William sai na gama kamar sabon rashin mutunci ya karo tafiyar san nan to ko dai an sake ɓata masa wani aikin ne ya dawo ya sauya gaba ɗaya" da tunani cike fal ransa ya nufi in da yake zaton zai samu Romeo, wato garden


Haka ko a kayi Romeo na zaune a wajen yana latsa wayar sa ya É—aura hannun sa É—aya a saman wuyar Brady yana shafa lallausan gashin Brady É—in, hasken fitullun dake wajen masu bada wuta launin sky blue ba karamin karawa face É—in Romeo kyau suka yi ba, wutar tayi dai dai da kalar idon sa, hakan gwanin ban sha'awa da É—aukar hankali, ga wajen ya kawatu iya kawatu, gwanin kyau.



Kusa da shi daddy yazo ya zauna cikin nitsuwa yace "Welcome My lion" shiru ya É—an yi kafin yace "Tnks" yayi maganar ba tare da ya kalli daddyn É—in ba, "My lion, i want us to discuss something" shiru yayi tare da ajiye wayar dake hannun sa a gefen sa alamar yana sauraron daddy kenan, cikin É—ari É—ari daddy ya fara magana "About your mum i want you to.... Bai kai karshen maganar ba ya dakata saboda juyowa da Romeo yayi a sukwane har sai da kwayar idon sa suka kara shining saboda ya waro su waje sosai, nan take daddy yaji harshen sa ya masa nauyi over, ya kasa ci gaba da maganar


kallon tsab Romeo ya masa kafin ya kau da kan sa gefe, murya kasa kasa kamar mai raɗa yace "get out!!" cikin sauri daddy ya miƙe ya bar wajen, ya koma cikin gida, jingi na kai da jikin sofar Romeo yayi tare da ɗaga kan sa sama kamar mai tunanin wani abun, zuciyar sa na masa zafi daddy ya tuno masa da babban ciwo dake zuchiyar sa wadda baya son tunawa kwata kwata a rayuwar sa, a wan nan hali wayar sa ta fara ringing, yana ji amma bai ɗago ba ma bare ya ɗauki wayar, har kiran ta katse, kira ta biyu ta shigo, hannun sa ya cusa cikin curly hair ɗin sa, yana ɗan shafawa a hankali tare da sauke ajiyar zuciya, kira na biyu ya yanke na uku ya sake shi gowa, a hankali ya ɗauki wayar kamar bai son taɓa wayar haka ya kawota sai tin face nashi tare da waro blue eyes nashi masu kwalli, zubawa wayar kyawawan eyes nashi yayi, na yan wasu sakan ni, sai da wayar ta kusa katsewa san nan ya sanya kyakkyawar yatsan hannun sa yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba, daga ɗayan ɓangaren TGA yace "Hello" shiru Romeo ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba,


A hankali ya furta "What is going on T?" Daga ɗayan ɓangaren TGA yace "tomorrow I will be on my way" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da ya sake magana ba, shiru shima TGA yayi yana jiran yaji me GAR zai kuma cewa


Har Tga ya cire rai da GAR zai amsa masa sai kuma yaji cikin wan nan sayyar muryan nasa yace "safe journey" ya kai karshen maganar ya ajiye wayar a gefen sa ba tare da ya kashe kiran ba, Tga da yaji shiru sai ya katse kiran, shiru GAR yayi tare da lumshe dara daran kyawawan blue eyes É—in nan nasa, kamar mai jin barci yayin da hannun sa ke saman wuyar Brady yana shafawa a hankali.


Lokacin da daddy ya koma palo duk sun gama cin abinci sun watse kowa ya wuce bedroom na shi, yana kokarin wucewa ya haura sama, James ya sauƙo, shirye yake cikin wani ɗan iskan crazy jeans baki sai t-shirt fara tas, ya zuba gold chain a wuya, ya sanya wata haɗaɗiyar Booth a kafar sa baƙa kalar wandon sa a kafar sa, daman shi gashin kan sa bai da tsawo sosai, ba ta kai ya tara ya ɗaure ba dan haka sai ya barta zube kawai, tasha gyara sosai, sai kamshi yake zubawa, kai da gani kasan wan nan wani waje mai mahimmanci a gare sa zai je,


"Where are you going James?" daddy ya tambaya yana duba time a jikin agogon hannun sa, 09:30 pm, a ta kai ce James yace "Party" yayi maganar tare da wucewa da sauri, yana kokarin ciro wayar sa daga aljihun wandon sa, hoton da ogan su ya turo masa a waya ta faÉ—o, dan yaje ya wanke hoton ya mai da ta na cati, É—aukan hoton daddy yayi ya zubawa hoton ido yana kallon face É—in Romeo sanye da face mask "what are you going to do with this pic James?" a sukwane James ya juyo tare da dawowa ya ansa hoton ya nufi hanyar fita yana faÉ—in "is it not my blood brother picture?" Shiru daddy yayi ya haura sama abun sa bai kawo komai a ran sa ba, shi kuma James ya wuce ya fice daga palon ya nufi parking space.


Sauri sauri ya É—auko motar sa ya fice dan kar Romeo ya tambaye sa ina zai je.


Yana fita kai tsaye *Flash dancing club* (gidan rawa) ya nufa, sai da ya kusa isa wajen san nan ya tsai da motar sa a bakin titi ya cire kayan da ya sako daga gida, ya sanya nasu na yan ta'adda, wato irin kayan mai kama da na yakin nan mai É—auke da wukaken ko ta kwana a jikin su, haka ya shirya tsab a kan titi ya cire duk wasu chain da ya sanya a wuya da hannun sa, ya bar agogon su kawai, san nan yasa face mask dan kar wanda ya san shi ya gane sa yazo ya faÉ—a wa daddy da Romeo.


Yana gama shiri ya ja motar sa ya wuce club ɗin, yana parking a parking space na su ya fito ya shige ciki, kai tsaye wani keɓaɓɓen ɗaki ya wuce,

a nan ya isko wasu fafaren Indiyawa suna jiran sa, zama yayi a saman kujerar dake wajen suka fara tattaunawa a kan abun da ya tarasu,


Good 3 hours suka ɗauka suna tattaunawa kafin daga karshe James ya miƙe ya nufi wani ɗan karami kofa dake wajen ya buɗe ya shige, suna zaune suna jiran sa.


Jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata jaka yazo ya miƙa musu san nan ya basu hannu sukayi musabaha tare da yin sallama, ya wuce ya fice daga wajen ya nufi motar sa.


A wan nan karon ma yana fita daga club É—in ya É—an yi tafiya kaÉ—an ya tsaya ya sauya kayan jikin sa ya mai da wanda ya fito da su daga gida, ya shirya tsab kamar yadda ya fito daga gida san nan ya wuce ya nufi gida.


Yana shiga gate na biyu tayi scanning na shi san nan ya wuce parking space, lokacin karfe É—aya sau ra minti 20 na dare.


Ko da yayi parking na motar ya fito sai ya fara lallaɓawa a hankali kamar mara gaskiya, musamman ma da ya shigo palon kasa, a hankali yake sanya kafar sa a floor ɗin dan kar wani yaji takun sahun sa.


Kamar daga sama yaji zazzakar voice an ce "where are you coming from?" A razane ya É—ago kan sa sama, dan ta saman kan sa yaji voice É—in, ganin Romeo tsaye a saman benen a bakin kofar shi ga part na shi ne yasa James sauke nauyayyar ajiyar zuciya a hankali, cike da tsoro yace "from my friend party" shiru Romeo ya masa tare da tsare sa da dara daran kyawawan blue eyes na shi, sanye yake cikin kayan barci riga da dogon wando farare kal masu laushi da kyau da tsada, kayan sun zauna a jikin sa sun anshe sa sosai kamar dan shi a kayi su, a wan nan karon ma a koi face mask a face na shi, dan shi idan ba barci zai yi ba baya rabuwa da face mask dan bai son jama'a su iya tantance face na shi, bai son su iya gane banbancin sa da TGA, dan kwarai suna kama amma suna da ban ban ci ta abu huÉ—u kawai, wan nan dalilin yasa bai son cire face mask É—in, har ya saba abun ya zame masa jiki, ya zamo idan bai sanya face mask ba ma baya jin daÉ—i.


Da wan nan daddaÉ—ar sexy voice É—in nasa mai kwantar da hankalin mai sauraro cikin nitsuwa yace "From today i forbide any body in this house going to party anymore" cikin girmamawa da rawan jiki James yace "Okey bro" sai kerma irin na marasa gaskiya jikin sa ke yi, duk a ruÉ—e yake, sai zufa yake duk da sanyin Ac dake ta shi a palon kirjin sa sai dukan uku uku yake, tsabar tsoro har kan sa na sara masa kamar zai fashe.


Juyawa Romeo yayi cikin nitsuwa ya taka ya koma cikin part na shi, ba tare da ya sake yiwa James magana ba, da sauri James ya haura sama har yana haÉ—awa da gudu, kallon É—aya zaka masa a wan nan yanayin da yake ciki kaga asalin mara gaskiya, yana shiga bedroom na shi ya faÉ—a saman gadon sa ko takalman kafar sa bai cire ba kirjin sa sai dukan uku uku take, yana murna da ya samu ya kubcewa Romeo, dan yasan ba dan dare bane yanzu da sai Romeo ya kama shi sai ya gano shi, saboda Romeo a koi shi da kaifin kwakwalwa da basira, ga saurin gane abu, ba'a banza yake The general of the army gaba É—aya ba.

Saboda tsorata da James yayi da kyar barci ta É—auke sa ko takalmin kafar sa bai cire ba bare aje ga zancen wanka da sa kayan barci, ya tsorata sosai dan ya san halin Romeo bai da wasa, kana wargi kaÉ—an zai kama ka.


*NIGERIA,*


*ABUJA*



Wasa wasa zazzaɓi ne mai zafi ya rufe Rimsha tana rubgume da zanen da tayi na GAR haka mum ta shigo ta same ta, a tsorace ta kira daddy, lokacin already ya dawo yana gida, yana zuwa ya taɓa jikin ta zafi kamar wuta, hannu yasa yana kokarin ansan zanen da ta rungume, cikin magagin barci da zafin zazzaɓi ta fara sambatu ta kankame zanen sosai tana faɗin "Jehan dan Allah ki kyale min zane na daddy ya hanani kallon GAR a Tv yanzu zanen kawai ya rage min duk wani video sa dake wayata zan goge dan ba zan iya kin bin maganar daddy ba, dan Allah ki kyalemin zanena idan kika ansa Allah zan iya mutuwa, ni GAR yana matuƙar burgeni dan Allah ki kyaleni"


Cike da tashin hankali daddy ya ɗago ya kalli mum wadda ita ma shi take kallon, tashin sense ja da baya kaɗan yayi murya kasa kasa yace "Munyi kuskure, mun yi kuskure tun farko da muka bar Rimsha tana kallon wan nan kafurin yanzu saboda na hanata kallon shi ne har zazzaɓi ya kamata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun tab ɗi jam a koi matsala" matsowa Mum tayi ta dafa sa tana faɗin "To yanzu me mafita?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Mafita shi ne mu kyaleta ta ci-gaba da kallon sa, a hankali mu raba ta da shi, idan muka ce zamu raba ta da kallon sa lokaci guda zata iya cutuwa kin dai ga alama yanzu to, ba zai yiwu mu ce lokacin guda ta dai na kallon sa ba, idan mukayi hakan mun zalunce ta, kuskure dai mun riga mun yi sai dai mu kiyayi gaba ki san yadda zaki yi kina zare mata abun a ranta a hankali hankali har ta rabu da abun dukka, yanzu zai wuce da ita hospital kome yake ciki zamuyi waya" ya kai karshen maganar tare da komawa wajen ya duƙa ya sameta cak a kafaɗar sa suka nufi waje sai sambatu take ga jikin ta zafi kamar wuta


jiki a mace mum tabi bayan su ta wuce bedroom nata, while gwaggo da Jehan kuma suna É—akin gwaggo basu san meke faruwa ba, ita ma mum tazo dubasu ne ta samu Rimsha cikin wan nan hali.


Kai tsaye hospital daddy ya wuce da ita, suna zuwa a ka anshe ta hannu bibbiyu, a ka fara bata taimakon gaggawa, shi kuma daddy sai yawo yake a bayan A&E yana tunanin mafita.



*KADUNA*



zaune suke gaba É—ayan su suna hira while Imran yana aikin latsar waya yana kallon hotunan Jelly,


cikin natsuwa Abba ya fara magana "Imran yaushe zaka koma school?" Ɗagowa Imran yayi daga kallon wayar nasa da yake cikin girmamawa yace "Next week zan koma" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Kai kuma fa Akil?" "Tare zamu wuce da Yaya Imran In Sha Allah sai mu rabu a Germany ya wuce nima na wuce namu School ɗin" Abba na kokarin yin magana Akila ta rigasa cikin shagwaɓa tace "Abba dan Allah nima zan bi yaya Imran, na gaji da karatu a Nigeria" Shafa kan ta Abba yayi tare da jawota jikin sa yana faɗin "Ba komai heartbeat zaki je amma ba yanzu ba sai kin kammala secondary ki san nan kije kiyi jami'a a can" kara lafewa tayi jikin Abba tana mai kaunar iyayen ta da yan uwan ta, Akila kenan heartbeat na kowa dake cikin gidan, har da masu bawa flowers ruwa da mai gadi duk kaunar ta suke, kowa son ta yake, ba iya gidan ba duk wan da ya zauna da ita sai ya so ta saboda kyan halinta da kaunan jama'a ba ruwan ta da rigima ga girmama mutane, tana son zaman lafiya, ga fara'a kowa na tane


Tana kwance jikin Abba ta jiyo wayar ta na ringing a bedroom na ta, da gudu ta miƙe ta haye sama ta nufi bedroom ɗin, wayar na gab da katsewa ta shigo, hannun ta har rawa yake wajen yin picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta cike da zumuɗi tace "Bappa ina wuni" daga ɗaya bangaren muryan Jelly ta daki dodon kunnen ta cikin kauɗi tace "Aunty Akila ni ce ba daddy ba" daɗi kamar Akila tayi ihu sai murmushi take bakin ta yaki rufuwa, ta kasa ɓoye murnar ta, cike da kaunar yan uwa ta tace "Jelly na ya kike ina kewar ki sosai yar uwata" a bangaren ita ma Jelly bakin ta ya kasa rufuwa saboda murna da farinciki ji take kamar tayi tsuntsuwa tazo ta kalli Akila, tana matikar son Akila over,


haka suka rinƙa hira Jelly na zuba mata shirme ita kuma tana biye mata, almost 1 hour suka ɗauka suna hira sai murmushin da dariya Akila keyi ji take kamar ta koma gidan su Jelly kawai da zama, sun kasa yin sallama da juna har sai da daddy ya anshe wayar suka gaisa da Akilan san nan ya katse kiran


Yana katsewa Akila ta fara ƙoƙarin neman layin su Umaisha dan su gaisa, sai dai kash a rufe tasamu layin, haka ta hakura ba dan taso ba, tana bala'i kaunar yan uwan ta sosai, rashin samun su Aafia a waya bai mata daɗi ba ko kaɗan amma haka ta hakura ba dan taso ba, ta miƙe jiki ba kwari ta fice ta koma Palo


Ko da ta dawo palon, yaya Imran da Akil duk sun tafi basu a palon sai Ammie da Abba, da suka zubawa Tv ido sosai suna kallon, yanzu sun samu saukin wayan nan dodannin dake zuwa musu kasan cewar su Imran na yawan yi musu karatun al Qur'ani mai girma a gidan, shi yasa tun ranar da suka ɓace basu sake dawowa ba, daman saboda tafiyar su Imran kano ne yasa abubuwan ke zuwa dan ba'a karatu kuma ba'a kunna kira'a, daman Abba da su Imran ke kunnawa, to shi Abba ya dawo ya samu bala'i ne shi yasa bai samu damar karatun ba, dan ita dai Hajiya Umaiya bata wani yin karatu Al Qur'ani sharholiyar ta kawai take, san nan faruwar wan nan abun yasa Hajiya Umaisha ta yi hankali sosai, ta rage wasu abubuwa yanzu duk wani hakkin miji tana kokarin ta sauke sa dan tsoron dodannin, yanzu ta dai na masifa da faɗa ta koma so silent kamar ba ita ba, daman shi kam Abba shiru shiru ne baya shiga har kan kowa abun da ke gaban sa kawai yake, haka suka koma ratuwar farincikin su kamar yadda suka saba.


*ABUJA*


Sosai a ka bawa Rimsha kulawa har sai da suka tabbatar ta dawo dai dai, daddy ya shiga damuwa over ji yake kamar zai yi kuka saboda kaunar da yake wa Rimsha gashi ta jefa kan ta cikin wahala.


Basu bar hospital ba sai da daddy ya tabbatar da tasamu lafiya sosai san nan ya ansa magungu nan ta ya wuce ya suka shiga motar sa suka bar hospital É—in, Rimsha ta samu sauki dan da kafar ta ta taka zuwa wajen motar daddy.


Suna isa gida, suka isko mum gwaggo da Jehan a Palo zaune cikin damuwa ko wani hali Rimsha ke ciki, mum na ganin su ta miƙe tana faɗin "Ya jikin nata dai?" kallon face ɗin Rimsha daddy yayi kafin yace cikin zolaya "GAR ya bamu magani ai" cool murmushi Rimsha ta saki har sai da dimple nata ya lotsa open teeth nata ya bayyana ga hakoran nata a jere tsab sai kyalli suke kamar gonar audiga, hakan ba karamin kyau ya karawa kyakkyawar face nata ba, duk da cewa ta ɗan rame saboda zazzaɓin, sleeping eyes nata sun kara haske sosai sun kara girma saboda yar ramar da tayi. Riƙo hannun ta gwaggo tayi suka haura sama dan taje ta mata wanka ta huta, wucewa daddy yayi ta nufi bedroom na shi yana faɗin "Ina son magana da ke boɗɗi" cikin sauri mun tabi bayan sa ita kuma Jehan tabi su gwaggo.


Zaune bakin gado ta isko sa yayi shiru kamar mai tunani wani abun, "lafiya daddyn Jehan?" Mum ta tambaya dai dai lokacin da take zama a gefen sa, dogon numfashi yaja tare da sauke wa a hankali ya ɗan juyo suna fiskantar juna "Wallahi ba lafiya ba" zaro ido waje mum tayi tana faɗin "Meke faruwa to?" Riko hannun ta daddy yayi ya fara magana cike da damuwa "kwana ki na ta tafiya zaɓe na ta kara gabatowa ni kuma sai kara samun baraza nake daga abokan ha mayya, baraza ta ko ina nake samu abun ya fara affecting ɗina na fara karaya, dan wasu ma ban san daga ina suke min barazanar ba, ina tsoron kada na jefa rayuwar ku a cikin haɗari bana son abun da zai taɓa min ku bana son tashin hankali ku, ina ganin zan hakura da siyasar nan kawai" cikin sauri mum tace "A'a barkama ni ban yarda da ka hakura da siyasa ba, kasan cewar adalin mutun irin ka mai gaskiya a siyasa babban nasara ne ga yan kasa, kana da tausayi kuma zaka taimakawa talakawa, na sani siyasa babban haɗari ne dan ba kowa yake son cigaba al'umma ba, amma jajirtattun mutane ire iren ka masu son tai makon talakawa bai kamata ku rinƙa karaya kuna sarewa haka ba, kama ta yayi ku rinƙa karawa kan ku kwarin gwiwa, na san cewa rayuwa a matsayin mai gaskiya yafi komai wahala a duniyar da muke ciki yanzu, dan dayawa daga cikin mutane sun ajiye gaskiya sun bi karya da ha inci a guje suna son kamawa su runguma, wasu ma har sun kama sun runguma ɗin sun yar da gaskiya, kayi rayuwa ba tare da cutar da wani ko tauye hakkin wasu ba yafi komai wahala a duniyar yanzu, babu mai tai makon ɗan uwan sa, jama'a da dama sun manta lahira sun rungumi duniya hannu bibbiyu, jama'a da dama sun manta cewa wanda ka bayar shi zaka tarar a lahira wanda kuma kaci a nan duniya zaka barshi, dan Allah barkama ka karawa kan ka karfin gwiwa wajen ganin ka tsaya tsayin daka ka ceto mana kasar mu, muna bukatar adalin shugaba irin ka, kasar mu na bukatar jajirtattun maza irin ka, aikin Allah na da wahala, ba'a shiga aljanna a na kwance a gado, duk wanda Allah keso da Rahma to sai ya jarrabe shi da wani abun, to ka ɗauka duk wan nan barazana da abokan hamayya suke maka jarabawa ce daga Allah, kuma ka dage ka ci jarabawar, san nan ka zauna da kowa zuciya ɗaya" duk wan nan hiran da suke cikin harshen turanci suke yin sa,

dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin yace "Kin san me?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a "Meeting da naje ɗazun sai da nayi dana sanin shiga ta siyasa, saboda a fillin Allah wasu daga cikin manya ke min baraza a kan na janye tun yanzu abun ya tsorata ni, shi yasa nake tsoron kar na jefa rayuwar ku cikin haɗari" kwanciya mum tayi a jikin sa cikin sigar soyayya ta fara magana "Barkama ka sani fa kafin mutun yaji daɗi sai ya sha wahala, musamman ma mutun mai zuciyar gaskiya irin naka to fa sai ka daure ka kawar da kan ka daga kan wasu abubuwan idan ba haka ba bazaka taɓa cin ma nasara ba, a zamanin yanzun nan duk wanda yace zai fito fili ya nuna cewa shi gaskiya yake so tofa makiya ba zasu taɓa bari ya kai labari ba sai ya dage da kai wa Allah kukan sa, yanzu dai ka manta da komai ka ci-gaba da gwagwarmayan ka kana addu'a muma zamu taya ka, In Sha Allah ba dai ɗan adam ba, sai Allah ya cika maka burin ka na ganin ka taimaki talakawa kuma ka raya mana kasar mu ta girma kamar sauran manya manyan kasashe na duniya In Sha Allah" ta kai karshen maganar tana riƙo hannun sa, murmushi ya saki har sai da dimple nashi ya lotsa, cike da so da kauna yace "Shi yasa nake son ki matata duk lokacin da na shiga damuwa kin san yadda zaki yi ki kwantar min da hankali, duk wata natsala ta idan na kawo miki, ba za'a fi 10mins ba kike samo mana mafita, Allah ya miki albarka ki taya ni da addu'a In Sha Allah burin mu zai cika bari naje nayi wanka yanzu na fito sai mu ci-gaba da hirar ko?" Gyaɗa masa kai tayi tana faɗin "Amin ya Allah" ta kai karshen maganar tare da tashi daga jikin sa, miƙewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta miƙe ta wuce wajen drawer kayan sa ta ciro masa kayan sawa da duk wani abun da zai buƙata ta dawo ta ajiye masa a bakin gado san nan ta haye saman gadon ta kwanta tana tunanin rayuwa.


After some days


*KADUNA*


A yau Akil yazo yin sallama da Umaisha zai koma makaranta, sanye yake da manyan kaya wato wata dakakkiyar yadi navy blue mai bala'i kyau da tsada, É—inkin half jomfa, kayan sun masa kyau, yau ma kamar kullun tsaye yake a kofar gida bai shiga ba, ya bawa gidan baya ya kifa kai da jikin mota kamar dai kullun, ya aiki mai gadi da ya kira masa matar sa, ko da mai gadi yaje Abbi baya nan ya tafi company shi kuma Irfan ya wuce Uk tun kwana biyu da suka wuce, gidan ya rage daga Umaisha sai Aafia, koda mai gadi ya sanar da su sakon Akil sai Umaisha tace "Kaje kace masa Abbi yace ya shigo ba zan kara fita ba" tayi maganar cike da tsoron abun da Akil É—in zai mata sai dai kuma ta sawa ranta ko kashe ta zai yi bazata ki bin umarnin Abbin ta tabi na Akil É—in ba.


Ko da mai gadi ya isar masa da sakon da Umaisha tace, ko kaÉ—an Akil bai damu ba, ba musu ya shigo cikin gidan, kallon É—aya zaka yiwa face nashi kasan yana cikin damuwa yau he look so silent kamar ba shi ba, bakin sa É—auke da sallama ya shigo palon already Aafia ta bar palon tun tafiyar mai gadi.


Cikin sanyin murya Umaisha ta amsa masa sallamar, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan sa tare da zama saman sofa, murya kasa kasa kamar mara lafiya yace "Jeki sanya hijabin ki kizo" da sauri tace "Yaya Akil a cikin gida ne fa ba waje ba" tsare ta yayi da ido na yan mintoci kafin yace "Ban isa in ce kiyi abu bane?" Girgiza masa kai tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom na su, ajiyar zuciya ya sauke tare da jingina kan sa da jikin sofa,


Jim kaɗan ta dawo cikin hijabi yana ja har kasa ɗan nesa da shi ta zauna tana faɗin "Ina wuni" tayi maganar tana kunbura kumatu, ɗagowa yayi ya zuba mata ido kasa kasa ya fara magana "Dan nace ki sanya hijabi ne kike ɓata rai haka?" Shiru ta masa tana jin haushi a zuciyar ta "Ina son ki sani duk macen da bata ɗauki hijabi a matsayin sutura ba ni a waje na da ita da dabba duk ɗaya ne, bana son mace da bata suturta jikin ta, bana son macen da bata daraja kan ta, hijabi shine darajar ya mace, ina son mace wayayyiya amma ba ballagaza ba, idan nace wayayyiya ina nufin mai wayewa irin ta addinin musulunci, ina matsayin yayan ki, kuma mijin ki, amma a yadda muke ni ban yarda da na rinƙa kallon ki haka ba hijabi ba, kuma ban kawo sadakin ki ba koda kuwa a cikin ɗakin uncle ne ba a palo ba, ina son kullun na ganki da hijabi har kasa idan nazo, yau bana jin daɗi jikina, bana son yawan magana dole ne yasa nazo miki sallama, ina son ki sani wallahi idan na tafi kika karya doka ɗaya daga cikin dokokin dana sanya miki wallahi 6 hours ya isa ya kawo ni in da kike, idan kuma nazo in ran ki yayi dubu sai na ɓata miki, san nan ki faɗa wa Uncle idan na dawo na nitsu zan kawo sadakin ki na ɗauke ki mu koma tare, abu na gaba ki faɗa wa Uncle ya dai na samin wasu dokoki tsakani na dake dan ke ɗin matata ce ko suna so ko basu so, dole ke matata ce, yanzu ma na shigo gidan nan ne ba dan komai ba sai dan bani da lafiya banason yawan hayaniya, amma daga yau ni ba zan sake shigowa ba, shi yasa ma ina dawowa zan kawo sadaki na ɗauke ki dan ba zan iya wan nan abun da uncle ke min nan ba" ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ciro kuɗi daga aljihun sa masu yawa rafar 500 ya ɗaura mata saman hannun sofa ya nufi hanyar fita "Yaya Akil meke damun ka?" Cak ya tsaya tare da juyowa ya zuba mata ido, ganin bai amsa mata ba yasa ta sake mai mai ta tambayar, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nima ban sani ba kawai bana jin daɗin jiki nane gaba ɗaya na rasa meke min daɗi" miƙewa tsaye tayi ta nufo sa tana faɗin "To kasha magani ne?" Zuba mata ido yayi ya kasa ɗauke idon sa daga kan ta, tun da yake bai taɓa tsayuwa ya kalli face nata da kyau ba sai yau, wow shine ka ɗai abun da yake furtawa a ransa,


har ta iso gaban sa bai sani ba, cikin girmamawa tace "In kawo maka maganin zazzaɓi" girgiza mata kai yayi ala'mar a'a san nan ya juya ya nufi hanyar fita.

Kukan shagwaɓa ta sa masa tana faɗin "To shi ne zaka tafi kuma bayan idan ka tafi yau sai bayan kusan shakara kafin na sake ganin ka" mamaki ne ya kama shi, a sukwane ya juyo cikin tsawa yace "Ke ni bana son munafurci yanzu kukan me kike?" Cike da tsoro tace "To ba kai ne zaka tafi ba kuma ni ban gan ka sosai ba idan ka tafi ya zan yi?" A fusace yace "A baya da baki sanni ba ya kike yi?" cak ta tsayar da kukan nata ta zuba masa ido, guntun tsaki yaja tare da wucewa abun sa, ya bar ta nan tayi mutuwar tsaye.



Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai


đź’žStar Ladyđź’ž