TRIPLETS (YAN UKU) BOOK 1 CMPLT

28-29

by @queenofsurprise1

💞TRIPLET'S💞




💞 FATEEMA MUSA💞

(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_





WhatsApp me for more information ***







Episode 28




Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa, cikin sauri ya kariso wajen ya sanya hannun sa ya ɗaba Amal ɗin, shiru bata ko motsi, su Aafia basu sani ba, sanya hannun sannan da yayi, ya kwashe dafin da ke jikin tane, ba dan haka ba suka taɓa ta mutuwa zasu yi suma.


Munafiki nan fa ya sanya musu kukan munafurci yana faɗin "Amal bata numfashi, Amal bata tare da mu, Shikenan munshiga uku" Aafia ta kasa magana ganin abun take kamar mafarki, ita kuwa Rufee ihu ta sa ta duƙa tana girgiza Amal ɗin tana kiran sunan ta, baya baya Anisa ta fara yi tana hawaye, ganin abun ita ma take tamkar a mafarki.


Shikuwa Man yana tsugunne sai kuka suke shi da Rufee, kan kace me jama'a sun taru a wajen, nan fa a ka ɗauki Amal a ka wuce da ita Hospital, a in da likita ke tabbatar musu da cizon maciji ne ya kashe ta.


Haka a ka ɗauke ta zuwa gida, dan aje a sallace ta a kai ta gidan ta na gaskiya, Aafia tsabar tsorata ta kasa driving na motar ta da kan ta, ta kai kan ta gida, sai dai Anisa ce ta jata zuwa gidan nasu.


Ko da ta shigo palo, a zaune ta samu Aunty tana kallo a Tv, taci kwalliyar ta kamar yadda ta sama tana zaune ta aza kafa ɗaya kan ɗaya.


Ganin Aafia wata zololo da ita jiki ba kwari ko sallama bata yi ba ta shigo palon, ba karamin ɗagawa Aunty hankali tayi ba, cikin sauri Aunty ta miƙe tsaye tana faɗin "Aafia lafiya meke damun ki" kuka Aafia tasa tare da zama saman sofa, dai dai lokacin Umaisha ta sauko kasa cikin shirin ta zata wuce school, jikin ta na sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga A shape ta sanya karamin gyale a kan ta sai kamshi take zubawa.


Da yar gudun ta, ta kariso cikin palon ganin Aafia na kuka, ita kan ta Aunty sai da taji jikin ta ya mutu, yau dai Aafia ke kuka to me ya faru da ita, ita kuwa Aafia kuka take tsakanin ta da Allah kamar yarinya karama, dan ta tsorata sosai shi yasa ma ta kasa zuwa gidan su Rufee ɗin, ba zata iya ganin sallar jana'izar Amal ba, hakan yasa ta nemi dawowa gida kawai.


Rungumeta Umaisha tayi tana faɗin "Aunty Afi lafiya meke faruwa?" Cikin kuka da kyar Aafia tace "Umaisha Amal ta mutu, Amal ta mutu Umaisha" zaro ido waje Umaisha tayi cike da tsoro tace "Ban gane Amal ta mutuba, ai na ta mutu ɗin? Ko dai mafarki kike ne?" Kara sautin kuka Aafia tayi tana faɗin "Umaisha da gaske nake wlh Amal ta mutu yanzu nan muna zaune da ita kawai tayi ihu ta faɗi kasa, sai gawa, an kai ta asibiti, dr yace saran maciji ne ya kashe ta, kuma su guyson sun duba ko ina a wajen basu ga snake ɗin ba" salati Aunty tasa tana faɗin "Kiyi hakuri ki mata addu'a ne kinji Aafia" cikin kuka Aafia taje dogon tsaki kasan cewar already Rufee ta shiga tsakanin su da Aunty ɗin kome zata musu ba zasu taɓa ganin farin taɓa.


Miƙewa Aafia tayi ta haye sama ta ci-gaba da kukan ta, ita ma Umaisha saman ta koma dan ta fasa zuwa school ɗin, dan lokaci guda itama tsoro ya kama ta, sai dai gani take kamar Amal bata mutu ba, tana raye, ita dai Aunty addu'ar nemawa Amal Rahma wajen Ubangiji tayi sannan ta koma ta zauna taci gaba da kallon ta, tana mamakin hali irin na su Aafia.


💞JELLY💞


Ba laifi jikin nata ya samu sauki sosai dan har ta farfaɗo, sai dai kuma me ta mance komai she lost her memory, saboda buguwar kai da ta samu, amma likita yace idan ta haɗu da abun da ya taɓa faruwa da ita a baya ko kuma wani da ta sani zata komawa dai dai, yanzu duk wani abun da wannan Hajiya ta tambaye ta sai tace bata sani ba, sai dai kuma still wannan shagwaɓa da bakin surutun nata yana nan bai mutu ba.


Haka dr ya sallame su, suka wuce gidan Hajiyar da Jelly, gida ne babban gida irin na manya manyan atrajirai masu faɗa a ji a kasar, mata huɗu ne a cikin gidan, gaba ɗayan su suna haɗe waje guda, ma'ana ba amusu part part ba, part ɗaya a kayi, mai ɗauke da katafaren palon kasa, to daga palon kasan ne zaka iya wucewa Part ɗin duk wanda kake so, amma duk a cikin palo guda.


Kai tsaye ɓangaren ta Hajiyar nan ta nufa da Jelly, sai kallon gidan Jelly ke yi kamar bata taɓa kallon wani abu makamancin hakan ba, suna shiga ta kai ta wani haɗaɗɗiyar bedroom mai bala'i kyau, yaji komai da ake buƙata.


Sai da ko da ta kai ta zata fita sai Jelly tace bata san wannan ba, ita dai Hajiya bazata fita ta barta ba, sai dai su zauna tare, sosai Hajiya ta lallaɓata tace taje tayi wanka tazo taci abinci, nan fa Hajiya taga ikon Allah dan kuwa Jelly dai ba abun da ta iya ga bala'i shagwaɓar tsiya ,ga bakin surutu kamar reza.


Kuka ta sawa Hajiya kamar yar karamar baby, dama yaya lafiyar kura bare tayi zawo, daman ita Jelly da lafiyar ta ma ya a ka kare da ita bare kuma an samu matsala ta manta komai tayi losing memory ai sai dai abun da hali yayi, sai hakuri kawai.


Haka Hajiya ba dan taso ba ta shiga toilet tayiwa Jelly zan kaɗeɗiyar budurwa wanka, ita a tunanin ta saboda matsalar da Jelly ta samu ne yasa ta zama haka, bata san cewa dama already jelly kam haka take ba.


Kayan da Nawid ya sai mata lokacin da suke hospital Hajiya ta sanya mata ɗaya daga ciki, sannan ta riƙo hannun ta suka fito palo dan ta zuba mata abinci sai taje itama tayi wanka ta ɗan miƙe.


Koda sukazo palo ta zubawa Jelly abinci tace taci, kafin ta dawo bari tayi wanka, kuka Jelly ta sanya mata tana faɗin "A'a ni karki tafi ki barni" Hajiya dai taga abun da yafi karfin ta, tunani ta fara yi karfa Jelly tace da ita zata kwana a ɗaki, in ko haka ne shi kuma Abbon Nawid ta kai shi ina kenan, tab lallai a koi babban matsala.


Haka Hajiya ta hakura ta zauna ta fara bawa Jelly abincin a baki, dan Jelly taki yarda taci abincin da hannun ta, wai sai dai a bata a baki, hakako Hajiya ta hakura ta rinƙa bata abaki, jelly na ci tana wasa, dan da alama abincin bashi a kan ta, ba yinwa take ji ba.




💞WASHINGTON DC💞



Zaune Romeo yake kusa da daddy saman bed ɗin dad, hannun sa riƙe da cup da kuma drugs, ya tsare dad da wayan nan dara daran idon nasa, yana jiran dad ya shanye drugs da ya bashi, sai faman kwaɓe fuska dad yake alamar baya son drugs ɗin, daman Romeo yasan halin sa shiyasa yake tasa shi a gaba har sai ya sha a gaban sa sannan yake kyalesa, da kyar da kyar dad ke tura drugs ɗin a bakin sa Romeo na bin masa da ruwa mai sanyi dake cikin kyakkyawan cup ɗin hannun sa.


Babu ko excuse Michael ya faɗo cikin bedroom ɗin yana kwaɓe fuska, ko kallon in da yake Romeo bai yiba, kusa da dad yazo ya zauna yana turo


Dark brown curly hair sa dad ya shafa yana faɗin "How far My Tiger?" Kara turo baki Michael yayi yana wani turɓune fuska, jawosa jikin sa daddy yayi yana ɗan bubbuga bayan sa alaman rarrashi, kamar wadda akayi wa wani abun, shiko Romeo a jikin sa ya ci-gaba da buɗe wa dad drugs yana bashi, idan dad yasa drug ɗin a baki, sai Romeo ya sanya masa cup na ruwa a ban nasa dan ya haɗiye maganin.


Calmly yace "Where is James?" Yayi maganar ba tare da ya ɗago ya kalli Michael ɗin ba, cikin sauri Michael yace "he is in the word room" miƙewa Romeo yayi bayan dad ya kammala shan maganin, ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin hannun sa rike da sauran drugs ɗin yana faɗin "you and James meet me in my room" ya kai karshen maganar tare da ficewa, shiru Michael yayi kamar mai tunanin wani abun, zuba masa ido dad yayi yana kallon sa, ba tare da wani yace da ɗan uwan sa uppan ba.


A ɓangaren James kuma.


Zaune yake kusa da Musharraf yana kallon sa, wani irin yana yi yake ji duk lokacin da ya kalli kwayar idon Musharraf, ji yake kamar ɗan uwan sa na jini, haka kawai yake jin kaunar Musharraf sosai.


Kallon sa Musharraf yayi kasa kasa yace "I want to pray, it's time for prayer" kallon diamond watch ɗin hannun sa James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Musharraf yace "Okey now what do you want?" "I want to perform ablution" miƙewa James yayi ya ɗauko ruwan roba a fridge, ya dawo ya ɗauko wani kwano na silver mai faɗi irin wadda marasa lafiya ke amfani da shi idan zasu yi alwala ko wani abun, saman gadon ya haye, da yake gadon yana da girma.

Hannu yasa ya ɗago Musharraf ya ɗan zaunar da shi tare da sanya masa pillow a bayan sa, abun da ya bawa Musharraf mamaki shine alwalar da James ya masa babu tangarɗa ko wani kuskure, kasa hakuri Musharraf yayi har sai da ya tambayi James, ya akayi yana Kristen ya iya yin alwala dai dai haka, yar murmushi James yayi yana faɗin "I knew it through my friend, i have a Muslim friend, he is of good character, i like him more than your expectations, I understood a lot of Islam perspective from him" sosai Musharraf yayi mamaki tare da ɗaukan kudirin in dai ko hakane suna da masani a kan addinin musulunci kuma sun san wasu daga cikin littafan musulunci to ba zai bargidan ba har sai ya tabbatar ya musuluntar da su, bai gama tunanin da yake ba ya jiyo muryan James yana faɗin "Don't allow uncle, dad, and the rest to know you are a Muslim, because All of these people that your seeing in this house they don't like Muslim, they hate Islam, especially dad, uncle Herry, but lion has a Muslim friend" sosai Musharraf yaji daɗin bayanan James dan ya kara samun makama da zai musuluntar da su, a iya ɗan zaman sa a gidan ya fahimci kowa na gidan yana tsoron lion da suke kira kuma suna shakkan sa, duk da bai taɓa ganin wannan lion ɗin ba, yasan dai yadda suke maganar sannan shine mai power a gidan, da alama shike juya kowa, amma Alhamdulila tun da shima lion ɗin yana da aboki musulmi hakan yazo masa da sauki, dan yana da tabbacin shima lion ɗin ba zai rasa sanin wasu abubuwa dangane da addinin musulunci ba, through wannan abokin nasa.


Ganin Musharraf yayi shiru ne yasa James yayi tunanin ko dai yaji tsoron dan nace masa yan gidan nan basa son musulmai ne, karfa ya shiga damuwa gashi kuma bashi da lafiya, tuna haka yasa James yace bari ya masa wata dabara dan karya sa kansa cikin damuwa yazo ya kara ciwo kan ciwo "No uncle don't worry, me a really like Muslim people, I'm thinking about there religion, sometime they are doing something good, I read some Muslim books, most of the things that I saw in the books are true, that's means they are not laying, which is why I believed in the books, I'm thinking about the religion, this is the reason why i hate our pasto, he is lying to us everyday, he is always talking about something that is not coming to pass" jin hakan ma ya sanya Musharraf ya kara jin daɗi, da tunanin James ba zai yi wuyar shiga musulunci ba, saboda shi ya fara gane gaskiya, zai yi saurin amsan kalmar shahada, shi kuwa James sai kokarin tattaro kalaman da zai kwantar wa da Musharraf hankali yake, dan bai son ganin Musharraf ya shiga damuwa saboda rashin lafiya da yake ciki.


"I want to see this lion" cewar Musharraf, girgiza kai James yayi kafin yace "give thank to god da a baya baka taɓa kallon lion ba, kuma ka roki Allah yasa kada kayi ido biyu da shi" "why?" Musharraf ya tambaya yana tsare James da ido, jinjina kai James yayi yana faɗin "kawai" "No James ni gaskiya ina son ganin sa" shiru James ya ɗan yi kafin yace "Anywhere yanzu dai i think yana wajen dad, yau ɗaya ga wata lokaci shan drugs na dad yayi, yana can yana bashi magani" cikin sauri Musharraf yace "meke da mun dad ɗin?" "Wine da yake shane before yayi affecting nasa over, yayi spoil na wasu abubuwa daga halittar sa, shiyasa something zakaga yana da saurin rikicewa, yana abu kamar like bashi da sense, kuma zakaga idan abu kaɗan ya faru zai birkice jikin sa ya fara kerma, baka ganin ko magana mukayi sometimes zaka ga jikin sa ya fara kerma kamar mai tsoron mu?" Shiru Musharraf ya ɗan yi kafin yace "to me yasa baku hana shi shan wine ɗin ba?" "We already stop him since before now, kuma yana shan drugs, by the God grace ya kusa samun lafiya ya koma kamar da" addu'a sosai Musharraf ya masa, James yana amsawa da Amin, sannan James ya sauƙo da kwanon ya je toilet ya zubar da ruwan ya dawo ya gyarawa Musharraf zama ta yadda zai ji daɗin yin sallar sa.


A wanna yanayin Micheal ya shigo ya same su, ɗaure fuska yayi kafin yace "who is this James?" Yayi maganar yana kallon Musharraf, "is my uncle my friend also" James ya bashi amsa, yayin da Musharraf kuma ya tada kabbara ya fara sallah a rigingine, juyawa Michael yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin "Lion want to see us, in his room now" kallon Musharraf James yayi yace "Uncle I'm coming" kasan cewar Musharraf yana sallah sai bai amsa wa James ɗin ba, shima James bai damu Musharraf ya amsa masa ba saboda ya san idan ana sallah ba'a magana, ya san haka a wajen friend nasa.


A tare suka jera shi da Michael zuwa part ɗin Romeo.


Bakin su ɗauke da excuse suka shiga bedroom ɗin Romeo, yana tsaye ya bawa kofar shigowa baya, ya goya hannun sa a saman kirjin sa, tun da sukaga haka suka gane ba lafiya ba, dan haka jiki ba kwari suka zauna a bakin katafaren bed ɗin Romeo.


Shiru Romeo ya musu, suma shiru suka zauna almost 30mins kafin Romeo ya juyo a hankali, fuskar nan tasa kamar hadari, dara daran blue eyes nasan nan, sun sauya launi zuwa ja, lausasan laɓaɓɓan san nan har wani kwalli suke kamar yasa lips balm saboda ya ɗan ciza su kafin ya juyo, ganin shi a haka ba karamin razana su James yayi ba, nan take suka sha jinin jikin su.


Rai a matukar ɓace, first time da Romeo ya fara ɗaga murya yayi magana, cikin zafin rai yace "I was thinking you are responsible, but you people are not, your misbehaves has jump from our uncle now to our daddy!! I most give you specifies punishment, daddy didn't deserve that miscresant from you, have you forgotten wen he was up and down for us, it's time to repay him, to provide happiness for him and draw him close to us, met me at my place!!!" yana kai karshen maganar ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, dukkan su sun fahimci kuskuren su na haɗawa da dad da suka yi tun ma Romeo bai fara basu horo ba, tabbas suna son daddyn su, amma basu san me yasa suke ɗaukan dad ɗin kamar su Uncle Herry ba.


Ganin Romeo ya fice ne, kuma baya son African time yasa suka miƙe da sauri suka bi bayan sa.


Kai tsaye wajen wannan filli na dawakan suka nufa, Romeo yasan babban kuskure ne ya bawa Michael wannan hukunci saboda ciwon sa, to amma bashi da zaɓi dole ya hukun tasu, saboda gobe kada su kara yiwa daddy abun da suka masa, sunyi babban kuskure, kuma sun san dad bai da lafiya amma haka suka rufe ido suka haɗe sa da su Uncle suka masa wannan tsiya, ya zama dole su karɓu hukunci dan gaba.


Zama saman ɗaya daga cikin manya manyan kujeru masu numfashi dake wajen Romeo yayi, sannan ya bada Umarni da a fito masa da dawakan sa, dan suyi tsre da Michael da James, abun da basu taɓa kwatantawa ba, yau zasu yi.


Haka kuwa akayi, suka fara tsare da wayan nan manya manyan dawakan masu jini a jika da ji da lafiya da karfi.


Sai dai abun mamaki, dawakan sun kasa wuce James, shi kam Michael tun ba'ayi nisa ba suka wuce sa, James ne ya sha fama da su har zuwa karshen wajen, kuma suka dawo dawakan basu wuce saba, ko kaɗan Romeo bai yi mamaki ba, ya danganta hakan da cewa dan jinin sane yasa dawakan basu wuce James ba, shi kuma Michael saboda laluran sa yasa suka wuce sa, so bai wani damu ba.


Ɗaukan su yayi suka tafi mataki na biyu, shi dai Michael har kuka ya fara yiwa Romeo dan ba zai iya jurewa ba, bashi da lafiya bashi da kwarin jure hakan, amma haka dole ya jure suka shiga mataki na biyu


Manya manyan karafuna Romeo ya sanya su ɗagawa masu bala'i nauyi, haka ya sanya jibga jibgan sojojin sa suka ɗaura musu wayan nan mayun karafuna a kan su da kuma hannayen su, sannan Romeo ya sanya su suyi tsayuwar sojoji, idan sukayi kuskuren sakin karfe ɗaya, to fa a kafar su zai faɗa musu, sai ya musu daga daga da kafa, saboda nauyin sa da girman sa, sai ya fashe musu kafa tsab, haka suka hakura suka riƙe karfen nan da iya karfin su na karshe, gashi Romeo yace tsayuwar 1h zasuyi a wajen, tuni Michael ya fara kuka, wi, wai, wi, kamar ƙaramin yaro, har da majina, ya saki ɗan karamin bakin nan nasa yana zubar da yawu ga majina ga hawaye, gwanin ban tausayi, shi kuwa James sai haɗa zufa yake amma bai yi kuka ba, kasan cewar ya samu ire iren wannan horo daga wajen ogannin sa.


Romeo ganin kukan Michael na neman ɗaga masa yankali ne yasa ya ɗauko Bluetooth ya sanya a kunnen sa, ya mai da kan sa kan screen ɗin wayar sa, ya daina kallon su, shi kuwa Michael sai kuka yake ya kasa shiru.


Gaba ɗaya tausayin Michael ya hana James samun nitsuwa, ji yake kamar ya sanya sojojin dake kewaye da su suna gadin sun nan, su ansa karafunan Michael su kara masa, su bar Michael ya koma ya zauna ya huta, sai dai kuma bai isa yayi hakan ba kasan cewar Romeo ne ke basu horon da kan sa.


Masu fi 30mins da fara tsayuwar ba, jikin Michael ya fara kerma, ya kasa tsayawa waje guda, kan kace me ya fara tangal tangal, gashi kuma idan ya faɗi kasa karafunan nan suka danne sa, sai dai wani ba shi ba dan mutuwa zai yi, Romeo kuwa ya sanya Bluetooth a kunnen sa hankalin sa na kan waya, bai san meke faruwa ba, su kuwa sojojin basu isa suyi wani abuba idan ba Romeo ne ya basu izini ba, koda kuwa faɗuwa Michael zai yi ba su isa su tare sa ba sai dai in Romeo ya basu izini.


Tafiya gaba ɗaya Michael yayi zai zube kasa, kamar wani walkiya haka Romeo ya miƙe ya tarosa yayin da wayan nan jibga jibgan sojojin suka ansa karafunan hannun sa a sukwane, rungume Micheal Romeo yayi, da kyar da kyar Michael ke mumfashi, nan take jikin sa yayi ya ɗau zafi over kamar wuta, sai kerma jikin sa keyi kamar ba lafiya ba, da hannu Romeo yayiwa sojojin nuni da su karɓi karafunan hannun James karya faɗi shi ma, a sukwane suka karɓawa James ɗin, da Romeo yayi niyar idan suka gama part two zasu wuce part three, dan yana son ya horasu da kyau, sai dai kuma ina hakan ba zai yiwu ba saboda Michael.


Cak ya ɗauki Michael saman kafaɗar sa suka wuce cikin gida, da kyar James ke jan kafa yabi bayan su, sai faman haɗa zufa yake yaji wuya sosai.


Saman katafaren bed nasa ya kwantar da Michael ya fara duba sa, yana mai jin ba daɗi a ran sa, James kuma bedroom nasa ya wuce dan yaje yayi wanka ya huta.


Mu leƙo Nigeria mu dawo


💞NIGERIA💞


A ɓangaren Hajiya da Jelly kuwa, Hajiya dai taga ikon Allah iya ganin idon ta, dan kuwa duk in da taje sai Jelly ta bita, taki yarda ta zauna ita kaɗai, har toilet idan Hajiya ta shiga sai Jelly ta bita, Hajiya na son tayi wanka amma ba hali dan kuwa Jelly dai taki yarda ta zauna ita kaɗai, ko abinci Jelly bata ci da hannun ta sai dai a bata a baki, daga karshe dai Hajiya da taga ba zata iya da Jelly ba sai ta kira ɗan ta Nawid da kuma Mijin ta a waya dan suzo ko zasu san yadda zasu yi da Jelly.


Ko da Nawid yazo sai cewa yayi, zai zane ta da bulala, nan fa Jelly tace ba'a haifesa ba ,dan kuwa tsayawa tayi ta riƙe kugu tace wlh in dai ya daketa sai ta rama, har ya zaro belt zai fara zaneta Hajiya ta dakatar da shi ta hanyar ce masa "Haba Nawid bakaga bata da lafiya bane? Dan Allah ka bita a hankali, kasan yadda nake son yarinyar nan kuwa, kasan yadda nake son ya mace kuwa, kai ka ɗai gare ni, ina burin samun ƴa mace Allah bai yi ba sai yanzu Allah ya bani kace kuma zaka takura mata, a'a ni na kira kane kawai dan kazo ka tayani lallaɓata ta zauna nayi wanka" zaro ido Nawid yayi yace "Haba Ummi ni da nake cewa idan ta samu sauki, miƙata wa hukuma za muyi dan su nemo iyayen ta" girgiza kai Hajiya tayi tana faɗin "Tab lallai Nawid, ai wannan yarinyar marainiya ce dan kuwa kaga a kan titi take yawo na bugeta, kuma wlh ko da ma ba marainiya bace dole iyayen ta su bani ita, dan ina son ta ba zan iya rabuwa da ita ba, kana ga yarinya kamar yar india tab, ni ai har na hango auren ka da ita" kasan cewar Nawid ya san halin Ummin sa, da bala'i son ƴaƴa mata hakan yasa yayi shiru kawai ya zuba mata ido tana ta fama lallaɓa Jelly, kamar wata yar Baby har da ce mata "my baby ki zauna ko idan na fito wanka zan goyaki muje muyi wasa" mamaki Nawid yake Jelly ta haukata masa uwa lokacin guda, girgiza kai kawai yayi ya fice daga ɗaki haushi kamar ya shaƙe Jelly.


Haka Hajiya ta rinƙa lallaɓa Jelly har Abbon Nawid ya dawo, suka haɗu sai lallaɓa Jelly suke, dan shima Abbo Jelly ta tafi da shi, lokaci guda yaji kaunar yarin yar a ransa, sai dai shi kauna na daban yake mata.


Da kyar Jelly ta yarda ta aminci suka zauna tare da Abbo a cikin bedroom ɗin, Hajiya ta wuce toilet da sauri dan taje tayi wanka.


Sai kallon Jelly Abbo yake, ya kasa cire idon sa daga kallon ta, ita kuwa sai faman turo baki take, ita kaɗai tana kunkuni, sai wani cool murmushi Abbo ke sakewa yana kallon face ɗin ta, dan turo wannan ɗan bakin nata da take ba karamin tafiya da shi take ba, ji yake kamar ya jawota jikin sa.


Haka Hajiya ta fito ta same su, Hajiya na fitowa Jelly ta miƙe ta rungume ta tana faɗin "Ke bakin ga wannan mutumin ba sai kallo na yake yana min dariya" ko kaɗan Hajiya bata damu ba, dan tasan shi ma Abbo yana bala'i kaunar ƴaƴan mata, dan haka sai tace "Sunana Ummi ba ke ba, shi kuma sunan sa Abbo baban ki ne, kin ji ko? Idan ya kalle ki ya miki dariya kema ki masa, zai ji daɗi, dan yanason farincikin yarsa" yar dariya Jelly tayi tace to, sannan ta saki Hajiya ta koma kusa da Abbo ta zauna tana murmushi


a ɓangaren shi kuma Abbo, gaban sa sai dukan uku uku yake lokacin da Jelly ke faɗa wa Hajiya yana kallon ta, ya san halin Hajiya da bala'i Kishi zata iya fara ruwan bala'i, sai dai kaunar da take wa ƴaƴa mata yasa bata kawo komai a ranta ba, kuma a tunanin ta Jelly bata da lafiya duk wani abun da zata faɗa kawai shirmene.


Tab akoi fa cakwakiya gidan su Nawid, dan da alama shi dai Abbo ya faɗa muje dai zuwa


Ɗaukan kayan ta Hajiya tayi ta koma cikin toilet dan shiryawa, saboda su Jelly suna ɗakin, shiryawa tayi tsab cikin wata dankareriyar shadda milk color ɗinkin doguwar riga, tasha aiki daga sama har kasa.


Bayan ta gana shiri ne ta fito ta riƙo hannun Jelly suka wuce Palo, miƙewa Abbo yayi ya biyo bayan su.


Saman sofa suka zauna Hajiya ta fara ƙoƙarin koyawa Jelly wasu abubuwan, irin su yadda ake gaida mutun da kuma matsayin su a wajen ta, na iyayen, sai kuma yadda zata rinƙa zama da mutane da yadda zata yi wanka da kan ta da sauransu, ba wani abun da Jelly ke ɗauka, Hajiya ke zancen ta kawai, shi dai Abbo da yaga abun nasu bana karewa bane sai ya miƙe ya musu sallama ya wuce office na sa, daman Hajiya ta kira shi ta sashi ya dawo.


Sai faman surutu Hajiya take wai tana yiwa Jelly bayani a kan yadda zata zauna a gidan, ko word ɗaya bai shiga kunnen Jelly ba, bare kuma kanta, a wanna hali wata budurwa ta fito daga ɗaya daga cikin part dake cikin palon, kallo ɗaya zaka wa yarinyar kasan yar duniya ce ta bugawa a jarida, dan wasu shegun riga da wando ne a jikin ta sun matseta, duk wani halitta dake jikin ta ya bayyana, ta zuba attachment a kai kamar wata dodanniya, ga wani uban glass da ta maka a ido kamar wata roka da glass, abun ba kyan gani wai an yi kwalliya


Kai tsaye hanyar fita daga palon yarinyar ta nufa, ko sannu bata cewa Hajiya ba kamar ma bata san da zaman ta a wajen ba


Kwatsam idon ta ya sauka kan, Jelly dake zaune sai faman turo baki take, a hankali matashiyar budurwan ta sauke glass ɗin fuskar ta ta ɗan kalli Jelly from head to toe na yan wasu mintoci kafin nan ta mai da glass ɗin ta fice daga palon, tana tafiya tana juyowa ta kalli Jelly tana wani lashe baki kamar tsohuwar mayya.


Ganin yarinyar yasa Hajiya ta kara zawa Jelly kunne a kan babu ruwan ta da yan gidan nan, dan basu da mutunci a cewar Hajiya, sai dai abun da Hajiya bata sani ba shi ne, Jelly fa bata jin ma me take faɗe hankalin ta na kan Tv dake kunne sai faman turo baki take.


Kai jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Hajiya baban Nawid, hmmm muje zuwa amma dai akoi show


Mu leƙo Rimsha mu dawo


👹DAULAR MUTUWA👹


Sanyin safiya ne ya ratsa ta, kasan cewar lokacin hunturu ya fara shiga, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, a razane ta miƙe zaune ganin kyakkyawar face ɗin matashin nan wato duna da ya canza halittar sa zuwa kyakkyawa, da sauri ta miƙe zaune tare da taja baya tana zaro ido, murmushi yayi kafin yace "Fine girl kin cika tsoro" yar wawwaigawa tayi kamar mai neman wani abu, a hankali tace "Ayla ina kuke?" Ɗan matsowa kusa da ita yayi yana faɗin "Suna ɗakin baba, ya kamata yanzu ki dai na jin tsorona" ja da baya Rimsha ta fara yi tana ambato sunan Allah a zuciyar ta a fili kuma ta kasa, dan yau ma gaba ɗaya ta tashi cikin wani yanayi, ta mance da komai na rayuwar ta na baya, yau ji take kamar ba ita ba jikin ta duk a sake.


A hankali ta miƙe jikin ta sai kerma yake tazo ta raɓa ta gefen sa ta wuce da sauri tayi waje, shi burge sa ma take idan tana irin wannan tsoron nata, son ta kuma karuwa yake a ransa.


Tab wannan shi ne soyayya tsakanin mutun da aljani.


Miƙewa yayi yabi bayan ta, kai tsaye ɗakin baba ta nufa, sai toshe hanci take, ita da kan ta bata son shakan warin dattin dake jikin ta, saboda yau kwana biyar kenan ba wanka.


Nan ta isko su Ayla sai hira da baba suke, kusa da Ayla ta zauna tana faɗin "Ayla wai ku bakwa wanka ne a gidan nan?" Cikin sauri Ayla tace muna wanka amma ga wanda yake so" "ai na ake yin wankan?" Ayla za tayi magana baba ya rigata da cewa "Meesha da yake shima yabi bakin Ayla, gaba ɗaya gidan sai suka mai da mata da suna meesha, "Meesha idan kina magana kina min yanayi da ɗana Nawazudden, sai dai shi farine sosai kuma baku kama, amma dai kina min yanayi da shi sosai, musamman idan kikayi murmushi dimple naki ta lotsa sai naga kamar Nawazudden ɗi na, ko yana ina yanzu oho, rabona da shi tun yana level 1 a Ahmadu Bello university Zaria" shiru Rimsha ta ɗan yi tana jin kamar tasan wanna suna da baba ya kira Nawazudden, a hankali tace "Ayya baba kila shima yana can yana kewar ka" murmushi kawai baba yayi, har sai da dimple nasa irin nata ya lotsa, shiru yayi bai sake magana ba, dawo da dara daran sleeping eyes nata tayi kan Ayla tace "ai na zan yi wankan Ayla? Ko dai a wajen da muke fitsarin nan ne?" duna dake tsaye a bakin kofa ne yace "Muje na nuna miki" make kafaɗa tayi cike da tsoro tace "A'a ni na fasa wankan ma" yar dariya yayi yana faɗin "My wife sarkin tsoro, ba wani abun da zai faru, raka ki kawai zan yi na nuna miki na dawo" zatayi magana baba yace "Tashi kije Meesha"


Ba dan taso ba ta miƙe cike da jin haushi ta wuce tayi gaba, duna yabi bayan ta, sai turo ɗan karamin bakin nan nata take, dai dai tsakiyar gidan suka hango su Barbushi daga ɗan nesa sun zo ɗaukan wasu yara wayan da aka samu mai yasan private part na su da idon da kodar su, shine za'a je a yanka su


Rimsha zatayi ihu ganin munin su Barbushi ya razanata, da sauri duna ya rufe mata baki, dan su Barbushi ba lura da su ba, kuma sun ɗan wuce su shi yasa basu lura da su ɗin ba, girgiza mata kai duna yayi kasa kasa yace "Kiyi shiru idan ba haka ba zaki bi layi" shiru tayi jikin ta sai kerma yake, dan ita bata taɓa kallon su Barbushi tana cikin hayyacin taba, wancan karon data gansu ba'a hayyacin ta take ba, kuma ga bala'i yinwa da take ji lokacin, shi yasa bata iya ganin su da kyau, bibbiyu take gani a wancan lokaci.


Su Barbushi na barin wajen Duna ya kamo hannun ta suka nufi hanyar bayi, cikin sauri ta fisge hannun ta tana faɗin "Bana so karka sake taɓa ni" hakuri ta bata dan ya manta da cewa ba'a taɓa matan Musulmai da ba muharramar kaba shiyasa ya riƙe mata hannu.


Kai tsaye wajen toilet ɗin suka wuce yaje ya nuna mata sannan ya tsaya a bakin kofa ta waje wai yana gadin ta, ita kuwa tace wlh ba zatayi wanka ba sai ya bar wajen, shi kuma yace ba zai tafi ba sai yayi gadin matar sa.


Da dai taga da gaske yake ba zai tafin ba kuma ai ba ganin ta yake ba, tun da yana ta waje, hakan yasa ta hakura ta kunna fanfo ruwa ya fara zuba, gashi ba wajen tara ruwan sai dai kayi wanka daga fanfon kawai, haka ta cire kayan ta, babu sabulu bare soso ruwa kawai ta rinƙa sheƙawa jikin ta da sunan wanka,


Tana gama sheƙa ruwan ta mai da kayan ta da sauri, ta ɗan leko kanta dan taga ko yana kallon ta, sai taga akasin haka, domin kuwa baya ya bawa toilet ɗin yana kallon cikin harabar gidan.


Da sauri ta fito ko sannu bata ce masa ba ta nufi hanyar komawa ɗakin baba


Kamar daga sama taji muryan sa yana faɗin "Me yasa kuke son zuba ruwa a jikin ku? Dan naga Ayla ma tana yawan zuwa ta zuba ruwa a jikin ta" ba tare da ta kalle saba tace "Saboda tsabtar jiki da kuma kiyaye lafiya" "manene tsabta?" Cewar duna, a nitse ta fara yi masa bayani a kan tsabta "Tsabta yana ɗaya daga cikin manyan abubuwa da addinin mu ya koya mana, ko ibada zakayi sai da tsabta, sai ka tsabtace jikin ka, domin da kyar ta iya kiran sunan Allah, domin Ubangiji mu mai tsabta ne, so aiki ma mai tsabta yake karɓa" "manene Ubangiji" ya faɗa yana kallon ta, kasa magana tayi saboda sun shaƙe mata wuya ji tayi kamar zata mutu, nan take ta riƙe wuyar nata da hannun ta ɗaya ta fara hawaye


ganin haka yasa duna ya fahimci meke faruwa, dan haka sai ya riƙo hannun ta guda ɗaya, yana riƙe ta taji kamar anyi ruwa an ɗauke wuyar nata ya sake, da sauri ta kwace hannun ta daga nashi, ta wuce ɗakin baba, zuba mata ido yayi tana tafiya yana kallon ta cike da so, sai mamaki yake a kan kullun idan tazo bashi labari a kan addinin su sai Queen ta shaƙe ta, hakan na nuni da addinin ta addini ne mai kyau kenan, me yasa su Queen basa son wayan da ke da irin addinin su my wife, dole na binciko dalili, sai jerowa kan sa tambayoyi yake a cikin zuciyar sa, yana tsaye ta kasa tafiya.


Ita kuwa tana shiga ɗakin baba ta zauna kusa da baba suka ci-gaba da hira kamar yadda suka saba.


💞KATSINA💞


A tare Jehan da Sadiq suka je gidan su Jehan da suka sayar, suka kwanshe musu kayan su dukka suka kai gidan su Sadiq, a ɗakin maman Sadiq suka zuba, Allah sarki maman Sadiq baiwar Allah ita tace su dawo gidan, su rinƙa kwana a ɗakin ta kafin suga me Allah zai yi, nan fa baban Sadiq yace bai san wannan ba sai dai su kama hayar ɗayan ɗakin dake kusa da na maman Sadiq, maman Sadiq tace masa yayi hakuri dan ɗakin can bashi da kyau idan ana ruwa yana zuba, kwanon sa duk ya huhhuje kuma ɗakin kiwon awakin sane a baya, nan fa ya taso zai ci mutumcin maman Sadiq, da kyar Sadiq ya bashi hakuri tare da ce masa sun yarda su Jehan zasu kama ɗakin su biya, nan ya musu kuɗin ɗaki shekara 20k, Sadiq yace zai sanar da su gwaggo zasu biya, Jehan na tsaye aketa wannan dirama kasan cewar bata wani jin hausa yasa bata gane komai da suke faɗe ba.


Sadiq da Yusuf suka haɗu suka gyarawa su Jehan ɗakin, ɗan canjin da Sadiq ya samu daga wajen Jehan, dasu yayi amfani ya sawo siminti yar awo sukazo suka kwaɓa suka toshe musu ramukan ɓeraye dake ɗakin, duk wannan dirama da ake ita dai Jehan tana tsaye ne kawai bata san ina a ka dosa ko me ake ciki ba.


Sai bayan su Sadiq sun gama gyara komai ne, ya samu ya yiwa Jehan yar gwari gwari yadda zata fahimter, bata nuna wani damuwa ba, taje ta ciro kuɗi daga account nata, kasan cewar ita a account nata akoi sauran 100k sai taje ta ciro 20k a wajen masu POS ta bawa Sadiq dan ya bawa baban sa kuɗin hayan ɗakin, ta bar ragowar 80k ɗin, sai lokacin ta tuna da cewa, Ibrahim fa fake face nata ya gani har ya dage tayi aiki a restaurant ɗin su, tuna hakan yasa ta samu Sadiq ta faɗa masa fake face nata Ibraheem ya gani


A nitse Sadiq yace mata "Ki godewa Allah ma da yasa ba asalin fuskar ki suna gani ba, kuma hakan ma yayi dai dai, dan ba wanda zai wani takura miki da zancen soyayya, duk da cewa shima fake face ɗin yana da kyau, amma ki sani asalin face naki yafi wannan kyau nesa ba kusa ba, to garama da basu ga na asalin ba, ko dan ki zauna lafiya kiyi aiki cikin kwanciyar hankali ba tare da takuran samari ba, yanzu ma sai kin shiryawa takurawar maza, dan na faɗa miki shima fake face ɗin yana da kyau.


Shiru Jehan tayi ba wani abun da ta gane bayan cewa face ɗin yayi.


To masu karatu me kuke tunani zai faru, a gidan su Sadiq da kuma restaurant? sannan ga gidan Hajiya baban Nawid, ga kuma soyayya tsakanin mutun da aljani wato, Rimsha da duna, ga kuma Aafia ta amsa zata haɗu da alhaji, shin ma wani Alhaji ne? Sannan ga kuma man a jefe, shin Musharraf zai yi nasara a kan burin sa na musuluntar da dad da familyn sa kuwa? Yaya Michael zai kare, yaya Umaisha za tayi idan Akil ya dawo? Sannan ga Man na son ta, yaya su Hajiya Umaiya za suyi da dodannin nan? Waye baba? Ku dai muje zuwa yanzu wasan yanzu zai fara sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai amma dai akoi show 💃💃💃🤪



Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪


💞Star Lady💞



💞TRIPLET'S💞



***




💞 FATEEMA MUSA💞

(💞STAR LADY💞)



*Gargarɗi*


_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_





WhatsApp me for more information ***







Episode 29


💞WASHINGTON DC💞



Da kyar da kyar Michael ke fitar da numfashi, ga jikin nan nasa kamar wuta, sai nishi yake kamar wadda ya tiki uban gudu, cire masa rigan jikin sa Romeo yayi, sannan ya ɗauko A box ya fara duba shi, dan cito rayuwar sa.


Kasan cewar already sun san da matsalar sun saba da matsalar, sai Romeo bai sha wata wahala ba wajen sai ta komai Michael ya dawo dai dai, kan kace me Michael ya ɓige da barcin wahala, miƙewa Romeo yayi ya mufi toilet dan yin wanka, mai da A box ɗin yayi first kafin ya wuce toilet ɗin.


A ɓangaren James kuwa shima wanka yayi, ya haye saman lafiyayyiyar bed nasa, yana sauke ajiyar zuciya, ba jimawa barci tayi awon gaba da shi.

💞NIGERIA💞

💞GIDAN ABBA💞


Tsaye Hajiya Umaiya take gaban dining table, taci kwalliya sosai kamar ba ita ba, sai kamshi take zubawa kamar anyi ɓarin turare a jikin ta, sai wani taunar chewing gum take kamar yan mata.


Da sallama Abba ya shigo palon ya sauko daga samma, ya sha mamakin ganin Hajiya Umaiya tayi kwalliya yau, kuma bata amsa masa sallamar da yayi ba, bai wani damu ba, ya wuce yaje ya zauna saman kujeran table ɗin yana faɗin "Ina Akila?" Bai kai karshen maganar ba ya dakata, sakamakon ganin yau Hajiya Umaiya girki ta musu da kan ta, ba abincin restaurant bane.


Daɗi ya sanya shi ya miƙe ya rungume ta yana faɗin "Yau da kan ki kika mana girki, gaskiya naji daɗi sosai, dole naci abinci na koshi" shiru ta masa ba tayi magana ba, kara matse ya yayi a jikin sa yana faɗin "Yau fa da alama Umaiya suna gaban goshi, dan naga anki min magana, ko dai nayi wani laifin ne ban sani ba? To idan nayi laifi a faɗa min na bada hakuri dan yau kin gamamin komai tun da kika mun gir... Bai kai karshen maganar ba yaga wata Hajiya Umaiya ɗin zaune a saman sofa ta zaro masa ido tana kallon sa, a sukwane ya saki Hajiya Umaiya da ya rungume yana kallon face ɗin ta, kwas kwas kwas ya jiyo ta bayan sa, tsoro ya hana shi juyawa, ji yake Kamar ya fasa ihu amma ba hali, gashi tsoro ya kamasa har fitsari yake ji, kamar zata zubo masa a wandon sa.


Bai ankaraba kawai sai ganin wata Hajiya Umaiya ɗin yayi tazo ta zauna saman kujerar table ɗin tana faɗin "Abban Akil wani abinci zan zubama?" Still dai tsoro ya hana shi juyawa yaga wacece, gashi kuma muryan Hajiya Umaiya yaji, sannan ga wata Hajiya Umaiya a gaban sa, ga wata saman sofa a zaune.


Kan kace me wasu Hajiya Umaiya ɗin su biyar sun bayyana saman kujerun table ɗin, ɗaya na daka a wata yar turmi irin na daka karunfari, ɗaya kuma tana tsosan ƙashi, ɗaya na shan tea, ɗayan kuma tana cin abinci, na karshen kuma ta zuba masa idon dara dara kamar zasu faɗo kasa, idon nata ba kyan gani gwanin ban tsoro.


A sukwane ya juya da nufin guduwa zuwa sama, kwatsam idon sa ya sauƙa kan face ɗin Hajiya Zainab matar Alhaji Mustapha, suna zaune saman sofa suna hira da wata Hajiya Umaiya, sai dariya suke suna tafawa, amma ba ka iya jiyo sautin komai, sai dai kaga bakin su na motsawa.


A guje Abba ya haye sama, da karfi ya banko kofar ɗakin sa ya shiga, ya mai da ya rufe, a tunanin sa bedroom nasa ya shiga ashe na Hajiya Umaiya ya shiga tsabar ruɗu, yana murza key ya juyo sai ganin asalin Hajiya Umaiya yayi tsaye gaban gado tana latsa wayar ta.


Saita nutsuwar sa yayi ya karisa cikin ɗakin, turɓune fuska Hajiya Umaiya tayi tana faɗin "Ina kuma ka fito?" Bata gama rufe baki ba sai ganin wani Abba tayi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya shigo, kallon face ɗin Abban asali tayi, ta sake juyawa ta kallin face ɗin wanda ya shigo yanzu, komai nasa iri ɗaya da Abba, kai Abba ne ma, sai dai sun zama biyu baka iya rabewa, tana kokarin yin ihu wani Abban ya buɗe kofar toilet ya fito yana faɗin "Hajiya ki shirya muje restaurant muyi breakfast ko?" ihu tasa ta haye saman gadon ta runtse idon ta tana jiran taji sun kashe ta kawai


ihun ta yasa Abba juyawa, aikuwa yana ganin masu kama da shi, ya fasa wani mahaukacin ihu ya watsa a guje, yana baza babban riga ya haye saman gado suka dukunkune shi da Hajiya suna jiran suji me zai faru gaba.


Tsawon lokaci suna hakan ba wani abun da ya faru, karjin su sai dukan uku uku yake gaba ɗaya sun rasa ina zasu sanya ransu, Hajiya sai kuka take ta rasa meke mata daɗi a duniyar nan, Allah sarki baiwar Allah duk ta rasa ina zata sanya rayuwar ta, sai numfashi sama sama suke fitarwa, gashi sun dukunkune kan su cikin bargo basa samun iska sai haɗa zufa suke, sun yi shiru suna jiran saukan bulala.


A hankali Akila ta turo kofar ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ganin iyayen ta a dukunkune a cikin bargo ne yasa ta juya da wuri zata fita Abba yayi saurin miƙewa dan yaji voice ɗin ta, waige waige ya fara yi a ɗakin babu kowa, shiru duk masu kama da shi ɗin sun tafi, a hankali ya kira sunan ta "Akila" juyowa tayi ta ɗan ricinar da kai tace "Abba ina kwana?" Sai lokacin Hajiya Umaiya ta taso tana faɗin "Akila baki ga kowa ba da kika shigo?" Girgiza kai Akila tayi tana faɗin "Ban gani ba" dirowa kasa daga saman gadon Hajiya Umaiya tayi sauri sauri ta fice daga ɗakin, dan kar abubuwan su dawo, shima Abba da sauri ya diro kasa tare da zuwa ya riƙo hannun Akila suka fice waje, yana tafiya yana waigo ɗakin, dan shi har yanzu bai yarda da wayan nan masu kama da shi ɗin sun tafi ba.


A palo suka tsaya Abba yace da Akila ta ɗauko mayafin ta suje restaurant suci abinci, to kawai Akila tace sannan ta koma sama taje ta ɗauko mayafin ta, dan daman yinwa ne yasa taje kiran su Abba.


Abba da kan sa yayi driving na motar suka fice daga gidan suka nufi restaurant kamar yadda suka saba.


To mu leƙo su Jehan mu dawo



💞KATSINA💞


Yau dai a ɗakin maman Sadiq Jehan ta kwana kasan cewar gwaggo na asibiti da mum, ita kaɗai a ɗaki kuma bai yi ba, shine maman Sadiq tace, tazo su rinƙa kwana har sai an sallamo su mum.

Kamar kullun maman Sadiq na tsakar gida tana shara, while Jehan na zaune saman kujera tana son taya maman Sadiq aiki amma bata iya ba, shine kawai ta zauna ta zuba mata ido tana kallon ta, yayin da shi kuma Sadiq yana yiwa maman sa wanke wanke, ita kuma amarya tana tsaye a bakin kofar ɗakin ta tana latsa waya, da alama kira take son yi, mama Hanan kuma tana kitchen tana kokarin hura wutar itacen su mai bala'i hayaki, dan ta musu ɗumamen towon jiya, abun gwanin ban sha'awa yadda suke a tsakar gidan.


By mistake kawai maman Sadiq irin ta ɗan sharo dattin da ɗan karfi, dattin ya watsu kaɗan ya haura saman barandar bakin kofar ɗakin amarya har wasu dattin suka taɓa mata kafa, a sukwane Amarya tayo kan maman Sadiq, ba kunya ba tsoron Allah ta ɗaga hannu zata mari maman Sadiq, da sauri Jehan ta miƙe ta riƙe hannun nata tare da wanke ta da wani mahaukacin mari ta tureta gefe, tana mata kallon sama da kasa


Kukan kura amarya tayi tayi kan Jehan da nufi duka, Jehan na tsaye ko motsi bata yi ba, amarya na zuwa zata kama ta da faɗa wani marin Jehan ta kara sauƙe mata tare da hankaɗe ta cikin faɗa tace "Wannan bata haifeki bane? Stupid wani dirty girl dake, wlh in dai ina gidan nan sai na gyara miki zama" duk wanna masifa da Jehan take cikin harshen turanci take yin sa


Da sauri Sadiq ya kariso wajen yana faɗin "Dan Allah Jehan ku bari ya isa haka" ita ma maman Sadiq abun da take faɗe kenan, dan suna gudun bala'i baban sadiq, ita kuwa maman Hanan daɗi taji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, dan daman kullun addu'ar da take kenan Allah ya kawo mai ci musu uban amarya koda sau ɗaya ne, wata kila zata rage rashin kunya da fitsari da take musu a cikin gidan nan


Faɗuwa kasa Amarya tayi tare da dafe cikin ta tasa ihu makircin tana birgima, har sai da baban Sadiq mijin hajiya ya fito daga ɗakin amarya, da sauri yayo gunsu yana faɗin "Wani ɗan tsinanniyar ya taɓa ki" duk da Jehan bata san me ya faɗa ba ta fahimci kamar zagi yayi dan haka sai tace "hy Old man be careful don't angry me" da yake baban Sadiq kai ɗin fanko ne babu komai a cikin ta sai mugun ta da jahilci da bala'i, sai bai san ma me Jehan ta faɗa ba, kawai wajen amarya ya nufa abun sa, yana ta surfa ruwan bala'i.


Nan amarya ta kwashi karya da gaskiya ta faɗa masa, har da ce masa Jehan da Sadiq sun ce zasu kashe ta da daddare, dan haka ya kore su daga gidan nan, Allah sarki maman Sadiq baiwar Allah nan take idon ta ya cika da hawaye dan tasan tsab baban Sadiq zai iya korin Sadiq daga gidan, itama dai maman Hanan idon nata da hawaye, dama kuma ita hawayen tun ɗazun yake idon ta saboda hayakin itacen da take kokarin hurawa ya kama yaki, saboda itacen ɗanyune.


Shi kan shi Sadiq sai da yaji wani iri dan bai son nisa da maman sa, kuma idan baban sa ya kori su Jehan yanzu ina zasu je, basu da kowa basu da komai.


Shi kuwa baban Sadiq sai wani cika yake yana batsewa yana lallaɓa amaryar sa yar gold yana bata hakuri, shegiya Naira, kuɗi sun haukata baban Sadiq Allah ka rabamu da iyaye masu son duniya.


Cikin kukan makirci amarya tace "Wlh ba zan zauna a gidan nan da wayan nan yaran ba, dole su bar gidan nan, marina fa wannan mayyar yarinyar tayi, kuma wanna shegen yaron Sadiq har da ce mata, wai ta ƙaramin wani marin dan bani da kunya ya tsaneni kuma sai ya kashe Ni, ni shegiya ce, ba dai irin zagin da basu min ba" Allah sarki Sadiq bawan Allah zaro ido waje yayi, yana mamakin kalaman amarya na sharrin da take musu, ita kuwa Jehan tana tsaye ne kawai ta zuba musu ido amma ba wani abun da take ganewa a maganganun nasu.


A fusace baban Sadiq yace "Yanzu kuwa zasu bar gidan nan, yan iskan yara, ai daman ba ƴaƴan albarka bane, wlh ba wanda ya isa ya taɓa ki ya zauna lafiya, ku fice min daga gida, daga ku har iyayen naku ban son ganin kowa" wayyo Allah kuɗi ta rufewa baban Sadiq ido baya ji baya gani sai zancen amarya ne kaɗai ke shiga masa kunne.


Nan fa Sadiq da maman sa suka shiga bawa amarya hakuri, ita kam Jehan tana tsaye.


Ganin maman Sadiq ta tara hawaye a ido ne yasa Jehan ta fahimci a koi matsala, dan haka sai ta matso tana tambayar maman Sadiq meke faruwa suke kuka.


Maman Hanan dake cikin Kitchen ita ce ta fito, kasan cewar ta ɗan yi karatu zuwa Jss 2 sai ta yiwa Jehan bayani cikin kwaɓaɓɓiyar turancin ta


Ba laifin duk da turancin na maman Hanan sai a hankali, amma Jehan ta fahimtar, dan haka sai ta ɗago kai ta kalli Sadiq kafin ta mai da kallon ta kan baban Sadiq dake ta surfa uban bala'i, karo na farko a rayuwar ta da taji ba daɗi dan zatayiwa baban Sadiq rashin kunya, amma bata da zaɓi dole ta koya masa hankali dan ta lura bashi da hankali.


Duk wani Hausar da ta iya ranar sai da ta tattaro shi dan tayiwa baban Sadiq magana yadda zai gane, cikin fushi ta fara magana "Babu in da Sadiq da maman sa zasu je, idan ma baka son ganin su a gidan ne, tofa sai dai kai ka fice daga gidan, dan sune da gidan yanzu, ke kuma stupid wlh ina nan gidan babu in da zanje sai na baki tarbiya tun da iyayen ki basu baki ba, da kake cewa mu fita maka a gida, haya muka biya ka, kuma munyi da kai sai after 1 year dan haka sai 1 year ta cika zamu bar gidan nan, da bana son gidan ka amma yanzu dan na baku tarbiya kai da wanna stupid ɗin dole zan zauna a nan, islamikali baka isa ka kori Sadiq daga gidan nan ba, maman Sadiq dai kana da damar ka koreta, amma ban da shi, islamikali sai dai kai ka fita ka barmusu gidan ba dai Sadiq ya fita ba, kuma idan kayi wasa wlh sai fushin Allah ya hau kan ka, a kan cewa da kake zaka kori ƴaƴan cikin ka daga gidan ka, mu kuma da muka kama haya, zaka iya kai mu court, a nan ne zakaga asalin yadda ake duniyan ci, amma fita gida bazamu fita ba, ina binka ta lalama ne because of your son, Sadiq is a nice person, if not wlh dana sanya ka kayi regretting abubuwan da kake wa bayin Allah nan, ke kuma stupid daga yau a gidan nan idan kika sake shiga harkan wani ko wata a cikin gidan nan wlh I will make you regret" ta kai karshen maganar tare da jan tsaki, ta juya zata wuce ɗakin maman Sadiq, a fusace Amarya ta jawota har sai da tayi baya zata faɗi, cikin fushi ta juya ta damko wuyar amarya ta shaƙe ta da karfi, rai a matukar ɓace tace "Ke na lura baki san magana ta hankali ba, bari ma miƙi da yaren ku na marasa kunya ta hakan zaki fi gane wa" hannu baban Sadiq ya kai zai mari Jehan ɗin, da sauri Jehan ta kauce tare da sakin wuyar amarya, ta juyo a fusace za tayiwa baban Sadiq tsawa, idon ta ya sauka kan face ɗin Sadiq, dogon tsaki taja kawai tasa kai ta wuce ɗakin maman Sadiq.


Amarya anji shaƙa sai zaro ido take ta kankame wuyar ta, bin bayan Jehan Sadiq da maman sa sukayi suka bar baban Sadiq da amarya a wajen, itama maman Hanan wuce wa tayi abun ta ta kyalesu nan wajen.


Kuka amarya tasa tana faɗin "Wlh gidan mu zan tafi ba zan zauna da kai ba, kuma karka kuskura naga kafarka a gidan mu, in dai ba ka kori wayan nan yaran ba" baban Sadiq anji kunya yarinya karama ta tsaya tana tsara masa magana har da gargaɗi da sharaɗi, yarinyar da Sadiq ma ya fita a shekaru, amma saboda son abun duniya, jikin sa har kerma yake yace "Yanzu kuwa zan kore su dan Allah kiyi hakuri ki dai na zancen komawa gidan kun nan, idan kika tafi ina zan sanya kai na" ya kai karshen maganar tare da nufan kitchen ya ɗauko itace daga cikin murhun maman Hanan, kai tsaye ya nufi ɗakin maman Sadiq, Jehan na zaune kusa sa yar katifar maman Sadiq shi kuma Sadiq yana zaune ta bakin kofa saman wata yar kujera, ita kuma maman Sadiq tana zaune saman katifar.


Kamar wani mahaukaci haka baban Sadiq ya faɗo ɗakin yana faɗin "Kuzo ku fice min daga gida ko yanzun nan na kashe ku ɗaya bayan ɗaya, yan iskan banza marasa albarka, yarinya uban ta ya sai muku gidan da zaku tsugunna saboda rashin albarka ku sata a gaba kuyi ta duka kamar an kawo muku jaka, to wlh baku isa ba, ko kuzo ku wuce ku fita ko kuma in make ku da icen nan.


Miƙewa sukayi dukkan su jikin maman Sadiq har kerma yake, Jehan kuwa shiru tayi tana tunanin yadda zata ɓullo wa baban Sadiq, can kome ta tuna, tace "Baban Sadiq we are so sorry zuwa gobe zamu barmaka gidan gaji, kuma kuɗin hayan ma da muka baka mun barmaka kyauta gobe da safe zan kara maka wani kuɗin ma" nan fa baban Sadiq ya fara dariya yaji an basa kuɗin hayan kyauta, kuma za'a kara masa wani, a tunanin sa abun da Jehan ta faɗa masa haka ne, bai san halin Jehan ba ne.


Sai washe baki yake ya fito daga ɗakin tare da yin wurgi da itacen hannun sa, ya karisa gaban amarya, yaje ya lallaɓa ta itama ya bata baki, da kyar ta yarda a kan gobe su Jehan zasu bar gidan, ta wuce suka koma bedroom nasu.


Kallon Jehan Sadiq yayi yace "Me yasa kika cewa baba haka?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "I'm sorry to say baban ka yana bukatar a gyara masa zama da kyau, kuma dole muyi hakan, yanzu dai ka kira Yusuf da Sha'aban, cikin dare irin 1 na dare kuyi dressing irin na manyan aljanu, ku shiga ɗakin baban naku, sai kuyi kamar ɓarayi ne ku, kada ku bari ya ganku, koda kun boye fuska kada ku yarda ku haska jikin ku da torchlight ya ganku zai iya gane ku idan ya ga jikin ku, ku tabbatar kun zane fuskokin ku ya zama irin na Magicians, sai ku shiga room ɗin, ku shaƙe murya ya zama irin na aljanu, ku masa barazana a kan idan ya sake shiga harkan wani daga cikin gidan nan sai kun dawo kun kashe shi, haka zaku masa zaku samu zaman lafiya da shi, ko bai zauna da ku dan Allah ba, ya zauna da ku dan tsoron aljanu karsu kashe sa" tayi maganar duk a kwaɓe sai haɗe words take, amma ba laifi Sadiq ya fahimci hausar nata.


Jinjina kai yayi kafin yace "Anya kuwa hakan zai yiwu? Baba fa wlh bayi da tsoro" "try it, zai yiwu" Jehan ta bashi amsa tana komawa ta zauna, to kawai Sadiq yace mata amma cikin zuciyar sa yana ɗar ɗar yadda abun zai kasance.


Kamar yadda Jehan ta basu shawara haka suka yi, ta saman cilip ɗin palon amarya ta baya suka shiga, sunyi dressing kamar wasu bokaye duk sun shafe fuska da toka da gawayi kamar ba lafiya ba, haka suka cire cilip ɗaya suka shige.


Kai tsaye wajen baban suka nufa, sai sharan barci yake saman gado amarya mai laushi, ya buɗe bakin nan kamar ka tsula masa fitsari a ciki, sai minshari yake


Yusuf ne ya fara taɓa su yana kokarin tashin su daga barci, shi kam Sadiq saboda tausayi ya kasa, kawar da kan sa ma gefe guda yayi yana hawaye, shi kuwa Sha'aban daman bai shigo ɗakin ba ya tsaya a Palo, dan kar baban Sadiq ya gansu, su uku ya fara zargin ko dai sune ba aljanu ba.


A firgice baban Sadiq da amarya suka tashi suna salati, dan a tunanin su ma ɓarayi ne, Sabon torchlight da Jehan ta bawa Sadiq kuɗi suka sawo, shi su ka dannawa baban su da amarya hasken a fuska, ga torchlight ɗin da bala'i haske kasan cewar saboda ne.


Sadiq ya kasa magana Yusuf ne ya shaƙe murya kamar aljanin gaske ya fara magana "Kai dattijo wajen ka mukazo" nan fa baban Sadiq ya fara salati yana kiran sunan Allah, ita ma amarya sai salati take tana zazzare ido, dan tsoro kamar zata saki fitsari a wando, har wani zufan hawala suke fitarwa, Sadiq ji yake kamar zai yi musu kuka, shi kam Yusuf dama ogane a zafin rai da rashin kunya dan haka ko a jikin sa, ya fara jerowa baban sa kashedi kala kala, sai amsa masa baban sa yake cike da girmamawa jikin su sai kerma yake, daga karshe Yusuf ya rufe da cewa yu aljanun Jehan ne wlh idan basu fita har kan Jehan ba sai sun dawo sun kashe su, daman Jehan ne tace musu suce haka idan sun zo tafiya, ai kuwa dai baba da amarya suka rinƙa basu hakuri, Yusuf yace musu su kwanta su rufe ido kar su kuskura su motsa sai da safe zasu tashi idan ba haka ba zasu shanye musu jini ko kuma su shanye musu kafafu su dai na tafiya, duk wanna zancen da Yusuf keyi Jehan ta bashi kalaman ta daura sa kan hanya.


Babu musu Baban Sadiq da amarya suka yi abun da Yusuf yace, gashi Sadiq ya dalle musu fuska da hasken torchlight basa iya ganin komai.

Sadiq ne ya tsaya yana haske musu ido har sai da su Yusuf suka haye saman celin suka sauka ta waje, sanan shima ya kashe hasken torchlight ɗin ya salallaɓa a cikin duhu yaje ya haye suka sauka ta baya.


Bayan sun sauka ne suka mai da cilin ɗin suka ɗan chogana shi suka wuce ɗakin su kirjin su sai dukan uku uku yake suna addu'ar Allah yasa kar baban su ya gane su ne ba aljanu ba, ita kuwa Jehan ta ɗaura su a kan hanya tana can tana sharara barci ta cikin kwanciyar hankali, dan yanzu ta samu peace of mind tun da za'ayi wa mum aiki, damuwa ya ragun mata sosai ta fara farinciki, amma ba kamar abaya ba.


Washegari bayan sun fito, Jehan ta shirya tsab cikin doguwar riga Abaya pink color za su wuce asibiti da Sadiq, daga nan Sadiq ya kai ta taga restaurant ɗin da zatayi aiki dan gobe Monday zata fara aiki a can, amma still fake face ne a fuskarta, dan tun da ta sawo fake face ɗin nan take yawo da shi ko ina bata taɓa cirewa, mutanen anguwa sunyi magana har sun gaji, sai tambayar ina rayinyar nan Jehan take suke yi, ko dai ta koma garin sune sai dai ba mai basu amsa.


A tsakar gida za su fita Sadiq da Jehan suka isko amarya, ko sannu basu ce mata zasu wuce amarya tayi saurin cewa "Sannun ku da fitowa" a sukwane Sadiq ya kalli Jehan, kashe ma shi ido ɗaya Jehan tayi suka wuce basu tanka amarya ba, sai da suka fita wajen Jehan tace "Karamar mara kunya, da Jehan yar sanda mai zaman kanta kike, wlh tsab zan gyara miki zama a gidan nan" cike da mamaki Sadiq yace "Jehan dan Allah shekarun ki nawa" "I'm close to 16 years" ta bashi amsa, mai mai ta wa yayi a ransa yarinya 16 years da wanna irin kwakwalwa da confidence haka abun da mamaki wlh, duk wani makirci da iya shege Jehan ta san shi, sai dai alhadulillah tana da ilimin addini kuma duk abun da zata yi bata saɓa dokan Allah, tana kokarin kiyaye wa.


Kai tsaye Hospital suka wuce, mum dai tana nan jiya iyau kullun sai dai a sanya mata ruwa, amma bata fargaɗo ba.


Zaune suka isko gwaggo saman kujerar da mai jinya ke zama, gaishe da gwaggo Sadiq yayi tare da tambayar ya jikin mum, "jiki da sauki" gwaggo ta bashi amsa, wucewa yayi ya nufi waje yana wa mum addu'ar Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗun ta, a tare gwaggo da Jehan suka amsa da ameen, Jehan ta dubi gwaggo tace "My gwaggo what do you want to eat?" Shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "duk abun da ya samu" sallama Jehan ta musu sanna ta fito ta samu Sadiq a waje tace suje restaurant ɗin da zata fara aikin sai ta saiwa gwaggo abinci a can, ba musu Sadiq ya miƙe suka tafi zuwa wajen asibitin bakin hanya su samu abun hawa.


Taxi suka tara suka shiga, suka tafi restaurant ɗin,


Tun daga bakin bakin gate ɗin tampatsetsen restaurant ɗin Jehan ta fara, yiwa wajen kallon sama da kasa, Sadiq ya lura da hakan sai yace "Jehan lafiya kike kallon wajen haka" guntu tsaki taja kafin tace "Dirty place" tayi maganar dai dai lokacin da suka karasa cikin restaurant ɗin, nan fa Jehan ta fara yiwa ma'aikatan dake wajen kallon raini kallon yan datti, da fara'a Ibraheem ya tarbe su yana washe baki, kara ɗaure fuska sosai Jehan tayi wai dan kar su raina ta, shi dai Sadiq idan da sabo ya saba da halin Jehan ɗin sa.


Jagora Ibraheem ya musu zuwa ya nunnuna musu abubuwan da ya dace Jehan ta sani, duk in da ta wuce sai ma'aikatan wajen sun mata sannu da zuwa, amma babu wanda tayiwa kallon mutunci ma bare ta amsa masa gaisuwar sa.


Abun da ya bata mamaki shi ne wasu ɗakuna da Ibraheem ya nufa da su, ashe restaurant ɗin haɗe yake da hotel ta ciki ita bata sani ba, tab lallai a koi cakwakiya.


Bata damu ba suka shiga ko ina Ibraheem ya nuna musu sannan suka dawo wajen reception, Jehan ta saiwa gwaggo shinkafa da miya steew aka mata takeaway.


Zasu tafi Ibraheem ya kawo mata rigar da wando nasu na aiki, kallon kayan tayi a wulakance, riga blue da wando baki, a takaice tace "For what?" Sai faman murmushi Ibraheem yake yace "uniform work, shi zaki rinƙa sawa idan zaki zo aiki" ɗaure fuska tayi sosai tace "Kayan da zan sa nazo ma kune zaku zaɓa min?" Ba tare da nuna damuwa ba Ibraheem yace "A'a Hajiya Jehan haka tsarin yake, abun da oga yace shi a keyi a nan" tirkashi kallon sama da kasa tayiwa Ibraheem kafin tace "Au sayata kukayi gaba ɗaya kenan?" Shiru Ibraheem yayi dan bashi da amsan tambayar nan nata


ganin Jehan zata jiƙa musu aiki yasa Sadiq ya ansa kayan daga hannun Ibraheem yana faɗin "Ba komai malam Ibraheem, karka damu zata sanya, sai goben idan tazo" ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli Jehan yace "Jehan muje ko, zanje gareji kin ga kuma rana nayi" ba musu ta wuce gaba yabi bayan ta, Ibraheem dai zuba musu ido yayi yana kallon Jehan kamar ya make ta yaji dan haushi, yar karama da ita sai iya shege.


A wanna karon abun hawa daban daban suka hau, dan Sadiq zai wuce gareji ita kuma hospital, ba yadda Sadiq bai yi da Jehan ba a kan ta amsa kayan uniform nata amma taki, ta kafe tace sam ita ba zata ansa ba, dan babu wanda ya isa ya zaɓa mata kayan da zata sanya in zata fita, haka Sadiq ya wuce da kayan garejin su ita kuma ta wuce hospital, daman haka suke kullun, idan Sadiq yazo ya gai da su gwaggo sai ya wuce gareji sai yamma idan zai koma gida sai yazo ya ɗauke ta su koma tare.


Tirgashi akoi fa cakwakiya Jehan dai tace bazata sanya uniform ba, wanna shine wasa farin girki, mu leƙo Washington DC mu dawo.


💞WASHINGTON DC💞


12:30Am


kamar kullum duniya dukka sun yi barci, shi kuwa yana zaune saman table chair na dining table na kasa yana latsa system, jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya fito da ita a ledar ta, gata da laushi tilis kamar audiga, kasan cewar gaban rigar a buɗe hakan ya bayyanar da kyakkyawar lallausan dark black gashin mai tsantsi kwance a saman faffaɗar kirjin, gwanin ban sha'awa dan sai kwalli gashin yake kamar ya shafa mata baby oil, gashin hannayen sa da na kafafun sannan duk suna kwance lup a jikin sa, kasan cewar gashin dark black ne shi kuma fatar sa farane kal hakan yasa gashin bayyana sosai, ya tara dark black curly hair sa ya ɗaure a baya, ya bar wannan na gaban goshin nasa ta karawa face nasa kyau over, yau ma kamar kullun sky blue light ne kunne a palon, hasken wutar ba karamin kyau tayi ba a kan face nasa, ya zubawa system nasa dake saman table wanyan nan dara daran blue eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali, kasan cewar ya sauke idon nasa kasa kaɗan yana kallon system ɗin, hakan yasa, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana dan idon nasa yayi kamar a rufe, yayi shiru yana ɗan cizan red lips nasa nan, kamar mai tunanin wani abu, ya kafe system da ido, ga jibga jibgan bodyguard na su a tsai tsaiye suna jiran yace abinci su bashi tissue ya goge bakin sa, already kamar kullun sun zuba masa duk wani abun da zai buƙata.


A hankali James ya fito daga bedroom nasa sai hamma yake alamar barci, wuce wa yayi ya nufi word room wajen Musharraf zai je yayi masa alwala, dan Musharraf yana sallar dare kullun, shi yasa ya roki James dan Allah karfe 1 dai dai ya rinka zuwa yana tashin sa dan ya samu yayi nafila, kasan cewar James Allah ya ɗaura masa kaunar Musharraf yasa baya wani damuwa kuma ya sanya abun a ransa, tun 12:30 yake zuwa wajen Musharraf su zauna suyi ta hira, sai 1 dai dai yake wa Musharraf alwala, kuma ya zauna yayi ta kallon sa har sai yayi nafila raka'a 8 sannan ya rufe da shafa'i da witiri, sai bayan ya gama dukka, James ke kwantar da shi ya wuce nasa bedroom yaje ya kwanta, kuma haka da asuba zai dawo yayiwa Musharraf alwalan sallar asuba, duk sojojin da bodyguard ɗin dake gidan basu iya yadda ake alwala ba shi yasa yake zuwa da kan sa yayiwa Musharraf ɗin, kuma yana laakari da shiya buge Musharraf ɗin da mota, dan haka alhakin kula da shi ya rataye ne a wuyar sa.


Zai wuce wajen Musharraf ya hango blue light na palo kasa a kunne, ko ba'a faɗa masa ba, yasan Romeo ne, dan shi kaɗai ne mai cin abinci da tsakar dare kamar wani aljani, wani lokaci kuma ba abinci yake ci ba haka kawai zai fito palon kasa ya zauna yana latsa system ko kuma wayar sa, da wuya ka gansa a palon kasa idan ba tsakar dare ba.


Fasa nufa wajen Musharraf yayi, ya sauƙo kasa wajen Romeo, saman chair ɗin kusa da Romeo ya zauna yana faɗin "well done lion" kamar dai kullun shiru Romeo ya masa kamar bai san da zaman sa a wajen ba, ɗaukan fruit yayi ya fara ci, a hankali ya matso da kan sa yana kallon cikin screen ɗin system da Romeo ke aiki a ciki, zaro ash eyes nasa waje yayi, har sai da fruits da yake ci suka kwaresa, nan take ya fara tari da karfi karfi, bodyguard ɗin dake tsai tsaye har suna rige rigen miƙa masa glass cup mai ɗauke da ruwa mai sanyi, da sauri ya ansa ya kafa a bakin sa yasha


Shi kuwa Romeo kamar bai san James na tari ba, aikin sa kawai yake, yana cizan lausasan laɓaɓɓan sa, sai bayan tarin James ya tsaya ne, ya ajiye fruit na hannun sa, ya miƙe zai bar wajen, gently in a cool Romeo yace "Come here" ba musu ya koma ya zauna, yana faɗin "here I am"....✍️✍️



Share fisabilillah 👏


To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪


💞Star Lady💞