01
FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
Free pages
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
_Page1 _
DARMANAWA GANDUN SARKI
A hankali motar ke tafiya kai kace matuƙin cikinta dole akai masa wajan tuƙata. Har motar ta gifta tareda danna horn daidai gaban wani katafaran gida, sai kuma ta dawo a slow.
Glass in motar aka zuge anan fuskar wata haɗaɗɗiyar matashiyar budurwa ya bayyana wadda a ƙiyasi na shekarun haihuwa, zata iya kaiwa shekara 22.
Iya duban fuskarta da zakayi, zai tabbatar ma da kyakykyawa ce ajin farko wadda hutu da jin daɗi ya bayyana a fuskarta.
Kallon mahaukacin dake zaune a jikin ƙarshen katangar gidansu tayi. tana hankalce kusan sati biyu kenan da wanzuwar sa a wajan, tun bata lura ba har ta lura da wanzuwar sa a wajan.
Kallon sa kawai takeyi tana nazartar sa, kana ganinsa kaga mahaukaci ziryan amma yanayin shigarsa kaɗai zai tabbatar ma da sabon hauka ne "may be is spiritual disorder" ta faɗa a fili cikin tausayawa.
Jan motar tayi gaba ganin mai gadi ya wangale mata gate in.
Shi kam mahaukacinnan sai zare idanu yakeyi ganin wata halitta a gabansa, dan har wani rakuɓewa yayi jikin katangar gidan sanda motar ta tsaya saitinsa.
Hancin motar ta ta danna cikin katafaran gidan da zakayi tsammanin ba mutum ɗaya bane ya mallake shi ba. Gida ne wanda a harabar gidan kawai ya isa ayi parking motoci sama da huɗu. cikin nutsuwar ta tayi parking motan, sannan ta fito cikin takun nutsuwa, wanda ga duk wanda bai santaba zaiyi zaton da gayya take takun, kai tsaye entrance na gidan ta nufa, hmmm tsaya baku labarin ciki ma ɓata Lokaci ne, just imagine.
Ɗakinta ta nufa tana shiga ta wuce toilet dan gabatar da uzurinta.
Shirya kanta tayi cikin simple dress na zaman gida sannan ta fito ta main palon gidan tsayawa tayi cak sanda takai idanunta kan dining area, wani huci ta furzar sannan tabi hanyarda zata sadata da ɓangaren matar gidan.
Hamshaqiyar mace ce zaune kan kujera tabi tayi balance akai kamar anan aka yita sai faman latsa waya takeyi. Jin motsin tafiya ne yasa ta ɗago kanta, murmushi ta saki da faɗin "welcome Aminiya"
Saida tasha ƙamshi Cikin yanayin ɓata fusaka tace "kawai an cuceni wallahi"
Kallon 'yar tata tayi cikin kulawa da faɗin "meya faru?"
Fuska kamar zatayi kuka tace "wai ace ansan nakusa dawowa daga school amma ace ba wanda ya damu da cikina ko aɗan tanadar min wani abun? ni wallahi karatun ba dole bane, dama matsamin akayi" ta ƙarashe tana kallon mahaifiyar tata data canza fuska lokaci ɗaya, cikin ɓata rai tace "Ni marainiyar wayon naki dana bada umarnin kar ayi abinci da wuri ko su Asaben da a haife sun haifeki ne suka cuceki?"
"Allah Sarki dady shi kaɗai yake iya fahimta na" ta faɗa batare data tanka mahaifiyar tata ba.
Ƙwafa uwar tayi da faɗin "ko dai shi ke goya miki baya kina wa mutane iskanci ba!"
Ɓata fuska tayi sannan tace "Allah mummy ke kaɗaice kemin wannan fahimtar ko su asaben idan ina rainasu ai sun sani" "nama fiki zuciyar tausayi wallahi" ta faɗa sanda mahaukacin nan ya faɗo mata a ranta
Ƙanƙance idanu mummy tayi da faɗin "ni kike faɗawa kin fini tausayi?" Sassauta fuskarta tayi daga kumbura ta da takeyi tace "kai mummy ke kawai burinki na faɗi magana mistakely yanzu sai kiyi syllabus a kansa" ta faɗa sanda ta ƙara sa jikin hannun kujerar da Mummy ta ke ta kwanta a jikinta.
Sauke numfashi Mummy tayi jin tilon gudar jininta a jikinta gyara yanayin fuskarta tayi da faɗin "nasan kinada zuciya mai kyau amma atimes sai naga kamar kinada 'yar rashin kunya kinga ni mahaifiyar kice, ba yadda zanso ace kina bakin mutane, ki dinga danne zuciyar ki kinji?" Ta faɗa sanda ta shafa mata kanta.
Kai ta ɗaga tareda ƙara mannewa jikin mahaifiyarta.
"Ya lectures?" Mummy ta tambaya da kulawa
Narke fuska tayi da faɗin "nifa Mummy banason karatun wlh, nikaɗai nasan wuyarda nakeji a SKY LINE su baruwansu da kuɗin mutum karatu kawai aketa gana mana"
"Na sani, hakkannan dai zaki daure ai shi kanshi kasuwancin da kike so yana buƙatar ilimi wanda zai sa ki samu tactics na yadda zaki gudanar da kasuwancin ki"
Bata iyayi mata magana ba dan yunwar da kecin cikinta, ga gajiyar makaranta.
BINAZIR kenan ya ɗaya tilo wajan ALHAJI MANI CIZO da HAJIYA MARIYA.
HAUSAWA SABON TITI
Da sallama ya shiga cikin matsakaicin gidan daidai masu rufin asirin ubangiji. Umma dake zaune kan tabarmar a tsakar gida ta ɗago kanta cikin fara'a ta amsa masa, kallonsa take cikin tausayi da kulawa har ya tako ya zauna gefenta kan tabarma.
Cikin salon tsokana dan gusar da wata shimfidaɗɗiyar damuwa data gani a fuskarsa tace "kaga manyan munafukan ƙasa". Wani kyakyawan murmushi ya yi da faɗin "ummanaaaa" yaja sunan naata. Itama murmushin tayi masa da faɗin "yanzu bagashi na samu ladarka ba, daka shigomin gida kamar wanda aka aiko da saƙon mutuw...." shiru tayi da bakinta ta kasa ƙarasa cigaba da kiran sunan da dukkan wani mai rai yasan da wanzuwar wannan suna kuma Aya ce sukutum cikin Ƙur'ani.
Shima shirun yayi kansa a ƙasa, kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyar sa.
Numfashi ya sauke da faɗin "Najaa bata nan ne?" "Tana ciki yanzu tagama yimana wanki ne ta shiga ta ɗan kwanta ta huta. Shiru ne ya ƙara biyowa baya.
Numfashi ya sauke tare da ciro kuɗi a aljihun wandon sa, ya ajiye gaban Umman nasa da faɗin "Ga wannan ba yawa, ku ɗan sarrafa
dan zan kwana biyu ban shigoba"
Cikin ɗan nuna ɓacin rai tace "maza kwashe kuɗinka, duka duka yaushe ka bamu kuɗin da zaka wani ƙaramin? Kai kanka kasan ina sana'a ta, kuma Alhamdulillah dan haka ka ɗebe abunka"
Wani murmushi ya saki da faɗin 'to ki ajiyemin, amma zaki iya ranta fa!" Kai kawai ta girgiza dan tasan kome zatayi bazai ɗebi kudinnan ba, ya riga ya mallaka mata kenan. "Allah ubangiji yayi maka albarka, ya dafa maka cikin lamuranka, ubangiji yaji ƙan......" "Ameen ya Allah" yayi saurin katseta tareda miƙewa ya nufi hanyar fita. Da kallo tabishi harya fice ajiyar zuciya ta sauke tareda share wata guntuwar ƙwalla data taru a idanunta.
Yau ma kamar kullum tana karyo kwana ta hangi wannan mahaukacin a zaune kamar kullum, a kwance yau yake kamar mai bacci har ta wucesa tana hangen sa ta side mirror in motan. Saida tayi wanka ta shirya cikin kayan zaman gida sannan ta fito main palo ta nufi dining. Saida tagama serving kanta sannan ta ɗebo abincin har zata kai bakinta sai kuma ta dakata mahaukacin nan ne ya faɗo mata a rai tunani ta shigayi idan tanajin yunwa haukata jama'an gidan take da mita idan ba a gama abinci ba, to yaya kuma shi da bai dama hankalin da zai tantance yanayin da yake, wa yake dashi dazai bashi abinci, shida kullum yake raɓe jikin gidan, ga unguwan nasu ko zai shekara anan ba mai taimaka masa dan ba wanda zai iya noticing insa ballantana asan da zamansa. Itama dan jikin gidansu yake zama kuma ita kullum tana hanyan yawon makaranta shiyasa tayi notice insa.
Numfashi ta sauke sannan taci abincin ta, saida ta ƙoshi sannan ta ɗibi abincin a wani plate ta rufe tanufi wajan mai gadi.
Duddubawa tayi taga mai gadin baya nan hakan yasa ta ware ɗa kwalin abayanta ta yafa a kanta, kai tsaye waje ta nufa da zaton samun mai gadin acan waje, ƙwafa tayi ganin baya nan, har zata koma ciki sai kuma ta tsaya cak, juyawa tayi ɓangaren da yake, a zaune ta ganshi ya ƙurawa ƙasa ido, haka kawai zuciyarta ta umarce ta dataje garesa ta miƙa masa abincin da kanta, basai ta wani aiki mai gadi ba.
Cikin nutsuwa da aji take tafiya a haka harta isa garesa, a firgice ya ɗago jin motsi a kusa dashi, ƙoƙarin mannewa yakeyi da jikin bango yana zaro ido kamar yaga sabuwar halitta, haka kawai taji ya kara bata tausayi.
Abincin ta ajiye a gabansa tare da yimasa nuni da hannunta kan yaci abincin, kallonta yakeyi cikin nuna rashin yadda tare da zare idanu.
"Bari na tafi idan tsorona kakeji, amma kaci abincin zan ƙarama wani anjima" ta faɗa tareda juyawa cikin takun ta mai jan hankali. Kallonta yayi, sannan ya kalli abincin, sai kuma ya girgiza kan sa, kamar wanda yaga abin tsoro a cikin abincin.
Tana shiga ciki ta tadda mai gadin, wani kallo ta watsa masa da faɗin "Allah ya kawo dady aikinka yazo ƙarshe" dattijon da yafi ubanta a shekaru ne ya fara mata kirari "Haba uwar masu gida, a koreni na kama ina kenan? Ayimin afuwa autar dady" ya ƙarashe cikin sigar roƙo.
Kallonsa tayi sama da ƙasa da faɗin *amma baba kasan baka kyauta ba saboda wannan gate in ake baka kuɗi duk wata amma kazo ka barshi ba tsaro? ina laifin ka kullesa kafin ka tafi?" "Kiyi haƙuri, banɗaki na shiga sha'afa nayi ban datse ba, amma gaba zan kiyaye"
Ko kallonsa batayi ba tayi shigewarta ciki.
Da kallo ya bita, yarinyar na birgesa wani lokacin, tanada zafi, amma nan da nan zata sauka, kuma idan mutum yayi taka tsantsan sai ka gama zama da itama bata yima komaiba, duk girman laifin mutum, ana mata kirari da autar Daddy zata haƙura, shiyasa data ce yakusa barin aikin bai damuba, dan ba har ranta ta faɗa ba, ɓacin raine kawai.
Abu kamar wasa, duk sanda ta dawo daga makaranta idan taci abinci sai tasa mai gadi ya kaima sabon mahaukacin dake zaune a jikin ginin gidan nasu, wani lokacin ma da kanta take zuwa ta kai masa, ba uwa idan masu aikin gidan sukayi mata ba daidai ba idan ta tanka Mummy ta hauta da faɗa sai ta fito waje nesa dashi ta zauna opposite insa tana kallon sa, har sai zuciyarta ta huce daga abinda akai matane zata bar wajen ta dawo gida.
Shi ko duk sanda tazo wajansa ba ƙaramin razani yake ba, kuma ita kanta ta fahimci hakan, shiyasa take nesa dashi idan tazo.
Yau ta tashi gidan ba daɗi saboda aminiyar ta, kuma mahaifiyarta bata nan kamar yadda su asabe suka shida mata. Saida ta shirya sannan ta fito a hankula ta nufi waje, kai tsaye wajan majnun ta nufa, ganinta maimakon yaji daɗi, saiya canza fusakrasa nan da nan tsoro ya bayyana a fuskar sa.
Ɗan murmushi tayi masa kaɗan ta fara masa magana kamar da mai hankali take "idan dadina ya dawo zanyi masa magana a ɗau potonka a yaɗa ko Allah zai sa a dace 'yan uwanka su gani, kuma zan masa magana ya kaika psychiatric hospital kaga acan zaka samu kulawa"
Shidai kallonta kawai yakeyi , kamar baysan wanzuwarta a wajan. Fahimtar hakan datayi ne yasa ta murmushi sannan tace masa "karka damu da zarar daddy ya dawo zan daina zuwa wajanka bazaka sake ganina ba". Sunkuyar da kansa yayi kamar wani mai tunani, murmushi ta ƙara yi da faɗin "ni kawai so nake na taimaka maka kaji ka daina jin tsorona" bai ɗago kan nasaba dai, da alama kamar ya fara yarda da itane a yadda ta fahimta, murmushi ta sake yi sannan ta miƙe ta fara taku a hankula, ƙarar motarda taji ne a kusa da ita yasata tsayawa a daidai nan itama motar ta tsaya juyawa tayi tana ɓata fuska dan ta gane mamallakin motar.
Zuge glass in motar akayi, Mummy ce ke kallonta cikin mamaki da faɗin "ke kuma daga ina?" Fuska ta ɗan yatsina da nuna side inda mahaukacin yake da hannunta wanda ya tsura wa motar Mummy idanu Kamar zai hango fuskarsa jikin motar. Ɗan haɗe fuska Mummy tayi da faɗin "BINAZIR Ni sa'ar kice ina miki magana da baki kina amsamin kamar ba kyaso ko kina magana da wata sa'arki?" Sassauta fuskarta tayi da faɗin "Mummy ficewa fa kikayi kika bar gidan ba tareda na sani ba" kallon ta Mummy tayi na ɗan sakannni da faɗin "shigo Mu ƙarasa gida" kai ta girgiza "no Mummy nafison nayi tracking da ƙafa" ta faɗa sanda ta fara takawa cikin takun ta na nutsuwa.
Kai Mummy ta jinjina sannan ta maida idanunta kan side mirror na motan, tana kallon direction inda 'yar tata ta nuna mata, mahaukaci ta gani zaune a wajan ya ƙurawa motan idanu yana zare idanu, numfashi kawai ta futar sannan ta kunna key ta taka motan ta nufo Cikin gidan.
Sanda Mummy ta shigo bata ga Binazir a falon ba, dan haka kai tsaye ɗakinta ta nufa. A zaune ta sameta da waya a hannu. ɗago kanta tayi jin motsi a ɗakin, ganin Mummy yasa ta ajiye wayan tana murmushi da faɗin "kinzo biko kenan" itama Mummy murmushin tayi tareda samun waje a kusa da ita ta zauna da faɗin "biko ai sai daddyn ki nikam kinsan ƙaniyarki zanci idan kikayi abinda bai kamata ba" murmushi tayi da faɗin "am freely nasan through out yau banyi laifi ba, dan yau har makwancinsu Asabe naje mu gaisa". Murmushi Mummy tayi na halin 'yar tata yanzu tayima abin arziƙi yanzu kuma zaku iya ɓatawa wani time ma idan taima mutum kyauta a irin doguwar godiyar nan da wanda akaiwa kyauta keyi zai ɓata mata rai.
Shiru Mummy tayi na ɗan lokaci Sannan ta kira sunanta "BINAZIR" kallon Mummy tayi da faɗin "na'am Mummy" "na tambaye ki daga ina kike kin nunamin saitin wani mahaukaci right?" Mummy ta tambaya. Jijjiga kai tayi alamun tabbatarwa. "Good" Mummy ta faɗa sannan ta cigaba "meya haɗaki da shi?" "Ni kawai tausayi ya bani Mummy, I meet alots masu mental disorder amma ban taɓa jin tausayinsu kaman wannnan ba" "why?" Mummy ta jefo mata tambaya tareda tsareta da idanu "bcos Mummy zaki gansu suna tafiya suna tsince tsince a titi suna kaiwa bakinsu amma shifa Mummy Yana zaune a waje ɗaya ne, kuma kinga arean mu babu wani trash dazai samu ya tsinta abinci a ciki yaci shiyasa nake kai masa abinci" numfashi Mummy ta sauke da faɗin "Aminiya ni nake baki shawara da nasiha kan taimako da tausayin na ƙasa dake ko?". Kai ta jinjina sama alamun hakanne, wani numfashi Mummy ta ƙara saukewa da faɗin "ki cigaba da yi, tausayi da taimako abune mai kyau amma ki dinga lura da wa'yanda zaki dinga taimakawan, Allah kuma yayi miki albarka daughter me" ta faɗa tareda janyota jikinta. Wani sanyi Binazir taji a cikin zuciyar ta, ƙara shigewa jikin mahaifiyar tata tayi da faɗin "Ameen ya Allah Mother me".
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*