FANSA KO ƘIYAYYA

03

by @109051246447263646587

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*


Free pages


_Page3 _

     


      Da sauri ta bishi da gudu a haukace tasha gabansa, kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai gefe yana sakin numfashi.

Wani irin tsanarsa ca ke yawo a zuciyar ta, cikin masifa tsiwa haɗe da kukan dake zuwa mata tace "ban taɓa sanin kai ɗin dabba bane sai yau, mahaukaci, butulu kuma maci amana" runtse idanunsa yayi dan jin maganganun da take maka masa, sosai suke masa ciwo a zuciya, sosai zuciyarsa ke tafasa, amma bazai gwada fushinsa ba a kanta, danba abinda ya kawo saba kenan.

Wani hawaye ta share tareda sauke numfashi mai ƙarfi kamar wadda tayi aikin wahala.

Tana shirin yin magana taga sauran jami'an sun tawo tareda Dady zasu fita, girgiza kai ta shiga yi tareda sakin wani irin kuka maicin zuciya, kallonta ta maida kan Majnun cikin wata irin karyayyar murya take faɗin "wanne irin mutum ne kai? wanne irin baƙar zuciya ce da kai? Ahalin da suke tsaka da tattauna yadda za'a inganta maka rayuwa kakeson tarwatsewa da tozarta wa? wanne irin butulu ne kai Mahaukaci!" Ta faɗa cikin Karaji tareda tsugunnawa tasa gwiwukanta a ƙasa ta rufe fuskarta da tafin hannunta da sakin wani irin kuka mai cin zuciya.

Lumshe idanunsa yayi tareda buɗesu lokaci guda. Numfashi mai zafi ya furzar ya kewayeta ya sauka ƙasa.

Dady ne yayi ƙasa da kansa sanda sauran jami'an suka wuce dashi ta inda Binazir ke durƙushe, zuciyar sa sai wani irin zafi take masa, shi kaɗai yasan yanayinda yake ciki dan dai Allah yayisa mai dakakkiyar zuciya ne kawai.

"Mariya na baki Amanar komai" ya faɗa sanda suke fita gaba ɗaya.

Sai alokacin Mummy ta saki wani marayan kuka tareda miƙewa ta rungume Binazir.

Jinta jikin Mummy yasa ta ƙara sakin wani kuka mai taɓa zuciya, kuka sukeyi sosai, kukanda ba mai iya lallashin wani a cikinsu.

Binazir ce tayi ƙarfin halin janye jikinta daga jikin Mummy, cikin ƙarfin hali da dakewar zuciya ta fara share hawayenta tareda tsagaita kukanta.

"Wannan faɗan nawane, dani yake, nice silar bashi daman sanin gidan nan kuma nice silar da zan zamo sanadin da komai irin sunan ahalin gidannan nan yaji, saiya firgita". Ta faɗa cikin alwashi tareda niƙewa.

Mummy ce tayi saurin dakatar da ita tareda riƙo hannunta da faɗin "ina zakije?" Ko kema tafiya zakiyi ki barni kamar mahaifinki?" Mummy ta tambaya cikin karyewar murya

Wani irin murmushi mai haɗeda zubowar hawaye Binazir tayi tareda riƙo hannun Mummy cikin nata.  "Bazan taɓa barinki ba Mummy, inaso ne na ɗakko wayan Dady dan na kira lauyansa na faɗa masa abinda yake faruwa" cika mata hannu Mummy tayi tareda jijjiga kanta alamar ta fahimta.

Bayan ta ɗakko wayan ne ta miƙawa Mummy da faɗin "ki buɗe securityn Mummy ki faɗa masa dukkan abinda ya faru" ta faɗa tareda barin part in Dadyn, dan wani irin karyewa zuciyar ta tayi, sanda taga photonsu ne ita da Dady a screen in wayar.

Da kallon tausayi Mummy ta bita, itama saida zuciyarta ta tayi sanyi sanda taga photon maigidan nata tareda gudan jininsu a fuskar wayar.

Tana kiran nomban lauyan ya amsa mata, ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba sanda yaji meke faruwa, kuma yayi mata alƙawarin zuwa Headquartern DSS in a daren dan jin yadda abin yake tareda yi mata alƙawarin gobe da safe zaizo har gidan ya faɗa mata yanda ake ciki.

   Sanda jami'an suka fito da Dady main palon, anan suka samu ma'aikatan gidan sun tsaya cirko cirko cikin tsoro, kallo ɗaya Dady yayi musu ya kauda kansa gefe da faɗin "karku damu, ku cigaba da aikinku Hajiya na nan".

Ƙasa magana ma'aikatan sukayi, dan abunne ya taɓa zuciyarsu sosai, ace ubangidansu da suke faharin kasancewar su a ƙarƙashin sa, dan baya yi musu mugunta ko kaɗan haka sauran iyalan nasa, mutumci ne kawai a tsakaninsu. ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, sanda mai gadi yazo har makwancinsu yana shaida musu wai wani mahaukaci mai zama a ƙofar gida yazo da jami'ai sun haura saman Alhaji. 

 Sanda su Dady suka fito waje, a jikin mota suka samu Majnun ya jingina bayansa a murfin motar, hannunsa goye a ƙirjinsa ya tsurawa ƙasa ido.

 Yanajin alamun su, ya ɗago kansa tareda tashi tsaye sosai. Kallo ɗaya yayiwa Dady ya kauda kai gefe tareda matsawa daga jikin motar, shi kam Dady wani murmushin takaici ya saki . sauran jami'an ne suka shigarda Dady ciki, tareda shiga suma cikin motan.

Kallon inda yayi rayuwa matsayin mahaukaci na tsawon wata guda yayi,  index and middle fingers insa ya ɗaga sama tareda saita su wajan da ya zauna again kuma ya ƙara ɗagasu sama (alamun Harbin bindiga) sannan ya janye yatsunsa ƙasa tareda sauke wani nauyayyan numfashi ya shige gaban motan driver ya jasu Dan Shi dama suke jira.

   Binazir kam, ɗakinta ta shige tasha kuka kamar ranta zai fita.  

Wai Dadyn ta, mahaifinda takeji kamar ranta, wanda shaƙuwarsu ta wuce iya ta ɗa da mahaifi, ta koma ƙaunar kai da kai, itace shi, shine ita wai yau shine za azo a gaban idanunta ana tuhumar sa da laifin shigowa da miyagun ƙwayoyi cikin ƙasa a Lokacin da yake tsaka da jin damuwarta dan magance mata ita kamar yadda ya saba.

The most painful, that fucking mental Wanda ta ɗau dukkan tausayin duniya ta ɗora a kansa, shine zai mata wannan irin butulcewar tareda yankan ƙauna?  Ta tsane shi, tsana kuma mafi muni, sannan ta ɗau alƙawarin ƙuntata wa ahalinsa, kamar yadda ya ƙuntata mata.

Wani kukan ta saki na tausayin halinda mahaifinta yake ciki a wannan daren, mutuminda rayuwarsa ke rabi da kwata a abroad wai yau shine cikin komar hukuma, hukuman ma ta Nigeria.

A iya saninta, mahaifinta ɗan kasuwa ne dake kasuwanci, kuma yake da hannun jari bila adadin a kamfanoni da dama, amma wai yau shi akewa ƙazafi da importation of illicit drugs.

 Maganar baba Mai gadi ce ta dawo mata a ranta, sanda take tambayarsa dalilan da kesa ayiwa mutm black magic  "ƙyashi da hassada"

Tabbas sune dalilanda yasa akayiwa mahaifinta wannan sharrin, kuma ta lashi takobin saita ga bayan ko wane wannan magauci na mahaifinta.

    Suna ƙarasawa Headquartern, aka shigar da Dady criminal prosecution room, anan aka fara tuhumar sa, inda ya nuna baisan abinda ke faruwa ba, duk iya binciken su, sun kasa gano abinda suke so ya amsa da bakinsa, Chief officer ne ya bada umarnin a kaishi ɗakin ajiya, for further investigation.

Duk wannan abin da ake, majnun na gefe, be yadda ya shiga ɗakin binciken ba, saida aka gama tuhuman Dadyn, sannan ya miƙawa Chief officer dukkan wani file daya ƙunshi case in Dady daya tattara.

   

A wannan daran kam, waɗannan masoyan ahali ba wanda ya samu damar rintsawa. Mummy, Dady da Binazir.

Kowa cikin ƙuncin zuciya yakeyi kuma kowa da abinda yake saƙawa a ransa.

       DADY

   Shi dama tun sanda Binazir tazo masa da batun wani mahaukaci, yaji hankalinsa bai kwanta da lamarin saba, shi yasa duk sanda zai fita ko zai dawo saiya saka idanunsa a kansa, kuskure ɗaya da yayi shine na kasa sa wani yayi spying insa dan ya lura da dukkan wani motsinsa amma ina Kasuwanci sa ya rufe masa idanu ya kasa wannan tunanin.

Iyalansa ne suka faɗo masa a zuciyar sa. Tabbas yasan suma iyanzu suna cikin mawuyacin hali, yana tausayin kansa amma yafi tausayawa tilon 'yarsa dake ƙoƙarin ta taimaki makashin mahaifinta cikin rashin sani. Numfashi ya sauke a fili tareda neman mafitar ubangiji.


    MUMMY

  Har tsawon wannan daren, ta kasa runtsawa kuma ta kasa tsaida hawayenta. Ba kuka takeyi ba, amma hawayenta sunƙi daina zubowa daga idanunta.  ita kaɗai tasan irin ɗacinda takeji a zuciyarta, kuma tasan bamai iya fahimtar yanayinta sai matarda irin hakan ta faru gareta.

Wai ace mijinta, kuma masoyi gareta, uba ga 'yar ta ace wai suna saka da Lokacin faranta ran junansu, tana tsaka da kai kukanta da damuwarta ga mijinta, mijinda takeda tabbacin atake a lokacin zai magance mata matsalolin ta, wai ace dai-dai wannan lokacin za'a kawo musu farmaki a rabata da mijinta tanaji tana gani, a manna masa ƙazafinda bamai iya fitar dashi sai Allah? Wannan wacce irin rayuwa ce?

Kukane yazo mata da sauti mai ƙarfi, ganin ba magani da kukan zaimata yasa ta miƙa tareda nufar toilet ta ɗauro alwala ta haukan sallaya, tareda ƙasƙantar da kanta ga ubangijin ta.


    BINAZIR

  tana zaune kan sallaya, sai tayi sallah kamar raka'a biyu, saita zauna kan sallaya tana tunani. 

Tunani takeyi na halinda mahaifinta yake ciki. Tasan da wuya ya iya rintsawa, ga baƙon makwanci ga kuma babban tabon mummunan ƙazafinda akayi masa a zuciyar sa. Tabbas tasan wannan abin bazai taɓa barinsa ya rintsa ba, zai zame masa babban tabo ne a zuciyar sa dan Dadyn ta irin mutanan nan ne masu ɓoye abu a ranau.

Fargabarta ɗaya, kada damuwa yasa zuciyarsa ta kamu da wani ciwon.

  Ita yanzu tayiwa kanta alƙawarin kuka da nuna damuwarta a fili, ita yanzu zuciyarta cike take da KIYAYYA da kuma son ɗaukar FANSA.

   *************************


   HAUSAWA SABON TITI


Naja ce zaune tana mitar wanke wanken da tayi na karin safe, duk tabi sai mita takeyi itake komai harda faɗin gaskiya iya zatasa YAYA ya nemo mata mai tayata aikin gidan.  

Umma dake zaune tana jan carbi ko cikanki batace mata ba, asali yi tayima kamar bayan ita dake zaune riƙe da carbi ba wata halittar.

Suna a wannan yanayin ne Naja ta tsinci muryarsa a soro Yana sallama. Da sauri ta kwanta kafin Umma ya ankare tana faɗin "wash Allah na". Umma dake lazimi taji tana wash tayi mata banza dan duk tunaninta mitar ce bata ƙareba.

  Shigowar sace tasa umma sakin fara'a tareda yimasa sannu da zuwa, sai kuma takai kallonta kan Naja data dage tana kiran sunan Allah. Carbin hannunta ta maka mata a jiki, tana shirin maka matane yayi saurin tarewa tareda zama kusa da Najan. hakanne yasa Naja miƙewa zaune da sauri tana sosa inda Umma ta daketa. 

 "Ai da ka barni da ita, yanzu fa tagama yimin mita da sababi dan tayi wanke wanke shine dan sharri tanajin muryarka zata kwanta tana kiran sunan Allah?".     Umma ta faɗa cikin takaicin halin Najan. 

Shidai murmushi yayi tareda bawa umma haƙuri dan inda sabo ya saba da faɗan umma da autar ta.

 "Ina kwana umma" ya katse sababin da umma zata farayiwa rabin jikin tasa. 

Umma ce ta saki tsaki da girgiza kai tana kallon Naja da faɗin "kinji haushi kekam wallahi, jira kike ya gaidaki ko?" Sannan ta maido da hankalinta kansa suka gaisa tareda tambayar lafiyar juna.

Kallon Naja yayi daketa ɓata fuska "tawan" ya kirata cikin muryarsa mai dukan zuciya.

Langaɓe kai tayi a kafaɗarsa fa faɗin "Ni wallahi Yaya kayi sauri kayi aure in tattara in koma gidanka kona samu 'yancina"

Wani ƙayataccen murmushi yayi tareda sosa gashin girarsa "kenan na nan bakida wani 'yanci?

Umma data saki baki galala tana kallon iskancin Naja sai kawai tayi ƙwafa da faɗin "Ni nama manta tun zuwanda kayi kwanaki na faɗama Bishirar gidan Babanku Garba tazo gaishemu".

  Murmushi ya saki da faɗin "Mun gode da zumunci, Yarinyar na ƙoƙarin hakan sosai" 

"Wallahi kam shiyasa take burgeni" umma ta faɗa har zuciyarta.

"Ina dan nace Yaya yayi sauri yayi aure ne umma kike kawo masa zancen waccan agwagwar to na haƙura"

"To rasa kunya ɓerar tanka" umma ta faɗa tareda kai mata duka.

Da sauri ya miƙe tsaye da ita, dukan ya goce, janta yayi zuwa ɗakinsa na soron gidan.

 Ƙwafa umma tayi da faɗin "zai tafi ya barni dake ne ai"

A can ɗakin nashi kam nasiha yake mata na yadda zata zauna lafiya da umma. "Nafa san halinki auta, kece kejan umma faɗa, kinga ni harna gama rayuwata da umma, bata taɓa zagina ba ballantana duka saboda ina kiyayewa"

"Zan kiyaye" ta faɗa tana sosa gashin kanta.

 Murmushi yayi tareda zaro kuɗi a aljihu ya miƙa mata dan yasan shine damuwarta. Aikam godiya kamar tayi masa sujjada sujjada dan har saida yayi kamar zai ƙwace kuɗin sannan ta bar ɗakin cikin murna.

 Numfashi ya sauke ƙasa. Allah yayisa mutum mai tsananin ƙaunar 'yan uwansa, dan baya taɓa haɗa kaunarsu dana wani a zuciyar sa. Ko a irin haɗuwa ta family, baya wannan karan in zaiyi abu ya haɗa da sauran no kai tsaye nasa yake warewa yayi saidai ayi dashi a bayan idanunsa, dan mai bakin tankawar wanda zai masa faɗa ya gyara bashida wannan powern a wajansa dan yariga da yayi wa ahalinsa tabon da bazasu taɓa manta shi ba. dan madai suɗin masu tsarkakakkun zukata ne shida Ummansa, da ba abinda zai kaisu taron familyn nasu.

  Ajiyar zuciya ya sauke na tuna wasu abubuwa marasa daɗi da suka samesu shekarun baya da kwanakin baya da baza'a Gaza irga adadinsu ba.

Runtse idanunsa yayi tareda buɗesu.

Wajan da yake ajiye muhimman abubuwanasa ya nufa, wani abu mai harafi 2 daya gaza fahimtan ma'anarsa ya ɗakko yana juyawa a tafin hannunsa, idanunsa ne yaji suna masa yaji yaji, hakanne yasa ya maida abin maɓoyarsa, jiki a mace yaja jikinsa yabar wajan, tareda ɗaukar manyan ƙuduri da fansa ga duk wanda ya aikata masa hakan.

Komawa yayi bakin katifa ya zauna har saida yaji zuciyar sa ta daidaita, sannan ya miƙe dan yin wanka ya nufi wajan nemansa.






*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*