04
*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
Free pages
_Page4 _
DARMANAWA GANDUN SARKI
Mummy ce zaune a kan ɗaya daga kujerunda ke main palon, Binazir na kwance kusa da ita akan kujera tayi pilo da ƙafafun Mummy suna sauraron bayanin da lauyan Dady yakeyi musu tareda gabatar musu da ɗansa SALIM a matsayin mataimakin sa mai taimaka masa kasancewarsa shima Lauya ne dan ayyuka sun masa yawa sosai "jiya naje Headquartern kamar yadda na alƙawarta miki, kuma na samu ganinsa, saidai yaƙi cemin komai, bai bani haɗin kaiba amma inaga Yakamata a bashi time for him to have flexibility in his mind".
Kai kawai Mummy ta jinjina, Binazir kam ajiyar zuciya ta sauke da tashi zaune tare da faɗin "Barrister inason zuwa wajan Dady". Kallonta yayi sannan ya girgiza mata kai yana Shirin magana Barrister Salim ya katse sa "Please Abi allow her to go".
Kallon Salim Barrister yayi sannan ya dawo da dubansa ga Binazir, saida yayi ɗan sakanni wajan kallon nata sannan ya sauke ajiyar zuciya da faɗin "banda kuka fa idan munje"
"No Abi, just take your way, zan rakata" Salim ya katse hanzarin mahaifin nasa.
Murmushin yaƙe tayi da faɗin "tun jiya kukana ya ƙare, I will maintain my self".
Kallon Mummy tayi data rufe fuskarta da hannun kujeran da take, wani numfashi ta sauke dan zuwa yanzu tasan nauyi ya hau kanta sosai dan tafi mahaifiyarta dakewar zuciya.
"Me zancewa Dady?" Ta tambayi Mummy cikin sanyin murya.
Girgiza kai kawai Mummy tayi ba tareda ta ɗago kanta ba.
Wani yawu mai ɗaci ta haɗiye tareda gyara hijabin jikinta ta fita waje cikin takunta na ƙasaita.
Da sauri Salim ya miƙe ya bita, dan tunda ya ɗora idanunsa a kanta, ya gaza samun nutsuwa.
Tunawa da bata ɗakko keyn motanta ba yasa ta dakata datafiyan, salim ne yasha gabanta da faɗin "yanaga kin tsaya?"
" Car key's" ta faɗa a hankali.
Murmushi ya saki da kaɗa mata keyn motansa a fuskanta da faɗin "let's manage mine" yaƙe tayi da faɗin "Nagode".
Cikin motan shiru, bakajin sautin komai saina injin motan dake tashi a hankula.
Gajiya yayi da shirun, sannan ya waigo ya ɗan kalleta kana ya maida kansa ga tuƙin da yake.
"Bansan me zance miki ba, but to be Frank, naji ba daɗi sosai na abinda ya faru da Dadyn ki kuma na tausaya masa mutum mai girma da karamci bai cancanci irin wannnan mummunan ƙaddarar ba, amma haka Allah ya hukunta sai haƙuri, kuma ina fatan Allah ya fito dashi ya kuma bayyana gaskiyansa da gaggawa". Lumshe idanunta tayi Sannan ta buɗe su at the same time. Tun jiya da abinnan ya faru, babu wanda yayi mata addu'a irin wannan sai shi kuma taji daɗin addu'ar ba kaɗan ba, danko ma'aikatan gidansu iyakacinta dasu ido ne kawai da fuskar tausayi da suke nunamata, kuma bata damuba dan tasan basira abincewa ne tayi musu uzuri dan basusan taƙamaiman abinda ke faruwa ba, they only saw the scene but not the captioned. Taji daɗin maganan Salim sosai hakanne yasa ta ɗauki Barrister Salim ta ajiyesa a wani waje mai daraja a zuciyarta.
Waigowa tayi ta kalli side insa, sannan ta maida kanta ga side inda take.
"Kasan wani abu?" Ya tsinci muryar ta tana tambayarsa da salon son suyi magana a dai dai lokacin da ya yanke tsammani daga jin sautin amsawar addu'ar da yayiwa Mahaifinta.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda faɗin "a'a, sai kin faɗa"
" Mahaukacin da nakeson taimaka shine yayima Dady wannan abin" ta faɗa cikin jin ɗaci.
"As how? More details please, wlh ban fahimta ba" ya faɗa muryansa da ɗan ruɗu dan dagaske bai gane ma'anar kalamanta ba, tareda gangara motansa bakin titi.
A hankali ta warwaremasa komai, tun daga farkon ganinta da mahaukacin a jikin gidansu har zuwa jiya.
Kallonta kawai yakeyi na tsawon lokaci, itakam wani irin ɗacine ya tsaya mata a ƙirji, saikuma ga hawaye kaman an kunna famfo, bata dakatar dasuba, dan tana ganin wani relief ta saamu a zuciyarta, tunda harta nemi wani ta faɗamasa abinda yake mata yawo a zuciya, na cin Amanar ta da baƙin azzalumin mahaukacin can da yayi mata.
Bai hanata kukan ba, sai kallonta da yakeyi cikin tausayawa, dan yasan kukan zai zama sassauci a ranta.
Saidai tayi Mai isarta, sannan ta share hawayenta, tareda gyara zamanta jikin kujerar tana sauke numfashi.
Shima numfashin ya sauke, tareda kunna motar yabar wajan ya fara tafiya a hankali.
Tunanin maganmanunta kawai yakeyi a ransa tabbas wannan ya wuce jami'in DSS saidai a kirashi da SPY.
Har sukazo headquarter bai ƙara cemata komaiba, kuma bashida abinda zaice matan a yanzu.
Haka itama bata damu da shirunsa ba, dan tasan duk wani mai hankali da zata faɗawa abinda ke faruwa, dolene ƙwaƙwalwarasa ta shiga nazari da mamaki na ɗan wani lokaci, saɓanin tata ƙwaƙwalwar da ta gaza nazari da dogon tunani sanda magaucinsu yazo musu a siffar mai taɓin hankali.
Sanda suka shigo Headquartern ji tayi zuciyarta ta tsinke, wani hawaye ne ya zubomata tayi saurin sharewa daidai sanda ta haɗa idanu da wani jami'i dake magana da ɗan uwansa, ɗauke idanunsa yayi a kanta tareda maida kansa gefe, ajiyar zuciya ta sauke, tabi bayan salim suka shiga ciki.
Da fari ba'a basu damar ganin Dady ba sai bayanda Salim ya gabatar da kansa matsayin lauyan, kuma ɗa sannan mataimaki ga lauyan Dady sannan aka basu wajan zama kafin a fito da Dady.
Binazir gabaki ɗaya ta tattara hankalinta ne ga inda wanda ya tafi dan kiran Dady yabi.
Zuciyarta ce ta kusan bugawa, sanda taga Dady a tsakiyan wasu jami'ai, ba alamun tabo ko shatin duka a jikinsa, amma kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci baya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ko misƙala zaratan.
Haɗiye abinda taji ya zomata wuya tayi tareda miƙewa a sanyaye sanda idanun Dady ya sauka cikin nata. Yaƙen murmushi tayi,
"You look handsome Dady" ta faɗa cikin ƙarfin hali.
Wani murmushi mai ɗaci ya sakar mata da faɗin "but You look ugly"
She can't hold it anymore, faɗawa tayi jikinsa ta ruƙunƙumeshi tana sakin wani irin kuka mai cin rai, runtse idanunsa yayi jin wani abu mai ɗaci ya caki maƙoshinsa.
Salim dake tsaye zuciyarsa fal tausayinsu ne yayi gyaran murya, hakan yasa Dady buɗe idanunsa.
Ya gane Salim dan sunsan juna a lokacinda yake kaiwa Barristern nasa ziyara har gida idan buƙatan hakan ta taso.
Gaisheda Dady yayi cikin girma, tareda jajanta masa. "Naji komai na abinda ya faru kuma insha Allah zamuyi iya ƙoƙarinmu nida Abi, fatanmu ka kasance mai bamu goyan baya, Allah kuma ya shiga lamarin"
"Ameen na gode sosai" Binazir ta faɗa sanda ta janye jikinta daga na Dady tana share sauran hawayen fuskarta tareda ƙarawa Salim wani girma a zuciyarta.
Dady kam kai kawai yake girgizawa tareda futar da hucin numfashi, shi kaɗai yasan me yakeji a zuciyarsa, haka zalika kuma shi kaɗai yasan me ma'anar wannan shari'ar zata haifar ga shida iyalansa, da duk wani masoyinsa, kai harma da maƙiyansa.
Jami'anda suka rako Dady ne sukazo maidashi, dan lokacin ganinsa ya ƙare.
Da sauri Binazir ta juya baya tareda runtse idanunta sanda sukasa Dady a tsakiya, gabanta salim ya dawo yana mata wani irin kallo na tsantsan nuna tausayinsa gareta.
Allah kawai take ambata a cikin zuciyarta.
"It's okay dear" Salim ya faɗa bayan ya tabbatar da su Dady sun ɓace a wajan.
Buɗe idanunta da suka sauya launi tayi a hankali ta saukesu kan fuskar salim.
Jinin jikinsa ne yaji ya tsinke da yadda yaga yanayinta, murmushi yayi cikin dakewa tareda nuna mata hanyar waje da hannuwansa da faɗin "can we?" Kai ta ɗaga masa sannan suka fita, suna zuwa compound na Headquartern taja ta tsaya.
Kallonta Salim yayi cikin neman sanin manufar hakan.
Idanunta ta runtse ta buɗesu kan Salim da faɗin "i have to see that bastard b4 I leave" ta faɗa cikin ɗacin zuciya.
Kai Salim ya ɗaga mata cikin nuna amincewarsa da hakan dukda yasan ba amincewarsa take nemaba, tadai faɗamasa ne kawai.
Har ta ɗaga ƙafa zata juya, sai idanunta ya hango mata wannan jami'in da suka haɗa ido dashi ɗazu sanda ta shigo cikin compound.
Tsaye yake jikin mota kansa duƙe yana daddanna waya da duka hannuwansa.
Ji tayi gabanta ya faɗi, sai yanzu take ƙare masa kallo, tabbas dukda yanzu a ainahin suffarsa yake, amma hakan bazaisa ta kasa ganesa ba dan ta karancesa sosai duk sanda take zuwa wajansa kallon ƙurilla kawai takeyi masa, sai yau ta godewa Allah daya samata sha'awar ƙaremasa kallo a sanda yake mahaukaci, tayu Allah yayi mata tanadin wannan ranar ne.
"See the Monster" ta faɗawa Salim tareda nuna masa inda Majnun ke tsaye.
Kallonsa Salim yayi sannan yabi bayan Binazir da tariga tayi gaba.
"MAHAUKACI!" ta faɗa cikin ɗacin murya mai nuna tsantsan tsana da ƙiyayya ga wanda ake yiwa magana s sanda ta isa gabansa.
Tsammm yayi da ransa, dan ji yayi ƙirjinsa ya buga. dakatawa yayi da danna wayan ba tareda ya ɗago kansaba.
Wani murmushin takaici ta saki da faɗin "yau kuma? Yau ni idanuwanka ke ƙin gani, idanuwanda kullum suke cikin nawa idanun a zare? Yau sune suke gudun fuskata?" Ƙala bai cemata ba, kuma bai ɗago kansa daga wayar ba, dukda ba dannata yakeba amma ya gaza janye hannuwansa da idanunsa akan wayar.
Waigowa tayi wajan Salim da kewa majnun kallon ƙyama da faɗin "can You imagine? su kansu idanuwansa sun shaida mamallakin su butulune shiyasa suka kasa dubana" dawoda dubanta tayi garesa tareda sauke wani numfashi, kallonsa take from head to toe irin kallon tsanan nan dan sotake ta fara gano makusarsa a jiki ta gayamasa magana son ranta kafin wani tanadin da zatayi masa gaba, tag in gefen aljihun gaban rigarsa ta gani, inda sunansa ya bayyana SAMIR , ita sai yanzu tama tuna da ainahin sunansa daya faɗa jiya a palon dadi. Ajiyar zuciya ta sauke da faɗin
" Kasani, yadda kasa ahalina cikin ƙunci nima saina sa naka, saina tarwatsa dukkan wani farin ciki da familyn ka suke taƙama dashi"
"ɗas! ɗas! ɗas!" ta mirza yatsunta suka bada sauti dai dai fuskarsa
"Mark my words" ta faɗa tareda barin wajen cikin takun gayya da izza.
Salim ne ya ƙare masa kallo
"Shameless" ya faɗa sanda yake barin wajan.
Sai a lokacin Sameer ya ɗago kansa yakai dubansa ga Salim daya riga ya juya baya.
Ajiyar zuciya ya sauke, tareda maida wayarsa cikin aljihun wandon sa yabar wajan.
Abubuwa sun rincaɓe bilhaƙƙi da gaske, dss sai bincike sukeyi akan case in Dady, so suke su gano komai, akan dadyy, amma yaƙi basu dama ko kaɗan, abu ɗaya ne yake cewa aduk sanda irin hakan ta tashi idan an shiga dashi prosecution room magana ɗayace yake faɗa "ban san me kuke nufi dani ba" so suke ya amsa laifinda ake tuhumarsa dashi amma abin ya gagara dan yaƙi amsawa kuma yaƙi buɗe komai.
Saboda kasancewar sa babban mutum ne a jihar yasa suke saurara masa amma idan yaƙiyi musu magana a gaba, zasuyi forcing insane ya amsa da bakinsa. dan so suke su gama komai nasu a sirri, batareda sanin sauran wa'yanda aka basu information akansu su ankare ba.
BINAZIR
tana kwance ɗakin Mummy Kamar mai bacci amma ba baccin takeba, damuwa ce kawai tayi mata yawa, kwata kwata bata fahimtar komai ba kuma ta iya gane komai dan rayuwa tayimata wuya sosai, wajan mutum ɗaya takejin sanyi wato Salim, dan yakan tattaro dukkan wani tausassan lafazi mai kwantar da hankali da samawa zuciya nutsuwa ya diresu a kunnenta, wanda a take zuciyarta ke amsar su.
wayar Dady dake gefen pilonda take ne yayi ƙara, kallon Mummy dake zaune kan sallaya tayi. Ajiyar zuciya ta sauke tareda buɗe saƙon. Alhaji KD taga an rubuta
" Ale Cizo kwana biyu shiru? Ka buɗe Gmail inka akwai saƙo, na barmaka, dan kayan wajan Ake isa fa yaƙi shiga, saura ƙiris a kama yarona bahago"
"Mummy yy". Binazir ta kirata cikin matuƙar firgici da ɗimuwa, ba abinda ƙirjinta keyi sai bugawa da ƙarfi.
Shafa addu'a tayi cikin nutsuwa sannan ta miƙe ta nufi wajan 'yar Tata. Miƙa mata wayar Binazir tayi, tareda runtse idanunta da ɗora hannunta kan ƙirjinta ta dafe tana girgiza kanta
Kallon screen in wayar Mummy tayi, tareda karanta saƙon. Runtse idanunta tayi sakamakon wani hawaye mai yaji daya zubo mata.
Jin shiru Mummy batace komaiba yasa Binazir buɗe idanunta da suke a runtse ta warasu kan fuskan Mummy. Ganin yanayin Mummy yasa ta kira sunanta, buɗe idanunta Mummy tayi tana kallon Binazir da har lokacin tana cikin fargaba da ɗimuwa.
" Me kika fahimta da wannan saƙon?" Binazir ta tambayi Mummy idanunta kafe cikin nata kaman ba mahaifiyarta takewa tambayan ba saboda firgicin da take ciki, ita bata zargin Dadyn ta, amma saƙon da akai masa na nufin komai dan zargi kala-kala yazo mata zuciyarta dukda saƙon a dunƙule akayi sa amma meya haɗa Dadyn da kasuwancin da za ace ana tsoron kar wani ya gani?
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke da faɗin "bazan ɓoye miki gaskiyarda kikeda haƙƙin saniba"
ƙara girman idanunta tayi tana kallon Mummy cikin ruɗu, Riƙe kanta tayi sakamakon wani irin sarawa da yayi mata tana fidda hucin numfashi
"Mummy banason Jan magana, ki faɗamin abinda kika sani kawai" ta faɗa cikin azabar ciwo.
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda rungumota ta kwantar mata da kanta a kan cinyarta, sannan ta riƙon hannunta cikin nata haɗe hannuwansu tayi waje guda.
" Ki sani bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa koda ta second ɗaya ce, mahaifinki ya kasance mutum mai nagarta da sanin yakamata, kuma mutum mai neman halal insa, amma bansan ya akayi ya caƙuɗe halal insa da wata ɓatacciyar hanya ba, abu ɗaya na sani ƙaddara ce ta kama mahaifinki bada jimawa ba, dan har a watanni biyar da suka shuɗe mahaifinki na tsaftatacciyar hanyar nema ne amma a cikin shuɗewar lokaci kaɗan ƙaddara ta faɗa mana mu duka dan Binazir da gaske DADY ya aikata laifinda ake tuhumarsa dashi" ta ƙarshe cikin karyayyar murya tareda sakin kuka.
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*