05
FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
Free pages
_Page 5_
Ji tayi dukkan wani sense organs dake jikinta sun dakata da aiki. wani numfashi dake shirin komawa cikinta ne ta jawosa da ƙarfi ta saukesa a zafafe wanda yayi sanadin dawowarta cikin hayyacinta.
Yunƙurin miƙewa takeyi amma Mummy ta dakatar da ita. wani yawu mai ɗaci ta haɗiye da faɗin "me kike tunani zanyi Mummy? magana zamuyi dake" ta faɗa a wahalce cikin matuƙar ciwo.
Cikata Mummy tayi tareda kallonta cikin tausayi tabbas tasan so take ta jure ta kuma danne abinda ke cikin zuciyarta amma ita tafison ta amayar da koda rabin abinda takeji a cikin zuciyarta ne dan amayarwar zaifi mata sauƙi da rage raɗaɗin zuciyarta dan tasan wannan lamarin ba irin abinda ake binnewa ne kawai a zuciya ba. Abin da babban ciwo ga 'yar tata.
itama sanda ta gano gaskiyar lamarin ba ƙaramin ɗimuwa ta shigaba ambaton sunan Allahn da ta ringa yine ya kuɓutar da ita daga faɗawa cikin mummunan yanayi a lokacin. Ajiyar zuciya ta sauke sanda taji Binazir ta tashi daga jikinta tareda maida idanunta gareta.
Kallon Mummy takeyi da idanuwanta da suka canza kala saboda tsananin ciwo da tashin hankali.
"Mummy" ta faɗa cikin rauni, sai kawai ta ɗora kanta akan kafaɗar Mummy tareda sakin wani irin azababben kuka maicin zuciya.
Runtse idanunta Mummy tayi tareda sakin ajiyar zuciya. a wannan karan kam dolene ta aro jarumta tasawa zuciyarta juriya dan 'yar tata tana buƙatar kulawarta.
Bata hanata kukan ba, saida taga kukan yana neman wuce ƙa'ida, sannan ta fara lallashinta cikin kalamai masu taushi da nasihohi, da ƙyar ta samu ta tsagaita kukan nata, amma sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai.
"Mummy zuciyata zafi da zugi takemin, ga raɗaɗin azaba Mummy kaman zan mutu" ta faɗa cikin yanayinda zai tabbatar ma da tana cikin matsanancin azaba da ciwo.
"Mummy nasan inason DADY Kuma mun shaqu dashi sosai amma a yanzu zuciyata faɗamin take da ba don Dady nakeyi ba a matsayinsa na mahaifi, yanzune nakejin wani sabon ƙaunarsa da tausayinsa a zuciyata a matsayinsa na mahaifina, Mummy duk daɗin da Dady ya samu da ribar kasuwancin sa namu ne tare mukeyin yadda mukaga dama da dukiyarsa, haka zalika Mummy dolene mu fuskanci wannan ƙaddarar tare".
Tsagaitawa tayi da kukan tareda ɗago kanta daga kafaɗar Mummy ta share hawayenta tana kallon cikin idanun Mummy, Numfashi ta fusgo da ƙarfi da faɗin "Mummy yanzune zaki nunawa duniya irin ƙaunarda kikewa mijinki, a yanzune zaki tabbatarwa da duniya keda Alhaji Mani Cizo kun zama abu ɗaya, kece shi, shi neke.
Dolene Ni dake da Barrister muga Dady domin sanin ta ina zamu fara taimaka masa, kuma dolene duk wani wanda ke irin wannan baƙin kasuwancin da Dady ya bayyana gaban hukuma dan bazan lamunci ganin mahaifina matsayin mai laifi shi kaɗaiba, dolene asamu ƙarin uban wasu" ta ƙarashe da sakin numfashi kamar wadda tayi tsere, yanayinta duk yabi ya sauya.
Ajiyar zuciya Mummy ta saki na tsoron yadda 'yar tata take magana a záfafe kamar tanayi a gaban sa'anta bada mahaifiyarta ba. Ita fargabanta ma kafa ace wani matsalan ne keson shigarta. Da sauri ta girgiza kai dan bata fatan wani abu mara kyau ya kasance ga tilon 'yarta.
Kallonta takeyi cikin tausayi, tabbas duk abinda 'yar tata ta faɗa gaskiyane, duk mugun ɗabi'un mijinta, dolene ta kasance a bayansa ballantana shi baida wata mummunar ɗabi'a da take gani face wannan ƙaddarar data samesa.
Maida idanunta tayi kan Binazir data rufe idanunta tana sakin numfashi.
Jin alamun ido a kanta, yasa ta buɗe idanunta, a fuskar Mummy idanun nata suka sauka.
"Kin san me ?" ta tambayi Mummy.
Girgiza mata kai Mummy tayi alamun bata saniba.
"Dolene Alhaji KD da Bahago su shiga komar hukuma, ki yiwa Barrister magana idan bazai samu zuwa ba, ya turo mana Salim" tayi maganar cikin jaddadawa tareda sauka a gadon tabar ɗakin.
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda yiwa 'yar tata fatan Allah ya sassauta mata zuciyarta kamar yadda yasawa tata zuciyar salama da dangana.
Binazir kam, kai tsaye ɗakinta ta nufa, tana shiga ta faɗa kan makeken gadon ta tareda sakin wani wahaltaccen kuka, kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita, saida taji numfashinta na shirin shiɗewa ne sannan ta tsagaita, bawai don tanajin tsoron tafiyar numfashinta ba, sai da haryanzu akwai amfaninda numfashin nata zai mata wajan tarwatsa rayuwar mahaukacin nan, da kuma tonawa Alhaji KD asiri shida yaronsa bahago dukda batasan wanene shiba, amma zata jagoranci hukuma wajan nuna musu saƙonda ya turawa Dadynta dan alƙawarin zuciyarta ne bazata bari a hukunta mahaifinta shi kaɗai ba, dolene a haɗa da sauran.
Tabbas Dadyn ta ya aikata abinda bata taɓa zato daga garesa ba amma hakan bazaisa ta juya masa baya na matsayin uba gareta ba, wadda takeda tabbacin dan su itada Mummy take fafutukar nema da sauran jama'anda ke ƙarƙashin sa.
Sanda Mummy ta faɗawa Barrister abinda yake faruwa, ba ƙaramin mamaki da firgici lamarin ya saka shiba, dan yasan wane Dady, bai taɓa zaton zai iya haɗa tsaftatacciyar dukiyarsa da wata hanya data saɓawa doka ba, shi yasama a karan kansa ya yadda ya zama lauyan Dady bawai dan kuɗinsa ba, sai dan yadda Dady yake tafiyar da lamuransa cikin Gaskiya da mutumci, amma sai gashi wata magana tazo ta daban. Tabbas ya yadda mutum tara yake bai cika goma ba. Da wannan tunanin ya kira Salim a waya kan ya samesa gidan Alhaji Mani Cizo.
Kusan Salim ya riga mahaifin nasa zuwa gidan dan abin nemane ya samu.
A bakin entrance na gidan ya samu Binazir zaune cikin tunani, ta jingina bayanta da jikin balcony.
A nitse yayi mata sallama tareda zama ɗan nesa da ita a wajan.
Jin alamun mutum a kusa da ita ne yasata saurin dawowa tunaninta.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin Salim tareda sakar masa murmushin yaƙe.
Martani ya maidamata tareda yi mata murmushi a tausashe.
"Abi ne yace nazo na samesa a nan, yana kan hanya, ni nayi tsammanin ma ya ƙaraso" ya faɗa sanda ya ankare da irin dubansa da takeyi.
Kai ta girgiza masa alamun a'a sannan ta lumshe idanunta.
Shiru wajan ya ɗauka, ba wanda ya ƙara yiwa wani maganna. Lokaci lokaci yakan saci kallon ta, har zuwa wannan lokacin idanunta a lumshe suke.
Zuwan Barrister wajanne yasa ta buɗe idanunta, gaishesa tayi cikin basa girma sannan suka shiga cikin gidan baki ɗaya.
A main palon suka samu Mummy zaune hannunta riƙe da karbi. Kusa da ita Binazir ta samu waje ta zauna.
Bayan an gama gaisawa ne Mummy ke faɗawa Barrister ƙudurinsu na son ganin Dady dan jin tabakinsa.
Shiru lauyan yayi sannan ya saki ajiyar zuciya da faɗin " shi wannan lamarin ba'a fiye bari ganin mutum sakaka ba, can Headquartern da banbanci da prison, Kuma bazan ɓoye mukuba, ganinku da zaiyi kunje kuma kuna tuhumarsa abin ba ƙaramin taɓa zuciyarsa zaiyi ba. Kawai ku barni dashi zan nuna masa munsan komai duka kawai wasu bayanai zai bamu dazai taimaka wajan sassauta lamarin"
"Sassauci?"
Binazir ta tambaya cikin tantama. wani yawu mai ɗaci ta haɗiya da faɗin " ba wani abu da zaisa ayiwa Dady sassauci kan case innan, saboda ya aikata kuma sunyi spying nasane dukkan wani motsinsa akan idanunsu yayi, kuma sun tattara dukkan bayanai nasani, maybe sunason jin Shi dawa suke harƙallan shiyasa suke sassauta masa amma sunsan komai kan Dadyyyy" ta faɗa cikin ɗaci tareda furzar da wani numfashi
"Ni yanzu burina na gaba shine mutuwar kasko, da kaina zan basu information kan wani abokin kasuwancin sa, dolene ta shafi uban kowa" ta faɗa cikin ƙunar zuciya.
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda riƙo hannunta cikin nata tana matsa mata a hankali.
Barrister kam shiru yayi yana mamakin tsautin yarinyar da maganganun ta haɗe da jinjina sadaukarwar ta ga mahaifinta.
Salim kam balance yayi a cushion Yana ƙare mata kallo, confidence inta ba ƙaramin motsa tsokar zuciyarsa tayi ba. Ajiyar zuciya ya sake sanda ta gama maganganu ta.
Barrister ne yayi wani ƙayataccen murmushi da faɗin "Naso ace Alhaji Mani yana ganin wannan tattaunawar tamu dan koda yaushe cemin yake ina tausayin Binazir yarinya ce, batada wayau batasan komaiba, kar a cucemin ita mutum baida tabbas. Allah sarki! duk zantukansa akan ya rayuwar ki zata kasance gaba!" Ya faɗa cikin tausayi.
Ƙasa tayi da kanta tareda fakar idanunsu ta share wata guntuwar ƙwalla data taru a gefen idonta.
"Salim" Barrister ya kirashi sanda yake miƙewa tsaye.
Ɗago kansa yayi yana kallon mahaifin nasa.
"We have to leave right now, muna buƙatar zuwa wajan Alhaji Cizo"
"Yes Dad" Salim ya faɗa tareda miƙewa suka fara tafiya, har yazo bakin fita ya dakata tareda waigowa ya kalli ɓarin da Binazir take, sannan ya fice daga palon.
HEADQUARTER
Sanda suka samu ganin Dady suka kuma shaida masa abinda ke tafe dasu, ba ƙaramin tashi hankalin Dady yayi ba.
"Yanzu Binazir da Mariya sunsan zancennan?" ya tambayi Barrister cikin raunananniyar murya.
Kai Barrister ya ɗaga masa da faɗin "just your support".
Numfashi Dady ya sauke da faɗin "tunda iyalina sunsan komai banda wani sauran buri kawai zan miƙa kaina, Ni Ni kaɗai aka kama da shaida mai ƙarfi kuma ni kaɗai za'a hukunta no need of involving someone else".
Yana gama faɗa ya miƙe yabar wajan.
Da ido Barrister yake binsa harya ƙurema ganinsa. Ajiyar zuciya ya saki tareda miƙewa tsaye, kallon Salim da fuskarsa ke cikin tafin hannunsa yayi.
"Mu tafi" Dady ya faɗa tareda ficewa. Miƙewa yayi ya fara tafiya daidai ƙofar fita cikin compound yaci karo da SAMIR.
Tokare ƙofan yayi yana kallon Samir head to toe. Tattare naman goshinsa Samir yayi yana kallon ikon Allah dan shi bai san saba kuma bai gane ma'anar tare masa hanya da yayi ba "excuse me" ya faɗa tareda nuna ƙofar shiga.
"Shameless Mad" Salim ya faɗa sanda yake barin bakin ƙofan.
Ƙara tattare naman goshinsa yayi haɗe da ƙanƙance idanunsa. Numfashi yaja ya sauke ta bakinsa a záfafe. tareda shafa sumar kansa sannan ya shige ciki.
Binazir ce a ɗakin Mummy zaune kan sofa, hannunta riƙe da biro da takarda ga wayar Dady a gefe. Numban Alhaji KD da text inda ya turowa Dady ta kwafa akan takaddan sosai takeson tayi bincike ta gano wanene shi tukun kafin ta aiwatar da shirinta na gaba, ranta duk a jagule yake gashi tayi ƙoƙarin shiga Gmail in Dady amma ta kasa.
Shiru tayi tana tunanin abinyi.
Mummy dake zaune bakin gado tana lura da duk wani motsinta ta girgiza kai tareda sakin numfashi yarinyar sosai take bata tausayi, dukta fita hayyacinta FANSA kawai takeson ɗauka. Baki ta buɗe daniyar yi mata magana, Asabe ta shigo ɗakin a firgice ko sallama babu. Binazir ce take kallonta a ƙufule dan ba ƙaramin katse mata tunani tayiba.
"Hajiya ga jami'ai nan sun shigo zasu haura saman Alhajj....." ai tun kafin ta ƙarasa Binazir ta miƙe a zafafe ta nufi hanyar fita.
" Ji mana Mahaukac!"
ta faɗa a kausashe dai-dai sanda ta iso farkon step na bawan saman Dady.
Ba tareda ya juyo ba ya dakata da tafiyar da yarage musu taku biyu su buɗe ƙofan palon Dady. Dolene sauran jami'ai suma suka tsaya tareda juyowa ganin shugaban tafiyar nasu ya tsaya.
Cikin izza take taku harta iso gabansa. Jinta a gabansa, yasa ya lumshe idanunsa.
Kallonsa take a zafafe daga sama har ƙasa. Wani huci ta furzar sannan ta fara magana
"Meyasa kunya bata isheka bane? bayan abinda kayi yanzu har Kanada ƙwarin gwiwar ƙara shigo mana cikin gida? ko kayi ajiya ne bamuda masaniya? To bari kaji, ba ruwana da kai kowane, tazarar shekarun da ke tsakanin mu, ko matsayinka, muddin ka sake ƙafarka ta taka cikin turakar mahaifina, to ka sani saina yaga maka rigar mutumcin da tunda kake a duniya babu wanda ya taɓa taɓata" ta faɗa tana huci.
Baki buɗe sauran jami'an suke kallonta da mamaki ganin yadda yarinya ke tsaye gaban team leadern su, tana faɗa mishi magana son ranta.
Mummy ma dake tsaye tsakiyan palon kasa ƙarasawa tayi ga 'yar tata, ido kawai ta zuba mata kamar yadda sauran ma'aikatan gidan da jami'an sukayi, haka kawai Mummy taji tana shakkar yimata magana. Shikam
Runtse idanunsa da suke lumshe yayi zuciyarsa sai wani irin tafasa takeyi, ajiyar zuciya ya sauke tareda buɗe idanun da suka sauya kala akanta.
Itama shi take kalla dan haka suka fara yiwa juna kallon ido cikin ido. Ajiyar zuciya ya sauke tareda zaro wata takadda a aljihunsa ya wareta daidai saitin fuskarta.
"Da amincewar Mahaifinki mukazo gidannan zamu binciki wasu kaya da ya bamu tabbacin suna a ɗakinss......."
"Sai me?" ta katse sa a zafafe "nace saime? Idan ka faɗi hakan a tunanika zuciyata zata buga na mutu ne kamar yadda kake fata? wai dan Allah anya makuwa kai mutum ne?" ta faɗa cikin ɗacin zuciya.
Shidai kallonta kawai yakeyi tareda sauke numfashi a hankali.
"Duba can kaga" ta faɗa tareda nuna ƙasan benen inda su Mummy ke tsaye.
Waigawa yayi ya kalli wajan a hankali sannan ya dawo da dubansa gareta.
Mahaifiya ta ce kuma matar sace, baka tunanin faɗin hakan zai iya tarwatsa zuciyar ahalinsa? To ubangiji ya riga daya tsareni daga sharrinka, Allah da kanshi yasan bakada imani da tausayi, bakada ilimi da tarbiyar faɗawa jama'a magana mai kwantar da hankali, ubangiji yasan irin ɗacin harshenka da bai furta alkairi batareda tunanin halinda mutum zai shigaba, shiyasa ya bayyana mana gaskiya tun kafin kazo ka ƙara tarwatsa mana zuciya a karo na biyu"
ta faɗa a masifafe tareda sauke numfashi tana huci.
Ajiyar zuciya ya sauke still idanunsa a kanta.
"Wallahi na rantse! Ba mai shiga cikin palonnan, ka Kuma gwada ka kani Dan wallhi sai an dau gawa" ta furta cikin jaddadawa tareda wurga Masa kallon tsana, ƙiyayya da ƙyamar.
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*