ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 11
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️11*
Da karsashinsa ya Tura Kofar Dakin Hajiya ya Shiga da sallama. ammh ciki d'akin Shuru sai dai Wani Ni'imantattacen kamshi Turaren Wuta Daya Daki Hancinsa.
Lumshe ido yayi kafin ya Bud'e su Fes yana bin Dakin da kallo har idonshi ya Sauka kan Hajiya Dake kwance kan gado Tana barci.
Cikin Sanyi Jiki ya karisa gabanta yana Kare Mata kallo. gabansa ne ya Fad'i ganin irin Ramar da Hajiya Tayi Duk ta Zabge Ba wannan kibar Nata da Cikar Fuska mai Cike da karamci, Tsaye yayi yana kallonta idanuwansa Sun kala Sun kara ja,yana ji kamar ya Durkushe Bisa kafafunsa ya saka kuka.
Hajiya ko dake barci dayake Duk Nisan barci Hayaniya kad'an ko Mutum ya matso kusa da ita Zataji yanzu Zata Farka.
Ahankali ta Bude idanuwanta Da Suka Shige Saboda Barci, Abunda tagani yasata Saurin Maida idanuwanta ta Rintse kafin Wasu Siraran Hawaye Su Zubomata ta Gefen Fuska,gyara kwanciya tayi Kafin ta Murmusa tana Fadin"Har Sai Yaushe ne Baffa Zaka zo gareni? Akullum bani da wani mafarki sai na ganin ka tsaye agabana.."Take Fad'a idanuwanta na Runtse tana kuma Share Hawayen da Suka zubo ta gefen Kunnenta.
Jin Abunda Hajiya ke Fad'i ne yasa baisan Sadda ya Durkushe gaban Hajiya ba lokaci d'aya yana kamo Hannunta Cikin karaya Da Nadama ya Furta.."Gani Agabanki Hajiyata ki Bud'e idanuwanki Da gaske wannan Karon Baffanki ne agabanki ba Mafarki kike ba."
Jin Muryan Baffa da kuma Hannunta daya Riko yasa Hajiya Bud'e idanuwanta Fes akanshi,Kuramai ido tayi kafin ta wani Zabura Kamar Zata Fadi, sai gata ta Diro kasa da Mugun karfi har kafarta tana Turgud'e Yayi Saurin Rikota yana kallonta.
Kafad'unshi Ta damka tana Girgiza Shi Take Fadin"Da gaske Baffa na ne Agabana..? Abdallah kai ne kuwa Ko dai haryanzu Ban Farka daga mafarkin dana sabayi bane na Kazo gareni.?
Tafad'a Hawaye Suna kwaranyomata Kana Duka hannuwanta Biyu tana Shafa Fuskarshi. Shima kukan yake son Saki ammh kuma Idanuwansa Sun bushe Zuciyarsa ne kad'ai ke iya Fassara Halin Bakin Cikin Dayake Ciki
Ganin haka kawai yasa ya Fada Jikin Hajiya yana Sauke ajiyar Zuciya yana Fadin"Ni ne Hajiyata Abdallah ki ne. Don Allah ki yafemin bansan meya Sameni ba.."
Yafad'a yana Runtse Ido Saboda yarda Kansa yake Saramai, Ai da hanzari Hajiya ta Kamkame Shi tana Dariya Had'e da Kuka tana Fadin"Alhamdulliah Allah Mun gode Maka daka amsa addu'armu ka dawo mana da Abdallah garemu" Take Fad'a tana kamkame Dashi tana Dariya da Kuka lokaci d'aya.
Yau Hajiya Duk ta Cire wannan alkunya ta Dan Fari ta na murna Zuwan Abdallah.
Daidai Lokacin Maman Fati ta Shigo dakin Hankalinta tashe, Asma'u na Biye da ita abayanta,Ganin hajiya Rumgume da Wani Saurayi ta na kuka yasa Suka yi Turus.
Maman Fati bata samu Zarafin mgana ba Hajiya ta ankare Dasu,Da hanzari ta Saki Abdallah tana Riko Hannunshi take Fadin"Maman Fati mu gode ma Allah. yau dai ga Abdallah yazo garemu"
Sai alokacin Maman Fati taga Fuskarshi,Waro ido tayi kafin itama ta karisa tana Damko hannunshi take Fad'in"Hajiya Da gaske Abdallah nake gaani ko kuwa Idona Ke min Gizo.?
Tafad'a kai tsaye tana Shafa Fuskarshi Kai ya girgiza kafin kawai ya Durkushe gabanta yana Rike da Hannunta yace"Maman Fati Ku min aikin gafara ku yafemin Wlh bansan meya Sameni har nayi wannan Tsawon Lokacin banzo gareku ba."Yafad'a yana Sakin Nishi Sama sama.
Kamosa Maman Fati tayi Tana Fadin"Ai mu ba Laifi tsakannmu Baffa. sai godiya Ga Allah daya Sa kadawo kana Cikin Hayyacinka"
Tafad'a Tana Dagosa, Hajiya Dake gefe banda Sharan Kwallah Babu Abunda Takeyi. kallon Maman Fati tayi tana Fadin"Kamar amafarki na ganshi Habiba Waya gaya miki Zuwanshi...?
Maman Fati tace"Asma'u ce tazo Da gudu tana Haki take Cemin ga wani Chan ya Shigo gidan. wai ya Shiga Har Dakin Hajiya,Ganinta atsorace yasa Na boyota nazo na gani"
Tafad'a tana waigawa bayan Inda Asma'u ke Tsaye sai dai Suka ga wayam, Bata adakin ita ko Asma'u Tunda Daga Hajiya Rumgume da Baffa tana Kuka Abun yayi Mata wani iri baya taja kawai Ta Fito daga dakin Tadawo Falo a zuciyarta Tana taya wannan Ahali Murna Dawowar Wanda Suka Dad'e Suna Nema.
Tsakanin Maman Fati da Hajiya Aka rasa wane yafi Rawan jiki. haka Suka Taso Shi Zuwa Falo suka Zaunar dashi kan kujera Suka jeru akasa Suna kallonshi Sun ma kasa gasgata idanuwansu na Yau Baffa ne agabansu.
Hajiya ko da kanta ta daga waya ta kira Mallam Tana Shaidamin ga Baffa yazo gida, Da farko ya zata Wasanta ne ya Tashi Sai da Maman Fati ta karbi wayar ta Rantse mai kana ya yarda,Hamdala yake tayi Acikin Zuciyarsa Tare da yima Allah Kirari Domin Shine Ke amsa Dukkan Rokon bayinsa.
Kafin kace kwabo An bugama su Anty Safina waya an sanar Dasu kowacce ta Cika Da mamaki. Nan da nan Suka ce gasunan Tafe ko yusuf dake Kaduna Sai da Hajiya ta kirashi, bayan Sun gama mgana da Hajiya Saboda ya Tabbatar Sai gashi ya kira Wayar M.A din,Yana dagawa yahau Tambayanshi Da gaske yana Bauchi..? mirmishi kad'ai yayi mai Batare Dayayi mgana ba. Saboda baida Abunda Zaice kalli yadda kowa ke Murna, Yana da Ranshi da Lafiyanshi Cikin kwanciyar Hankali ammh ya bar iyayensa da yan'uwansa Cikin kewarsa da Son ganinshi har na Tsawon Wasu Shekaru?Shiko mai ya Shiga kansa Ne.?
Asma'u na gefe Tana kallon Abun Mamaki. tana jinjina girma da Tasirin da Abdallah keda Shi Wajen iyayensa da yan'uwansa, Bata gama Mamaki ba sai da Mallam ya dawo haka Abdallah ya Fad'a jikinsa Lokaci Daya kuma ya Saki kuka,Kamar wani karamin yaro yana Fadin Su yafemai Shida Hajiya.
Shikanshi Mallam d'in Saida ya Share kwallah saboda Tsausayin Abdallah, sai yanzu ya kara yarda an Shiga Tsakaninsu ko daga yadda Abdallah ke Fadin baisan meya Faru Dashi ba ammh kwata kwata Aka Ciremin Tunanin Bauchi aransa,
dasu gabadaya.
yanzu ma Yana Zaune kawai yaji in bai Taho Bauchi ba kamar Zai Mutu haka ya dinga ji.
Ranar fa Ansha Koke koke,haka Suma da Su Anty Nafi suka zo Fad'awa jikinsa Sukayi Suna kuka, nan fa Rasuwar Farida ta dawo musu Sabuwa,Abun gwanin ban Tsausayi. Shiko Abdallah Bayason kannensa Suga Rauninsa,ammh kam ya Zubda da kwallar Rashin Farida Sosai, Haka su Fati da Suka Dawo Suma Sunyi mamaki ganin Baffa,sai Suka fara Dari Dari dashi sai da ya mika musu hannu yana kiran Sunayensu kana Sukaje gareshi ya Daukesu yana Tambayansu Ajinsu Nawa a mkranta.
Ranar dai Ashashen Hajiya aka Ayada Zango Tsakanin Mallam da Hajiya da Maman Fati da Su Anty Nafi ba'san wa yafi wani Rawan jiki da murna kan Baffa ba.
Asma'u dai Shashen Mamn Fati ta koma ta kwanta Don itama Wani lokacin bata Shiri da Hayaniya,Balle kuma bata Son ganin kukan Babba Sun had'a ido da Abdallah Lokacin dayake ma Mallam kuka yana Rokonshi gafara,yanayin yadda ya kalleta sai Da taji jikinta yayi Sanyi, Shiyasa ta Fito Daga dakin Ta koma Shashen Maman Fati
Sai Zuwa chan ne Hajiya ke Cigiyarta Maman Fati tace tana Shashenta ta kwanta,anan nema take Fad'ama Baffa Asma'u ce yar Wajen Habiba Yarta dake Dutse bai bama mganar Muhimmanci ba, dayake Tun Asali ma Shi bamai Yawaan mgana bane. ko yanzu ma Dayake Zagaye Cikin yan'uwashi kallon Farko zakamai ka fahimci Fuskarsa ta bayyana Farincikin daya ke Ciki, ammh kuma Fuskarsa bata Nunawa yana zaune yana kallonsu,sai sun sakoshi ya d'an Saki Fuska yayi Mirmishi kad'ai.
Ranar Farinciki ga iyalan Proff ba'a mgana. Domin atare da Mallam Sukaci abinci cike da kauna, Kuma tare Sukayi alwala Suka Fita Zuwa masallaci Su uku Shida mahmud,Sai la'asar Asma'u ta Fito,ta koma Shashen Hajiya su ka gaisa Dasu Anty Nafi don Lokacin da Suka zo idonsu ya Rufe da ganin Dan'uwansu.
Rumgumeta Hajiya tayi Cike da Farinciki tana Fadin"Asma'u kinga Baffa na ko..? yau Abdallah ya Dawo garemu."
mirmishi Asma'u ta Saki kafin tace"Nagani Hajiya, sai mu godema Allah don hakika babu Abunda ya gagari Allah.."gyad'a kai Hajiya kafin tace"Gaskiya ne Ma'u. Shiyasa kike burgeni har nakeji araina Dama dama ace Yau nice na Haifeki dana fi kowacce Uwa sa'ar samun y'a ta gari."
Maman Fati ce tace"Ai ko yanzu Hajiya Asma:u ba ya'ta bace Wlh Har Abada tana Mtsayin yarki ce." Jin haka yasa Hajiya tace"Na sani Habiba kuma nagode da wannan kyautar taki."Dariya Su Anty Nafi Suka sakama Hajiya,suna mata Tsiyan Ciwo ya kare Tunda Baffa ya dawo. dakuwa ta aika musu tana Dariya mai Cike da Nishad'i.
Suna sallar La'asar basu Zauna ba Suka Shiga kichen yau Hatta da Maman Fati Cewa Sukayi ta Huta,su zasu Dafa abinci. Da Asma'u da Anty Nafi da Anty Safina,Hajiya ko Da maman Fati Suna tare da Mallam da Baffa Ashashensa.
Mallam na karamai Fad'an ya Dage da addu'a kuma yadaina Sakaci da ibada,ya amsa da Insha Allahu zai kokarta, Yana Falon Mallam din wayarsa keta bugawa tana Neman Dauki,Daya Duba yaga mai kiran sai ya kashe,Sai daga baya ya Turamata Text sai kirata later baya gari ne yana Bauchi.
Polina Taga Sakon Abdallah sai Hankalinta ya kwanta Don ta Zata wannan Shegiyar matar tashi mai kama da Tarwad'a ce ta tsareshi ammh jin yana Bauchi sai hankalinta ya kwanta.
ammh tayi mamaki Duk da Abdallah yataba Fad'amata Shi haifaffan bauchi ne. iyayensa da yan'uwansa na chan,ammh Ita dai Tunda take dashi bata taba ganin yaje ba.
ko kuma Yayi waya da wani Nashi Sai Yusuf Shima ba Sosai ba,Ta taba mai Tambayan meyasa baya Zuwa ganin iyayensa sai yake cemata baisan Dalili ba,ammh koda yana son Zuwa baisan meke hanashi ba.
Jin haka yasa polina ta saka aka Mata Bincike kan Abdallah da Abunda ya Shafeshi, Dayake Duk wani Iskanci sun san shi,wani Boka ne A lagos Arne ma baiga Ruwan musulunci ba.
Shi ya sanar da ita kaf Sirrin Wasila game da Abdallah, Abun yabata mamaki taji Takaichin Wasila da Tsanarta Sun kamata,Kuma ta tabbata ba Son gaskiya takema Abdallah ba, Tunda Zata iya Cutar dashi Ta rabashi da iyayensa.
A nan ne ma Bokan ke Fad'amata akwai wata yarinya zata Shigo Rayuwar Abdallah, Itace Zata Ceceshi daga hannun Wasila ammh kuma akwai Duhu sosai acikin al'amari daga Dukkan Alamu Zata Sha Wahala.
Jin haka yasa Polina ta kudiri Niyyar Ita kuma Zata bada dukkan gudummuwarta Wajen Kwato Abdallah daga Hannun Wasila, bata kuma Taba Nuna ma Abdallah tasan komai ba.
Don Wasila ta Riga ta zama wata masifa gareta don ko laifinta baya kaunar yaji, Tayi murna Sosai da Zuwanshi Bauchi tasan ko ba komai Aikin Wasila ya Fara lalacewa.
*****
Wasila ko Tun wajen 6pm ta iso gida Dayake Samuel yayi Gudu Sosai,tana Shigowa Su Jamila basu gida Sun Tafi yawon iskancinsu.
ta koma Shiga bedroom dinsu Ta iske Abdallah baya gida,kuma Tun tana Hanya take Kiransa bai Daga ba, Hankalinta duk ya tashi koda Suka kariso gida bata Cikin Natsuwarta.
Ranta ya baci Wayarta ta Daga ta kira su Hafsat ce ta Daga kiran Fad'a ta hau yi musu Tana Tambayan Suna ina..? Jamila ce ta amshi wayar tana Fadin"Suna Club ammh yanzu zasu dawo .
Bata damu ba balle Tayi musu Fad'an Zuwa Club dinsu da sukayi.
Tambayansu Ta Shiga yi Ina Dee?
Jamila tace Su koda Suka tashi Da Safe ya Fice Daga gidan
Ammh kuma kafin Su Fito Sunga Emeka ya Dawo da Mota Shi kad'ai,jin haka yasa hanjin Cikin Wasila ya Kad'a, Katse wayar Tayi tana Zufa haraban gidan Ta Fita da gudu kamar Zata kife,tana karema Pradon motar Abdallah kallo, Ashe Tun lokacin da Suka Shigo motar na wajen Rud'ewar datayi ne yasa bata Lura ba.
Cak ta tsaya tana karema Motar kalllo kafin ta Shiga kwalama Emeka kira, Yana dakinsu yaji kiran Madam da Gudu ya Fito,Tunda nesa ta Fara jehomai Tambayan ina Oganshi?
Durkushewa yayi gabanta Don baka isa kama Wasila Mgana Atsaye ba sai ta Mareka bayan taci Ubanka. Kuma daga Ranar kabar aikin agidan,kuma ta Zauna don Wasila ce Mijin Abdallah Kuma matar.
sai Abunda takeso akeyi kuma sai Wanda Tagama Damar aiki dashi Zatayi Shi Abdallah Dan bi ne kawai kamar Rakumi da akala.
Lokacin da Emeka ke Sanar da Wasila yakai Yallabai Airport ya Shiga jirgi Zuwa Bauchi.
Hannu ta Dafe akirji kamar Zata kifa Saboda Tashin Hankali Cikin gidan ta Rumtuma har tana Turgud'ewa Saboda Tashin Hankali Emeka da Samuel har Suna kunshe Dariya, saboda Ganin yadda take Tafiya,Tana Komawa cikin bedroom dinsu ta Dauko wayarta Hannunta Bisa kai ta Shiga laluban Momcy,
Momcy naganin kiran Wasila gabanta ya Fadi,tana dagawa Sai taji ta Fashe mata da kuka tana Sanar da ita"Shikenan Momcy Sun Cika burinsu, koda na Dawo Abdallah yatafi Bauchi Yau Momcy ya zanyi,Wlh Zuciyata tana Zafi da Zarar na Tuna yana wajen makiran Tsofafun iyayen nan nashi wanda basu kaunata da Abdallah."Shuru Momcy tayi Takaichin Wasila na Cikata Ganin tana Neman lalata musu aiki ammh sai Ta Danne.
Lallashinta ta shigayi Tare da Kara Tunatar da Ita Mganar Boka da Abunda yace tare da Tabbarmata da Cewa kada ta damu da Zarar ya dawo tunda ba achan zai Dauwama ba. Zata koma wajem Boka asake Sabon Zubi wannan karon zasu Sha mamaki, Da wad'anan maganganun Ta kwantarma Wasila hankali Suka Rabu Zuciyoyi ba Dadi.
Bata hakura ba Cigaba da kiran Abdallah tayi bai Daga ba,sai ga Wasila kamar zata Zauce, daga Falo Zuwa upstair Tayi safa da marwa kamar Sau Ashirin Saboda Bacin Rai.
Ta kasa Zaune ta kasa tsaye, sai Chan Taga Text dinshi na ban Hakuri Cewa zai kirata da Safe,sai lokacin Taji Sanyi, Su hafsat da Suka Dawo akansu Ta Wuce Takaichi da Masifa ta hau yi musu wai meyasa basu Hana Abdallah Tafiya ba ,Su Abun ma dariya ya basu Suka fara Tunanin Kila Anty Wasila ta Fara Tabuwa Saboda Soyayyar Abdallah ne.
*****
Iyalan gidan kaf yau ashashen Mallam Sukayi Dinner Dare.
Don Daga Anty Nafi har Anty Safina kowacce Sai da Ta tambayi kwana aka Barta kana Tazo, Asma'u Duk ta Takura Saboda Data d'ago ido sai Sun Had'a ido da Abdallah Ita gani take kamar Hararanta yake.
Shikuma Tun ganin Farko dayayi mata Dazu Zuciyarsa ke Bugawa, Yarasa dalili Kuma Duk Sanda ya kalleta sai yaji Faduwar gaba, Ido kawai yake sakamata ammh Duk sai taji ta tsargu.
Haka dazu lokacin Suna jera abinci a babban Dardumar da aka Shimfid'a atsakar Falon Mallam ita da Anty Nafi da Anty Safina,sun Sun Fita ita kuma ta kawo Jug din Zobo sai gashi ya Shigo Sun Dawo masallaci da Mallam, Da ta ganshi sai da ta Rude a daburce ta Gaisheshi Sai da ya wani kalleta akaikace Kana ya amsa da Lafiya,daganan ya Zauna bisa kujera yana Latsa wayarsa Da Sauri ta ijiye Abunda ke Hannunta ta Fice Zuciyarta na Gudu Aranta tana Fadin"Wannan ya cika mugun Hali goben nan Zan tafi.."
Babu Wanda ya Fahimci Halin data ke ciki, tana dai Zaune tana Tsakuran abinci kanta na kasa tana jin Su Anty Safina suna ta waya da Anty Zainab da Yusuf Nan taji Suna Fadin Suma gobe suna hanya. Ta kosa tatashi Don Gabanta Fad'i yake, Kuma suna Saitin Juna ita dashi data dago zasu Hada ido, kuma ita Fuskarshi Tsoro yake bata Baya Fara'a ko kadan.
Cikin ikon Allah sai wayar Aisha ya Ceceta da hanzari Ta daga kiran tana mai Tashi ta Fice Daga Falon,.
A fakaice ya bita da kallo Cikin Ransa yana yaba Tsarin Halitarta don Tana Da duk Abunda yake so ajikin Mace Shashen Maman Fati ta koma bayan Sungama waya da Aisha Sallar Issha'i tayi Ta koma ta kwanta batasan Sadda Hiran Falon Mallam ya Tashi ba, Barci tasha Sosai sai Around 4 ta Farka,Yau ta makara tatashi Tayi ta Fad'a Tiolet Ta dauro alwala tazo Ta tada Sallah, ita kadai ce Adakin kenan Maman Fati a d'ayan bedroom din ta kwana Don Taji Shigowarta da Asuba tagani ko ta tashi.
Hajiya ko da ya'yanta kunsan kwanan Zaune Sukayi wajen 12 mallam ya cw kowa yaje kwanta ,akabar Abdallah anan Shashen Mallam din ya zai kwana.
dama aleady Tun tuni Dakin kwanansa na Shashen mallam din ne, Shashen Hajiya Suka koma suka dasa hirar, ammh Suma basu barci ba don Sai da dukkansu Suka dauro alwala Sukayi Nafilfilun godiya ga Allah.
harda ita kanta Hajiyar sai bayan sallar Asuba kana kowacce Takoma barci Tana Ramuwar barcin da bata samu jiya ba.
*Janafty*