ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 12
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️12*
Duk da Asma'u ba tayi Wani barcin kirki ba, bai hanata tashi akan Lokaci ba.
Ko data idar da sallar Asuba ma Bayan Tagama Azkar din Safe, Bata koma ba Fita tayi Zuwa babban Falon gidan inda ta tarar Da Maman Fati nata aikin Had'a Abun kari a kichen.
Gaisheta Tayi Cike da kulawa kafin ta tambayeta Dame Zata Taimakamata?
Firan Dankalin Data keyi ta Sakarmata ita kuma Ta koma wajen Dama garin kunun da Zata dama ma Mallam suna cigaba da Hira jefi jefi, Inda take son Mamanta kenan bata da yarda wata yar aiki tayima mijinta abinci ba, Tunda hajiya bata da lafiya ita keyin girki kullum sai dai indan Yalwa tazo ta taimakamata da Wasu ayyukan kamar Su wanke wanke da Gyara gyaren Waje
Tagama Fere Dankalin kenan Ta dora Koskon Suya ta Kalli Maman Fati tana Fadin"Mama yau fa zan koma."
Dakatawa tayi da Zuba Ruwan Zafi acikin Fulas Tana Fad'in"Yau kuma Ma'u nasha sai gobe.?
Girgiza kai Asma'u tayi kafin tace"A'a dama yau Abba ya bani kuma ko ba Haka ba gobe ina da Zuwa asibiti." Shuru Maman Fati tayi kafin tace"Toh Shikenan ki karya sai kiyi Haraman Tafiya kada kiyi Dare, ai mun gode.."Dakai ta amsa mata kafin ta Cigaba da Abunda takeyi Ita kuma Maman Fati Ta dauki Fulas din Ruwan Zafin Ta Fice Daga kichen.
Kafin Wani lokaci Asma'u ta kammallah komai,tana Kokarin gyara kichen din sai ga yalwa tazo ,suka gaisa ita ta karbeta ita kuma ta Koma daki tayi Wanka ta Iske har Maman Fati ta Shirya su Fati Cikin kayan Haddarsu Ita da Mahmud.
Sai Tura baki Suke suna fad'in bazasu ba,Maman Fati tace Dolensu kuwa Dariya Abun yabama Asma'u aranta tana Fadim"Kuruci Dangin Hauka.."
Koda ta Fito wankan Maman Fati bata a shashen ,kayan jikinta Ta maida Tunda Jakar kayanta gabadaya yana Shashen Hajiya.
hijabinta ta Maida kafin Ta Fito daga Shashen Maman Fati Zuwa Shashen Hajiya,Tana Shiga da sallama dashi tafara Had'a ido yana Zaune akasa kusa da kafafun Hajiya,yana sanye da Jallabiya mai Ruwan Toka.
Fuskarsa Fayau ammh kuma ta bayyana Rama Kad'an, gabanta ne ya fad'i Duk sai ta Daburce sanda Hajiya Dasu Anty Safina ke amsan Sallamanta.
Cogewa tayi abakin kofar takasa Shigowa kanta na kasa,hajiya ce tace"A'a Asma'u kariso mana,jiya kuma sai aka min Yaji ko..? Tafada Tana yar Dariya,Jikin Asma'u Asanyaye ta kariso chan nesa da Hajiya ta Durkusa tana gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska tana kara Fadi'n"Haba Ma'u kuma Shikenan jiya sai kika gudu wajen Habiba ko..? Kanta na kasa tace"Ba haka bane Hajiya, barci ne ya kwasheni bansani ba"
Hajiya ta Kad'a kai tace"oho koda Naji. kin tashi lafiya.."?Ta amsa da lafiya lau kafin ta juya barayin Su Anty Nafi ta gaishesu Amal yar wajen Nafi ce ta rarrafo wajenta sai ta yunkura ta dauketa tana Satar kallonshi.
Kanshi na kasa yana Latsa wayarsa dakyar tace"Ina kwana..."Yana jinta ammh ya basar kamar bada Shi take ba, ya Lura yarinyar Tana da jin kanta sai da Hajiya tace Baffa bakaji Ma'u na gaisheka bane,kana ya Dago yana amsawa da lafiya kawai Daga haka ya Maida kanshi ga latsa wayarsa.
Asma'u ko kanta na kasa tana Wasa da Amal ammh duk Sai taji ta takura,gashi tana Son tashi ta Shiga dakin Hajiya ta Dauki kayanta, kuma ta kasa Don sai ta Wuce ta gabanshi.
shiyasa tayi Zamanta Kanta na saka tana wasa da Amal dake hannunta.
Maman Fati ne ta Shigo dakin Dauke da wani babban Farantin kayan karyawansu bayanta yalwa ce itama da Wani Farantin Anty Nafi ce tatashi da Sauri ta karbeta tana gaisheta, amsawa tayi Cikin Fuska kafin su gaisa da Anty Safina ta juya suna gaisawa da Hajiya,Tana jinsa yana gaida Mamanta ta amsa tana mai Tsiyar Wanda ya bar gida Ganin Asma'u Zaune yasa tace"A'a Asma'u baki Shirya ba? Kada fa kiyi Dare Bisa hanya Baida amfani"
Da Mamaki Hajiya ta kalleta tana Fadin"Ta Shirya Zuwa ina...? Maman Fati tace"Dutse Zata koma Hajiya, dazu take Fad'amin Babanta yau yace Ta dawo kuma gobe tana da aiki."
Hajiya tace"Kai da Wuri haka Ma'u?Gaskiya banji Dadi ba, Da kin bari Zuwa gobe"
Kanta na kasa tace"Hajiya Nima na So haka, ammh ina da Aiki ne gobe Da Safe Shiyasa"
Jin haka yasa Hajiya tace"Toh Shikenan Ba komai, mun gode Sosai sai Kuma yaushe kenan in kin Tafi Ma'u..? Dan Mirmishi tayi kafin tace"Insha Allahu zan Dawo Hajiya.."Kad'a kai Hajiya tayi kafin tace"Haka dai kike cewa Ma'u ammh kila ai sai Wata Shekara Biyun.."Dariya Su Anty Nafi suka saka ma Hajiya.
itama Asma'un sai da ta Dara,Dakyar ta mike tana mikama Anty Nafi Amal tana Fadin bari ta Shiga ciki Ta had'a kayanta ta gabanshi ta Wuce Kafarta na Rawa Zuciyarta kamar ta Fito saboda Tsoro.
Kwata kwata mutum baida Rahama afuskarsa wannan Ai matarshi ta Shiga uku ko acikin yan'uwa baida Fara'a.
Anan Dakin Hajiyan ta Sauya kayan Jikinta ta Sanya Wata Atamfarta Riga da Sikat ne,wadanda suka mata Cas ajiki.
Duka kayanta ta Hada waje Daya, Mayafin mahadin kayan ta Dauko ta yafoshi Bisa kanta kafin ta Dauki karamin akwatin babbar Jakar Na hannunta Ta Fito, inda Allah ya Taimaketa wannan karon bashi afalon Maman Fati ta tarar da Hajiya sai Su Anty Nafi Kila ya koma Shashen Mallam.
Ranta yayi sanyi Har Saida ta Sauke ajiyar Zuciya. ganinta da kaya yasa Anty Safina tace"Wai ke Ma'u saurin me kikeyi Haka..? kin ma karya kuwa? girgiza kai tayi kafin ta Zauna akasa tana Fad'in"bani son nayi Dare ne Anty Nafi, Mganar Abun kari kuma ban cika sakama cikina komai in Zanyi Doguwar Tafiya ba"
Hajiya tace"A'a Ma'u Kefa Likita ce ke ke gayamin Illar Rashin Cin abinci don Allah matsa ki Zuba Abunda kikeso kici, Ina Mamman yake in ya dawo daga kai su Fati Daga mkranta yazo ya kai ki har chan Dutsen"
Ba Asma'u kad'ai ba Hatta Maman Fati taji dadi Sosai. Asma'u Tace"Ayi haka Hajiya wahalan Zatayi yawa daya Mikani Tasha na hau ta haya."
Daure Fuska Hajiya kafin tace"Amma yi Ma'u ki karya kawai banison gaddama in kun gama Zaki Wuce ina Shashen Mallam"
Tafad'a tana tashi ta Fice Daga Falon.
Ko karyawan Sama sama ta karya Ruwan Tea kad'ai tasha sai Soyayyen kwai don Mutumin ta ne,Tana gamawa ta koma dakin Hajiya ta wanke bakinta da Hannunta ta Fito, lokacin Maman Fati ta Fita inda tace ta Sameta adakinta,Akwatinta Anty Nafi ta dauka Zuwa Shashen Mallam ita kuma ta Shiga wajen Mamanta.
Cikin bedroom dinta ta Sameta gefen gado, Dukawa tayi gefenta tana Fadin"Gani Mama.."
Wata leda ta Bata da Turaman Zani guda hudu aciki tace "Gashinan ki Tafi dashi, Dikakken naki ne,keda Aisha sai Wanda ba'a Dinka ba d'aya ki ma Ammi d'aya kuma Matar Babanki Halima, Ga wannan,"
Tana Mika mata kudi, Hannu bibbiyu Asma'u tasa hannu ta karba tana godiya idonta Duk ya ciko da hawaye, mikewa Tayi tana Fadin"Ki gaida kowa da kowa. kada ki manta da Addu'a Asma'u Aduk Halin da kika Tsinci kanki Domin Ita addu'a takobin Mumini ne. Allah yayi miki albarka, zaki biya wajen su Kawu ne kiyi musu sallama.."?Kan Asma'u na kasa tana Share kwallar data taho mata tace"Eh zan biya,dama ranar dana zo bamu hadu da kawu ba, Nagode Mama Allah ya saka miki da alheri.."Tafada kwallah na Zubomata.
Tsausayinta ya kama Maman Fati ta Rumgumota tana lallashinta da Hannunta ta sanya ta Share mata hawaye.
A falon Mallam Suka tarar dasu dukkansu,ko Shima Mallam din baiji dadin Tafiyarta ammh kuma babu yarda ya iya,20k ya bata Hajiya ma 10k su Anty Nafi kowacce sai ta bata Turmin Zani.
Anty Safina ta Had'amata da Turaren Jiki wato Humra mai kyau da kamshi Asma'u tarasa kalamar godiya Babu Abunda Zatacema wad'anan mutanen Sai Godiya Abunda yabata mamaki Baffa na wajen Ammh ko Dago kai baiyi ba Daga karshe tashima yayi ya Shige wani Korido inda Zai sadashi da Dakunan barcin Shashen Mallam din Lokaci daya yana Kanga waya a kunnensa.
Da kallo ta Bishi asace Aranta tana Fadin"Kowa na gidan nada Mutumci ammh banda Shi"
Harda Mallam acikin masu mata rakiya Zuwa haraban gidan Inda Mamman Zai kaita. su Anty Nafi su suka sanya mata kaya amota,Da zata Shiga mota sai da kwallah ta Zubomata ta Rumgume hajiya da Su Anty Nafi Maman Fati ko na baya. Taki bari ma Su had'a da Asma'u bata son Kawaichinta ya kare ne, Tashiga gidan gaba kenan Sukaji Hon koda megadi Ya bude get Motar yusuf ta sawo kai Shida Zainab da ya'yansu da Annie.
nan fa waje ya Karad'e da murna Ita dai Asma'u bata Fito daga cikin Motar ba Zainab ta leko Suka gaisa ko Yusuf din Daga Nesa ta Hangeshi.
Har Suka Fice daga haraban gidan Suna d'agama juna Hannu.
*****
BAUCHI
Zuwan su Yusuf yasa kewar Asma'u Bata taba su Hajiya Sosai ba.
Nan aka sake sabon Zaman Hira gida ya Gama Had'uwa, Baffa ko da Yusuf suna gefe suna Hira Jefi Jefi domin Baffa dama ba ma'aboci Mgana bane sai Ta Kama Ranar in kaga Ahalin sai kaji Sun burgeka Ganin yadda kowanne Fuskarsa ya cika da Annuri lalle Baffa Shine jigon Gidan Proff.Abdallah Azare.
Mallam Bai Fita ba Aranar Sai Zuwa da yammaah Suka Fita Shi da Yusuf Wanda Hajiya ce Take da Labrin inda zasu, Ko Baffan Bai sani ba yana dakin Hajiya kwance acikin Bedroom dinta Gajiya yayi da Hayaniyarsu Nafi yashiga ciki ya kwanta.
Chan ma Bai samu Runtsawar ba Saboda Kiran Wasila kamar mayya sai lokacin ya samu Kiranta, Kuka Reras take sakin Mai Tana Fadin yayi Tafiyarsa Bai Sanar Da ita ba,Lallashinta yafarayi Yana Fadamata Tafiyarce Tazo ba Shirin Shiyasa.
Nan Wasila Tace Ko ya gayamata Ranar Da Zai Dawo ko Itama gobe ta Biyoshi Bauchi,Jin Haka yasa hankalinshi yatashi Domin yasan yadda iyayensa da Yan'uwansa Suka Tsani Wasila Zuwanta bazai Hafar da d'a Mai ido ba.
Hakuri yadinga Bata Yana Tabbatarmata cewa da Zuwa jibi Zai Dawo,Duk da Bata yarda ba ammh Taji dadin gane Haryanzu Abdallah Nata ne ita Kad'ai Sun Dade Suna Mgana a waya tana Narkemai kamar Wata yarinya Kafin su Rabu Shima Shigowar Hajiya yaji shiyasa ya Yankee Kiran.
Hajiya Bata Kawo komai Ba don data Shigo Saurin Runtse ido yayi kamar Mai Barci so Bata gane Komai ba,lekasa tayi Kafin ta Dafa kanshi Cike da Tsausayawa kamar Wani karamin Yaro, blanket taja ta Rufemai Kafafu kafin ta Fice tana Rufemai kofar.
Kofar ya Kurama ido Yana Sakin ajiyar Zuciya, Polina ya Lalubo itama din Kukan Shagwaban ta sakamai ammh ita na tayi kewarsa ne,ammh Bata Nuna damuwarta ba kamar yadda Wasila Ta Nuna Na Zuwanshi Bauchi Hirarsu Sukasha Cikin Romantic love kafin Suyi Sallama,Yana nan kwance Yana Tunanin Yadda abubuwa Suka Faru Dashi kamar amafarki Barci Mai Nauyi ya kwashe,dama Kuma ga Hayaniya tasa kanshi yayi Nauyi.
Suko Mallam da Yusuf wajen Wani abokin Mallam sukaje Wato Mallam D'abarani Wanda ya kasance Malami ne na Boko Dana Addini ya Shahara Kuma yayi suna Wajen Bada mgungunar Musulunci Kama daga kowani Cuta har Zuwa na Sammu.
To abokin Mallam d'in ne Sunyi karatun Addini tare Wajen Wani malaminsu Dake Azare, akwai kyawawan alaqa Sosai atsakaninsu ko lamarin Abadallah ma Yana Fad'amai Yana sakasu Cikin addu,'a toh adaren Jiya Sunyi Mgana da Mallam yamai bayanin Zuwan Abdallah da wasu Karin bayanai Shine yace gobe da Yammaah yazo ya Sameshi agidanshi Su kara Tattaunawa,shine ya nemi Rakiyar Yusuf Suka Tafi Tare.
A D'anjuma goje Mallam D'abarani ke Zaune da iyalansa Nan Su Mallam sukaje dayake yasan da Zuwansu aka saukesu Cikin Babban Falon da yakan Sauke bakinsa masu Muhimmanci.
Bayan ya Fito sun gaisa sai Kuma bayanai Suka biyo baya Sai da Mallam Da'barani yagama jin Komai kafin yayi gyara Murya yace"Masha Allah Naji Duka bayananka Mamuda mganar gaskiya ayadda Duka abubuwa Suka Faru yaron naka Sihiri ke Dawainiya Dashi..."
Gyada Kai Mallam yayi Yana Kallon Yusuf Wanda Shima ya Natsu Yana Sauraran Jawabin Mallam Da'baranin , Ganin sun yi Shuru ne yasa Mallam din ya Cigaba da Fadin"Kuma kowa yasan Cewa Sihiri gaskiya ne Don ma Anuna mana gasgastan Hakan Sai da ya Kama Shugabanmu Annabi Muhammed (SAW)..."Suka Cike Salatin gabadayansu kafin ya Dora da Cewa"Toh mganar gaskiya itace mu bamu Isa mu yi abunda Allah bai Tsara ba Sai dai zamu Mika Al'muranmu ga Allah, akwai addu'o'in karya Sihiri Wanda Za'a Tofasu Aruwa, nasha ne Dana Wanka sai Kuma Garin magarya da Zan Had'amai da Wasu Karin magunguna da Zai Dinga Sha Yana Wanka Dashi da izinin Allah Duk Sihirin Dake jikinsa Zai Warware da yardan Allah.."
Gabadaya daga Mallam Har Yusuf suka had'a Baki Wajen Fadin"Allah Shi yarda..."Daganan Mallam D'abarani ya kalli Proff.yana Fadi'n"Karka damu Komai Zai Daidaita sai dai Kuma Adage da addu,'a domin Ita Addu'a makamin Mumuni ne,Wannan ne yaron wajen Naka..? Yafad'a Yana Kallon Yusuf.
Mallam yace"Bashi bane Akaramakallahu. Shima wannan din Duka na wajena ne,Abokin Abdallah ne Kuma Yana Aure da Yata,kaga ko Duk anzama Daya"
Mirmishi Mallam D'abarani yayi kafin yace"Hakane Masha Allah, toh Abunda za'ayi Yanzu ku bani nan da Zuwa gobe da Yammaah Zan kira ka sai ka Turo a karb'i Magungunan da Ruwan Addu'an tare Da bayannin Yadda Za'ayi Amfani Dashi. da yardan Allah indai yayi Amfani Dashi yadda yadda ya Dace Komai zai Daidaita da yardan Mai duka.."
Mallam yaji Dadi nan yayi ta ma Mallam D'abarani Godiya da Zasu Tafi ya Bashi 30k ammh yaki Karb'a 5k Kadai ya Cira Suma yace Kudin Siyan mganine ammh ko Sisinshi bazai Karba ba, don Abdallah Shima D'a yake gareshi,Haka suka Rabu Cike da Mutumta juna.
har bakin Mota ya rakosu suna Kara Sallama da Mallam kafin ya Shiga Mota Yusuf yaja su bar anguwa Zukatansu Cike da Faricikin Nasara.
Koda suka Koma Suka labartama Hajiya Da Maman Fati yadda Sukayi da Mallam D,'abarani hakika Sunji Dadi sosai,har suka kasa boye Murnansu, Baffa dai baisan wainar Da'ake Toyawa ba,don Dakin Hajiya ya Wuni kwance.
Sai Bayan la'asar ya tashi Bayan yaji kansa ya lafa,shashen Mallam ya Koma yayi Wanka, Yusuf ya matsa mishi Suka Fita Zaga gari amotarshi, Duk da Rabin Surutun na Yusuf ne ammh Bai damu ba,domin Yafi kowa sanin Baffa ba ma'aboci Mgana bane.
Ammh duk da haka yaji Dad'in Fitansu don Yana Tunamai da lokacin Kuruciyarsu Shida Yusuf,sunyi yawo Sosai sai After Issh'i suka Dawo Gida.
Washegari Yusuf yaje ya karb'o Sakon Wajen Mallam D'abarani, Bayan ya Kira Mallam awaya yace azo a Karb'a, bayanin Komai na Cikin Wata Farar Takarda Jakarne Guda na Ruwan Addu'an sai Wata jakar Kuma Cike da Haden Haden Magunguna.
sai wasu Rubuttatun Addu"o'i na Tsari Wanda Annabin Tsira ya Koyar damu,bKoda Yusuf ya Kawo Sakon Mallam ya Karba Da kanshi ya Kira Baffa har Shashensa Da daddare ya Damkamai Magunguna Bayan yamai Nasiha Mai Shiga jiki, Baffa bai da ta Cewa illah saka Hannu ya Karb'a Hannu bibbiyu domin bayason ya Nuna gardama balle Shima Yana bukatar Wani abun da Zai Tallafeshi don Wani lokacin in yayi Wani Abu sai yafara Tunanin kamar Bashi ba.
Hajiya ko Dataji lbrin An Damkama Baffa magungunar Da kanta ta karbi Jarkunan Magungunar,ta Kai Dakinta ta Kuma Umarcesa Shashenta Zai Dinga Zuwa Yanasha in Lokacin yayi Bai yi gardama ba ya amsa Mata da Toh,kowa yaji Dadin Haka Saboda A kula Da Shansa Ko zasu Samu Waraka kan Abunda ke Damunsu Shekara da Shekaru.
Kwana uku Su yusuf Sukayi Suka Koma Saboda Wajen Aikinsa Suma Su Anty Nafi Bayan Tafiyarsu Yusuf Mallam ya Tarkatasu kowacce ta Hada kayanta ta Koma Gidan Mijinta Cike Da kewar gida, aka bar Baffa da iyayenshi Wadanda keji kamar su lasheshi, Hajiya da Maman Fati Harda Mallam ba'asan Wanda Yafi wani Kula da Shan mganin Baffa ba,Hajiya da kanta take Zubamai Wanda Zaiyi Wanka Dashi Bayan ya Fito Kuma ta ta sashi Har sai yasha nasha.
Addu'o'in kuwa Yana Kokarin Karantawa Duk da Yana Da Rauni wajen Addu'a ammh wannan karon ya Dage Saboda idon iyayensa Dake kansa.
Wajen Sati Daya Baffa ya kwashe agida Yana Amfani da mgungunarshi Kuma Alhamdulillah Sun ga Chanji Shi kanshi yanajin Chanje chanje ajikinsa, Lokacin dayayi Sati yaso komawa Porthercourt ammh Mallam yahana yace yabari yagama shanye mganinsa,Allah barshi in Zai Koma sai yatafi da Wani Tunda dama na Sati Dayane Duka Magungunar.
Hakanan ya Hakura ya Zauna Bayan ya Kira Office dinsu yadauki Excuse.
Wasila Ko takusa Haukacewa Da Rashin Abdallah,Bata Wanka balle Kwalliya Koda yaushe Cikin Kuka take da Rantsen Rantsen Cewa Sai Su Hajiya da Mallam Sun gane Kuransu.
Saboda Tsabar Firgicin Da Wasila ke ciki ko Su Jamila Basu sha ba ,Abu kad'an sai Tahau Zaginsu da Masifa,Ga dai Dukiya Abdallah ya barmata Don Duka ATM's dinsa suna Hannunta Bayan uban Kudin dayake ijiyewa agida, ammh Duk Basu da Wani Amfani awajenta,Abdallah shine Cikon Rayuwarta Tanajin Rayuwarta Zata Raunana matukar Babu Abdallah Shiyasa lokaci kad'an Duk ta Fita Kamaninta kallo Daya Zakamata Ka Gane Bata Cikin Hayyacinta.
Koda yaushe Cikin Kiran Momcy take tana Mata Kuka, Tun tana Bata Baki Har Ta daina Daga Kiranta Domin Bata Son Shigen Kulafuncin Wasila da Wutar Cikinta yasa ta lalata musu aiki ya Dawo Dasu baya.
Hajiya Kudirat Ganin Abun na Wasila Yana gabane ba baya ba,yasa ya Ta Shirya tazo har Porthercourt ,ta kwana Biyu Tana Kara Lallashin Wasila tana Kara Jadaddamata Duk Tsiyan Iyayen Abdallah Dole Su barshi ya Dawo Tunda aikinshi Yana Nan.
Ta kyaleshi Zai Dawo ya Sameta ita Kuma bazatayi Jinkirin Zuwa wajen Boka ba Da Zarar ta Samu lbrin Dawowar Abdallah, da Haka ta Kashe bakin Wasila ta Daina Shigen Haukan Datakeyi ammh fa Bata Daina Nuna damuwarta ba Don Har Rama tayi Tsabar Ta sama kanta Bala'i
****
DUTSE
Asma'u Bata Kai ma Aisha Sakonta ba Sai a Karshen Sati Ranar Lahadi Bata da Zuwa asibiti ta Shirya tun Safe ta tafi Gidan Aisha ta Wuni Suna ta Hira Bayan ta Bata Sakon Maman Fati.
tsalle Aisha ta daka tana Murna Haka da Fahad ya Dawo Ta dauko tana Nunamai Tana Murna,shima Yana Nuna murnanshi Sosai Nan ta Wuni sai yammaah Fahad din da Aisha da Amir suka kawota gida kamar suce ta Zauna agidansu Saboda yadda Suke Sonta da Kuma Mutumtata Koda suka Kawota sun Dade Wajen Ammi kafin Su Tafi ita Kuma Asma"u Ta Koma gida.
Tunda Asma'u tadawo Gida Kullum da Safe Sai ta Kira Hajiya Sun gaisa sai Taji ya Jikinta? Nan Zasu Sha Hirarsu da Hajiya Abun na Mata Dadi Jin Hajiya jiki yayi Sauki Sosai Koda Maman Fati Suna Mgana kowani Lokaci Kuma Itama ta Tabbatarmata da Cewa Hajiya jiiki yayi Kyau Sosai,Wato Asma'u ta Lura Duka Farincikin Hajiya na wajen Baffa ne,Ji daga Zuwanshi Hajiya ta Samu Sauki,lalle Uwa uwace ammh ba Domin Haka ba Miye Abun kwallafara rai akan Wannan gayen Dan Wulakanci?
Domin Tuni ita ta Sakashi Acikin Jerin Sahun Marasa kirkin Gidan Proff.
Awannan Satin Haihuwar Rabi'a ce ke Dawainiya da Umma Don ta Haihu ta Haifi yan biyu Duka Maza.
Wanda Yasa Umma ke Kara bude Hanci ita adole ya'yanta sunyi Aure Kuma Suna hayayyafa har Wani Taku Zaka ga tanayi, wannan Haihuwar Tasha bambam Duk da Hauhuwarta na biyu kenan Dayake Mijinta Dan Boko ne Tsarin Iyali Sukeyi,Umma ta Saki bakin Jaka tayi Hidima Sosai Kuma ta Saka Hajiya ta matsama Abba Shima ya Bata kudad'e ,na Hidimar Suna Domin Shagali na musamman Ta Shirya nata a gida ,Bayan Wanda Za'a gudanar agidan ,Bayan Kuma Wanda Za'a gudanar A Jigawa Gidan maijego.
Asma'u batayi Gigin Cewa zata bi Su Anty Bilki Jigawa ba Wanda Suka tafi Tun ana jibi Suna Ita Dasu Anty Rukayyah da Fa'iza sai Maryam da kursum Sai Anty Amarya da Mama Gidan dai gabadaya Suka dad'e, itama harda ita Abba yace Atafiyar ammh sai ta Zame da Cewa Ranar Tana da Zuwa Asibiti Duk da Ranar Bata Dashi ammh tasan In ta Sake taje toh karshenta Ta Dawo DUTSE Tana Kukan Bakinciki Domin Banda Fa'iza da Anty Amarya ba Wanda Zai Mata Kallon Sani balle Hartaji Dadin Zuwanta Sunan.
Ashe Bata Tsira ba, Don Ranar Sunan da Ummah Tayi Nata taron agidan Ita da kawayenta da Yan'uwanta Sai da Asma'u ta Zubar da Hawaye, Ranar a Asibiti ta kwana wajen 8 na safe ta Shigo Gidan,Tana Rangaji kanta ke Saramata Sakamakon Jiya Bata Wani Samu Barci ba aiki yayi Musu yawa.
Tunda ta Dawo Taga Gidan Cike Ta Shigo Dakinta ta Sakayo Ta kwanta,Sai Bayan Azahar ta leko Nan ta Iske Ana Hadar Hadar Arziki Baba lami ce ma ta Tuna da'ita ta Kawo Mata abinci Duk da baza Taci ba ta Karba karta gwale Baba lami din.
Fitowarta yasa wasu Daga Cikin Dangin Umma Suka Fara yada Mata Habaici Suna Zaginta da Kuma Gulmar wai taki Aure tana Zaune agida tana yawon Iskanci Tanajin wata Na Fadi'n Aiko Taji Haushi gata ga Zaman Gidan Tunda Shi ta Zaba,wata Kuma Cewa tayi Bamai Aurenta ta Tsufa agida don Ance ta kusa Arba'in Domin ta girmi kowa agidan
Bata Gama jinsu ba ta Koma Daki tana Danne Kukanta kan Katifarta ta Fad'a tana Sakin Kukanta Lokaci d'aya kamar Wata karamar yarinyar, Aranta tana Jin kodai Tama Allah Wani Laifi ne dayake Horata ta wannan Hanyar?
ammh Ba irin Kalan Addun'an da batayi ba akan Allah ya bata Miji na gari Wanda Zai Dauketa Daga wannan Zaman kunci Daya Fara isarta.
Har suka Gama Shagalinsu suka Watse Bata Kara Gigin Fitowa ba,
Da daddare Kuma Hajiya iya ta Shigo har Dakinta ta Dasa nata Wai Bakinciki da Mugun Hali ya Hanata Bin Yan'uwanta Zuwa Jigawa Suna.
hartana ce mata wai Sai dai ta Mutu ammh Haihuwa Yanzu ya'yan Umma Suka Fara. Saboda Bakinciki ko Kulata Batayi ba, Illah Maida kanta Datayi kan Littafin Azkar din Dake Hannunta Gefe Daya tana Dauke Guntun Hawayen Daya Zubomata da karamin yatsar Hannunta.
*Janafty*