FANSA KO ƘIYAYYA

08

by @109051246447263646587

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*


Free pages


_Page8 _

   Ajiyar zuciya ya sauke tareda ƙoƙarin barin ɗakin 

  "SAMIR" Dady ya kira sunansa a karon farko cikin sanyin murya dakatawa yayi da tafiyar tareda juyowa hannayensa sanye cikin aljihun wandonsa.

 "Bansan mai zance ma ba, ban kuma san mai zan maka na goge tabonda nayi maka kaida ahalinka ba, amma a bisa hakan inaso ka yafemin dukda neman yafiyar batada wata amfani amma tabbas na cutar daku, kuma wallahi ban ƙara aikata irin hakan ba kuma a lokacin ne karona na farko sakamakon hodar dana shaƙa" Dady ya faɗa cikin ɗaci da ƙunar zuciya.

Numfashi Samir ya sauke tareda runtse idanunsa sannan ya buɗesu akan Dady,   "shiyasa muke yaƙi da masu harkar miyagun ƙwayoyi, dan daidai yake da aikata ta'addancin a ƙasa, kai kaji ya akeji mutum fita yake a hayyacinsa ya aikata dukkan wani aikin ta'addanci and you are also involved" ya faɗa tareda sauke numfashi sakamakon wani abu dake dukansa a zuciya.

Dady ne ya sunkuyar da kansa ƙasa dan sosai yakejin Kunyar yaron namijin ƙoƙari yayi tareda ɗago kansa yana kallon wani ɓari daban,

"Kamar yadda ka nema a rubuce Samir, na baka Auren BINAZIR!!"

 "What?" Binazir da shigowarta ita da Salim kenan kalaman Dady suka daki kunnanta.

    Sanda suka shigo suka buƙaci ganin Dady, anan ake shaida mata yana ɗakin bincike shide OS.

Wani mahaukacin ɓacin raine ya danno zuciyarta a lokacin , batasan me wannacan Majnun in yake nufi dahar zai shiga ɗakin bincike shida mahaifinta, kamar Salim yasan mene a ranta ya buƙaci a kaisa ɗakin a matsayinsa na lauyan Dady, ba tareda wani jayayya ba aka kaisu har bakin ƙofan.

A ƙalla sun kusan minti goma a tsaye amma ba wanda ya fito ba kuma ajin abinda ke faruwa a ciki, hakanne yasa ta harzuƙa tareda danna kanta ciki ganin hakan salim ya bita da sauri dan dakatar da ita amma ina ta riga da ta banke ƙofan a dai dai sanda kunnenta ya jiye mata yadda Dady ke jaddada ya bawa babban maƙiyinsu ita a matsayin matar aure.

Ina hakan bazai yiwu ba tasan Dady ba a hayyacinsa yakeba.

Shi kanshi Salim maganar ba ƙaramin dukansa tayi a ƙirji ba, hakanne yasa ya lumshe idanunsa ya jingina da jikin ƙofan tareda ambaton sunan Allah.

A haukace ta nufi wajansa cikin sauri ta cakumo wuyansa da faɗin "mahaukaci me kake nufi dani? Meya haɗa case in Dady dani da zaka buƙaci a baka aurena a rubuce, ko duk cikin salon haukanne?" ta faɗa a masifance.

Wani murmushi yayi mai wuyar fassaruwa tareda janye hannuwanta daga jikinsa.

Hakanda yayi ba ƙaramin baƙanta mata rai yayiba, shiyasa ta saki wani murmushin takaici tareda faɗin 

"Sai Yanzu na gano manufarka butulu, watakam Kanada wata manufa a kaina shiyasa ka biyo ta wannan sigar? to ina mai shaida maka Butulu ka fara ƙirga kwanakin mutuwarka" ta faɗa a haukace tareda buga table in dake wajan.

Salim har wannan lokacin yana jingine jikin ƙofa idanunsa a lumshe, shi kaɗai yasan raɗaɗinda zuciyarsa keyi masa.

Shi kam Dady kansa ya sunkuyar tareda ɗaukar File innan ya rungumesa a ƙirjinsa haɗe da runtse idanunsa.

OS kam kallonta yake sama da ƙasa sannan yaja numfashi da faɗin

"Na gaji dajin kalmar Butulu a wajanki, shin wanne irin butulci ne na taɓa yimiki?" Ya tambayeta tareda ɗaga mata gira..

Kallonsa takeyi a mamakance, 

"Tabbas sai yanzu na tabbatar da wanene kai butulun mahaukaci kawai" ta faɗa cikin ɗaci da tsanarsa sosai a zuciyarta.

Saman kansa ya shafa da faɗin "a iya sanina ban taɓa kai kaina gareki ba, asalima kece kika dinga shishishige min, dan tun farkon haɗuwarmu nayi ƙoƙarin nisanta kaina dake ta hanyar nuna tsorona gareki amma kika ƙi, burinki koda yaushe na saba dake Ni kuma burina a koda yaushe shine na nisanceki". Ya dakata tareda sauke numfashi

" Da ace nazo amai gadi ko driver ko wani abu makamancin haka da saiki kirani da Butulu tunda har cikin gida na shiga, gudun a amince dani na saɓa yasa na zaɓi zama a mai taɓin hankali dan kar kowa ya raɓeni harna gudanar da bincikena, but sai gashi kin liƙemin har naji ya kamata na aureki da ƙarfin ikona babyy!" Ya faɗa cikin kashe mata ido ɗaya

"Allah ya isa " ta faɗa cikin sakin kukan abinda yayi mata tareda nufar Dady

"Kanajin abinda yake cewa Dady? Kallon iskanci fa yayi min? magana fa nakeyi Dady kamin shiruuuuuu!" Taja maganar cikin Muryar kuka tareda durƙushewa a wajan.

Salim dake bakin ƙofa ya kasa jurewa ya tunkareta a zafafe 

 "NEVER" 

Samir ya furta tareda shan gabansa, kai ya girgiza da ƙara faɗin 

" Never try it in your life, nasan kai ba kurma bane, You had abinda mahaifinta ya faɗa so Please stay aside"

Kallon raini Salim yakeyi masa wata dariya ya saki ta rainin wayau da faɗin  "lallai kam I see, wannan shine za a kira mijin aure? Mijinda ya kasa sharewa yarinya hawayenta gaban mahaifinta, ina ga ba idanunsa a wajan?". Salim ya faɗa cikin izgili

  Wani wulaƙantaccen kallo Samir yayi masa tareda ɗauke idanunsa a kansa.

Dady kam har lokacin kansa na a ƙasa , abu biyu ne ke damunsa na farko content in file inda ke hannunsa , na biyu kuma Binazir dake duƙe gabansa tana kukan fitar rai, da yanada yadda zaiyi daya share mata hawaye amma bashida yadda zaiyi, hakanne kaɗai gatan da zai iyayi mata.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kira sunanta a sanyaye bata ɗago kanta ba, ba kuma ta amsa ba amma ta rage sautin kukanta kaɗan. 

 "Inaso muyi magana dake, ki share hawayenki"

Ɗago kanta tayi tana kallon mahaifin nata ido cike da hawaye.

Sauka yayi akan kujerar da yake ya dawo gabanta shima ya durƙusa.

 "Binazir" ya ƙara kiran sunanta tareda goge mata hawayen fuskarta.

Bata iya amsawa ba, amma idanunta na a kansa.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda riƙon hannunta "kin yadda ni mahaifinki ne kuma bazan taɓa cutar dake ba? still idanun ta sa masa ba amsa, wani ɗan guntun murmushi yayi tareda girgiza kansa sannan ya saki numfashi  "Sadaukarwa kawai nake buƙata gareki Binazir, ban taɓa nan taimako a wajanki ba amma a yau gani durƙushe a gabanki ina mai ƙasƙantar da kaina da ki taimakamin ki rufamin asiri kiyimin biyayya, ƙin yimin biyayya daidai yake da tonuwar wani rufaffen babban ta'addancinda na taɓa aikata a watannin da suka shuɗe, idan kin amshi aurannan to ki sani ni kika taimaka kika rufuwa asiri, mahaifinki kika taimaka, dan Allah ki tt..." 

Ƙasa jurewa tayi ta fizge hannunta tareda rufeasa baki tana girgiza kanta.

Wai Dadynta, mahaifin ko me tayi daidai ne, mahaifinda mahaifinda dukkan wani na'urar sa dake buƙatan tsaro to mabuɗin sirrin sunanta ne, mahaifinda Mummy ta bashi shawarar ƙara aure kozai samu ƙaruwar ƙwayayen haihuwa amma sai ya furta  "bazan iya ƙara aurena bawai dan banaso bane a'a sai dan bazan taɓa iya yiwa Binazir kishiya ba nasa ayi mata 'yan uba ba, ko kuma azo a shiga tsakanina da ita ta hanyar asiri da tsubbu". Mai yimata wannan ƙaunar yau shine durƙushe gabanta yana neman ta rufa masa asiri yana shida mata rufuwar asirinsa naga gareta ne, ita wacce iriyar zuciyace da ita idan har bazata taimaki mahaifinta ba? Tabbas dako tayi asara kuma da ita ya kamata a kira da Butulu bawai Majnun ba.

 "Dady" ta kira sunanshi cikin sanyin murya, "idan har amsa aurannan shine rufin asiri da kwanciyar hankalinka, to ina me tabbatar ma na amsa Dady kayi yadda kaga zakayi dani ina kuma roƙon dan Allah idan Kanada wata buƙatar a wajena kayi gaggawar sanarmin zan kasance mai yi maka biyayya Dadyyyy......."

Ta faɗa tareda rushewa da wani sabon kukan tsanar Majnun na ƙara tasirantuwa cikin zuciyarta.

OS ne ya kira azo a maida Dady

Salim ne ya juya cikin ɗacin zuciya

"Salim"

Dady ya Kira sunansa.

Juyowa yayi cikin sanyin jiki da amsawa

"Dan Allah ka cema mahaifinka inason ganinsa gobe yazo shida mai ɗakina"

"Insha Allah" ya faɗa tareda barin ɗakin daidai sanda masu tafiya da dady suka shigo dan tafiya dashi

Wani kukan ta saki sanda aka tasa Dady a gaba daidai da zai fita ya juyo da faɗin "Allah yayi miki albarka, Allah ya farantamiki kamar yadda kikayimin" sannan yasa kai ya fice ya barta da ƙara rushewa da sabon kuka.

Komawa yayi ya zauna saman table ya ɗora ƙafafunsa akan kujera yana kallonta. 

Ajiyar zuciya ya sauke da faɗin "kinafa cikamin kunne da ihu"

Ɗiffff taji kukan nata ya ɗauke tareda ɗago kai tana kallonsa, bayan hannuwanta biyu tasa ta share hawayen ta duka tareda miƙewa tsaye tana masa kallon ido cikin ido

 "Idan har kukan baƙin cikinda nakeyi shine ihu, to kasani nan da lokaci ƙalilan muddin auranmu yayiwu za'aji ihu kala-kala a cikin ahalinka ka rubuta ka ajiye" ta faɗa cikin alwashi tareda hankaɗe kujerar da ya ɗora ƙafafunsa akai da nata ƙafar tabar ɗakin a gadarance.

Saura kaɗan ya yo gaba ya faɗi ƙasa, amma cikin ikon ubangiji hakan bata faruba sai ya dire kan ƙafafunsa.

Da kallo ya bita harta ɓacewa ganinsa sannan ya lumshe idanunsa tareda sakin ajiyar zuciya shima ya fice.

  Kai tsaye wajan motan salim ta nufa ta buɗe ta shiga.

A ciki ta samesa ya haɗa kai da sitiyari. Ajiyar zuciya ta sauke tareda sassauta fuskarta da kuma muryar ta sannan ta kira sunansa

"Salim"

Ɗago kansa yayi ya zuba mata idanuwansa da suka sauya kamanni.

Gabanta ne taji ya buga sakamakon yanayin sa dan tunda take dashi bata taɓa ganinsa a irin hakaba sai yau

"Me ya sameka?" Ta tambayesa cikin kulawa.

Runtse idanunsa yayi sannan ya buɗesu a kanta da faɗin "ba komai" bai ƙara magana ba yaja motar yabar wajan, ji tayi jikinta yayi sanyi sosai da basu saba 'yar haka ba, har sukazo gida bamai wa wani magana. Tana ƙoƙarin fitane ya dakatar da ita tareda kiran sunanta.

Dakatawa tayi da fitan tareda waigowa tana kallonsa.

   "Ayyuka zasuyi min yawa a wannan lokacin maybe har zuwa bikinki bazam ƙara haɗuwa ba, for all that dear, i wishes you all the best" ya faɗa tareda sauke ajiyar zuciya ya jingina kansa jikin kujeran tareda lumshe idanunsa.

Wani irin sanyi taji jikinta yayi, haka kawai taji ƙwalla a cikin idanunta, hannu tasa ta share tareda sakin numfashi

"You are such a good friend Salim, and will never forget your kindness" dakatawa tayi tareda ciro wani diamond ring dake maƙale a thumb in hannunta 

"Salim" ta Kira Sunansa 

Buɗe idanun yayi akanta 

Miƙamsa ring in tayi 

"Please ka karɓa a matsayin kyauta tsakanin nida kai kasa shi a hannunka har zuwa lokacin da zakayi aure ka haiwu ka haifi mace idan ta girma ka bata kace kyautace daga wata aminiyarka mai ƙaunarka mai girmamakaaaa......" kasa ƙara sawa tayi tareda sakin wani kuka mara sauti sannan ta ajiye masa zoben tareda ficewa tabar motan da sauri.

Wani zazzafan numfashi ya fitar yana bin hanyarda ta bi, saida ta ɓacewa ganinsa sannan ya maida idanunsa kan zoben, ɗauka yayi yasa a little finger insa Yana jujjuya hannun, ƙara ɗago kansa yayi ya maida kan hanyar da ta shiga, sannan ya sauke numfashi tareda jan motar a hankali yabar wajan.

 Ɗaki ta wuce tareda sakin wani kuka mai ɗaci. Kukan sabo dan a kalaman Salim ta fahimci bankwana yakeyi mata a fakaice tasan ba wani aiki da zaiyi yana gujewa haɗuwarsu ne kawai, dukda batasan mene SO ba amma ta fahimci irin kulawanda Salim ke bata ba iya matsayin Client ya ɗauketa ba, ya Bata wani matsayi daban a zuciyarsa.

Tabbas ta rasa mai ƙaunarta, dan tun sanda wannan iftila'in ya faru gasu, shine mutun na farko daya jiɓance ta, kafin danginda yanzu cike suke a gidan kamar ana taro.

Wani numfashi ta sauke tareda share hawayenta jin muryar wata ƙanwar Dady na kiran sunanta a bakin ƙofan ɗakin nata.

    HAUSAWA SABON TITI

   " Umma"  Naja dake zaune kan kujeranda ke palon masu ta kira sunanta.

 "Ina jinki" umma ta faɗa a taƙaice tareda cigaba da kwaɗon zogalenda ke gabanta.

  "Ji nayi zancen auran Yaya shiru ba wani motsi"

 "Ban fahimta ba?" Umma ta tambayeta a kaikaice

Murmushi ta saki tareda muskutawa ta gyara zamanta, sannan tace

"Har yau banji yacemin wani abu gameda maganar ba" 

"Sannu Garba" Umma ta jefa mata magana.

Baki ta turo gaba tareda miƙewa 

"Ai nasan zuwa yanzu dai ya dawo daga masallaci, na tambayesa da kaina" ta faɗa tareda nufar ƙofa.

Da kallo Umma ta bita tana girgiza kai "Allah ya shirya" ta faɗa a bayyane tareda maida hankalinta kan abinda takeyi.

Kai tsaye ɗakinsa ta nufa, ta kuma ci sa'a ta sameshi.

Da sallama ta shiga tareda neman waje ta zauna a ƙasa kusa da katifa. 

Yana zaune kan katifan ta shigo ba tareda ya amsa mata ba ya tsareta da ido dan yasan haka kurum bazata shigo ba, wani abun take nema a wajansa.

"Yaya" ta faɗa sanda ta ɗau wani kwalban turare dake kan katifan

Gira ya ɗaga mata.

   "Kaiii Yayaaa!" Ta faɗa a shgwaɓe tareda ɓoye fuskarta tsakanin cinyoyinta.

Murmushi yayi da faɗin 

"Ina jinki to"

"Nace dama naji shiru banji kace Antin tawa na gaidani ba, ko batasan da zamana bane?" Ta tambaya tareda sauya yanayin fuskarta.

Wani ƙayataccen murmushi ya saki tareda miƙewa tsaye

"Ki gyaramin ɗaki zanje wajan umma na dawo yanzu" ya faɗa tareda barin ɗakin.

      Saida ya gama cin kwaɗon zogalenda Umman tayi sannan ya tattara hankalinsa waje guda sannan yace    "Umma an bani auran BINAZIR".






*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*