FANSA KO 茦IYAYYA

11

by @109051246447263646587

*FANSA KO 茦IYAYYA?* 馃挃


*漏锔廇untiMamee*


Free pages


_Page 11_

      CIKIN COURT

  Sanda aka zo case insu Dady dashike case in a hannun jami'ai yake, kuma sun jima a hannun jami'ai ana gudanar da bincike sannan kuma saida suka ha蓷a kowacce iriyar hujja suka gurfanar dasu gaban Shari'a, hakanne yasa ba wani 蓳ata lokaci kotu ta yanke musu hukuncin Life in Prison.

Da fari Kotun shiru tayi tsit bayan yanke hukunci, zuwa wasu sakanni kuma ta蓷au hayaniya, wanda shirun har lokacin da aka fara hayaniya Mummy bata cikin hayyacinta, sakamakon numfashinta daya 蓷auke na wucin gadi, wata relative in Dady dake kusa da itane ta ankare da yanayinta hakan yasata saurin jijjiga ta tareda kiran sunanta da 茩arfi wanda ya jawo hankalin nakusa dasu , da sauri aka kewayeta ana jijjigata, cikin wani wahalallan yanayi ta fusgo numfashi ta saukesa a gajiye, sai kuma ta fara girgiza kanta kamar an kunna famfo ruwan hawaye ya shiga biyowa ta idanunta. Suma sauran da suke dabda sakin kuka na hukuncin 蓷an uwansu amma ganin yanayin Mummy ya dakatar da nasu yanzu kuma ganin tana hawaye duka suka rungume juna tareda sakin kuka maicin zuciya kukan ba茩in ciki da tausayi irin kukanda mutum keyi idan wani iftila'i ya samu 蓷an uwanka.

Duk abinda sukeyi akan idanun Dady dake magana shida Samir da kuma Lauyansa tareda kawunnan Mummy da suka zo yimasa jaje.

Aunty Lubabatu ce tayi 茩arfin halin tsaida nata kukan da fa蓷in "kuyi ha茩uri kuzo muje muyi masa sallama kafin a tafi dasu" ta fa蓷a cikin rauni, hakan yasa sauran share hawayensu tareda cika juna, har zuwa lokacin Mummy Kai kawai take girgizawa idanunta na kwararan hawaye, taimaka mata sukayi ta mi茩a sannan suka nufi wajansu Dady.

Suna zuwa ta fa蓷a jikinsa tareda sakin wani marayan kuka maicin zuciya.

Samir ne ya shafa kansa tareda fara jaa da baya yabar wajan da baya, sanda ya fito harabar kotun idanunsa yakai saitin inda tayi parking motanta, ya 蓷an jima a tsaye yana kallo wajan kana ya furzar da iska ta bakinsa tareda barin wajan.

Duk yadda Dady yaso lallashin Mummy tayi shiru abin ya faskara har akazo tafiya da su Dady, kai kawai ya girgiza tareda kallon Aunty Lubabatu daketa ha蓷iyar zuciya "ki kulamin dasu Lubabatu kicewa daughter ina godiya shine kotazo muyi salllam ko?"

"Ya Allah" Aunty Lubabatu ta fa蓷a da 茩arfi tareda runtse idanunta ta bawa ruwan idanunta damar zubowa.

Murmushi mai cin zuciya Dady ya saki tareda 蓷auke idanunsa daga kansu a haka har aka fice dasu, saida kowa ya fita a kotun sannan su Aunty Lubabatu suka mi茩arda Mummy tareda fitowa daga kotun. Wajan motarta suka nufa da ita suka sata a gidan baya 蓷aya daga relatives na Dady ta shiga driver seat.

Batasan mene actual abinda ke faruwa ba but ta fahimci an gama komai dan tanajin maganganun su Aunty Lubabatu da suke bawa Mummy baki.

   "YA HAYYU YA QAYYUMU BIRAHMATIKA ASTAGIITHU ASLIHLI SHA'ANI KULLAHU WALA TAKILNII ILA NAFSII 茒ARFATA AYNI"

shine abinda taketa nanatawa har lokacin kanta na a du茩e kan sitiyarin a haka Aunty Lubabatu tazo ta sameta ita da Aunty Suwaiba, bu蓷e motan sukayi suka shiga ciki ba tareda kowa yayi magana ba.

Ajiyar zuciya Aunty Lubabatu ta sauke da fa蓷in  "idan bazaki iya driving inba na kar蓳a"

Sai alokacin ta 蓷ago kanta, tareda dakatawa da addu'ar da takeyi. Numfashi ta sauke tareda kunna motan..

Kusan a tare motoci hu蓷un suka iso iso 茩ofar gidan Dady.

Mota ta farko ta Barrister, sai ta Biyu ta iyayen Mummy sai motan Mummy dana Binazir.

  A main palo duka suka zube a 茩asa, mazanne ka蓷ai ke saman kujera. Palon yayi tsit bakajin komai sai sheshshe茩an kuka da 茩arar sakin numfashi da ajiyar zuciya.

茒aya daga cikin kawunnan Mummy ne yayi gyaran murya tareda magana.

 "Dukkan abinda ya faru ya rigada ya faru kuma 茩addara ce da jarabta ta Ubangiji wadda ba wanda yafi 茩arfinta a cikin mu, tsakaninmu da Alhaji saidai muyi masa fatan Allah yasa hukuncin da akai masa ya zama kaffara kuma Allah yasa hakan ya zama izina ga 'yan baya, kuma inaso kusani Bamu rabu da Alhaji ba har yanzu, kusani ba mutuwa yayi ba yana nan da ransa kuma zai cigaba da rayuwarsa kamar kowa kuma cikin 'yanci dan irinsu Alhaji ba'a takura musu a prison dan suna rayuwane kamar a cikin gidajensu, komai nasu dabanne building abincinsu duk da banbanci dana sauran, dan haka muyi ha茩uri mu sakawa zuciyoyinmu dangana muna tare dashi saboda munada ikon ganinsa muyi hira dashi ba mutuwa yayi ba kawai Allah ya hukunta bazanuyi rayuwa kusa dashi bane, kuma 茩in ha茩uri da dangana kaman muna jayayya da Ubangiji ne". ya 茩arasa a hankali sakamakon ta蓳uwa da zuciyarsa tayi na tuna alkairan surikinnasu ga ahalinsu dama wanda ya ji蓳ancesu.

   "Gaskiya kam wannan maganan haka take" Barrister ya 蓷auka.   "Nasan wasu basu Sanni ba anan amma inada ala茩a sosai da Alhaji danni ne lauyansa, kuma nasan abubuwa da dama gameda Alhaji wanda dayawa daga cikinku basu sani ba, Kuma inajin matu茩ar ciwo a zuciyata fiyeda tsammanin ku amma dolene a jure a fuskanci gaskiya, abarwa Ubangiji komai a kuma koma ga Ubangiji Allah yasa mudace" ya fa蓷a tareda share zufar goshinsa da handkachif in hannunsa"

 "Sannan akwai maganar Auren Binazir da shine zancen mahaifinta na 茩arshe daya jaddada mana a kotu" 蓷ayan kawun Mummy ya fa蓷a jiki a sanyaye yana tuna yadda Dady ke shaida musu lalle kar wanda ya kawo masa ziyara ba tareda goron auren Binazir ba, wanda hakan ba 茩aramin ta蓳a musu zuciya yayi ba, har sunajin kamar wasiyya yake basu.

Sai alokacin Binazir dake kwance jikin Mummy ta tashi zaune tana sharar hawayenda ke idanunta.

"Wanne irin hukunci aka yanke masa? ta tambaya murya a raunane.

Ajiyar zuciya Barrister yayi tareda furta "Life in prison" a hankali kamar bayason wani yaji shi. 

"Humm" kawai tace tareda runtse idanunta dan dama tasan hakan ne zai kasance kuma ai dan basu bawa Shari'a wuya bane, dasai an ha蓷a musu da wani hukuncin ko tarar, maida kanta tayi jikin Mummy tareda cigaba da addu'o'in da duk sukazo zuciyarta, idanunta ta lumshe, hakan ya bawa hawayenta damar fitowa.

 Shiru falon yayi, ganin hakan mazan suka mi茩e sukayi sallama da juna tareda fa蓷in sai sun ha蓷u gobe a gidan Barrister.


  Sai yamma ya isa gidan Baba Garba, ai Labari na zuwarwa Bishira zuwan Samir gidansu ka蓷an ne ya rage bata shi蓷eba sanda 茩aninta yake bata labari, tuni ta figi mayafi da jakanta dan yin siyayyan tarbar masoyi.

 A sitting room ya sauka, bayan sun gama gaisawa da Baba Garbanne yake shaida masa yanaso Gobe aje a nema masa aure.

"To to tooo Ai ba komai Allah ya kaimu goben" Baba Garban ya fa蓷a baki washe dan har yanzu yana shakkar yaran shi kansa yasan baiyi musu adalci ba.

Kwatancan gidan Barrister ya bashi, tareda fa蓷in  "sai ka bani account nombanda zan turama ku蓷in zuwa anjima kuma zan ha蓷ane harda sadaki"

  "Ka barshi kawai Samir wannan zanyi matsayin gudummawata" Baba Garban ya fa蓷a idanunsa kan Samir dan ganin yanayinsa, ilai kuwa ha蓷e girar sama da 茩asa yayi tareda kauda kai gefe. 

Shirune ya biyo baya, kowa da abinda yake sa茩awa a zuciyarsa.

   "Tsawon wanne lokaci kake so a saka bikin?" Baba Garba Ya tambaya dan yanke shirun da kuma son sanin yadda abin zai kasance Gobe.

Saida ya 蓷anja lokaci sannan yace "duk yadda dai Yakamata amma karya wuce wata biyar" 

  "Anya zai isa har ka gama shirye shryenka? anya baza a 茩ara ko wata biyu bane?"

"Kamar yadda ka sani na rigada na kammala gini na, kuma ina zaton shine mai matsalan, so nagama da Wannan kai shedane" ya fa蓷a idanunsa fes akan na Baba Garban.

Kai ya jinjina da fa蓷in " na fahimta wai ina nufin sauran hidimomin biki kaga ga b......." 

   "Shi yasa nace ka turomin account nombanka , banason taimakon kowa da Allah na dogara harna kai zuwa wannan matsayin" ya fa蓷a tareda ha蓷e fuska, dan ya fahimci me Bappannas ke nufi, zato yake zai bu茩aci wani abun daga garesane? NEVER shi baya bu茩atar komai dukda ha茩茩insa ne amma yariga da ya rufe wannan babin a rayuwarsa.

 Baba Garba kam shan jinin jikinsa yayi shi baisan wanne tsugudidin bane yasa yace a 蓷aga bikin kamar shi zaiyi masa auren? 蓷an satar kallonsa yayi ta gefen ido ya sauke Ajiyar zuciya da fa蓷in  "insha Allah bazai wuce wata biyar inba, maganan ku蓷i kuma nariga da nayi niyya dan haka kayi ha茩uri ka barni na ida niyya ta Allah ya ha蓷amu a ladan"

Iska ya fitar ta bakinsa tareda mi茩ewa tsaye    "na gode" ya fa蓷a tareda ficewa daga 蓷akin, a bakin 茩ofa yaci karo da Bishira da uban faranti a hannu, da sauri taja baya tareda gaidashi cikin in'ina, fuska sake ya amsa mata sannan ya ra蓳a ta gefenta yabar gidan.

 Wani mahaukacin numfashi ta saki tareda tsugunnawa a wajan, haka kawai taji 茩irjinta na bugawa.

 jin alamun ana tunkaro inda take ne daga cikin siting room yasa ta mi茩a jiki a muce ta nufi cikin gida.

 Galala mamanta take kallonta da fa蓷in  "ya haka kuma?" 

"Ya tafi" ta fa蓷a jiki a sanyaye tareda ajiye farantin a wajan ta nufi Cikin 蓷aki.

Da kallo uwar ta bita sannan tayi 茩wafa tareda bin 'yar tata cikin 蓷akin

************************************

   WASHEGARI

 Baba Garba da shida rakiyar wasu 'yan uwansa suka je gidan Barrister neman auren Samir, Hannu bibbiyu Barrister da kawunnan Mummy da sukazo dan cika sau茩on amanar Dady garesu. 

Sosai akayi raha da barkwanci inda Baba Garba ya bada ku蓷in neman Aure ha蓷eda sadaki, sosai hakan yayiwa su Barrister da蓷i, ba 蓳ata lokaci su Barrister suka tsaida ranar Aure nan da wata uku da fari Baba Garba yaso a 茩ara ya zama wata biyar amma su kawu suka kafe kan hakan bazaiyu ba suma Umarnin Mahaifinta sukebi kuma sunada tabbacin shi Samir in yasan da zancen Dan agabansa jiya Dady ke shaida musu a kotu. 

Hakan akayi kowa ya tafi tareda farin ciki a zuciyarsa, ba uwa Barrister da yake ganin zai sauke wani nauyi ne da Ubangiji ya 蓷ora masa.

  Sanda Baba Garba ya Kira Sameer ya shaida masa halinda ake ciki a waya, lumshe idanunsa yayi ya saukesu a bakin 茩ofar gidansa daya kusan wata biyar da gamawa.

"Nagode Allah yabar zumunci" ya fa蓷a tareda kashe wayan ya mayar aljihu.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda bu蓷e gate in gidan ya shiga.

Gida ne ginin zamani wanda ake cewa mu ha蓷u a palo,  kana bu蓷e 茩ofar zaka shiga haraban gidan inda zai 蓷auki mota 蓷aya, daganan sai entrance door idan ka shiga babban palo ne mai 茩ofofi hu蓷u a ciki, 茩ofa biyu a hannun dama biyu a hannun hagu. 茩ofofi biyu na hannun dama idan ka bu蓷e bedroom ne a kowanne 茩ofa da toilet insa a ciki sai 茩ofofin hannun hagu 茩ofa ta farko bedroom ne da toilet kamar wancan amma bai kaisu girma ba, sai 茩ofa na biyu kitchen ne ha蓷e da store sai wata 茩aramar 茩ofa dazai kai mutum ventilation na gidan.

Ba laifi sosai gidan ya tsaru, saida ya bubbu蓷e ko ina ya tabbatar ba inda ke bu茩atar gyara sannan ya rufo palon ya fara zagaye ventilation inda ke kewaye da tukwanan flowers kala-kala irinsu hibiscus, sun flower, alovera, queen of the night, gasunan dai kala-kala wanda suka 茩ayata gidan fiyeda cikinsa a yanzu.

 Idanunsa ya lumshe tareda bu蓷e su lokaci guda, sannan ya saki ajiyar zuciya ya fito daga gidan.

   Saida ya gama komai nasa sannan ya nufi 蓷akin Umma tareda sallama, a kwance ya sameta Naja nayi mata tausa, kusa da Najan ya samu waje ya zauna tareda kama 茩afar Umma 蓷aya ya 蓷ora kan nasa 茩afafun ya fara matsawa.

  Naja ce ta gaidasa ya amsa sannan yace "ta jima dayin baccine ?" Kai ta 蓷aga masa sama, iska ya fitar ta bakinsa tareda ajiye 茩afar yana 茩o茩arin mi茩ewa ne yaji ta kira sunan Naja tareda janye 茩afafunta tana yun茩urin mi茩ewa zaune, hakanne yasa ya koma inda yake zaune yana jiran ta gama watstsakewa.

Idanunta ne ya sauka cikin nasa sanda take gyara zamanta, "yaushe kai kuma ka shigo?" ta tambaya cikin mamaki.     "Yanzu" ya amsa a ta茩aice, sai kuma ya gaisheta sannan ya ladabta mata batun sa ranar auransa nan da wata uku da gudunmawar da Baba Garba ya bada.

 Wani Mahaukacin gu蓷a mara ma'ana Naja ta saki tareda surar MP inta dake gefenta tayi 蓷aki dan cashewa kamar ba dare ba.

Abu 蓷aya sukayi shida Umma wato girgiza kai tareda nemawa Naja shiriya.

"Kace gobe fita ta kamani dole naje nayiwa Garba godiya" ta fa蓷a idanunta a kansa.

Ha蓷e fuska yayi kamar bai ta蓳a dariya ba, saida ya mula dan kansa sannan yace "bafa shi yabani 'yarsa ba, kawai ku蓷i ya bada" ya fa蓷a a kausashe

" Yoo ai kyautar 'yar ma dan baka nema bane ninasan da gudu zai baka" Umman ta fa蓷a cikin maida masa martani.

  "Hmmm" kawai yace tareda mi茩ewa yana fa蓷in  "bafa inda zakije Umma, ai ke matar wansa ce, kome ne keya kamata a dinga zuwa har wajanki bawai ke kije ba" ya ida fa蓷a tareda ficewa.

 "Sannu Ubale" Umma ta fa蓷a da iyakacin Muryar ta yadda zaiji,

"Ai shida yake Uba a wajanka naga kana bashi girma da zuwa gaidashi ko? mai shegen ru茩on tsiya aiba banza Naja takeda wannan ba茩ar zuciyar ba, ashe 蓷akkowa tayi, ca nake ka manta komai ashe lumbu lumbu kakemin? To sai naje nayi godiya dan Ni ina mutumta mai mutumta nawa, a'to". Shi tunima harya kai 蓷aki baiji sababin da umma takeyiba,  kwanciya yayi a makwancinsa tareda lumshe idanunsa, da sauri ya bu蓷e su tareda 蓷aukar wayarsa ya shiga contact yayi dialing.














*Contact me 馃憞

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*