ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 13
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️13*
Sai da Baffa ya kwashe Sati biyu Cur a Garin Bauchi kana ya Koma portharcourt.
Wanda Kafin yatafi sai da Mallam yakara Zuwa Wajen Mallam D'abarani ya karb'o Mai Wasu Ruwan Addu'o'in wanna Karan a kananan Goran Swan ne Daya na Wanka D'aya na sha ne,sai wasu Addu'o'in da ya sake Rubutamai Kuma Alhamdulillah Sunga Chanji Sosai Shi kanshi Abdallah yafara Dawowa Cikin Hankalinshi.
Ta jirgi ya Koma Portharcourt Wanda Mallam da kanshi ya kaishi Har Filin jirgi na Abubakar Tafawa balewa Dake Bauchi Shida Mamman.
Hajiya ko da Su Anty Nafi da Baffa Zai Tafi Rikesa Sukayi Suna Kuka, Domin gani suke in yatafi To sai Yafi da Da dadewa kafin yazo Gida, Hajiya ko Takasa Tsaida Hawayenta Saida Abdallah ya Duka Yana Share Mata Hawaye Yana Tabbatarmata da Cewa bazai Kara kwatatanta Abunda yafaru abaya ba.
Insha Allahu Zai Dinga Zuwa Gida akai akai da Zarar Bukatar Hakan ya taso, da wanna Kalaman ya Taushi Zuciyar Hajiya Suka Rabu Cike da Kewa,haka ma Maman Fati da su Mahmud Suka Rike hannayensa kamar kar yatafi,sai da Mallam ya Ankarar Dasu Cewa Jirgin da Zai bi saura Lokaci Kad'an ya Tashi kana Suka Sakeshi Yafad'a Mota Shida Mallam Mamman ya Fice Daga haraban Gidan Suna Daga Musu Hannu.
shi kanshi Baffa Yana Jin Wani kwarin gwiwa acikin Ranshi Hawayen Hajiya Yafi Komai Dagamai Hankali, yanajin Shi kanshi baya kyautama kanshi Wanda baisan Dalili ba,ammh yayi alqawarin Gyara kurakuranshi na baya da yardan Allah.
Su Mallam Basu Baro Airport ba sai da Jirgin su Abdallah ya Tashi ya Lula Sararin Samaniiya, shi kanshi Mallam kafin su Rabu sai da ya Dinga Jaddama Abdallah kada ya Sake yayi Wasa da Amfani da mgungunarshi. Kuma Kada ya Koma ya Shagala ya Manta da Addu'o'i tare da Azkar, Cike da ladabi Abdallah ke Fad'ama Mallam Cewa Insha Allahu Zai Kiyaye, Da haka suka Rabu Bayan Sun Rumgume juna,shi kanshi Mallam sai da ya Share kwallah, Yana Fatan Allah Yasa Karshen Wahalansu Kenan Akan Baffa.
Daganan Cikin Mkranta ya Wuce Zuciyarsa Duk ba Dadi, Gida kuwa duk Sai yazama Wani iri.
Hajiya Dakinta taShige ta kwanta tana Tunanin Zucci, Aranta Tanajin Lokaci yayi da yakamata Itama ta Motsa Domin Tunda Har Baffa hankalinsa yafara Dawowa gida, to ya kamata Abnemi wani Abu Wanda Zai Kara karkato Dashi na Har Abada.
Wanda ko Matarsa Bata Isa tahanashi Zuwa garesu ba, tana wanna Tunanin Har barci ya kwasheta,su Anty Nafi Basu Dade ba kowacce taKoma Gidan Mijinta Hajiya ma Bata Tashi ba lokacin, Maman Fati sukama Sallama da Zasu Tafi,haka Gidan ya Wuni Babu Wani Walwala.
shi kanshi Mallam din har ya Dawo Bai da Wani karkarshi Hankalinsu Bai kwanta ba sai da Abdallah ya Kira wayoyinsu ya Sanar Dasu ya Sauka Gida lafiya.
hatta Maman Fati Sai da ya Kira, shine Zuciyarsu ta Dan kwanta Suna Kuma ji Aransu Insha Allahu Sukeda Nasara.
*******
PORTHARCOURT
Wasila Bata da masaniyar Dawowar Abdallah Domin Bai kirata ba.
Wacce ke kwance bisa Daya daga Cikin kujerun Falon kallo d'aya Zakamata ka zata Ta Shiga Haukane Saboda yarda Ta Dawo kamar Wata Mahaukaciya Sabon kamu Saboda Tashin Hankali.
sanye take da Riga da wando,wandon mini ne Kuma ya kamata Sosai,sai Wata karamar Riga Mai Kama da Shimi, Iyakarta Cikinta Don ko Cibiyarta Bata rufe ba,kitson Attachement din ya Tsufa Duk ya Fara Tugewa Saboda Dad'ewa. Fuskarta Duk ta kode hartafara Wani Tambarin Baki baki, da wasu kananan kuraje na kazanta Idanuwanta sun Kad'a sunyi Jawur, da alamun Wuni Suke Suna Zubar kwallah.
Ita kad'ai ce a falon. su Jamila Suna dakinsu Domin yanzu Indai Anty Wasila na Falo suka Fito Sun bani da Masifa Duk sai Ta nemi Hucewa akansu, yanzu ba Halin Su Shiryawa su Fita club in Suka Dawo takama Bala'i Sai Sun Raina kansu.
Gabadaya ta takura Musu ta damesu Kuma so ko Tsausayamata basa yi, Su dai Kawai Suji Dadi su Hole Tunda ita ta sakarmusu ammh yanzu ta Fara chanza Musu ko Kudi bata Basu balle Su Fita su Ji Dadin Rayuwarsu.
shiyasa Suma suke banza da ita Suyi Shigewarsu daki Ko zata Shekara Tana Kuka ko a haban Zaninsu, toh ko su emeka da Jospen Basu Tsira ba kuskure kad'an Mutum Zaiyi Sai ya Raina kanshi Ranar Har Sai da ta Shararama Josepen mari, Wai takan ya Kawo mata lemon Fanta ita Kuma Maltina tace,shine Kawai ta kasheshi da Mari.
Toh ya ya iya Banda Hakuri Domin ba karamin Aikinta bane ta Bashi Red Card.
Emeka na Zaune Cikin dakinsu inda Suke kwana Shida Samuel, wayar Abdallah ta Sameshi Cikin Rawan jiki yadaga Kiran Ko kafin yayi mgana Abdallah ya Rigashi da Fadin yazo ya Daukesa yana Filin jirgi.
Bai jira cewarsa ba ya datse Kiran, da hanzari Emeka ya Mike Saboda Rawan jikin Dawowar oga ko tsayawa baiyi ba ya Zari key din Motar Abdallah Wanda ke hannunshi ya Fice da Sauri, sai da ya Shiga motan ya Tada ita kana ya Lura da Samuel Dake Mai mgana,Hannu kad'ai yad'aga masa kafin ya zuba Hon megadi ya wangalemai get ya Fita da gudu Cikin Motar M.A Wato Bakar prado.
Wasila Dake Zaune Taji Karan Hon da Bude Get, da hanzari ta Mike ta Isa ta Window Falon,ta Bude Labulen wajen ta leka sai dai Bata ga kowa ba sai Kyallin Ficewar Emeka.
Kai ta girgiza tana mamakin Ina Emeka zashi da Motar Dee,lalle Zai ci Kaniyarsa komawa tayi tazauna tana Jijjiga jiki da kafa kamar wata basarakiya.
Emeka Yana Zuwa Airport Yaga Abdallah Yana Tsaye Yana Jiransa , Yana sanye Cikin Shadda Fara Riga da wando Dinki tazarce dauke da Hulan Zanna bukar ,iren iren kayansa ne Dake Gida,Wanda Tunda Wasila ta tarwatsa Rayuwarsa baya ma Zuwa Gidan balle Suyimai amfani.
sai Hannunsa dauke da Wata karamar Jakar matafiya Wanda Mallam ya Zubamai Gorunan Ruwan Addu'o'in a ciki, da Kuma Littafan Addu'o'in Tsarin Daya Siyo Domin Abdallah.
Tundaga Nesa Kwarjinn Abdallah ya Daki Emeka azahirin gaskiya ko Suit Abdallah ya sakar Yana Da Baiwar Haiba ta Kamala Atare Dashi. balle Daya saka manyan Kaya ai sai Emeka Yaga yakara Mai Wani girma a idanuwansa jikinsa na Rawa ya Nufeshi Yana Fadin"Welcome Oga.."Hannu kad'ai ya Daga masa Batare Dayayi mgana ba, illah Tafiya daya farayi Da hanzari Emeka na binsa Yana Kokarin karban Jakan Dake Hannunsa ammh sai yahanasa Lokaci Daya Yana Fadin"Thanks.."
Dole Emeka ya kyaleshi Sai da ya kwashi Gudu ya Isa Wajen Mota ya budemai Gidan Baya ya Shiga shikuma ya Zagaya Gidan gaba Ya bude ya Shiga Suka Fice Daga Airport din da Hanzari.
Basu Wuce Gida Direct ba Abdallah yace yafara kaishi Office, sai da Suka je ya Iske tarin Aiyuka Da fayel fayels, Bai iya Taba Komai ba Saboda Aikin yayi yawa,Sai dai Zuwa gobe gaisawa Kawai Sukayi da Sauran ma'aikatan Dake kasanshi Suna Mai barka Da Dawowa.
Daganan Gida yace Emeka yawuce Dashi gida Bayan ya Turama Polina Sakon ya Dawo gari yanzu.
Wasila na Zaune Taji Hon da Kuma Karan Bude Get.
Da hanzari Ta Mike,Saboda Yadda Takejin kanta ko Suturta Jikinta batayi Tunanin yi ba Takama Hanyar Fita daga Falon,ta Kunno kanta Kenan Sai suka kwashi karo da Abdallah. Har Saida Suka kume Goshin Juna, Baya Sukaja da Sauri Kowa na Dafe goshinsa Yana Kuma bin Dan'uwansa Da kallo. Wasila data ga Abdallah kamar Daga sama
Ta Waro ido Tana Binsa da kallo bakinta da Jikinta na Rawa take Fadin"Dee...is u...? Take Fad'a Tana Nunashi.
Mirmishi ya Saki Kawai Yana binta da kallo Cike da mamaki.
bai samu Zarafin mgana ba Tayo Rimi rimi Ta afkamai tana Sakin Ihu kamar zararriya.
Karfinsa ne Ke jikinsa Shiyasa ya Tari Wasila da Hanzari Bata kadasu ba, ihunta Shi ya Fito da Josepen da Su Jamila Hankali tashe ,ammh Kuma sai Sukayi Turus ganin Abdallah.
Wasila bakinta yakasa Rufuwa Ta kalli Su Jamila tana Fadin"Kun ganshi ko? My Dee ya Dawo gareni dama na riga na fad'a mu ku a Abdallah bazai Taba juyamin Baya ba Wayyo Allah."
Take Fad'a Tana Hawayen Farincikin, Jamila da hafsart Suka Saki ajiyar Zuciya Suna ma Abdallah Sannu da Zuwa Jospen kuwa bakinsa yaki Rufuwa, Riko Wasila yayi Yana kallonta Banda Mirmishi Babu Abunda yake Mata. Jakar Hannunsa take Son Karba ammh ya Hanata,Kallonsa take Tana Kara Shafa Fuskarshi Hannunta ya Riko da Karfi Yana Fadin"Noory ba fa mafarki kike yi ba Nine.."Yafad'a lokaci d'aya Yana Kara girman idanuwansa.
Fad'awa tayi Gefen Kafad'ansa tana Fadin"Wlh Dee na Fidda Rai dazaka sake Dawowa gareni. na dauka su Hajiya Sun Rabani dakai Kenan har Abada."Tafad'a daidai lokacin da Suke Haura Steps zuwa Cikin Master Bedroom dinsu
Mirmishi ya sakarmata kafin yace"Why..? Ko Shiyasa Duk Kika Rame? Ki kwantar da Hankali Ba mai Rabamu sai Allah. Kuma me Kika masu Hajiya da Zasu Raba mu ? Ba ma Wanda ma ya damu Dake gaskiya.."Ya Fad'a Yana Kara kallonta Cike da kyamar Kanta Dake tashin Wari .
Gabanta ya Fad'i tayi Cak tana kallonshi Daidai lokacin da Suka Shiga Bedroom dinsu.
Cikin karyewar Murya tace"Hakane. ammh bazaka sake tafiya ka bar ni ba ko Dee..? Tafad'a tana Wani Narke Murya, Yana Ijiye jakar Hannunsa bisa Gado yace"Dama ba barin ki Nayi ba. naje Duba iyayena ne Wanda na Dad'e banje ba, Suna da hakki akaina Wanda in ban Sauke ba Allah Zai iya kamani, nasan Kuma kema Zaki so Mijinki yazama Mai Sauke Nauyin Iyayensa ko..? Karki damu in Zan Koma sai mu Koma Tare Gudun Kar na barki ki Kara Shiga Wata damuwar.."
Tsurewa Wasila tayi Atsaye Tana bin Abdallah da Kallo Yana Tube kayan Jikinsa Cikin Rawan Murya tace"Bauchin Zaka Koma Dee...? Bai ba mganarta Muhimmanci ba yace"Eh mana ai Daga yanzu Insha Allahu Duk Bayan 2 weeks Zan Dinga Zuwa Chan banson na Kara sakasu adamuwar Dana sakasu Afarko Noory.."Yafad'a Yana Jan Towel din Dake Rataye a cikin wardrope dinsa ya Daura Kai Tsaye Kuma ya Shiga Tiolet din ya Rufo.
Baya Wasila taja Hannunta Dafe da kirjinta Idanuwanta Sun Fito waje Wayyo ta shiga uku Wani irin Abu ne yake Shirin Faruwa da ita..? Kalli Yadda Abdallah yake Fad'amata mgana Babu wannan tsoron Da Jin Mganarta da Tsananin Son da yake Mata..? Lalle Tayi Kuskuren Babba Data bama wad'anann Tsofaffun Dama Har Suka Samu Damar Kusa Rabata da Abdallah yazama Dole Ta Mike Tsaye Ta Nuna Musu Wacece Wasila. wlh ko Zatayi Yawo tsirara Sai Ta Kara Mallakar Abdallah Atafin Hannunta kamar yadda ta Sameshi Da Farko.
Bata jira komai ba Ta Fito Daga D'akin da Hanzarin Bibbiyu Take Had'a Step kamar zata Kife Falo ta Isa ta Rarumi wayarta Dake Kan Kujera ta Lalubo Momcy Wacce Ringing Uku Ta Daga Cike da Masifa Wasila ke Fadin"Momcy Abdallah ya Dawo Daga Bauchi yanzunan.
ammah Kuma Sun Gama lalatamana komai Yanzuma gayamin yake Zai Dinga Zuwa Duk Bayan Sati biyu, Momcy Kada ki Bari Shegun iyayen Nan nasa su sake Nasara akaina.
In Boka D'andugaji bazai Iya ba Ki Nemi Wani mana.
So nake a rabasu Rabuwa Ta har Abada Zasu San Da wa Suke Zencen."Takarishe Fad'a Tana Huci kamar Wata macen Zakanya.
Dariya Momcy ta Kece Dashi kafin tace"Yaro Yaro ne Baisan Wuta ba sai ya Taka. ki kwantar da Hankalinki Tunkafin kizo Duniya Boka D'andugaji keman Aiki Kan Mahaifinku Kuma Bantaba ganin Nakasu ba Sai Nasara.
Kema kisa aranki Bazaki Taba ganin Nakasu a Al'amarinki ba Wasila. Barni dasu Zan Nuna Musu Basu Isa ba Wlh Gobe in Allah ya kaimu zanyi Sammako Naje na Samu Boka, Ki dai ki kwantar Da Hankali Abdallah Naki ne,Kuma Zai Cigaba da Zama na ki Har Abada"
Mirmishi Wasila Tayi kafin tace"I Trust u Momcy. sai najiki.."Daga haka ta yanke Kiran Kafin ta Tsaya Tayi Shuru Kada Kai Tayi Kafin ta Haura Steps da Sauri Tana Komawa Bedroom din ta Iske Abdallah ya Fito Daga Wanka Yana gaban dressing Mirror Yana Tsane kanshi Da karamin Towel din Dake Hannunsa.
Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin tafara takawa Zuwa gareshi Ta Baya yaji Ta Rumgumeshi Tana Fadin"I miss u Dee..."
Bai Mata mgana ba illah Waigowa Dayayi ya Bambareta Daga Jikinsa Yana Fadin"I know. ki Shiga kiyi Wanka Noory ."Tsam tayi Tana Kallonsa Jakar dayazo Da ita ya Dauka kafin ya ijiyeta Saman stool din gadon Da Kallo Wasila ta Bishi Sanda yake karisawa gaban Wardrope din D'akin.
Ba tare Data Kara mgana ba ta Nufi jakar Tana Budewa Hannu ta saka ta Fito da Gorunan Rubutun Tare da Farar Takardan Mai Dauke da Addu'o'in a rubuce Gabanta yafad'i Da Sauri Ta waiwaya tana Fadin"Dee menene wannan..? Tafad'a tana Raba ido.
Waigowa yayi Yana Kallonta Da Sauri yabar Abunda yake ya kariso Gareta yakarba Duka Abubuwa ya maidasu Cikin karamar Jakar Yana Fadin"Mgunguna ne. Karki Kara Tabasu Ba Abun Wasa bane."
Yafad'a Yana Daukan Jakan Cikin Wardrope ya bude ya Turata Wasila Dake Tsaye Taji Wani Jiri na Dibanta in Tagani Daidai Addu"o'i ne Tagani Arubuce Toh Ruwan fa namene ne..? Bata Gama mamaki ba Taga Abdallah ya Shirya Cikin Riga da wando na kamfani mai tsada Agaban Idanuwanta ya Shimfid'a Sallaya ya Tada sallaar Azahar din Data kubcemai Bata Gama mamaki ba Sai da taga ya idar Taga ya Daga Hannu ya dad'e Yana Addu'a kafin ya Shafa.
Tana Tsaye Ammh Ji takeyi Jikinta kamar ba Nata ba, Ninke sallayan yayi ya waigo Yana Kallonta Cike Da mamaki ganin yadda Ta Wani Chanza gabadaya ga A.c ammh Tana Zufa,Bai Kai ga mgana ba Tayi Wuf Tafad'a Tiolet tana Rawan Kafa.
mele Baki yayi kafin ya Dauki wayarsa ya Fice Daga d'akin yana Lalubo Nombar Polina Domin Kewarta ne Yafi Damunshi ba na Wasila ba.
Kuma Yaga alamar Duk Dabaran Da Zaiyi Mata Bazata barshi Yafita ba balle Haryaje Wajen Polina.
******
Asma'u ta sanya Abun a ranta na irin Cin Zarafin da Yan'uwan Umma da Hajiya iya Sukayi mata
Tunda ga Ranar Walwalarta Ta ragu ko a Asibiti sai da Sister bahijja tayi ta Tambayanta ko Bata da lafiya ne..? Tace lafiyanta kalau, ganin batason Mganar ne yasa Ta Rabu da ita ammh yadda Ta karanci Asma'u ladan Tasan Akwai Abunda Ke Damunta,Kuma sanin Halinta na Zurfin Ciki sai Bata mtsamata na Sai Taji Kome ke Damunta baa.
Tundaga Lokacin Ta rage Fitowa Tsakar Gidan kamar Da da zata Fito suyi Hira da Anty Amarya ko Su Baba lami.
ammh yanzu Ta dinke in Ta Dawo Daga Asibiti tana Daki kwance ko Tana karatu ko Tana Danna waya,in ko Bata da Aiki in tagaji da Zama Gidan Ammi take Tafiyarta sai yammah Tadawo. ko su Anty Amarya da Suka Dawo Ta Fahimci Wani Abu na damun Ma'u ammh sai Bata yi karambanin Tambayanta ba Sanin Halinta na Shigen Zurfin Cikin ammh A Cikin Ranta Tana Addu'ar Allah ya Kawo ma Asma"u Dauki Da gaggawa.
Itako Asma'u Duk da damuwar Mafarkan datake yawan yi Kwana biyun Nan da Zarar ta kwanta barci na wani bawan Allah Wanda ba'a Bayyana Mata Fuskarshi ba, Yana Cikin Wani katon Rami Mai Dauke da Kunamu da macizai da Wasu Ababen Marasa kyan gani.
Ta Cikin Rami yake Miko Mata Hannu alamun Ta taimakeshi Sai ta rasa yadda Zatayi Dankwalin kanta take cirewa ta Yayyaga ta kullah Ta wurgamai ya Kama Kenan tana Kokarin jawoshi har ya Kusa Fitowa, sai ga Wata Mata ta bayyana Itama bataga Fuskarta ba Tayi Wurgi Da ita ta Fadi gefe Kuma tatura Mutumin ya Koma Cikin Ramin Tana wani Dariya Mai ban Tsoro.
adaidai lokacin Asma'u ke Farkawa a firgice Tun Ranar Data Fara wannan Mafarkin Abun yake Damunta Data Farka Bata komawa Barci Zata Dauro alwala tazo Tafara sallah Tana Rokon Allah ya kareta Duk da Bata da ilimin Fassaran Mafarki Abun Yana Damunta ganin Ba sau Daya ba Tataba Mafarkin Ba Koma miye Toh tabbas Yana Bukatar Taimakonta ne.
Abun mamaki Kuma Mafarkin Datayi Na karshe Taji Ana Kiran Sunanta Da Karfi Daga Cikin Ramin,ko Tayi Niyyar Zuwa gaban Ramin Don Taimakonshi Wannan Muguwar Matan Bata barinta Abun Duk ya bi ya Dameta kafin Wani Lokaci Ramarta da Damuwarta Sun bayyana Ajikinta da Kuma Fuskarta.
*Janafty*