Mutum Mugu Ne

18

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     18


Shiru tayi bata ce komai ba, ya sake maimaita tambayarsa still tak'i magana.

"Ziha had'a min ruwan tea d'in nan" yace mata ganin bata da niyyar masa magana

Ta sauka daga kan gadon taje ta had'a tea d'in ta kawo, mik'a masa tayi batare da ta kalli fiskansa ba.

Bai k'ar'ba ba yace " idan kin gama shan tea d'in ki had'a min kayana, I'm leaving tomorrow"

Da sauri ta d'ago ta kalleshi shima d'in ita yake kallo.

Fiskarta d'auke da damuwa tace " Uncle tafiya kuma, baka gama warkewa ba" 

"Yes Naziha, dole na bar muku gida tunda kin nunamin ni barene ban kai ki gayamin damuwarki ba. Gara kawai na tafi"

Yana gani tayi raurau da ido, idonta ya ciko da hawaye " Uncle kayi hak'uri Dan Allah, wallahi ba abinda kake tunani bane. Daddy yace kar na gayawa kowa"

Rufe laptop ɗinsa yayi ya tura gefe ya zuro k'afarsa k'asa yana kallonta har lokacin tana tsaye rik'e da mug a hannunta. Hannu ya buga gefensa alamar ta zauna kusa dashi, ba musu ta zauna amma jikinta yayi sanyi.

"Kina nufin ni kowa ne kenan?"

"A'a, I mean kai ba kowa bane....no, Kai kowa ne, ........ya Allah!" ta dafe kanta saboda ta rasa gane ma bayanin da zata yi

Murmushi yayi yace " an haifeki a Kano amma baki iya Hausa ba"

Ya k'ar'bi tea d'in ya d'an k'ur'ba sannan ya mik'a mata yace ta sha.

Bai kuma cewa komai ba sai data gama shanye tea d'in sannan ya d'an gyara zamansa yana kallonta sosai, fiskarsa ba alamar wasa yace " Naziha kin san dai musulmi d'an uwan musulmi ne ko?"

Ta gyad'a kai

"Wani alkawari na miki jiya?"

" Ehm ehm..kace zaka kula dani tamkar Azra, that you'll be like a father to me"

"Kenan ba kya son kulawata?"

"I'm sorry Uncle, zan gaya maka"

Nan ta zayyane masa abinda ya faru da ita a Hotel , attempting rape da aka mata da kuma yadda ta samu ta k'wace kanta kafin mutumin ya cimma burinsa.

Ya ji tausayinta sosai sai dai abin bai zo masa da mamaki ba dan yasan rayuwar yanzu son zuciya yai yawa, abinda baza ka so ayi maka ba ko a yi wa wani naka amma sai ya zamana kai zaka yiwa d'an wani.

"An kama shi?" Ya tambayeta

" Uncle babban mutum ne fa, koda an kama shi ba abinda za a masa"

" Daga yau kin dena aiki a hotel d'in nan" ya fad'i kai tsaye

Ta kalleshi da mamaki "dama Daddy ya mayar dani kitchen yanzu kuma ya bani hutun kwana uku"

"Ba kitchen ba ko office ne kin dena zuwa daga yau, zanyi magana da uncle d'in naki. Ba zai yiyu na zuba ido wani abu ya same ki ba, aiki a hotel kin dena shi har abada kin ji?"

Shiru tayi tana tunanin yanzu ya Daddy zai ji gobe idan Uncle Sajid yace mishi bazata kuma yin aiki ba, bayan shi da yake guardian d'inta yace zata cigaba da aiki.

Kat'se mata tunani yayi da cewa " ina da dalilin cewa bazaki kuma aiki a wajen ba, kina tunanin kin tsira idan kin koma kitchen, mutum da kike gani fa mugu ne, idan yai niyyar muguntarsa sai dai Allah ya kiyaye"

Yai ajiyar zuciya ya cigaba " barin baki wani labari, labarin da ban ta'ba gayawa kowa ba sai yanzu.

Inaso ki godewa Allah dayasa wannan mugun mutum bai samu dama akanki ba, domin ni anci galaba akaina, I was just helpless on the floor, couldn't do anything about it. I was raped Naziha"

Da sauri ta kalleshi fiskarta cike da mamaki,tsoro da tambayoyi.

Shin ko dai 'yan liwad'i ne? Tunda tasan Amurkawa suna da gay dayawa .

" Kina mamaki ko?

Ba abin mamaki bane duba ga shekaruna yanzu da kuma tafiye tafiye danayi a duniya dan ak'alla idan ban manta ba naje k'asashen da zasuyi sama da 40.

Nayi mu'amala da mutane iri iri, kuma naji labarai makamancin haka daban daban, saidai kullum 'bacin rai na shine duk abinda nake dashi duk k'arfina ban iya hana faruwan hakan ba I was completely helpless."

Ita dai Naziha sororo tayi tana kallonshi

" Kwana biyu mukayi amma I feel comfortable talking to you Ziha, shi yasa zan gaya miki wannan magana.

Kin san ku mata da kwashe kwashen k'awaye, you just met someone amma sai ku bashi lasisin shiga rayuwarku ba tarema da kun karanci ko shi waye ba, balle halayensa.

About 5yrs ago na je Los Angeles wani aiki, saboda nayi zama acan so inada gida, Ina dawowa da dare wife d'ina ta kirani, wai akwai wata k'awarta 'yar Nigeria ta zo LA yin wani abu zata wuce Dubai amma an cancel flight ɗinta sai washegari, so shine ta bata address d'in gidana ta kwana kafin washe gari ta wuce dubai d'in"

Girgiza kai yayi, alamar har yanzu yana jin haushin abinda matarsa tayi masa

" Imagine Ziha! Bama neman izinina take yi ba ta riga ta aiwatar da abinne take gaya min, karnazo na samu bak'uwar ya zama min abin mamaki.

Na isa gida na tarar da bak'uwa ashe tayi kusan two hours agidana, da shike akwai wani tsoho mai kulamin da gidan Mr Williams kuma tayi masa bayanin Zaytunah ce ta turota shi yasa ya barta.

Bayan na dawo Mr Williams ya tafi saboda dama baya kwana. Daga yanayin matar na gane cewa ba mutuniyar arzik'i bace, so muna gaisawa sama sama na tafi d'aki, nayi abinda zanyi na kwanta.

Washe gari na tashi na shirya na fito dan karyawa saboda dama ni nake had'a breakfast da kaina, Mr Williams yakan gyaran gidan ne ya tafi.

Dana fito na samu wancan bak'uwar ta had'a breakfast abin haushi ma wai ashe ta riga tasan I'm allergic to egg, take gayamin wai recipe da tayi ba k'wai aciki.

Bcox I didn't trust her kawai na d'auki mug na had'a tea da kaina nasha na tashi, abinda ban saniba shine ajikin mug d'in ta tsiyaya maganin.

Na tashi Ina tafiya na ji hajijiya before I knew it kawai na fad'i k'asa, gaba d'aya jikina yayi lakwas ko hannuna ban iya d'agawa. Ina gani wancan tsinanniyar ta fara aikata mission d'inta and I couldn't do anything.

Mr Williams ne ya shigo gidan after 20mins yana tunanin ma na fita aiki, sai ya tarar da mu a haka" Sajid ya ja numfashi idonsa yai ja daka ganshi kasan ransa a 'bace yake sosai.

"Zuwan Mr Williams shiya dakatar da tsinanniyar nan ta kwashe kayanta ta gudu, Mr Williams ya taimaka min ya kaini kan kujera jikina bai koma dai dai ba sai after 2hrs.

to this day babu wanda na tsana a duniya irin Matar nan. Bayan abinda ya faru nayi bincike akanta wanda feedback dana samu yasa na k'ara tsanarta.

Ziha ki yarda dani aikinki a hotel ya k'are daga yanzun"

Ziha hawaye ne taf a idonta, wace irin macece wannan marar imani haka, ba kunya ba tsoron Allah.

"Je ki kwanta dare yayi, zanyiwa Uncle d'inki magana gobe"

Rasa mi zatace masa ma tayi domin abin ya d'aure mata kai. Da k'yar ta had'a kalmomin da takega zata iya gaya mishi a wannan lokaci " Uncle I'm sorry, I'm very sorry"

Murmushi yayi,wanda tasan bai kai zuci ba yace " je ki kwanta kawai"

Tana fita daga d'akin ya sauke ajiyar zuciya, tambayar kanshi yayi miyasa ya iya gayawa Naziha labarin nan bayan ko Zaytunah bata sani ba, miyasa yake jin dad'in magana da Naziha bayan shi bai cika yiwa mata magana ba. Zaytunah ma da take matarsa baya iya yin wasu personal tad'i da ita saboda yasan halinta. Amsar da ya bawa kanshi shine Naziha is different, Naziha ya d'auketa ne tamkar 'yarsa.


....... KADUNA...........


Tunda Layla ta tafi ya samu kansa da yawan tunaninta, zuwan Aaliyah hutu shi ya d'ebe masa kewarta.

Yau sunday zai mayar da Aaliyah makaranta, sun iso ya d'an mata fad'an tayi karatu saboda jarrabawar WAEC da zasu fara.

"Abba gobe Layla zata dawo"

" Ya aka yi kika sani?"

" Muna chatting jiya take gayamin, Abba sonka fa take yi"

Yad'an had'e rai yace " ita ta gaya miki hakan?"

" A'a amma nina fahimci hakan kuma kaima kana sonta"

Hararanta yai yace " yaushe kika san so Aaliyah? da har zaki gane Layla sona take, kema kin fara kula samari ko?"

Dariya tayi, tasan tsakaninta da mahaifinta ba wani shamaki takan iya gaya mishi magana son ranta.

"Abba Allah bani da saurayi, ni dai nasan tana sonka kuma kaima kana sonta, Dan Allah kawai ka aureta"

Ya kama kunnenta d'aya ya murd'a " ke ko da shegen sa'ido, waya gaya miki Layla Kadi Maikud'i zata iya auren manomi kamar ni"

"Abba son gaskiya baya duba wannan"

Ya ja karan hancinta yace " ki maida hankalinki karatu wannan maganan ba naki bane"....

Har ta tafi tana dariyan Abban nata saboda har yanzu kallon yarinya yake mata, baisan yanzu ta wuce tunaninshi ba.

Haka kawai ya ji labarin dawowar Layla yasa shi farin ciki.

Washe gari tun k'arfe takwas ya je gidansu ya kuwa samu anata gyaran gidan daga wajen ma'aikatan ya ji labarin tarema zasu dawo da Mom.

K'arfe goma dreban Mom ya je d'aukosu a airport.

Suna zaune tareda mai gadi amma idanunsa na bakin gate d'in.

Ana haka suka ji horn, yana zaune har motarsu ta shigo. Tashi yayi ya isa wajen da aka parker motar dansu gaisa da Mom kafin ta shiga cikin gidan, sai dai zuciyarsa kwad'ayin ganin Layla kawai take yi ba komai ba.

Lokacin da ta fito ba k'aramin kyau ta masa ba, tayi wani fresh da ita sai glowing take yi.

Suna gaisawa da mom ta wuce su idonta sanye da bak'in eye shade, yayi mamakin halin ko in kula data mishi yana ce mata 'Hajiya Layla barka da dawowa' amma ta yi kamar bata ganshi ba.

Har bayan la'asar yana sa ran fitowar Layla amma shiru. Chan yai ta maza ya shiga gidan, mai aiki ya samu a falo yace ta mawa Layla magana kafin ta tafi sai ga mom ta sauko.

"Alyasa'a lafiya dai ko?"

"Lafiya Hajiya dama ina tambayane ko Layla zata fita yau"

Mom tayi murmushi " ai Layla a gajiye take gashi fushi take da kowa yau din nan, ina ga ba inda zata je"

Jiki a sanyaye ya fita daga falon bai so haka ba, yaso ace ya sake ganinta ko sau d'aya ne.

Wasa wasa kwana biyu da dawowar Layla amma bai kuma ganinta ba, kuma bata neme shi ba. Hakan yasa shi tunanin ko lafiya.

*

Zaune take kan kujera tana sauraron maganganun Daddynta wanda bai juma da dawowa ba.

"Layla labarin nan naji dad'inshi duk da cewa tuni munyi magana da senator Alhaji Wada akan had'aku da babban d'ansa sai dai kuma farin cikinki ya fi min komai a duniya, tunda akwai wanda kike so shikenan"

Murmushi tayi dan batasan daddy zai yi saurin amincewa ba.

"Wani hanzari ba gudu ba, wayeshi wanda kike so d'in? Miye matsayinsa a k'asar nan?"

Anzo wajen, dama mom ta riga ta gayamata ta hak'ura dan ba yadda za'ayi Daddynta ya amince.

Muryarta na rawa ta fara bayani "daddy Wanda nake so ba kowa bane Kuma ba d'an kowa bane, temporarily yana aikin driver yanzu amma manomi ne kuma......"

Cikin tsawa wadda daga ita har mom sai da suka razana Alhaji Kadi ya fara magana " Talaka, Layla kina kiramin tsiya da talauci a gidana, wallahi duk randa kika sake kiramin talauci a gidan nan sai kin gamu da ɓacin raina" tashi yayi zai bar falon Mom d'in sai ya tsaya ya juyo ya kalleta yace " na baki wata d'aya kiyi tunani, idan baza ki iya auren d'an senator Alhaji Wada ba to ki nemo wani dai dai da ke, bayan one month grace dana baki auren dana shirya miki tun farko shi za'a yi" yana gama fad'in haka ya fita

Layla ta fashe da kuka, Mom ta zo ta rungumeta tana lallashi....


Kamar da wasa ya ji k'aran shigowar text wayarshi lokacin daya fito daga sallar Isha, yana dubawa yaga sunan Layla, tunda ta tafi sai yau ta neme shi.

Ya karanta text d'in kamar haka:

*AY Ina jiranka yanzu, akwai inda zamu je*

Da sauri ya k'arasa gidan koba komai yau zai sake ganinta. A Cikin motan da zasu fita ya sameta dan haka yana zuwa ya tada motar. Har suka yi nisa da gida babu wanda yace da wani komai, lokaci zuwa lokaci yana satar kallonta, tayi tagumi tana kallon titi.

"Ina muka nufa Layla?"

Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe masa da kuka,

"Subhanallahi" ya fad'i sannan ya nemi waje ya yi parking.

"Layla lafiya? miya sameki?"

Saida tayi kuka mai isarta sannan da kanta tayi shiru ta kalleshi ido cikin ido tace " AY ina sonka, ka aureni dan Allah"

Ajiyar zuciya yayi sannan ya fara tunanin wani irin amsa zai bata, ya riga ya gane cewa tana sonshi d'in, amma bai d'auka har zata iya fitowa fili ta gaya masa ba.

"Na san ko kai wanene kuma na san dalilinka na aiki agidanmu, AY ka taimakeni dan Allah ka aureni, wallahi ba zan iya rayuwa da wani ba idan ba kai ba"

"Layla" ya kira sunanta a hankali har lokacin bai san takamaimai mi zai gaya mata ba

" Ka daure koda baka sona ka aureni kodan ka samu damar bincike sosai akan mahaifina, Daddy wata d'aya kawai ya bani kafin nan idan ka amince sai muyi aure a 'boye daga baya sai mu gayamusu"

"Layla kiyi hak'uri ki amince da za'bin mahaifinki, shine kwanciyar hankalinki"

Ta goge hawayen dake fiskarta tace " AY ka fi so na mutu kenan?, Tunda na tafi babu ranar da bana tunaninka, Kaine mutum na farko daka shigo rayuwata ka haskakata ka nutsar dani addinina, ta dalilinka na rabu da duk wani girman kai, ta dalilinka na fara tunanin makomata wadda da ban ta'ba tunanin hakan ba, I LOVE YOU, AY. Kai ne mutum na farko dana fara so. Idan baka soni ba zan iya rasa rayuwata"

Bugun kirjinshi ya yawaita shima d'in yasan yana jin wani abu gameda Layla duk da yana k'ok'arin yakice hakan.

" Layla inaso kiyi istikhara ki nemi za'bin Allah, ba dole ne abinda kike so ya zama alkhairi a gare ki ba"

"Istikhara na nawa AY?, bayan wanda nayi a masallacin Manzon Allah da wanda nayi a masallacin Ka'aba, akwai saura kuma. AY tunda nabar k'asar nan babu randa bana kai kukana ga Allah and it's always you I see, koda second d'aya banji sonka ya ragu mani ba, sai ma k'aruwan da ya yi"

Yanzu kam jikinsa yai sanyi " ki bani kwana uku zan yi shawara"

Daga haka bai ce komai ba yaja mota suka koma gida ita d'inma bata kuma cewa komai ba.

Bacci kam gagararsa yayi, maganganun Layla suna masa yawo a kwanya. Duk ta inda ya 'bullo ba shi da mafita, harga Allah idan yace bayason Layla yai k'arya, idan ma yace bayason aurenta to yaudaran kansa zai yi. Sai dai babban tashin hankalinsa shine mutum irin Alhaji Kadi da ake masa zargin yana tsafi idan ya auri Layla ba tareda yana so ba komai zai iya faruwa.

Aaliyah, ba zan bari dalilin nawa farin cikin na saka rayuwarki cikin hatsari ba. Ke kad'ai gareni yanzu. K'arshe dai ya tashi ya rok'i Allah yana neman mafita.

Ita d'inma Layla bata sami nitsuwa ba tunanin hukuncin da AY zai zartar ya hanata barci.



.......BAUCHI........


Ba laifi jikin Abba ya warware dan yau zai fara fita lectures, bayan ya gama yin breakfast Nazira ta rakashi har wajen motarsa sai daya tafi sannan ta shigo gidan.

Tun rasuwar Waheeda bata bi ta kan wayarta ba sai yau, ta bud'e wayar tana duba sak'onni daketa shigowa yawanci na ta'aziya ne, goge gogen abubuwa takeyi ta shiga phone records taga akwai wani record guda d'aya har zata goge sai tace bari taji k'ila wani waya da tayine hannunta ya danna record ba tare da ta sani ba. Tana kunnawa jikinta ya fara rawa muryan Waheeda ce, wayarsu ta k'arshe kafin mutuwarta.

Alhamdulillah ta fad'i tareda sujjada a k'asa hawaye fal a idonta, tabbas wannan hujja ce mai k'arfi da zata iya karawa da Alhaji Kadi. Ta yi saurin saving audio d'in a Gmail ɗinta sannan ta fara kiran Nuhu saurayinta police dake aiki a Kaduna wanda ya sanar da ita rasuwar Waheeda.

Bayan ya d'auka ta masa bayanin abinda ke faruwa da kuma evidence da ta samu.

"Kul Nazira kar ma ki fara k'ok'arin shigar da k'ara wallahi zaki sha mamakin yadda za'ayi fatali da hujjonki k'arshe ma a kama ki da laifin sharri, a Nigeria fa muke"

Cikin kuka take rok'onshi "Dan Allah Nuhu ka taimaka min kaga kai d'an Kaduna ne kasan ya abubuwa suke acan"

"Nazira kenan kaman ba a Nigeria kike ba inda mai kud'i akoda yaushe shi ke da gaskiya. Alhaji Kadi da kike gani idan za a lissafo masu kud'in KD guda biyar idan baiyi na d'aya ba zai zo na biyu. Kiyi hak'uri kawai"

Ai yana bata hak'uri kaman ingizata yake kuma yi. Ganin ba hak'ura zata yiba yace mata akwai wani d'an uwan matarsa tsohon d'an CID ne zai tambayeshi abin yi, da haka suka rabu.

"Insha Allah Alhaji Kadi saina tona maka asiri duniya tasan abinda kakeyi" .........



..... KADUNA.......

Washe gari....

K'arfe bakwai saura aka fara k'wank'wasa k'ofar gidan sa, ya je ya bud'e k'ofan.

"A'a Nuhu manya kune da sassafe haka"

"Munce mu zo yanzu saboda samunku a gida sai a hankali"

Gaisawa suka yi sannan ya mishi bayanin Nazira da abinda ya sami k'anwarta.

Da sauri AY yace ya kunna mishi audio d'in yaji. Dama Nazira ta riga ta tura masa.

Sai daya gama ji sannan yace "wannan evidence ne amma bai kai evidence da zai sa ta ci galaba akan Alhaji Kadi ba, ana zuwa kotu cewa za su yi had'a audio d'in aka yi"

"Yanzu Yaya Alyasa'a ya za'ayi kenan? Wallahi tabi ta damu wai tanason tona asirin Alhaji Kadi nikuma nace mata da kamar wuya"

AY ya nisa yace "yanzu ka turamin audio d'in sannan ka bani numbarta zan mata wasu tambayoyi" ........

Lokacin da Nuhu ya tafi ya jima yana jin audio d'in ya saka ya kuma maimaitawa. Mik'ewa yayi tsam yace "Dole na aureki Layla domin idan asirin mahaifinki ya tonu za ki fi kowa shiga tashin hankali, when that happens I promise I will be there for you"

Da wannan ya kira numbar Nazira. Sun jima suna magana daga nan ya shirya zuwa gidansu Layla dan ya sanar da ita hukuncin daya yanke......


......JOS........

Yau a gajiye ta dawo daga restaurant dan haka tana gyara jikinta ta kwanta sai bacci. Cikin bacci take jin muryan Kabir k'asa k'asa ta d'an bud'e ido amma bata ganshi gefenta ba, zoom ta mik'e zaune bayan taji abinda Kabir d'in ke fad'i " wallahi nayi missing fiskarki, ki bani dama na sake ganinki ko sau d'aya ne"

Ta tashi ta nufi band'aki inda takejin maganar na fitowa, ta kasa kunne tana jinshi zuciyarta na bugawa da sauri sauri, yadda taji Kabir na mak'e murya wa mace yasa ta shiga tashin hankali. Juyawa tayi ta koma kan gado ta kwanta kamar mai bacci, yayi kusan minti goma kafin ya fito daga bayin shima ya bi lafiyar gado, har asuba bat rintsa ba, tunanin shegiyar da mijinta ke nema ya cikata, ada taso ta tada hankalin Kabir adaren nan ta nuna masa ta ji wayar da ya ke yi, sai dai tana ga yin hakan zaisa ta kasa gano wace tsinanniyar mijinta ke kulawa, Dan haka ta daure.

Da safe kamar ba komai ta tashi tayi duk abinda ta saba, Kabir na shiga wanka ta d'au wayarsa ta duba wayarsa ta k'arshe jiya da dare abin mamaki sai taga sunan namiji wai Nazim sai kuma ga shigowar text daga numbar kamar haka:

*Ya Muhammad nagode da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi ka gaidamin Hajiya*

Tana gama karanta text d'in ta fita sai taga ashe transfer na airtime yayiwa numbar har na dubu biyu. Da sauri ta d'auko wayarta ta fara kwafan numbar saiga sunan Nazima ya fito 'baro 'baro a nata wayar.

Hannunta ya fara rawa jikinta yana 'bari da k'yar ta ajiye mar wayar ta d'au jakarta ta fita, yaranta na mata magana ta yi banza dasu.

Tana isa restaurant d'in ta shiga office d'inta tace a kira mata Nazima bata ma jima da zuwa ba.

Tana shigowa office d'in ta d'an rusuna za ta gaida Hajiyar ta ji saukan mari a fiskarta bata ankara ba Hajiyar ta sake kwad'a mata wani mari...

"Dan ubanki Nazima da abinda zaki saka min kenan ki k'wacemin miji, saboda ke butulu ce" duka ta fara kai mata ta ko'ina, Nazima na kuka tana bata hak'uri amma ina, ko sauraronta bata yi.

Sauran Ma'aikatan ihun Nazima ya ja hankalinsu zuwa office d'in amma kafin su k'araso Hajiya Raudha ta riga ta gama buga kan Nazima jikin gini wanda yasa ta fad'i sume jini na zuba daga kanta......

Bayan awa uku.....

Duk yadda yayi a bashi bail d'in matarsa amma abin ya faskara, kawai ya kira Muhammad Shabbir k'anin Raudhan yake sanar mishi abinda ya faru cewa Raudha ta yiwa d'aya daga cikin 'yan aikinta duka harta fasa mata goshi kuma yayan yarinyar babban d'an sanda ne yasa an kamata.

Cike da takaici Shabbir yace zai kira wani suyi maganan sannan, shima zai kamo hanyar Jos yanzu.

......Hajiya Salma zaune take kan kujera idonta taf da hawaye, Khairy na gefe itama tayi tagumi. Sallama Yaya Isa yayi ya shigo d'akin sanye da uniform.

"Hajiya ta farfad'o kuwa?"

Daga Hajiyar har Khairy babu wanda ya kalleshi balle yasa ran zasu bashi amsa.

Ya d'an tsugunna gaban Hajiya yace "Insha Allah sai Raudha ta d'an d'ani bak'in wahala a wajena"

Cikin 'bacin rai Hajiya tace "idan baka bar d'akin nan ba sai na maka baki, miye zaka yiwa Hajiya Raudha bayan kaine silar komai, idan da kana kula da k'annenka wannan abu zai faru, Babu wanda ka sani daga kai sai matarka. Tsakani da Allah Isa kud'in Jamb ya gagareka biyawa k'annenka, kud'in Jamb....." kuka ya kufce mata, jikinsa yai sanyi. Tabbas maganar Hajiya gaskiya ne saboda su rufawa kansu asiri Nazima ta fara aiki da Hajiya Raudha.

Shi kansa ya rasa miyasa baya iya taimakawa 'yan uwan nasa uwa uba mahaifiyarshi.

"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri ki dena zubda hawaye saboda ni, wallahi nayi nadama ki tayani da addu'a, Nima ban san ya akayi nake k'in kula daku ba"

Jin kalamanshi yasa jikinta yai sanyi.........



........ LAGOS........


Washe gari an jima ana tattaunawa tsakanin Sajid da Daddy daga k'arshe dai dole ya hak'ura Funmi zata dena zuwa aiki.


Gaba d'aya lokacin da Daddy ya gaya mata hukuncin daya yanke sai ta ji ba dad'i ta san dole ya ji haushinta a ransa. Amma ga mamakinta sai yace mata Sajid ya fishi gaskiya idan har yana son kula da ita yadda ya kamata aikin hotel ba nata bane.

Bayan sun fita ta shiga guest room ta tattaro kayan Sajid masu datti har da under wears ta wanke masa tas, ta sani koba komai Sajid is old enough to be her father dole ta kula da kayansa Ta gyara masa d'akin, da kayan suka bushe ta gogesu da shike dama ta iya gugan maza saboda lokacin Papa na da rai tana masa guga, Yaya AbdulBar ne ya koya mata.

Yau da wuri ya dawo gidan k'arfe hud'u da rabi, ya ji dad'in ganin d'akin a kimtse gashi kayansa an wanke an goge, dama yana tunanin gobe idan zai fita zai mik'awa Ishola ya kai masa dry cleaning.

Sallamarta ya kat'se masa tunani, ya amsa mata yace ta shigo.

"Uncle sannu da dawowa ya aiki"

Zama yayi gefen gado yace " kece zan miki sannu ai, nagode fah"

Ta d'anyi murmushi

Yace "Ziha akwai aikin da zakimin Dan Allah kafin na gama watsa ruwa"

"Ok Uncle"

Ya mik'o mata wani envelope yace akwai wasu documents anan inaso kije kimin photo copy ɗinsu kashi uku, na manta har Ishola ya tafi ban bashi ba.

Ta amsa da hannu biyu ta fita.

Koda ta dawo a k'ofar gidansu ta sameshi yana zaune akan plastic chair fari, ta mik'a masa ya amsa yace ya gode.

Koda ta shiga gida bin bayanta yayi da kallo "da mi zan saka miki Naziha, kin min taimakon da bazan ta'ba mantawa dake ba" ya dai cigaba da duba takardun yana cewa bari yai winning case d'in nan tukunna kafin yasan next step da zai yi akan Ziha.......