FANSA KO ƘIYAYYA

13

by @109051246447263646587

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*


Free pages



_Page13 _

    Waro manyan idanunta tayi sannan kuma ta ƙanƙance su lokaci guda sannan tasaki tsaki tareda kauda kanta gefe tana sakin numfashi a hankali.

  Shafa sumar kansa yayi da faɗin "an very scared wai ace yarinya ƙarama kamarki ta mallaki such gidaje ba tareda sanin iyayenta ko wani relatives intaba?   Wanne irin rayuwa kikeyi kuma a ina kika samu miliyoyin kuɗi haka keda ba kasuwanci kikeba?" Ya faɗa cikin ɗan ɓacin rai idanunsa cikin nata.

Waigowa tayi tana masa kallon sama da ƙasa sannan ta tsaida fuskarta kan nasa wani numfashi ta saki da faɗin "inaji idan ka kaini Headquartern naku sainafi jin tsoronka, and i warn you for the last time just live my world" ta faɗa tareda juyawa dan barin wajan.

   Ji tayi ya riƙe mata hannu tareda finciko ta ta dawo baya in a serious tone ya fara magana "kece Yakamata ki tsaya a limit inki, and ni bazan kaiki headquarter don bincike ba, ba don inajin tsoronki ba sai dan abu guda idan na bincike ki matsayin jami'i indai banda hujja ko kuma kika musa dolene akwai iya lokacin da zan rabu dake kin sha ruwa but ina tuhumarki ne matsayin mijin da zai aureki, dolone nasan wacece ke na kuma san irin matar da zan aurr....."

" Then saika fasa auran ai ba dole akai maba naga kai ka nema da kanka, kuma ka sakar min hannu " ta katse sa itama cikin fusata tareda zare masa idanu. 

Ajiyar zuciya ya sauke tareda daidaita fuskarsa, idanunsa ya lumshe sannan ya buɗe su kan hannun nata dake riƙe cikin nasa.

  "Wacece ke? Kuma me kike aikatawa a ɓoye ba tareda sanin iyayanki ba? and wanene wakilinki a secret life inda kike dahar zai tsayamiki ki mallaki dukiya har haka Ya kuma kasa faɗawa relatives inki?"  Ya tambayeta ba tareda ya ɗauke idanunsa dake kan hannunta ba.

 Wani kallo tayi masa da faɗin "never wlh bakada wannan kwarjinin da matsayin a rayuwata, and stay away of my site Kuma advice tunda baka san wace niba why not ka nemi Dady a prison da janye Yarjejeniyar dake tsakaninku instead of yin bincike kan abinda bazai amfanama da komai ba?" ta faɗa tareda sa idanuwanta cikin nasa.

Ɗayan hannunsa yasa ya shafo sumar kansa da faɗin "Never, nima never wannan yarjejeniyar kamar rubutu ne akan dutse, kuma tuhumarki bazan taɓa dainawaba koda hakan zai zama ƙarshen rayuwata saina nemo wacece ke, saina gano wacce iriyar kura ce ke mai lulluɓe da fatar akuya, amma for now zan barki cos banda wani hurumi dake, but ki jira nanda 3months sai nasa ki kinyi magana a inda bai daceba BINAZIR" yana gama faɗa ya murɗa mata hannu tareda cikashi ya taka yabar wajan.

  Da kallo take binsa cikeda mamakin ƙwarin gwiwar sa, amma fa zuciyarta ba abinda takeyi sai bugawa bana wasa ba, dan ya matuƙar firgita ta, a tunaninta wannan abin ya rigada ya zama past, bazai taɓa dawowa ba, sai gashi wannan Majnun in yanaso tado mata da wani mummunan ciwo a rayuwarta.

 Saida yayi taku uku sannan ya juyo tareda buɗe murya  "ina tayaki murnar, gidajanki na maƙwabta da gidan auranki" yana faɗa ya juya cikin isa.

Saura kaɗan jiri ya kwasheta, tayi saurin dafe motar dake kusa da ita tareda daidaita nutsuwarta, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta nufi cikin gida jiki mace.

  Koda ta shiga palon harara Aunty Lubabatu ta wurgo mata da faɗin "kedai kinji haushi, to me kika tsayayi dahar ya shigo shi kaɗai?" Fuska ta ɓata tareda shigewa ciki, ƙwafa Aunty Lubabatu tayi da faɗin "zaki nemeni ne ai"


(Idan banda Dady, Mummy, da Samir, ba wanda yasan dalilin auran Binazir ko Barrister a dunƙule Dady ya faɗa masa zancen auran amma bai gaya masa dalili ba)


  Da dare tana kwance shiru tana tunani, tunani mai zurfi, tunani takeyi ya akai yasan da wannan batun yama akayi ya iya tono mutaccen rayuwarda ta jima da binnesa?

Wayarta ce tayi ƙara tareda katse mata tunanin da takeyi,  ajiyar zuciya ta sauke dan tasan koda bata duba screen inba, tasan wanene, dan nambobin mutane uku ne kacal da tayi savin da kanta a cikin wayar, Dady, Mummy sai Salim Kuma Dukansu tasan ba mai kiranta a daidai wannan lokacin sai shi daya ajiye nombansa da kansa cikin wayar tata ta ƙarfi da yaji.

Tsaki ta saki jin wayar ta cigaba da ƙara, a fusace taɗau tareda katse kiran.  Tana ƙoƙarin ajiye wayar taga saƙo ya shigo, ƙura idanunta tayi akan screen tana kallon saƙon, haka kawai taji gabanta ya faɗi haka kawai taji tanajin tsoron saƙon, runtse idanunta tayi, tareda buɗe su kan screen in, wani numfashi taja ta fitar dashi ta bakinta tareda danna saƙon.

    "Me kike tunani? badai harkin fara tsorata dani ba? Karki damu as i said na ajiye wannan maganar a gefe harsai kin kasance a inuwata just nakira na sauke haƙƙina naji lafiyarki ki kwanta lafiya"

   Wani nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke tareda lumshe idanunta, harga Allah taji sanyi a zuciyarta da saƙonda ta gani, dan a tunaninta ba haka saƙon yake ba..

Gyara kwanciyar ta tayi tareda cigaba da tunanin wata rayuwa data tsinci kanta a ciki tun lokacinda ta take secondary school.

  Shima ajiyar zuciya ya saki sanda ya tura mata saƙon, shi mamaki yakeyi wai ace ƙaramar yarinya kamarta da mallakar kadarori batareda sanin iyayenta ba and idan bazai manta ba, tsawon shekara biyu kenan da siyan gidajan tun lokacin da yakeyin ginin gidansa, shi sai a ɗazuma ya tuna da fuskar yarinyar, tabbas itace, meke faruwa? wani numfashi ya saki, dolene yayi bincike sosai a kanta amma zai bari ba yanzu ba, sai tazama mallakinsa tukun yadda zaiji daɗin tuhumar ɓoyayyen wakilin nata da hujja mai ƙarfi.

************************************

 Sosai Bishira ta kwanta ciwo, hakan ya fusata Maman Bishira da ta je ta tsaya kan gadon Baba Garba Yana bacci ta fara zazzaga masa ruwan tijara, aikam tashi ɗaya bai dubi tarin 'yayanda ke tsakaninsu ba kamar yadda itama bata dubi tarin iyalansa suka tara tareba take masa fasifa kamar ɗan cikinta aiko da mari ya fara mata, kafin ta dawo hayyacinta ya fizge wayarda yake canjin system insa da ita yayi ta maka mata, tun tana daurewa harta kasa ta saka ihu da kuka, saida yayi mata liƙis sannan ya barta da faɗin "mahaukaciya kawai babbar banza babbar wofi kin girma bikisan kin girma ba, to koda kike ganin nayi sanyi to uban malaminda kike ganin yayi nasara a kaina, nace uban Ubanku kedashi, shekaru ne suka sani sanyi ba bokankiba Wallahi" ya faɗa cikin huci "son zuciya tareda kaidinki yasa na biyewa ruɗin shaiɗan ada dahar na aikata musu abinda na aikata, amma a yanzu koshi Samir yacemin yanason 'yarki bazan goyi bayansa na sakamakon ɗabi'unki data ɗakko wanda nima ƙaddara ce ta sami auroki" ya faɗa a fusace tareda shureta yabar ɗakin.

   Bishira dake kwance a ɗakinsu ita da ƙannanta guda uku sukaji ihun maman tasu tareda muryar mahaifinsa.

  "Mun bani mama ta taɓo tsohon zaki" wani ƙanin Bishira da ya faɗa tareda miƙewa yabar gidan.

Tun daga ranar ba wanda ya sake tada maganar Samir da Bishira a gidan sai ita da abin yake mata ciwo, gashi shi bai taɓa cewa yana sonta ba ballantana ta kirasa tayi masa zagin uwa da uba ko zataji zuciyarta tayi sanyi.

************************************

 A haka rayuwa yaci gaba,  

        Binazir

na fama da abubuwa uku a rayuwarta, na farko son zuwa wajan Dady amman Barrister ya hana yace saiya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa Dady na baya buƙatar kowa yazo wajansa ba tareda goron auran Binazir ba, wannan abin na matuƙar ɓata mata rai da sata cikin wani yanayi, gashi sosai takeson ganinsa, 

abu na biyu shine fargabar data cika mata zuciyarta gameda wani ɓoyayyan sirri nata na wata bahaguwar rayuwa data taɓa Yi sanda rana secondary School sai gashi mutuminda takeda burika na ɗaukar fansa a kansa da yawa yana son ya ƙara tarwatsa mata rayuwa nason gano rayuwarda ta taɓa binne babinta a tarihin ta, wanda baisan hakan ƙara rura wutar ƙiyayyarsa yayi a zuciyar taɓa.

 sai abu na uku shine takurar da yayi mata, yabi ya addabi rayuwarta da text ko kira, kwanakin baya har kiransa tayi ta zagesa tas kan takurar da yayi mata, amma saboda son ƙurar da ita saiya tura mata saƙon ❤️ ta WhatsApp.

     OS

Shi damuwarsa ya barwa Allah tareda maida komai ga ubangijinsa amma abu ɗaya ya ƙudurta tareda shine gano wacece Binazir, wacce irin rayuwa takeyi a bayan idanun mahaifanta? Tabbas zai gano wannan amma ba yanzu ba kamar yadda ya alƙawarta .

A wannan lokacin aka ƙara masa girma tareda kyaututtuka na bana mamaki saboda jajircewarsa da yayi, a lokacin ne kuma aka bashi cikakken iko na gudanar da case inda ya buƙata a bashi amma saboda matsayinsa bai kaiba a lokacin sai aka haɗa shi da case in Dady da alƙawarin yana gamawa za a bashi dama sai kuma yadda ya gudanar da case in cikin lokaci ƙanƙani tareda sadaukar da rai cibiyar hukumar su ta jiha baki ɗaya ta ƙara masa babban matsayi, ƙarin albashi tareda kyaututtuka daya samu na karrama wa daga takwarorin hukumar su, a Lokacin kam da sunansa ya karaɗe gidan rediyo, hotonsa da labarinsa a social media ,. Ƙaramin haukanne kawai ya rage Bishira batayi ba, amma ta sawa ranta ko zatayi yawo tsirara saita mallaki SAMIR.

Umma kam damuwarta bamai yawa bace kuma bamai tsayawa a rai bace ita dai tana tausayin Bishira, sai kuma tunanin shin yaya wai ita sirikar tata tana son ɗan tane ko kuma da wata a ƙasa?  Amma ita ko mene tanayi musu fatan alkairi da kyakyawan zato.

    MUMMY 

Damuwarta ɗaya mijinta kewarsa da kuma tausayin sa, ta sani ta rigada ta yi sallama da wani farin cikin rayuwa, ita yanzu rayuwarta ga Allah take, kuma dama dukkan rayuwarta ko ada ga Ubangijinta yake.

********************************

 Komai kaga an saka masa rana, to kawai ka jirayi lokacin zuwansa, abu ba asa masa ranaba ma yazo ya faru ballantana wanda ake ƙidayarsa kullum.

   Ayau Dubban Al'umma suka shaida ɗaurin auren BINAZIR MANI CIZO dana SAMIR ABDULLAHI a ƙofar gidan Barrister Umar Ƙani.

A daidai wannan lokacin tana cikin 'yan uwa sunata yimata tsiya taji ƙirjinta yayi mummunan bugawa, ita dai nata yaƙene kawai dan wani irin abune ke taso mata a zuciya kaman zatayi amai. Ga gida cike yake da dangin Dady dana Mummy.

Silalewa tayi ta shige toilet tareda fashewa da wani irin kuka, saida tayi Mai isarta sannan ta share hawayenta tareda wanke fuskarta ta fito. Da kallon tausayi suka bita dan a tunanin su alhinin biki ne, basusan abinda takeji yafi ƙarfin alhinin mutuwa ƙarewar na biki.

   Mummy ce ta shigo tareda sallama amsa mata Mutanen ɗaki sukayi tareda tsokanar ta murmushi kawai tayi sannan ta kalli Binazir da faɗin

" Barrister nason ganinki a compound" miƙewa tayi jiki a saluɓe tareda ɗaukar wani hijabi da batasan kona wane ba ta zura a jikinta, tare suka fito itada Mummy har compound, sosai Mummy ta ƙara yi masa godiya sannan tabar wajan.

 Gaishesa tayi ya amsa tareda tsokanar ta da "Amarya" yaƙe kawai tayi masa ya sunkuyar da kanta ƙasa.

 Umartar ta yayi data shiga cikin motar, kai kawai ta iya kaɗawa sakamakon wani irin tsinkewa da zuciyarta tayi, hakan yasa ta kama murfin motar tareda runtse idanunta ta buɗe, wani mahaukacin turare ne daya daki zuciyarta yasata saurin buɗe idanunta.

 Karaff idanunsu suka sauka cikin na juna yana hakimce a bayan mota yasha wata dakakkiyar shadda data saje da kalar jikinsa, kallonta yayi sama da ƙasa sannan ya wurga mata hararar  tareda ɗauke kansa.

  * Wai bazaki shigo bane?" Da sauri takai dubanta gaban motan, wani ƙanin Mummy ne da sanda abinnan ya faru akace baya ƙasar yayi tafiya.

Ware ido tayi na mamakin ganin sa dan suna Good time da kawunnanta, murmushi ya sakar mata da faɗin "zafa mu makara" da sauri ta shiga motan tareda sauke ajiyar zuciya. Barrister ne yayi Bismilla a fili tareda jan motan, gaida kawunnata tayi tana masa complain na rashin zuwansa cikin shagwaɓa, shidai murmushi yayi da faɗin "idan an girma dai asan an girma" ya faɗa tareda yi mata nini da gefenda Samir yake.

Shidai jinsu kawai yakeyi shida Barrister Dan Shi har murmushi yakanyi a hirar tasu.

Tsuke bakinta tayi tana cigaba da shaƙar ƙamshin turare har sukazo prison.

Sanda Barrister yayi parking da faɗin "Bismillah"

 Wata faɗuwar gaba tareda fargaba ce ta saukar mata lokaci guda, hakan yasata fasa yunƙurin fita da tayi tareda komawa da baya ta dafe saitin zuciyarta.

Saida ya tabbatar su Barrister sun gama fita sannan ya gyara zamansa tareda fuskantar ta.

  "Alhamdulillahi, ina tayamu murnar aure" ya faɗa sanda ya riƙe hannunta dake dafe a saitin zuciyarta. Fizge hannun tayi tareda jan wani dogon tsaki sannan ta buɗe marfin motar ta fice a fusace.

Murmushi ya saki tareda cire hular kansa ya shafa sumarsa ya maida hular  " 1_0 (one zero) ya faɗa a fili Sannan shima ya buɗe ƙofar ya fito ya nufi inda suke jiransa a tsaye. Tare suka jera suka shiga ciki, suna bada sunan Dady cikin minti 5 aka kirawo musu shi.

 Wani irin runguma tayiwa Dady tareda sakin kuka sanda ta ganshi, sosai zuciyarta ta taɓu na ƙaunarsa da tausayi sa. A fakaice ya share ƙwallar idanuwansa tareda ɗagota daga jikinsa yana maida dubansa ga su Barrister, wani kyakyawan farin hoto Barrister ya ciro daga aljihunsa ya miƙawa Dady fuskarsa ɗauke da murmushi.

Hannunsa har kakkarwa yake wajan karɓa, da sauri yakai goron bakinsa da furta "ALHAMDULILLA"











*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*