ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 15

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



     *🅿️15*



Karfe 11:30am Ta yima Su Mallam Akofar get din gidansu Asma'u da yake Mallam yasan Gidan Tun Lokacin da yazo ya Dauki Asma'u ya Kaita School of Nursing Birnin Kudu.

Yusuf ne ya Fito Daga Motar ya Karisa Jikin Get din ya kwankwansa megadi ne yazo ya Bude Karamar Kofar ya Leko Yana Tambayan waye..? Ganin Yusuf bakuwar Fuska ne agareshi Shiyasa ya fiito ya Karbi Hannun da Yusuf ke bashi Suka Sarke Musabaha,Yusuf ne yace"Don Allah Megidanan na Ciki Kuwa..? 


Megadi yace"Eh Alhaji na Ciki Bai Fita ba, Shi kuka Zo Gani..."?Yafad'a yana Leken Proff.daga Cikin Mota ganinsu ba wani Alamun Raini Cikin Kamala ,Yusuf ne yace"Eh Don Allah Ko Zaka Shiga Ciki ka mana Mgana Dashi..? megadi yace"Yanzu Kuwa.."Yajuya Da Hanzari Zuwa Cikin Gidan Koda Yayi Sallama a Babban Tsakar gidan Umma ce ta Amsa Daidai Lokacin Data Fito Daga Kitchen Hannunta Dauke Da Wani Katon Tire na Kayan Breakfast Din Abbane Dayake Baya karyawa Da Wuri ya Riga ya saba sai rana ta d'aga.

Amsawa Tayi Tana kallonshi. Rankwafa Yayi Yana Fadin"Ina Kwana Hajiya.."Kai Tsaye ta Amsa Tana gyara Zaman Farantin Hannunta, Cikin girmamawa yace"Hajiya Dama Alhaji ne Yayi Baki Suna waje sunce nayi Musu Mgana Dashi.."Umma Tace"Baki Kuma..? Daga ina Kuma Habu..?

Kansa na kasa yace"Wlh Bansani ba Hajiya ammh Dagani Manyan Mutane ne gaskiya.."Jin Haka yasa Umma Wucewa Zuwa Kofar Da Zai Sadata Da Shashen Abba Tana Fadin"Ok kace Gashinan Zuwa Bari na Sanar da shi yanzu.."Da Tom ya Amsa Kafin ya Fice Da Sauri Itama Ta Karisa Falon Abba Bakinta Dauke Da Sallama.

Abba Dake Kokarin Saka Hulan kansa Ya amsa Wanda Ke Tsaye a tsakiyar Falon Yana Kara gyaran Zaman Hullan kube d'in Din Dake Kansa, Center Table Din Dake Tsakiyar Falon Taja ta Ijiye Tiren Dake Hannunta Tana Bin Abba Da Kallo Kafin Tace"A"a Alhaji Naga kana Sanya Hula badai Fita Zakayi ba..,? Gafa Breakfast Dinka Na Kawo maka.."

 Mirmishi Yayi Yana Gyara Zaman Babban Rigar shaddan Dake Jikinsa Lokaci Daya Yana Kallon agogon Fatan Dake Hannunsa yace"Bar Abun Karyawan nan Mandiya Ina da Haduwa da Alhaji Hadi a company Kuma ya Kirani Tun dazu Cewa ya Iso Ni yake Jira. Saboda haka Sai na Dawo Kawai.."Fuskarta ba Dad'i Tace"Shikenan.."Yana Kokarin Ficewa Daga Falon ne Umma Take"Au Alhaji."Tafad'a Tana Bin bayansa Waigowa Yayi Lokacin Yana Saka Wani Budadden Bakin Takalmi.

 Umma Tace"Kaga na Manta Yanzu Da Zan Shigo Na gamu da Habu Megadi ya Shigo Wai kayi Baki Ana Sallama Dakai.."Kallonta Yayi kafin yace"Haba Mandiya Kinsan da Haka Kuma Tunda Kika Shigo Baki Fadamin ba? ai sai Suce An shanyasu Fisabillah.."Umma take"Yi hakuri wlh na Sha"afa ne.."Kai ya Gyada kafin yace"Ok ya Wuce Bari Naje na Gani Kila Dagachan na Wuce bani key din Motar Chan.."Ya Fada Yana Nuna Mata Key din Dake Kan Kujera Da Hanzari Ta Dauko Ta Mikamai ya Karba Ya Fita Tana Mai Adawo Lafiya.

D'akin Hajiya iya Ya leka sai ya Tarar Da Ita tana Ta Sharar Barci Bai Tashe ta ba kawai ya Fice Da Hanzari Saboda Bakin Da'a kace Suna Jiransa awaje.

 Koda Abba ya Fito Haraban Killace Motocin Gidan Bai ga kowa ba Sai ya Dumfari Get Yana kwalama Habu Kira,Wanda ya Fito Da Gudu Daga karamin Dakinsa Dake Gefen Get din,ganin Alhaji yasa yaRankwafa Yana Gaisheshi Amsawa Yayi yana Fadin"Ina Bakin Da Suke Son Ganina.."?

 Cike Da Ladabi Habu Megadi yace"Suna Waje Alhaji.."Kallonsa Yayi kafin yace"Haba habu meyasa Kabarsu awaje, ai Daka Bude Musu get din Sun Shigo.."Kan Habu Megadi na kasa Yace"Ayi Hakuri Alhaji.."Ya Wuce Yana Fadin"Bakomai.."Da kansa ya Bude Karamar Kofar ya Fice Kafin ma Habu ya Kariso.

 Shiko Yusuf habu na Shiga Cikin Gidan ya Koma Cikin Mota yana Gayama Mallam Gashinan Zuwa, Wayar Yusuf aka Kira Sai ya Fito Daga Motar ya Jingina da motar Yana amsa Kiran,Bai Dade ba Sai ga Abba ya Fito ganin Yusuf Jingine Jikin Mota yasa yagane Sune ke Nemansa Cikin Natsuwa ya Karisa Ga Yusuf din Wanda Tunda Yaga Fitowarta Abba yayi Saurin yanke Kiran.

Cikin Fara'a Suka Tarbi Juna Bayan Sunyi Musabaha, Abba na Kallon Yusuf yace"Bawan Allah Ban Shaideka ba,kuma Ance Kana Sallama Dani.."Yusuf ya kalli Abba Zaiyi Mgana Kenan Mallam ya Bude Murfin Motar Ya Fito yana gyara Zaman Gilashin Idonsa.

 Hannu ya Mikama Abba Sukayi Musabaha kafin Mallam yace"Alhaji nine ke son ganinka Indan ba Damuwa Ni Sunana Proff.Mahmud Abdallah Azare Nine Mijin Tsohuwar Matarka Habiba.."Jin Haka yasa Abba ya Kalli Mallam Yana Yar Dariya yace'Oh Allah Sarki Sannunku Da Zuwa,Masha Allah Ku Shigo Daga Ciki ai bakwa Tsaya Daga waje ba."

Mallam yace"Toh ba Damuwa"

Abba yayi Gaba Suka Rufamai Baya Har Zasu Shiga Gidan Abba ya Waigo Yana Kallon Yusuf yace"Bawan Allah Daka Shigo Da Motar Ciki daga ciki ko? Yusuf ya Juya yana Fadin"Toh Abba.."Motar ya Shiga Suko Su Abba Suka Karisa Ciki Ta Kofar Wajen Haraban Gidan Abba ya bude Kofar Falonsa Suka Shiga.

Shikuma Yusuf habu Megadi ya Wangalemai Get ya sulala Da Motarshi Ciki ya fakata Kusa Da Ta Abba,Fitowa Yayi ya Kulle Motar Shima Yayi Sallama Cikin Falon Yayin da Mallam da Abba Suka amsa Yusuf ya Shiga yasamu Gefe ya Zauna Yana Gaida Abba,Amsawa Yayi Cikin Sakin Fuska kafin ya Mike Yana Fadin"Ina Zuwa.."

Mallam yace"Ba laifi.." Da Sauri Abba ya Fita ta Kofar Cikin Gida Yana Kwalama Umma Kira, wacce Ke Daki Ta Fito Da Sauri,Hajiya iya ma data farka daga barci yanzu Sai Da Ta Fito, Anty amaryace Dama Tana Tsakar gidan,Cikin Mamaki Umma Ke Fadin"Gani Alhaji Lafiya Naga k Dawo..? Yana Gyara Zaman Haban Babban Rigansa yace"Kedai Bari Ban Tafi ba Daman Bakin nan ne na Shigo Dasu Daga nesa Suke Maza Ahad'a Abinci Da Abun Sha Don Allah akawo Musu Falona.."Hajiya iya ce Tace"Ladan Wasu Baki ne Wanna Naga kana Ta Rawan jiki..?

Ya Juya Zai Koma Ciki yana fad'in"Iya masu Muhimmanci ne, Don Allah Halima ko Mandiya ku Hanzarta.."Yafada Yana Wucewa Shashen Nashi,Anty Amarya ce Ta Mike Zata Shiga Kichen Hajiya Iya ta katseta Da Fadin"Ke Halima Dawo, Ke Mandiya hada Musu Komai ki Mika Falon Ladan.."Tafada Kai Tsaye tana Wani Hade Rai.

Anty Amarya Takalli Hajiya iya ta Danyi Mirmishi Duk Da Tagane Manufarta sai Ta Dawo da Baya Tana Fadin"Toh ai Bakomai Nida Ita Din Duk Daya ne, Dama ganin yace ayi Sauri ne Shiyasa na Mike.."Tana Gama Fadin Haka ta Shige Dakinta Umma Da Hajiya Suka Bita Da Harara Kafin Hajiya Iya Tace"Hanzarta Mandiya Kinga yace Bakin masu Muhimmanci ne, kila ma Manyan Mutane."Umma Tace"Toh.."Ta Nufi Kichen.

Dama Already Da Safe Su Baba lami Sun Dafa Ferfesun Kayan Ciki,sai Soyayyen kwai Da Kuma plantains, harda Soyayyen Buredi sai Ruwan Zafi da Kayan Tea,Shi Ta Hada awani Babban Faranti Shima Mai Kyau Da Tsari Daki TaKoma Ta Sanyo Mayafi, ta Mai Kyau Ta Dauki Tiren Ta Nufi Shashen Abba.

 Suko Su Abba Suna Kara gaisawa Da Mallam Kenan Sai ga Umma Tayi Sallama Suka amsa Ta Shigo Taja center Tablen din Dake Wajen Bayan Ta Sauke Farantin Kayan karyawan Abba Ta Dora Wanda Ta Shigo Dasu, Dan Rankwafa Tayi Tana Gaishe Da Mallam ya Amsa Kansa na Gefe Ita ko Kallonsa Take Duk da ba Sosai Ta ganshi ba Ammh Tabbas Dattakonsa Da haibansa Sun Daketa Kuma ga Dukkan alamu Hutu Da Naira Sun Zauna Mishi.


Fita Tayi Daga Falon,Da Hajiya Iya Taci karo Cikin Rad'a Take Tambayanta"Su waye..? Umma Tace"Bansani ba Iya bantaba Ganinsu Sunzo Wajen Alhaji ba, ammh maganarsa ne Manyan Mutane ne.."Dariya Hajiya Tasa batace Komai ba Ta Shige Dakinta Aranta Tana Tunanin Toh wad'anan Bakin Daga ina..? Kuma miye Dalilin Zuwansu..? Bata Da Amsa Shiyasa Ta Koma Bisa Kujera ta Zauna Tana Jiran Bakin Su Tafi Taji meke Tafe Dasu.

 Abba ne yace"Ga Abun Karyawan nan Don Allah ku ci.."Mallam ya Murmusa Yana Fadin"Bakomai Alhaji Mun Karya Daga Gida kafin mu Fito..."Abba Zaiyi Mgana Mallam Yayi Saurin Cewa"Karka ce Komai, Kafin mu Tafi Zamu Taba Wani Abun.."Abba ya Gyada Kai Yana Fadin"Shikenan.."

Mallam ne ya Gyara Zama Yana Fadin"Alhaji ladan Nasan Zuwa Yanzu Zuciyarka Na cike Da Mamakin Zuwana ko..? Ya Gyada Kai Yana Fadin"Hakane. Tabbas Ammh Ina Fatan Lafiya..? mallam yace"Karka Damu Lafiya Lau Sai Alheri, abunda Ke Tafe Damu Babban Al'amari ne Domin Nazo Nema ma D'ana Abdallah Auren yarka Asma'u ne. Kuma Ina Fatan Cewa Zaka Bamu Domin mu Hadu Wajen Kulla Alheri Kuma Mu Rabauta Wajen Raba ladan Wad'anda Suka Kulla Alherin."

Tunda Mallam yafara Mgana Abba ya Washe Baki Farinciki Sun Mamayeshi Mallam na Direwa Abba ya Karba Da Cewa"Masha Allahu. Alhamdulillah Naji Dadin Wannan batun Mallam, Kuma Ina Mai Farincikin Shaida maka Dama Chan Asma'u Taku ce,Kuna da Iko Akanta Kodon Auren Mahaifiyarta Daka keyi Bakomai Wlh Allah yasa Alheri Zamu Kulla Wannan ne Dan Wajen Naka..?

Yafad'a Yana Nuna Yusuf Wanda Ke Gefe kanshi Na kasa, Mallam ya Murmusa kafin yace"A'a bashi bane Dan' uwansa ne ,shi Yana Porthercourt Ma'ikacin Costom ne Yana Chan Yana Aiki Yana kuma Zaune Da matarshi achan, Wannan Yusuf Kenan.."Abba yace"Masha Allah Allah ya Taimaka.."


Mallam yace"Ameen. Hakika naji Dadin Mganarka Sosai, Mun Kuma Gode Sai Dai Ina Rokon Wata alfarma Ta Biyu,.Ina So kafin mu Koma Bauchi Atsaida Mana Lokacin Aurenan Nan Da Sati Biyu In Babu Matsala.."Abba yace"Mezai Hana Mallam,? ai Dama Mijin Ake Jira Kuma yazo ai baza'a Tsaya Wasa ba,Yanzu Abunda za"ayi Bari na Kira Makocina Ayi Komai Dashi Duk da Duka Abun na gidane.."Yafada Yana Dariya Farincikinsa yaki Boyuwa.

Waya ya daga ya Kira Baban Aisha Mallam Wada,aka Kuma yi sa'a Yana gidan Jin Bayanin da Abba Yayimai na Maneman Auren Asma'u ne Suka Zo yasa Suna Zaune Da Ammi ya Mike a hanzarce ya saka Takalmi yacemata Yana Zuwa Ya Fice Da Hanzari.

Dayake Gida Dayane Tsakaninsu Cikin Lokaci Sai Gashi Afalon Abba,Nan Suka gaisa Da Mallam din Domin Dama yataba Ganinshi Sanda Ammi Taje Bauchi Wajen Habiba yabiya Ya Daukota,Bai Gama Mamakin Zuwan Mallam din ba Sai da Abba ya karantomai Abunda Ke Tafe Da Mallam din 

Hamdala da Kirari kadai Baban Aisha Yakeyi Acikin Zuciyarsa kafin yasaki Kabbara Lokaci Daya Yana Fadin"Lalle Allah ne Abun Godiya Wato Alhaji Ladan Ina ji ajikina Wannan karon Mijin Asma'u ne na Gaske yazo, Dama wadanchan Duk ba Mazajenta bane Shiyasa Suke Tafiya,Kai Naji Dadi Sosai Allah Ya Tabbatar Da Alheri Kuma Allah yasa Alheri ne Zamu Kullah."Duka Falon Suka Amsa Da Ameeen.

 Mallam yana Mirmishi Jin Dadi yace"Masha Allah,Naji Dadin Haka,yanzu Zamu Bada Sadaki da Kudin Nagani Ina so,Yusuf Fito da Kudin Dake Hannunka.."Yusuf Yayi Saurin Zaro Kudin Dake Aljihunsa Cikin Wata Bakar Leda ya Mikama Mallam, Shikuma ya Karba ya Mikama Abba,Shikuma ya Karba Cike Da Mamaki kafin ya Mikama Baban Aisha.

 Mallam yace"Wannan Kudin Duka Dubu Dari Bakwai ne,.."Gabadaya Abba da Baban Aisha Suka Zaro Ido,Mallam Bai ba mamakinsu Muhimmanci ba Yacigaba Da Cewa"Duba dari biyar Sadakin Asma'u ne, Dubu Dari Biyun Kuma Gaisuwan iyaye.

Kayan Saka Rana Suna Mota,Yusuf Maza ka Fita kayima ko Megadin nan Mgana ya Taimaka maka ashigo Dasu.."Yafada Cike Da Dattako.

Da Hanzari Yusuf ya Mike Yana Fadin"Toh Mallam.."Yafice Da Sauri Abba Da Baban Aisha Suka Kalli Juna kafin Baban Aisha Yace"Ammh Nake ganin Mallam Wannan Kudin Sunyi yawa,Duka fa Abun na Gida ne.."Mallam ya Murmusa Yana Fadin"Karku Damu Wannan Kudin baiyi Yawa ba, Sadaki Yana Daga Cikin Darajan Aure Annabinmu ya Sanar Damu Sadaki Baya Yawa Kuma Baya Kadan,Mganar Kuma Duk Abun Gidane Hakane Asma' u Da Abdallah Duka Dayane awajena Saboda Haka Don Allah banison Kukara Cewa Komai Indai Bana Fatan Alheri bane.."Daga Abba Har Baban Aisha Kasa Mgana Sukayi Farinciki Hade Da Dattako da Karamci Irin Na proff.yagama Kashe Musu jiki.

Basu Fita Daga Cikin Wannan Mamakin ba,su Yusuf da Habu Megadi Suka Fara Shigowa Da Kwalayen minti Sai Da Suka Jera 12 kafin Su Shigo Da Huhunan gora Suma 12 sai kwalayan cingam Suma 12,sai Tabarmu Suma 12 sai Buhun Shinkafa 4 sai Katan din Taliya 4 na macaroni 4 Buhun Semonvita4 Shima,Haka Abba Da Baban Aisha Suka Saki Baki Suna bin Kayan da Kallo Mallam ne ya Katsesu Da Fadin"Ga Kayan Sa Rana Nan,Insha Allahu Nan Da Sati Biyu Zamu Zo Daurin Aure.."Yafada Yana Yar Dariya. Baban Aisha ne Ke Hamdala Kafin yace"Masha Allah Komai Yayi Allah ya Kaimu Da Rai da Lafiya Allah yasa Munada Rabon Gani.." Su Abba Suka Amsa Da Ameen Mallam ne Ya Mika Hannu ya Dauki Fulas din dake Dauke Da Ruwan Lipton Wanda Yaji Citta ya Tsiyaya awani Karamin Kofi ya Kurba Sau Biyu kafin ya Mike Yana Fadin"Masha Allah Toh Mu Zamuyi Harama. Sakamin Nombar Wayarka Alhaji Koda Wani Abu ya Taso.."ya Fada Yana Mika Masa wayarsa,Abba da Baban Aisha Suka Mike Atare Abba ya Karbi Wayar Ya Sakamai Nombarshi Nan da Nan ya Kirashi Shima Yasamu Na Mallam din Musabaha Suka Sakeyi Shida Abba Da Baban Aisha, Har Bakin Mota Suka Rakosu Suna Godiya Shima Mallam Din nayi,Yusuf ya Shiga Mazaunin Direba Mallam ya Bude Bangaren Mai Zaman banza,Har Suka Fice Daga Haraban Gidan Su Abba Na Tsaye Suna Binsu da Addu"an Isa Lafiya.

Baban Aisha ne YaKalli Abba Yana Fadin"Alhaji Ladan kaga Ribar Hakuri ko..? Dama Wani Jinkirin Alheri ne Wlh Banga Yaron Da Asma'u Da Zata Aura ba Ammh Dattakon Mahaifinshi Kadai Ya Isa Ka Fahimci Lalle Asma'u Ta Dace Sai Fatan Allah ya Sa Alheri Acikin Al"amarin..".

Abba ya saki Ajiyar Zuciya Yana Fadin"Hakane Wlh Mallam Wada. Hakika Allah ne Kadai Yasan Abunda ya Boye Game Da lamarin Ma'u Nima Naji Hankalina ya Kwanta Da Wannan Auren Fiye Da Wad'anda Suka Nemeta Abaya..Allah Ne Abun Godiya."

 Baban Aisha Yace'"Hakane. Ni Zan Shiga Gida ga Wannan Kudin.."Abba ya girgiza Kai kafin yace"A'a Ka Rikesu A hanunka Ba Kudina Bane Sadakin Asma'u ne, Zan Damkamata Kayanta Insha Allahu Yanzu Dai Ka Rike Hannunka Tukunnah.."Mallam Wada Baiyi Gardama Ba Sukayi Sallama Da Abba ya Tafi Da Kudi Gida Cike Da Fara'a Yana Zuwa Ko Zama baiyi Ba Ya Damkama Ammi Kudi Yana Sanar Da It's Sadakin Yarta Ma'u ne.

Ganin Tashiga Rudu yasa ya Zauna ya Warware Mata Komai,Ai Ammi batasan Sadda Ta Rike Hanci Tana Sakin Guda ba Bakinta yaki Rufuwa Saboda Murna Mallam Wada Kallonta Yake Yana Girgiza Kai Domin Babu Shakka Duk Wani Masoyin Asma'u In yaji Wannan Lbrin Sai Ya Tayata Murna.

A gidan Abba Kuwa Cikin Gida Ya Wuce Daganan Tun Atsakar Gidan Yake Kwalama Umma Da Anty Amarya Kira Da Mama.

Shiyasa kafin ya Kariso Kowacce Ta Fito Harda Hajiya Iya Tana Tambayan Ko Lafiya,..?Kallon Umma Yayi Yana Fadin"Ina Asma'u..? Yau banganta Tazomin Sallama Zata Wuce Wajen Aiki ba.."?


in Abunda yace ne,Yasa Hajiya Iya Taja Tsaki Kafin Tace"Au Dama Saboda Haka kake ta Kwalama Mutane Kira Ladan..? Kai ya Girgiza kafin yace"Bashi bane Iya Ammh Tana da alaqa da Kiran Danike Muku.." Da Mamaki Suka Bishi Da Kallo Kafin Suyi Mgana Anty Amarya Tace"Bata Je Asibiti ba Yau Tana Daki kwance Tun Jiya Batajin Dadi.."Abba yace"Ashh Shine Bansani ba..? Meke Damunta..? Anty Amarya Tace"Zazzabi ne,Ammh Dazu na Lekata na Mtsamata Ta Karya Tasha magani Har Tasamu Barci.."

Jnjina Kai Abba Yayi Kafin ya Saki Ajiyar Zuciya Yana Fadin"Allah ya Bata Lafiya. Dama Abunda Nakeson Shaida Muku Dazun Bakin Da Sukazo Wajena,Toh Manema Auren Asma'u ne Atakaice Dai Sunzo Nema Kuma Na Basu Kuma sun Nemi alfarma Asanya Musu Ranar Aure Nan Da Sati Biyu, Na Amince Kafin Dai Su Tafi Har Sun Biya Kudin Sadaki Dubu Dari biyar Kudin Gaisuwan iyaye Dubu Dari Biyu,ga Kuma Kayan Saka Rana Chan Acikin Falona.."

Tunda Abba Yafara Mgana Umma Da Hajiya iya Ke Binsa Da Kallo,Tunda ya Ambaci Manema Auren Asma"u Hankalinsu ya Tashi Umma Bata Razana ba Sai Da Abba ya Ambaci Uban Dukiyar Wai Da Sunan Sadakin Asma"u Ido Ta Kwalalo Waje Tana Fadin"Dubu Dari biyar..? Ita Asma"un aka Kawo Mawa..? Abba ya Kalleta Da Mamaki Kafin yace"Eh Dubu Dari Biyu Kuma Kudin gaisuwar iyaye.."

Ai Sai Ummah Ta Dafe Bango Saboda jirin Dake Neman Kadata Ita,Hajiya iya Kuwa Sototo Tayi Tana Raba Ido, Mama cE Tace"Masha Allah. Allah Sanya Alheri.."Tafada Fuskarta Bata bayyana Halin Datake Ciki ba.

Anty Amarya Ko Juyi Ta Saki Hannunta Rike Da Hanci ta Saki Guda Mai Kara"Ayyiriri...Ayyiriri..Ayyirri...Rana Bata Karya Sai Dai Uwar Diya Taji Kunya,Kai Masha Allah Asma'ul Husna Tayi Goshi.."Take Fada Tana Juyi Cike Da Farinciki.

Hajiya iya ce Ta Shanye Mamakinta Tana Fadin"Ikon Allah Shikuma A Ina Yake Wannan yaron Daga Zuwa Sai Saka Rana ba Wanda Yataba Jin Lbrinsa "Abba yace"Ba bako bane Yaron Wajen Inda Mamanta Ke Aure Ne,mahaifin sa yace yaron Babban ma'aikacin Costom ne yana Porthercourt Yana Aiki Chan Yake Zaune Shida Matarsa..."Ai Umma sai Taji Wani Gudawa Na kartamata a Ciki.

Hajiya iya Tace"Topha.."Tafad'a Tana Wani Mele Baki,Hanyar Dakinsa Abba yayi Yana Fadin"Iya kuzo kuga Kayan Sa ranar Wlh Nama kasa Mgana.."Yafada Yana yin Gaba,Da Sauri Hajiya iya tabi bayanshi Ita Da Mama kowa Na Saurin Zuwa Ganinan ma idonta Itako Anty Amarya Ta Tsaya Bama Su Baba lami Kanu Wad'anda Suka Fito Saboda Jin Gud'anta.

Ai Hassatu Naji itama Ta Saki Gud'a Wanda yakara Saka Umma Jin Kashi na Kamata, Baba Lami ko Hamdala Take Saki Tana Nuna Murnanta, Anty Amarya na Dariya Ta Kalli Umma Tana Fadin"Umma bazaki Ganin Kayan Arzikin bane.."Umma na Dariyan Yake Tace"Zani Cikina ne Naji ya karta Muje.."Anty Amarya na Kanne Dariyanta Tayi Gaba tana Shewa Tabar Hassatu Na Juyi a Tsakar Gida,Umma ko Bin Bayan Anty Amarya Take Ammh Bata Cikin Hayyacinta Dubu Darin Bakwai Din da'aka ce an Kawo Da Sunan Asma'u Kad'ai Take Nanatawa Tana Tunanin kaf ya'yanta Ba Wacce Aka Taba biyama Sadaki Sama Da Dubu Dari. Kai kaf Gidan ma ,Ammh Yau Asma'u ce A kawo ma Wannan Uban Dukiyan...tabdijam.








*Janafty*