ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 16

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



     *🅿️16*


Koda Su Anty Amarya Suka isa Tsakiyar Falon Abba Sun Iske Mama Da Hajiya Iya Tsaye Suna Bin Kayan Da Kallo Abba Na Gefe.

Baki Hajiya Iya Takama Tana Fadin"Wai Ladan Ko bakaji Dakyau bane, Wannan Kayan Duk na Asma'u ne."?

Ɗan Mirmishi Yayi Kafin yace"Tabbas Iya, Sadakin na Wajen Mallam Wada nace Ya Ijiye Awajensa Tukunnah, Dayake Lokacin Da Shi Mahaifin yaron ya Bukaci Sanya Lokacin Bikin Sai na Kirashi Awaya Sai Gashi ya Kariso.."

Anty Amarya ce ke Zagayen Kayan Tana Kara Sakin Gud'a Hajiya Iya ta Dago Tana Kallonta Cikin Takaichi Tace"Wlh In Kika Sake ma mutane Wannan Sakarci Zaki Fita Halima, Haba Kinbi Kin Damu Mutane Hala Asma'u ce Farkon Aurarwa Agidan nan..? Tafada Cike Da Zafin Rai Da Bakinciki.

Jin Haka yasa Anty Amarya Rufe Bakinta Tana Fadin"Allah Baki Hakuri Hajiya, Ba Yau Aka Fara Aurarwa ba. Ammh ni Wannan Shine Na Farko awajena Don Asma'u Tamkar ɗ'iyata nake Kallonta.."Tsaki Hajiya Iya taja Takaichin na cinta, Umma Tabi Da Kallo Wacce Ke Gefe Tana Bin Tulin Kayan Da'akace Na Saka Ranar Asma'u ne da Kallo Bakinciki kamar ta sakama Kayan Wuta Haka Takeji.

Mama Kuwa Tana Tsaye Ita kad'ai Tace"Allah ya Sanya Alheri.."Babu Wanda ya gane Abunda Ke Zuciyarta Hajiya iya ce Ta kalli Abba Tana Fadin"Anya Ladan Abunda ka yi ka kyauta kuwa..? Abba yace"Me Nayi Kuma iya..?

Tacigaba Da Fad'in"Toh na Wannan Uban Kayan Daka Karba, kana ganin bazamu Zama Abun Zund'e ba a fara yawo Damu Agari ace ka Saida Asma'u Kuna Ranar Aure Sati Biyu kamar Wata Kaza, Karka Manta Akwai Fa Shirye Shiryen fa Daza'a gudanar Sai nake Ganin kamar Lokacin Yayi Kusa.."Tafad'a Tana Kallonsa.

ɗan Mirmishi Yayi Kafin yace"Ko Daya iya, Karki Manta Itama Asma'u Tamkar ya Take Agaresu, Da Farko na Fara mgananar Kayan Sunyi yawa Sai Ya Rufemin Baki Da Fad'in Daga Yaron Wajen Nashi Har ma'u Duka ƴa'ƴansane So bayason Wani Korafi Zai Mata Abunda Yafi Hakama.."Jin Haka yasa Bakin Hajiya iya ya Mutu Anty Amarya Tace"Gaskiya ne Kam..Duka Nashi ne.."

 Bakin Ciki ya Kusa Kashe Umma Ta Juya Ta Fice Daga Falon Cikinta na Juyawa ,Dakinta Ta Shige ta fad'a Tiolet Da Gudu Saboda Yadda Taji kamar Gudawar Ta Fara Zubomata.

Abba ne yacema Hajiya iya" Iya ko Za'a Kai Kayan Nan Ɗakinki ne.."Da Hanzari Tace"A'a barsu Anan.."Daga Haka Itama Ta Juya Ta Fice.

Abba ya Bisu Da Kallon Mamaki,karshenta Mama ne da Anty Amarya Suka Kama Kayan Da suka Shiga Dashi ɗayan Bedroom din Dake Shashen Abba.

Asma'u Ko Tana kwance Tana Barci Saboda Mganin Datasha Kamar Amafarki Takejin hayaniyar Su Baba lami kamar Harda Muryan Anty Amarya, Mikewa Tayi Tana Salati Lokaci Daya Taji zazzabin Dake Jikinta ya Sauka Hakama Ciwon Kan Nata,Saukowa Tayi Daga Kan Katifarta Ta Shiga Tiolet Tayi Wanka Tana Fitowa Ko Mai Bata Shafa ba Ta Zura Dogowar Rigarta Baka,Ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallar Azahar Domin Ta Duba Agogon Wayarta 1:30pm na Rana 

Ta idar Da Sallan Kenan Sai ga Anty Amarya Ta Turo Kofar ɗakin Ta Shigo Ganinta Zaune ne yasa Ta Washe Baki Tana Fadin"A'a Amaryar Sati biyu kin Tashi..? Ya karfin Jikin naki Yanzu..? Mikewa Tayi Tana Kokarin Cire Hijabin Jikinta ba bama Mganar Anty Amarya Ta Farko Muhimmancin ba Shiyasa Tace"Da Sauki Anty Wlh Koda Nashi Naji Ni Sakayau.."Dariya Anty Amarya Ta Saka Tana karisawa Gareta Tana Fadin"Masha Allah Dama, Zazzabin Na Barin gidane ma'u Allah ya Amshi Addu'armu Ina Miki Murna Nan Da Sati Biyu Kinzama Amarya.."

Kuri Tayima Anty Amarya Da Ido Kafin Tace"Amarya Kuma Anty..,? Bangane Mganar ki ba.."?Tafad'a Cike Da Mamaki ,batasan Dalili ba Sai Dai Taji gabanta Na Fad'i Lokaci Daya Kuma Jikinta Ya fara yin Sanyi..."Baki Anty Amarya Tarike Kafin Tace"Ikon Allah, Kodai bakisan Meke Faruwa bane..?

Asma'u Tace"Meya Faru Anty Amarya Wlh Bansani ba..? Tafada Idanuwanta Na Fitowa Saboda Tsoro.

Kafad'unta Anty Amarya Ta Dafa kafin Tace"Kwantar Da Hankalinki Abun Alheri Ne ya Sameki Damu Gabadaya. Kuma Nayi Farincikin Jin Nice Ta Farkon Wacce Zan Sanar Dake Wannan Lbrin,Dazu Nan Mijin Mamarki Suka bar Nan Gidan.."Ido Asma'u Ta sakar mata Kafin tace"Mallam..? Anty Amarya Tace"Eh Mganar Bata da Yawa Atakaice yazo Mganar Nema ma ɗa'nsa Aurenki ne, Kuma har Babanki ya bashi Har An saka Rana Sati biyu, sun bada Sadaki Dubu Dari biyar Kudin gaisuwar iyaye Dubu dari biyu ga Kuma Uban Kayan Arziki Wai Kayan Saka Rana.

Gaskiya Asma'u kin yi Goshi Domin Naji ajikina Wannan Karon Allah ya Karbi Addu'anmu Zaki Zama Amarya.."


Wani Dum!Taji Jikinta Na Rawa Ta Sauke Hannayen Anty Amarya Daga Kafad'arta Taja Baya Bakinta na Rawa Tace"ɗansa K.ku...ma..? Ta Fada Zuciyarta Na Tsinkewa Tana So Takama Sunan Ammh Bakinta Yayi Nauyi Anty Amarya Ta Bita Da Kallo Kafin Tace"Eh Wai Ko Wanda Ke Aiki A Porthercourt ne kamar Dai Haka Naji..."Da Sauri Asma'u Ta Dafe Baki Tace"Ya Baffa...,? Tafad'a Da Alamun Tambaya Hade Dana Ficewar Hankali.

Dariya Anty Amarya Ta Saka Kafin Tace"Kaji min Ja'ira Ashema Kin sanshi Toh Inaga Shine.."Ai Ma'u batasaan Sadda Ta Dora Hannu Akai ba Zuciyarta Na Gudu,Ya Baffa ne wlh Shine Domin Gidaan Proff ba Wani ɗa Bayan Baffa.

Toh Shine yace Yana Sonta Ko kuwa. ? Ina Wannan Mai Jinkan Da Isa Da Wulakanci bazai Taba Cewa Yana Sonta ba.! Kuma Wai Har an Saka Rana..? Ya Zatayi Da Rayuwarta Kullum Addu'arta Allah ya Bata Miji Na Gari Wanda Zata je Taji Dadi.

ammh Sai Gashi Lokaci D'aya Wani Baffa yaShigo Rayuwarta Wanda Take Samun Lbrinshi Wajen Yan'uwansa Yadda Matarsa Ta mallakeshi Baya ganin Kowa Sai Ita, Toh Ita Yanzu In Ta Aureshi Menene Makomarta Duk da Ta Tabbata shikanshi Baffa Baisan da Wannan Mganar ba Aikin Mallam ne Da Hajiya.

Duk Surutan Da Anty Amarya ke yi Asma'u bata jinta Harta gama Ta Fice.

Kan Katifarta Asma'u Ta Sulale Tana Jin Wani Al"amari Shiba na Farinciki ba, Kuma bana Bakinciki Ba Tarasa Gane Kanta,ayadda Take neman Miji ido Rufe Bata Dauka Zataji Wannan Lbrin Ta gagara yin Farinciki ba.

Tana ganin Su Mallam Sunyi gaggawa Domin Baffa ba Ajinta bane,Bata Taba Kawo ma Kanta Miji Irin Baffa ba ,saboda ba Irin Kalarta bane, Kwantawa Tayi Kan Katifan Tana Kurama Silin ɗin ɗ'akin Ido Gefe na Zuciyarta Na Na nata Sati biyu..? Runtse Idonta Tayi Tana ji Kamar ba Ita ba,Tarasa Gane Wani yanayi Take Ciki, Hawaye me Suka taru Acikin Idanuwanta Har Suka Zubo,Tarasa Kukan me Take na Bakinciki ko na Farinciki Itama Zatayi Aure Kokuwa Tana Ji Azuciyarta Duk Abun ɗayane Irin na Bayane Shima Haka Zai Tafi ya Barta Da Katon Tabo,Shima ya Shiga Jerin Lissafinta.


******


A Bauchi Kuwa Haka Su Mallam Suka Koma Da Daɗaɗɗan Lbri Mai Dadi.

Hajiya Bakinta yaki Rufuwa Ta gagara Boye Muryanta,Maman Fati Kuwa Abun yazomata Haka Kwatsam Bata Zata Baban Ma'u zai Yarda Lokaci Daya Ba ,Duk Da Tayi Murna ammh Sai Bata Bayyana Murnanta Saboda kawaicin Datake Game Da Asma'u Ammh Ta Kudiri Niyyar Kiran Asma'un in Ta Shiga Daki Saboda Kada Taji Lbrin Daga Sama.


Hajiya Ko Jikinta Na Rawa Ta Kira Su Anty Safina Tana Labarta Musu,Haka Sukaji Mganar Daga Sama Anty Safina Ta Saki Ihu Lokaci Daya Tana Fadin"Hajiya Ma'u fa Kikace..? Wow Wlh Hajiya Na Yarda Kinfi Kowa Sanin Abunda Ya Dace Da Yaya Baffa..."Take Fad'a Tana Dariya Itako Anty Nafisa Ihu Ta saka Bayan Ta Buga tsalle Tace"Wlh Hajiya Kun iya Tsari Ma'u Ta Dace Da Rayuwar Yaya Baffa 100% wlh Kuma Wannan Karon Ne Zamu Nuna ma Duniya Yaya Baffa Yayi Aure Don Wlh Hajiya Biki Zamu yi na Bugawa A Mujallah.."Tafad'a Tana Dariya,Hajiya ko Tace"Kwarai Da Gaske Hajiya Nafi.."Haka Suka Kasance Cikin Farinciki Da Lbrin Da Hajiya ta Basu.

Yusuf ko Sai Washegari ya Koma Kaduna Bayan Sun gama Mgana Da Mallam akan Shi Zai Kira Abdallah awaya yace yazo Yana Son Ganinshi Allah barshi Sai ya Sanar Dashi, kowa ya yarda Da Hukuncin Mallam Ko Banza za'ayi Komai Cikin Lokaci Batare Da Sanin Wasila ba,balle Ta Bada Gudummuwar Lalata Komai.

Shima Haka Yaga Murna Wajen Zainab Sanda yake Bata Lbrin Abunda Ke Faruwa,Duk da Baitaba ganin Asma'u ba Ammh yadda ƴan'uwan Baffa Da Iyayen Baffa Ke Murna game da Haɗin yasa Aranshi Cewa Tabbas Asma'un Ta Had'u Ta Kowani Fanni Shima Murna yake, Yana Fatan Abdallah Shima yazama mutum kamar Kowani Namiji.

Ammi Kuwa Da Kanta Da Kira Maman Fati Tana Murna Da Farinciki, Maman Fati Mirmishi Kadai Take Saboda Jin Zuciyarta Na Mata Sanyi kafin Sugama Waya Sai Da Maman Fati Ta Roki Ammi Kan Taje ta Duba Mata Asma'un Ta Kirata Bata Daga ba, Da Toh Ammi Ta amsa Kafin Su yanke Kiran,Bata Tsaya Wasa Ba Ta dokama Aisha Kira,Lokacin Da Aisha Kejin Lbrin Abunda Ya samu Rabin Ranta Tana zaune gefen cinyar Fahad ammah Sai Gashi ta Diro Daga Kanshi Ta gurfana Kanta Akasa Bayan Ta Kalli gabas, Ta Dade Cikin Sujjudan Tana Kwararoma Allah Kirari Kafin Ta Dago Fuskarta Yayi Shabe da Shabe Da Kukan Farinciki Harda Majina,ita Dai Ammi Tunda Taji Shuru Ta yanke Kiran Tasan Murna ne ya Hana Aisha Mgana.

Fahad ne Ya Rud'e ganin Aisha Na Kuka, Ya Tarairayota Yana Tambayanta Ko lafiya?

Fadawa Tayi Jikinshi Tana Sakin Kukanta, Amir Dake Gefe Ganin Momynshi na Kuka,Shima Sai ya Rugo ya Fad'a Jikinta yasaki Kuka.

hankalin Fahad atashe ya Dagota Yana Tambayanta,Tana Matse Kwallah Take Sanar Dashi Lbrin da Ammi Ta Bata, Shima Farincikin ne ya cikashi Haka ya Dagata cak yana juyi Da Ita Acikin Falon,Dariya Take Tana Hawaye Lokaci Daya, Amir Shima Yana Tayata Dariyan.

Ai Ba Bata Lokaci Aisha Ta Matsama Fahad su Ka Shiryo suka Nufo gidansu Asma'u Motar Fahad ko Gama Tsayawa Batayi ba akofar gidansu su Asma'u ba ta Bude Murfin Mota ta Kwashi Gudu Ta Shige Gidan aguje Kamar Wacce aka Cemata Anyi Mutuwa.

Tundaga Tsakar Gidan Take Kwalama Asma'un Kiran Wacce Ke Cikin Dakinta Ammi Tazo Suna Mgana Taji muryan Aishan Da Gudu Ta Fito Suka Tarbi Juna Daga Waje suka Kamkame Juna Jinta Ajikin Aisha yasata Ta Saki Kukanta Wanda Take Makaleshi Bayanta Aisha Ta Shiga Bugawa kafin Taja Hannunta Su Fada Dakinta Don Taga Su Hajiya Umma a Tsakar Gida Sun Zubo Musu Ido.

Gefen Katifarta Ta Zaunar Da Ita Tana Dariya Take Gaida Ammi Sai Lokacin Amir ya Shigo Da Gudu.

Asma'u Ya Rumgume yana Gaisheta Rikosa Tayi Tana Amsawa Kan Cinyarta Ta Zaunar Dashi,Shikuma ya Sanya hannu Yana Share Mata Hawaye Yana Fadin"Mommyna Kibar Kuka, Kinga Mami Tun Agida Take Ta Kuka.."Mirmishi Asma'u Tayi Kafin Tace"Nabari My son Kaji.."


Aisha ce Ta Dakamata Duka Kafin Tace"Ke Rabin Raina. Innalillahi A Ina Kuka Hadu? Ammi Tacemin Yaron Hajiya ne,Wannan Zuwan Naki Ne Kuka Hadu Da Juna? Allah Mun Gode Maka, Kai Rabin Raina Za'ayi Burauba Wlh Sai Munyi Biki Wanda Ba'a Taba yi ba Na Rantse.."Tafad'a Tana Dariya Ammi cE Tatashi Ta Fice tana Dariyan Aishan.

sai Da Ta Fita Kana Amir ya Tashi Daga Kan Cinyar Aisha ya Bita Waje Da Gudu,Kallonta Asma'u Tayi Kafin Tace"Nifa Rabin Raina Yadda kikaji Mganarnan Daga Sama Haka Najita, Nifa Bamu Taba Mgana Dashi ba,sai gaisuwa Itama din ba Kodayaushe ba,Wannan gayen Mugun Dan jinkai ne,yadda Kikasan ba Hajiya Da Mallam Suka Haifeshi ba."Dariya Aisha Ta Saka Kafin Tace"Da Gaske Rabin Raina,Na Fara Fahimta Kin Fara Sonshi Dama Tuni Karki Damu Wannan Karon Insha Allahu Sai Anshafa Fatiha kina Da Hotonshi Don Allah."

Harara Asma'u Ta Makama Aisha Kafin Ta Mike Tana Fadin"Eh Ina dashi .."Tafada Tana Fadawa Tiolet Lokaci Daya Tana Fadin"Zanyi Wanka.."Kai Aisha ta Dagamata Tana Dariya, Wayar Aisha Ta Dauka Dake Kan Katifarta Nan Taga Missed clls din Hajiya Harda Maman Fati,Tana Cikin Duba Wayar Sai ga Kiran Maman Fati, Dauka tayi Suka Gaisa Kafin Tace Asma'un Tana Bayi.

Maman Fati Ce Tace"Aisha Sai Kukaji Lbri Daga Sama.."Mirmishi Aisha Ta Saki Kafin Tace"Umh Bari Mama Nayi Murna sosai Kingannin Tunda Ammi Ta Sanar Dani Banzauna ba Sai Da Nazo,"Maman Fati Tace"Nima Haka Naji Zencen Daga Sama,Sai da Hajiya da Mallam suka Gama Shirya Komai kana Suka Sanar Dani, ki Kara Bama Asma'u Hakuri ki Koma Shawartaceta data Kara Dagewa Da Addu'a In Abdallah Mijinta ne,In kuma Ba Mijinta bane Zata Ga Komai Ya Warware Ammh Ina mata Fatan Wannan Karon Karshen Wahalarta Kenan.

Da Ameen Aisha Ta Amsa Daidai Lokacin Da Asma'u Ta Fito Wanka Daure Da Zani Fuskarta Na Fitar Da Digon Ruwa,Wayar Aisha Ta Mikamata Tana Fadin"Ga Mama.."Karba Tayi Suka gaisa Kafin Mama Ta Fara Mata Nasiha Sosai.

Lokaci Daya Jikin Asma'u Yayi Sanyi Tana Fatan Allah yasa Wannan Karon Ta Samu Ta Auri Saboda gushar Da Damuwa Daga Fuskokin Masoyanta mussaman ma Mahaifiyarta Wanda akalaamanta Suna Cike Da Damuwa.

Koda Suka yanke Kiran Ka Shirban Asma'u ke Kuka Tana Tunanin Itako Aduniyarnan Batason Wani So Hajiya Da Mallam suke Mata Da Har Sukayi Tunanin Had'ata Aure Da ɗ'a mafi Soyuwa Agaresu ba.

 Lalle Bata Da Kalmar Da Zata Gode Musu Sai Dai Tayi Fatan Allah ya sakamusu Da Alheri Ita Kuma Allah yabata Ikon Yima Mijinta Biyayyah Da Kuma Kyautata Musu.

Kokafin Zuwa Dare Hajiya Da Ya'yanta ba Wanda Bai Kira Asma'u Yana Murna ba, Hajiya Ko Tambayi Asma'u Tayi da Cewa Ta Amince Da Wannan Zabin..,? Ita Wacece Da Za tace Bata Son Baffa..? Ita da'aka Taimakamawa..? Hajiya Ta Tabbatartama Da In Bata So Wlh Za'a bar Mganar Saurin katse Hajiya Tayi Inda Ta Nuna Amicewarta Murnan Hajiya ya Kasa Boyuwa Godiya Taketa zubama Asma'u kamar Tayi Mata Kwallah, Haka Anty Safina data kira Guda ta Sakarmata Akunni Tana Dariya.

Taji Ta Wani Irin ganin Yadda Yan'uwan Baffa da iyayensa Suke Nuna Mata Kauna, Wata Zuciyar Tace"Ba wannan bane Abun Jin Dadi Asma'u Shi Uban gayyar In Bai amsheki ba Ai kina Cikin Mtsala.."Wannan Tunanin Shi ya Ragemata Farincikinta.

Sai Wajen 10pm na Dare Kana Aisha Tatafi har Kofar Gida Asma'u Ta Fita Ta Raka Aishan Suka Gaisa Da Fahad Shima ya Tayata Murna yana tsokanarta Da Amarya.

Dariya Kadai Takeyi Batayi Mgana ba Aisha Ke Biyemai Suna Tsokanarta, Bayan Sun Tafi ne Ta Shigo Cikin Gida Nan Sukaci karo Da Abba Kiranta Yayi Suka Shiga Falonshi,Shima Nasihar Yayi Mata Kafin ya gangara Ga bayanin Abunda ya Wakana,yakuma ce Ta Shiga Ciki Taga Kayan Saka Ranarta A Kunyace Ta Mike Ta Shiga Tagani Bakinta bude Takebin Uban Kayan Da Kallo,Bama Wannan ba Uban Kudin Da'a ka Kira Da Sunan Sadakinta da Dukiyar Aure Shiyafi Razanata,Abba Yakara Mata Sosai Kuma Ya horeta Datayi Hakuri Da Gaggawan Da yayi mata,Dama Babban Burinshi Daya Rage mishi Yaga Yau ya aurar Da Ita,Kuma Yana ji ajikinsa Wannan Karon Sai Ya Aurar Da Ita,Cikin Zuciyarta Sai Da Ta Amsa Da Allah yasa.

Ko Kafin Gari ya Waye Lbrin ya samu ƴaƴan Umma Da ƴaƴan Mama, Fa'iza ce Kadai Dataji Tayi Murna Sosai Da Sassafe Sai Gashi Tazo Karo Sukaci Da Asma'un awaje Ta Shirya Zata Wuce Asibiti Nan Fa'izan Ta Rumgumeta tana Tayata Murna Sosai Asma'u Taji Dadi Har Sai da Ta bayyana Haka afuskarta,Wanda Daga Hajiya iya har Umma da Mama Ba Wacce Tace Mata Kanzil sai ma Wani Kallo Da Suke Binta Dashi Tun Jiya.

Ko Dayake Har gwara Mama Bata Ganta Tun Jiya ba.

Anty Amarya ce Kadai Ta Nuna Murnanta na Badini Dana zahirin, Su Anty Rukayyah Da Anty Bilki Da Sukaji Lbri kamar Suyi Bindiga Saboda Bakinciki Haka Suka Baje Afalon Umma Suna Nuna kyashi Suna Fadin Kaf gidan nan Ba Wacce Ta Samu Abunda Asma'u ta Samu.






*Janafty*