ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 17
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️17*
Kwana Uku da Saka Ranar Auren Asma'u da Baffa Mallam ya Kira shi a waya Ranar yana Office Cikin girmamawa, suka gaisa nan Mallam ya Sanar Da Baffa Cewa Gobe in Allah ya Kaimu yazo yana son Ganinshi. Baffa Yaji mamaki Ammh kuma yakasa tambayan Mallam d'in ko lafiya..? Sai ma Cewar Da yayi Insha Allahu Gobe yana Tafe.
Mallam yaji Dadin hakan nan Suka Datse kiran zuciyar Abdallah Na Tunanin to Meya Faru wannan kiran Gaggawan haka.? Ganin Baida amsane yasa ya Watsar da maganar Ya cigaba da Harkokinshi.
Koda ya Tashi daga office Gidan Polina ya yada Zango sai bayan Sungama tambalewansu kana Da zai Tafi yake Sanar da ita gobe In Allah ya yarda Zashi bauchi.
Tayi mamaki Sosai Har Saida ta tambayeshi ko lafiya? yace Mata baisani ba Mallam ke Nemansa,bata Nuna Rashin Jin Dadinta ba, illah kamkamesa Da tayi tana bayyana mai yadda Zatayi kewarshi gobe.
Lallashinta ya hau yi yana Fad'amata Karta damu Kwana Daya Zaiyi ya Dawo ba Dadewa Zaiyi ba, Da haka Ta Rakoshi har bakin Mota.
kafin ya Tada Motarshi ya Fice Daga Haraban Gidan Tana Dagamai Hannu Cike da Kewa Da Kuma Soyayyah Mai Tsanani.
Bai Kariso gida ba Sai Da Ya Tsaya ya Sallaci sallar Isha'i a wani ƙaramin masallaci dake cikin unguwarsu Dake babu Musulmai Dayawa, shima masallacin Musulmai ne ma'aikata Dake Zaune a unguwar Suka Kirkireshi dole bai shigo gidan ba sai around 10pm na Dare.
Ranar da Kanshi ya Tuka kanshi Zuwa Office sakamakon Emeka bayanan ya Tafi Binne gawan kakarshi tada Mutu A Delta.
A falo yaci Karo Da Jamila Da Hafsat sunci Uban kwalliya cikin kananun kaya,Kowacce Surar Jikinta ta bayyana a waje.
Wasila ce tsaye Tana Musu magana Tana Mika musu Kudi lokaci Daya, Koda yaShigo kallo d'aya yayi, musu ya Kauda kanshi,yafara Haura Steps d'in bene.
Wasila ce Tayi Saurin mika musu Key din Mota da Kudin Hannunta kafin tace"Ku dawo gida gobe da Wuri ok.."Kai Suka gyad'a Mata kai Kafin Ta juya Ta Fara Taka Steps Din Benen Zuwa Master bedroom Dinsu Acikin Ranta Tana Kirga kwanakin Da Boka yabasu, Zatayi maganin Abdallah Domin Talura kwana biyun nan Har Wani Sha mata kamshi yakeyi.
Tana Shiga bedroom din Taganshi yana Saka Kayanshi Cikin wata Karamar jakarsa cike Da Kissa ta Nufeshi Ta Rungume shi Ta baya Tana Fadin"Sannu da Zuwa my Dee."
Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Yauwa Noory ya gida..? rausayar dakai tayi Bakinta ta Saka Daidai Kunninshi Kafin tace"Gida ba Dadi Dee, Ban san meyasa ba Yanzu baka zama gida sosai, bansani ba ko Nine ce Nayi Maka Wani laifi..?"Tafad'a Tana Wani Narkemai ajiki.
Ajiyar Zuciya ya saki kafin ya Zage Jakar dake hannunsa ya Waigo yana Rike duka Kafadunta yace"No Ba Haka bane, Aiki ne yamin yawa a office ammh Nikam Babu Abunda Kikamin gaskiya.."Yafad'a yana Sakinta Kafin ya karisa gefen makeken gadon nasu ya Zauna Kallonsa tayi Kafin tace"Wai Dee Ina zakane Naga Kana Had'a Kaya..?
Bai Kalleta ba Ya Haye gadon yana Lullube ƙafarsa da Wani blanket din dake gefen gadon.
sai da ya kai kansa Bisa Filo kana yace"Bauchi Zani. Ammh bazan dad'e ba juz kwana Ɗaya zanyi, Next tomorrow Insha Allahu Zan dawo."Daga Haka ya Rufe idanuwansa yana Karanto addu'ar Barci, Sai da ya Sha fama Duka jikinsa kafin ya Saka Hannu ya Latse Wutar Dake barayinsa.
sai ga Dumlight yakawo mai Kalar duhu, Wasila dake Tsaye Tunda ya ambaci Zashi Bauchi Taji Zuciyarta ta Tsaya kyam Tadaina aiki na Wani Lokaci mai Tsawo.
Gabanta Fad'i yake, Tana so ta Kurma ihu aAmmh kuma Sai Ta Rufe bakinta da Hannuwanta,Taja kafafunta ta Fice Daga bedroom Zuwa Falon Kasa.
Ranta gaba-daya baya mata Daɗi, Kan kujera Ta Fad'a Tana Dafe kanta Lokaci Daya Take Nanata Bauchi acikin Ranta,Wasu Zafafan Hawaye ne Suka Zubomata Saboda yadda Zuciyarta ke Tafasa.
wayarta Ta Jawo Ta Shiga kiran Momcy Ammh Abun Haushi Harta mata ƙira wajen goma ammh bata Ɗagaba ba Ran wasila ƴaƙara ɓaci kamar tayi bindiga saboda bakinciki.
Reras ta kwanta tana kuka kamar wata zararriya, banda zagin iyayen Abdallah da ɗura musu zagi Babu Abunda wasila keyi, gashi Momyc taki daukan wayanta gasu Jamila basunan sun Tafi party sai da safe zasu dawo.
bata da wanda zata kira ta Fad'amawa taji dadi,nan ta sulale kan cafet din Daya Malale Tsaƙar Falon gaɓaɗaƴa Saboda bala'i batasan Sadda Barci ya ƙwasheta ba,sai da Asuba Dataji Abdallah Na Tada ita Lokacin ya dauro alwala yana Shirin Fita Zuwa masallaci.
domin ƴanzu Abdallah baya wasa da ibada Tun bayan Dawowarshi Daga bauchi komai ya chanza Daga Rayuwar Abdallah don yanzu yadaina Sakaci da Ibada sosai yaji mganar Hajiya da Mallam.
Koda ta tashi ya Riga ya Fice Zuwa masallaci Cike da wani karin Takaichin data kwana Tashi Ta saki kuka mai cin rai Harda bubbuga kafa kamar wata yarinya,ganin babu mafita ne yasa ta Mike Ta Haura Zuwa bedroom dinsu Fuskarta duK a kumbure.
Saboda kukan Datasha kamar ba gobe,Ko data Shiga Dakin sai Da takara gwada Nombar momcy Still dai No Answer kan gado tafad'a tana sakin kuka ko tamayi Tunanin tashi tayi sallah batayi ba,tananan kwance Har Abdallah ya Dawo Daga masallaci, ganinta kwance sai bai Mata mgana ba yana Zaton bayan ta idar da sallah ne Takoma ta Kwanta.
Tiolet ya Shiga yayi wanka agurguje domin jirgin karfe 7:30am zaibi Zuwa Bauchi har ya Fito yazo yana Shirinsa cikin American Suit masu Ruwan Toka ya matse Wuyansa Da Tie,dinsa Jikinsa na Tashin kamshin Turarensa gurin ma'ajiyar Takalmansa ya Nufa yaja Wani Rufaffe Baki na Fata mai kyau ya saka Ta Gefen ido yake kallon wasila wacce ta Kura masa ido tana Tsiyayan Hawaye.
Cike da Mamaki ya Mike yana Kallonta Lokaci Daya yace"Noory wht wrong wit u Naga kina Kuka..? Jin Abunda yacene yasa Ta Saki Kukan Da Tundama Tana Yinshi acikin Ranta, ganin haka yasa ya Karisa gareta Daga kan gadon ya Rikota jinta ahannunsa yasa Tafadamai Tana Fashewa Da Kuka Shikuma ya Rumgumeta yana bubbaga bayanta alamun Lallashi.
Cikin kuka Wasila ke Fadin"'Why My Dee? menayi maka ka chanzamin kwatakwata yanzu baka kaunar zama kusa dani..? Baka son Hira dani..? Baka san kallona..? Uwa uba Kuma yanzu baka Kaunar Had'a Shimfida dani kadaina Damuwa Da Abunda ya Dameni ba Ruwanka Dani yanzu kuma Ka Shirya Zaka Tafi Ka barni..'Tafad'a Tana kara Sakin kukanta.
Ajiyar Zuciya ya Sauke yana Rumgume da ita yace"Am srry my Noory stop craying duk ba Haka bane. Sometimes na gaji A office so in nadawo gida i Need some rest dat why zakiga Wani lokacin Bana Zama sosai dake kamar da, buh am srry kibari nadawo ba Dadewa zanyi ba Gobe Insha Allahu Zan dawo Komai Zai Tafi Normal kinji.."Kai Ta gyada mai kamar Wata Munafuka kafin yace"Ok...zan tafi Noory.." Yafad'a yana Duba agogon Fatan Dake daure Atsitsiyan hannunsa.
Tare Suka Sauko Daga kan gadon yana Rike Da Hannunta.
Narke Fuska tayi Tana Fadin"Dee wai meya Faru ne a bauchin Naga baka Dade Da Dawowa ba..? Jakarsa ya Rataya yana Rike da wayarsa yace"wlh bansani ba Nima Jiya Mallam ya kirani kan Yau Na Taho yana Son ganina,Insha Allahu ba Wata Mtsala So Don't wrry kinji ko..?
Gyada kai Tayi ammh Gefe Daya na Zuciyarta Na Lukude Aranta Tana Fadin"kiran Mallam ai ba alheri bane awajena. Tsohon banza kawai.."ammh afili sai ta Waske da Mirmishi, jakar Hannunsa ta karb'a Suna Rike Da Hannun Juna Har Zuwa Falon kasa.
suka iske josepen na jera breakfast a saman Dining Rankwafawa yayi yana gaishesu Abdallah ne kadai ya amsa,ammh banda Wasila Wacce Zuciyarta Ke kama da bakin gawayi Saboda Tafiyar Abdallah Bauchi again.
kowa yasan ka'idar Abdallah baya karyawa Da Wuri Dat why ma Wasila bata Damu Da tace Ya Tsaya yayi Taking breafsat dinshi ba.
A haraban gidan suka ci Burki Inda Wasila ta Shiga kwalama Sumel kira,Da Hanzari Ya Fito ganin Madam da oga yasa ya Zube kasa yana gaishesu.
A yatsine Wasila ta amsa, Kafin ma Abdallah yayi mgana ta Jefamasa key din motar Abdallah Bugati, Prado din da ita Su Jamila Suka Fita Jiya,Yana karba Bai Tsaya ba ya Nufi parking space ya Fito da Motar.
kafin ma Wasila ta Barshi su Tafi sai da Aka dau Lokaci Haka ta Kamkameshi tana Kuka,dakyar da lallashi ya samu Tabarshi ya Shiga gidan baya ta Mikomai Jakarsa tana Sharbe Kwallah Hannu ya Dagamata Sanda Samuel ya Zuba Hon megadi ya Wangale get Suka Sulala waje.
sun Fito kenan Sukaci karo da su Jamila Zasu Shiga Motar ta Cika da Music,aguje suka Shiga gidan kamar marasa Tunani,da kallo Abdallah ya bisu kafin ya Kada kai Wani Abu yana Taruwa acikin Ransa, ammh kuma Bazai iya Furtama Wasila ba. ko kuma Su Yan iskan kanninn Nata ya Taka musu burki don yaga iskancin nasu yana Wuce gona da Iri.
Wasila na Komawa Cikin bedroom dinsu wayarta ta Shiga kara, tana ganin Momcy ce Ke Kira Ta Hanzari Ta Daga Tana Fadin"Mekenan kikayi Momcy,anya Bokan nan ko yayi aikinsa yadda yakamata..?Cike da Kosawa Momcy tace"Kamar ya..?bangane ba Wasila..?
Cike da Bakinciki tace"Momcy Abdallah ya Tafi Bauchi yanzu,wai wannan Shigen Tsohon Malamin Uban nashi ya na Nemanshi.."Gaban Momcy ya Fadi Ta Dora Hannu akai kafin Ta waske tace"Toh Shine mene..?Saura fa kwana biyu ne Sharadin boka ya cika,kinga ya cikane Baki ga aiki da cikawa ba.."Cike da Sanyi Wasila tace"A'a Momcy.."Hajiya kudirat tace'Toh kuma meyasa kike Hakane? Plz wasila Kada kibarI Zuciyarki Tajaki ki lalatamana aiki,Dolensa yaDawo gareki Domin Naki ne Shi Na Har Abada so Kidaina ma Daga Hankalinki kinji my Dota.."
Ajiyar Zuciya Wasila ta Sauke Kafin tace"Naji Momcy ammh..."plz wasila Kidaina yawan wannan korafin Bakijin mganata ko.."Momcy ta Katseta cike Da Tsoro,Ranta abace tace"Is ok Momcy.."Daga Haka ta yanke Kiran Daidai Lokacin da Su jamila Suka Shigo Falon A hargitse kowacce idonta baya Buduwa Suna Had'a Hanya Suna Bugan juna,alamun sun kwana sunyi makas jiya Da kallon Takaichi Ta bisu,Har suka Shige dakinsu.
Tsaki Taja kafin ta tashi Ta Isa Kan Dining,lokaci Daya Tana kwalama Josepen kira, domin ita bata Sarving din kanta Sai dai ayi Mata,jikinsa na Rawa yafito ganinta Zaune yasa bai Tsaya Tambayan ba'asi ba ya Shiga Hadamata Abunda yakamata itako Tana Zaune Tana Wani cijewa.
fuskarnan babu Annuri ko kadan,Lokacin ne Kuma Sukaji bude get,Samuel har ya Dawo Daga kai Abdallah Airport, cikin Ranta ko Tsinema Mallam kawai take, Tana Tunanin yadda Zatayi dashi matukar Abdallah ya Dawo hannunta Don Wlh Bazatamai Dadi ba,Don talura Duk Shine Silan lalacewar Komai Nata game da Abdallah
******
Karfe 11am da wani na Safe Mai adaidaitan Daya Daukosa Daga Filin jirgi ya Diresa akofar Gidansu.
Fitowa yayi bayan ya Sallameshi ya Nufi Bakin get din yana Bugawa koda Megadi ya Leko ganin Yallabai yasa ya Budemai Karamar Kofar yana Gaisheshi Tare damai Sannu da Zuwa,vFuskarshi ba Wata Fara'a ya amsa kafin ya Nufi Hanyar Da Zai Sadashi da Babban Falon gidan,Lokaci daya yana Bin Haraban gidan da Kallo,ganin babu Motar Mallam din Zuciyarsa tabashi ya Fita.
Fitowar Maman Fati kenan Daga Kichen taji sallam,tana Daga kanta Suka Hada ido Da Abdallah,Cike da Murna Da Farinciki ta Ware ido Tana Fadin"A'a ikon Allah wanake ganin kamar Baffa.."Mirmishi yasaki yana karisowa Falon ya Duka yana gaida Maman Fati Kanshi ta Dafa Tana Fadin"Masha Allah,sannu da Zuwa ya hanya..? Kansa na kasa yace"Alhamdulillah Mama." yafad'a yana Mikewa Daidai Lokacin da Hajiya Ta Fito Daga Shashenta Tana Fadin"Maman Fati Baki mukayi ne,Naji kina mgana ne..?
Maman Fati Ta Juya Tana Dariya tace"eh hajiya Babban bako ma kuwa Baffa ne.."washe baki Hajiya Tayi Duk da mallam ya Shaidamata ya Kira Abdallah ammh bata zaci zuwansa da Wuri Haka ba.
kafin ta kariso ya karisa gareta,yana kokarin Rankwafawa ya gaisheta Hajiya ta jawoshi jikinta Ta Rumgumeshi Tana mai Maraba da zuwa Abunda ya bashi Mamaki, domin yafi kowa sanin yadda Zuciya take mai kunyar Dan Fari,ko kallonshi bata cikayi ba.
Kan Daya Daga Kujerun Falon ta Zaunar Dashi kafin ta Zauna gefenshi Suna kara gaisuwa ita kuma Maman Fati kichen Ta Nufa Ta Hadomai Kayan karyawa Domin Tana Da Tabbacin Bai karyaba Wani Lokacin Akidan Abdallah irin Ta Mallam ne,ba kasafai suke son karyawa Da Safe ba.
Nan suka Ta sashi Shida Hajiya Sai ya Ci ya koshi,wanda Rabon da yaci abinci irin Haka har ya Manta barinma Soyayyen Plantain din yaci Dayawa Sosai,bayan ya gamane, Maman Fati ta Kwashe kayan Ta maida kichin bata Dawo Falon sai Ta Fara Haraman Daura girkin Rana Tabar Hajiyar Da Baffan Su Zanta.
Bayan Fitar Ta ne Baffa ke Tambayan hajiya Mallam,tace ya Shiga mkranta Dazu,ammh bazai Dade ba yanzu zai Dawo.
kai ya Gyada Mata kafin su Cigaba Da Hira,Duk da Hajiya ke Hiran ammh Baffa na Kokarin bata amsa da Mirmishi ko gyada kai Saboda Shi ba ma'abocin Surutu bane,itako Hajiya Dadine ya Kamata na D'anta ya Dawo gareta Ko ajikinta Ita dai Kawai Labarai Take ba Baffa.
Shiko yana jinta ne kadai,Aranshi yaji Dadin ganin Hajiya ta samu Sauki Sosai Ammh Kuma bai iya Tambayarta ba Don Hajiya Ta Tsinke Da hira bata Son ma Akatseta.
Sai bayan Azahar Mallam ya Dawo Gidan Lokacin Har Abdallah yayi sallar Azahar dinsa adakin Hajiya yaji Shigowar Mallam din,bai Shiga Wajensa ba Sai da Yagama waya Wasila Wacce ke Ta kiransa ,hajiya na Dakin sanda Suka Fara mgana da Wasila yadda Hajiya ta Tsani ko Sunan Wasila a ambata,Shiyasa tana jin Sun Fara mgana ta Fice tabarmai Dakin cike da Takaichi sai da ya gama ya Sameta Ashashen Mallam.
Koda yaje ya Iske Mallam ya baje Atsakiyar Falonsa yana Cin Tuwon Shinkafa miyar ogun Wacce Taji Naman Rago,da Manshanu Nan mallam yace Maza ya Kariso yazo yasaka Hannu, bai da yarda Zaiyi Haka ya Wanke Hannunshi cikin Wata Roban da Mallam ya Wanke,ya saka hannunshi Suka fara cin Tuwon Shida Mallam Hajiya na Gefensu Annuri ya cika Fuskarta,Maman Fati ko na Shashenta taje Tayi sallar tayi Wanka..
Sai da Suka kamallah cin abinci suka Wanke Hannu, Abdallah yaji Dadin Tuwon,domin ya Manta Rabonsa da Tuwon lalle Duk wanda yabar gida gida ya barshi.
sai da Suka Natsu kafin Mallam ya Maida Hankalinshi kan Abdallah yana Fadin"Abdallah...'"Juyowa yayi yana Kallon Mallam din kafin yace"Na'am mallam..."Yafad'a yana Sunkuyar Da kanshi.
Cikin Dakewa da Dattako Mallam yace"Kasan Dalili da yasa na Kira ka nace Kazo ina Son ganinka..? Girgiza kai Abdallah yayi batare Da yayi magana,Mallam yace"Toh ba Mgana bace mai Tsawo,mu suwaye awajenka..?Abdallah ya Dago yana Fadin"Ku iyayena Ne Mallam.."yafad'a cike Da Mamakin Tambayoyin Mallam din.
Jinjina kai Mallam yayi Cikin Gamsuwa yace"Toh Alhamdulillah,Naji dadi daka Fahimci Haka,Kasan mu iyayenka ne. Kuma Muna da Daraja da kimar da zamu Zabamaka Abunda Muka ga ya Dace Dakai.."Hajiya tace"Sosai ma Mallam.."Abdallah dai baice Komai ba kansa na Kasa ammh Zuciyarsa Tafara Zargin Da wani Abun.
Mallam ne yacigaba Da Fadin"toh hakan ne ya Faru bayan Tafiyarka Mahaifiyarka Tazo da Wata Shawara Muka Zauna Muka Tattauna al'amarin kuma Alhamdulilah munsamu Matsaya, Abun Nufi Shine Mun Yanke Shawarar Nema maka Aure akaro Na biyu,Domin Dama Musulunci yabaka Dama, Atakaice Dai har Naje na Samu Mahaifin yarinyar Kuma Mun Fahimci Juna,Har An baka Mata,yau saura kwana goma Sha Daya a Daura Maka Aure Da Ita.."
A razane Abdallah Ya Dago bayan yaji karshen bayanin Mallam cikin Wani yanayi yace"Aure Kuma..?mata ?Wata Matar kuma Mallam..? Hajiya ce ta karbe da cewa"Aure dai Wanda ka sani,Mata kuma ba Kowa bace,Face Asma'u yar Wajen Habiba wacce kagani Azuwanka na Baya.
Dum! Kawai Yaji kansa ya dauka kafin yaji ya Sara masa! Dago kansa ya yi lokaci d'aya ya Sakarma Hajiya Ido,yana so yayi mgana ammh yakasa Hajiya ko ta cigaba Da Fadin"Babanka ya Biyama Sadaki, Muhalli kuma kada kadamu Shima zamu Nema,bama bukatar komai Daga gareka sai amincewarka. Kuma Wlh in ka Sake ka Sanarma Shegiyar Matar nan naka Sai Naci Mutumcinka Inda Mukayi mganarnan, nan zaka barta,Ranar Daurin aure zaka Rike Domin Muna Bukatar Zuwanka Wajen.."Tafada Tana Nuna Bacin Ranta,Mallam na gefe kamar Zai Tanka sai kuma yayi Shuru.
Abdallah ya Dafe kai yana Kallon Hajiya kafin yace"To..toh..hajiya Wai Duk me..me ya kawo hakan ne,Nifa bance inason kara aure ba,Wai ma Yarinyar ne tace Muku Tana Sona ne.? Koko ce muku Tayi muna Soyayyah? I swear Ni banta ganinta ba,Infact ma ko Kasheni Zaku yi bansan kamaninta ba.."
Yafad'a yana Rarrabe Numfashi kamar Wanda Aka Tsamo Daga Rafi.
Hajiya ke Binsa Da Harara,Mallam ko kai ya ijiye gefe yana Dan Murmusawa Cike Da Takaichi.
*Janafty*