ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 18

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



     *🅿️18*


Hajiya ce tace "Bata ce mana tana sonka ba, mune muka ga dacewar hakan kuma muka zartar a matsayinmu na iyayenka.

wanda muke ganin muna da kima a idanuwanka muna da damar da zamu yanke duk wani hukunci akanka kuma ya zartu Abdallah, aure ne kuma dolenka ka karɓeshi bama buƙatar komai naka harta da muhalli mu zamu samar maka amincewarka kaɗai muke buƙata, in shima bazamu samu bane sai ka sanar damu." Ta ƙarishe cike da ɓacin rai.

Ido Abdallah ya kafa mata kafin ya sadda kanshi ƙasa, zuciyarsa ne tayi nauyi yama kasa magana ganin haka yasa Hajiya ta cigaba da faɗin "Nace zaka amince ne ko kuwa sai ka ƙara nuna mana iyakarmu a karo na biyu? Saboda kaga mun ɗaga maka ƙafa kana abunda kaga dama, wlhi Abdallah wannan karon indai ka bijirema umarninmu wlhi bazan taɓa yafe maka ba..." Ta faɗa tana tsiyayan ƙwallah.

Mallam ne yace "Ya isa Hajara, rabu dashi kinsan dai baki da lafiya don Allah ki bar tada wannan maganar.." Bata saurari Mallam ba, ta miƙe ta fice daga falon tana goge fuskarta da haban zaninta.

Ajiyar Abdallah ya sauke yana bin Hajiya da kallo jikinsa yana ƙara yin sanyi, cikin muryan kasala yace "Kuyi haƙuri Mallam na amince da zaɓinku Allah ya tabbatar da alheri.." Cike da murna Mallam ya washe baki yana faɗin "Masha Allah, naji daɗin maganarka Abdallah, Allah yayi maka albarka. tashi kaje kabama mahaifiyarka haƙuri tayi fushi da kai.." Miƙewa yayi jiki asanyaye ya fice zuwa shashen Hajiya.

 Hajiya na zaune gefen gadonta tana tsiyayan hawaye Abdallah ya shigo ya daÉ—e a tsaye yana kallonta hannunsa duka biyu suna zube acikin aljihun wandonsa, Hajiya taji shigowarsa amma saboda haushi ko É—aga kanta batayi ta kalleshi ba. 

Numfashi ya ijiye kafin ya ƙarisa gabanta ya durƙusa duka hanuwansa ya sanya ya riƙo hannuwan Hajiya yana kallonta kafin a hankali ya fara faɗin "Hajiya don Allah kiyi min aikin gafara ki daina kuka, na amince da abunda kuka zaɓa min.." Jin haka yasa Hajiya ta ɗago tana kallonsa haƙoranta duka awaje tace "Da gaske kake Abdallah..?" Kai ya ɗaga mata kafin ya samu zarafin magana Hajiya ta miƙe ta ɗagosa ta rungumesa tana saka mai albarka harda godiya kafin ta ɗagosa tana faɗin "Naji daɗin haka Baffa, na tabbatarma zaka ji daɗin zaɓin da muka yi maka, taso mu koma shashen Mallam mu cigaba da tattaunawa kasan abun yazo.."

Ta fada da murna tana yar dariya, tana riƙe da hanunshi har shashen Mallam ɗin, ganin Hajiya ta dawo tana dariya yasa Mallam ya fara tsokanarta da uwar Abdallah, itako tana dariya, nan Hajiya ta zauna ta tanƙwashe ƙafa tana ƙara zuzutama Abdallah kyawawan halayyar Asma'u, shiko yana zaune yana jinta sai dai yayi mata murmushin ƙarfin hali kawai, zuciyarsa bugawa take duk sanda ya tuna da Wasila, gaba ɗaya kanshi ya kulle bashi da yarda zaiyi ne, amma maganar gaskiya a tsarin rayuwarshi bayan Wasila wata mace bata burgeshi in ma auren zai ƙara toh sai dai ya ƙara da Polina don ko ba komai yanayin tsarinta yayi dai dai danashi, kuma sosai yarinyar take tafiya dashi.

Yana cikin wannan tunanin yaji muryan Hajiya na sanar da Mallam bata yarda Asma'u ta zauna a ko'ina ba sai cikin gidan nan, Mallam ne ya dakatar da ita da faÉ—in in akayi haka zasu shiga hakkinsu da yawa, kuma ko ba haka ba itama Asma'un baza ta sake ba duba da mahaifiyarta a gidan, hakama Abdallah sai dai cikin gidajensa dake GRA za'a duba É—aya asaka Asma'un a ciki.

Duk da Hajiya bataso haka ba, amma maganar Mallam gaskiya ce, kuma tunda gari daya ne ana kusa, sai ta amince, shi dai Abdallah zuru kawai yayi musu bai ƙara saka musu baki ba, suma basa ambatonsa a ciki domin kamar yadda suka faɗa amincewarsa kaɗai suke buƙata, ko maganar lefe Hajiya da Mallam yaji suna maganar Safina da Hajiya zasu Kano su haɗo komai, saboda ko ance Maman Fati taje zatace bazata je ba.

Hirar bata tashi ba sai da aka kira sallar La'asar suka fita shida Mallam, koda suka dawo É—aki ya shige ya kwanta saboda baya son hayaniya ga dagula mai lissafin dasu Hajiya sukayi.

Washegari nayi yabi jirgi ya koma bayan su Mallam sun jadadda mai yazo É—aurin aure kuma yayi musu alkawarin zai zo, Hajiya kuwa kunnenshi taja akan kar ya kuskura ya sanarma Wasila komai sai daga baya, ya amsa mata da Toh, shima ai ba karan hauka ne ya cijeshi ba, don har yanzu asirin shakkar Wasila bai sakeshi ba, koda ya isa Portharcourt Office ya wuce sai dare ya koma gida bayan ya fara biyawa wajen Polina sun biya bashi kafin ya koma gida. 

Wasila taji mamakin ganin Abdallah ya dawo kamar tayi ihu da tsalle saboda murna, tana ji a ranta ƙila aikin boka ne ya fara aiki domin dama gobe ne wa'adin boka zai cika, farin cikinta ya kasa ɓoyuwa ranar dai dole tasa Abdallah ya kusancenta domin tayi kewarshi sosai da sosai.


Washegari Wasila ta dinga binsa da kissa da kisisinar sai ya gaya mata abunda Mallam yace mai da yaje Bauchi, amma sam Abdallah yaƙi yarda ya gaya mata illah cemata da yayi babu komai, duk ƙwaƙwar Wasila haƙura tayi ganin bata samu komai ba, kuma bataji komai ba, ganin Abdallah bai canza mata ba, yasa ta kira Momcy tana sanar da ita aikin boka na kyau sosai, hankalin Hajiya Kudirat ya kwanta zuciyarta tayi sanyi acikin ranta tana addu'ar Allah yasa kafin wani abu ya ɓullo boka ya fito daga aikin daya shiga bata son Wasila taji labarin bata samu ganin boka ba, tsab zata tada haukan zuwa wajen wani bokan wanda faruwar hakan tamkar rugujewar duka sirrunkansu ne daga ita har Wasilan


  


*******


Ta kowani ɓangaren shirye shirye ne ke gudana karma gidansu Mallam suji labari domin shiri suke na musamman, Mallam da kanshi ya saka a bugo mai katin ɗaurin aure nashi na kanshi ya fara rabawa abokansa da yan'uwa da abokan arzuka.

Yusuf kuma bai damu da jiran Abdallah ba wanda bayan sun koma sunyi magana dashi sau ɗaya, da yayi mai maganar shirin biki, sai Abdallah ya kauda zancen bai bama Yusuf wata dama ba, shiyasa shi kuma ya ƙyaleshi, shima yasanya an bugo musu katina masu kyau, har guda ɗari biyu 200, bayan kuma na waya daya turama kowa, kama daga yan'uwa zuwa abokan karatunsu da Abdallah, da kuma abokan zaman arziki, hatta Abdallah sai da aka turamawa, yana gani ya goge yana sakin tsaki kamar wanda aka turo mai mugun abu.

Maganar gidan da Asma'u zata zauna kuwa cikin gidajen Mallam ne dake GRA ya bama Abdallah ɗaya halak malak, bayan an saka masu gyara sun ƙara gyara gidan, dan matsakaicin flat ne mai ɗauke da haraban parking daga cikin gidan kuma babban ɗaki ne sai 2 bedroom masu ɗauke da toilet, sai ƙaramin kichen dake falon chan gefe kuma wajen zaman dining ne, sabon gidane Mallam ya siya babu abunda aka zuba a gidan.

sai dai yasha gyara ta ko'ina abun sai wanda ya gani, ɓangaren kayan lefe kuwa Hajiya bata samu zuwa ba Anty Nafisa da Anty Safina Mallam ya buɗe ma bakin aljihu suka tafi Kano suka shaƙo akwatuna 12 maƙil cike da kayan arziki, dama da yake Anty Safina business ɗinta kenan so tun kafin suje ta riga tayi waya da wanda take siyayya a wajensa ta sanar dashi suna buƙatar kayan aure complete akwati dozen, suna zuwa suka iske komai ya kammalla, lissafi kawai sukayi suka turo mai kuɗinsa ta banki Mamman daya kawosu ya dinga jidan kaya zuwa cikin mota da yake ma shi ya kaisu har Kano ya kuma koma dasu.

Maman Fati da taga irin naira da dukiyar da aka narkama Asma'u sai da tayi ƙwallah saboda farin ciki acikin ranta tana fatan Allah ya basu zaman lafiya, achan Dutse kuwa gidan su Asma'u ba wanda ke shiryama bikin Asma'u sai Anty Amarya wanda da farko Abba Umma yasa a gaba amma hasada da ƙyashi suka ƙi barinta sak, balle da Abbana yace bazai taɓa sisi daga cikin kuɗin sadakina ba, hakkina ne, miliyan ɗaya ya ciro daga banki yace ayi min siyayyan duk abunda ya dace, ganin wannan kuɗin shi ya fito da hassadan Umma data Hajiya Iya sarari kowa ya ganesu har Abba, don Umma buɗe wuta tayi tana faɗin Abba yayi albuzaranci mai zai hana ayi min komai da kuɗin sadakina, nan da Abba ya taso mata yace ta faɗa masa ita duka ya'yanta akwai wacce ya cira sisi daga cikin sadakinsu...? Duka da kuɗinsa yayi musu komai a matsayinsa na uba a garesu, haka itama Asma'u 'ya take a wajensa zai mata duk abunda yayi musu domin tana da hakki akansa ganin haka ne yasa Hajiya Iya kama bakinta ta shiga yima Umma faɗan meyasa zata yi haka? Sai da suka koma ɗaki ta hau yi mata faɗan tayi kuskuren faɗama Ladan haka, lura da yadda ya fara zargin da wani abu a ƙasa, wannan dalilin ne yasa daga Hajiya Iyan har Umma ba wacce Abba ya nema ya kira Anty Amarya da Asma'u ya sanya musu kuɗi, yace su tafi tare kasuwa ta zaɓi Furnitures da take so da kuma kayan kichen da sauran kayan buƙata, Asma'u sai da tayi ƙwallah saboda farin ciki tayi ta godiya Abba na saka mata albarka, Anty Amarya ko ta amshi kuɗi da hannu biyu ta kuma tabbatarma da Abba cewa za'ayi komai yadda ya kamata, yaji daɗi sosai domin tun ba tun yau ba yana yabama Halimar wajen kula da Asma'un da kuma yarda ta ɗauketa 'ya a gareta.

Anty Amarya bata yi sanyin gwiwa ba ta samu Ammi da maganar kuɗin da Abba yabama Asma'u domin siyayyar kayan aure, Ammi bata yanke hukunci ba sai da ta kira Maman Fati ta sanar mata abunda Ke faruwa, ran Maman Fati yayi daɗi sosai, amma duk da haka sai ta sanarma Ammi da zata turo kuɗi dubu ɗari biyu a account ɗin Baban A'isha, a ciro a ƙara ayima Asma'un siyayya, Allah sarki uwa kenan kiwo Maman Fati keyi awajensu saboda auren Asma'u in ya tashi, ganin abun yazo ne tun shekaran jiya ta kira Kawu tace asaida komai abada kuɗin jin maganar Ammi yasa ta kira Kawu tana tambayanshi ko kuɗin sun haɗu..? Nan ya sanar mata sun haɗu, ba tayi kasa a gwiwa ba ta tura mai account nombar Baban A'isha, shi kuma washegari ya bama babban ɗanshi Muntari ya tafi banki ya tura kuɗin.

 Asma'u bata bisu Ammi kasuwa ba saboda kunya, kuma gashi tana zuwa wajen aiki bata fasa zuwa ba.

duk da ba tasan makomar aikin nata ba, babu wanda ta sanarmawa zatayi aure sai da taga biki ya rage saura sati ɗaya kana take sanarma Sister Bahijja, wacce taji abun daga sama, har saida ta nuna ɓacin ranta, haƙuri Asma'u ta shiga bata tana sanar da ita abun agurguje yazo shiyasa, Sister Bahijja tayi murna sosai ta kuma yi alƙawarin zuwa bikin Asma'un, kuma ita ta sanar da 'yan asibitin labarin auren Asma'un duk da ita Asma'un bataso haka ba, suna ta mamakin abun amma basu damu ba, sanin zurfin ciki irin na Ma'u, kowa sai tayata murna yake ita abun ma sai ya koma bata kunya.

Ammi da Anty Amarya sun fito da Ma'u da kayan É—aki masu kyau domin gado suka zaÉ“ar mata mai kyau Royal bed, da kuma Italian bed, bayan kujerunta masu kyau na Royal Chairs, sai kayan kichen É—inta suma komai da komai na buĆ™ata, har da dinning Area don Ammi da kanta ta kira Hajiya ta tambayeta yanayin wajen zaman Ma'u ita kuma ta sanar da ita, a gidan A'isha aka ajiye kayan tunda Abba yace karsu damu akai kayan chan, indai an siya abunda ya kamata su Umma da Hajiya Iya suyi, amma hatta da Mama basu da labarin komai, don Anty Amarya sai dai ta shirya ta fita bata ce musu gata zuwa ba cikin kuÉ—in Maman Fati ne suka siyo buhun fulawa da suga da kuma jarkan man gyada, domin toye toye.


Biki ya rage saura kwana huÉ—u Hajiya ta kira Ammi da kanta ta sanar da ita su Anty Safina na bisa hanya zasu kawo kayan lefe, cike da farin ciki Ammi ta zari matafi ta leĆ™a gidansu Asma'u ta kira Anty Amarya tana sanar da ita, guÉ—a ta saki tun daga É—aki har tsakar gida, inda Hajiya Iya ke zaune tana hutawa, lokacin da safe wajen 9am ne, tun kafin ma su tambayeta tace baĆ™i suna tafe daga Bauchi da lefen Ma'u, Umma dake É—aki ko leĆ™owa ba tayi ba Mama ce ma ta leĆ™o tana kallon Anty Amaryar, Hajiya Iya kuwa ko tankawa batayi ba, Hassatu ne suka fito cike da farin ciki suna tambayanta me za'a girkama baĆ™i, kichen suka shiga tana sanar dasu, yayinda Ammi ta koma gida, A'isha ta kira awaya tana sanar da ita, ihu ta buga tana murna, nan da nan tace yanzu zatayi kunun aya da pepe meat tazo dashi, Ammi taji daÉ—i sosai tace sai tazo.

Asma'u ba tasan wainar da'ake toyawa ba saboda tana wajen aiki, kuma ba wanda ya kirata, ƙarfe 12:30 da rabi baƙin Bauchi suka iso, da kwatancen da Maman Fati tayima Mamman, koda suka iso wayar Ammi Anty Safina ta kira kamar yadda Hajiya ta sanar dasu ita tazo tayi musu jagora zuwa cikin gidan bayan Mamman da megadi sun fara jidan manyan akwatunan suna shiga dasu cikin gidan, wanda Anty Amarya ta share ko'ina ta baza babbar tabarma atsakiyar gidan anan su Mamman suka dinga jera jeren akwatunan masu launin pink, Umma dake ɗaki jin guɗan Anty Amarya ya sata fitowa ita da Anty Bilki da Anty Ruƙayyah sai Fa'iza wanda ta kira su kamar abun arziki akan suzo yau za'a kawo kayan Asma'u, ya'yan Mama kuma Maryam ce kaɗai tazo, basu tsinke da al'amarin ba sai da suka ga angama jera akwatuna dozen.

kafin su Anty Safina da Nafisa su shigo kowacce tayi shiga ba raini fuskarsu kuma ɗauke da fara'a Ammi ne da Anty Amarya sai wasu tsirarun maƙotan da Anty Amarya ta aikamawa suka hau yi musu sannu da zuwa, Mama ma ta fito tana musu barka da zuwa, Hajiya Iya ko gaisheta sukayi ta amsa tana binsu da kallo, cike da wani yanayi, Umma ko kasa fitowa tayi tana daga ƙofar ɗakinta, tana raba ido zuciyarta na bugawa lokaci ɗaya tana nanata sunan Asma'u a cikin ranta, Anty Bilki da Anty Ruƙayyah ne suka ƙarisa suna yaƙen dole, Fa'iza ko tabi Anty Amarya kichen suna kwasoma baki kulolin abinci da abun shan da'aka haɗa musu. su Anty Safina sun zauna kenan sai ga A'isha ta shigo da uwar kula da kuma wani ƙaton jug da wani ƙaton kwando, ganin har baƙin sun iso yasa ta zauna tana gaisawa dasu Anty Safina, da yake sun san juna cike da fara'a suke amsa gaisawanta yayin da ta tura musu kwandon gabansu Anty Safina ne ke faɗan hidimar tayi yawa sufa 'yan gida ne domin daga Asma'un har Yaya Baffan nasu ne.






*Janafty*