ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 20
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️20*
Hausawa sukace Rana bata karya sai dai Uwar D'iya Taji Kunya.
Yau dai itace Ranar da za'a Daura Auren Asma'ul Husna da Angonta Abadallah, Tun misalin 10am na Safe tawagar yan Daurin Aure Ta Mika Motoci goma Tsala Tsala na Alfarma cike da Kuma Mutanen kwarai Da Dattako kama Daga Yan'uwa da abokan Arzuka da abokai da makusatan Mallam aciki. Harda Mallam D'abarani atawagar Mallam, sun Tafi Su Hajiya nata Fatan Zuwa lafiya da Dawowa lafiya.
suma Daga Cikin Gida Hidima ta kacame,Maman Fati kuwa Tun Daren Jiya ta kwana sallar dare da Fatan Allah ya Tabbata da Wannan Aure, ba ita kadai ba Hatta su Hajiya basu Zauna haka ba, Suma addu'ar Suke Allah ya sa Adaura Auren Lafiya.
Abangaren Asma'u kuma Kun Riga Kunsani bata Wasa Da Gayama Allah Kukanta da Kuma Tsayuwar Dare, Kwana tayi Sallah Tare da addu'an Allah ya Tabbatarmata da alheri yasa Adaura wannan Auren Lafiya.
A'isha dake kwance Saboda tana Fashin Sallah Sai da Tama Asma'un Hawaye Itama Daga Kwancen Tana addu'a acikin Ranta Allah yasa iyakar wahalar kenan.
Suma tun Safe Anan Gidansu Asma'un Sunata Shiryen Shiryen zuwan yan Daurin Aure,Abangaren Asma'u Amarya kuwa Tun Safe Data tashi Taji Jikinta baya Mata Dadi.
gadai ta nan Tun Wajen 8am na safe Su A'isha suka Matsamata tayi Wanka ta Sanya Daya daga Cikin kayan Akwatuna Wani Leshi ne Ubansu,cbatayi Kwalliya ba Saboda A'isha tace Ummu Salma Kawarsu Wacce Sukayi Islamiyya tare Zatazo Tayi mata Kwalliya, Tana Cikin uwar Dakin Ammi ita da Amir yana Ta Mata Fira,Ammh Bajinsa take ba Kawai Wani Sashe na Jikinta na bata Wani Abu zai Faru.
gabanta kuma na Yawaita Fad'uwa, Ammh sai Tayi ta addu'an ko da Safe Dataje gaida Abba sai da Tayi kuka Da yake Mata Nasihan zaman Aure Haka kawai Takeji kamar fa Bazata bar Dutse Ayau ba.
Ammh bata Furtama Kowa ba,Duk da duk wanda ya Kalleta sai ya Fahimci bata da Walwala, A'isha ma Duk ta Damu Tana Ta Tambayan Asma'u ko lafiya sai tace Mata bakomai.
Ko kafin 12 na Rana tayi Har Asma'u ta Canza kaya Inda Ummu Tazo Tayimata kwalliya mai Tsari.
wannan karon Wata Atamfa ce ke Jikinta Super wax, Mai Uban Tsada da yarari,Abun da Zai baka Mamaki ana kamallama Asma'u kwalliya ta fara Kukan Da Batasan Dalili ba balle Dataji Lbrin yan Daurin Aure Sun Fara cika gidansu Ciki Harda su Kawu Daga Dutse Suma Mota Guda.
Su Anty Bilki duk gidansu Ammi suka Dawo Saboda Gulma, Asma'u tayi kyau Hartagaji da kyau,ga lallenta Baki da Ja,wanda yakara haskata,Su Sister Bahijja da Yan Wajen aikinsu da sukazo Tun dazu Suka Fara Rige Rigen Daukanta Hotuna.
Ammh Asma'u Taki Tsayawa Kuka Kadai Take yi ,A'isha ta Damu da Wannan Kukan na Asma'u Ammh sai Ammi tace ta Rabu da Ita kada ta Matsamata kukan Rabuwa da gidane,da Kuma Farincikin yau Allah Zai Cikamata Burinta.
Duk da A'isha bataso haka ba Ammh Haka Ta Rabu da Asma'u Ta Kira Fahad awaya yazo ya Dauketa Taje ta karbo abinci da suka Bada akayi musu,sai gashi Ta Dawo da Uban Kololin Shake da Shinkafa Fried rice ne da Alale sai Kunun Aya da Zobo, Lokacin da Tadawo Fahad ya Ijiyeta kenan ya Taimaka mata Sun Sauke Kololin kenan Motocin Angawaye da Iyayensa Suka Fara Fakawa Akofar gidan Su Asma'u lokacin karfe 12:30pm Lokacin Daurin Aure ya kusa,Ammh sai an isar da sallar Azahar za'a Daura Auren A masallacin Dake Kusa Dasu.
Liman Huzaifa dama Shike Dauramusu Aure,A'isha ta Shiga da Lbrin karisowar mutanen Bauchi.
Asma'u na Ciki na Ji,sai Taji kanta yayi Mata Nauyi Ammh sai Bata Nuna ba,Tunda Kawayensu Sun Fara Zuwa Suna Tare Da ita Suna Ta Mata Shakiyanci.
Koda su Mallam Suka Fiffito Daga Motoci gaiggaisawa Suka Farayi dasu Abba, kowa kagani yaci gayu ba Raini Ango kuwa Yana ta Kunci Da Komai ya Saka gezner nan da Yusuf ya Dinkamusu mai Babban Riga, Shima Sai da yace Sai Hadashi da Hajiya Kana ya Sanya kayan Ammh Tun Asali manyan kaya basa Burge Abdallah yafison yaga ya Tsuke Cikin kananan kaya.
Kuma Abunda baisani ba Manyan kayan Sunfi Amsar sa Sosai Kuma Sun Fi Fitomai da Zatinshi na Cikakken Namiji.
Ko Ayau din Ma Mutane Dadama sai Hamdala Suke tare Da Taya Asma'u Murnan Samun Gwarzo mijin irin Abdallah.
Wanda kaf ya'yan Ladan ba Wacce Ta samu Miji kamar na Asma'u Shikanshi Fahad Yaji Natsuwa ta Kamashi lokacin Da'aka Nunamai Mijin Asma'u Sai da Yaje suka gaisa, dashi da Yusuf, har Hotonshi ya Daukan ma A'isha,Suko mazajen Su Anty Rukayyah Tuni Suka Fara Raina kansu,Domin Susan Wannan ya Zarce Tsara Sosai.
Fuskar Abdallah bata Saki Ba, Ammh kuma bai Mugun Daure Fuska ba,Kallo daya zai Maka kwarjininsa ya Dakeka Sosai,yana gefe shida Yusuf da Wani kamal abokinsu Tun Suna Mkrantan Abu Zaria,Yusuf ya yagayyatosa.
Mallam ne yace Suzo Suyi Alwala An kira sallah,cikin Lokaci kankanin Jama'a kowa ya Daura alwalansa kafin Manyan Mutane Da Kuma Waliyan Amarya Dana ango Suka Shiga Cikin masallacin Domin Baida Girma sosai, Sauran Jama'a ko Awaje akaja Sahu Ciki Harda su Abdallah,Tsawon Mintina Sha biyar kafin a isar da Sallar,lokacin 1pm ta Wuce Harda Minti goma,nan da nan aka Sanar da Za'a Daura Aure yanzu.
Liman Huzaifa ya Motsa kafin Mallam da Mallam D'abarani Su Matso kusa Inda Abba Da baban Aisha Suke Zaune yana Rike da Sadakin Asma'un.
Nan da nan Mallam ya umarci da Mallam D'abarani Yayima Abdallah Walicci,Shikuma Liman yama Asma'u cikin Abinda bai gaza Mintina Ashirin ba Aka Daura Auren *ABDALLAH MAHMUD ABDALLAH AZARE* Da Amaryarsa *ASMA'U LADAN SHERIFF* Kan Sadaki Naira Dubu Dari biyar Lakadan ba ajalan ba,Hakama Mai Shele ya dinga Sanarwa A lasifakan masallaci,
Daga gidan Ammi Ana ji, haka Daga cikin Gidan Abba, Asma'u na Zaune Tunda Taji Sanarwarn An Daura Auranta Zuciyarta ta Tsinke sai sabon Kuka Share Share.
A'isha ce Tazo Ta Rumgumeta Itama Tana Kukan Farinciki,chan Bauchi Yusuf ya kira Zainab awaya ya Sanar Da Ita Yanzu aka Daura Aure,ai sai gida ya Rude da Murna,Maman Fati ko Daki Ta Shige Takai goshinta gabas Tana Kwararoma Allah Kirari daya bata Ikon Ganin Auren Ma'u Wanda Da Dade Tana Fata Da Buri.
Abdallah ko Tunda aka sanar An Daura Aure yaji kansa yamasa Nauyi ko jama'ar dake mikamasa Hannu Suna mai Murna yake kawai yakeyi jinsa yake Kamar bashi ba.
******
Dagachan Bangaren Kuwa Wasila ne Da Hajiya Kudirat Zaune Agaban Boka Dandugaji.
Sun Sadda kai kasa,kamar Wasu marayu,Masu Neman Abasu abinci ko Sutura, Allah ya Tarfama garinsu Nono Suna Zuwa Suka Tarar da Boka ya Fito Daga Bukarsa Tun Bayan yayi Sati biyu cur aciki Domin ya Kammallah Aikinshi.
Tunda suka Shigo wajen Minti Talatin kenan Boka na Zaune yana Ta Tsafe Tsafenshi Cikin Wata kwarya dake gabansu,Saura Biyu Wasila Na Neman mgana yana Dakatar Da Ita.
Hajiya Kudirat ne Zungurinta, Dole Taja bakinta Ta Tsuke,basu da Tsammani sukaji Boka ya Saki Wata Mahaukaciyar Dariya mai Cike Da Tsoratarwa Nan da Nan Momcy da Wasila Suka Kamkame Juna Suna Numfashin Tsoro indonsu Duk ya Fito,kai Boka Dandugaji kad'a kafin ya sakarmusu Jajayen idanuwansa ya Furta Cikin Wani Amo mai Sauti da Kara.
"Dama na Shaida muku Tabbas Abdallah Zaije Bauchi, Kuma Zuwansa Dole ne, Saboda iyayensa sun tashi Tsaye Akanshi Sosai,Yadda Bazamu samu Nasaran yin Wani aiki Akanshi ba,Koda kikazo Kwanaki Koda Kin samu Ganina babu Abunda zan Iya Miki sai Komai ya Kammallah.."Yafad'a yana kara Saka Wata Dariya,Cike da Mamaki Wasila Ke Bin Hajiya Kudirat da Kallo.
Ashe dama Bata Samu ganin boka ba Shine ta Yimata karya? Hajiya Kudirat ko Mur Tasha taki kallon Wasila ta Maida Hankalinta kan Boka Wanda Ke Cigaba da Babbaga Dariyansa cikin Dariyan ne ya Cigaba da Furta.."Dama mu A Akidar aikinmu Bama gaggawa kuma Haka Zalika Bama Mu'amala da mai yinta, Akullum ina kara Gargadinku kada Ku mana gaggawa a aikin mj Domin Watarana Zaku Tashi Cikin Danasani."Momcy tace"Hakane Boka, Toh yanzu Mecece Mafita? Muna so Kwata Kwata Iyayen nashi Subar Ranshi ne,Ya Daina Tunasu Kwata Kwata"
Bai Kalleta ba Sai da ya Dau Tsawon lokacin kafin ya saka Wata Dariya mai kama da An Shakeshi yace"Aiki zai yi kyau Yanzu Haka, Ammh kuma Abdallah yafara Kokarin Subucemiki Wasila cikon Tauraronshi na Uku ya bayyana Gareshi Ayanzu Haka Danike Muku Wannan Mganar Abdallah na Garin Dutse a jahar Jigawa a unguwar gida Sittin,an gama Daura masa Aure da Matar da Itace zata zama Silar lalata Dukkan Shirin ki Wasila itace Zata Tsarwatsaki ki Zama kamar ba'ayi ki ba."
Ba Wasila kad'ai Ta Tarazana ba Hatta da Momcy sai Da ta Razana Ta Fiddo ido Waje Hannunta Dafe akirjinta, Wasila ko Tsalle Ta buga sai gata Gaban Boka tayi Zaman ya bori tuni Dankwalinta ya Cire daga kanta Uban gashin Dogin dake Kanta ya bayyana Waje,Cikin Wani Yanayi da Fitar Hayyaci tace'"Au...Au....re.....Abdallah...boka Kamin Rai Don Allah ka Shiga Tsakanina da iyayen Abdallah ka Kashesu duka Harda Matar,Wayyo Ni Wasila na Shiga Uku..."Take Fad'a tana Kuka Sosai Hawaye Na Bin Fuskarta kamar da Bakin kwarya.
Boka bai Mata mgana ba,momcy ce Ta Karisa Ta Riko Wasila Tana Bata hakuri Ammh Ina Sai Wani Fizgewa take Kamar Wata Mahaukaciya Sabon Kamu,Shiko Boka Hannu ya Dora saman kwaryar gabanshi Sai Hoton ga ABDALLAH ya Fito baro baro sanda yake Ta Hannu Da Mutane ana Tayashi murna,Duk Da Fuskarsa bata Saki ba,Ammh yana ta Yake sama sama.
Daga Wasila Har Momcy kuri Sukama kwayar da ido,Wasila ko Fad'in Take "Shine Boka Don Allah Kamin rai Na Shiga Uku wlh bazan Iya Rayuwa Babu Abdallah ba,Kuma bazan jura ganinshi Da Wata Ba, Boka kayi komai In Takama A Haukatar dasu suda shegiyar yarinyar daya Aura,Shikuma Asake mallakamin shi Boka Dakai kai kad'ai na Dogara.."tafad'a Tana Sharbe Hawayenta had'e Da Majina.
Boka yayi Wata Karamar Dariya yana Fadin"Karki Damu yarinya Tunda Kika Dogara damu Mu kuma Zamuyi miiki aiki Koda Na Dan lokaci ne, Mganar gaskiya babu Yadda Muka iya da Iyayensa da Matar daya Aura Domin Yarinyar Dama Chan Tana Cikin Zanen Kaddaranshi kuma Akwai zuru'a Sosai atsakaninsu uwa uba Ita din Wata kariyace gareshi abokiyar Arzikinshi ce, Kuma bata Zauna ba Tsaye Take ga Kanta da addu'a babu Aljanin da Zai iya Kusantanta Batare Daya Kone ba, Ko Jinin Haila Take bata Rabo da Addu'a"an Neman Tsari,hakama Iyayenshi Bazamu iya dasu ba.
sai dai Shi yaron da Muka saba cin Nasara Akanshi, Ayanzu Haka Zan Turamai Wani Aljani Wanda Zai Fadeshi yafad'i.
Sannan ya kuma gusar mai Tunani kowa,kada yaji Mganar Kowa sai Taki,kuma ya Baro Da Shi Daga Garin Zuwa gareki acikin kowani Hali. Sharadi na Farko in yazo Gareki Baida Wacce yake Gani Tamkar Uwarsa da Ubansa Sai Ke,Ke Kuma Kiyi kokarin kafin Wayewar garin jibi ku bar Kasar nan Dake Dashi Har na Tsawon Wata Biyu Domin Matukar Kuna kasar nan Toh aikin Zai iya lalacewa nan da Lokaci kad'an..."
Wasila ta Kalli Momcy bayan jin bayanin Boka kafin Momcy Tace"Wato dai Boka yau Abdallah Zai baro Duk inda yake Zuwa Wajen Wasila? kuma Zuwa Wayewar garin Jibi Sun bar Kasar nan ko.."?Bai Mata mgana ba Illah ido daya Zubamata kafin yace"Koma yaya ne..? ko yau ko gobe Zai zo Gareta. Kafin dai Jibi suyi Nesa da kasarnan in ba Hakaba Akwai Matsala Babba.."Da Sauri Wasila tace"Boka Zanyi yadda kace, Dama takardan Annual Leave Dinshi Ta Karshen Shekara Ta fito So Bani Da Mtsalan Tafiya Dashi ko'ina ne. Nagode Boka daka Dawomin da Abdallah Zuwa gareni,Wannan karon Sai Na Nuna ma iyayen Abdallah basu isa Su Tozartani ba.."Tafad'a Tana Huci.
Gyada kai Boka yayi Kafin yace"Komai Zai Tafi daidai Indai kikayi Abunda Nace, Zuwa Jibi Kada ku Zauna akasar nan,Sai Sharadi na Karshe Kada Ki kuskura kibari Abdallah ya kusanci Matarshi Domin da Zarar Maniyinshi da Maninyinta ya Hadu Waje Daya Kifara Kirga Zanen Kaddaranki Daga Lokacin Domin komai Naki zai lalace, Gargadi na Karshe Kada ahada aikinmu da na wani in Hakan Ta Faru ba Ruwanmu komai da Kika aikata Zai Dawo kanki ne."
Wasila Da Momcy Suka Gyada kai kafin Suyi Mgana Boka ya Zuba Wani Abu Cikin Kwaryanan lokaci Daya ya Daga musu Wasila Hannu yana Fadin"Ku Tashi Ku Fita Lokacinku ya Kare..."Da Hanzari Suka Mike, Bayan Wasila Ta Ijiyema Boka Kudin Dake Hannuwanta,Wanda Batasan iyaka ba su kafice Da Sauri ammh Zuciyoyi su Cike Da Farincikin samun nasara,har Suka Fice Daga Dajin,ba wanda yayi mgana.
Koda Suka Isa Gida Wasila batama Momcy Mganar karyan Datayi mata,ganin Haka sai Momcy ta basar,suna Komawa gidan Wasila tayi Shirin Komawa Porthercourt bayan Sungama Shirya yadda Komai Zai Wakana Suka Rabu Momcy na Kara Jaddamata Data kula,Har Motarsu Ta Fice Daga Haraban gidan Inda Samuel ke Tukata Momcy Na Tsaye Tana Daga Musu Hannu.
*******
Achan wajen Daura D'aure kuwa Abdallah na Cikin Tsakiyar mutane Ana Ta bashi Hannu Tare damai Fatan alheri,Su Mallam kuma na Cikin Masallacin basu Riga Sun Fito ba
Kawai Sai Abdallah yaji Wani Abu yaShigeshi Lokaci Daya Kamar ansakarmai guduma atsakar kanshi Cikin Fitan Hayyaci ya Dafe kanshi yana Layi.
Idanuwansa Sunyi Jawur Yusuf Dake gefe ne ya Ankare Da Halin Da Abdallah ke ciki Ammh ko kafin ya Yunkuro Zuwa Gareshi ya Sulale ya Zube Awajen yana Wata Fizga yana bangare bangare Kirjinsa na Sama Da kasa ƙafafuwansa na Shurawa kamar Wani Wanda ake Zare Ranshi.
Da Gudu Yusuf da Sauran Mutanen Dake Kusa Suka Nufeshi Cikin Tashin Hankali.
*Janafty*