ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 21
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️21*
Yusuf da Kamal ne Asahun gaba Wajen Isa Kusa da Inda Abdallah Ke Kwance Yana Shure Shure.
Yusuf ne ya Tallaboshi Cikin Wani Tashin Hankali Wanda ya Bayyana Daga Fuskarshi Zuwa Cikin jikinsa.
Cikin Muryan Fitan Hayyaci yake kiran Sunanshi."Abdallah...Abdallah ka Tashi meya Sameka...? Ammh Ina Abdallah sai Wani Kara Shure Shure yake idanuwansa Suna Kulle Tamau,Hulan kanshi ya Ciremai kamal kuma ya Ciremai Babbar Rigar Jikinsa Yana Mishi Fifitata.
Nan da nan Mutanen Dake Wajen Hankalinsu Yafara Zuwa Wajen Abunda Ke Faruwa, kafin kace Kwabo An Zagaye Su Ana Kallon Ikon Allah,Ciki Harda Fahad Wanda Hankalinsa Ke Matukar Tashe, Mikewa Yayi yana Ciro Wayarsa Daga Aljihunsa da Hanzari ya Kira Mallam awaya yana Sanar Dashi Abunda Ke Faruwa Cikin Tashin Hankali,wanda Har Muryansa ta Canza Kwallah Sun Taru agefen Idanuwanshi.
Mallam da dasuke Tare Dasu Abba Acikin Masallaci Suna gaisawa Da Jama'a ya samu Kiran Yusuf Cike da Tashin Hankali Mallam ke Salati. yana Sauke Wayar ya Sanar Dasu Abunda Yusuf ya gayamai Wai Abdallah ya Fadi Awaje.
Da Tashin Hankali Su Abba da Baban A'isha da Mallam D'abarani Suka Fito Daga Cikin Masallacin, Dakyar Suka Kutsa Cikin Jama'a Zuwa Wajen da Abdallah ke Kwance yana Shure Shure.
Lokacin da Mallam yayi Tozali Da Abdallah Sai da Jikinsa ya kama Rawa Durkusawa yayi gabanshi yana Girgizashi lokaci d'aya yana Kiran Sunanshi,Hakama Su Abba na Tsaye Suna Salati.
Mallam D'abarani ne ya Duko yana kallon Abdallah kafin ya Sunkuya ya Tofamai Addu'a Sai yayi kamar Yabar Zabure zaburen sai kuma ya Cigaba da yi, Yusuf ne yana Sharan hawaye yace"Mallam mu kaisa Asibiti kalli Abunda Abdallah yakeyi..? Yafad'a yana Kokarin Dagosa Mallam D'abarani ne ya Dakatar Dashi Da Hannu yana Fadin"lalurarshi bata Asibiti bace, Shawara Dayace Ku Sanya shi Amota Mu koma Gida Sai Munsan Abun yi.."Yafad'a yana Kara Kallon Abdallah.
Yusuf Zaiyi Mgana Kenan Mallam yace"Ku Daukesa Kusashi Amota.."Yafad:a cike Da Dattako,Da Kuma Kokarin Boye Tashin Hankalinsa ba Musu Yusuf da Kamal da Wasu yan'uwa Suka Taimaka sukama Abdallah Rikon Talala Har Cikin Mota.
Shi kuma Mallam yaja Abba gefe dashi da Baban A'isha Yayi mgana dasu na Tsawon Minti Goma kafin Naga Sun Sarke Hannu Sunyi Musabaha, Abun mamaki Babu Wanda yabi Takan Asma'u amarya Da'aka Tsara cewa bayan Daurin Aure Za'a Wuce Da Ita, Ammh Saboda Abunda Yafaru Cikin Tashin Hankali motocin Bauchi Da Tawagar Angon Suka bar Kofar Gidansu Asma'u
Kafin kace Kwabo mgana tafara Yad'a Gari Da Dangi,Domin da Yan Daurin Aure,da Wanda yaji Lbrin Duk inda Suka Zauna Sai Sun Bada Lbri, Lbrin ya isa Cikin Gidan Abba Inda mijin Anty Rukayyah yafara Kiranta yana Tsegunta mata wai Ana Daura Aure Abdallah ya yanke Jiki ya Fadi Harda Kari, Jini Ta Hanci Ta Baki,yana Ta Zabure Zabure Kamar mai Kamun Hauka, Harda Ce mata Dama Yasan cewa Aljaniin Daya Aure Asma'u bazai Taba Barinta Tayi Aure ba
Umma Dataji lbarin ita da ya'yanta Yadda Ku kasan su Zuba Ruwa akasa Susha Saboda Murna Umma Fad'i Take, Dama Za'arina na baya yi Nasara ba, na yanzu ma Ai bazai kai Lbri ba Duk da ya juya kwanjinsa Harya Kafa Tarihin Dauramata Igiya ukun Da Na baya Suka Kasa,Hajiya iya kuwa Tana Ji Tafara Fad'an,wai dama Ta Fad'a Asma'u Bata da lafiya, gashinan Zata Kashe Dan Mutane.
Su Anty Amarya ne da Wasu Dangin Abba Suka Shiga Damuwa,Mama ma na Daki ita Da ya'yanta Suna Ta Maida Zencen yadda Mazajensu Suka Karanta musu.
Achan gidan Ammi kuwa Lokacin da Lbrin yazo a bakin Kawu, Asma'u na Uwar Dakin Ammi ne,Ammh Sai gata Ta bayyana Atsakar gida inda Kowa Ke Tsaye Cirko Cirko Ana salallami.
hannu Ta Ɗora Bisa Kai Idanuwanta na Zubar da Kwallah da gudu,ƙafafuwanta Suka Daina Daukanta Bata Da Wani Zabi Illah Zubewa kasa asume kamar Matacciya A'isha Dake Gefe Itama Tana Kuka Tayi kanta Ita da Sauran Kawayensu.
Ammi da Su Goggo Jummai Sai Sharan Hawaye suke Suna Tsananin Tsausayama Asma'u domin Hakika Taga Jarabawar Rayuwa..
Nan da nan Taron Biki ya Tsaya Cak aduka gidajen yatashi Daga Gidan Biki ya koma Gidan Koke,
koke, mussaman ma gidan Ammi, Asma'u ko Su A'isha Suka Shafamata Ruwa Ta Farfaɗo Tana Kuka, kuka mai Taba Zuciyar Mai Sauraro Tunani Take Acikin Ranta,Kila ita Kaddaranta Kenan,Yau gashi An Daura Mata Aure Ammh Kuma ga Duk alamu kila Dashi Kadai Zata Tsira, ba Wanda yace Tayi Hakuri ko Tabar kukan Data keyi Domin Am Mata Abun Kuka Gwara Ta Koka ko Ta samu Sauƙin Abunda Ke Damunta acikin Zuciyarta.
kowa ka gani yayi Tagumi,Abba ma Falonshi ya koma Shida Baban A'isha Suna Jajanta lamarin Wanda Kowa yakasa Dora Komai akan Faruwar Lamarin. Tunda ango Dai lafiya lau yazo,kuma kowa ya ganshi Ammh Abun da Zai Daure ma Mutane Kai Ana gama Daura Aure ya yanke Jiki Ya Fadi Shin Wannan Wani Irin murdaddan yanayi ne.
******
Karfe 3 da wani Abu na Rana Su Mallam Suka Shigo Bauchi, kuma Tunda ga Dutse har Zuwa Bauchi Abdallah na Cikin Wannan Halin.
Koda Motocin suka Shigo Haraban gidan,Gidan ya kacame da Hayaniyar yan Biki Da Kuma Tashin Waka ,Ashe su Anty Safina ne Suka Kunna Home Theater Suka Kai Falon Mallam Suna Rakashewa da Wakar Zee baby. Saboda kaucema Idon Jama'a Sai Mallam yace Su Yusuf Su Shiga da Abdallah Shashensa ta Kofar Waje,Shikuma ya Tsaya Suna mgana da Mallam Darabani inda Yake Sanar dashi Akwai Sihiri ajikn Abdallah bayan Kuma Bakin Aljanin dake Tare Dashi Wanda Shine Silar Faruwar Abun da ya Faru A Dutse.
Mallam ya Shiga Tashin Hankali kamar yayi Kuka,Mallam D'abarani yace kada ya Damu yanzu Zai Koma Gida ya Had'o magunguna yazo Da Kuma Wasu Daga Cikin Dabi'nsa don Da Bukatar sai aanyima Abdallah Rukiya,Dahaka Suka Rabu Duka Zukata Babu Dadi.
Suko Su Anty Safina Suman tsaye Sukayi ganin An Shigo da Baffa Kamar baya Numfashi, Kan Doguwar Kujeran Falon Suka Shimfidar da shi Yusuf ne ya Kashe Kid'an Dake Tashi yana Kallon Anty Nafisa yace"Ba kid'a bane agabanku Yanzu, Mikewa Tsaye zamu yi Da addu'a wlh Shegiyar Matar Baffa Bazata Taba barin shi ya Huta ba. yanzu Awajen Dauren Auren ya yanke Jiki ya Fadi yana Zabure Zabure."Yafad'a yana Kallon Abdallah Wanda Ke Wani Taso da kirji kamar mai Ciwon Farfadiya.
Hannu da Kirji gaba-daya Su Anty Nafisa Suka saka kafin Su Fashe da Kuka atare.
Durkushe Suke gaban Baffa Sai ga Hajiya Tashigo ita da Maman Fati Ana Rige Rigen Shigowa Hankalinsu Tashe,domin cikin jama'ar Dake Falon aka Samu wanda Yakai ma Su Hajiya Lbrin A dawo da Baffa kamar gawa.
Hajiya tada Tsorata Da ganin Baffa Ta Daga Hannu Ta Ɗora Bisa Kai kafin tace"Na Shiga Uku Ni Hajara,Yusuf meya Faru Da Baffa ko Hatsari kukayi..?Tafada cike Da Firgici Yusuf ne ya Sauke ajiyar Zuciya kafin ya Fara Basu Lbrin Abunda ya Faru ,bai gama karisawa ba Hajiya tayi kasa Zata Fadi Mallam da Shigowarsa kenan Yayi Saurin Tallafota cike Da Tashin Hankali yace"habiba Riketa muje ciki, kai Yusuf ka Rufe kofar Falon nan ta Cikin Gida ka Zauna da Abdallah bari na Kira Dr Nura yazo ya Dubata.."yafad'a yana So Yana Tsabar Jarumtarta Da Hanzari Maman Fati Takama Hajiya Tana Sharan Kwallah, suka Kaita Dakin Mallam,Shikuma Yusuf ya Kori Mutane yan bani Na iya Ya garkame Kofar Falon, yayinda Gefe Daya Su Anty Nafisa Keta Kuka, Kamal abokinsu Yusuf Kuma Ya Wuce gida Da Niyyar anjuma zai Dawo.
Tsawon Minti Talatin kafin Dr Nura ya Shigo Falon, Shima ya Shiga Tashin Hankali ganin Baffa cikin Wannan Halin,yaso ya tafi Dashi Asibiti,Ammh Mallam ya Hana Ganin lalurar bata Asibiti bace Hajiya kad'ai ya Duba yayi mata Alluran Barci Jininta ne yayi Bala'in Hawa Allah Ya Takaita Abun Sanda Zata Fadi An Riketa Da Yanzu Ta Fadi Shikenan Sai Nakasa kuma.
Maman Fati ke gefenta yanzu tun Tana Sharan Kwallah aboye Har Kukan Datake Boyewa ya Fito Sarari Duk kawaichinta game da Asma'u yakasa Boyuwa Kuka Take Tanayi tana Sharan Hawaye Mallam ne Dake tsaye ya Kalleta yana Fadin"Wai Habiba bazaki bar Kukan nan Haka ba..? Kuka bashi da Wani Amfani sai Cushe Zuciyata da kara Shiga Kunci Duk Abunda Kika ga ya Faru Rubutacce ne Daga Ubangiji Kuma An samu Nasara Tunda Ayanzu Suna Matsayin Mata da Miji da Izinin lahi bazasu yi Nasara a kanmu ba Zamu gayama Allah Shi zai mana maganin Komai.."Maman Fati na Share Kwallah Tace"Mallam Wani Hali Ma'u ke Ciki..? Nasan Cewa ba Kowa Bane Zai Fuskanci Abunda Ya Faru..? Ma'u tana Cikin Matsala Ni nasani Tun Lokacin ba ma ance Ita ke Koran Samarin ta Da kanta Toh inaga Sunga Abun ya Faru yau, gari Zai Dauka ne Dalilin Asma'u ne Komai ya Faru, Mallam ina Tsausayin yarinyarnan Tun Tasowarta Batasan Dadin Rayuwa ba Sai Wahala.."Mallam ya Sauke Ajiyar Zuciya kafin yace"Ki kwantar Da Hankali Insha Allah ba Abunda Zai Faru kamar yadda kike Tsammani Hakika Musulmi dama Shi ake Jarabta Kodon gwada Imaninsa, muciga da gayama Allah Insha Allahu Asma'u da Baffa Zasu Zauna karkashin inuwa Daya Watarana Su Zama Ababen Alfaharinmu su Da Ya'yansu..."Maman Fati Tace"Allah yasa Jikinta asanyaye kafin yace"Toh Mallam Shi Baffa Ahaka Za'a barshi baza'a kaishi Asibiti agani ba...."?
Mallam yace"Munyi mgana Da Mallam D'abarani yace Lalurar Baffa bata Asibiti bace, yanzu haka ya koma gida ya Hado Wasu magunguna,kuma zai zo da Dalibansa guda biyu don yace akwai bakin Aljani ajikin Baffa So Sai anyimai Rukiyyah.."Maman Fati Ta Dafe Kirji Tana Salallami Cikin,kuka Take Fadin"Oh ya Allah Wannan bawa Naka yaga jarabawa Allah Ka bashi Ikon Cinyewa ya Allah..."Take Fad'a Tana Sharan Kwallah.
Mallam na Gefe kanshi akasa,babban Rigar Dake Jikinsa Tana Salubewa ita kad'ai Saboda Tashin Hankali dayake ciki Hajiya Kuwa na Kwance Tana Barci Ammh Daga Ganin yadda Take Fitar Da Numfashi Awahale ne Kuma Cikin alamun Ciwo.
Har Wajen Mangariba Shuru Mallam D'abarani Ya dai kira Mallam Awaya ya Sanar Dashi Sauran Magungunar ne bai samu ba,sai yanzu Ammh gashinan Zuwa Bayan sallar Mangariba.
Yusuf dake Falo Tare Da Baffa Mallam ya Umarta Daya Tashi Su Tafi masallaci,Su Anty Safina su Zauna Dashi kafin Su Dawo, Yan Biki kuwa Tuni kowa ya Watse Sai Na Jiki Jiki kadai Suka Rage Kowa kagani yayi Tagumi babu Fara'a Daga Masu Salallami sai masu Sharan Kwallah.
Anty Zainab ce ta Fara Tashi Ta Shiga Tiolet ta dauro Alwala adakin Inda Hajiya Ke Kwance Maman Fati ta Fita Zuwa Shashenta Domin Tayi Sallah, ganin da Anty Safina Tayi kamar Yaya Baffa yadaina Shuren Daya keyi alamun ya Samu Barci ne yasa tace Nafisa Ta tashi Suje Suyi Sallah Su kafin su Yusuf su Dawo.
Suna Tashi Suka Ka Shiga Dakin Da Hajiya take Kamar Almara sai ga Abdallah ya Mike Kamar bashi ba, kansa ya Dafe yana Wani Numfarfashi Ware Ido ya Dinga yi kamar Wanda yake Neman Wani Abu Zabura yayi ya mike Yana Fadin"Wasila..."Cikin Fitan Hayyaci Aljihunsa Wandonsa ya Laluba yaji Walet Dinshi na jikinsa Bai Tsaya Wani Abu ba Yafice Da Sauri Kamar Wanda Zai Tashi Sama, Har yazo Ya Wuce ya Fita Daga Get din ba Wanda ya ganshi sakamakon Duka Suna masallaci Harda Ko Da Baba Megadi,Sauri Sauri Abdallah ya Dinga yi Har Yayima gidansu Nisa Kafin ya samu A daidaita yakai Shi Tasha.
in kukaga Abdallah Alokacin zakuyi Tunanin kamar Tabin Hauka ne ya Sameshi Domin kanshi Babu Hula Ƙafarsa ba Takalmi Wayarsa ma agida ya Barta Dagashi sai kayan jikinsa,Sai agogon Dake Daure Atsitsiyan Hannunshi.
yana Zuwa Tasha yayi Sa'a irin Doguwar Motarnan Zata Tashi Da Hanzari Ya Shiga Yana Sauke ajiyar Zuciya kamar Wanda Yayi Gudun Tsere duk wanda ya Kalleshi Saboda Zatinsa ba Wanda Ke Tunanin Bin Halin Dayake Ciki da Kallo Domin Afuskarsa Tana Cike Da kamala ne Sai Dai Fuskar nashi Ta Nuna Baya Cikin Natsuwarsa.
lokacin Da Motar Ta tashi Harda Sauke ajiyar Zuciya kamar Yaron Daya Dade yana Neman Nonon uwarsa Bai samu ba Sai yanzu, Gaba-daya Duniyar Batamai Dadi Babban Burinshi ya Isa Gaban Wasila ya Fadi ya Roketa gafara In ba Haka ba Jiyake Kamar Zai Mutu.
Su Mallam Suna Fitowa Daga Masallaci motar Mallam D'abarani na kawowa, Shida Wasu Dalibansa guda biyu,dauke da Kur'ani da Kuma Wani Abu mai Kama Radio.
basu Wani Tsayawa Gaisawa ba Suka Rankaya Suka Shiga Cikin gidan,sai dai me..? Suna Zuwa Falon Suga ga Wayam babu Abdallah A inda Yake Kwance Cike Da Mamaki Mallam yace"Ikon Allah ko Abun ya Sakeshi ne..? Yafada yana Kallon Yusuf Wanda gabanshi Ke Fadi bai Samu Zarafin mgana ba Su Anty Safina Suka Fito ganinsu Tsattsaye yasa Anty Nafi Tace"Lafiya kuwa Mallam..?
Cikin Fitan Hayyaci Yusuf yace"Ina Abdallah da muka barku Dashi..? Cike da Mamaki Ta Zaro ido Tana Fadin"Nan...nan muka barshi Anty Safina tace mu Shiga muyi Sallah Tunda munga kamar ya samu Barci ne ko Anty..? Tafad'a Tana Kallon Anty Safina Dake Raba ido.
Mallam da Zuciyarsa ta Tsinke Lokaci Daya yace"Yusuf duba Dakin chan kila yana Ciki.."Yafada cikin tsoron Abunda Zuciyarsa Ke Tunani
Da Sauri Yusuf ya Nufi Cikin Dakin Ammh Sama Ko kasa Babu Abdallah kuma ga kayansa Da Wayarsa nan bai Dauka ba,Wasa wasa dai An Nemi Abdallah Sama Ko Kasa an Rasa Mallam na Tsaye Sai da ya Zauna yana Fadin"Innalillahi Wa'inna illaihirraju'un..."Yafada Cikin Wata Murya Yusuf ko Tsawa da Masifa ya Shiga Durama Su Anty Nafisa yana Fadin meyasa Suka Barshi shi Kad'ai.
Mallam D'abarani ne ya Dafa Kafad:ar Mallam yana Fadin"Tabbas Hasashena ya Tabbata Aljanin Da'aka Turoma Abdallah Tafiyayyene. Anturo Shine Da Niyyar Dama Ya Rabosa Da Garinanan Zuwa Inda Tasirin Sihirin Jikinsa yake, Ammh Duk da Haka baza muyi kasa A gwiwa ba, Zamu cigaba da Gayama Allah Kuma Kuyi Hakuri Karku Tashi Hankalinku Da Izinin lahi Da Kuma karfin Ayar Allah Abdallah Zai Dawo Gidan nan Da Kafarshi karka Damu."
Mallam ya gyada kai yakasa Mgana,Maman Fati Da Shigowarta yanzu Kenan Daga Dakinta yanzu Suka Gama Waya Da Ammi Suna Janjanta lamarin Nan Take Sanar Da Ita Tunda Asma'u Taji Abunda ya Faru Take Kuka yanzu Haka Jikinta yayi Zafi A'isha da Anty Amarya Da Fahad Sun Kaita Asibiti Har ambata Gado Bisaga Umarnin Abba.
Maman Fati Tayi Kuka Wanda Batasan Iyakarsa ba,Tazo Ne Da Niyyar Tambayan Mallam ya Barta Ta tafii Dutse Gobe Ko Hankalinta ya Kwanta,Ammh Sai Kuma Tazo Ta Iske Sabon Lbri mai Taba Zuciya da Ƙwaƙwalwa.
******
Duka wad'anan Ahalin guda biyu ba Wanda ya Samu Runtsawa Wannan Daren Sai Irin Su Umma da Ya'yanta Wanda Abun yayi Musu Dadi Suna Ta Bada Lbri Suna Dariyar an gama musu karyan Dukiya da Arziki Toh yanzu sai Suga Feleke.
kilama Mijin Sakinta Zai iya yaga An kusa Kasheshi Sututai dai ba Ma'ana ballantana kan gado yadda Kukasan basu Hada Komai da Asma'u ba, Hajiya iya ko ajikita Tana Daki Kwance Tana Hutawarta. Mama Kuma ba Wanda Ke gane yanayinta Dama Ammh Ko yayane Ta Shiga Har Gidan Ammi Ta Duba Asma'u Harta Dafa Kanta tana Bata Hakuri,Anty Amarya ce Da Su Ammi ke Cikin Damuwa ba Kadan Ba.
Asma'u dai a Asibitin Doctor Sambo Ta Kwana bayan Zazzabin Jikinta Dayayi Zafi. Jikinta yana Kad'awa Tare Da Had'uwan Hakora Lokaci Daya Abba yace Akaita Asibiti Suna Zuwa Kuma aka basu gado, Saboda yadda Jikinta yayi Zafi Sosai,gidan Su Hajiya kuwa Zukata Sun Raunana Ba Wanda ya Iya Runtsawa saboda Damuwa Fargabarsu Daya Taya In Hajiya Ta Farka Zasu Bata Wannan Bakin Lbrin Basu Da Wannan Karfin gwiwan.
*****
Karfe 8am na Safe Abdallah ya Buga Get Din Makeken Get dinsa bayan ya Sallami mai Keke Napep din Daya Daukosa Daga Tasha Sai da Safen nan Suka Iso Kwana Sukayi Ahanya.
lokacin Da Inyamurin Megadi ya leko yaci karo Da Fuskar yallabai da Kansa Jiki na Rawa ya Bud'e masa yana gaisheshi Cike Da Mamaki ammh Ina Ko kallonshi baiyi ba Ya Rumtuma Cikin Gida Da Gudu yana Fadin"My Noory Where are u...? Plz come Out my Eyes Want To See u.."Yake Fad'a Cikin Halin Fitan Hayyaci Megadi dasu Samuel da Emeka Suka Bi Abdallah da Kallo Zuciyarsu Cike Da Tashin Hankali Had'e Da Mamakin Meya Faru Da Yallabai Haka ya Shigo Kafa Babu Takalmi kamar Wanda Akayi Wasan kura dashi Ya Kwace Dakyar.
*Janafty*