ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 22

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



   *🅿️22*


Wasila Dake Zaune Cikin Makeken Falonta Kafarta Daya kan Daya Tana ta Danne Dannen Waya Ko ajikinta gefenta Jamila ce Da Hafsat Suma Kowacce Na Kwance Ta Baje Tana latsa waya kamar amafarki Sukaji Muryan Abdallah Daga Waje yana Kwalama Wasila kira.

Zumbur wasila Ta Mike Ta fita Waje Da Sauri bayan Ta Wullar Da Wayar Hannunta akan kujera, Ganin Tafita Da Gudu ne yasa su Jamila Suma Suka Rufamata baya,domin Sunyi mamakin Yadda Wasila Ta Dawo Daga Bida Ranta fes kamar Babu Abunda Yafaru Nan ko Tasan Meta ta taka ne.

Tana Fita Suka Ci karo Da Abdallah yana Kokarin Shigowa Falon,cikin Wani Fitan Hayyaci Ya Rumgumeta lokaci d'aya yana Kamkameta kamar Wani Zai kwace Mishi Ita Fad'i Yake"Don't leave me my Noory I can Do Without u..."Yake Fad'a yana Tusa kanshi kan Dokin Wuyan Wasila Lokaci Daya yana Wani Lumshe Ido Kamar yaron goyen da ya jima bai ji Dumin mamansa ba.

Wasila Da taji Kamar Ansakata Acikin Aljanna Sabida Murna Da Farinciki Ammh Saboda Ta Gwada Abdallah da Kuma Kara Tabbatar da Tasirin Aikin Boka Dandugaji, sai Ta yi Saurin Kwace Jikinta Dakyar Tana Zubama Abdallah Harara, Cikin Fitan Hayyaci Yakara Nufarta Sai Tayi Azamar Matsawa baya Tana Fadin"Don't Touch me Abdallah I Hate u. ni zaka ci Amanata Ni Wasila Zaka yaudara? Ashe Aure iyayenka za su yi maka ammh Baka Sanar Dani ba kasa Kafa Katafi ko? Fine Yanzu Takardata Zaka Bani Na gama Zama Dakai I Swear"

Tafad'a Tana Wani Jijjiga Jiki ammh Gefe na Zuciyarta Cike Da Jin Dadi, gefe Daya Kuma Tana kara Sarawa Ma Aikin Boka Dandugaji ganin Yadda Abdallah yataho Ko Takalmi bashi Akafarshi.

Jin Abun Wasila tace Ne yasa Abdallah Rudewa Cikin Wani yanayi Dayake Ji kamar Yayi Hauka ya Durkusama Wasila yana Kama Kafarta Cikin Wani Amo yake Fadin"Karki min Haka my Noory Wlh Ba Kowa agabana Sai ke, Bazan Iya Rayuwa da Wata mace ba bayan ke ba. Kece Farincikin Abdallah In kika Barni Wlh Mutuwa Zanyi plz Kiyi Hakuri Gani gabanki Kiyi min Duk Hukuncin Daya Dace Dani."Yafad'a lokaci d'aya Kawai Sai ga Hawaye Suna Kwarayoma Abdallah ba Wasila kad'ai ba Hatta Su Jamila sai da Suka Zaro Ido ganin Abdallsh Durkushe yana ma Wasila Kuka.

Su Emeka ko kamkame Juna Sukayi shi da Jesepe Abun ya basu Tsoro Balle josepen daya Daura Hannu akai yana Fadin"Jesus."

Wasila kamar Tana Yawo Acikin gajimare saboda Farinciki Cikin Wani Juya ido Tace"Hukunci Daya Zan yankema maka Umarni nake Baka ba Shawara ba, Katashi Mu Shiga Ciki na Shiryaka Yau Nakeso Mu bar kasar nan Dama already yau da Safe Na Tura Emeka yaje Airport yamana Buking din Jirgi ZuwAa paris kuma Na Riga na Kamamana Hotel mai kyau da Tsari Ta Webset dinsu, so Zamu Tafi Chan Muyi Hutun karshen Shekararmu achan I hop kaji ni ."Tafad'a Tana Wani Kallonsa Kasa kasa.

Jikin Abdallah na Rawa Yace"yes mah.."yafad'a yana Mikewa Da Hanzari Wasila Tatafi Ta Rumgumeshi, Tana Fadin Tayi Kewarshi Shima matseta yayi yaana Share Kwallah kamar Wani yaro karami Suna Kamkame Da Juna Suka Shige Cikin Falon, yayin da Hafsa da Jamila Suka bi juna Da Kallo kafin Su Saka Dariya Lokaci Daya Suna Tafawa.

kafin Kuma Su Daure Fuska ganinsu Emeka na Kallonsu Suma Cikin Takun yanga Suka Shige Ciki Suka bar Su Emeka da Bude Baki.

Cikin Abunda Baifi awa Daya ba Wasila da Abdallah Suka Gama Shirinsu, Wasila ce Tama Abdallah Komai Ta Kuma Had'amusu kayansu, ta Umarci Emeka da yazo Ya Kwasa zuwa Mota Duk da basu Dibi Wani kaya ba Sai Abubuwan Da Ke da muhimmanci Sauran kayan Sawan in Sunje Zasu Siya Komai 

Zasu Tafi Wasila Ta Damka musu Hafsat Daya Daga Cikin Atm din Abdallah Tare Da Duka Makullan Mota Dana Gida, Harda Tarin Makudan Kudi Tace Yanzu Gida yazama Nasu Kafin Su Dawo So Suji Dadinsu Suma.

ihu Suka saka Suka Rumgumeta Suna Murna, Bayan Tayi Musu gargad'in kada Subar Wani Ahalin Abdallah ya Tako Mata gida.

Haka kuma ta Sanar Dasu Emeka da Megadi, Abdallah dai Na tsaye yadda Kukasan Rakumi da Akala Haka Wasila Ke Jan Ragamar Rayuwar Abdallah Tana Rike Da Hanunshi shiko yana Binta kamar Wani Dolo, Itako Tana Wani Taku Tana Yamutsa Fuska kamar Wata boss Haka Suka Shiga Mota Emeka ya Fice Dasu Daga Haraban Gidan Su jamila Na Daga musu Hannu cike da Murnan Gida yazama Nasu.

Suna Zuwa Airport Saura Minti Goma Jirginsu yatashi, Sai alokacin Wasila Ke Tambayan Abdallah Ina wayarsa yace Baisani ba,Ranta yamata Dadi Yadda Komai Zai Tafi kan Tsari Nan da nan Aka Fara Kiran Sunaye.

Har akazo kansu Ba Dadewa jirginsu ya Lula Sararin Samaniya Lokacin da Wasila Ta Kwantar Da kanta Jikin Abdallah Tana Mirmishin Mugunta Tace Afili..."Lokaci na Yafara Daga yanzu..."


*****


Sai da Asma'u Ta Kwana Uku a asibiti kafin a sallamota Ta Dawo Gida Ammi Ce Da Anty Amarya Ke kula da ita.

Goggo Jummai sun koma Tun jiya, cike da Alhini Aisha Kuma Ta Koma Gida sai dai Tana Kawo Abinci Tazo Ta Wuni Mama tazo Ita Da Umma Wacce Tazo ganin Kwakwaf Fuskarta Cike Da Annuri Ganin yadda Asma'u Ta Dawo Ta Rame Kamar ba Ita Ga Yawan Kuka da Zullumi.

Abba na Zuwa Kullum Shima Gwanin Ban Tsausayi Ranar Da'aka Sallamota Diret Gidansu aka Wuce Da Ita Allah Sarki dakin Datayi Tunanin Tayi Bankwana Dashi Ashe Da Sauranta Anan Tasake Komawa Asma'u Ta Daina Kukan Sarari Sai Dai na Zucci kawai Duk da ba Wanda Yakara Sanar Da Ita Sabon lbrin Batan Shi Abdallah Domin Maman Fati ta Kira Su Ammi Take Shaida musu, Hankali fa Sun Tashi Ainun Aisha ma Tayi Kuka Sosai koda yaushe Cikin Lallashin Asma'u takeyi 

Abba ko Mallam ya Kirashi Awaya yamai bayanin Komai ya Kuma Roke alfarma Dakatar Da Tarewar Asma'u har sai an karya Asirin Dake Jikin Abdallah Don yanzu Hakama Ranar da Suka Dawo ya Gudu Daga gida.

Abun yabama Abba mamaki Yana ta Salati Acikin Ransa yana Mamakin Mata irinsu Wasila,Ya gamsu da bayanin Mallam na Zaman Asma'u agida domin kartaje chan Babu Miji kuma Tashiga Wani Hali gwara Tana Gida In Komai ya Daidaita sai Asan Abunyi Shi Tsoron Abba ma Kada Shed'aniyar Ta illatamai Asma'u Duk da yana yabonta Wajen Kokarin Ibada Yaji kuma ya kara Tsausayama Abdallah Sosai Kuma Shima yayi alkawarin Sashi acikin Adduarsa.

Abba da kanshi yagayama Iya Abunda Ke Faruwa Agabanshi Sai Ta Nuna Kamar Ta Janjanta nan ko yana Tashi Tatafi Dakin Umma Ta labartamata.

Umma Taji Farinciki ya Saukar mata Dama Babban Burinta kada Asma'u Ta Auru Tafisu ta kare Rayuwarta agantali Ahaka Zata Tusama Habiba Bakinciki.

Tasan Karshenta ma Matar Tashi Ta sanya Abdallah ya aikoma Da Asma'u Da Takardan sakinta Murna Kamar ta Zuba Ruwa akasa Tasha,Ita ke gayama Mama Ita kam Ta Tsausaya Sosai.

Tunda Abun nan ya Faru Asma'u bata yarda Ta Fito ko kofar Dakin Kullum tana Kwance, Tana Tunanin Rayuwarta in tagaji Tatashi Tayi alwala ta Fara Karatun Qur'ani Tanayi Tana Kuka Gwanin Ban Tsausayi Abincinta Sai dai Su Baba Lami Su Shigo mata Dashi.

Anty Amarya ce ke lekota Sugaisa da Safe Ammh Banda Umma da Mama balle Hajiya Kunyartacciyar Tsohuwa.

Ranar Tana Jinsu Ta Fita Gaida Abba Umma Na Kofar Dakinta Ita da Anty Bilki Suna ganinta Suka Sheke Da dariya Har Umma na Fad'in kyama gaji Ki Fito ne Don Kila ma ya Sakeki Fad'ama na ne Ba'ayi ba.."Hajiya ko na Cikin Dakinta tace"Ina Zai iya, ke Jinin Habiba Fa Bala'i ne Sai Da Ladan Ya Saketa Gidan nan Muka Samu Lafiya ai Wlh Matarshi Tayi Dubara Gwara Data Rabasu Wlh.."Dakin Abba da Bata jeba Kenan Ta Koma Daki Tana Kuka Tama kasa gane kan mganarsu Domin ba wanda yagayamata ga Abunda ya Faru da Kuma Guduwar da Baffa yayi.

Sai Washegari ne Ta samu kiran Hajiya Wacce Mallam da Kanshi ya Sanar da Ita Abunda Ke Faruwa bayan Ta ji Sauki Ta Tambayi Abdallah, Hajiya tayi Kuka Sosai Kamar Ranta Zai Fita Tana Nuna Nadamar Kawo Shawarar Hada Auren Baffa Da Asma'u yanzu ga Abunda ya Faru nan,Haka ta Keta Rokon Maman Fati Gafara Maman Fati tace Bakomai Wannan Abun Daya Faru Rubuttaciyar Kaddara ne.

hajiya bata Kara Shiga Tashin Hankali ba Sai Da Mallam da Yusuf Suka Tafi porthercourt office dinsu Abdallah Suka Fara Zuwa nan aka Tabbatar musu daya na Cikin Hutunsa na karshen Shekara Wajen Sati Daya Kenan Rabonshi da office.

basu karaya ba Suka Nufi gidanshi nan ko inyamurin megadin nan ya Hanasu Shiga yace Madam Taba da Umarnin Kada Abar Wanda basu sani ba Su shiga. Ran Yusuf ya baci yafara Fad'a ammh Sai Mallam ya Hanashi 

suna Bakin get Su Jamila Suka Zo Sukayi Hon ya Bude Musu Shiga gidan suna Cikin pradon motar Abdallah.

Zasu Tafi kenan sai ga Emeka yadawo Zai Shiga gidan ya gansu Toh Dama yasan Yusuf lokacin Daya Taba Zuwa Wajen oga Shi Ya kaishi Airport ya Hau Jirgi Cikin girmawawa Emeka ke gaida su Mallam Suka amsa Fuskarsu ba Annuri nan yake Fad'amusu oga dashi da Madam basu Country Sun bar kasar Tun Wajen Kwana Hudu kenan 

nan yake Shaida musu oga ya Dawo Arude kamar baya Cikin Hankalinshi yana Ma Madam Wasi Kuka,kusan Inyamurin Mutum bayason yaga Wani Abu ya Samu Wanda Yake aiki karkashinshi Sunfi wasu musulmanmu Rike Amana.

Daga Mallam Har Yusuf Sun Jike da Mamaki had'e Kuma da Tsoro.

Haka suka Dawo Bauchi ba Wani lbri mai Dadi, Dama wayar Abdallah na Hannun Yusuf Tun Tafiyarshi ya Kasheta Domin bashi da Bukatar Kunnata.

Haka Suka Koma ma su Hajiya da Bakin lbari , wanda yakara Saka Hajiya Cikin Nadamar yin Tunanin Zasu Naasara akan Wasila Shine Ta Kira Asma'u Tana Kuka Tana Bata lbrin Wasila Tayi Nasaran Kara Rabasu da Abdallah Kuma Ta Gudu Dashi ,lbrin ya girgiza Asma'u Wanda Tana Zaune Ne Sai Da Mike Tsaye,Hajiya Na Bata Hakuri Tana Kuka,itama Kukan Take Cikin Zubar Hawaye Tace"Hajiya Kibar Kuka Don Allah Wlh babu komai Wannan Abunda Da Kikaga yafaru Rubutaccen Kaddara ne Daga Rabil Izzati Kuma Nayi miki Alkawarin Ni Asma'u bazan Karaya ba Insha Allahu Da Karfin Addu"a Hajiya sai Alkadarin Matarnan Ya karye Abdallah ya Dawo kamar yadda yake abaya Ko Fiyema Da Haka.

Sai ga Hajiya Dake Kuka Ta Dawo Dariya Tana Fadin"Allah Ma'u...Asma'u naji Dadi Insha Allahu Kece Uwar ya'yan Baffa, ke zaki zama sanyin Idanuwanshi Abun alfaharinshi Da Yardan Allah sai yazo yana mana godiyar Aura masa Ke Da Mukayi Allah ya inganta Rayuwarki Asma'u Allah ya Tsareki Allah ya sakama iyayenki da alheri Allah yayi Miki albarka Nagode Nagode.."Tafad'a tana Share Kwallah,kafin Ta yanke Wayar Saboda Kukan Dayaci karfinta. 

Asma'u Ta Sulale akasa Tana Kuka Lokaci Daya Tana Danne Bakinta karya Fito, Tsausayin Iyalin Proff na Ratsata,Tsausayin Abdallah ya kamata Taji kawai Tana kuka 

Ashe Haka Su Hajiya keji Lokacin Da Dansu yayi Nesa dasu..?kalli yadda Ta Dawo Saboda Kawai An Daura Mata Ya Jingine Ta,Bata Taba Sonshi ba Ammh Tashiga Gagarumin Damuwa Toh inaga Iyayenshi da Yan'uwanshi Musamman Hajiya Lalle Zama Bai ganta ba,Mikewa Tsaye Zatayi Da Addu'a Da Ibada Duk da Tana iya bakin Kokarinta.

Ammh Sai ta Dage Damtse Domin yakar Wannan matar ta Abdallah Wace bata da barbashin Imani Acikinta Ranta Lokaci Daya Taji karfin Gwiwa ya Shigeta ta Sanya Hannu Bibbiyu Tana Share Kwallarta Kafin Ta mike Da Hanzari Ta Nufi Wardrope Dinta Tafara Bincikan Wasu Littafan Addu'o'inta Dake Ciki Da Gaggawa.


********


Polina Kuwa Bayan Rabuwarsu Da Abdallah da Kwana 1 Ciwonta ya Tashi Wanda Daga Ita sai Kawarta Rabeca dake lagos sai Likitanta Wanda Ke Dubata Anan Asibitin Water Side Hospital parthercourt suka san Dashi

Polina Tun kafin Haduwarsu Da Abdallah Likitoci Tun Tana Lagos Suka Tabbatar mata Da tana Dauke Da Blood Cancer Wato Cancer Jini Kenan, Wanda Akwai limit Din da In yakai Ajikinta Zata Mutu.

Lokacin Tayi kuka Sosai Hartaso Tabar Harkar Bariki ammh Rabeca Taba Ta Shawaran In Tabar Bariki Watake Dashi Tunda Duka Iyayenta Sun Mutu Daga Allah Sai Harkan bariki ne Gatanta,Da Wannan Shawarar Ta Watsar Da Komai Ta Cigaba Da Watsewarta ammh Tana Zuwa Asibiti Time To Time Tana Karban mgunguna.

Haduwarta Da Abdallah Da Dawowarta Porthercourt Da Zama yasa Ta Sauya Asibiti da Likitan Dake Dubata, Rabeca Tayi Tayi Ta sanarma Abdallah polina Taki Tace Bazata Taba gayamai ba Kada Yatada Hankalinta Lokaci Kawai Take Jira Takusa Barin Rayuwar Abdallah ,Ammh bayan Itama Ta Taimaka mai,wajen Kwato shi Daga Hannun Shegiyar Matarshi Wasila wacce Babu Allah Acikin Ranta.

Ganin Halin Datake Ciiki ne yasa ta Daga waya Takira Rabeca Tace Tataho wacce Tataho daga lagos Hankali Tashe Domin Tun Suna Yara Suke Tare Da polina Sun Dauki Junansu yan'uwa Musamman ma polina Da Duk kudin Datake Samu Wajen Abdallah Tana Turama Rabeca Nata kason.

Bayan Tazo ne ganin Halin Da Polina ke Ciki ya Sanya Ta Kwasheta Zuwa Water Side hopital inda Likitanta Dr James ya Amsheta Ciikin gaggawa yana Fad'a Don Har polina Tafara Fitar Da jini Ta Hanci Ta Baki Saboda Ciwo.

Sai dai Ta Kusa Sati asibitin kafin Taji Sauki Su Dawo Gida lokacin kuma polina Ta dinga Kiran Wayar Abdallah akashe Abun yabata Mamaki kuma ya Dagamata Hankali Rabeca ne Ke Lallashinta,ganin An Wuni an Kwana bata Samu Wayar Abdallah ba Sai Ta Roki Rabeca kan Ta rakata Office Dinsu Abdallah Batayi musu ba Suka Shirya Suka Shiga Motarta Suka Tafi.

Suma dai bayanin da'akayi ma Su Mallam akayi Musu, Hankalin Polina bai Kara Tashi Sai da Sukaje Gidan Abdallah Suma Ko Shigen Inyamurin Megadin nan yahanasu Shiga Kuma Yaki amsa Kowacce Tambaya da polina Ke jefanshi Dashi 

Ranta ya baci Suka Shiga Mota Suka Koma Gida Polina na Jin Aranta Koma Me ya Faru Ta Tabbata bamai Dadi bane.

Da safe kawai Sai ga Emeka yazo Acikin Motar Abdallah,Dayake Jiya gaya Zuwansu,Nan ya Kwashe lbrin Komai ya Sanarma polina Harda Zuwan Iyayen Abdallah da Wulakancin da Wasila Tace ayima Duk Wani Ahalin Abdallah indan yazo kan Bala'i Polina Taji Bala'inta ya Tashi Ta Dinga Zazzaga masifa yarensu na Yarbanci Tana Gumduma ma Wasila ashar,Nan da nan Ta dauki alkwarin Sai Ta Nuna ma Wasila Ita karamar yar Bariki ce Zatayi Wannan Aikin Kodon Sakama Abdallah Da Abunda yayi Mata.

Washegari Ita da Rabeca Suka Hau Jirgi Suka Isa Birinin ikko Wajen Arnen Boka na Kan Dutse Wanda Yatabama polina Binciken Halin Da AbdallaH ke ciki, Suna Zuwa polina Ta Zayyanamai komai Nan Take yayi Wasu Tsafece Tsafecenshi kafin ya Zayyana musu polina mugun Asirin da Wasila Tayima Abdallah da auran da aka d'aura masa har da sunan Asma'u sannan ya fad'a musu yanzu Abdallah ya na yi ma wasila Kallon Uwace gareshi Sabida Tsabar Biyayyah

Polina tace Tana So Boka Ya Warware Asirin Abdallah ya Dawo Cikin Hayyacinsa,sai Boka ya Sanar Da Ita bazai Sabu ba Asirin bamai iya Warwareshi Sai Bokan daya Had'ashi Sai dai akwai mafita kwara D'aya Itace Sai Dai a sakema Abdallah Wani Asirin Wanda Zaiji Duk Duniya ba Wacce yakeson rab'a sai Asma'u Domin Inhar ya kasance da ita Toh Tabbas Dukkan Makarin Wani Asiri Zai Fara Warware Da kanshi.

Polina tace Indai ya Tabbatar Da Abdallah Zai Dawo Gida To ya aiwatar.

nan ko ya Shaidamata Da Gudu ko Zai Dawo Gida Kuma ya Nemi Asma'u Koda Cikin Fitan Hayyacine.

Da haka Suka Rabu da Boka Arnen Dutse Bayan Sun Cikashi Da Kud'i masu yawan gaske.





*Janafty*