ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 23
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️23*
*PARIS*
Abdallah da wasila dai Ana kasar paris, Ana jin Dadin Rayuwa Domin Tun Zuwan su garin bayan Sun Sauka hotel D'in Da Wasila Tayi Musu Buking Tun Suna Nageria da Suka Zo da kansu Har Airport Suka Daukesu Zuwa Cikin Hotel d'in.
Abdallah ya Zama Rakumi da akala Domin Wasila Kejan Ragamar Rayuwarsa Gabadaya ko Hajiya da Mallam baya Musu Irin Biyayyah Da yakema Wasila, Itako ganin Ta Samu Dama Sai Ta shiga Fito da Iskanci Kala Kala.
Tasha Saka Abdallah Kuka Yana Durkusa Mata yana Rokonta karta barshi,Bazai Iya Rayuwa Babu Ita ba, Itako Tana Barazanar Zata Rabu Dashi,In kuka ga Abdallah Sai Kun Tsausayamai Saboda yadda Ya Rame,yayi Kasumba gadai Kudi Da Jin Dadin Rayuwar Ammh Kuma sam Zuciyarsa ba Hutu
Kullum Sai Sun Fita Zaga Gari Sune Wajen Shakatawa,kanti kanti Ba Inda Basa Zuwa Kudin Abdallah Ko Sunyi Kuka Kamar Na Baitil Mali Haka Wasila Ke Facaka Dasu, Duniya Ta Bude Mata Sabuwa Gata Ta Kara Mallakan Abdallah akaro na Biyu. Kuma Babban Jin Dadinta yadda bashi da Waya a Hannunshi ba Wanda Ke Jinshi Ta Tabbata Ko Haka Tabar Su Mallam Ta Dand'ana Musu Bakinciki Fiye Da Wanda Suka Kunsa Mata.
Sai ma da Sukaje Chan Ta Siyamai Waya Da Layi Ta Bashi Nombarta ne Kadai Aciki,Domin Tace Abdallah Nata Ne Ita Kad'ai.
Wasila na Waya Da Momcy Suna Kara Jin Dadin Aikin Boka Dandugaji, Hakama Su Jamila Tana waya Dasu, sukuwa basu kaunar ma Su Dawo Sun Fi so Suyi ta Zama achan.
saboda In Suka Dawo Jin Dadin Su Zai Ragu, Abdallah ko na gefe Ko kwakwaran Motsi bai Isa yayi Ba In ba Da izinin Wasila ba.
Kamar Wani Dolo Haka ta Maidashi Komai sai dai Ya saka ido baya Iya Mgana,Wasila ce Uwarsa Itace Ubansa Domin Biyayyah yake Mata kamar wani bawanta Haka Zalika Yana mugun Shakkarta Da Tsoronta.
******
Bayan sati biyu.
Bayan Sati biyu a Lokacin Yayi Daidai Da Sati Hud'u Fa Faruwa Daurin Auren Asma'u Wanda Zuwa Lokacin Har Asma'u Ta Daina bayyana Damuwarta Sosai Bisa Yarda Su Ammi basu Barta Haka ba.
Balle Aisha da Koda Yaushe tana hanyar Zuwa wajenta duk don Taga Asma'un Ta Warware, Sai Dai Kuma alkawarin Data Dauka na Tarwatsa Wasila da addu'a Bata fasa ba.
Addu'a Take ba Dare Ba Rana Kullum bata barci Kwana Take Sallah Da Gayama Allah,game da Umma Da Hajiya iya Ta Daina Bi Ta Kansu Don Ta Lura Harda Jahilci Acikin Al"
Al'amarinsu.
Abangaren Su Hajiya ma Basu ba Zauna Sun Maida lamarinsu ga Allah, Mallam Dabarani ma Na Tsaye kai ga addu:a yace Su Mallam Su kwantar Da Hankalinsu Komai Zai Wuce.
Hajiya ce Dai Jiki ya Rikice Sai Ahankali, shine ganin Abunda yafaru Ga Asma'u Tana Zaune agida sai Mallam ya Kira Abba ya Rokeshi kan Ya bar Asma'u Takoma aikinta Zai Taimaka Wajen Debe mata Kewa Kafin Abubuwa Su Daidaita, zai kira chan Asibitin nasu yayi mgan Ba Gardama Abba ya Amince Kuma ya Kira Asma'un Da kanshi ya Sanar Mata,Hakika Taji Dadi Ko ba komai Zata Ji Kuma Kewa da Damuwa Zasu Ragun mata.
Ranar Data Koma aiki wai Taga Ruwan Habaici da Mgana Wajen Umma Da Hajiya iya Harda yan' anguwa Data Fito kafin Ta Isa Titi ta samu adaidaita sai da Ta Kusa kuka Tsabar yadda Take Shan Nuniya,wai ga Mai aljanun Amarya Da Suka Kashe Wanda Zata Daura Ranar Daurin Aure Haka Taji Wani Matashi na Fad'a daga Majalisarsu.
Bata gani Sosai Ta Tsaida mai adaidaita Har Ta kai bakin Asibiti Tana Tsiyayawan Hawaaye
Ko acikin Asibtin ma Da yawa Wasu Suna ta gulmanta don lbri fa ya bazu Ko'ina Sister bahijja ce Kad'ai Ta Tareta da Murnanta Duk Da Suna Wajen Sanda Abun ya Faru,Ranar dai Asma'u bata Wani Saki Jikinta ba Sister bahijja ce Ke Ta mata Fad'an Karta saka Damuwa acikin Ranta ba Wanda ya Isa yayi Abunda Allah bai yi ba.
Ranar dai bata saki Jiki ba Sai Washe gari kana Ta Warware ammh Kuma Tana jin Kunyar Kallon da wasu Mutane Suke mata.
***
Abdallah ne Kwance Bisa Makeken Gadon Hotel din Da Suke Ciki,Yayi Kwanciyar Rigingine.
yana Sanye Da Riga Da Wando blak and White masu kyau da Tsada Fuskarsa Tana Fitar da Wani Annuri Na kyau Da Zatinsa Sai dai kuma Ta bayyana Ramarsa
Mikewa yayi A kasalance Yana Rangaji ya Fad'a Tiolet ya sakarma Kanshi Shower Ko Kaya bai Cire ba, Idanuwansa Na Rufe ruwa na Zubarmai Yau Tsawon Kwana Biyu Kenan Kullum Ya zauna ko ya kad'aice ko ya Kwanta sai yayi Mafarki ya kebance da Asma'u Abun kamar Wasa Karamar mgana Ta zama Babba.
Domin Tun yana Danne Abun Har yanzu bazai iya Juriya Yana Jin In bai Kusanci Asma'u Azahiri ba Babu Abunda Zai Hana Bai Mutu ba, Wani Lokacin In Abun Ya Tsomai kamar yayi Tsuntsuwa ya ganshi agaban Asma'u yarinyar Da Bashi da Wani lbri Akanta Banda Sanin Dayayi An Daura Musu Aure Ammh Tunda ga Lokacin Baida Masaniyar Komai a kanta.
Gashi Wasila bata Da Niyyar Su Koma gida, Dazu ma Da Zata Fita Tace Yazo Su Tafi Yana Cikin Wani Hali na Bukatar ya jishi Ajikin Asma'u Shiyasa Yazama kamar Mara Lafiya ganinshi Kwance Ne yasa tafita ta barshi bayan yace Mata baya Jin Dadi.
Kwata Kwata Tsoron Wasila yake ji Bazai iya Gayamata Abunda Ke Damunshi ba, Kuma bawai basa Making luv da Wasila bane No,Sunayi Ammh Wannan karfin Disire dayake Ji Ta na finKarfin Hankalinsa gani yake Kamar bashi ba Tamkar Wani ne Ke Sarrafa Rayuwarshi.
Da Wannan Tunanin Yayo Wankan Tsarki ya Fito,yana zuwa ya Shafa mai ya Sauya kaya, laluben Inda Zaiga pasport dinshi Yashiga yi Allah ya bashi Sa'a yagani Cikin Wata yar Jakar Wasila Indan Allah ya Taimakeshi Tare Da Duka ATMs Dinshi Bai Dauka ba sai ya Zari na First bank Tare Da Kuma Diban Kudaden garin Wanda Suka Chanza Shida Wasila, Wayarsa ya saka acikin aljihu ya Fice Daga Hotel din cikin Sassarfa kada Su Ci karo Da Wasila.
Airport ya Nufa yaje yama kanshi Buking din jirgin da Zai Koma Nageria Aranar, yaci Sa'a ya samu Wanda Zai Yada Zango a lagos ne batare Da Bata Lokaci ba Cike Cike ya Tabbata. Cikin Abunda Baifi awa Daya ba Jirgin ya Tashi Daga paris Zuwa Nageria Kuma Dama Jirgin na yawo ne,Yan kasuwa ne Aciki Mazauna Nageria da Jajayen Fata Masu Huldar Kasuwanci A nan Gida Nageria.
Lokacin da Suka iso Jirgin bai yada Zango ako'ina ba sai A Filin Jirgin murtala muhammed International Airport lagos, Wajen Misalin Biyar na yammah yana Sauka ya Kara Neman Jirgin da Zai Tafi porthercourt ya samu Sai dai Kuma sai wajen 6 na yammah Aiko Hakanan Abdallah ya Jira ammh yadda Kuka san yana Kan kaya ya Kosa yaganshi yana Cikama Asma'u aiki shine Agabanshi yanzu Domin Ji yake Kamar Ana Zazzagama jikinsa Wuta Saboda Azalzalar Da Kuma Muradin Asma'u.
Shida da Wani Abu na yamma Jirgin yatashi bai Diresu ako'ina ba sai International Airport Porthercourt, Suna Sauka Ya Fito Daga Filin Jirgin ya Tari Taxi dama Tun a lagos ya Ciro Kudi Daga Asusun Bankinsa, Bai Diresa ko'ina ba sai anguwar Elelewo akuma Kofar get din gidanshi Ya Fito yabama Mai Taxi kudinshi Shi Kuma ya Karisa Jikin get din yana Duba agogon Fatan Dake Hannunsa 9 na Dare Daidai ajiyar Zuciya ya sauke Lokaci Daya Yana Tunanin yau komai Dare Sai Ya Isa Dutse.
Buga get din ya Shiga Megadi yazo da Wata Fitilar mai bala'in Haske bayan Kuma Hasken Kwayayan gidajen Dake Wajen Sun Haska ko'ina Cikin katuwar Muryansa Yake Fadin"Who is Dat...? Haushi Ya kama Abdallah Cikin Tsawa yace"Common Jare open d Door..."Jin kamar Muryan Oga yasa Ya Bude Kofar ammh Duk da Haka bai yarda ba Sai dai yakara Haskashi cikin Mamaki yace"Oga na u..? Tureshi Abdallah yayi Ya Shiga Gidan yana Fadin"Am not..,where is Emeka..? Emeka...? Ya Tambaya Lokaci Daya yana Kwalama Emeka Kira.
Emeka da Samuel dake Dakinsu Zaune Suna cin abinci Sukaji Kamar Muryan oga da Gudu Suka Fito Illai ko Shine Zubewa Sukayi Suna gaisheshi Bai amsa ba Illah Binsu da kallo Daya keyi Lokaci Daya Kuma yana Karema Gidan Kallo Kamar ma babu Kowa agidan,vkanshi ya Dafe Kafin yace"Bring d car Now..."Yafad'a yana Kallon Emeka da Hanzari ya Mike Dama already key din Motar na Hannunshi Ta Wajen Samuel ne Su Jamila Suka Fita Dashi.
Shiko Motar oga kiri kiri yake Hanasu Key har kararshi Sun kai Wajen Wasila Taku mayi alqawarin in Tadawo Sai yagane Baida Wayau Tunda Ba Motar Ubanshi bane.
Tuko Motar yayi Zuwa gaban Abdallah Shi Kuma ya Bude Gidan Baya ya Shiga Kafin ya Sako kanshi ta glass yana Fadin"Kada ka kuskura ka fad'a ma wani na dawo kaji ko.? Yafad'a yana kallonsu Samuel da Hanzari Suka Daga kai Suna Fadin'Yes Sir..'kad'a Kai yayi Kafin ya maida Kanshi ya jingina jikin Kujeran Motan yana Fadin"Go..."Da Hanzari Emeka ya saki Hon megadi ya Bude Musu Suka Fice Da Gudu Sai da Suka Dau Hanya ne Kana Abdallah Ke Tambayan Emeka yasan Dutse yace ya sani Abdallah yace Toh Chan zasu Emeka yaji Mamaki Dutse adaren Nan Tabdijam Su da Isa Sai da Safe duk ko Da Gudun Da Zasuyi.
*WASHE GARI*
Sun Shiga garin Dutse da Misalin karfe 7:30am na Safe Duk da Uban Gudun Da Suka Kwana Sunayi Ahanya,afarkon gari Suka Tsaya Abdallah yayi Sallar Asuba,da Sauran Sallolin da Suka subu cemai Jiya.
Abdallah bai Dawo Daga Zurfin Tunanin Daya Shiga ba sai da yaji Emeka na Tambayanshi Ina Suka Nufa gashi Sun Iso Dutse, Nan fa Gizo ke Sakar Domin Abdallah bazai Iya gane Hanyar gidansu Asma'u ba,Shuru yayi yana Tunanin Mafita gashi Baida Nombarta baida Nombar Kowa Balle yakira Cikin ikon Allah Sai Yusuf ya Fad'omai Arai Domin yana Da Nombar Hajiya Da Mallam akansa ammh Bazai iya Kiransu ba.
Nombar yusuf ce Ta Rage Wacce ya Haddace Da Azama ya Fito Da Wayarsa ya Cire Layin da Wasila ta Sakamai na Chan ya karyashi ya saka Sabo wanda ya siya Ya latsa Nombobin Yusuf ya Doka masa Kira.
Yusuf na Shirin Fita Aka kira wayarsa Ganin Babu Suna yasa ya Daga yana Fadin"Hello...."Daga Chan Bangaren Abdallah yace"Hello Yusuf Abdallah ne."Da Hanzari Yusuf ya zaro ido yana Fadin"Wani Abdallah...? Wai Baffa ne...? Yafad'a Cikin Fitan Hayyaci Zainab dake Had'amai Tea dataji ya ambaci Abdallah Tabar Abunda Takeyi Ta zubamai ido.
Cikin Dauriya Abdallah yace"Eh Ni ne" Yusuf ya Jinjina kai Cike Da Mamaki ammh akasan Ransa Godema Allah yakeyi Kafin ya samu Zarafin mgana Abdallah ya Rigashi Da Fadin"Plz Yusuf taimakonka Nake Nema nombar Yarinyar nan zaka Taimaka Ka Turomin.."Cike da Mamaki Yusuf yace"Wata yarinya...? Sai da Abdallah ya Dafe kai kafin yace"Asma'u."Yusuf ya Yi Jagale Kafin yayi mgana Abdallah ya Katse Wayar Zainab ya Kallah Wacce ta Kwalalomai ido Neman karin bayani
Hanunsa ya Tura Cikin Aljihun Wandonsa Kafin yace"Abdallah ne ya Kira wai Na Turamai Nombar Asma'u." Zaro Ido Zainab Tayi kafin tace"Alhamdulillah...Allah yasa Alkadarin Shegiyar matar Nan nashi ne ya karye."
Yusuf yace"Ameen Bani Nombar nata Na Turamai.."Da Hanzari ko Zainab Ta Dauko Wayarta Ta Bashi Nombar Asma"u ya Turama Abdallah.
kafin ya fita Sai Da ya Gargad'i Zainab da karta sake Ta Fadama kowa ,Tace Insha Allahu ba Wanda Zata Fad'amawa
*******
jiya Aikin kwana Asma'u Tayi Misalin karfe 8 da wani Abu na Na Safe.
Sun gama Round Dinsu Ita Da Sister Bahijja, Suna Had'a Kayansu Taji Wayarta Dake Cikin Jaka Tana Kara Da Hanzari Ta Fito da Wayar sai Taga Bakuwar Nomba bata Daga ba Har ta yanke Jakarta Ta Rataya Wayar Na Hannunta Suka Fito Ita da Sister bahijja Daga Cikin Asibitin.
Suna Tafiya kafin Su isa Get Aka sake Kira Ta Daga wayar Tana Fadin"Assalamu Alaikum...."Daga Chan Bangaren Muryan Ta Daki Abdallah Cikin Muryan Kasala Ammh mai Cike Da Haiba yace"Wa'alai kumus Salam..."Dam! Asma'u Taji Gabanta ya Fad'i Tsayawa Tayi Kawai Batare Data cigaba Da Tafiya ba Kallonta Sister Bahijja Tayi Sai Ta Mata alamaa da Hannu Da zata tafi sai ta ta kad'a mata kai kawai Ta Wuce.
Jin Shuru na Wasu Mintina yasa Abdallah yayi karfin Halin Fadin"Kina ina ne yanzu.? Cikin Rud'ewa Da Son Gane Muryan Waye Asma'u tace"Wa..waye...? Mirmishi ya saki yana Cije baki kafin yace"Abdallah ne..."Ras!gaban Asma'u ya Fad'i Taji kafafunta Sun Fara Rawa Bata Samu Damar mgana ba yace"Ina Garinku Kina ina ne yanzu ina Son Haduwa Dake.?
Dif Asma'u taji Kamar Ta Daina ji,Jin Shuru ya sanya Abdallah yace"Hello kina jina.."Dakyar tace"Ina...ina Asibitin Da ni ke aiki..."
Kai Tsaye yace" Wani Asibiti? Cikin Fitan Kalamai Asma'u Tace"General Hospital..."Katseta Yayi Da Fadin"Ok ki Fito bakin Get Ki jirani gani nan Zuwa ok ."Da kai Ta amsa Saboda Bakinta yayi Mata Nauyi Katse Wayar yayi Lokaci Daya yana Umartan Emeka Dasu Tafi General Hosptal Din garin.
Asma'u kuwa Dimuwa Ta Shiga Bayan ya Katse Kiran Tana Bin Wayar Da Kallo Gani Take Kamar Amafarki ba Gaskiya bane,Abdallah ya Kirata..? Kuma yace Gashinan Zuwa yana Son Ganinta...? Koma Menene Taji Dadi Tana Kuma Fatan Allah yasa Addu'arsu Ta karbu Ameen.
Da Hanzari Ta Karisa Bakin Get Din Asibitin Ta Tsaya Tana Wurga ido Gefe Daya Tana Kara Kokarin Gyara zaman Jakarta Dake Rataye A kafad'arta.
Kurama Titi Ido ta yi tana so taga ta Ina Abdallah Zai Bullo.
*Janafty*