ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 26

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_



*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


  

     *🅿️26*



Karfe 7:30 pm na Dare Suka Isa Bauchi Lokacin har an sallame Sallar mangariba Hon Emeka ya zuba akofar makeken get din gidansu Abdallah Da Gudu megadi yazo ya wangale musu get din Suka Sulala Ciki.

 Asma'u wacce ke Kwance Bisa Kirjin Abdallah Tun Barowarsu Dutse Ya Dan Fara Shafa Fuskarta Yana Fadin"Husna...mun iso.."Dakyar Ta Bude ido Jin Mota Ta Tsaya ne yasa Tace"Mun iso ne yaya Abdallah...?

 Kai ya Daga Mata Kafin yace"Yes sarkin Barci Mai kuka Tana Barci Kuma." Yafad'a Da Sigan Zolaya Tura Baki Tayi kafin Ta Balle Murfin Motan Ta Fito Tana Rike Da Jakarta Shima Abdallah Fitowa yayi Megadi Daya Fahimci Abdallah ne Da Gudu ya Kariso yana Gaisheshi Ya Amsa Fuskar ba Walwala kamar ba yanzu yake Mirmishi ba.

Asma'u bata Tsaya ba Ta Nufi Cikin Gida Tana Tafiya Ahankali Saboda Rauninta Domin Kowa Tayi Tafiya da Sauri Sai Taji Zafi.

Sallama Ta Doka A babban Falon Gidan Wanda Babu Kowa sai Karan Talabijin,Shashen Mallam Ta Kalla Taji Shima Karan Talabijin Din Daga Barayinsa Ta Fara Taku Zuwa Shashen Hajiya sai ga Maman Fati Ta Fito Daga Shashenta Zata Shashen Falo Sukayi Kicibis Da Ma'u.

Cike da Mamaki Take Kallonta Kafin Tace"Ma'u...? Asma'u kanta Na kasa Tace"Na"am Mama...!"

Baki Maman Fati Ta Kama kafin Tace"Na Shiga Uku Daga Ina Kike Da Wannan Daren..? Kuma baki Kira waya Kince Kina Tafe ba..? Mirmishi Asma'u Tayi Kafin Tace"Bani kadai bane Mama Tare Muke da ya Abdallah yana Waje."'Ido Maman Fati Ta Zaro Cikin Mamaki Kafin Tace"Wani Yaya Abdallah..? Ko Baffa kike Nufi..? Kai Asma'u ta d'aga  Zata sake Mgana Kenan Sai ga Abdallah ya Sawo kanshi Falon bayan ya Umarci Megadi daya Sauki Emeka adakinshi Kafin Zuwa gobe.

Maman Fati Da Mamaki da al'ajabi Suka Mamayeta kasa Mgana Tayi Banda Kallon Ma'u lokaci Daya Tana Kallon Abdallah Kamar Wacce Ta Warke Makanta, Mirmishi Abdallah yayi yana Karisawa Kusa Da Ma'u Ramkwafa yayi yana Fadin"Mama..."Sai Kuma Rauni ya Shigeshi yayi Shuru idanuwansa na Chanza Launi Ai sai Maman Fati Rikoshi Ta saki Murya Tana Fadin"Hajiya Mallam Ku Fito Kuga ikon Allah Kuzo Kugani Kai Allah Abun Godiya..."Take Fad'a Tana Shafa Fuskar Abdallah.. 

Hajiya Dake Zaune Cikin Falonta Tana kan Darduma bayan Ta iddar da Sallar mangariba Tana Addu'o' kamar amafarki Taji Muryan Maman Fati Tana Kiran Sunanta Dana Mallam,Da Hanzari Ta Mike Ko Hijabin Jikinta bata Cire ba Ta Fito Da Gudu 

Hakama Mallam da Sauri ya Fito yana gyara Zaman gilashin Idonshi Domin Lokacin yana Karatu ne Haka su Fati ds Mahmud Dake Daki Suna Homework Suma Suka Firfito Sai Dai Duka Tambayoyin Su Hajiya ya Makale ne Lokacin da Suka Ci Karo Da Abdallah da Ma'u.

Mallam Kurama Abdallah ido Yayi yana Kallonsa Hakama Hajiya Maman Fati ne Take Fadin"Yanzu Naga Sun Shigo Wlh Shida Asma'u..."Tafada Tana Bayyanar da Murnanta, Hajiya Cike Da Hawaye a idanuwanta Ta Kurama Abdallah ido kafin Ta Kada kai Ta Juya Da Hanzari Abdallah ya Taka Zai Bita Mallam ya Dakatar Dashi Da Fadin"Kai Abdallah..."Waigo yayi Idanuwansa Sun Koma Jawur Ganin Mallam Tsaye yana Kallonsa yasa ya Tafi Da Gudu Garesa Ya Fada Jikinsa Lokaci Daya yana Kuka yake Fadin"Mallam in kuka ki Yafemin Wlh Zan Kara Lalacewa Rayuwata Zata Shiga garari Fiye Dana Baya, Yafiyarku agareni da Addu'anku Gareni Ita Ke Rike Dani har yanzu Mallam,Don Allah ku yafemin Bani da Masaniyar Abunda Yafaru.."Yafada yana Jin jijiyoyin kanshi na mikewa Bayansa Mallam yake Bubbugawa Alamuun Lallashi kafin yace"Karka damu Mu iyayenka ne Bazamu taba Gudunka ba, Mun yafemaka ko Itama Ta Yafemaka bacin Rai ne Karka Damu anjuma kadan Zata Sauko, naganka da Asma'u ina ka Daukota.."Dago Kanshi yayi kafin yace"Agidansu Mallam,Na Dauko Tane Ta tare Agidan Mijinta Domin na Nuna Muku na Chanza Na Fara Daawowa Abdallah na na bata.."Mirmishi Mallam ya Saki kafin yace"good News..Masha Allah,Allah ka Shiga Tsakani Nagari Da Mugu.."

Yafad'a yana Dafa Kafadan Abdallah kafin ya kalli Asma'u yana Fadin"Habiba duk kawaicin ne, Kinbarta a Tsaye..."Yafada yana yar Dariya da Sauri Asma'u Ta gaisheshi Maman Fati ko batayi mgana ba Ta Wuce kichen Tana Fadin"Bangane ba,ai gidan ba Bakonta bane.."Mirmishi Asma'u Tayi Kafin Ta Nufi Shashen Maman Fati Mallam da Abdallah Suka Bita Da Kallo.

Mallam ne ya Katse Abdallah Da Fadin"Kaje ka bama Mahaifiyarka Hakuri ka Sanar da Ita ga Ma'u ka Daukota nasani Zatayi Farinciki."Gyada kai Yayi kafin Cikin Sanyi Jiki ya Fara Taku Zuwa Shashen Hajiya,Mallam yabi Shi Da Kallo Har ya Shige Baya ya Koma yana Fadin"Alhamdulillah...."

 Da sallama Abdallah ya Shiga Bedroom din Hajiya sai ya Sameta Zaune gefen Gado Tana Share Kwallah Karisowa yayi ya Durkushe agabanta yana Kallon ta Kafin ya Riko Da Duka Hannayenta yana Fadin"plz Hajiya Forgive me...Kina min Kuka So Kike in Shga Bala'in Fiye da Wanda Na Shiga abaya...? Kiyi Murna Abdallah ya Fara Dawowa Ainihin Abdallah Mahmud Azarensa Hajiya ga Ma'un ki chan Naje Har Gidansu na Daukota Gobe zamu Tare agidanmu Hajiya i promise u zan Rike Ma'u Da Amana inna Cutar Da Ita Daidai da Rana daya Allah ya Mata sakayyah.."Yafada Cikin Muryan Rauni..

Hajiya na Kuka Ta Mike Ta Dago Abdallah Ta Rumguneshi Tana Fadin"Ban taba Rikeka araina ba Baffa,Kullum Tsakani na Dakai Addu"a ne akan Allah ya Kwatoka Daga Hannun Wannan Shedaniyar Matar naka, Na yafemaka Naji Dadin Dauko Ma'u Dakayi Baffa Allah ya albarkaci Aurenku gobe da Safe sai Ku Koma Gidanku Tunda yanzu Dare Yayi.."Saboda Murna Baffa Baisan Sadda yayi ma hajiya kiss agefen Kumatu ba Keyarsa Ta Make Tana Dariya Shima Yar Dariyan yake kafin ya Fito da Wayarsa yana Kira Nombar Ma'u.

Asma'u Wacce Idar da Sallarta kenan Na la'asar din Data Kubcemusu da mangariba Tana Zaune Tana azkar Maman Fati na Gefe Tana gyara kayansu Fati ammh Rabin Hankalinta na Kan Ma'u Wacce Take Kallonta Cike Da Farinciki da Murna Rayuwar Ma'u yafara gyaruwa,wayar ma'u Tayi kara Wacce Ke Cikin Jakarta Jikinta asanyaye Ta Tashi Tana Tafiya ahankali Ta Isa Inda Jakarta yake Maman Fati na Binta da Kallon Mamaki ganin Ma'u na Gwale kafa kamar yar koyo.

Tana Fitowa da Wayar Taga Nombar Da Abdallah ya Kirataane Da Safe Tana Dagawa Yace"Kizo Mamanki na Nemanki Husna..."Mirmishi Ta saki kafin Tace"Na idar da sallah ne ganin nan Zuwa.."Ok yace kafin Su yanke Kiran Tahowa Tayi Tana Duba wayar ahannunta nan Ta Tarar da Missd clls ba adadi na Aisha Harda Na Fahad sai na Ammi Dana Anty Amarya Mirmishi Tayi Domin Tana da Tabbacin Aisha Taji lbrin Komai, Kallon Maman Fati Tayi Bayan Ta Ijiye wayar akan madubin Dakin Take Fadin"Mama zani Shashen Hajiya mu gaisa.."gyada mata kai Maman Fati Tayi Ita kuma Ta Fara Taku Zata Fice Maman Fati Tace"Asma'u..."

Juyowa Tayi Tana Fadin"Na'am Mama..."Maman Fati Ta Hade Rai Tana Fadin"Zo nan..."Ba musu Ta Nufeta Lokaci Daya Tana Tsarguwa da Irin Kallon Da Maman Fati Ke binta dashi Kusa da Ita ta Durkusa ahankali Tana Cije baki, cikin Manyantaka Maman Fati tace"Meya sameki kike Tafiya kina gwale kafa..? Gaban Ma'u ya Fadi Ta Sadda kai Tana Wasa da gefen Hijabinta Sake Kallonta Maman Fati Tayi kafin Tace"Magana nake..? Nace meya sameki kike Tafiya ba Daidai ba..?

Tafad'a Tana kara Hade Fuska,Cikin In ina Asma'u ke fadin"Ba...bakomai...mama.."Tsura mata ido Maman Fati Tayi Duk Tasan Halin yarta ammh kasancewarta Uwa gareta Dole Ta Lura da Komai nata Cikin Dauriya tace"Abdallah yayi miki Wani Abu ne..? Kunya Takama Asma'u Ta sadda kai kafin Ta gyada Kanta,Dan Mirmishi Maman Fati Ta saki kafin Tace"Baki Shiga Ruwan Zafi bane..? Kanta na Kasa Tace"Na Shiga..."Rausayar dakai Tayi Tana Fadin"Ok Shikenan Tashi Kije Kidaawo Ina Jiranki.."Da Toh Ma'u Ta amsa kafin Ta Mike Ta Fice Daga dakin Maman Fati Na Binta da Kallon burgewa.

Tana Zuwa Hajiya Tatashi Ta Rmugumeta Cike Da Farinciki Falo Hajiya Taja Hanunta Suka Fito Ganin Abdallah na salla Adakin Hajiyar,Haka Hajiya tataasata da Godiya da Nasihu Tare Da Rokonta Alfarma Ta Dage Wajen Ganin Abdallah ya Daina wasa da Ibadarshi sunanan Zaune ya Fito ya Nufi Shashen Mallam,Sun Kusa Kai Wajen Awa Daya Suna Hira da Hajiya kan Ta Mata sallama Tatafi Shashen Mamanta bayan Ta sanar da Hajiya Zata Dawo.

Tana Zuwa Already Maman Fati Ta Riga Ta Hadamata Ruwa mai Zafi Tana Shigowa Tace Maza Ta Tube ta Shiga Tiolet ta sake Gasa kanta,Kunya na Cin Asma'u tamike Ta Shiga Tiolet din Kuma taji Dadin Ruwan Da Dade Tana Gasa Jikinta Kafin Tafito koda Ta Fito Maman Fati bata dakin Rigar Jikinta ta Maida Tunda Duka kayanta na Mota.

yunwa taji Tana ji Sai Ta Hada Tea tasha Kafin Ta kwanta Bata koma Shashen Hajiya ba ganin Dare yayi Maman Fati Kuma Tana shashen Mallam,cikin su Fati Da Mahmud Ta Shige bayan Tayi Addu'ar barci Ta Shafesu Wayarta Takashe sai gobe zata Kira Aisha Suyi mgana 

Bata kara saka Abdallah a idonta ba Sai da Safe dataje gaida Mallam,Ido kawai ya sakarmata yana Kallonta Ita kuma sai Taji kunya Dakyar ta gaisheshi ya amsa yana kara sakarmata Ido kasa kasa.

wanka kad'ai Sukayi bayan sun Karya Su Mallan Suka Tarasu Suka yi musu Nasiha Sosai Kafin Su Umarce Mamman Daya Tukasu zuwa gidansu bayan Mallam yabama Abdallah Key din Gida.

sanin Baizo da kaya ba Sai ya Diba kayansa Dake Nan aka saka amota bayan Ankwashe Duka kayan Asma'u daga Motar Abdallah Zuwa na Mamman, kafin su Tafi sai da Abdallah ya sallami Emeka yace ya Koma porthercourt Shi Ba yanzu zai Dawo ba,bayan ya Kuma gargadeshi Da Karya Kuskura ya sanar da Wasila Inda yake,akwai Amana Sosai tsakaninshi Dashi ya Tabbatarmai Da Cewa Insha Allahu ba Wanda zai Fad'amawa 


Babu Rakiyar Kowa Asma'u Ta isa Muhallinta Tayi Mamakin irin Dukiyar da'aka Narkamata bayan Kuma Abba yabata Sadakinta A hannunta yace Hakkinta ne,Data Fadama Mamanta sai tace taje ta sakasu abanki.

Ita da Abdallah Suka Shigar da Duka akwatunta ciki bayan Sun sallami Mamman, Shi ya Taimaka mata Suka Share Inda yake da Kura Tunda yaga Bata Jin Dadin Jikinta,suna gamawa Sukayi Wanka Abdallah Kwanciya yayi Saboda ya gaji Ita Kuma Ta Fito Falo Da Wayarta Ahannun Tana sanye Cikin Riga da Sikat na Atamfa cikin kayan Akwatunta ne Ammi ta Kira Su ga gaisa Inda Take sanar da ita Tana Gidanta addu'a Ammi Tayi ta kwararama Ma'u kafin Su yanke Kiran Anty Amarya ta Kira Sukayi mgana sai Kuma Ta Kira Abba shima Suka gaisa cikin kunya Tace gata adakinta albarka yayi ta sakamata.

Aisha ce Ta Karshe Wacce Tana Daga Kiran Tafara sakin Guda Tana Shakiyanci Dariya Ma'u Keyi Tana Kara Jin Kaunar Aisha, Aisha taji Kamar tayi Kuka Dadi Sanda Asma'u ke Sanar da Ita gata yau Zaune adakinta na Aure Ihu Aisha ta saki Kafin Tace Don Allah Ta Hau Wsop yanzu Zata Kirata Video call.

Asma'u na Dariya ta kashe Ta Shiga chart bayan Ta Bude Data,nan da nan ko Sai ga Kiran Aisha da Azama Ta daga Suna kallon Juna,ihu Aisha ta saki Tana Hawayen Dadi Ganin Asma'u zaune Acikin Falonta Tana Hawaye Take Fadin"Komai nada Iyakarsa Rabin Raina i cant belive yau kice Zaune Adakin kanki. Wlh Bansan Irin Murnan da Zanyi ba Rabin Raina Ina Tayaki Murna Shiga Sabuwar Rayuwa Allah ya Kawo Sanadi Nan da Wata Tara.."Tafada Tana Share Kwallah Itama Asma'u Sharan Kwallah Take Tana Fadin"Wlh Rabin Raina Nima na kasa yarda Ashe Zanga wannan Ranar.."Dariya Aisha ta saka Kafin Tace"Realy kila ma Kin Kara Zama amarya Angonmu ya More ko.."Harara ta makamata kafin Tace"Uwar morewan..'Tafad'a Tana Dariya Shewa Aisha ta saka Tana Fadin"Shegiya Wlh karya Kike Daga ganin idonki kinsha Wuya,.."Asma'u Tace"Ai ni ba Raguwa bace Irinki Banza Babu Abunda Kika Fahimta Tafada Tana Dariya Aisha tace"Ke wai Ina Cute and Handsome Mijin naki Kinfa nasan Naga Hotonshi Wajen Fahad Tunda ganan Nasan Rabin Raina Tayi Nesa Baki Da Tsara Tawan.."

Asma'u tace"Yana Ciki ya Kwanta ne," Dariya Aisha Tayi kafin Tace"'Ah lalle Dole yayi Ramuwa Nasan Kawar Tawa ba Dama"

Zaginta Asma'u tayi kafin Su Cigaba da waya Tana bata Lbrin Abunda Hajiya iya da Umma suka Dinga Cewa Sanda Abdallah yazo Daukanta ammh bata sanar da Ita Zuwansu Hotel ko bakomai Wannan Sirrinsu ne Ita da Abdallah 

Sun d'au Tsawon Lokaci kafin Su yanke Kiran,Itama Ma'un barci ne a idonta nan Kan kujera ta Kwanta nan da nan barci Mai Dadi ya Kwasheta.


******


Achan paris kuwa Wasila Hauka ne Kadai batayi ba Ga wayarta Ta Lalace Sanda Ta Bugata Da Kasa, Sai da Ta Fita Ta Siyo Wata Wayar Kana ta Kira Momcy ta Samesta.

nan ko Ta Fashe mata da Kuka Tana Sanar da Ita Abunda Ke Faruwa Cikin Tashin Hankali Momcy Tace"Na Shiga uku ni Kudirat Yaushe akayi haka..? Wasila na Kuka Tana Shaidamata Wajen Kwana Uku kenan.

Ashar Momcy ta Dankaramata Kafin tace"Kuma don Ubanki kika kasa Kirana ki Sanar dani, Toh Uban me ya Zaunar dake baki Dawo mun Koma Wajen Boka ba Tunkafin Komai ya Dagulemana."Wasila na Kuka Take Sanar da Momcy ga Abunda yafaru bata Taho ba,ajiyar Zuciya Momcy ta Sauke kafin Tace"Ya illahi..kai Abu Duk ya Dagule lokaci Daya Nima Nan Ina Cikin Damuwa Domin Abbanku yafara Chanzamin karki Damu Gobe zanyi sammako Zuwa Wajen Boka.."Da Haka Suka Rabu Da Wasila Duka Zuciyoyinsu ba Dadi Duk da Momcy Ta Tsorata da Lalacewar Abubuwabsu Lokaci Daya ammh bata karaya ba 

Washegari nayi Tayima Gidan Boka sammako sai dai Kuma Lbrin Dataji Wajen Boka bamai Dadi bane Domin Tana Shiga Bukar Boka ya saki Dariya yana Fadin"ki koma inda Kika Fito Domin bani da Abunda Zanyi muku. kun Manta Sharadi na nace Kada Ku bari ya Kusanci Wannan yarinyar ammh Bakuji ba, Toh komai ya lalace Ku Koma Gida Kujira Lokacin da zaku Amshi Sakamakon ku Ahannunku,Kuma kada Ku sake Ku bari Ku Had a Ido Dashi Duk Tsiya karku bishi Inda yake Ku Dakata Ku jira har yazo Inda Kuke In Kukayi Gangancin Zuwa In da yake Zaku Tozarta Domin a Halin yanzu Duka Sihirin jikinsa Ya warware Domin Iyayensa Sun Taimaka Wajen Karya wasu Haka Kuma yarinyar Itama Ta Taimaka wajen Karyewar Duka Sihirinshi Kuma Indai Yana Tare Da Ita Har Abada Ba Sihirin da Zai Kara kamashi...."Yafad'a yana Kecewa Da Wata Dariya mai Firgitarwa yana Fadin"Ki Fita ki barnan...kuma karki yi Tunanin Zuwa Wajen Wani Boka ba'a Hada aikina da Wani Yin Haka Tamkar Karban magijin Lalacewarku ne Dake da yarki Na Har abada..."yafada yana Wani Shakuwa kamar mara Hankali.

Jikin Hajiya Kudirat na Rawa Ta Fashe da Kuka Tana Fadin"Ka mana Rai Boka Don Matsayinka Karka bari Komai ya lalace nasan zaka iya.."Dariya ya saka kafin yace"Dama kun zauna ne Kuna Cin Duniyarku Da Tsinke Kun Manta akwai Ranar Karban Abunda Kukayi...? Hahhahha...Toh Kunyi Kuskure Ko Ni nan Da Kika ganni Nima Ina Jiran Karshena Ne Domin nasan bazatayi kyau ba Aljannah ko Kamshi ta bazamu Ji ba sai dai Don Rahamar Ubangiji,Baku Dogara da Allah ba sai da Mu,Mukuma sai muyi amfani Da Wannan Damar mu kara Dilmiyar Daku,Ki Fice Kibani Waje Karki Kara Zuwa Inda Nake Kuje ku Jira Sakamakonku ."Yafad'a Yana Dariya Da Gudu Hajiya Kudirat ta Fice Daga Bukar Tana Kuka.

Saboda Tashin Hankali bata iya Gayama Wasila komai ba ,Kawai Cemata tayi Ta Kokarta Ta daawo akwai matsala Jin Haka yasa Hankalin Wasila yaTashi,Dama gashi Ta Rame ba ci ba Sha sai Kuka.

kwana Biyu Tsakani sai ga Samuel ya Kirata awaya yana Sanar Da ita Jamila da Hafsat Suna kwance Dukkansu ba Lafiya,Rudewa Wasila Tayi kamar Ta Zaune Momcy ta Kira ta Gayamaawa Jin Haka yasa Ta Shirya Ta Nufi gidan Wasila sai dai Hankalinta ya Tashi na ganin Yadda Hafsart Ta Dawo kamar Kwarangwal Saboda Ciwo jamila ma Ta Jeme bata Komai sai Amai Cikn Tashin Hankali Momcy Ta kwasheshi Sai Asibiti,Momcy Suma Tayi gau Sanda Likita ke Sanar Dai ita Hafsart Ciwon HIV kanjamau ne Yaci Jikinta Domin Ta Dade Dashi Ita Kuma Jamila Tana Dauke Da Ciki har na Tsawon Wata Hudu.

Haka Momcy ke Kuka Data Farfado Kamar Ranta zai Fita Tunaninta Shikenan Komai yazo karshen Komai yana Zuwa musu Daki Daki,bata iya Sanarma Wasila Har aka sallamosu Su Daga Asibitin Toh mezata musu Komai ya Faru Dasu itace Sila Domin Ita Ta Wargaza Rayuwar ya'yanta da Kanta.

Kwana Daya Dawowarsu Daga Asibiti Alhaji Armaya'u ya Kirata yana Masifa Kuma yace Duk Inda Take Ta Dawo Gida,jin Muryansa Cikin Bala'i yasa Bata Tsaya Ba Ta Koma Bida Cike Da Tashin Hankali Ta barsu Hafsat Su Kadai Cikin Halin Ciwo.

Sai da Wasila Ta kara Sati biyu Kana Ta Dawo Nageria bayan An Bude Filayen Jirage, Abunda Tazo Ta Tarar yasa Jininta ya sake Sama Momcy ke Sanar Da Ita Abunda Ke Damunsu Jamila,Uwa uba Kuma ga Wani Tashin Hankali Babansu Jiya sai da ya Barta Kwance Saboda Duka ya Kwace Duka Abubuwan Daya Mallaka mata.

Yanzu Hakama yan'uwanshi Aure Zasuyi mishi,ya Kori Duka yan aikin Gidan,Ya Kulle Store Abinci sai yaga Dama yake Bata Ya Kulleta Acikin Gida Bata Da Halin Fita,Ga Kuma Abunda Boka ya Sanar Da Ita.

Ihu Wasila Ta Dingayi Tana Fadin"Never..it can Be..."Kamar wata Zararriya,Kuka Tayi Kuwa Kamar Mahaukaciya, Jamila dake Dama dama ne Take Tayata Kukan Hafsat ko Tana Kwance Ko Iya Tashi batayi mai Imani bazai Iya Kallonta ba Saboda Wasu Kuraje Da Suka Feso mata ba kyan gani,Wasila Bata ji Gargadin Da Momcy Ta Mata ba,Ta Kudiri Niyar Bata Zauna Rayuwarta Ta Kare ba,Tasan Wani Boka a hanyar Maiduguri nan Ta Daka sammako Washegari Samuel ya Kaita taje Tana Kuka Tanamai bayani nan yace Karta Damu Ta bada Kudin Aiki Ta Koma gida Wannan Karon sai Abdallah ya zama Tamkar Karenta,Da Murna Ta Zubemai Kudi Kafin Ta Koma gida bakin cikinta ya Ragu Kuma Batare Data sanar da Momcy ba.

Wasila Ta Kira Emeka da Samuel Ta Turkesu kan Su Sanar da Ita Ina Abdallah yake,Nan suka ce basu sani ba Kirkiri Emeka yaki Fada Wasila Ta Birkice Tana Tsorata Cikin Dare Duk Sanda Ta Tuna Abdallah ya Kunsanci yarinyarnan Haka zata Dinga Ihu Tana Faman Zage Zage.

Polina Kuwa Tagama Duka Shirinta na Barin Rayuwar Abdallah,Tagama Hada Duka kayanta Tayi alkawarin Harta da Motar da Abdallah ya Siyamata baza tatafi Dashi ba,Ita da Rabeca Ne Zasu Koma lagos.

bayan Tagama Rubutama abdallah Wasika Ta Hada da Key din Gidan daya Siyamata da key din motarshi Sai da Suka gama parking din komai Rabeca Ta Fita Ta Kira musu mai Taxi ya Kwashesu Suda kayan bayan Polina Ta Rufe Gidan Direct gidan Abdallah Suka Nufa Don Emeka ya sanar da Ita wasila is back so Tana Son Kafin Tatafi sai Ta sanar da Wasila komai Taji Da Kunnanta Ta kuma Sanar Da Ita Itace Mganinta Tunda Ita Bata da Imani.







*Janafty*