ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)
Chapter 28
*ZAMAN GIDANMU*
_(Mai cike da kunci)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*🅿️27*
Suna Zuwa Bakin Get din gidan Suka ma mai Taxi mgana kan ya Jirasu kad'an Su Shiga gidan nan Su Fito, shiko yace ba Damuwa Su Shiga Su Fito Indai bazasu Dad'e Sosai ba polina Tace Ka daDamu yanzu Zasu Fito
Wannan Karon Shegen Megadin bai hanasu Shiga ba Tunda Madam Tadawo Harara Polina ke Sakarmai Sanda ya Bude musu karamar Kofa Suka Shiga gidan.
Domin da farko Tayi Niyyar Wlh Da yahanasu Shiga sai Ta Nunamai Ta Fishi zama yar Bariki, Duk da Polina bata Taba Zuwa Gidan ba ammh Tayi mamakin Girman Gidan Abdallah Sosai Haka dai Suka Karisa Shiga Kofar Da Zata Sadasu da Kayatattacen Falon Gidan Ita Da Rabece Wacce ke Sanye Da Wata Figilalliyar Riga Wacce Da Kad'an Ta Wuce Cinyoyinta, Sai Gashin Attachement Wanda Ta bazoshi sai Wani Combos dake Kafarta.
Polina Kuwa Tana sanye da Wani Karamin Wando ya Matseta Wanda Ko Cinyarta bai gama Rufewa ba sai Wata Riga Bata da Tsawo ko Cibiyarta Bata Rufeba, Irin Mai Daurewan Ta Wajen Ciki,kanta ya Sha kitson Attachement kanana kafarta Sanye Da Wani bakin Takalmi Sawu Ciiki kamar na masu aikin Gona.
Fuskarta babu Fara'a ko kad'an Don yadda Take Tafiya ma kad'ai Zaka Fahimci AShirye Take.
Wasila na Zaune a falon Tana kan kujera Ta Zabga Tagumi da Hannun Biyu, Duk ta Rame ta Kwarjane Kamar ba Wasila ba
yau kan nan ba Attachement Ainihin Gashinta ne mai Kama da Hammatar Dan Iska ko Fakin bazai yi ba, Jamila na Kwance Akasa Chan gefe Tana bin Sanyin Tayels Wasila Data kalleta sai Taji Kamar Tatashi Ta yankata Saboda Bakinciki.
Abun da yake Karamata Haushi Na Yarda Jamilar ke Tsirtar da yawu Duk ta Kazanta Falon, Don ma Tana saka Josepn yana gyarawa,ammh Abun na Bata Haushi Kuma Tayi Tayi Ta Sanar Da ita Wanda yamata Ciki ammh tace Bata sani ba ammh Wlh Bazata Yarda Da Iskanci ba Asibiti Zata kaita Azubar da Cikin, Hafsat ko Tana Daki bata Fitowa saboda Yadda cutar ta bayyana ajikinta Abubuwa Goma da Ashirin Suma Wasila yawa Tana ta Zuba idon Ganin Abdallah ammh Shuru.
Babu ko Sallama Su polina Suka Shiga Cikin Falon Domin basu iya ba,Wasila Dake Zaune Tayi Tagumi Ta Dago Tana Kallonsu Ciikin Mamaki kafin tace"Plz su waye ku...?
Polina tayi Mirmishi Tana bin Falon Da kallo ayatsine Gefe daya Kuma Rabeca ta Samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Tana Taunan Cimgam.
Jamila Dake Kwance Ta Dago Tana Karema Su Polina kallo Wacce Ta nufi Inda Wasila Ke Zaune baki Bude Tana binsu da Kallo Tana Zuwa Tadaura Kafarta Daya Kan kujeran Hartana Taka Yatsun Wasila Cikin Kallon Banza da Tsana polina tace"U bitch Ashe Tsafin Bokan Naki na Karya ne Da Iskanci Tunda Bai Taba Baki Lbrina ba.." kun san Dayake polina tayi Zaman lagos so Sun zauna da Hausawa ba laifi Sun Ji Hausa
Baki Wasila Taka ra wangalewa Kafin ta Furta"Bo...boka...? Bakinta na Rawa Cike da Gadara Polina tace"Yes...dat wht i mean, Shegiya mara Imani Nazo ne na sanar dake Koni Wacece Bayan Na baki Narrative din Story din Nice Mganin Iskancinki Don Ubanki.." Tsorata Wasila Tayi Da Yanayin polina ganin yadda Take Mata mgana Daga gani Ta fita Bariki.
Rabeca Dake gefe Tace"Common ki mareta ne may be zata Fi gane bayaninki.."Tafad'a Tana Dariya Wasila Taji Tsoro ammh Sai Da Dake Ta Mike Tana Fadin"Bangane me kuke mgana akai ba plz Su waye ku...? Polina tayi Dariya kafin Tace"Am polina by Name Kuma ni Karuwar Abdallaah ne mijinki Since 4yrs muna Tare Dashi Tun bayan Auranku Wanda baki K'ullashi Ta Hanyar Allah ba da gaskiya ba" ta fad'q lokaci daya tana Jifanta da Wani Kallo.
Jikin Wasila ya Fara Rawa Cikin Fitan Hayyaci Tace"No na laya...I know my Dee bazai Taba Cin Amanata Ba karya Kuke Kafuran Banza.."Bata Karisa ba polina ta Kasheta Da Wani Gigitaccen mari Har sai Da Ta Koma Kan Kujera Ta Zauna Dafe Da Kunci Tana bin polina da Kallo, Wacce Ta Fiddo Wayarta Ta binciko Hotunan Da Suke Dauka da Abdallah Wani Lokacin ma Babu kaya ajikinsu Sai Blanket Da suka Rufe Da kasansu da shi Nuna mata Polina keyi Tana Wucewa gasunam Kala kala Iya kallonka.
Wasila ta Zama Out of Control Saboda Tashin Hankali bata samu Zarafin mgana ba Polina Tace"Mijinki Abdallah yamin komai a rayuwata ,Shegiya Bariikin ko na Banza ne Kina nan Kina Haukan banza Shi yake Dauke Da Nauyina ya Siyamin Mota da Gida Anytime ya Fita office muna Tare, ammh dayaa ke Mumu ce ke,mummmunar Fuskarki har Cikin Zuciyarki ne,Ke Kina Takamar Ke yar iska ko..? Toh Yau Kinga Wad'anda Suka Fiki iskanci da Bariki, Nice nan na Kirawo Abdallah ya Dawo kasarnan kuma yaje ya had'u Da Matarshi Domin bani da Wani Buri na kafin Na bar Rayuwar Abdallah Naga na Tarwatsaki kuma Thank god Kin Fara gani Daga yanzu Zuwa Wani D'an wani Lokaci Zaki Ci Ubanki sai Kin Yi yawao Tsirara Atiti Goat." Tafad'a Tana Huci.
Wasila Data Ji Wani Tashin Hankali da Bakin ciki Sun Ziyarceta Ta Mike Da Sauri Ta Cakumi Wuyar Polina tana Fadin"Never. Sai na Kasheki yanzu nan Tunda Kikayi Sanadiyar Lalatamin Aikina Kika Kuma Raba.."Bata karisa ba polina ta Dauketa da Mari Rabeca Data Taso Ta saa Kafa Ta Kwasheta Ta Fadi basu yi Wata wata ba Suka Tarun mata Suna Duka Kamar Allah ya aikosu Tun Wasila na Ihu iya karfinta Harta Daina.
Jamila ko Dake gefe ganin Abunda Ke Faruwa Ta Rarrafa da Tafiyar Maciji Ta Shige Daki Domin Yadda Take ganinsu Rabeca Manyan Yan Duniya ne Tsab Itama zasu Had'a Da Ita Su Jibga Tana Shiga dakin Hafsat dake kwance Tana maida Numshi Tana Tambayan Ihun Wa Takeji Jamila tace"Anty Take Shan Lakada Wajen Wasu Yan bariiki, Nafara Tunanin Anty da Momcy Sun Fara girban Abunda Suka Shuka.."Hafsat bata kara mgana ba sai Nishi Take Sama sama.
Su Polina ko basu bar Dukan Wasila ba sai da Suka ga Ta Kusa Daina Motsi kana Suka Barta Suka Mike Suna Haki Da Kafa Polina ta Shure wasila Kafin Ta Dau wayarta Data Fadi Gefe Sanda wasila ta Shaketa.
Ficewa Sukayi Daga Falon Suka bar Wasila na Maida Numfashi Sabida Wahala, Ta daku fa ba karya Domin Ko Yatsanta Bata iya dagawa Saboda yadda Su Rabeca Suka Daki Hallita.
Suna Fitowa Suka ciro da Emeka dawowarshi Kenan, basu Wani Tsaya Wata mgana ba Polina Ta Mikamai Takarda da keys din Mota dana Gida tace ya Tabbatar ya Damkama Abdallah Indan ya Dawo. Sanin Mai Taxi na Jiransu yaasa Suka Fita da Sauri Allah ya Taimakesu mai Taxin yana Da Hakuri ammh yace zasu karamai Kudi Suka ce Sun yarda Tasha ya kaisu Suka sallameshi Inda Suka samu Motar da Zata kaisu Birnin ikko Domin anan Suka Had'u da Abdallah ammh Wannan Karon babu Wanda yasan Inda Zata Koma.
Wasila Dake Kwance Tana Kuka Muryanta Bata Fita So Take Tatashi,ammh Takasa Cikin Ranta Ja masu Polina Allah ya isa Kad'ai Takeyi ammh Sabida Karfin Hali bata fara Nadamar Abunda Ta Aikata ba.
sai ma Tunnin Ta koma Wajen Boka na Chan Maiduguri Tamai bayanin Har yanzu Shuru babu Abdallah ba Dalilinshi,Tana Bukatar Asake Mata aiki Domin Haryanzu Tana ganin Akwai sauran Dama.
******
BAYAN WATA DAYA
Bauchi.
Hausawa Sunyi gaskiya da Suke cewa Soyayyah Ruwan Zuma kasha Kaba masoyi.
Domin Tsantsan Soyayyah mai Had'e da Kauna Son Juna,Tattalin Juna.kula Da Juna, Kafa kafa da Juna,Hade Tsantsan Fahimtar Juna Shike gudana Tsakanin Abdallah da Asma'u.
Acikin Wata Dayan da Suka Shafe Suna Hutunsu Azahirin gaskiya Kowa ya Fahimci Hallayar Dan'uwanshi Barin ma Asma'u Wanda Ta Fahimci Abdallah Is a Nice person.
Wata irin Soyayyah yake Nuna mata mai Tsayawa Azuciyar masoya,Ga Uwa uba Natsuwarsa da Kamalansa ga Tsausayi ga Mutumta wanda ya Ke Tare Dashi Shiyasa kada ka yankema Mutun Hukunci Daga Haduwar Farko Batare Daka Zauna Dashi ba, da Wad'anan kayawawan Dabi'un nashi ya samu Nasaran Samun Zuciyarta Koda yake Miskili Marason Hayaniya agabanta Dabam yake,Bai Tsabbatarma Kansa Tun ganin Farko yafara son Asma'u ba sai da Hajiya ta Zaunar Dashi Tabashi Lbrin Asma'u Daga Farko Har Karshe Allah Sarki Husnanshi Ashe Taga Rayuwa, Tundaga Lokacin ya Ninka Kulawar Dayake Mata He alwys Treat Her Like A Queen,In Kuka ga Asma'u bazaku ganeta ba She Change At all,Ta Yi Kiba Fatar Jikinta Ta Murje Takara Fari alamun Tana cikin Kwanciyar Hankali.
Su Anty Safina sai Dai Sukaji lbri Daga sama Sun sha Mamaki da Murna basu yarda sai da Suka Zo Suka gani Hakama Yusuf da Zainab Sunzo Sun Kwana Daya sun Koma.
babu Inda Abdallah Ke Zuwa Shike Zagewa ya Shiga Kichen ya Taya Husna Girki Domin Tun Farkon Tarewarsu Su Hajiya Suka Fara aiko Musu Dashi Asma'u Ta Hana Tace Zata Fara Girki wannan ne d First Time da Abdallah yaci Girkin Matarsa Wasila Kuwa Baitaba Ganin Ko Ruwan Tea Ta Dafa ba, Kullum sai da Josepen Yayi Shine Kuku bayama Tunanin Ta iya.
A yanzu Abdallah ya gama Dawowa Cikin Hayyaci Domin Duk Wasu Sihiri Dake Jikinsa Sun Gama warware,Shi Har mamaki yake Tayaya ya Auri Wasila..? Domin bata acikin Tsarin Irin Macen Dayake Muradi sam. Asma'u tayi amfani da Wannan Damar Takara Gyara Rayuwar Abdallah da Ibada,don yanzu Ko Tsayuwar Dare Zatayi Tare Dashi Suke yi sai Asuba Suke komawa bayan Sun Idar da Sallah.
Suna Fita yawo in Suka gaji da zama,ko Suje gidan Hajiya Su Wuni sai Dare Su Dawo Ko Kuma su Fita Su Sha ice cream ko Kuma Ranar akwai Suki Yin girki Su Fita cin Abinci Hankalinsu Kwance.
Dakyar Yakaita gidansu Anty Safina Tayi Musu Wuni Domin baya son Abunda Zai Rabashi Da Husna Domin Ta Riga ta Zama jinin Jikinsa
Tun kafin Suyi Shirin Komawa porthercourt ya gudanar da Wani Aiki ya Tafi bankunan dayake da Asusun banki dasu ya Chanza Atm da Passaword dinsa Domin Tunda yadawo Cikin hayaccin yagane Irin Barnanar Da Wasila kemai da Dukiya sai ya Dauki Mataki Kana ya Kira Emeka awaya yace Zai Turomai kudi Yaraba Biyu Rabi yabama Josepen Rabi yabama Samuel Duk yace Su Koma garinsu ya sallamesu bawai Don Sun mai Laifi ba No sai don Abdallah yanzu ba Irin na baya bane na yanzu He is already Back To his Sense.
Suna kuka Suna komai Suka Karb'a Suka Tafi Domin Samun Irinsu Abdallah a uban gida sai An Tona, Daganan ya Umarci Emeka daya Karbi Duka Keys din Motocin Gidan Wanda Ke Hannun Samuel Ya Rike a Hannunshi Kada ya Kuskura Ko Wasila Tamai mgana ya Bata ya amsa Da Toh. Aiko Illai Wasila dake Cikin Matsanancin Tashin Hankali Ta Turke Emeka akan ya gayamata da Wani Dalili Yazo ya sallami su Samuel Hala Shi ya Daukesu Aiki? Ko kallonta baiyi ba Don Abdallah yace Komai Zatace Kada ya Tankata Kawai Lokaci yake jira.
Wasila Ta Fara Zargin Abdallah ne ya sakashi Hankalinta yaTashi batasan Wani Hukunci Zai yankemata ba inya dawo Gashi babu Mota balle Ta Koma Gidan Boka ga Hafsat jikinta na Kara Zafi ba Kudi Domin Taje Banki Ciro Kudi daga Abu yaki Cirowa Harda Kokarin Shiga Banki Takai complain Aiko Dakyar Tasha don Anso Kamata amatsayin Barauniya.
Ta Dawo Gida Tana Kuka ga Momcy ba'a Samunta awaya Domin Dad dinsu ya kwace Komai yayi Aurenshi yan'uwanshi Dama Kullum Addu'a Suke akanshi Toh yanzu Allah ya Kwatoshi Shiyaasan Basu damu da Halin Da Hajiya Kudirat ke Ciki ba,Wacce Dad dinsu ya Maidata Boysquaters,Sai tayi kwana biyu ba Wanda ya Bata abinci Tana Cikin Ukabar Rayuwa Gashi tana Bukatar Jin Halin da Wasila ke Ciki.
Bangaren su Umma Kuwa Dama Hausawa Sunce Hassada gamai Rabo Taki ne, Domin Umma kam Tashiga Halin Bakin ciki Da Tarewar Asma'u Duk da ba Haka Taso ba Domin Duk Watsewar Auren Ma'un Umma ce Ke Shiga Tana Fita Har Abun ya lalace yadda bata Kaunar Habiba Tun Farko haka Ta Tsani Ma"u bata Kaunar Taga Taci gaba.
Hakama Hajiya iya wacce Bata da Wani Dalili sai Na Tun Farko bata so Ladan ya Auri Habiba ba,Uwa uba Kuma Fifikon Datake Nunama Umma Acikin Matan Ladan Duk Domin Ta Farantamata.
Umma bata yarda Da Cewa Asma'u Tarewa Tayi ba sai Tafara Tunanin Kila anyi Hakane Don Akauda Idon Mutane Shiyasa Ta kasa Natsuwa sai da Ta Tura Su Anty Rukayyah Suka Tafi Har Bauchi sai dai Suka Kira Ma'u suna Tambayanta tana gidanta ne ko tana gidan Hajiya don Suji? Cikin Murna tace Tana gidanta,Su Anty Rukayyah Sun Raina kansu sanda Suka Isa gidan Ma'u domin basu iya ganeta ba Ganin yarda Tayi Kiba Tana Walwali Tarba na Mussman tayi musu sai Murna take Ita mai yan'uwa suna nan sai ga Abdallah ya Dawo Daga gidansu Hajiya nan suka ga Inda ake Soyayyah Da Tattalin Juna Domin Ma'u na Jin sallamansa Ta Fita da Gudu Ta Daneshi Shi Kuma ya Dagata cak yana Juyi da Ita Tare Suka Shigo Falon yana Rike da Hannunta nan Take Sanar dashi Yayyinta ne Suka Zo Daga Dutse Cikin Sakin Fuska suka gaisa Daganan ya Shiga Ciki ita Kuma Ma'u Ta shiga kichen Ta Had'amai Abunci Awani Faranti Ta Shigarmai Dashi Ciki
Ai sai suka kara Raina kansu da Mazajensu, Suka kuma sadakar cewa Ma'u fa ta Zarce Tsara Kam sai Hakuri sai da Sukaci Suka Sha sai la'asar kana Sukayi Haraman Tafiya Wanda Asma'u Ta Shiga Tagayama Abdallah 10k yabasu Suyi Na Mota Suka Karba Suna Murna Suna ma Ma'u Godiya Har Suka isa Bauchin Lbri Cigaban Rayuwar da Ma'u Ta samu Sukeyi da Wannan Lbrin Suka Koma ma Umma wacce Taji Zuciyarta Ta Kusa Bugawa Ranar agaban Fa'iza Suka zo Suna ba Umma lbri Wanda yama Fa'iza Dadi Sosai Acikin Ranta tana Fad'in Ko ba Komai Sunga Raina Kama kaga gayyah
*******
Hutun Abdallah ya Kare Da Wajen Kwana Hud'u kenan Shiyasa ya Fara Shirin Komawa Poerthercourt ammh Kuma yace Kafarsa kafar Ma'u.
wanda Hajiya tace bazai sabu ba bazai Tafi da Ma' u chan ba saboda Kada yazo Dashi da Muguwar Matarshi Su Tasa Ma'un agaba Babu Maceci sai Allah.
ganin Abdallah ya Shiga Damuwa ne yasa Mallam ya Lallashi Hajiya Da Cewa Ta Kwantar Da Hankalinta ta barsu Su Tafi Tare Shine masalaha,Kuma kada Ta kara saka Tunanin cewa Wasila Zata kara Nasara akansu Har Abada Alkadarinta ya Karye.
Da wannan mganar Hajiya ta Sauko Ammh sai da Ta sanya Abdallah ya Dauko mata Ma'u Ta Tambayeta ko zata Bishi Cikin Kunya Ma'u tace Eh Domin yanzu Duk Duniya bata Kaunar Wani Abunda Zai Rabata da yaya Abdallanta.
Nan Hajiya Ta Rumgumeta Tana Murna Haka Shima Abdallah kamar ya goyata Maman Fati ko Duk da Kawaicinta kan Ma'u ammh kowa ya Kalleta yasan Tana Cikin Farinciki Ingantar Rayuwar Yarta.
Hajiya ce Ta Umarci Abdallah da Kafin Su Tafi yakai Ma'u Dutse Tayi sallama da iyayenta, Haka kuwa akayi Washegari Suka Shiryata Ita dashi Mamman ya Daukesu sai garin Dutse,wanda sai dai suka ganta Kamar Daga sama.
lokacin Data Shiga Cikin gida Bayan Tabar Abdallah afalon Abba Suna gaisawa,Har ita kanta Umma bata iya gane Ma'u ba Anty Amarya ko Rumgumeta tayi Tana Murna ganin yadda Rayuwa Ta Maidama Ma'u Mama da Umma da Hajiya Sun Zama kauyawa akan kallon Ma'u da kayan dake Jikinta nan Take sanar dasu Tazo Yi musu sallama ne, Zasu Koma parthercourt Wajen Aikinshi Mama da Anty Amarya Suna ta Mata Fatan Allah ya kaisu lafiya.
Umma ko Bakinta yamata Nauyi,Hakama Shima Abdallah ya sanar ma Abba Wanda Ke ta saka musu Abdallah Kwarjinin Abdallah ya Cikamai ido Acikin Ranshi Masha Allahu kawai yake fadi Domin Tabbas Asma'u Ta dace da samun Gwarzo Miji Haka Shima Duk cikin Surukanshi ba Kamar Abdallah.
Sai ga Abdallah Har Cikin Gida Ma'u Ta Shiga Dashi daki Daki,da dakin Umma ya Fara bayan Sun gaisa da zai Fito ya bata 10k ta karba Hannunta na Rawa domin kaf Surukanta ba Wanda ya Taba Bata 5k ballatana 10k, Daganan sai Dakin Mama ita ta saki Jiki Sun gaisa sosai Ita ma 10k din ya bata ta karba Tana ta saka albarka sai Dakin Anty Amarya Wanda Sudan Jima,kafin Su Tafi ita 20k ya bata Saboda Yana Daraja Wanda ya Mutumtamai Husnarsa.
Dakin Hajiya iya Kuwa sai da Ma'u Ta maida mata Martani Ta Riko Hannun Abdallah Tana Fadin yau ga Mijinta ta Kawo Mata Har daki Toh Ta sani Shi Aure Lokaci ne Kuma Rabonka baya Wuceka Duk inda mutum yake,Hajiya iya Taji Kunya sai Wiki Wiki da Ido Take 20k Abdallah yabata Suka Fita Suka Barta Duk jikinta yayi sanyi Domin Itama kaf Mazajensu Anty Rukayyah ba Wanda ya Taba bata ko asi bama sa zuwa gaida Kowa.
su ya'yan son Nata yau ga Wanda bata zata ba yama ta Kyautan Data Tsayamata arai, Hatta su Baba Lami da Hassatu Ma'u ta sanya an basu kudi Domin Suma Bazata Ta Manta dasu ba.
Abba ma 20kk ya bashi Dakyar ya Karba Suka Rabu bayan yayi Musu Nasiha Sosai har Kofar gida Mama da Anty Amarya Suka Rako Su Ma'u Suna Musu Fatam Allah ya kaisu lafiya nan Suka ci karo da Fa'iza nan Itama ta samu Rabonta Tana ta Godiya Daganan Gidansu Ammi Suka Shiga Inda Ammi Ta Rumgume Ma'u Harda Hawayenta Nan din ma Har Ciki Abdallah ya Shigo Suka gaisa Basu samu baban Aisha ba Yafita Itama 20k Abdallah ya Bata Suka Tafi Tana Kwarara musu albarka.
Daganan sai gidan Aisha Wacce Tunda Ma'un Ta sanar da Ita Takasa Zaune da Tsaye ta Shirya musu Abinci mai Rai da Lafiya, lokacin da Ma'u da Aisha Suka Had'u Tsalle Suka Buga Suka Rumgume Juna,Haka Amir Shima yana Ta Murna ga Momysa Tazo.
Fahad ne ya Fita Waje Ya Shigo da Abdallah Sukuwa Sun Manta Sun Tsinke da Hirar yaushe gamo Har Aisha na sanar da Ita har gidanta Sister Bahija tazo Ganin bata Zuwa Asibiti kuma bata samunta awaya nan Ma'u tace Eh Ta Fadamata Don Sunyi mgaana ta waya,:Nan Suka Ci Abinci Sukayi sallah kana Sukayi Shirin Tafiya Wanda Amir ya sanya Kuka sai yabi Asma'u Dakyar ta lallasheshi Da Cewa Gobe zata Zo Ta Daukesa 20k Abdallah yabama Amir. iyayensa Nata Godiya Har bakin Mota Suka Rakosu Suna Musu Fatan Sauka lafiya Aisha ko da Asma'u suna chan gefe Suna Kus kus Aisha na Karamata Wasu Sirrika sai da Fahad yaJanye Aisha kana Ma'u Ta Shiga Mota Harda Kwallarsu Ita da Aisha Abdallah ya jinjinama Kaunar Dake Tsakanin Husnansa da Aisha wacce Ma'un bata boyemai komai ba na game da Rayuwarsu Shima kafin su Tafi sai da Suka karbi Nombar Juna Shida Fahad.
Washegarin Ranar da Suka Dawo Abdallah yaga ma musu cukun Cukun Tafiya,Da daddare Kuma ya Dauketa Zuwa Gidan Kawu Tayi Musu Sallama Daganan Suka Biyo Gidan Su Hajiya Nan din ma Nasiha Suka Dinga yimusu Sai Wajen 11 suka Dawo Gida Washe gari Kuwa karfe 10am na Safe Jirginsu ya Daga Zuwa portharcourt Duk da Basu Dibi kaya da Yawa ba Dagasu sai karamar akwati Daya wanda Ma'u ta sako Wasu kayanta.
lokacin Da Jirgin ya Tashi Asma'u na Kwance bisa Kirjin Abdallah Idonta na Lumshe Take Fadi Acikin Ranta."Allah Mai iko da Bawansa Karka Cire rai. da Rahamar Ubangiji Domin Rahamarsa Tana da yawa.."
*Janafty*