ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 29

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



     *🅿️29*


Da Hanzari Ta Yaga Sikat din Atamfar Dake Jikinta Lokaci Daya Tana Yamutsa gashin Kanta Tana Dariya Tana Kuma Kuka Lokaci daya.

Tana Soshen Soshen Jiki Musamman ma Gabanta Take Fad'in"Baka isa ba Abdallah yadda bazan Haihuwa ba kaima ba Macen Da Zata Haihu dakai.."

Take Fad'a Tana Yaga Rigar Jikinta Cikin Mintina Ta Yaga Duka kayanta ya Rage Daga Ita sai Bra da Underwear, Shekowa Tayi Da Gudu TaNufi Hajiya Abdallah yayi Hanzarin Tare ta Ya Tsinke Wasila da Wani Wawan Mari Yana Fad'in"Baki da Hankali ne...? Dama Na dad'e da Sauwake Miki Wasila Tunda Na Fahimci ko ke Wacece, Lokaci Kawai Nake Jira Na sanar dake Kuma gashi Lokacin yayi Kina Duniyarnan Zaki ga Na Tara Zuru'a da Ma'u Kuma Asirinki bazai Kara min Tasiri ba Kije na Sakeki Saki Uku Wasila Daga Karshe kuma Allah ya Isa Tsakanina Dake."Yafad'a Idanuwansa Suna kad'awa Saboda Bacin Rai.

Wasila Dake Dafe Da Kunci Ta Wani Saki Dariya kafin Ta Zube Kasa Tana Fadin"Ka sakeni fa Kace...? Wlh karya kake Bazan Taba Rabuwa dakai ba, Nifa na Maka Asiri ka Haukace akaina Nida Momcy Mukaje gidan Boka Mukasa Aka Mallakeka Kuma Aka Rabaka da iyayenka..nina...nina..."Haka Wasila Ta Dinga Tonama kansu Asiri Duka Abubuwan da Suka Aikatama Abdallah sai da Tafad'a Kafin Ta Fara Fizge Fizge Tana Soshen shoshen Jiki Duk inda Ta Sosa Sai Jini ya Fito Ta Kuma lashe da Hannunta 

Hajiya da Asma'u Suna Tsaye Suna Kallon Ikon Allah Ma'u Ko Tsoro ne ya kamata na Ganin Abubuwan da Wasila Keyi na Alamar Fitar Hayyaci, Kamkame Hannun Hajiya Tayi Tana Makyarkyata, Abdallah Yana Gefe Hannunshi Sarke a kirjinsa, yana Kallonta kamar ya samu Tibi.

Hajiya ko Kabbara Take Cikin Zuciyarta kafin Ta Furta Afili Tana Fadin"Allahu Akbar. Allah yayi gaskiya Dayace Kada Ku Had'ani Da wani Hallitana Wajen Tarayyah. Kunyi Iya Abunda Zakuyi gashi Lokaci Kankani kina Girban Abunda Kika Shuka..."Ina Wasila Bata Jinta banda Soshe Soshe Da Karta Naman Jikinta ba Abunda Take Tana Faman Mganganu Ita Kadai Tashi Tayi Tana Nuna Abdallah Tana Dariya Kafin Tayo Kanshi yaja baya Hajiya ta kama Hannun Ma'u Suka Matsa Gefe Tana Fadin"Kai Abdallah Tafa Haukace Maza kakira Jami"an Tsaro Kafin Ta Mana Illah.

Abdallah baiyi Mgana ba Saboda Ganin Wasila Ta Nufoshi Da gudu Tana Neman Rikeshi ya sanya Hannu ya Riketa yana Kwalama Emeka kira da Megadi da Gudu Sukazo Wasila ya Nuna Musu yana Fadin"plz Take her To dis Room.."Yafad'a yana Nuna Musu Dakin da Zasu sanyata Da Hannu Wanda Dakin da ada yake kiwon Zomo ne Mutuwa yayi Da Hanzari Suka Kamata Tana Fizge Fizge Tana Wasu Surutai Suka Shiga da Ita dakin Dakayar Suka Kulleta saboda yadda Take Kokarin Sai Ta Fito.

Ajiyar Zuciya Abdallah ya Sauke Kafin yayi Gaba yana Fadin"Mu Shiga Ciki Hajiya..."Kada Kai Tayi Kafin Tace"Allah ya kyauta..."Ma'u Ko Idanuwanta Har Sun Ciko da Kwallah Saboda Tsausayin Rayuwa da Kuma Tsoron Allah Daya Kara Shigarta.

Haka Suka Shiga Ciki ita dai Bedroom dinta ta Wuce Ta Shiga Wanka Hajiya ko Tana Falo Ita da Abdallah Suna Kara Jinjina lamarin Haka ma Ma'u Abun yaki Barinta Ranta, Koda Ta Fito Wanka Zuru Tayi Duk Jikinta yayi Sanyi,sai da Hajiya ta Shigo ganin Halin Data Shiga Ta Zaunar da Ita Tana lallashita Har Ta saki Ranta Tea hajiya Ta Had'amata Shikuma Abdallah ya Fita ya Siyo Abinci Koda ya kawo Hajiya ce Kad'ai Taci ma'u Har Tayi Barci sallama ya yi maata ya Shiga Dayan Bedroom Din yayi Wanka da sallah ya Kwanta yana Tunanin Rayuwa Da Irin Abubuwaa da Wasila Ta furta da Bakinta ta Aikata gashi yau Tana Girban Abunda Ta Shuka.

Washegarin Abun na Wasila ya Huce Tunani Domin Ko kafin Gari ya Waye Tagama Tsige gashin Kanta Tsab Ta Koma Kuma Tana Tsige Na gabanta Wa'iyazu billah, Abun sai Wanda ya gani Dole Imani ya kamaka Haka Take Buga Kofar Dakin Tana Iface Iface da Fizge Fizge Daman Kofar Tana da Kwari Ammh da Bata Dashi Da Tuni Ta ballata Ta Fito.

Akwana na Biyu Ne Hajiya Tace Ya Kira Mahaifin Wasilan ya sanar Dashi Halin Da'ake Ciki Baiyi Gardama ba Ya Kirashi ya sanar dashi Ammh sai yace yayi Kyau a saketa Tabi Duniya dama Shi ya dace Da Ita.

Jin Haka yasa Hajiya Ta karbi Wayar Tamai Nasihan Hannunka baya Taba Rubewa ka Yanke ka yar,Dole da yayi Hakuri Wasila yarsa ce naHar Abada, Hakuri ya bata yace Zai Zo da kanshi,Da mganar Kwana Daya sai gashi yazo Shida Kaninshi Halin da Suka Tarar da Wasila yayi Muni Sosai. mahaifinta yayi Kuka Sosai nan yace zasu Tafi da Ita Ammh Sai da garada Wajen Goma Suka Taru kana aka iya Daureta Suka sakata amota Suka Tafi Ita da bidda. Chan ma Din Wani Daki na Mussaman aka sata aka Kulle Duk Wanda yazo yaga Halin da Wasila Ke ciki sai ya Kara Tsorata da Duniya Jamila Data Ganta ta Razana Nadama Ta kara Shiganta Wacce Cikinta ya Tsufa Har Bata iya Barci ba Neman Gafaran Allah kawai Tana Gode mishi Da Batayi Mutuwar Wulakanci Irin Wanda Momcy Tayi da Hafsat Ba, Kuma bata Tozarta Irin yarda Allah ya Tozarta Wasila ba Wacce Duk Ta Cire Komai na Jikinta Tsirara Haihuwa Uwarta Take Duk Tajima Kanta Rauni bayan Ta Gama Illata Farjinta Abun ba Kyan gani Wannan Abun ya zama Izina ga Mata masu Bin bokaye Wlh Kisani Karshenki bazai Kyau ba

Hajiya Sati Daya Tayi Shirin Komawa Wanda Ma'u bataso ba Harda Kukan Zata Bita Abdallah ya Hana,Dole Ta Hakura Itama Hajiyar Bata Matsa ba, Su suka Rakata Har Filin Jirgi sai da Suka ga Tashinta kana Suka Komo Gidan Daga Ma'un Har Abdallh Abunda ya Faru da Wasila ya Dakesu Kuma Sun gane Cewa arayuwar nan In baka Bi Allah ba Wlh Kana Tare Da Ganin Masifu Kala kala, Hajiya ko Mamman yazo ya Dauketa daga Filin Jirgin Abubakar Tafawa balewa Bauchi Itama Haka Ta Koma Wannan Lbrin Mara Dadin Ji da Sauraro Mallam ya Jinjina lamarin Kowa Jikinsa yayi Sanyi Tun Balle yadda Hajiya Take basu Lbrin yadda Wasila Ta Dinga Tonama Kanta Asiri dasu Anty Nafi Sukaji ko ajikinsu Allah ya kara ma suka ce Alhakin Yaya Abdallah bazai Barta ba dama.

Wasila fa Abunta yana kara gabane Domin yanzu Tafara Saka Hannu tana Cizgo Naman Gabanta Tana ci Wayyo Rayuwa Wlh mu aikata mai kyau Mu Guji Shirka da Sabama Allah,Dakin Datake Ciiki banda Wari Babu Abunda yakeyi Babu Mai matsowa Kusa da Wajen sai dai Daga Nesa Anan Cikin Wannan Halin Watarana Da Daddare Ta Balla Kofar Ta Fita da Gudu ba Wanda ya sani sai da gari ya Waye aka Farga An bita ammh Shuru ba'a Ganta ba Ta Nausa Cikin Gari ba Wanda ya sani,Jamila ce Mai Kukan Nadama da Dansani Wanda bai Da Ranar Karewa 


*******


Bayan wasu wattani.


Cikin Asma'u yashiga Wata na Bakwai Har Tafara Zuwa Awo Wanda Cikin yayi Girma Sosai Duk Wata kula Ta Duniyarnan ba wanda baya Mata Tazama yar Gata gaba Da baya Koda Yaushe Su Hajiya Cikin Kiran Suke Suna Tambayan lafiyanta Harda Maman Fati ba'a Barta abaya ba.

Hakama Abbana Shima yana Kokarin Kira yaji ko ina lafiya,yan gidanmu Sun san Ina da Ciki ammh bayan Anty Amarya da Mama Wacce Naga yanzu Ta Chanza Ba kamar Da ba,kuma gaskiya ko abaya Bata Nuna Tsana Kirkiri ba Koda tana Wani Mugun Nufi game da Ni Toh bata bayyana ba.

Abdallah babu Abunda bai Siya na Haihuwa na ba Tunda akayi Scanining aka ce Yan Biyu zan Haifa Wo Ranar Kamar Zaiyi Hauka Saboda Murna,Ni Wani Lokacin Har Tsausauyi yake Bani in Naga yadda yake Rawan Jiki game da cikin Wani Lokacin Kuma Bana ganin Laifinsa Tunda yadade Bai samu Haihuwa ba Wanda ya kamata ace Yaran yaya Abdallah Sun Girma Ammh Dayake ya hadu Da Muguwar Kaddara Daga Wasila ga Yadda Allah Ya Rubuta.

Tunda Cikinta ya Shiga Wata Na Tara Hajiya Ta Kira Abdallah Tace Maza ya Tattaro Ma'u ya Dawo da Ita gida Ta Haihu wanda Abdallah baiso ba kamar yayi Kuka gashi Lokacin bashi Da Wani Hutu a office Mallam ya fadawa ko Zai ma Hajiya mgana Shima sai ya Goyi bayanta Babu Yarda ya Iya Haka ya Fara musu Shiryen Shiryen Tahowa Wanda Itakanta Ma'u Tana son Komawa Bauchi Ammh Kuma Tana son Kasancewa Da Mijinta Wanda Take Matukar So, Ammh bata da yarda Zatayi Ana gobe Zata Tafi bayan ya gama Hada Mata kayanta Ta Shigo da Katon Tsinin Cikinta ta Iskeshi yana Zaune Gefen Gago yayi Tagumi Ranshi Duk ba Dadi.

A hankali Ta Isa gareshi Ta sanya Hannu Ta Zare Tagumin Nashi A Hankali ya Dago yana Kallonta idanuwanshi Sunyi Jawur Kamar zai Mata Kuka kai Ta kad'a kafin Tace"Babe. bafa Mutuwa zanyi ba da Zarar na haihu Lafiya,Ina gama Arba'in Zan Dawo Nima mai zan Zauna in yi Achan ga Bugawar Zuciyata anan..."Tafada Tana Shafa gashin Kanshi Cikin Wani Salo.

Lumshe ido Yayi kafin ya Bude Yana Sauke ajiyar Zuciya, kafin ya Sanya Hannu ya Rikota ya Zaunar Da Ita Kan Cinyarsa Yana Kallon Kwayan idonta yace"Sugarlip kinsan na Saba dake Ina Tsausayin Kaina ne Ta yarda Zan Fara Wata Rayuwa baki. Babe Am gonna Miss u Like crazy Wlh.."Yafada Yana hada Hancinsu Waje Daya,Jikinta ne yayi sanyi Ta Tallobo kanshi Tana Dora Harshenta Bisa Lebenshi Tafara Dan Ciza Kafin Takama Tana Tsotso Kama Bakin nata yayi da karfi Suka Fara Kissing din Juna In Romantic Way. cikin Lokaci kadan Suka Rikita Junansu da Wani salo Wanda Ko Tsinin cikin Jikinta Ma'u bataji Haka ta Zage Tabama Abdallah Hadin kai Domin Ya Warware Daga Damuwar Daya Shiga. Sai da Komai ya Kamallah kana Ya Dauketa Suka Shiga Wanka Suka Dauro Alwala Sukazo Sukayi Sallar Issha'i da Shafa'i da wuturi kana Suka Kwanta Kamkame Da Juna Kowa na gayama Dan'uwanshi Irin da kewar Zaiyi Nashi


Washegari Jirgin Karfe 8am na Safe Abdallah da ma'u Suka bi Zuwa Bauchi karfe 12 da wani Abu Suna Falon Gidansu Kowa kamar ya Cinye Asma'u Saboda Tsausayi nan Suka Iske su Anty Safina Hajiya ko Kamar Ta Goyata Saboda Murna Tunda Suka Zo Tana Shashen Hajiya Abdallah abinci kadai yaci yayi salla,Bayan Sunyi mgana Da Mallam kan Cewa Asma'u Zata Koma Gidanta ne Yau Su Anty Nafi Zasu je Su Share Gidan Su Gyara So Tare Da Hajiya zasu Tafi Ta zauna Da Ita Tabe Baki Abdallah yayi Don Shifa Haushin Hajiya da Mallam yakeji Sun Rabashi da matarshi da la'asar ya koma portharcourt Saboda Haushi Daga Hajiyar Har Ma'u Basu san Tafiyanshi ba sai Bayan Yatafi aiko Ma'u Harda Kuka Wai Babe yaTafi bai Mata sallama ba,Maman Fati Tsaki Taja Su Anty Nafi Ko Dariya suka sakata Mata Hajiya ce Ta zage Tana lallashinta Dakyar Tayi Shuru Tana Sauke ajiyae Zuciya kamar Wacce Tayi Gudun Tsere.

Haka ko akayi Washegari na Koma Gidana Nida Hajiya Bayan Su Anty Safina Sunzo Sun gyara Ko'ina ammh Hajiya tasa An Samomata Wata yar aiki Yar Dattijuwa Baba sa'a Saboda Rage Wasu aikace aikace Tunda Ita kanta Hajiya ba Ishashiyar Lafiyan Gareta ba.

Saboda Ita Girki da gyaran gida da Su Wanke Wanke Ita Kuma Hajiya na Kula da Asma'u,kwananta Hudu da Dawowa Bauchi Wata Ranar Jumma'a Da Safe Tatashi Da Naguda,nan da Nan Hajiya Tayima Mallam Waya aka Turo Mamman yazo da Mota ya Kwashesu sai wani Private Hospital Kainuwa Suna Zuwa aka karbeta sai labour room.

Ma'u Ta Dandana Azaba Haihuwa Ta Dinga Kuka Tana Salati Tana Kiran Zata Mutu Bata Haihuwa ba sai Washegari da Safe Ta Sullobo kyawawan ya'yanta Masu kama da Ubansu kamar yayi Kaki Duka Mata masha Allahu Haka Kowa ke Fadin Sanda Hajiya ta Kulla Alkawari da Mtn Duka Contact dinta ba Wanda bata Kira Ta sanar Dashi lbrin Haihuwar Ma'u ba Bakinta kamar Gonar Auduga saboda Murna wai gata ga Matar Baffa da ya'yansa Allah Abun godiya.

Abdallah Suna Meeting Da C.G contoller general dinsu Daya zo Daga lagos yaga Kiran Hajiya bai Daga ba sai da Suka Fito Taron yana Kokarin Kiranta ne Yaga Kiran Fahad yana Dauka bayan Sun gaisa yashiga mai Murna Ido ya Zaro yana Fadin"U mean Sugarlip dina Ta Haihu ..? Fahad na Dariya yace"Wlh yanzu Ammi Ta Kira Rabin Ranku Tana Sanar da Ita yan Biyu Kyawawa."Ai sai kawai Sauran abokan aikinsa Suka ga Ya Yanki Gabas ya Zubo yasa goshinsa akasa yana Zubama Allah Kirari Ya Dade Kafin ya Dago yana Share Kwallah Farinciki nan yake Sanar dasu Matarshi Ta Sauka ansamu Yan Biyu Duka Mata,nan Kaga yadda ake Mikama Abdallah Hannu Ana Fadin"Congratulaton Sir." Shiko Bakinshi ba Control yana Fadin"Tanque...Tanque..."Wasu Dayawa Sunyi mamaki Domin Abdallah baya Dariya Balle Wata Doguwar Mgana ammh yau kan Sun Kulla alkawari da dariya.

Tunkafin yakai Ga Kiran Hajiya Kiran Yusuf Ya Shigo Shima yana Tayashi Murna Haka Duka Kannensa Su Anty Safina,wacce Tace Tana Asibitin Ya Shiga Wasop Ta Turamai Hotunan Ya'yan Nashi Wannan baya Gabanshi Hajiya yafara Kira First yana Tambayanta Ina Sugarlip Hajiya Tace Tana Dakin Hutu Tana Hutawa Nan Hajiya Tamai Barka ya amsa yana Ta Dariya. Daganan sai Kiran Mallam ya Shigo Shima Barka yamai Tare da addu'an Allah ya sanyama Yaran Albarka,Haka dai Abdallah ya Cigaba da Amswa Wayoyi kala kala,Har Zuwa dare Bai samu Ma'u ba sai da garin allah ya Waye Tun Asuba ya Doka mata Kira Tana Gani Lokacin Ta Farka Mirmishi Ta saki Lokacin Da Hajiya Ke Fadin"Hala Baffa ne..? Ke don Allah Dauki Wayarki Wlh ya Damemu Mutane Tun Jiya Kamar akanshi akafara Haihuwa.."

Batace Komai ba Taga Kiran YanaJin Ta Dauka ya Fara Fadin"Aminci Allah Tare da Rahamarsa Su Tabbata Tare Dake yake ma'abociyar Fara'a Kwarjini da Zati yake Macen Kwarai. Ina Rokon Allah ya Saka Miki Fiye da Kokarin ki my Sugarlip Am So Happy Wlh bansan Wani Farinciki Nake ciki ba, na yi alkwarin zama da ke har karshen Rayuwata." Yake Fada Cikin Zumud'u LumShe Ido Tayi kafin Ta Bude Tana Fadin"Tare dakai Ma'abocin Karamci da Kula. Antin For u my Babe Haihuwa yanzu Na Fara Zazzage maka sai nayi Dozin Insha Allah.."Ihu ya saki yana Dariya Itama Dariyar Take Hajiya DaKe Gefe Ta Fice Ranta Cike Da Farinciki da Mamakin Yaushe Abdallah yazama Mara Kunya.

Kwana Biyu Nayi aka sallameni Daga Asibitin Tun Ina Asibiti Nakara Jin Kaunar Mamata Ina Tunanin Ashe Itama Wuyar Dataci Kenan Sanda Zata Haifeni Lalle Uwa Uwa ba Abun Wasa Bane Shiyasa Aka ce Ko Daukanta Zakayi Awuyanka kana Zagaye Ka'aba da Ita baka Biyata Silin Gashin Hakkinta Akanka ba,Allah kabamu Ikon Yima Iyayenmu Biyayyah Ameen.

Gidanta aka Wuce da Ita Direct sai Ranar Ta samu mgana da Aisha Wacce Ke Ihun Murna Tana Fadin Jibi Insha Allahu Zata zo Sai bayan Suna, Abun ya ba ma Ma'u Dariya Maman Fati batazo Asibiti ba sai dai Ta Kira awaya wai Kunya Takeji Kuma Ita Uwar Miji Ce Hajiya ce Uwar maijego Hajiya Ko Tace Bakomai Dama ba Wanda ya gayyaceta agidanmu.

Goggo Jummai ce Tazo Tana Taimakama Hajiya Haka SukeJi Da Ma'i Suna Kuma Kula da yan Jikokinsu, Daga Anty Amarya sai Mama da Abba Suka Kira Ma'u Suka mata Barka Banda Umma da Hajiya iya Fa'iza Ce kad'ai Ta Kira ta A yan Dakin Umma. sai Ya'yan Mama dukkansu ba Wanda bai Kira ta ba Kuma Sun yi mata alkawarin zasu zo Suna In Allah ya yarda.

Abdallah Duk Kokarinshi ya samu Zuwa ammh ba Hali Domin Akwana Hudu da Haihuwar Aka Turashi Wata Samenir a Birnin lagos Dole ya Tattara ya Tafi Ammh Kullum baya Barci sai da Hoton yaran akirjinsa Wata Soyayyah yake Musu Wanda baisan Iyaka ba Ma'u Kuwa Arana sai ya Kirata Sau Goma sai Hajiya ta Gaji Ne Ta Karbe Wayar Ta Zazzageshi Kana ya Kashe yana Tura baki yana Fadin"Wai Ita Hajiyan nan Haka akeyi Shikenan Araba Mutum da Matarshi Kuma ace Bazai Kira ba.."

Dama Tun Suna parthercount Akwatu Guda Abdallah yayi mata na kayan Fitar Suna kayan Jarirai Kam kai kai iya kallonka Mallam Tun Ana Jibi Suna Aisha ta iso Ita da Ammi da Anty Amarya Da Mama. Ana gobe suna kamar a Mafarki sai gasu Fa'iza da Anty Bilki da Rabia wai Anty Rukayyah Mijinta ya Hanata Zuwa Zuwa chan kuma sai ga ya'yan Umma kulsum Fati da Maryam Hakika Kowa Da'n Uwanka yake yana Dadi Naji Dadin ganinsu sosai Har nakasa boye Murna Na,Tun ana gobe Sunan Mallam ya yanka sa Har Biyu,Abinci Suna Kowa Komai da Komai aikatau Su Anty Safina Suka Bada,Ranar Suna Kuma da Safe Mallam ya kara yanka sa Guda Daya da Raguna Firda Firda Guda Biyar Da Safen Kuma Abdallah ya Kirani yana Fadamin Mallam Zaizo yanzu zaima Yara Huduba da Sunaan Habiba da Hajara Wato Hajiya da Maman Fati Kenan.

Wlh Farincikin Da Ma'u ta yi ta kasa Boyewa haka ta Dinga Kwararama Mijinta Addu'ar Nasaran Rayuwa Shiko yana Mirmishin yana Fadin"Anty Tin For U My Sugarlip" Basu Dade da Gama waya ba sai ga mallam yazo Lokacin Tuni goggo Jumai Tagama yi musu Wanka an Shiryasu Ciki Wasu kaya masu Kyau Nima nayi Wanka na Sanya Wata Gezner Wanda Abdallah ya Saka aka Dinkamata Tunda ta sakata Duk inda ta Gifta sai am Kalleta saboda yadda Take Daukan Ido pick colour ce Akallah zata bama 75k baya Nan Mallam yayi Musu Huduba bayan ya Digamusu Ruwan Zamzam abaki Sai Lokacin Kowa yaji Sunan Wai Hajiya baki ya ki Rufuwa balle Maman Fati Ta kasa Boye Murnanta Tana Gida Daga Ita sai Wasu Daga Gidansu Kawu Hatta Su Fati da Mahmud Tun Jiya Suka zo.

Taro fa Yayi Taro Wanda Cirewa Kawai Ma'u ta ke yi ta na maidawa Hannayenta Kuwa Da Wuyanta Suna kyalli Zinare wanda Abdallah ya Siyamata Duk inda ta Gilma yan'uwanta Kebinta da Kallon Sha'awa Domin Kaf Dinsu Ba Wacce Tayi Dacen Miji kamar Asma'u ta zama Super Star awajensu kamar Ba ita bace Wannan Ma'un Wacce Tayi Zaman Kunci abaya ba.

Kayan Suna kuwa na ta tara su bata san Iyaka ba Yan'uwan Abdallah Sun Mana kara Sosai Sun kashemana Dukiya Anty Zainab ma da Annii Sunzo Daga kaduna suma da kayan arzikisu Kala kala Abun sai Wanda yagani anci ansha Kamar ma An Ture Saboda gashinan amanya Kololi kaci Abunda Kakeso Babu Mai Hanaka Koma Diba zakayi Duk Ka Diba akwaishi Daga Gidan Mallam Aka bama masu gyara Naman sa din dana Raguna sai dai aka kawoshi amanyan Robobi Asoye kawai sai Dai ci washegarin Suna Su Anty Amarya da Mama dasu Fa'iza da ya,'yan Mama sukayi Haraman Tafiya da Zasu Tafi Hajiya tace Kowacce nabata Tirmin Atamfa Daya Nama Kuwa Da Drink Katan Katan na basu nace Su Tafi dashi Na bada Turmin ATamfar Hajiya iya Dana Umma Nama Kuwa awata katuwar Roba na Cika musu Suka Tafi Dashi Harda Wata karamar Roba Wannan Abba nace Su kaimawa Domin yamin Gata Turaman Atamfa Hudu ya Dinkamin da kayan yara Ya Kuma aikomin Da Kudi 20k duk da yasan yanzu nafi Karfinsu Haka Kuma na Had'asu da Kudin Mota Suka Tafi Suna Murna Tare Da Fatan Alheri Gareni Don Sun Fahimci Sawun Giwa ya Wuce Na Rakumi Su Aisha Kuwa sai da Suka kara Kwana Ita da Ammi Suma da Zasu Tafi Haka nayi Musu Sha Tara na arziki Domin Aisha da Fahad Suma Sun yi min Ranar da Ba Wanda yayiminshi Har Kuma Gobe Sunakan Yiman.

Haka Muka Rabu Cike da Kewa Kamar kada Su Tafi Gida ya Rage Dagani sai Goggo Jumai da Hajiya ,suma yan gidansu Kawu Sunyi Kokari akaina Sun Kawo Yajin Jego Da Sauran Kayan amfani Suma ban barsu Hakaba Domin Allah ya Azurtani Suma Nawane Dole nayi Musu.

Koda Su Anty Bilki Suka Koma da Wanan Shataran Na arziki Zuciyar Umma ya Kusa Bugawa Hajiya iya Kuwa ta Karbe Tana Murna Sosai Umma ma Ta Karba Domin Bata da Yarda Zatayi Tinda Allah ya Darajani bata Isa taTozartani ba.

Tafara saki da al'amarin Allah gashi Duk kiyayyar Data Nunama Maman Ma'u Da Asma'u ita kanta, yau gashi Allah ya Daga Darajanmu Tana ci Da ita da y'yanta ta Karkashin su.

Haka Abbana ya Kirani yana ta sakamun Albarka Domin kaf ya'yanshi ba wacce baya ma Kayan Fitar da Suna da Kudi Kamar yadda ya aikomin Dashi Ammh ba Wacce Tataba aikomai da Ko Kashi.

Shiyaasa Ba Nuna Sonkai ba Dani da Mijina yana alfahari damu Domin Duk bayan Kwana Biyu sai Abdallah ya Kirashi Sun gaisa sabanin Mazajensu Anty Rukayyah Wani Sai ya Shekara bai ganshi ba.

Abdallah bai samu Lokacin Zuwa ba sai da Na Kwana Ashirin da Uku Shima din Agurguje Kwana Daya yayi ya Juya saboda Bashi da Wani Hutu yanzu Yazo yaga ya'yansa Wad'anda Mukema Lakabi da *AINA DA AIMA* muka Rabu akan sai dai idan Na Dawo Haka na cigaba da Wanka na Hajiya da Goggo Jumai Suna Kula dani Tunda na Haihuwa Suke Kula dani Da Gyara Ni Ita da Hajiya babu Ruwansu Hakika nafi Kowacce Mace Sa'an Samun yan'uwan Miji Na gari.

Maman Fati Bata taba Zuwa Gidana ba Har nayi Arba'in ni Naje gidan Mallam na Kwana Inda Goggo Jummai Ta Koma Gidan Bayan Su Mallam Sun Rakata da Godiya da Kuma Sha Tara na Arziki.

Mamman ya kaini Dutse na Kwana hudu Dani da Su Aina Dina Wadanda Suka Fara Wayau gashi Nonona mai Kyau ne Sunyi Bulbul Kamar ya'yan Turawa Haka Nima na Zama Kamar Wata baturiya,Wannan Zuwa Abun Mamaki Har Dakin Anty Amarya Hajiya Iya Tazo Muka gaisa Ta Dauki Su Aina Tana Musu Wasa, Umma ce dai sai Ahankali Haryanzu Tana Fama da Ciwon Hassada

Abbana ma ya Dauki Su Aina ya ta musu Addu'a Banzo Haka Domin Booth Din Motar Shake da Kayan Abinci Wanda na Kawo ma Abbana da Kuma Anty Amarya Agidan Aisha na Kwana Daya Muka Wuni Muna Hira Kafin Na Tafi Har Gidan Anty Bilki da Anty Rukayyah naje Wadanda Ke Cikin Wahalar Rayuwa ga Ya'ya Sun Hadu da Mugayen mazaje, 5k naba Kowaccen su Kamar Suman Sujjada Saboda Godiya Fa'iza ma naje Gidanta ita su dasu Maryam Wanda Gwara su bangansu Cikin Mummunar Kammnina ba, Sister Bahijja naje Gidanta Wanda Dama Tun Ina parthercourt Mukayi Waya Da Ita Tacemin Tayi Aure Na dade Agidanta Muna Hira Itama Tabar aiki Tana Zaune Ita da Uwar Mijinta mai Sonta Itama Cikin Gareta Har ya Fito.

Duka Duka Kwana Hud'u Nayi Mamman yazo ya Daukeni Na Koma Bauchi na bar Yan Gidamu na Lbrin Ban Sha'awan Dana Koma Nida Ya'yana.

Dama Haka Rayuwa Ta Gada Abunda yabaka Dariya Watarana Shi zai saka Kuka.






*Janafty*