ZAMAN GIDAMMU(Mai cike da kunci)

Chapter 30 END.

by @jamilaumarjanafty

*ZAMAN GIDANMU*

_(Mai cike da kunci)_


*Wattpad:JamilaUmar315*

*Mallakar:Janafty*

*Arewabook:Jamilaumarjanafty*



       *🅿️30*


*Karshe.*


 Ta na komawa ta fara Shirin Komawa parthercourt Wanda Hajiya Ta ce Tare Da Baba Sa'a Zata koma Kuma batare Da Rakiyar Kowa ba, Haka ko akayi Ba ta Tafi da Wasu kaya ba sai Akwati Daya Wanda ta asaka Kayan su Aina aciki Da Abubuwan da Zata Nema.

 Mamman yakai su Airport nida Baba Sa'a Wacce zata Dinga Taimakamata da Rainon Su Aina,Suka Hau Jirgi bayan Ta Kira Abdallah ta Sanar dashi, Farinciki ya Cikashi Yace da Zarar Jirginsu ya Sauka Ta Kirashi Zai Turo Emeka yazo ya Daukesu Shi yana Office aiki yamai Yawa,Haka ko akayi Jirginsu na Sauka Ta Kira Abdallah Ta sanar Dashi Shi kuma Ya Tura musu Emeka yazo ya Daukesu Zuwa Gida Ita da Baba sa'a Wacce Ke Rike da Aina Ita Kuma Ma'u Tana Rike da Aima Ahannunta.

Lokacin da Megadi ya Wangale musu get din Gidan Asma'u Taji mamakin ganin Sauye Sauye Acikin Gidan Kama da Karin Wasu Motoci Dake Cikin Tamfol da Kuma Fulawars masu kyau da Tsari da'aka Shuka bayan Tafiyarta har Sun Fito.

Abun yabama Ma'u sha'awa Acikin Ranta Tana yaba Komai na Abdallah Yadda yake Dabam Acikin Maza Haka Komai Nashi Yake Daman Irin So Special din nan

 Lokacin da Emeka ya Daidaita Zaman Motan A parking space Ya Zagayo yazo ya bude musu Suka Fito Ita da Baba Sa'a, da Hanzari Emeka ya Bude Booth ya Dauko Akwatin Ma'u ya Nufi babban Shashen Gida ma'ana Inda Wasila Tayi Mulkinta.

Galala Ma'u Ke Binshi da Kallo Kafin Tayi Mgana Wayar Abdallah ya Shigo wayarta Tana Dagawa Kafin Tayi mgana Taji yace"Wlcm back Home my Sugarlip. Karki ce Komai my Dear sai inda na Dawo Ok.."Gyada kai Tayi Tana Mirmishi kafin Tace"Ok Babe..."Daga Haka Suka yanke Kiran.

Tana Cema Baba sa'a Suje Haka Suka bi bayan Emeka har Zuwa Shashen Inda Ma'u Ta sake Bakin Ganin Kamar an sake Komai na Cikin Flat din Ko'ina yana kalli ban Sha"awa Ashe Tun bayan Tafiyarta yasa Aka Fita da Komai Na barayin Aka Kona Don yace bai yarda Da Kayan ba, Aka sake Sabon Fenti na yarari da Zamani Akayi Feshi Saboda Shifa Har yanzu kyankyamin Wajen yake ammh Saboda yafi Girma Kuma Shi Yana Dauke da Upstairs ne Kuma Shi Abdallah yana Kaunar Rayuwa A Upstairs.

 Har Emeka yaFice Ma'u na Bin Ko'ina da Kallo Cike da Sha'awa Wasu Kayattatun Kujeru ne Suka Kawata Falon Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ma'u Tazauna Tana Fadin Masha Allah bayan Ta Umarci Baba data Zauna. Aina ta bata Ta Fara Zagaya Duka Dakunan Shaahen Ko'ina An chanzamai Komai Tsab kamar Mutum bai Taba Rayuwa awajen ba, Daya Daga Cikin Bedroom din Dake kasa Ma'u Ta sauki Baba sa'a Ita Kuma Ta Haura sama Bedroom da aka sakama Master Bedroom Ta Bude Ta Shiga Sai Da Ta Kusa Shidewa Komai na Ra"ayinta aka saka White And pick Wow.. Haka kawai Ma'u Ke Furtawa Komai kayanta na Jere Acikin Dakin Abun sai Wanda Yagani sai Wani Dake Kusa Dashi Wanda Shi Kayan Dakin Black and White ne Kayan Abdallah ne Aciki alamun nan Ne Nashi,Akwatinta Taja Cike da Murna ta Shiga Dashi.

Dakin Baba Sa'a Tashiga Ta Karbi Su Aina ta basu Nono kafin Tafada Kichen Ta Iske Komai na Bukatar Girki Akwai Shiyasa nan da nan Ta Kunna gas Ta Fara Kokarin Dora Dinner Saboda Abdallah Cikin Lokaci sai gashi Tagama Sakwara da Miyar Agushi Sai Ferfesun Ganda da Kuma Lemon kankana Data Hadamai da Kunun aya ,dama already Su Ta farayi Tasanyasu A frigde kafin Tagama Girkin Yayi Sanyi Illai Kuwa Cikin Lokaci Tagama Jera komai Bisa kayatacen Danning Din Dake Falon,Ta Haura sama ta Shiga Wanka agurguje Ganin Har Bakwai TaWuce Lokacin sallar mangariba yayi .

Ta dad'e Abayin Tana Wanke Kanta kafin Ta Fito Manta ta Shafa Olive Duk bata Damu da Makeup ba yau Tayi bayan Ta Shafa Hoda ta sanya Jambaki kalan Kayan Jikinta Wani Material ne,Shara Shara Mai Santsi Kuma Mai kalan pick da Blue ne Kuma gashi da Mannewa ajiki Duk sai ya lafe mata Duka Cikar Kirjinta Dana Kugunta Suka Fito Bata Sanya Dankwali ba sai Ta gyara gashinta Ta Fakashi Ta baya bayan Ta Shafamai Tana kyalli Tana cikin Fesa Humrarta ne Wanda Aisha ta Bata Taji Karan Hon din Mota Lokaci daya Kuma da Bude Get. Mirmishi ta saki kafin Tayi Hanzari Tagama Shafa Turaran Aduka Lunguna da Sakon Jikinta,Ta Fice Daga Dakin Daidai Lokacin Shi Kuma Abdallah ya Shigo Falon da Sallama Fuskarshi na bayyana Fara'a Jin Falon ya Hade da Kamshin Abinci Dana Turaran Wuta da Baba sa'a Ta Kunnah.

Tundaga Nesa ya sakarma Ma'u Ido Itakuma Cike da yanga Take Saukowa Daga Step din Daya bayan Daya kasa Jure jiranta yayi Da Sassafar ya isa gareta ya Dagata Cak ya Sauko Da Ita Tsakiyar Falon Tana Dariya Direta yayi kafin ya Ware Mata Hannuwanshi Da Gudu Ta Fada Kirjinsa Atare Suka saki ajiyar Zuciya Lokaci Daya Suna kamkame Juna Kanshi ya Tusa Ajikin Wuyanta yana Fadin"I miss u my Sugarlip...."Tana Kara Shigewa Cikin Kirjinsa Tana Fadin"Miss u More Babe..."Sun Dade Suna Rumgume da Juna Kafin Su saki Juna Kowanne na Bin Dan'uwansa da Kallo Cike da So Da Kauna.

Hannunta ya Riko yana Fadin"Masha Allah My Sugarlip sai bayan Tafiyarki Nasan Sai Kina Gidan nan ya Cika complete Wlh da Bakina Ko'ina Empty buh ammh Kalli Daga Dawowarki Komai ya Dawo Daidai Tunda na Shigo nakejin Kamshi me Matata Ta Shiryamin ne..? Yafad'a yana Leken Kololin Dake Diniing Area.

Kunnanshi Ta kama tana Fadin"Sai kayi Wanka munyi sallah Tukunnah Nima Murna In Fito na Tarbeka bai barni nayi Sallah ba.."Mirmishi ya saki ya Jawota jikinsa yace"where is my kids...?Tace "Suna Wajen Baba sa'a Harma tayi musu Wanka ka bari ka natsa sai suzo su gaishe da Abbunsu ko.."Gyada kai yayi yana Fadin"Antything For my Madam.."Dariya tayi Tana Kama Hannunshi Suka Haura sama.


 Ita Ta Had'amai Ruwan Wanka ya Shiga yayi Duk yaso Tazo Su Sake Yi Tare Ta Zille Ta Gudu yana Fitowa ya sanya Jallabiya ya jamusu Jama"i Sukayi sallar Mangariba.

daganan ya Shirya Cikin Wasu kananan kaya Riga da Wando White and Blue, Hannunsu Sarke da Juna Suka Sauko Kasa Ma'u Ta Zaunar Dashi kan Daya Daga Ciikin Kujerun da Suka ma Dining din Kwanya Kafin Tafara Zubamai sai da Ta Fara Diban na Baba sa'a Takaimata Kana Tazo Tayi Sarving nashi Wai Ranar Taga Santi Abdallah dama ma'aboci Son Sakwara ne yaci Sosai Hakama Kunun Aya sai da yaji Jikinsa ba Waje Kana Suka Tashi Suka Dawo Falo Ma'u Ta Shiga Dakin Baba Sa'a Suka Fito Tare Ita Tana Dauke Da Aina Ita Kuma Aima Duka Ma"u Ta Mikamai Ita Kuma Baba sa'a Ta Gaisheshi ya amsa Cikin Sakin Fuska kafin Takoma ciki Ta barsu nan Haka Abdallah ke Ta Mamakin Su Aina yadda Sukayi bulbul dasu Wasa ya Fara musu Ita kuma Ma"u sai Ta Maida Hankalinta Wajen Kallo Inda ake Watsa Wani American Film A Mbc action.

basu Tashi ba sai da Lokacin sallar Ishha"i Tayi Ma'u ta karbesu Ta Maida Ma Baba Sa'a Sukuma Suka Koma sama Suka sake alwala Sukayi sallar Daga karshe Sukayi Shafa'i Da Wuturi, Ko addu'a Basu Samu Yi ba Domin Abdallah ya kosa Ya Kasance da Ma'unsa Rumgumeta Yayi yana zame Rigar Dake Jikinta yana Fadi Cikin Wata Murya mai Cike da Kewa Da Muradi."I Want u..."Ya fad'a yana Shafa Chest din Ma'u Wacce Ta Narkemai tana Fadin"Me..too..."Tafad'a Tana yar Kara sanda ya matse mata kumatu.

 Ba'a Kara Jin Duriyarsu ba Sai da Safe Da Ma"u Ta Fito Hada Breakfast Ta Iske Baba Sa'a Afalo Dasu Aina Wadanda Tamusu Wanka Ta gyara su Tsab Cike da Kunya Ma'u ke gaisheta domin jiya Cemata Tayi Bari Tazo Ta Dauki Su Aina,ammh Shuru Itako Baba sa'a Ko ajikinta bazata Hanasu More Rayuwarsu ba 

Agurguje Ma'u Ta hada musu Abun Karyawa Ta Koma Daki Koda Tayi Wanka Ta Shirya Cikin Riga da Sikt din Atamfa,Fita tayi Falon Kasa Ta Dibi Abun Karyawar Baba sa'a ta kaimata Daki Ta Dawo Falo Suna Hira sai dai Fitowar Abdallah kawai Tagani ya Matse Cikin American Suit masu Ruwan Toka,Ya matse Wuyansa da Tie Da Mirmishi yake Kallon Ma'u yana Rike da Briefcase dinsa Ahannunsa sai Wani Key din Mota Ahannunshi.

Mikewa Ma'u Tayi Tana Fadin"Kai Babe ko ka jirani Nazo na samu Ladan Shiryaka.."Bai Mata mgana ba ya Duka yanama Su Aina Waasa Baba sa'a na gaisheshi ya amsa yana Kallon Ma"u Kafin yace"Don't Wrry My Sugarlip Na Huttasheki Muje Na karya Muje Waje I hv a Suprise For U Dear..."Batayi Gardama Ba Ta Mike Ta Riko Hannunshi Suka Nufo Dinning Tazaunar Dashi Tayi Sarving Dinshi Suka Ciyar da Juna Kafin Ya Mike yana goge Bakinshi da Tusseu ya Rikota Kan kujera ta Dauki Mayafinta Suka Fita daga Falon yana Fadin"Komai kika gani Juz Ki Kulle baakinki Sugarlip Kinsan Komai Nawa Naki ne Kamar yadda Nima Nake Naki.."Dariya Tayi Har Suka karisa parking Space Inda ya Umarci Emeka daya Ciro Tamfol din Dake Jikin Wata Mota Matrix, Black colour,Lokaci Daya Abdallah na Damkama Ma'u Key din Motar Ahannunta yana Fadin"gift dinki ne na Zama Dani My Sugar sannan Kinbani Abunda Banyi Zato ba Wato Kids..."Zaro ido Ma'u Tayi kafin Tace"Me...?motar nan yanzu Tawa ce Babe ?

Kai ya gyad'amata yana Dariya ai da Wani Uban Tsalle Ma"u Ta Dane Abdallah Lokaci Daya Tana Fashewa Da Kuka Bayanta Abdallah Ke bugawa Alamar Lallashi Dago Kanta tayi Tana Hawaye Tace"Nagode Nagode Sosai Babe Allah ya Biyaka da Aljannah ka sanya Ma'u tazama Sarauniya Abun Alfaharim Kowa Bani da Bakin Godemaka Nagode ..."Tafada Tana Tsiyayan Kwalla kafin Ta Nufi Motar Tana Shafawa Tana Kukan Dadi Abdallah na Gefe Yana kallonta yana Dariya Ganin Kukan Nata naso yayi yawa ne yasa Ya Rikota yana Fadin"Shiii...Stop Craying kinji..."gyada kai Tayi Tana Share Kwallah Kanta ya Shafa yana Fadin"zan tafi Madam.."peck ta bashi A Kumatu Tana Fadin"Allah ya Tsaremun Mijina Abban Aina da Aima.."Mirmishi yayi kafin yace"Ameen Adorable Wife...Tanque.."dakyar Suka Rabu ya Shiga Mota Emeka yaja Suka Fice Daga Haraban Gidan Tana Daga Musu Hannu.

Da gudu Ta Koma Cikin Falon Tana Kwalama Baba sa'a Kira Tana Fitowa ta Rumgumeta tana Fad'amata Babe ya Siyamata Sabuwar Mota nan Baba sa'a Ta tayata Murna Ranar Ma'u Tayi Tana kiran yan"uwa da abokan Arziki Tana gaya musu Tayi Mota Harda Abba sai da Ta Fadamawa Aisha Ko Data Kirata Tana Fad'amata Ihu Ta saka Harda Tsalle Tana Taya Aminiyar Nata Murnan Samun Cigaban Rayuwa Kowa yaji sai yayi Murna Banda Irinsu Umma da Cutar Hasada Tazame musu Ciwo.


******


BAYAN SHEKARU BIYAR


Shekaru Biyar Da Suka Gabata Abubuwa Dadama Sunfaru Ammh Na Farinciki yafi Na Akasinsa na yawa.


Rayuwa Babu yarda Batayi da Bawa Haka Zalika Hassada gamai Rabo Taki ne,Kuma komai na Duniya yana da Lokaci Da nashi Sanadin Duk Abunda kaga baka Sameshi anan Duniya ba Kai dai ka Mika Bukatanka ga Allah To Tabbas Abun ba Rabonka bane Allah yayi Maka Babban Tanadi Agidan Aljannah.

Ayau ni Asma'u Ladan Shariff Na zama Sawun giwa ta Take Na Rakumi Na Taso Da Rayuwata Cikin wahala Wanda Har Nafara Tunanin Kila Allah ya Manta Danine ammh Sai gashi Da Lokacina yayi Komai ya Fara Cikin Sanadinsa gashi yanzu Nida Gwarzon Mijina mune Bangon da Majinginar Gidanmu Mun zama Shalele Hade Da Yan Lele agaresu,sakamakon yanzu Girma ya Kama Abba Kuma Kasuwar Auduga yanzu ta Rage So ya kasance Nauyi yamai yawa Sosai.

Umma da Hajiya iya Sunga Karshensu Domin Karshenta Hassada Shekaran Data Gabata Abdallah ya kaisu Makka Dukkansu Da Ita da Mama da Anty Amarya da Hajiya iya da Kawuna Da Goggo Jumai sai Hajiya da Maman Fati da Mallam da Ammi da Baban Aisha da Annie,muma mun Je Shekara biyu da Suka Wuce Mu Shida Nida Abdallah da Aisha da Fahad Sai Yusuf da Zainab, Domin yanzu ba Irin Da bane Domin Ashekarun Biyun da Suka gabata ya samu karin Girma Zuwa *C G CONTROLLER GENERAL ABDALLAH MAHMUD AZARE* Wanda yanzu Haka Mun bar Porthercourt Mun Koma Lagos da Zama a Victoria Island

Babu Abunda Zancema Abdallah sai godiya Domin ya Zamemin Mijin Marainiya Babu Abunda baya Bani Duk da Naso ya baarni Na Cigaba da Aiki ammh ya Hanani Ammh Duk Watan Duniya 10k yake Bani bayan Kuma Ya Budemin Wajen Business na Hada da Kudin Sadakin Aure na da Wanda yake Bani Ina Tarawa Na bude Shagon Costimetisc and Boutique na sai da kayan mata Irin Su Dogayen Riguna,Shoe,bag,etc Agarin Kano Wanda na samu Wani yana Kularmin Da Kasuwanci Shiyasa Nafi Karfin Wasu Kananan Kudina,Koda Wata Hidima tataso sai dai Nayi Batare da Sanin Abdallah ba.

 Ayanzu Haka nayi Haihuwata biyu bayansu Su Aina Da Aima na Kara Haihuwan Mazaje Wato Mahmud sai mace mai Suna Aisha,wacce saboda Kaunar da Aisha Ta Nunamin yaasa Nayi Mata Takwara yanzu Aisha kadai Ce agabanmu Wacce Mukema Lakabi Da *AILA* Aina da Aima Suna Gidan Hajiya Domin Kam Duk Sonmu da Su Zauna Wajensu Kakaninsu Sun Kwacesu mahmud Kuma yana Gidan Aisha da Fahad Mum basu Halak malak sakamakon Tun bayan Amir Aisha bata kara samun Wani Cikin ba Shiyasa Muka bata Mahmud yana Zaune Awajenta sai Fati Datake Zaune a hannuna Ta Girma ta Fara Zama Budurwa Muka sakata Mkranta Direba na kaita yana Dawo da Ita .in kuka ganni bazaku ganeni ba saboda yadda na Zama Babbar Mace Kudi Sun Zauna ga Jin Dadi Ayanzu haka Motocina na Hawa Guda Hudu Kuma Mijina ya yarjemin ba Inda bana Shiga da Motata agarin Lagos,Emeka Tun Muna Parthercour Sanda Aka Maido da Abdallah Lagos ya sallameshi Bayan ya bashi Motar Daya Siyama polina Hade Da Gidan Yace Ya Koma garinsu yayi Aure yazo Da matarshi Su Zauna Tare Bayan ya bashi Jari Suka Rabu Cike da Kewa Domin Tabbas Sun Saba Da Juna Sosai,Sai kuma Ya samo Wani Ghali Daga Bauchi Muka Taho Dashi Shida Matarshi Lauratu Yana Tuka Abdallah matarshi Kuma Tana Zaune A Boysquaters Tana Shgowa da Safe da Yamnah Tana Taimakamin Da aiki, Tunda Baba sa'a Jikanta ya samu Aiki Akaduna bayan yayi Aure yazo Ya Dauketa yatafi da Ita Duk Da ma'u bata so ba, Ita kuma Iyayen Wasila sai da Sukayi Shekara Biyu ba lbrin Wasila sai Chan Wani yace ya ganta a Sulaja Tana Hauka Tuburan Ko kafin Aje sai akaji lbrin Wata Babbar Mota Ta takata Tayi Daga Daga da Naman Jikinta ba Wanda Yayi Tuninin Zuwa sai dai Aka Mata Fatan Dacewa Jamila ce Kadai Dataji Tayi Ta Kuka Domin Ta Haihu ta samu Namiji Anas Wanda ya Shekara Hudu Aduniya Kullum TaKalleshi Sai Tayi Tir da Rayuwarta Domin Tana Tunanin In ya girma ya Tambayeta Ina Mahaifinshi Bata da Amsan Da Zata bashi Kai Ginshikin Tarbiya Uwace Da Inda Allah ya baka Uwar Banza Mai Budurwar Zuciya sai Dai Indan Allah yasoka da Shiriya Abdallah Kuma bai Yarda Alhaji Armaya'u ba Shima yana Turamai da Sako akai akai,polina ma Abdallah ya Hadu da Rabeca Inda Take Sanar dashi Tun bayan Wata Hudu da Barin polina porthaercourt Ta Mutu Abdallah yaji Babu Dadi,haka ya Dawo yana Fadamin Nace Allah ya kyauta.

Sannan kullum cikin Istigifari yake yi da neman gafara Allah yana tunanin kada Laifinsa watarana ya shafi ya'yansa da yake ji dasu matuka.

Kuma yasan zina ba shi ce ammh ya na Fatan tubansa ga Ubangiji da Halin da wasila ta jefasa ya zame masa mizani akan haka.


Abangarem Gidanmu Kuwa Tuni Umma Taga Ishara Allah ya Nuna mata Iyakarta Duka ya'yanta Guda Uku aka sakomata Lokaci Daya Anty Bilki Mijinta sai da yamata Dukan Tsiya ya Koreta kan ya Kara Aure Ta Mari Amaryarshi Ita Kuma yana Dawowa Tahada Karya da gaskiya Shiko ya Mata na Jaki ya Koreta Da Saki Daya Ita Kuma Anty Rukayyah Mijinta ya Saketa ne saboda Halinta na Gulma da Munafunci Anguwa gabadaya Zundenshi Akeyi Saboda Gulmar Datake Hadawa Agari Shima yagaji ya sakota sai Rabi'a Wacce Itama Wata Ta kwacemata miji Tunkafin Aure ya sakota Kuma Kowacce Da Uban ya'yanta Suka Dawo Gabam Umma Suka Jabe gashi yanzu Abba Ba Irin Da bane Babu Abun Duniya.

kuma daman yace Shi ba Wanda zai Kira Don Su Anty Rukayyah basu Darajashi ba Shiyasa Suma Mazajen nasu basu Kallonshi Da Mutunci,Hajiya iya Dake Goyon bayanta Itama Ta Dawo Rakiyarta Ta Fahimci Duka Daya Ne Kuma Dan Hakin Daka Raina Shike Tsolemaka ido Gashi yau Taje ta Sauke Farali Dalilina banda Kayan Abincin da Abdallah ke aiko dashi Duk Wata da Kudi Daga Bauchi ake kawowa Ta hannun Mallam Suma Suna Cikin Kwanciyar Hankali Domin Abdallah Shine Komai Su Anty Safina ba Wacce Bata Zauna da Kafarta ba Kowaccensu yabasu Jari Suna Kasuwanci Hadda Anty Zainab Wad'anda Suma Yusuf ya samu Karin Girma Suna Birnin Tarayyah Abuja Suna zamansu Lafiya.

Ummah Tayi Kuka kamar Ranta Zai Fita yau ga ya'yan Datake Fariya Akansu Sunyi Aure Gasu An sakomatasu Bata da yarda da Zatayi Kuma ta yarda Hakkin Ma'u ne Ke Bibiyarta Kullum Cikin Kuka Take da Nadamar Abunda Ta Aikata garemu Ni bansan Abunda Ke Faruwa ba sai da Jikin Abbaa yayi Zafi yana Fama da Ciwon Sugar kana Mukazo Gida Nida Abdallah Aiala da Fati Daga Bauchi muka Fara Sauka agidanmu bayan Abdallah ya Siya nashi Kato Mun Koma muna Sauka indan Munzo sai bayan Mun Huta muka zo Dutse,Sai da na Shiga Gaida Umman ne Nagasu Anty Rukayyah Tun Kafin Ma na Tambaynta tafara gayamin Tana Kuka Anan Take Neman gafarata Tana Fadin Ita Ta Dingamin Asiri Tana lalata Aurena banyi Mamaki ba Illah na Cemata na Yafe mata nasan Ko a Haka Allah ya Barta Taga sakayyah.

Abdallah naje Nama mgana nace Ya Taimaka, Shine ya shigo Har Cikin Gida yayi Mgana da Umma yaba Kowacce 20k su Fara saana Kuma Su Mazajen nasu Ya karbi Nombar Wayarsu yace Zaiyi Mgana Dasu Umma da ya'yanta Kamar su Kwantamin Saboda Godiya Dama Haka Rayuwa Ta Gada Gashi Ni da Mamata Mun zama Abun Tinkahonsu

Abba Kuwa Wani private Hospital muka kaishi Aka bashi Gado Ana kula Dashi Abdallah ya Biya Komai Kafin Mu Tafi Mun koma Bauchi da Kwana Daya aka sallami Abba Ya Koma gida yaji Sauki Albarka ko munshata Abakin Abba Nida Abdallah,Muna Komawa Lagos Da Sati Daya Umma Ta Kirani Tana Kuka akan Nama Abdallah Godiya Ya Tallafin Rayuwarta Data ya'yanta Harda Mazajensu Ashe bayan ya karbi Nombobinsu Kiransu yayi Yace Kowannensu ya TuroAccout Nombarshi ya Tura musu kudade yace Su Kara jari Kuma yayi Musu Nasiha Su Maida Matansu Basu Watsamai Kasa A Idoba Kowacce Mijinta yazo ya Dauketa Bayan Yabada Hakuri Ganin Haka yasa na Bama Fa'iza Nima 30k da Kudina Domin Wahalar da Abdallah Keyi da yan'uwana dani Kaina bashi da iyaka Addu"ana Nake mai Allah ya Hadamu Dani dashi a Aljannah Firdausi.


********

Ina Bedroom Ina Shirin Barci Abdallah na Chan Na Jirana Wata

Arniyar Rigar Barci Na saka mai Kama da Naked Mai Raga Raga ne, Turare na Dinga ma kaina Bari Dashi,bayan Ta Tufke gashina da Band Nasaka Silafas Dina na Tafi Dakin Abdallah ammh sai da Na Leka dakin Fati na Iske Suna Kallon Cartoon Ita da Aaila,Direct na Wuce Bedroom Dinshi Da Sanda Na Tura Kofar yana Zaune atsakiyar gadonshi Jikinshi ba Riga sai Wani Bakin Three quater dake Jikinsa Fuskarsa sanye da Wani Farin Glass Laptop dinsa ne agabansa yana Ta Faman Aiki yabama Kofa baya.

Lallabawa Na Dingayi Har Na isa Gareshi na Hau gadon Ta saka Hannu Na Rumgumeshi Ta baya,Ajiyar Zuciya ya sauke Kafin yace"Sugarlip....umh.....Sai yanzu Ko Ni nayi Fushi.."yafada Yana Turo Baki,vDariya nayi na Sako Kaina na Kwantar a kan laptop din ina Fadin"Na tsaya Shiryama ka kaina nefa Babe.."Tafada Ina Matse Bakinsa,Jagale yayi yana Kallona Kafin ya Jaye Laptop din Chan Gefe bayan ya Kasheta gabadaya ya Dagoni dakyau na zauna Akan Cinyarsa glass din Idonsa ya Cire Yana bina Da Wani mayen Kallo.

Lumshe ido Nayi Kafin na Dora kaina Bisa kafadanshi Shi Kuma ya sanya Duka Hannuwanshi ya Zagayo Kuguna dashi yana Dad'a kankameni,Ajiyar Zuciya Na Sauke Ina Fadin" A Words can Never Express How Lucky Am to hv u Babe...ka Wahala dani Ka Wahala da iyeyena da yan'uwana,Bani da Abunda Zan Biyaka sai dai Nayi Ta Fatan Allah ya Albarkaci Rayuwarka Data ya'yanka Hade Data Iyayenka Madallah da Samun Miji Irinka Jajirtattacen Kuma..."Ya katseta lokaci d'aya ya na Matseta har sai Da Tayi yar Kara Tana Tura baki Kafin ya Sausauta Rikon Dayayi Mata Dago da Kanta Tayi Hawaye Sun Cika idonta Tana Fadin"In namaka godiya kace Bakaso Meka ke so Nayi Maka ni Kuwa Awannnan Duniyar...? 

Tafada Hawayenta Suna gangarowa Mirmishi yayi kafin ya sanya Harshe yana Lashe Hawayenta sai da ya Tsotse Tas kana ya Dago yana kallonta Cikin Kwayan Idanuwanta yace"Babu Abunda Nake Bukata Sugarlip irin Ki Zauna dani! Ki rayu Dani...! Kuma ki Mutu Dani..! Kece Rayuwar Abdallah Kece Farincikin Abdallah Dalilinki Abdallah yazama Haka So Kisa Aranki da *ABDALLAH MAHMUD AZARE* da Dukiyarsa gabadaya Suna karkashin ikonki ne *MRS ABDALLAH MAHMUD AZARE*...."yafada Cikin Bege da So Mai Tsanani.

Lumshe ido Tayi Kafin Ta Bude Tana Fadin"Shi kadai Ka keso...? Ya Gyada mata kai batayi Wata Wata ba Ta Dora Harshensa Kan Bakinshi Tafara Sumbatarshi Sai da Ta mai Sumba mai Tsawo Cike da Kwarewa kafin tace" _Zan zauna dakai. Kuma Zan Mutu Dakai Abadan Dani Dakai Zo mu zauna.._ Tafad'a Tana Kara Kamkameshi Shima Riketa yayi Dakyau kafin ya Maida akalan Wasan Ahannunshi Cikin Lokaci Kadan lbrin ya sauya salo Suka Rikita Junansu da Zafafan Soyayyarsu Mai Tsayawa Azuciyar Wanda Ke Muradi.


ALHAMDULILLAH...ALHAMDULILLAH....ALHAMDULILLAH...


Alhamdulillah Allah na godemaka Godiyata Tabbata ga Allah (SWA),Domin da Ikonshi Komai ke Faruwa,kana Salati da Aminci Su Tabbata ga Shugaban Halittun Duniya Annabi Muhammed (SAW), domin da Ikonshi ne Ayau na kamallah Wannan Littafin nawa Mai Suna ZAMAN GIDANMU,ina Fatan Abunda Na Rubuta Daidai Allah Yabani Ladanshi Kuskuren Danayi Allah ka yafemin Saboda Dan Adam Tara Yake Bai Cika Goma ba.







*Janafty*