Makauniyar sharia

Chapter 5

by @kyautadagaallah10

*Makauniyar Shari'a*

_Sai a Lahira_


NA


_*IKILIMA ADAM

_( kyauta daga Allah)



***)


SHAFI NA BIYAR


Cikin tsananin mamaki take kallon Matar da ta bata magani tasha a Kauyen Daguzau , lumshe idanunta tayi , sannan ta kara bude su ahankali , stil dai itadin dai take gani da murmushi akan fuskarta.


Bude murfin motar matar tayi ta fito cikin shigarta na doguwar riga habaya baki mai adon tsone tayi ronlin kanta da bakin gyale. Numfashi ta fesar cikin rawar murya da zallan mamaki ta ce , " Amatullah kece anan gun wa kukazo anan Garin ? ." shiru tayi tana sauraren amsar daga bakin Amatullah da ta tsura mata idanu.


Amatullah dukar da kanta kasa tayi , idanunta na kallon kasar dake kasa , sannan ta kallon gefen titi yanda motoci ke safa da marwa , kamar ba za tayi magana ba ta ce , " yau mu kazo kuma anjima zamu koma , zan tafi inda aka aikeni." tayi maganar tana kokarin wuce ta .


Jin an kamo hannunta yasa ta saurin waigowa suna face din juna , ahanzarce ta sauke idanunta akasa , gabanta tsananta bugawa ya keyi gab-gab da karfin tsiya .


Tsinkayar muryan Matar tayi tana fadin " Meyasa kike tsorona , naga haduwarmu ta farko haka ki kayi , ko nayi miki kama da muguwa ne ".


Saurin Girgiza kai Amatullah tayi alamun ba haka bane . Cikin rashin son magana kamar an mata dole tafara fadin " Hajiya kiyi hakuri , kawai ban damu da yawan magana bane , kuma nagode da kulawarki gareni aranar farko , kamar yanda nace miki munzo ne yau zamu kuma hakanne babu karya ." tana kai karshen zancen ta gimtse bakinta tayi shiru.


Matar kallonta take tare saka hannu cikin jakarta zaro wayarta tayi tare da duba time , kana takara maida shi acikin jaka , again idanunta yana kan Amatullah wacce take karewa kallo tun daga sama har kasa , dan yau ta ganta cikin sutura ta mutunci ba kamar haduwarsu ta farko ba .


" Daman kunada yan uwa a ghetto ne ? ." ta jefo mata tambaya tana kara tsura mata idanu.


Amatullah kalmar ghetto sosai ya shige cikin kunnenta , cikin zuciyarta take maimaita daman sunan unguwar da muke zaune ghetto , tsoron kada Matar tagane karya take mata ne yasa ta fadin " Nima bansan munada yan uwaba saida Papy ya kawoni nan kuma kinga anjima kadan zamu bar garin nan ". tana kai karshen zancen ta fara kokarin barin wajen .

Daga sama taji muryan Matar tana fadin " Amatullah kai ni in gaishe da Papynki ".

Firgit ta waigo kamar saukar aradu taji maganar ta doki dodon kunnenta . Shiga duniyar tunani tayi tuno da lokacin da hirarsu da Papy inda yake fada mata kada ta kuskura ta kawo wani ko wata da sunan azo gansa ko ataimaka musu in tayi gangancin yin haka , zata rasa shi na har abada , wani gumi me zafi ne ya fara karyo mata a fuskarta . Murya na rawa ta ce" , Papy ya je kasuwa baya nan , kuma sauri nake kada ace na dade bandawo ba ." bata jira cewar ta ba ta diba aguje tana gudu tana waige waige.

Da zallan Mamaki Matar take kallonta har ta bace mata da gani , ta dade nan tsaye tana ta jiran ganin dawowarta. Abin da bata luraba shine , Amatullah ta labe c'en gefe daya tana kallonta.


Ganin kamar ba dawowa zatayi ba , hakanan ta hakura tashige motarta tayi tafiyar ta


Amatullah ganin ta tafi ne yasa ta fara sauke boyyayen ajiyar zuciya. sannan ta samu wuri ta dan zauna tana hutawa , kusan mintina talatin ta dauka kafin taci gaba da tafiyarta tana yi tana waiwaye adon tafiya kada matar nan tana bayanta. Daidai kusan masu siyar da lemun zaki ta karaso , har gaban me saida lemun ta tsaya , shikuwa yana ganinta a hanzarce ya karaso tare da tambayar me take bukata, itakuwa nan da nan ta kankance murya cikin roko da magiya ta ce " Don Allah kabani sadaka ko da ta abincine , wallahi bamu da abinda zamu ci ". takai karshen zance tareda yin kasa da kanta , duk firar da suke wani matashin saurayi da baze wuce shekaru talatin ba yana kallonsu daga c'en gefe abin shisha ne agabansa yana zuka sai tada hayaki ya keyi a gabansa.


Me saida lemun ,abun fifita ya dauka yana korar kuda da suka cika mishi farantin lemu , kana ya kara kallonta da jajayen idanunsa kamar gauta , bakinsa mai dauke da dattin haƙora ya bude yafara magana.


" Kin san dai bazan baki sadaka ba , bayan ni baki bani komai ba , in kina son kudi , kinga dakina anan kusa yake sai in kwatanta miki kije c'en ki jirani , Kinga har dubu daya ma zan iya baki yanda kike me kyaun din nan ". ya karashe zancen yana washe mata haƙora .

Duk da bata fahimci me yake nufi amma tabbas tasan , inda abun arzikine baze ce ta je dakinsa ba , cunno baki gaba tayi tare da fadin " anan zaka ban abin da zaka ban in kuma babu kacemin na tafiya ta kawai basai kasa nayi tafiyar wahala ba". ta karashe zancen cikin tsiwar da bata san ta iya.


Kokarin yin magana yake ya ji an nausa masa wawan mari a fuskarsa , cikin razana yake kallon *Karfin Iko* hannunsa rike da kuncinsa ya ce , " me nayi maka ne ?." yakai karshen zancen cikin tsananin tsoro da fargaba , da baya baya ya fara yi domin kauce masa.


Amatullah tunda Karfin Iko ya yi mari rintse idanunta tayi ji take kamar ita ce , ze kai wa mari sakamakon yanda taga jijiyoyin hannayen sa murmudaddu su ka mike . Khausassen Muryan Karfin Iko ne ya katse mata tunaninta jin yana fadin " Kai banda dan iska ne , iskancin naka harda yan Yara matasa wannan Yarinyar duka nawa take da kake son yin lalata da ita akan abinci". ya karashe zancen cikin daga babban muryansa .


Jama'ar dake wajen sosai suka shiga fadin " Amma kai dai Hamisu mai lemu ba zaka iya canza halinka ba . Wani gurgu dake kan keken guragu karasowa wajen ya yi tare da soma zagin Hamisu mai lemu , hakuri ya shiga bawa Karfin Iko yasan sarai yanzu sai yahau dukan mai lemu inda dakyar zasu iya kwatarshi .

Karfin Iko huci yake sama- sama kana ya dawo da kallonsa kan Amatullah da ta rintse idanunta dan tsananin tsoro da fargaba , ahankali ta fara yunkurin bude idanunta ,tana budewa idanunsu suka tsarke cikin na juna ita da Karfin Iko , aguje ta sake rufe idanunta. Sautin muryansa ta ji yana fadin " Yan mata kamar nawa kike bukata kudin cin abincinku? ". ya yi shiru yana busa sigari kamar ba shi ya yi magana ba. Gurgu dake kan kekensa , cikin tausayawa ya ce , " Yan mata Karfin Iko yana magana ba a kyaleshi babu amsa kinji ko ." gyada masa kai tayi ba tare da ta kalleshi ba , shikuwa Gurgu da sauran jama'ar dake kallon abinda ya faru duk sun koma mazauninsu suna Allah wadai da halin mai lemu , Hamisu mai Lemu zama ya yi rike da kuncinsa yana satar kallonsu.


Ganin ba za tayi magana ba yasa Karfin Iko zaro dubu goma daga Aljihun wandonsa , kamo hannunta yayi ya saka mata a hannu cikin yin kasa da murya ya ce , " ni yayanki ne , dan haka da kinzo nan wajen , in baki ganni ba kice a nuna miki Karfin Iko duk inda nake zasu nemo ni kinji ko ?." gyada masa kai tayi ba tare da ta dago kanta ba. Shikuwa sata gaba yayi tare da mata rakiya saida ya tabbatar ta fice sannan ya dawowarsa.


Itakuwa tafiya take cikin sauri saurinta tana tafiya tana waige waige , saida ta kusa hanyar Gidan nasu sannan ta daidaita nutsuwarta direct wani shago ta nufa , inda anan ne ta samu tasiye gawayi da kayan abincinsu na kwana biyu , nan take dubu goman yakare Nigeria ana fama da tsadar Rayuwa . Harda ledan pure water tasai musu tana jin dadi yau zata sha ruwan pure water dan a kundin tarihin rayuwarta sau daya ta taba sha tun awannan kauyen da wata mata ta sai mata hade da magani sai yanzu da zata kara sha . tana isa Gidan iske Papy tayi zaune ya tasa Rediyo agabansa , ganinta yasa ya sakar mata murmushi ganin yanda ta shigo da kayan abinci alamun yau zasu ci su koshi . nan ta zayyana masa duk abinda yafaru tun daga kan matar data tsaida ita akan titi har kalaman mai lemu da taimakon da Karfin Iko ya yi mata. Papy kuwa maimakon yayi murmushi sai taga ya rintse idanunsa yana girgiza kansa alamun tarin damuwa , cikin sassaita nutsuwarsa ya ce " Amatullah karki bari wani yazo inda muke kinji harsai inni da kaina na baki izini , ko kinason ki rasani ne ?". Ahanzarce ta girgiza kai alamun a'a .


" to kada ki sake yarda ki kula wannan Matar tunda har takeson sai taga Papynki , sannan kuma duk Namijin da zece kuje dakinsa yabaki kudi ko wani abu kada kiyarda dashi kice bakyaso kin Yarda?." nan ma gyada masa kai tayi .


Murmushi ya sakar mata yana mai jin nutsuwa tattare da ita tare da shafa kanta yana mata addu'a . Cikin jin dadi Amatullah ta fara kokarin yi masu Girki duk da ba iyawa tayi ba Papy ke koya mata yanda ake girkin.


*Unguwar Asokoro*


Ridwan Zaune a office dinsa shi da Mansur suna shawara akan sabbin ma'aikata da zasu dauka , wayarsa ce ta fara ruri yana dubawa yaga Anisa ce , be bata lokaci ba wajen daga wayar , daga cen bangaren ta ce , " Yaya Rid , Mamy ta ce , kaba drever izini yakaita asibiti bata jin dadi , kuma tace babu kudi ahannunta ".


" zan kira shi , kudi kuma saina dawo ai nasan akwai ragowar kudade a hannunta , ko tana nufin har sun kare ne ? ".

A zafafe Mamy ta Karɓe wayar daga hannun Anisa cikin tsananin bacin rai ta ce , " Ridwan har ni zaka ringa fadin maganganun akaina kullum kaine kyautar Gida da mota da kudade kai ne bada zakka , wajen bada taimako kullum kaine sahun gaba , Amma Rid.......".

" Dakata". shine farkon kalmar da ya samu damar fitowa daga bakinsa .

" Mamy shin k..............


Makauniyar Shari'a taku ce .

Domin son magana dani ***



Share and comment pls